Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (1)

waka

BABI NA DAYA

SHIMFIƊA

1.0 GABATARWA

A nazarin adabi da al'ada na kowace al'umma akwai muhimman abubuwa da ke bijirowa masu buƙatar nazari na ƙwaƙƙwaf.Wannan bincike za a gudanar da shi ne domin bayar da gudummuwa a fagen adabin Hausa musamman abin da ya shafi waƙa.Kasancewar waƙa na ɗaya daga cikin adabin al'ummar Hausawa,kuma muhimmiyar aba da ke da tasiri a rayuwarsu.Tasirin yasa ake amfani da ita don faɗakarwa da nishaɗntarwa da wa'azantarwa da kuma ilmantar da al'umar Hausawa.Bisa wannan dalili ne aka ga ya dace a yi nazari a kan Ginin Tsarin Wasu Kalmomin Zamfarci A Wasu Waƙoƙin Kilasik.

Wannan kundi an kasa shi zuwa babobi biyar.Bibi na daya za a yi tsoƙaci a kan munufar bincike da dalilin bincike da hasashen bincike da muhimmancin bincike, da dabarun bincike da farfajiyar bincike da hujjar cigaba da kuma kammalawa.A babi na biyu za a yi waiwayen ayyukkan da suka Gabata masu alaƙa ta kusa da ta nesa da wannan aiki.Domin masu hikima na cewa "Na gaba idon na baya" A babi na uku za a yi bayani game da tarihin wannan mawaƙi tun daga fara waƙarsa har zuwa matsayinsa a yau.

A babi na hudu za a yi tsoƙaci kan yadda mawaƙin ke amfani da kalmomin Zamfarci a cikin jerin gwanon waƙoƙinsa.A babi na biyar kuwa za a kammala wannan bincike, tare da kawo shawarawri da ra’ayin mai bincike da kuma ratayen wasu waƙoƙi da aka yi amfani das u.

 

1.1 MANUFAR BINCIKE

Manufata ta gudanar da wannan bincike ita ce yin tsakure gwargwadon fahimtata a kan bayanan masana da kuma dalibai 'yan'uwana da suka gudanar da bincike a kan adabi da al’ada da harshe daban-daban. Za a gudanar da binciken a kan waƙoƙin Kilasik da kuma karin harshen Zamfarci.Domin ƙara fitowa da fasaha da hikimar da Allah ya yi wa kilasik don dalibai 'yan'uwana su san muhimmancin da karin harshen Zamfarci yake da shi,da kuma irin gudumuwar da wannan  mawaƙi ke bayarwa wajen bunƙasa karin harshen Zamfarci.

 

1.2 DALILIN BINCIKE

Kamar yadda Hausawa ke cewa, "Ruwa ba ya tsami banza " wato,komai da ake yi akwai dalilin yin sa,.ba haka kawai ake yin abu gaba-gaɗi ba, musamman a fagen ilimi.Wannan bincike za a gudanar da shi ne domin zaƙulo wasu kalmomin Zamfarci da irin tsarin da waɗannan kalmomin suke da shi a cikin waƙoƙin klasik, domin amfanin masu bincike da 'yan'uwana musamman daliban ilimi da za su biyo baya a wannan fanni.

1.3 HASASHEN BINCIKE

Wannan bincike za a aiwatar da shi ta yin hasashen gano kalmomin Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin Kabiru kilasik. Da irin hikimomin wannan mawaƙi,da irin yadda yake amfani da azanci yayin sassaƙa waɗannan kalmomin a cikin waƙarsa.Haka kuma,wannan bincike zai yi  tasiri wajen sanin matsayin karin harshen Zamfarci da yadda ake amfani da shi don binciken harshen Hausa da gudumuwar da yake ba adabi musamman a fagen rubutattun waƙoƙin siyasa.

1.4 MUHIMMANCIN BINCIKE

Ana iya cewa dukkan wani abu da mutum zai gudanar, ko ya aiwatar da shi,to ba zai yi shi ba sai ya tabbatar cewa yana da amfani gare shi da sauran jama'a musamman idan ya shafi fagen ilimi.

Saboda haka, wannan bincike yana da muhimmanci ƙwarai da gaske ba ma ga fagen ilimi, ko ga mai nazari kawai ba, har ma ga masu sha'awar waƙoƙin siyasa.   Bugu-da-ƙari, binciken zai haɓɓaka wannan fannin na adabin Hausa ta hanyar fito da hikimomi da fasahar wannan mawaƙi, a fili domin masu saurare da sha’awar waƙoƙinsa su amfana da abubuwan da yake faɗa cikin waƙoƙinsa.

Haka kuma,wannan bincike zai tattara waɗannan kalmomi ta yadda masu nazari za su sami ɗan abin dubawa a wannan bagire.

1.5 DABARUN BINCIKE

Na yi ƙoƙarin amfani da mahimman dabaru ko hanyoyi  na musamman, wajen gudanar da wannan bincike. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da binciken littafai  da kundayen neman digiri daban-daban  da aka wallafa a wannan fanni. Da kuma duba mujallu da takardun ƙarawa juna sani da aka gabatar a makarantu da jami'o'i daban-daban da masana suka yi a wannan fanni. Na yi amfani da Mp3 na waƙoƙin Kabiru kilasik.

Haka kuma, na ba tattaunawa da masana daban-daban da masu ruwa da tsaki a wannan fage na ilimi muhimmanci ƙwarai domin samun ƙarin haske ta yadda wannan aikin zai samu nasarar kammalawa. Domin masu hikima sun ce “Ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba" .Na kuma yi ƙoƙari na ganin cewa na gana da wannan  mawaƙi don samun cikakken sahihin ko ingantaccen bayani mai cike da ƙamshin gasikya daga gare shi.Domin Hausawa na cewa "Waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi" . Bugu-da-ƙari, na ziyarci ɗakunan karatu na Jami’o’i domin samun wasu bayanai masu alaƙa da wannan aiki nawa.Waɗannan su ne hanyoyi ko dabarun da na bi don gudanar da wannan bincike.

1.6 MATSALOLIN BINCIKE

Gaskiyar Hausawa da ke cewa, “kowa ya ci zomo ya ci gudu,” `tabas haka ne,domin kuwa na cikaro da matsaloli da dama a wajen gudanar da wannan bincike. Wanda suka shafi ƙarancin kayan aiki isassu, kasancewar ban samu wani magabaci da ya keɓanci wannan bagire na Nazarin  kalmomin Zamfarci A Wasu Wakokin Kabiru Kilasik ba. Amma bayan faɗi-tashin da na yi ta yi na ziyartar ɗakunan adana littafai da kundayen digiri na cikin makarantu da dama, da hirar da na yi da Mawaƙin da wasu mutane daban-daban ya taimaka sosai wajen warware waɗannan matsaloli.

1.7 HUJJAR CIGABA DA BINCIKE

Hujja, ko dalilin da ya bani damar cigaba da wannan bincike nawa shi ne, dukkan ayyukkan da suka zo hannuna ban ci karo da aiki ɗaya ba irin nawa.Duk da cewa masana da dama da kuma daliban ilimi sun yi aikace-aikace masu ɗimbin yawa dangane da wannan mawaƙi,amma babu guda ɗaya tilo mai taken aikina. Sai dai kama,masu hikima sun ce,"Kama da wane ba ta wane " Wannan dalili shi ya bani sha'awa da ƙarfin guiwar cigaba da wannan bincike.

1.8 FARFAJIYAR BINCIKE.

Wannan bincike zai taƙai ta ne kacokan kan waƙoƙin Kabiru Kilasik. Binciken zai ta’allaƙa ne a kan Nazarin kalmomin Zamfarci da suka ta'allaƙa a waɗannan wakoki kamar ha

 

Waƙar Saratun Mamuda mai taken "In An Ba Albasa Ruwa Karo Na Biyu" (2011)

Waƙar Bilya Shinkafi mai taken "Taka Lafiya Ɗan Sadauki"

Waƙar Usman Ɗankalili mai taken "Dodo Magajin Dodo" (2015)

Waƙar A.N.P.P Baku Da Niya mai taken "Ciki Da Gaskiya Wuƙa Bata Huda Shi (2016)

Babu shakka wannan bincike an keɓance shi ne  a kan Tsarin Ginin kalmomin Zamfarci A Wasu Wakokin Kilasik.

1.9 KAMMALAWA

Sanin Muhimmancin bincike da dabarun bincike da kuma,Hujjar cigaba da bincike tare da fahimtar dalili da hasashen wannan bincike, abu ne mai matuƙar muhimmancin gaske.Da wannan farfajiyar bincike na naɗe wannan babi,da kuma Kammalawa r kanta.

Post a Comment

0 Comments