Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (2)

NA

ABDURRAHMAN LAWALI

Tsafe-tsafe 

BABI NA ƊAYA

SHIMFIƊA

1.0 GABATARWA

Da sunan Allah mai rahama, mai jinƙai. Allah ya dada tsira ga Annabi Muhammadu (S.A.W). Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da ya halicci al’umma daban – daban.

Al’ummar Maguzawa, al’umma ce, mai matuƙar muhimmanci dangane da nazarin al’adun Hausawa. Domin kuwa wasu na da ra’ayin cewa duk Bahaushe, asalinsa Bamaguje ne. Kasancewar su Maguzawa ba su da wani harshe sai Hausa.Don haka idan ana magana a kan al’adun Hausawa, to yana da kyau a yi nazari a kan al’adun Maguzawa. Wannan ne ya sa nake ƙoƙarin yin bincike a kan Maguzawan Kwatarkwashi, domin neman takardar kammala karatun digiri na farko.

A cikin wannan aiki nawa mai taken “Tsafe-tsafen Maguzawa: Nazari a kan bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi”. Na yi ƙoƙarin fito da yadda su Maguzawan na Kwatarkwashi ke aiwatar da tsafe-tsafe a lokacin bukukuwansu da suka danganci Aure, Haihuwa, Kaciya, da kuma Mutuwa. Don haka, na kasa wannan kundi nawa zuwa babi biyar, kuma kowane babi yana ɗauke da bayanai na wasu abubuwan kamar yadda mai bincike ko karatu zai iya gani.

A cikin babi na ɗaya an duba abubuwa kamar haka:

  1. Gabatarwa
  2. Manufar bincike.
  3. Dalilin bincike.
  4. Farfajiyar bincike.
  5. Dabarun bincike.
  6. Hujjar ci gaba da bincike.
  7. Bitar ayyukan da suka gabata.
  8. Naɗewa.

A babi na biyu kuma za a yi bayani a kan Maguzawa, kamar haka:

  1. Ma’anar Maguzanci
  2. Ma’anar Maguzawa.
  3. Su wane ne Maguzawan Kwatarkwashi? Duk a cikin babin sai kuma daga ƙarshe na naɗe wannan babi da taƙaitaccen bayanin abin da  babin ya ƙunsa.

A babi na uku, a ciki za a feɗe biri har wutsiya dangane da wannan aiki. Domin nan ne ƙashin bayan aikin yake. A nan za a fito da ma’anar tsafi shi kansa, sannan ma’anar buki, da tsafe – tsafe a bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi.A ƙarƙashin waɗannan bukukuwa, za a kalli tsafi a bukin Aure, tsafi a bukin Haihuwa, tsafi a bukin Kaciya, da kuma uwa-uba tsafi a bukin Mutuwa, duka  daga Maguzawan Kwatarkwashi da kuma naɗewa.

Babi na hudu shi ne babin da ke ɗauke da bayanin al’adun bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi.

Sai kuma babi na biyar wanda ya yi bayanin kammalawa, sakamakon bincike da manazarta.

1.1 MANUFAR BlNCIKE

Kamar yadda aka sani cewa, duk wani abu na rayuwar yau da kullun, yana da matuƙar amfani, ko da kaɗan ne. A takaice, ba tare da wani dogon zance ba, kasancewar zaɓen fanni na “Tsafe – tsafe a bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi” don gudanar da wannan bincike akwai abubuwa muhimmai da ake bukatar a fito da su. Kamar abin da ya shafi harakokin rayuwarsu a cikin al’ummarsu, da kuma dangantakarsu da sauran al’umma. Wannan bincike abu ne da zai ilmantar ko kuma shi kanshi wani fannin ilmi ne da za a yi amfani da shi, musamman ta fuskar bincike, kamar masu nazari a makarantu daban – daban.

Bayan haka kuma, gudanar da wannan bincike abu ne muhimmi domin zai kasance abu mai fa’ida ga kowa musamman waɗan da ake sa ran za su duba shi domin amfani da shi ta fanni daban – daban. Kuma zai zamo wani fanni na nazarin wasu al’adun al’umma a cikin al’ummar Hausawa. Haka kuma wannan bincike zai kasance ma’adanin tarihin rayuwar waɗancan al’ummomi. Haka kuma zai ilmantar da ɗalibai musamman masu nazari a kan al’adun Hausawa.

1.2 DALILIN BINCIKE

            Dalilin wannan bincike shi ne domin gano yadda su Maguzawa ke gudanar da bukukuwansu da irin yadda suka kasance suna gudanar da al’adunsu, da zamantakewarsu a wancan zamanin. Wannan bincike da na yi zai taimaka wa ɗalibbai masu karatun harshen Hausa domin sanin al’adun Hausawa waɗanda suka gabata.

1.3 FARFAJIYAR BINCIKE

Domin samun nasarar wanann bincike dole ne a keɓe shi zuwa ga wani muhalli, wato yankin Kwatarkwashi a Jihar Zamfara. Duk da yake ana samun wasu Maguzawa a wasu wurare daban da na Kwatarkwashi a kasar Hausa, wanda ni ban doshi can ba. Na taƙaita kan yankin Kwatarkwashi kawai. A cikin kowane aikin bincike akan keɓe shi ga muhallin da ake son a yi nazari a kansa. A bisa waɗannan dalilai aka ga ya dace a keɓe wannan bincike a Ƙasar Kwatarkwashi kamar yadda aka gani a taken binciken.

Duk wani nazari da za a yi a wannan binciken, ya keɓanta ne kawai ga yadda ake gudanar da tsafe – tsafe a bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi. Domin fito da wata al’ada da ta keɓanci wani yanki na al’ummar Hausawa domin ganin yadda suka ɗauki wannan al’ada da matukar muhimmanci har ya kai suna aiwatar da wasu tsafe – tsafe a lokacin da suka keɓe domin aiwatar da wannan al’ada.

1.4 DUBARUN BINCIKE

Kamar yadda muka sani, samun nasarar kammala wannan aiki zan bi hanyoyi daban – daban wajen tattaro bayanai don samun nasarar kammala wannan bincike nawa. Haka kuma zan bi wasu hanyoyi da suka dace wajen gudanar da wannan binciken waɗan da suka haɗa da ziyarar wurare daban – daban da zan iya samun duk wani bayani da zai taimakawa binciken. Misali

Zan ziyarci ɗakunan karatu don karanta littattafai da wasu masana suka wallafa waɗan da za su taimaka mani ƙwarai da gaske, tare da nazarin waɗansu kundayen bincike na wasu dalibai da suka gabata masu alaƙa da wannan aiki.

Kuma zan yi ƙoƙarin tattaunawa da wasu tsofaffi waɗan da suna daga cikin Maguzawan, tare da ziyarar inda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, da kuma irin al’adunsu na tsafe – tsafe.Domin ganar wa ido yadda suke gudanar da wannan rayuwa ta al’adar tsafe – tsafe kamar:

  1. Gidan Zalla
  2. Kwatta (shi Sarki)
  3. Dashi
  4. Gulubba
  5. Madaci

Wannan shi zai ba ni damar gano haƙiƙanin gaskiyar yadda tsafe – tsafen ke gudana, kuma ya taimaka man wajen samun bayanai kai tsaye. A cikin mutanen da zan tattauna da su akwai waɗanda suka gudanar da wannan rayuwa a wancan lokacin.

1.5 HUJJAR Cl GABA DA BlNCIKE

Dukkan wani aiki da aka gabatar ko kuma aka so a gabatar, akwai dalilai ko hujjoji da suka jawo hankalin mai bincike ya kafa hujja da za ta ba shi dama ya ci gaba da wannan bincike.

Don haka wannan aiki na bincike a kan Maguzawan Kwatarkwashi da na ke so na gabatar ina da hujjojin da na dogara a kansu na yin wannan bincike.

A bisa dalilan da muka ambata a cikin ayukan da suka gabata na ga ya dace, ka da a riƙa yin tuya ana mantawa da albasa, wato na ci gaba da rubuce – rubuce a kan tsafe-tsafe a bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi. Koda yake wasu sun yi nazari a kan wannan ɓangaren, amma ba su yi cikakken bayani ba game da wasu al’adun Maguzawan Kwatarkwashi. Wannan ya ba ni hujjar cewa in zurfafa bincike a kan fannin da ake magana a kan al’adun waɗannan mutane.

Ganin irin muhimmancin da ke cikin wannan bincike ya sa na yi ƙoƙarin gabatar da shi domin na bayanmu da ke tafe waɗan da ba su da wata masaniya a kan tsafe – tsafe a bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi su san wani abu a kan al’adun Maguzawan Kwatarkwashi. Wato har su samu damar ƙara bincike daga in da na tsaya.

Domin wannan shi zai taimaka musu wajen neman wani ƙarin bayani dangane da tsafe – tsafe a bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi, sannan su san wani abu dangane da tsafe – tsafen Maguzawan.

1.6 BITAR AYUKKAN DA SUKA GABATA

A cikin wannan babi wato bitar ayukkan da suka gabata haƙiƙa na  ci karo da ra’ayoyi daban – daban na masana, da kuma manazarta har  ma da malamai da kuma ɗalibai duk ba a bar su a baya ba. Domin sun yi  ayukka masu dangantaka da wannan aiki, wato a kan Maguzanci da Maguzawa da kuma tsafi. Wasu daga cikin ayukkan da suka gabata da muka ci karo da su sun hada da:

Bunza A. M. (2006) a cikin littafinsa mai suna “Gadon feɗe al’ada,” a cikin babi na biyu, ya yi cikakken bayani a kan abin da ake nufi da tsafi, sannan kuma ya kawo abubuwan da ake amfani da su wajen tsafi, kuma ya bayyana rabe-raben tsafi da yadda ake tsafi, domin samun waraka ko kuma buwaya.Sannan kuma a ƙarshen babin ya kawo tsafi a rayuwar Bahaushe ta yau.

Sarkin Sudan I. A. (2008) a cikin wata maƙala da ya gabatar mai taken “Maguzawa” a sashen nazarin Harsunun Naijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, ya kawo asalin kalmar Maguzawa da kuma ma’anar ita kanta kalmar Maguzanci. Duk dai a cikin wannan maƙala, ya bayyana muhallin Maguzawa, wato wuraren da ake samun Maguzawa a ƙasar Hausa, da kuma tarihinsu. Bugu da ƙari, ya bayyana rayuwar Maguzawa, ma’ana yadda mutane ke kallonsu. Sannan ya bayyana suturar da Maguzawa kan yi amfani da ita. Daga ƙarshe ya kawo ire-ircn sana’oin da Maguzawa kan yi, domin samun abin da za su biya ma kansu buƙatu na yau da kullum.

Sarkin Sudan I. A. (2008) a cikin wata maƙala da ya gabatar mai taken “Tsafe-tsafen Maguzawa da suka shafi Aure da Haihuwa” a sashen nazarin harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman Danfodiyo sakkwato, ya kawo ma’anar kalmar tsafi da kuma aure a cikin bayaninsa. Har wa yau ya kawo magungunan farin jini da na neman aure, bai tsaya nan ba ya ƙara da cewa a al’adar Maguzawa tare da al’adun tsafi tafe suke wuri ɗaya. Daga ƙarshe kuma ya yi bayani a kan Maguzawan da suka yi fice wajen gudanar da al’adun tsafe – tsafe kamar irin su ɓacewar jinjiri, da tabbatar da iyaycn jinjiri da kuma tsagar gado, domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Al – Hassan H. da wasu (1982) a cikin Littafinsu mai sunu “Zaman Hausawa" Sun taɓo duniyar Hausawa tare da bayanai a kan aure da kuma haihuwa, da tarbiya, da sana’o’in gargajiya, da sarauta, da kuma muƙamai waɗan da ke zagaye da masarauta. Illa dai suna magana game da duniyar Hausawa amma ko kaɗan ba su tabo imanin Bahaushe ba wanda ya gada daga uwaye da kakanni kafin addinin Musulunci ya kawo gare su. Mun sani cewa Hausawa suna da hanyoyin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum a duniyarsu, idan ko za a yi maganar abin da ya shafe su a gargajiyance, ya zama dole a taɓo hanyar ibadarsu, wato tsafi. Amma su babu inda suka taɓo ɓangaren sa.

Madawaki I. da wasu (I968) A littafinsu na “Hausa Customs”, Waɗan nan masana sun tsunduma ne cikin binciken al’adar Bahaushe tun daga haihuwarsa zuwa mutuwa.Sun yi bayanai dangane da bukin suna, da kuma bukin aure, da sakin mata (Rabuwar aure). Suma waɗannan marubuta sun ƙara bayani game da bukukuwan Hausawa. Misalin waɗannan bukukuwansu ne bukin mutuwa, da bukukuwan da ake yi a cikin shekara kamar na sallah da na shara. Amma duk bayanan da suka yi sun yi ƙoƙarin bayyana al’adar Hausawa, ba su yi wani bayani ba game da tsafi da al’ummar Hausawa suka gudanar ba, balle ma su yi wanda Arawa suka aiwatar. Amma sun yi magana a kan bori ne kawai.

Abubakar A. (1994) a kundinsa na digirin farko (BA Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato ya yi bayanai game da cututuka da nau’oin magungunna ta hanyar amfani da saƙe – saƙi  da hakukuwa a gargajiyance wanda idan ana magana a kan cuta da magani a wajen tsafi yake da faɗi da yalwasa. Amma shi ɗan abin da ya kalato bai kai ga kawo bayanan cutukan da ake samu ta hanyar tsafi ba, balle ya yi maganar warkarsu ta hanyar.

Tadurga U. I. (1997) a kundinsa na (B.A Hausa), bai yi ƙasa a guiwa ba domin ya yi bayanin ma’anar tsafi, da ire – iren tsafi, da kuma kayayyakin tsafi.Ya kuma bayyana tsafe – tsafen dakarkari, da kuma tasirin Hausa a kan tsafin dakarkari.

Sarki H. A. (2000) a littafinsa mai taken “Tarihin zuwan Musulunci Afirika da shigowarsa a kasar Hausa”.Ya yi bayanai ne tun daga inda al’ummar duniya gaba ɗaya ta sami kanta a cikin duhun Maguzanci, inda ya bayyana al’ummomi daban – daban da kuma abin da suke bauta kafm zuwan Annabin rahama ciki har da Hausawa.Ya bayyana bautar da su Hausawa suka yi a dutsin Dala da ke Kano. Ya taƙaitá bayani a kan Kanawa kawai, kuma mun sani akwai ƙabilu da yawa a kasar Hausa ban da Kanawa.

Mashi B. U. (2001) a kundin digirinsa na farko (B.A Hausa), a Jami’ar Usman Danfodiyo Sakkwato, mai taken “Maguzanci” nazarin a kan al’adun Maguzawan Bula Gundumar Mashi. Ya yi magana a kan Maguzanci da Maguzawa, da bambancin Maguzawa da waɗan da ba Maguzawa ba.Haka kuma da bukukuwansu da wasanninsu kamar kokuwa, da sauransu.Abin da bai burge ba a nan idan ana zance a kan Maguzawa ana sa ran tsafi ya mamaye bayanin, amma sai ba muga hakan ƙarara ba.

Safana Y. B. (2001) a kundin digirin farko (B.A Hausa), a Jami’ar Usman “Danfodiyo Sakkwato, mai taken “Maguzawa Lezumawan” (babban kada) ya yi bayanai game da wuraren bautar Maguzawa da yanayin bautarsu da sauran al’amurran da suka shafi Maguzawa, yadda suke gudanar da auratayya. Illar da take a nan ita ce bai gayamana tsafe – tsafen da suke yi a wajen tafiyar da al’amurran su ba sosai.

Junju (2001) a littafinsa mai taken “Musulunci a Afurika” ya dubi yanayin Musulunci da Maguzanci da zamanin gabanin mulkin mallaka zuwa yau; Shaihin Malamin ya yi waiwaye sosai dangane da abin da ya shafi rayuwar Musulunci a Aflrika, da yaɗuwarsa. Amma bai ba mu haske sosai ba game da yanayin al’adun Malam Bahaushe ta gargajiya ba, sai dai ya kalleta ne kawai ta fuskar addini.

Gobir Y. A. (2002) a kundin digirin na biyu (M.A Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato mai taken “Iskoki a idon ‘yan bori da masu Rukiyya” ya yi bayani sosai dangane da iskoki a idon ‘yan bori da ma’anar iskoki da kuma rabe – rabensu a wajen 'yan bori, da kuma sunayen iskoki masu kama da mutane kawai bai feɗe biri har wutsiya ba.

Maikano M. M. (2002) a kundin digirinsa na (BA Hausa), Jami’ar Usman Danfodiyo Sakkwato, mai taken “Maguzawan Yari – Bori”. Marubucin ya yi bayani a kan tsafin Magiro da kuma hanyoyin bautar Maguzawan Yari – Bori da tasirin addinin Musulunci akan sha’anin tsafinsu.

Waɗan nan suna daga cikin ayukan da aka gabatar a kan Maguzawa da tsafe-tsafe da bukukuwan Hausawa. A wannan aikin zan yi ƙoƙarin nazarin ko bincike a kan “Tsafe-tsafe a bukukuwan Magugawanw Kwatarkwashi”.

Post a Comment

0 Comments