Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Sarautar Fawa
A Garin Gusau (4)
NA
ABDULRASHID S. PAWA
Phone Number: 08132326047
Email: abdulrashidspawa@gmail.com
BABI NA UKU
TAƘAITACCEN
TARIHIN GUSAU DA SANA’O’INTA
“DA ƊAN
GARI AKAN CI-GARI”
3.0 GABATARWA
Wannan babi
zai yi magana ne a kan taƙaitaccen
tarihin Gusau, da mutanen garin da ke ciki, domin a san su ko waɗanne irin
mutane ne, haka kuma wannan babi zai yi magana a kan ma’anar sana’a da ire-iren
sana’o’in mutanen garin Gusau da suka haɗa da Noma da Ƙira
da Fawa, Wanzanci da kuma Su (kamun kifi) da sauransu.
Haka kuma
wannan babi zai yi magana a kan ma’anar sarauta, da amfanin sarauta da
matsalolin sarauta, da kuma ire-iren sarautun gargajiya da suka haɗa da:
Sarautar Noma da Sarautar Ƙira da
Sarautar Fawa da Sarautar Aska, da kuma sarautar Ruwa.
3.1 TAƘAITACCEN
TARIHIN GARIN GUSAU
“Gusau ta
Sambo Dandin Hausa”
Gusau ta
Malam sambo kowa ya zo abi nai shi gusa”. An kafa garin Gusau a shekarar
(1811), garin Gusau na ɗaya daga cikin manyan garuruwan tsohuwar
jahar Sakkwato, kafin daga bisani ya zama babban birnin jahar Zamfara a
shekarar (1996) yadda kundin bayanin ƙasa na
shekara (1920) ya nuna garin yana bisa kan titin Sakkwato zuwa Zariya ne,
kilomita (179) tsakaninsa da zariya (210), kuma tsakaninsa da Sakkwato. Daga
gabas ya yi iyaka da ƙasar Katsina da
Kwatarkwashi, daga Arewa, kuma ya yi iyaka da Bunguɗu ta ɓangaren kudu
kuma ya yi iyaka da ƙasar Ɗansadau
da kuma Tsafe (Gusau, 1979:7).
Malam Sambo Ɗan
Ashafa shi ne ya kafa garin Gusau wanda yake shi da jama’arsa ba ruwansu da
harkokin da suka shafi bautar iskoki, ko tsafi, irin wanda Hausawa ke yi kafin
zuwan addinin Musulunci, Garin Gusau baya da tarihin jahiliya. Haka tasa duk
al’adun Gusauwa al’adu ne irin na Musulunci, kuma shigowar wasu mutane wato baƙi
a garin na Gusau ba ta gurɓata waɗannan
kyawawan al’adun ba, don kuwa mafi yawan baƙin da ke zuwa
Malamai ne na Musulunci da Almajirai, Fulani da wasunsu da kan zo garin don
tsira da addininsu da mutuncinsu da kuma dukiyarsu.
Ta ɓangaren faɗa kuwa, duk
Umarnin da zai fito zai kasance na da dabra da abin da musulinci ya yadda da
shi na, kyawawan ɗabi’u da
al’adu musamman, kuma da yake, kusan duk sarakunan da aka yi a garin Malamai ne
na Musulunci masu taƙawa da tawali’u.
Da wannan
shinfiɗa ne al’adun
garin Gusau ke gudana dabra da koyarwar addinin musulunci da kyawawan al’adu
irin na Fulani da Hausawa waɗanda basuci karo da shari’a ba.
Irin wannan
yanayi ne kwararowa baƙi da ƙungiyoyin
mutane daban-daban musamman a zamanin Sarkin Katsinan Gusau Malam Muhammadu
Modibbo (1867m/1282h – 1877m 1291h) tasa garin ya samu bunƙasa a cikin ƙanƙanin
lokaci.
Samun sukunin
gudanar da harkokin addinin Musulunci waɗanda suka shafi
karatu da karantarwa da kuma ibada batare da wata tsangwama ba. Samun cikakken
tsaro ga rayuka da dukiya sakamakon ganuwa da garin yake da shi. A haka sai aka
wayi gari babu abin da ya shama mutanen garin Gusau kai sai harkokin karatu da
noma da kuma kasuwanci.
Nan take sai
haɗuwar waɗannan ginshiƙan
rayuwa guda uku a wuri ɗaya ya samar da wani kyakkyawan yanayi a
garin da kuma samar da nagartattar aƙida da yalwar
arziki da kwanciyar hankali suka kama ƙasa suka bunƙasa
a garin.
Zuwan Bature
da cinsa, ƙasar Hausa da shinfiɗa tsarin
ilimin boko, yasa wasu al’adu tsiruwa. Ana cikin haka sai ga shari’ar Musulunci
ta sake kunno kai ta godaben Tajdidi wannan sabon lamari a wannan ƙarni
shi ma ya kawo canje – canje na al’heri ga al’adun mutanen garin Gusau a
matsayin shi na babban birnin jaha. Mutane da suka shahara da gudanar da
tafsiri a masallatan juma’a da wasunsu a garin na Gusau.
A bisa ƙididdiga
da taƙaitawa garin Gusau a daidai lokacin da aka
gudanar da wannan aiki yana da masarauta ɗaya (1), babban Sarki
ɗaya (1),
Wakilai, uwayen ƙasa goma sha uku (13); yan majalisa goma sha
takwas (18), Sarautun fada, kuma akwai kimanin ɗari ɗaya da huɗu (104),
masallatan juma’a ashirin da uku (23), ƙananan
makarantun boko sittin da huɗu (64), matsaƙaita kuma
arba’in da uku (43). A ya yin da ake da manyan makarantu guda huɗu (4) rak,
makarantun allo kuma guda talatin da ɗaya (31). Haka kuma
akwai manyan kasuwanni guda uku (3); kamfanin kasuwanci kuma ashirin da bakwai
(27).
A yayin da
ake da manyan Malaman addinin musulunci tsakanin rayayyu da waɗanda suka
riga mu guda sittin da biyar (65), bankunan kasuwanci kuma da na Noma akwai
guda ashirin da uku (23) a yayin da ake da attajirai manya da matsakaita da ƙanana
da masu tasowa kimanin ɗari da talatin da biyar (135) da sauran
abubuwa da dama.
Daga lokacin
da aka kafa garin Gusau an yi sarakuna kamar haka:
1. Malam
Muhammadu Sambo (1806
– 1827)
2. Malam Abdulƙadir
(1827
– 1867)
3. Malam
Muhammadu Modibbo (1867
– 1876)
4. Malam
Muhammadu Tuburi (1876
– 1887)
5. Malam
Muhammadu Giɗe (1887 –
1900)
6. Malam
Muhammadu Murtala (1900
– 1916)
7. Malam
Muhammadu Ɗangidan (1916
– 1917)
Waɗanda suka yi
sarautar Gusau baga gidan Malam Sambo ba sun haɗa da:
1. Malam Ummarun
Malam (1917
– 1929)
2. Muhammadu Mai
Akwai (1929 –
1943)
3. Usman Ɗan
Sama’ila (1943
– 1945)
4. Ibrahim
Marafa (1945
– 1948)
5. Muhammadu
Sarkin Kudu (1948
– 1951)
6. Alhaji
Sulaiman Isah (1951
– 1984)
Dawowar
Sarauta gidan Malam Sambo
1- Alhaji
Muhammadu Kabir Ɗan Baba (1984
– 2015)
2- Alhaji
Ibrahim Bello (2015
– Date)
_____________________
An samo
wannan bayani a cikin Gusau, A.R (2014) “Mai Dubun Nasara” Al-Huda Ɓentures, Sabon Gari
Gusau, Jihar Zamfara.
3.2 MUTANEN
GARIN GUSAU
“Shimfiɗar Fuska ta
fi ta Tabarma”
Mutanen garin
Gusau Hausawa ne da kuma Fulani, amma a kan samu wasu ƙabilun daban-
daban baƙi da suke zuwa daga wani wuri. Mutanen garin
Gusau akwai su da son junansu da girmama baƙi, da kuma
taimakon juna. Da yawa mutun ke raba gidansa ya ba baƙo, ya zauna
aro ko kuma kyauta don girmamawa ga baƙo da
taimakonsa sun zauna zaman lafiya da jin daɗi kamar dangi
ɗaya.
Saboda
kasancewar mutanen garin Gusau na zaune da junansu lafiya da kuma son baƙi
da suka zo, ya sa duk wanda ya zo Gusau ko da da kwana ɗaya ne baya
son ya barta, idan ma ya barta to, Gusau kan zame masa abar so ya dawo mata.
Har ma ma’aikata da ake kawowa daga Sakkwato idan sun zo ba su son tashi don
jin daɗin zaman
garin domin ba fitina ba kuma tashin hankali.
Mutanen garin
Gusau, mutane ne masu son baƙin dake zuwa
wajensu, son baƙi da ke gare su ya samo asali ne tun daga
magabata da suka ce; “Gusau baƙi za su cika
ta fal har a rasa wurin da zasu zauna” Don haka mutumin Gusau baya gudun baƙo,
ko daga ina ya zo yana maraba da shi. Akwai lokacin da Sarkin Katsinan Gusau
Muhammadu Mai Akwai ya shirya wuraren shagulgula don baƙi su shigo
garin wannan shi ne asalin kirarin.
“Gusau
ta Sambo Ɗandin Hausa”
Allah ya
horewa mutanen garin Gusau wadata da yalwar arziki, kasancewar ƙasar
Nom ace mutanen garin manoma ne ‘yan kasuwa da ke saye da sayarwa da kuma
sauran sana’o’in da suka haɗa da Ƙira, Fawa,
Wanzanci, Su (kamun kifi), da sauransu da dama.
3.3 MA’ANAR
SANA’A
“Sana’a
Maganin zaman banza”
Masana sun
tofa albarkacin bakinsu wajen kawo ma’anar sana’a daga cikin su sun haɗa da.
Bargeri
(1986) ya bayyana ma’anar sana’a da cewa sana’a na nufin duk wata hanyar saye
da sayarwa kuma sauran al’umma da ɗan adam ke yi domin samun kwabon
kashewa da buƙatunsa na yau da kullum.
Yahaya
(1992); ya ce sana’a hanyace ta amfani da azanci da hikima da sarrafa albarkatu
da ni’imomin da ɗan adam ya
mallaka don buƙatunsa na yau da kullum. Don haka kenan
sana’a aba ce wadda mutum ya jiɓanci nufin samun abin masarufi don
gudanar da harkokin rayuwa.
Haruna da
wasu (2011) a cikin wata takarda da suka wallafa mai taken sana’o’in Hausawa na
gargajiya da ke kwalejin Ilimi ta-tarayya da ke (FCE) Zaria. Sun bayyana
ma’anar sana’a da cewa aba ce wadda yin kimiya da fasaha da ni’imomin da ke
tattare da ɗan adam da
sha’anin kasuwanci na saye da sayarwa da ciniki.
3.4 IRE-IREN
SANA’O’IN MUTANEN GARIN GUSAU
“Sana’a
maganin zaman banza”
Gusau kamar
kowace ƙasa cikin ƙasashen Hausa
ta tashi da yin sana’o’in gargajiya iri-iri kuma ta shahara da kwarewa ga resu
daga cikin su akwai Noma, Ƙira, Fawa,
Wanzanci, Su (kamun kifi) da sauran su da dama.
3.4.1 SANA’AR
NOMA
Noma sana’a
ce da ake yi domin samun abinci da za a ci da kuma wanda za a sayar domin samun
kuɗin da za a yi
amfani da su wajen gudanar da lamurran rayuwa na yau da kullum. Noma na ɗuƙe
tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yattaras, Noma wata tsohuwar sana’ace da aka
gada tun kaka da kakanni domin samun abinci. A kwai sarakunan noma a garin
Gusau suka shahara ga harkar noma daga cikin su sun haɗa da.
Sarakunan
Noma na Gusau
1. Sarkin Noma
Aliyu Mairiga (1955
– 1960)
2. Sarkin Noma
Amadu (1960
– 1973)
3. Sarkin Noma
Muhammad Kwazo (1973
– 2009)
4. Sarkin Noma
Hassan. (2008
– Date)
3.4.2 SANA’AR
ƘIRA
Ƙira
sana’a ce da ake yi domin samar da kayan aikin noma a lokacin rani, duk da yake
ana yinta a kowane lokaci domin samun kayan aikin gida na yan da kullum, ƙira
wata daɗaɗɗiyar sana’a
ce mai matuƙar muhimmanci da ake amfani da ita wajen
samar da kayan yaki domin kare kai da kuma dukiya. A garin Gusau akwai
sarakunan ƙira da suka haɗa da.
Sarakunan Ƙira
na Gusau
1. Sarkin Ƙira
Idi (1970
– 1985)
2. Sarkin Ƙira
Ali (1985
– 1990)
3. Sarkin Ƙira
Alh. Mamman Maƙerii (1990
– 1995)
4. Sarkin Ƙira
Alh. Sani (1995
– 1999)
5. Sarkin Ƙira
Rufa’I (1999
– Date)
3.4.3 SANA’AR
FAWA
Fawa babbar
sana’a ce mai daɗaɗɗen tarihi
wadda ta samo asali mai kyau, fawa sana’a ce wadda ake sayen dabbobi a yanka
domin samar da nama domin ci ko sayarwa ga jama’a, kamar shanu, raguna, tumaki,
raƙuma da sauransu, Fawa sana’a ce wadda ake yi
domin samar da nama ta hanyar yanka dabbobi, mahauta na sarrafa nama ta hanyoyi
daban-daban da suka haɗa da gashe da tsire da kilishi da ragadada da
sauransu.
A garin Gusau
akwai sarakunan Fawa da suka haɗa da:
Sarakunan
Fawa na Gusau
1. Sarkin Fawa
Ummaru Tsoho (1935
– 1940)
2. Sarkin Fawa
Muhammadu Mande Ɗan Arba (1940 -1945)
3. Sarkin Fawa
Muhammadu Ala (1945
– 1955)
4. Sarkin Fawa
Alhaji Ibrahim Shago (1955
– 1973)
5. Sarkin Fawa
Alhaji Abdullahi Bawa (1973
– 1973)
6. Sarkin Fawa
Alhaji Shehu Malami (1973
– Date)
3.4.4 SANA’AR
WANZANCI
Wanzanci wata
tsohuwar sana’a ce da aka gada tun kaka da kakanni, babu wata al’umma da ba ta
da irin wannan sana’ar domin ta kasance ta shafi tafiyar da rayuwar al’umma,
sana’ar wanzanci sana’ace ta amfani askar aski domin yin aski da gyaran fuska
da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da koshiya domin cire hakin wuya da
sauransu. Kasancewar wannan sana’a daɗaɗɗiyar sana’ace
ya sa akwai sara kunan aska a garin Gusau da suka haɗa da:
Sarakunan
Aska na Gusau
1. Sarkin Aska
Mai Kaɓau (1955
– 1965)
2. Sarkin Aska
Bube (1965
– 1972)
3. Sarkin Aska
Idi (1972
– 1977)
4. Sarkin Aska
Mamman (1977
– 1980)
5. Sarkin Aska
Bala (1980
– Date)
Bayan sarakunan
aska na gari da aka yi akwai sarakunan aska na shiyoyin garin Gusau da.
Sarakunan
Aska na Shiyoyi
1. Sarkin Aska
Alhaji Mamman–Shiyar Madawakin Gusau (1980– Date)
2. Sarkin Aska
Ali ‘yar gwaiwa – Shiyar Galadiman Gusau (1984–Date)
3. Sarkin Aska
Ummaru – Sabon Garin Gusau (1990-Date)
4. Sarkin Aska
Bello – Tudun Wada Gusau (1995-Date)
3.4.5 SANA’AR
SU
Su sana’a ce
mai daɗaɗɗen tarihi,
kuma ta samo asali mai kyau. Su sana’a ce ta kamun kifi da sauran naman ruwa,
akan shiga ruwa ko dai kai tsaye- a yi amfani da hannu, ko kuma a yi amfani da
wani abu don kama kifi. Ana kamun kifi ne domin a ci ko a sayar domin samun kuɗin da za a yi
amfani da su wajen tafiyar da al’amurran rayuwa na yan da kullum.
Masuntan da
suka shakara a fannin ruwa su kan taimaka wajen gano mutane ko wani abu da ya ɓata cikin
ruwa, don haka ne ma garin Gusau yake da sarakunan ruwa da suka haɗa da.
Sarakunan
Ruwa na Gusau
1. Sarkin Ruwa
Musa Bade (1955
– 1960)
2. Sarkin Ruwa
Isihu (1960
– 1975)
3. Sarkin Ruwa
Wakkala (1975
– 1980)
4. Sarkin Ruwa
Alhaji Idi Lalan (1980
– Date)
3.5 MA’ANAR
SARAUTA
Sarauta aba
ce wadda ta ƙunshi yi wa jama’a jagoranci da ɗaukar
nauyinsu da jan ragamar gudanar da harkokinsu na yan da kullun sarauta
shugabanci ce da shimfiɗa mulki da iko a bayan kaka, kuma halifanci
ce da Allah ke ba da ita ga wanda ya zaɓa. Sarkin shi ke ba
da umarni, ya yanke hukunci ga mutanensa, haka kuma ya yi masu sulhu ya sasanta
tsaƙaninsu, ya yi masu kyauta ya tausaya masu ya
girma masu ya kuma darajjasu a matsayinsu na mabiyansa masu mashi biyayya.
Hakan yasa
aka samu wasu hujjoji na adabi daban- daban daga cikinsu akwai waƙa
da karin magana da sauransu.
Waƙar
Sani Aliyu Ɗandawo – Ta Sarkin Minna Ummaru, akwai wasu
baitoci da yake cewa:
“Sarkin Minna Shiryayye,
duba ko ga shiri nai ga Mutane da
Dawaki,
Duk abun da akai duniyar ga Allah ya
yi ma Ummaru.
Ya baka
Mutane kuma ya baka ƙasagga ka riƙa
kar kayi wargi,
Iya kacin Ɗan
Sarki ga rayuwar shi yi sarki
Ummaru ya yi sarautar Minna ya cimma
na hwarko.
Ya kai faruku Minna yau sai yadda
kayyi,
Yanzu kai ka kiran kowa ka hwaɗa mai ya ji
sarki,
Ummaru
ja a sakamma.
3.5.1 AMFANIN
SARAUTA
“Sarauta
garkuwa ga ƙasa:
Amfanin
sarauta na da matuƙar yawa ga rayuwar
al’umma, domin ta kasance shugabanci ce da
jagorantar rayuwar al’umma.
Kasan cewar
sarautar shugabanci ce yasa kowace irin al’umma ta duniya ko da ba su da sarki
to suna da wani mai shugabantarsu. Idan ko basu da mai shugabantarsu to wannan
al’ummar ba za ta cigaba ba, haka kuma amfanin sarauta ya ƙunshi fannoni
daban-daban na rayuwar al’umma domin kare su da dukiyoyinsu da yi masu shari’a,
tare da yi masu adalci, da sasanci a tsakanin su, da tallafa masu tare da yi
masu kyauta da tausaya masu da sauran su. Akwai hujjojin adabi da suka tabbatar
da haka daga cikin su sun haɗa da:
Waƙar
Sani Aliyu Ɗandawo - Ta Sarkin Gombe Shehu a cikin waƙar
yana cewa:
“Sarakunan farko da yau da duk wanda
ya yi Sarkin Gombe,
Ba ai irin ka mai dubun komai ba, ba
ai irinka mai Dawaki ba,
Allah shi ja zamanin Shehu,
Amin muna ta addu’a kullun.
Mutan Gombe
tun ana yaƙi ba a kai maku faɗa ba tun
farko,
Bale na yanzu in an zo,
Gambun gabas
na Sarkin yamma tun zamanin ana yaƙi,
Da anga Gombe sassani ya kai,
Kwasassan
Gombe Shekara huɗu, bana yazzo zai ga Gombe ta can za,
Kamar ba Arewa kazzo ba,
Haddai a ce maka gidan Sarki,
Kamar irin ginin ƙasar
Turai.
Haka kuma akwai
waƙar Alh. Musa Ɗanƙwaito
– Ta Sarkin Muri Ummaru Abba.
A wasu
baitotan ya na cewa:
“Ku Sarakuna duk na zamani,
Ku ɗauki halin
Ummarun Abba,
Ku sarakuna duk na zamani,
Ku ɗauki halin
Ummarun Abba.
Ranar yaƙi,
Baiji tsoro ba,
Kuma ranar kyauta,
Bai ji tsoro ba.
Inna gida
zaune Alhaji Musa nigga takardar Ummarun Sarki,
Sai yace muje Jalingo,
Ɗan ƙwairo
na sauka Jalingo,
Raj Juma’a nis sauka Jalingo,
Sai niyyi kiɗa a gidan
Galadima.
Galadima da ya sallame ni,
Ran assabar sai nijje gidan Sarki,
Ɗanƙwairo
nan niyyi hira Sarki yayman kyauta ta mamaki,
Alhaji Musa Ɗanƙwairo
ga babbar riga ya baka ga kufta.
Kuma ga alkibba ga rawani, kuma ga jar
hula, hadda agogo da takalmansu.
Ɗan ƙwairo
ya baka Two thousand,
Gautan kiɗi da shi da
Marafa,
Kowane ga babbar riga tai, su biyu
sai yab basu two thousand.
Yaran Ɗanƙwairo
goma sha uku kowa riga da Two Hundred Naira,
An kayi total anka haɗa kuɗin kwairo da
na yara,
Sun zama Fiɓe thousand siɗ hundred Naira,
Su Ummarun Abba yab bani.
3.5.2 MATSALOLIN SARAUTA
Kowa ne
lamari na rayuwa ba ya rasa wasu matsaloli a cikin shi, haka ma sarauta a
kan samu wasu matsaloli a cikinta.
Sarauta tana da matsaloli idan aka samu rashin shugabanci nagari kan haifar da
rashi, ko in kula ga haƙƙoƙin
jama’ar da ake shugabanta, haka kuma a kan samu matsalar tauye haƙƙi
wajen yin hakunci ga jama’a, mafi yawan sarakuna idan ba na gari ba ne sai su ƙasance
suna zaluntar jama’arsu. Akwai rashin kyautatawa jama’a da rashin yi masu
kyauta da kuma rashin ko in kula ga rayuwarsu da kuma dukiyoyinsu.
3.6 IRE-IREN
SARAUTUN SANA’O’IN GARGAJIYA
Kowa ce
sana’a tana da mai jagorantarta ko mai shugabantarta, hakan kan ƙarawa
Sana’ar ƙima a idon duniya, ƙwarewa da
kuma nuna ƙwazo da kuma gado shi ke sa waɗanda suka
shahara ga sana’o’in su su zama masu jagorantar masu sana’ar daga cikin
ire-iren sarautun sana’o’in gargajiya sun haɗa da;
sarautar Sarkin Noma, sarautar Sarkin Ƙira, Sarautar
Sarkin Fawa, sarautar Sarkin Wanzamai, sarautar Sarkin Ruwa da sauransu.
3.6.1
SARAUTAR SARKIN NOMA
Sarautar
Sarkin Noma ta samu ne daga sana’ar Noma, Sarkin Noma shi ne mai wakiltar ko
shugabantar masu wannan sana’ar ta hanyar tsara hanyoyin kiyaye lafiya da
dukiyar masu wannan sana’ar tare da shinfiɗa dokoki da
zartar da hukunci a garesu.
Ana samun
wannan sarauta ta hanyar gado ko jarunta ko kuma ƙwarewa ga
sana’ar, kuma sarki ko hakimin gari ke ba da ita, haka kuma akwai wasu ƙananan
sarautu da ke ƙarkashin sarautar ta Sarkin Noma da:
Galadiman Noma, da Jagaban Noma, da Madakin Noma da sauransu.
3.6.2
SARAUTAR SARKIN ƘIRA
Ita ma sarauta
ce da ake samunta ta hanyar gado, ko ƙwarewa kan
sana’ar, Sarkin ƙira shugaba ne na gungun masu sana’ar ƙira
shi ke tsara hanoyin gudanar da kasuwanci, ta hanyar shimfiɗa dokoki da
umarnin da ya bayar ga jama’arsa. Haka kuma wannan sarauta sarki ko hakimin
gari ke ba da ita, akwai wasu ƙananan
sarautu da ke ƙarƙashin ta da
suka haɗa da; Madakin
Ƙira da Galadiman Ƙira, da
sauransu.
3.6.3
SARAUTAR SARKIN FAWA
Sarautar da
tafi kowace muhimmanci a sana’ar Fawa ita ce Sarkin Fawa. Wannan Sarauta ana
samun ta ne ta hanyar gado ko ƙwarewa kan
sana’ar, sarautar fawa jagoranci ne, ko shugabanci ne na masu gudanar da
sana’ar fawa, Sarkin Fawa shi ne shugaban mahauta, mai jagorantar sana’arsu ta
hanyar shinfiɗa dokoki
wajen tafiyar da mulki, tare da hukunci, da kare rayuwarsu da dukiyoyinsu, da
sada zumunta a tsakanin su mahauta rundawa, da sauran masu sana’ar gargajiya.
Ita wannan sarauta sarki ko hakimin gari ke ba da ita, haka kuma akwai ƙananan
sarautun da ke ƙarƙashinta da
suka haɗa da; Wakilin
Fawa da Ajiyan Fawa da Sarkin Zango da sauransu.
3.6.5
SARAUTAR SARKIN WANZAMAI
Sarautar
Wanzanci babbar sarauta ce a ƙasar Hausa,
babu wata al’umma da ba ta da ta’ammali da harkar Wanzanci, domin ta shafi ɓangaren
lafiyar al’umma. Sarkin Wanzamai shugaba ne na masu wannan sana’a, shi ne mai
jagorantar su ta fuskar mulki tare da shinfiɗa dokoki
wajen tafiyar da harkokin wanzanci. Sarautar wanzanci daɗaɗɗiyar sarauta
ce da aka gada tun kaka da kakanni, ita wannan sarauta sarki ko hakimin gari ke
ba da ita. Ana samun ta ta hanyar gado ko kwarewa a kan sana’ar wanzanci, haka
kuma akwai ƙananan sarautun da ke ƙarƙashin
ta da suka haɗa da;
Galadiman Aski da Madawakin Aski da Majidaɗin Aski,
Ajiyan Aski da sauran su.
3.6.5
SARAUTAR SARKIN RUWA
Sarautar
sarkin ruwa, sarauta ce mai matuƙar muhimmanci
a ƙasar Hausa, Sarkin ruwa shi ne mai kula da
duk wasu lamurra da suka shafi ruwan gari, haka kuma shi ne shugaban duk wasu
masu sana’ar su, wato masunta, ta hanyar tsara masu dokoki da yin hukunci gare
su. Sarautar Sarkin ruwa tana taimakawa wajen gano wani abu ko wasu mutanen da
suka ɓata cikin
ruwa, ita wannan sarauta ana samunta ta hanyar gado ko shahara a kan sana’ar
su, sarki ko hakimin gari ke ba da ita. Haka kuma akwai wasu ƙananan
sarautu a ƙarƙashinta da
suka haɗa da Taru da
sauransu.
3.7
KAMMALAWA
Wannan babi
ya yi magana a kan taƙaitaccen tarihin
garin Gusau, da mutanen da ke ciki, da ire-iren sana’o’insu, haka kuma wannan
babi ya yi magana a kan ma’anar sarauta da amfaninta da kuma matsalolinta daga ƙarshe
babin ya yi magana a kan ire-iren sarautun sana’o’in gargajiya na garin Gusau.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.