Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (1)
NA
ABDURRAHMAN LAWALI
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan aiki ga mahaifana, Alhaji Lawali Jamalu Rawayya da
Hajiya Hassi ‘Yan dotondaji da kuma abokina Jafar Usman Badarawa.
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki Mai kowa Mai komai, tsira da amincin Allah su tabbata ga
shugaban talikai kuma cikamakon Annabawa, Annabi Muhammad (S.A.W). Cikin ikon
Allah da yardarSa da amincewarSa Ya ba ni ikon kammala wannan aikin bincike,
domin samun takardar shaidar kammala digiri na farko a sashen koyar da harsuna
da al’adu, a Jami’ar tarayya Gusau, jihar Zamfara.
Bayan haka, ina miƙa godiyata ga mahaifana a kan ɗawainiyar da suka yi da ni tun yarantata har zuwa wannan lokaci da na kammala karatun digirin farko. Allah Ya saka
masu da mafificin alherinSa. Haka kuma ina mai nuna godiyata da farin cikina ga
malamina wanda ya yi ɗawainiyar duba mani wannan aiki, watau Malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi bisa umurni da
shawarwari da ya bayar, Farfesa Balarabe Abdullahi kan irin taimako da
shawarwari da ya bayar don ganin na samu nasarar kammala wannan bincike. Allah
ya saka masu da mafificin alherinSa.
Har wa yau, Ina miƙa godiya ta musamman ga malamaina Malam Musa Abdullahi Zariya, da Malam
Adamu Ibrahim Malumfashi, da Malam Isah S. Fada a kan irin taimako da
shawarwari da suka ba ni, domin ganin wannan aiki ya kammala. Allah Ubangiji Ya
saka masu da Aljannar Firdausi. Sauran malaman da ba a ambaci sunayensu ba
saboda ƙarancin lokaci, ina yi masu godiya bisa taimakon da suka ba da domin cimma
nasarar kammala wannan aiki. Har wa yau ina miƙa godiya ta musamman ga Shugaban
Sashe, Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, da Farfesa Magaji Tsoho Yakawada, da Dr
Yakubu Aliyu Gobir da Dr. Abdullahi S. Gulbi da sauran malaman da suka koyar da
ni har na kai ga samun nasarar kammala karatuna. Allah Ya saka masu da
alherinSa.
Godiya ta musamman ga yayannina Basira Lawal da kuma Bela’u Lawal da ƙannaina Bashar Lawali da
Habiba Lawali bisa shawarwari da ɗawainiyar da suka yi da ni har zuwa kammalar wannan karatu nawa.
Bayan haka, ina miƙa godiyata ga abokan da na yi karatu da su kamar su Jafar Usman, da
Shafa’atu Salihu Labbo, da Bashiru Haruna, da Aminu Murtala, da Umar Yahaya
Dogara, da Bilya Umar, da Sadiya Kabir Sama’ila Aliyu, da Mukhtar Muhammad da sauransu,waɗan da lokaci bai ba da damar lissafawa ba. Allah Ubangiji
Ya sakawa kowa da alherinSa, Ya sa Aljannar Firdausi ta zama makoma a garemu
baki ɗaya.
Ba zan manta da Yunusa Aliyu Guraguri ba, wanda ya ɗauki lokaci dare da rana wajen buga wannan aiki cikin
na’ura mai ƙwaƙwalwa da kuma sauran mutanen da suka ba da tasu gudunmuwa ta kuɗi ko ta kayan aiki. Ina fatar Allah ya yi wa kowa
sakamako na alhairi, ya kuma sa wannan aiki ya zama jagora ga duk wani mai
bincike ko nazarin tarihin Maguzawan Kwatarkwashi amin.
Ƙarshe ina miƙa godiya ta musamman ga
malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi bisa ga ɓata lokacinsa da ya yi wajen dubawa da kuma gyare – gyare da ya yi na
wannan aiki. Allah ya saka masa da alhairinsa, ya albarkanci zuri’arsa amin.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.