Ticker

6/recent/ticker-posts

Shaye-Shaye A Garin Gusau (6)

 Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Shaye-Shaye A Garin Gusau (6)

NA

BASHAR ISYAKA

Shaye-shaye 

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 GABATARWA

Babi na biyar kammalawa, wannan babi na biyar shi ne na ƙarshe wanda ya ƙunshi taƙaitawar aikin da aka gudanar, sakamakon bincike, shawarwarin marubuci, naɗewa sai manazarta.

5.1 KAMMALAWA

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWA) da ya ba ni ikon kammala wannan aiki, wanda yana ɗaya daga cikin sharuɗɗan kammala karatun mallakar takardar shaidar Digiri na ɗaya.

 

Lura da irin mawuyacin halin da matasanmu suke ciki game da gurɓacewar rayuwa ta hanyar amfani da miyagun ƙwayoyi, shi ya ba ni ƙwarin gwiwa wajen gudanar da wannan bincike.

Haƙiƙa a wannan binciken na gabatar da abubuwa daban-daban waɗanda suka haɗa da ma’anar shaye-shaye. A wannan kundin bincike na ji cewa shaye-shaye wani abu ne da ke haifar da maye, kuma an ji irin abubuwan da ke haifar da maye waɗanda suka haɗa da, giya, wiwi, shalinsho, da dai sauransu.

Haka kuma an ji illolin da ke tattare a cikin wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye, da nau’o’in mutanen da ke shan abubuwa masu haifar da maye. Bugu da ƙari an bayyana tarbiyya da cewa reno ne na ƙananan yara ta hanyar nuna masu abin da ya kamata da nuna masu abin da bai kamata ba. Sannan a hore su da su guje shi domin su zamo masu kyakkyawar ɗabia, abubuwan da ke kawo taɓarɓarewar tarbiyya tare da kawo hanyoyin da za a bi domin magance matsalar.

 

Bayan haka a cikin wannan kundin bincike nawa an bayyana irin hanin da addinai suka yi dangane da mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye da kuma ƙoƙarin da gwamnati ke yi da wasu ƙungiyoyin sa kai na ganin an kawar da wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye. Daga ƙarshe an bayyana hanyoyin da za a bi a magance wannan matsala baki ɗaya.

 

5.2 SAKAMAKON BINCIKE

Sakamakon bincike shi ne yake bayyana irin abubuwan da shaye-shaye ke haifarwa ga rayuwar masu yin sa da kuma al’umma da ke kewaye da su, kadan daga illolin da ya haifar da lalaci, jahilci da zaman kashe wando. Haka kuma yakan haifar da rashin lafiyoyi daban daban ga rayuwar mai yinsa. Haka kuma illolin shaye-shaye ga al’umma, masu shaye shaye sukan dami al’umma da sace-sace, fizgen wayoyi, fyaɗe, sare-sare, da sauransu.  Daga ƙarshe, sakamakon binciken ya gano irin illolin da shaye-shaye ke haifar wa ga masu yin shi da kuma al’umma baki ɗaya.

 

Misali yawan mahaukata da masu ciwon faɗuwa a sanadiyar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauransu.

5.3 SHAWARWARI

Kasancewar wannan bincike nawa, bincike ne wanda ya shafi shaye-shaye da faɗakarwa ga al’umma. Tabbas wannan mumunar ɗabi’a abar ƙyama ce da ke ci gaba da gudana a cikin wannan al’umma tamu. Saboda haka, shawarwarin da za ni bayar a cikin wannan bincike nawa mai taken “Shaye-Shaye a Garin Gusau” su ne kamar haka:

 

1.      Shawara ta farko da za ni bayar ita ce akwai buƙatar gwamnati ta sanya wannan fanni na tarbiyya a cikin manhajar karatun ƙananan makarantu. Domin inganta tarbiyar yara kafin su balaga har su san abinda ake nufi da shaye-shaye da ayyukan baɗala cikin al’umma, domin yaro tun yana ƙarami in ya ƙyamaci abu ko da ya girma ba zai yi shi ba. Wannan zai taimaka ainun wajen kyautata tarbiyar yara kafin su kai manyan makarantu.

 

2.      Bayan haka, ina mai ba da shawara ga ɗalibbai ‘yanuwa na masu nazarin harshen Hausa su ƙara faɗaɗa bincike a wannan fanni domin ƙara fitowa da illolin shaye-shaye fili don masu wannan mummunar ɗabi’ar su guje ta baki ɗaya.

 

3.      Haka zalika, akwai buƙatar marubuta littafai su tashi tsaye tuƙuru, su ci gaba da wallafa littafai waɗanda ke nuni a kan illolin wannan mummunar ɗabi’a. Sannan ya kamata masu gudanar da wasan kwaikwayo su bayar da tasu gudunmuwa wajen shirya wasanni, waɗanda ke faɗakarwa dangane da rashin kyawon wannan ɗabi’a ta shaye-shaye.

 

4.      Daga ƙarshe ina ba da shawara musamman ga malaman Firamare da na sakandare da su tsaya tsayin daka wajen bayar da tasu gudunmuwa a lokacin da suke koyar da yara domin tarbiya ba ta rataya ga iyaye ba kawai har da Malamai.

Waɗannan su ne shawarwarin da na bayar a cikin wannan bincike da na gudanar. Da fatan za’a karɓi shawarwarin da na bayar domin cimma nasarar kawar da wannan dabi’ar baki ɗaya.

 

5.4 KAMMALAWA

Wannan babi kammalawa ce ta aikin da aka gudanar akan shaye-shaye, babin ya yi bayani akan abubuwa kamar gabatarwa, taƙaitawa game da aikin da a ka gudanar, haka kuma an bayyana sakamakon bincike, da shawarwari/ ra’ayin marubuci, daga ƙarshe sai manazarta.

MANAZARTA

Tuntuɓi masu gudanarwa.

Post a Comment

0 Comments