Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Nazarin Kalmomin Zamfarci A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Kilasik (2)

waka

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 GABATARWA 

Waiwaye adon tafiya.Masu iya maagana sun ƙara da cewa ‘ tuna baya shi ne roƙo’. Wannan babi zai yi bayani a kan ayyukan da suka gabata.Za ayi,ƙoƙarin duba ayyukkan da aka yi masu alaƙa da wannan bincike. Domin Hausawa na cewa "idan kabi wanda ya fi ka dole a bi ka" Dan haka wannan waiwaye zai shafi ayyuka masu alaƙa da wannan bincike kawai,amma wannan alaƙa za ta iya zama ta kusa ko ta nesa.Abu ne mai muhimmanci ƙwarai da gaske a duba wasu ayyuka da suka gabata masu alaƙa ta kusa da ta nesa.Domin masu hikma sun ce " na gaba idon na baya " Yin hakan zai bada damar samun makamar inda kowane aiki ya sa gaba da kuma matsayinsa a wannan fage na ilimi.

Gaskiyar masu hikima da ke cewa ‘Abin da babba ya hango daga zaune yaro ko ya hau sama bai hango shi’ wannan zance haka yake, duk wani abin da mutun zai gudanar idan har yana buƙatar cin nasara,akwai buƙatar ya duba tafarkin da masana suka bi dangane da wannan abu. A wajen gudanar da wannan bincike an duba ayyukkan da suka gabata waɗanda suka yi magana a kan waƙa, da kuma harshe.An duba kundayen bincike neman digiri na daya da na neman digiri na biyu, da mujallu da rubtattun littafai a Jami'o'i daban-daban.

2.1 Kundayen Bincike

Akwai ayyukka da dama da aka yi masu nasaba da wannan bincike. Daga cikin wadanda suka zo hannu akwai:

Abubakar U. da Ibrahim S.K. (2016) A binciken su sun bayar da ma’anar waƙa da zambo da habaici da irer-iren su, sun bayar da tarihin Kabiru kilasik. Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da nawa aikin, domin kuwa,duk muna magana ne a kan mawaƙi guda, kuma   a kan bagere daya wato, waƙa.Sai dai banbabncin nasu aikin da nawa shi ne sun yi nazari Zambo da Habaici, ni kuma a kan ginin kalmomin Zamfarci a cikin waƙoƙin Kabiru kilasik.

            Ɗangulbi (2003) a cikin kundin digrinsa na biyu ya yi bayanin tarihin kafuwar siyasa a Nijeriya. Kuma ya yi bayanin wasu jigogin waƙoƙin siyasa na janhurira ta huɗu, kamar jigon faɗakarwa, da jigon yabo, da jigon zambo da habaici, da sauransu. Haka kuma ya dubi waƙoƙin inda ya fito da siffantawa, da kinaya, da alamtarwa da dabbantarwa, da abuntarwa, a cikin wasu waƙoƙin janhuriya ta huɗu. Sannan kuma ya yi sharhin wasu waƙoƙin ja’iyyun ANPP da PDP.Wannan aiki nasa yana da alaƙa da nawa aikin, domin duk suna magana ne a kan rubutattun waƙoƙin siyasa na janhuriya ta huɗu. Sai dai bambancin aikinsa da nawa shi ne, shi ya kalli rubutattun waƙoƙin siyasa daban-daban ya yi nazarinsu. Ni kuwa aikina ya keɓanta ne ga rubutattun waƙoƙin siyasa na Kabiru Kilasik.          Mansur.M (2017) A nasa kundin ya kawo ma’anar waƙa da jigo da salo da tsari.Wannan aiki yana da alaƙa makusanciya da  akin nawa domin yana magana ne a kan tarjamar wasu waƙoƙin Kabiru Kilasik, kamar yadda na ke nazin wasu kalmomin Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin Kabiru Kilasik.Saboda haka yana da kyakkyawar alaƙa da binken da nake gudanawa.     

Abdullahi Y.(2016),Ya kawo ma’anar waƙa. ya yi taƙaiccen bayani kan waƙoƙin siyasa.Wannan bincike nasa yana da alaƙa da nazarin da nake gudanarwa, domin ya yi shi ne a kan waƙa ya kuma taɓo waƙoƙin siyasa, fannin da nake bincike a kai.

Garba M.M (2016), Ya bada tarihin Attahiru Jega ya kuma kawo ma‘anar waƙa da sharhin waƙar da aka yi wa Jega ta biyu.Wannan kundi yana da alaƙa da nawa binciken.

Buhari Ɗ. (2010) Ya bada tarihin sarki Zazzau Aminu. Ya kawo wasu daga cikin makaɗan fada irin su: Jankiɗi da Narambaɗa da sauransu. Wannan bincike nasa yana da rawar da yake takawa a nawa nazarin.Sai dai aikin nasa a kan waƙoƙin baka na sarata ne, ni kuma a kan rubutattun waƙoƙin siyasa ne na Kabiru kilasik.

Muhammad B.B (2015), Ya bada ma’anonin waƙar baka da salon waƙar baka da kuma tsarinta.Inda ya yi cikakken sharhi a kan jerin sarƙe a waƙoƙin baka.Babu  shakka wannan kundi yana da nasaba da nawa, duk da kasancewarsa a kan waƙokin baka aka yi shi.Ni kuma  a kan rubutattun waƙoƙin siyasa.

 Talatu I. (2012),a kundinta na neman digin farko da ta gabatar a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, Ta kawo ma’anar waƙa da waƙoƙin pdp.Wannan kundi yana da muhimmanci da kuma alaƙa ta kusa da nawa binken.

Aliyu N. (2011),a kundinsa na neman digiri na biyu, ya kawo ma’anar waƙa da kuma waƙoƙin siyssa, da adawar da ake nunawa a cikin waƙoƙin siyasa. Wannan bincike yana da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da nawa aikin.

Muhammad S.A (2012), a kundin neman digirinsa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zarira,ya bada tarihin Jankiɗi da wasu daga cikin waƙoƙinsa da salon waƙoƙinsa da jigon waƙoƙinsa.Ya kuma kawo ma’anar waƙa. Wannan kundi na da nasaba da nawa binciken.

Ibrahim B. (2011) Ya kawo tarihin Sardauna da kuma waƙoƙin da aka rubuta a kansa ya yi sharhin wasu daga ciki. Wannan kundi na da rawar takawa a nawa kundin.

Aishatu (2012) ta yi bayanin a kan rubutattun waƙoƙin siyasa, da ma’anar salo da ier-irensa da kuma ma’anar sarrafa harshe. Kuma ta yi bayanin salo da dabarun jawo hankali da kuma sarrafa harshe a wasu waƙoƙin jam’iyyun PDP da ANPP a jihohin Kano da Jigawa.Haka kuma ta kwatanta wasu waƙoƙin jam’iyyun ANPP da PDP tare da kawo kamanci da bambancin salon waƙoƙin.

     Binciken Aishatu da nawa suna da alaƙa, domin domin duk an yi bincike ne a kan rubutattun waƙoƙin siyasa na Hausa. Sai dai ita ta kalli salon sarrafa harshe a cikin wasu waƙoƙin na jam’iyyun PDP da ANPP a jihohin Kano da Jigawa, ni kuma kuwa a aikina nazrin ginin kalmomin Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin Kabiru Kilasik.

Mashi (1986) a kudin digirinsa na biyu, ya yi bayanin ma’anar waƙa da tarhinta da rabe-rabenta, haka kuma ya kawo ma’anar siyasa da manufofinta, da kuma tarihin kafuwar siyasa a ƙasar Hausa.Har wa yau kuma a cikin kundin bincike ya yi bayani sigogi da rabe-raben waƙoƙin siyasa da kuma matsayin makaɗan baka a cikin siyasar jam’iyya.Sannnan kuma ya yi sharhin wasu waƙoƙin jam’iyyun NPC da NEPU da kuma PRP.

     Wannan bincike da nawa suna da alaƙa domin duk suna magana ne a kan waƙoƙin siyasa na Hausa. Bambancinsu shi ne, nasa aikin bincike ne a kan waƙoƙin baka na siyasa na janhuriya ta ɗaya da ta biyu. Nawa aikin kuwa nazarin ginin kalmomin Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin siyasa na Kabiru Kilasik.

Abazarri (2008), A nasa kundin binciken neman digiri na ɗaya. Ya bayyana tarihin rayuwar Aminu ala da waƙoƙinsa da yadda yake tsara waƙoƙinsa da ire-iren waƙoƙinsa da yanayin waƙoƙinsa.Bayan nan kuma ya kwantanta waƙoƙin ala da na mandiri, har ila yau ya kwatanta waƙoƙinsa da na fim, ya kuma nuna yadda za a nazarci waƙoƙin.Wannan bincike yana da alaka da nawa binciken.

Hamza R.A (1998) Ya kawo ma’anar waƙa da kuma rubutattun waƙoƙin siysa da aka yi a wannan lokaci.Wannan bincike yana da nasaba da nawa.

Adamu (2002) Ya kawo tsokaci da masana suka yi kan ma’anar jigo da jigon so da jgon bege da jigon faɗakarwa da jigon siffantawa ya yi bayani ɗaya bayan ɗaya a kansu.

Har ila yau ya kawo mawaƙan da suka yi waƙar da waƙoƙinsu da jigoginsu da salon sarraf harshe da warwarar jigo da tsarin waƙar.Wannan kundi na da alaƙa da nawa bincike.

Abdullahi (2001) Manazarcin ya yi ƙoƙarin kawo ma’anar waƙar baka, da waƙoƙin mata musamman na daka da reno da daɓe. Wannan bincike yana da alaƙa da nawa.Sai dais hi a kan waƙoƙin baka ya yi nasa binciken, ni kuma a kan waƙoƙin siyasa na Kabiru kilasik.

Ibrahim (2008), ya bayyana cewa akwai hanyoyi uku da  masana suka bayyan wajen nazarin waƙa, hanyoyin su ne:

  1. Jigo
  2. Zubi da tsari
  3. Salon sarrafa harshe

Wannan bincike yana da alaƙa da nawa,domin yana magana ne a kan hanyoyin nazarin waƙa

Salamatu (2006) ta bada ma’anar waƙa ta kawo waƙoƙin siyasa..Wanda wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin, kancewar nazarina  a kan waƙoƙin Kabiru kilasik ne shi kuma mawaƙin siyasa ne.

Husaini (2007) Ya bada ma’anar waƙaya karkasa waƙoƙi kan jigo wato,jigon gargaɗi da faɗakarwa da yabo.Wannan bincike yana da dangantaka da nazarin da nake.

Isma'il (1985),Ya fara ne da ma'anar fada makaɗan fada da kuma abin da waƙarsu ta ƙunsa .Makaɗan sun hada: Buda Ɗantanoma da kuma Ibrahim Narambaɗa,rayuwarsu da ayyukkasu.Da kuma zababbun makaɗan Fada na zamani waɗanda suka hada Musa Ɗankwairo da Sa'idu faru.Wannan bincike yana da alaƙa da nawa,domin yana magana ne akan waƙa, kamar yadda nake nazari akan waƙa.Sai dai nasa aikin a kan waƙar baka da mawaƙn fada ne,nawa kuma a kan rubutattun waƙoƙin siyasa na Kabiru kilasik.

Umar (2002) A nasa binciken na neman digiri na ɗaya da ya gabatar a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria,Manazarcin ya bayyana ma’anar bara da kuma matsayin bara a cikin al’ummar Hausa da kuma nau’in waƙoƙin bara da ire-iren bara da kuma lokutan da ake yin wannan bara.Wannan kundi yana da dangantaka da nawa domin a kan waƙa ne kuma ya kawo ma’anar waƙa a ciki.

Wakalla (2008),ya yi tsokaci ne a kan tarihin Haruna Uji, ƙurciyarsa da yadda ya fara waƙarsa tare da kawo bakandamiyar waƙarsa.

Bayan nan ya kawo ma’anar jigo inda ya ce “jigo wani saƙo ne ko wani abu ne da waƙa ta ƙunsa,Wannan bincike yana da alaƙa da nawa domin ya bada ma’anar waƙa da jigo da tarihin mawaƙin da salon waƙarsa.Waanan bincike yana fa alaƙa da nawa, duk das hi a kan waƙoƙin baka ne, ni kuma rubutattun waƙoƙin siyasa na Kabiru kilasik

Sa'adatu (1995),ta yi cikakken sharhi akan wasu waƙoƙi kamar Tabarƙoƙo da Hawainiya da Sabuwar Nijeriya da kuma Lebura, a cikin waƙoƙin fasahar Aliyu na Aƙilu Aliyu.

A takaice wannan bincike na da alaƙa da nawa,saboda. ta yi nazari ne a kan Zambo da Habaici a rubutattun waƙoƙi,kamar yadda nake gudanar da nawa bincikn a kan rubutattun waƙoƙi. Saboda haka akwai alaƙa a tsakanin bincikenmu.

Ibrahim A. (2000) Ya bada tarihin Zamfara ya kawo Zamfarci da bambancin Zamfarci da daidaitacciyar Hausa. Babu shakka, wannan aiki yana da nasaba da nawa, kuma ya taimaka wajen ɗora ni a kan hanya, kancewar aikina ya shafi karin harshen Zamfarci. Kenan wannan nazari na da alaƙa ta kusa da nazarin da nake gudanawa.

Maharazu B.A da wasu(2008)A kundinsu na neman digiri na farko a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. A ciki sun yi bayanin Zamfarci da rabe-raben Zamfarci da gidan Zamfarci, da sauransu. Wannan aiki yana da alaƙa da nazarin da nake a kai. Saboda bincikena ya kunshi karin harshen Zamfarci, a cikin waƙoƙin Kabiru kilasik..

Sule (2011) , ya yi bayani a kan Ɗankwairo da ire-iren waƙoƙinsa, waƙoƙin fada waƙoƙin noma da na jama'a da waƙoƙin ta'aziya da waƙoƙin siyasa.

Bisa la'akari da cewa wannan bincike ya ginu ne a kan waƙa, kuma, an taɓo waƙoƙin siyasa inda Kabiru kilasik ya ƙware.Ya nuna cewa wannan nazari na da alaƙa da nawa, ta fuskoki da dama.

Muhammad Y.T (2003)A ƙudinsa na neman digiri na farko, a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Ya bayar da tarihIn Dankurma Gombe da kuma jigogin waƙoƙinsa  da salon waƙoƙinsa, Wannan bincike yana da tasiri da kuma alaƙa da nawa bincike, domin kuwa, a kan waƙa aka gudanar da shi.

Sayinna A.(2003),Ya ba da abubuwan da ake yabon mutum da su, da matsayin yabo a adabin Hausa da dangantakar yabo da kirari. Kuma ya bada ma'anar Zambo da Habaici da dalilin da ke sa a yi su. Saboda haka, wannan bincike yana da alaƙa da nawa binciken saboda a kan waƙa ne aka gudanar da shi.

Saminu (2006), Ya ba da tarihin waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa, sannan ya kawo tarihim sani Shu'aibu (Sani Dangiwa), da Haruna Aliyu Ningi (K.K), da  Aminu Ibrahim Ɗandago.Ya kawo waƙar "Adon Gaskiya Baya Ɓata" da Waƙar Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi.

Wannan bincike yana da nasaba da nazarin da nake gudanarwa domin akan waƙa ya yi shi.Kuma ya taɓo waƙoƙin siyasa,, in da nan ne nawa binciken ya fi mai da hankali musaman waƙoƙin siyasa na Kabiru kilasik.

2.2 Bugaggun Littafai

Masana da dama sun wallafa littafai masu alaƙa da wannan nazari. Daga cikin littafan da suka zo hannu akwai:

 Bunza A.M  (2017), ya yi bayani cikakke wanda zai iya zama jagora ga duk wani mai gudanar da bincike na neman digin farko da na biyu da mai Phd, kai da ma duk wani mai gudanar da bincke a fagen ilimi. Ya yi bayani a kan ma’anar bincike da dabarun bincike da mahimmancin bincike da matsalolin bincike da bitar ayyukan da suka gabata da sauran fannonin da suka shafi bincike ta fuskar adabi da al’ada da harshe. Wannan littafi ya zama turba ko in ce ya share man fagen binkena tare da zama jigo ko fitila mai haska man hanyar gudanar da wannan nazari. Haƙiƙa Hausawa sun yi gaskiya da suka ce "Tafiya da babba daɗin yaro"  wannan littafi ya ba ni gudummuwa sosai wajen gudanar da wannan aiki.

 Bunza A.M (2013), Ya kawo cikakken tarihin Narambaɗa da iyalansa da abokansa da Waƙoƙin sa, da iren-iren waƙarsa da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarsa na yau da kullum.Wannan gagarumin littafi ya haɗa abubuwa da dama masu muhimmancin gaske ga wannan nazari nawa. Gaskiyar masu iya karin magana da ke cewa, "Ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba"  Haƙaƙi wannan gagarabadon littafi ya zame mani jagora ga wannan bincike.

Ibrahim Y.Y (1988), ya yi bayani a kan ɓangarori da dama, a ciki har da tarihin samuwar rubutattun waƙoƙi.wanda ya taimaka a wajen gudanar da wannan bincike.

  Ɗangambo A. (2007) ,ya yi cikakken bayani a kan waƙa, ya ba da ma'anar waƙa da hanyoyin nazarin waƙa da sauransu.Kuma wannan littafi yana da matuƙar muhimmancin a wannan bincike.

Sani M.A.Z  (1999),ya yi bayanin ilimin furuci da lokutan Hausa in da ya taɓo ginin jimala, wanda ginin jimla ya shafi bincikena domin haka wannan littafi yana da alaƙa ta kusa da wannan nazari. Kuma ya taimaka ƙwarai da gaske.

Gusau S.M (1996), ya yi rubuta dangane da tarihin rayuwar makaɗa da mawaƙa guda talatin da uku (33), haihuwarsu da nasabarsu da asalinsu da ƙurciyarsu da sana'o'insu da yadda suke tsara waƙoƙisu da falsafarsu da sauran ayyukkan da suke yi a rayuwarsu ta yau da kullun.Wannan aiki yana ba da haske dangane da makaɗa, don haka a iya samun saurin fahimtar darussan da suke kunshe cikin waƙoƙinsu,wanda zai zama haske a wannan nazari.

Ibrahim (1983), ya yi bayani a kan makaɗan sarauta da jigoginsu da kuma salon sarrafa harshe.Kuma ya yi bayani kan makaɗan jama'a a waƙoƙin kasuwanci. Ya yi bayani a kan Sana'a da makaɗan Maza da sauransu.Saboda haka wannan litafi yana da alaƙa da bincikena.

Dunfawa (2003),Ya bayar da ma'anar aruli da ƙafiya, kari wato da Balaraben kari da Bahaushen kari,.Haka kuma ya kawo sauti (zahafi) da gwauron sauti da tagwan sauti da sakiyar illa da sakiya mai ragi da kuma sautin rabawa. Sannan ya kawo amsa-amo da amsa-amon gaɓar sauti da babban amsa-amo da karamin amsa-amo da amsa-amon farawa da amsa-amo mai zaman kansa da kuma amsa-amon sauti.

Wannan littafi yana da muhimmanci domin yana nuna mizanin waƙa da masana suka rubuta masu alaƙa da wannan bincike.Wannan aiki yana da alaƙa ta kusa da nawa, domin ya yi cikakken bayani akan amsa-amon ciki da amsa-amon waje, wato babban amsa-amo da ƙaramin amsa-amo.Wanda duk mai nazarin rubutattun waƙoƙi dole ne ya san su ya kuma fahimce su, domin yana ɗaya daga cikin abinda ya bambanta rubutattun waƙoƙi da na baka.Bugu da ƙari ya kawo ma’anar waƙa.

Gusau S.M (2008),Ya bayyana tarihin Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi da waƙoƙinsa. Wannan littafi yana da muhimmanci ga wannan bincike.Domin ya bayar da ma’anar waƙa da kuma yadda ake yin nazarin waƙa, duk cewa shi a kan mawaƙin baka ya gudanar da wannan aiki ni kuma nawa a kan waƙoƙin siyssa na Kabiru kilasik.

Gusau S.M (2008) ya  bayar da tarhin waƙoƙin baka a ƙasar Hausa yanayinsu da sigoginsu da suka haɗa da kiɗa na Hausa da kayan yinsa. Kuma ya binciki makaɗan baka na Hausa da halayyarsu da nau’o'in waƙoƙin baka na Hausa da kuma turke da ire-irensa a wƙoƙin baka na Hausa.

Wadannan littafai suna da muhimmanci domin sun tabo wakokin siyasa, muhimmin fagen da nake gudanar da bincike a kan shi.

Maƙaloli

A ɓangaren Maƙaloli masana da dama sun yi rubuce-rubuce a kan batutuwa masu alaƙa da wannan nazari. Don haka za a iya cewa sun bayar da gudummuwa wajen gudanar da wannan bincike.

Dumfawa da Yahaya (2010), Sun bayyana irin bijirewa da yaudarar da 'yan siyasa ke wa talakawa.Wannan maƙala a kan 'yan siyasa aka yi ta,kuma tana da alaƙa da wannan bincike,kasancewar waƙoƙin da nake bincike na siyasa ne,kuma mawaƙin mafi akasarin waƙoƙinsa duk na siyasa ne. Kuma 'yan siyasa su ne abokan mu'amalarasa.

Usman (2011). ya gabatar da wasu turakun waƙoƙin baka na Hausa. Kamar ilimantarwa da faɗakarwa da wayar da kai da wa'azantarwa da yabo.Wannan maƙala ta na da nasaba da wannan bincike domin a waƙoƙin da nake nazari duk akwai kwatankwacin waɗannan ababe.

Funtua (2011), ya gabatar da tarihin rayuwar shata da waƙoƙinsa a fagen rayuwar al’umar Hausawa kamar: kirari da zambo da raya sana’a.Wannan maƙala tana da alaƙa da nawa nazarai domin a kan waƙa ya gudanar da ita.

Bello (1976) ,Marubucin ya bayyana cewa kiɗa ya zama jinin ɗan Adam. Bayan haka ya rarraba kiɗan maza da kiɗan sana’a. Wannan maƙala tana da laƙa da bincikena.Domin a kan waƙoƙi aka gabatar da ita, kuma ni ma nazari na a kan waƙoƙi ne.

2.2 TARIHIN ZAMFARA A TAƘAICE

Ƙasar Zamfara ta kafu tun a ƙarni na sha biyar (15 century). Ta kasance a bangaren Arewancin Nijeriya, A lardin Sakkwato inda  daga baya ta kasance a matsayin jiha. Ta ƙunshi ƙananan hukumomi guda goma sha huɗu,tare da hidikwatarta da ke garin Gusau.Ta yi iyaka da Jihar Sakkwato a arewa.A jihar Katsina kuwa,ta yi iyaka ne ta gabas.Sannan ta yi iyaka da jihar Kaduna a ɓangaren kudu.Daga ƙarshe,ta yi iyaka da jihar Neja da jihar Kabi ta ɓangaren kudu maso yamma.

A ɓangaren faɗin kasa kuwa, jihar Zamfara tana da kimanin murabba'in kilomita dubu talatin da takwas da ɗari huɗu da arba'in da takwas (38,448). Kamar yadda sauran jihohin arewacin Nijeriya suke, ita ma jihar Zamfara tana da yanayi huɗu a shekara.Akwai yanayin "rani" dana "hunturu" wanda ke farawa a watan Nuwamba zuwa watan Mayu.Sai kuma yanayin "kaka" dana "damana" da kan fara daga watan Yuli zuwa watan Oktoba (wannan bayani, an samo shi daga littafi mai suna (Zamfara As It Is).

Jihar Zamfara tana da manyan gulabe guda huɗu, Gulaben su ne: Gulbin Bunsuru da gulbin ka,da gulbin Zamfara da gulbin Gagare.Haka kuma akwai manyan tafkuna guda biyu.

Tafkunan su ne; tafkin gulbin kakale da tafkin Bakura. Baya ga waɗannan manyan tafkuna, akwai kananan tafkuna irin su tafkin saru,a cikin ƙaramar hukumar Gummi,da tafkin Jena a ƙaramar hukumar Zurmi.A ƙaramar hukumar mulki ta Maradun akwai babban dam wanda ake kira dam ɗin Bakalori.

Ana hasashen cewa jihar Zamfara tana da yawan mutane kusan miliyon biyu da dubu ɗari biyu ta talatin da ɗaya da ɗari huɗu da biyu (2.231,402).Amma a ƙididdigar da aka sake yi a shekarar alif dubu biyu da shida (2006 21-03) lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Obasanjo. Sakamakon ƙididdigar ya nuna cewa jihar Zamfara na da kimanin mutane million uku da dubu ɗari biyu da hamsin da tara da ɗari takwas da arba’in das hid, (3,259,846).

2.3       ZAMFARCI

Kafin a cigaba da bayani game da Zamfarci, yana da kyau in ƙaci a kan harshe, da karin harshe. Domin Zamfarci karin harshe ne a cikin kare-karen harsunan ƙasar Hausa.

Harshe wata tsoka ce da ke cikin bakunanmu wadda muke magana, muke cin abinci, muke shan ruwa kuma muke haɗiyar yawu da shi.

Masu yin nazarin harshe sun yi ƙoƙarin ba da ma’anarsa a ilmance sun bi hanyoyi daban-daban domin su fahimtar da dalibansu wannan ma’anar amma ga baki ɗayansu sun yi ittifaƙi a kan wasu abubuwa kamar haka: - Harshe suna ne gama-gari mai nufin hanyar sadarwa ɗaya cikin hanyoyi uku na sadarwa. Biyun su ne: Rubutu da Ishara. ( Yakubu S.Z. 2014-P 115).

Masana da dama sun bada ma'anar harahe. Daga cikinsu akwai:

Fagge (2001), ya ce, "Harshe wata hanyar sadarwa ce da ɗan Adam yake amfani da shi mai ma’ana wanda kuma yake haka ne a kowacce al’umma da ke zaune a doron ƙasa take fahimtar abubuwan da ke ƙunshe a zukatan Jama’a kamar tunani, ra’ayi, hikima, sha’awa da sauransu”.

Ladan (1996), ya ce: "Harshe abu ne da ya ƙunshi alamomi da ɗan Adam yake amfani da su wajen bayyana tunaninsa, ya cigaba da cewa alamomin harshe sun ƙunshi sautukan da ake furtawa a jajjere, kuma ake amfani da su cikin tsari"

Azare (2011), ya ce:” Harshe tsararriyar hanya ce da mutane ke amfani da ita wajen isar da saƙon da yake zukatansu ko tunaninsu, watau mai kyau ko maras kyau, na farin ciki, ko na nuna damuwa ta hanyar furuci. Allah (SWT) ya halicci ɗan adam tare da harshe ya halicce shi, tun lokacin Annabi Adam(AS) tare da Hauwa’u, Allah (SWT) ya sanar da Annabi Adam (AS) dukkan komai-da–komai harma da harasa da za’ayi magana da su.(          Ƙur’ani Sura Baƙara,Aya Ta 31)

A taƙaice za mu iya kiran harshe da furuci, ko sadarwa, ko kuma, hanyar sadarwa a tsaƙanin al'umma.

Shi kuwa, karin harshe yana nufin bambance-bambancen da ake samu tsakanin masu magana da harshe.Ta sanadiyar bambancin wuraren zama, ko nisantar juna.Ga abin da masana suka ce game da karin harshe.

Amfani (1993), cewa ya yi, "Karin harshe bambanci ne da ake samu ta fuskar kalmomi da furuci da kuma sadarwa.Karin harshe yakan faru saboda dalilai: Saboda yankuna da ake samu tsaƙanin al'umma masu amfani da harshe guda, kuma domin bambancim muhalli ga mutanen da ke amfani da harshe guda".

Yakasai (1998), ya bayyana cewa, " Karin harshe na nufin yadda wani gungun al'umma ke maganaa cikin harshe guda wanda ke da alaƙa da tarihin  al'umma da ke magana da shi".

Trudgil (1974-17), ya ce " Karin harshe na nufin bambancin da ake samu a cikin harshe tsakanin kalmomi nahawu da kuma furuci".

Neil Skinner (1977:8) ya nuna cewa, "Karin harshe wani bambanci ne da ake samu a cikin harshe, sai dai baya nuna cewa wani harshe ne na daban".

Shi kuma Kamus na Encyclopedia (uolume 4.16 Edition), ga abin da ya ce, "Karin harshe wani bambanci ne da ake samu a cikin harshe,Wanda wani bangare na mutane da suke amfani da shi, bambancin ya shafi kalmomi da nahawu da kuma furuci wanda hakan ya bambanta shi da wani karin harshe na wannan harshe".

karin harshe shi ne ya bambanta sauran harsuna wajen tsarin sauti, da fadar kalmomi  da kuma kirar jimla. Wato irin waɗannan bambance-bambancen suna da nasaba ne dangane da irin yanayin wurin zama da zamantakewa da kuma abubuwa da suka shafi rayuwa.

Zamfarci yana daya daga cikin karin harsunan  da ake magana da su a ƙasar Hausa. Sama da mutum miliyon biyu ne ke amfani da harshen Zamfarci.Kamar sauran kare-karen harshen Hausa, Zamfarci ya banbanta ta hanyar  sigogi da suka shafi ginin jimla da gundarin sauti da ginin kalma da ma'ana.

Ta hanyar waɗannan ne za mu iya fahimtar Zamfarci, a kan sauye-sauyen da ake samu tsaƙanin baƙi da baƙi ko wasali da wasali daga daidaitacciyar Hausa zuwa Zamfarci. Saboda haka yana da kyau mu san cewa Zamfarci yana ɗaya daga cikin kare-karen harshen Hausar yamma,yayin da sauran kare-karen suka haɗa da kabanci da Gobiranci da Sakkwatanci da kurfayanci da Arewanci.

Dukkaninsu  karin harsuna ne masu zaman kansu,kuma suna da alaƙa da juna ta hanyar furuci.

Kasancewar ƙasar Zamfara ta yi iyaka da wasu jihohin arewacin Nijeriya,ya haddasa samuwar rabe-raben Zamfarci. Daga wani yanki na wata ƙaramar Hukuma zuwa wata.Saboda haka za a duba wasu daga waɗannan ƙananan hukumomi.

Daidaitacciyar Hausa   K/ ANKA

Baci              Kwana

Gyaɗa            Gujjiya

Aure              Amre

Kananzir.         Barahuni

Kookoo.           Kunuu

ƙyaure.            Gambu

Tsumma.           Ragga

Daidaitaciiyar Hausa      K/ BAKURA

Zogala            ‘Yam Makka

Rantsattse                   Rantcattce

Ritsimi                       Rintcimi

Tseeree                     Tceeree

Tsimi                          Tcimi

Waatse                       Waatce

 

Daidaitacciyar Hausa K/ BUKKUYUM

Feɗe                                        Heɗe

Feƙe                                        Heƙe

Feesa                                      Heesa

Leefe                                      Lehe

Refe                                        Rehe

Shafew                                   Shahe

 

Daidaitacciyar Hausa                      K/BUNGUƊU

Saɓa                                        Swaɓa

Safa                                         Swahwa

Fanti                                       Hwaranti

Mtsi                                        Matci

Tsiri                                        Tciri

Kintsi                                     Kintci

 

Daidaitacciyar Hausa                      K/KAURA

Kuli                                                    Bakuru

Riɗi                                                     Kantu

Awara                                                Shala

Ganwo                                               Tarɗi

Bayi                                                    Yauce

Zogala                                                ‘Yam makka

Daidaitacciyar Hausa                      K/ MARU

Ƙuli                                                     Guru ko ƙuli-ƙuli

Awara                                                Ƙwai da ƙwai ko awara

Bayi                                                    Makewayi

Kananzir                                            Barahuni

Cingam                                              Bazuka

 

Daidaitacciyar Hausa                      K/ MAFARA

Zauna                                                 Zamna

Tauna                                                 Tamna

Shuka                                                 Shubka

Sauna                                                 Samna

Fiɗa                                                     Hiɗa

Fari                                                     Hwara

Daidaitacciyar Hausa     K/ SHINKAFI

 

Taushi                                                Tabshi

Shuka                                                   Shikka

Farce                                                     Hwarce

Faci                                                      Hwaci

Faɗa                                                     Hwaɗa

Faɗuwa                                             Hwaɗuwa

Faifai                                                 Hwaihwai

Fansa                                                    Hwansa

 

Daidaitacciyar Hausa  K/ ZURMI

Lafiya                                                        Lhiya

Auki                                                           Abki

Saurayi                                         Samrayi

Tunki                                                     Tumkiya

Farce                                            Hwarce

Fari                                                         Hwari

Farmaki                                                   Hwarmaki

Daidaitacciyar Hausa                            K/B.MAGAJI

Fashi                                                       Hwashi

Hantsi                                                     Hantci

Kafaɗa                                           Kahwaɗa

Fira                                                             Hira

Fifiko                                                          Hihiko

Littafi                                                      Littahi

Safiya                                                       sahiya

Rufe                                                          Ruhe

Kwatsewa.                                                Kwatcewa.

Wannan shi ne takaitaccen bayanin Zamfarci da misalan Zamfarci kamar yadda aka gani.

2.4 MA’ANAR WAƘA

Idan ka hadu da mutum a kasuwa ko a bakin titi ko a wani wuri na gargajiya,ka tambaye shi abin da ake nufi da waka da Hausa, abin da zai iya fada maka shi ne,jan magana ko nanata zance kan wani abu da ake son yi.Shi ya sa za ka ji mutum yana cewa kullun ina wakar zan zo mu gaisa amma abun ya faskara.Kenan wakar abu na nufin ka yi ta kururuta batu ko jan batu a zuci na tsawon lokaci amma ba aikatawa

Waka wani azanci ne da ake ta hanyar zaben kalmomi wadanda ke kunshe da hikimomi da ake rubutawa ko a rera da fatar baki cikin sautin murya na musamman.

Masana da dama sun bayar da ma'anar waƙa.Kmar haka:

Yahaya (1985) ya ce, “ waƙa ta ƙunsh ƙololuwar hikima da tunani ɗan Adam ta yin amfani da ƙwayoyin muryoyi aunannu cikin kalmomi zaɓaɓɓu wanda ake jeran ta su cikin tsari fitacce,ƙayyadadde,rababbe ta yadda za su fa’idantar, wanda ake rerawa a kan Karin murya ƙayyadadde  kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman.

Yahaya (1997), cewa ya yi "waka tsararriyar maganar hikima ce da ta kunshi sako cikin zababbun kalmomi da aka auna domin maganar ta reru,ba furtawa kurum ba".

Dangambo (1982) ya bayyana cewa " waka wani sako ne da aka gina kan tsararriyar ka'ida ta baiti ko dango da ake rerawa kan kari ko amsa-amo; da sauran da sauran ka'idoji da suka shafi daidaita kalmomin"

Muhammad (1980), cewa ya yi "waka tana zuwa ne ta sigar gunduwoyin zantuka wadanda ake kira diyoyi kuma ake rerawa da wani irn sautin murya na musamman".

Gusau S.M (1993),cewa ya yi " waka magana ce ta fasaha a cure a wuri daya a cikin tsari na musamman"

Zaruk da wasu (2010), sun ce: “Waƙa magana ce cikin sarrafaffiyar murya wadda ake rangwanɗawa bisa wani tsari”

Tsoho (1983), ya ce “Waƙa ba tare da banbanta rubutatta ko ta baka ba,salo ne na tsara kalmomi yadda za su ba da sauti mai rauji ko daɗi da kuma ma’ana yadda za ta gamsar da yawancin masu saurarenta”

Hadiza (2007), a nata nazarin ta yi ƙoƙarin ba da ma’anar waƙa da cewa”Waƙa zance ne sarrafaffe,ayyananne wanda da shi ake bin hawa da saukar murya,mai zuwa gunduwoyi layuka da ake rerawa bisa wani daidaitaccen tsari,wani lokaci tare da kiɗa.

Saboda haka,za mu iya cewa waƙa wani azanci ne da ake shiryawa ta hanyar zaben kalmomi waɗanda ke ƙunshe da hikimomi da ake rerawa da fatar baki ko a rubuta a cikin sautin murya na musamman, a kuma rerata a rubuce.

2.5 WAƘAR BAKA

Waƙar baka abu ce mai daɗaɗɗen tarihi a rayuwar al’umma, domin idan aka yi la’akari dangane da nazarce-nazarce da malamai, da manazarta da dama suka yi,za a tarar da mabanbabntan ra’ayoyi a kan asalin ita kanta wakar.Haƙiƙi waƙoƙin baka suna da asali kuma sun sami karɓuwa a zukatan al’ummar da ake amfani da harshensu wajen a gudanar da ita,kasancewar suna da muhimmanci wajen gudanar da ita,kasancewar tana da muhmmanci a wajen bayyana halin

rayuwar al’ummar da kumabayyana hikimominsu.Waƙoƙin baka suna da tasiri a cikin zukatan al’umma ga mai ilimi ko maras ilimi.Wani lokaci har ma wanda baya jin harshen da ake amfani da shi,yakan yi sha’awar muryar waƙoƙin.

Masana da dama sun yi tsokaci wajen ba da ma’anar waƙar baka dangane da fahimtarsu.Waɗannan masana da manazarta waƙoƙi sun haɗa da:

Gusau (2003), da (2014), Umar (1987), da Yahaya (1981), da Ɗangambo (1982), da Malumfashi (2011), da sauransu.

Ɗagambo (1982), ya bayyan waƙar baka da cewa,”Wani furuci ne a cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi a cikin wani tsari ko ƙa’ida,da kuma yin amfani da dabara ko salon armashi”.

Umar (1987), ya ce,” Wakar baka ko waƙa, ita ce nau’in gunduwoyin zance da ake kira ƙayyadajje,kuma ake rerawa da wani irin sautukan murya na musamman”.

Tanko (2010), ya bayyana cewa, “Waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin  hikima da azanci,da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa a rera cikin sautin murya,da amsa-amo, kari da kiɗa da kuma amshi”

Sa’id (1981), ya faɗi cewa, “Waƙar baka ita ce wadda ake rerawa dan jin daɗi a ajiye ta aka a kuma yaɗa ta a baka”

Yahaya (1979),cewa ya yi,”waƙar baka tta ƙunshi wasu abubuwa muhimmai kamar zaɓen kalmomi da kuma sarrafa su cikin hawa da saukar murya tare da hikima,”

Yahaya (1997), ya bayyan ceawa,”Wakar baka wata tsararriyar maganar hikima ce wadda aka tsara da wasu zaɓaɓɓun kalmomi masu ma’ana kuma aka rera ba faɗa kurum ba, wadda ake iya  amfani da kiɗa da nufin isar da wani saƙo”.

Yakawada (1ss983), ya ce “Waƙa ba tare da banbanta rubutatta ko tabaka ba,salo ne na tsara kalmomi yadda za su ba da sauti mai rauji ko daɗi “.

 Bisa la’akari da maganganum magabata. Za mu iya cewa,.waƙar baka wata aba ce da ake shiryawa da ka a adana a ka a kuma rera da fatar baki,a cikin wani irin sauyin murya na musamman. Ana ganin cewa mata su suka fara waƙar baka.Irin waƙoƙin reno,waƙoƙin daɓe,waƙoƙin biki.da sauransau.

2.6 SAMUWAR RUBUTACCIYAR WAƘA

Yanayin samuwar rubutattun waƙoƙi a ƙasar Hausa,za mu iya raba su zuwa loƙuta kamar aji huɗu,na farko kafin zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa, na biyu tun daga zuwan addinin musulunci ƙasar Hausa har ya zuwa ƙarni na goma sha shida zuwa ƙarni na sha takwas (16-18),na uku ƙarni na sha tara da ƙarni na asShirin.

Abin da masana suka fi raja'a a kai shi be kafin zuwan addinin musulunci ƙasar Hausa, Hausawa ba su da ilimin Larabci,saboda haka ba su iya rubutu ko karatu ba.Wannan shi ya sa ake ganin a wancan lokaci ba su da wata rubutacciyar waƙa.Waƙar da aka tabbatar akwai ta ita ce waƙar baka ta farko ta farauta.Sannan ta ibadar gargajiya kamar ta kiraye-kirayen bori da sauransu.

Duk da haka wasu masana sun bayyana cewa wata ƙila lokaci mai tsawo da ya wuce hausawa sun taɓa cin karo da rubutu. Suka kuma bayyana cewa akwai tarihin wata rijiya a kano mai suna "Akwa" wadda ake ganin cewa ita wannan kalmar ta "Akwa" na nufin ruwa kuma an bayyana cewa lokacin da daular waɗannan mutanen da haɓaka sun shigo ƙasar Hausa.Haka ma an ce a wajen ajiye kayan tarihi na London akwai wani dutse da aka yi ajamin Hausa a kansa da harshen Yunananci, wannan rubutun ma dai ya daɗe sosai.

Haka kuma akwai waɗansu zane-zane da aka samu a kan wasu duwatsu a Birnin Kudu an ce su ma daɗaɗɗu ne ƙwarai.Wannnan ya nuna muna cewa ana kyautata zaton cewa Hausawa sun taɓa cin karo da 'yan rubuce-rubucen da ba su taka kara suka karya ba,abin da ke nuni da cewa ga dukkan alamu ba a taɓa samun wata tsararriyar rubutacciyar waƙa ba.

A cikin ƙarni na goma sha bakwai zuwa na sha takwas (17-18),an samu ci gaba da yaɗuwar addinin musulunci da samuwar malamai waɗanda suka yi suna da daukaka a tannin addinin musulunci. A wannan ƙarni na goma sha bakwai aka samu wali Ɗanmarina da wali Ɗanmasani. Waɗannan malamai dukkansu sun yi rubuce-rubuce da damar gaske.Misali, wali Ɗanmarina ya rubuta waƙoƙi da dama waɗanda suka haɗa da: Daliyya da Nuniya da waƙar Sharun Tana da sauransu.

Wali Ɗanmasani ya rubuta waƙoƙi irin su sharhen Ishimawi da Ishiriniya da Alfazazi da sauransu.

Haka kuma akwai malam Muhammad na Birnin Gwari da ya rubuta waƙoƙi kamar haka: Ma'akuba da Gwahiratu da Bilahirarmu da sauransu. Sai kuma malam Shitu dan Abdurra'uf Wanda ya rubuta waƙoƙi kamar haka: Fassarar Arshada da waƙar Wawiya da jirmiya (waƙar tuba) da sauransu.

Duk waƙoƙin da suka yi suna magana ce a kan madahu, da gargaɗi,da wa'azi da koyar da shika-shikan addini.

A ƙarni na goma sha tara kuwa,Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da almajiransa da yaransa sun rubuta waƙoƙi da dama a cikin harshen Larabci da Fillanci da Hausa da nufin yin kira ga jama'arsu da shuwagabanni da su kula da harkokin addini su kuma gyara halayyarsu ta fuskar ma'amala da jama'a.

A ƙarin na goma sha tara lokacin da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da almajiransa suka rayu,lokaci ne da mutane suka tashi tsaye wajen neman ilimin addinin musulunci. Saboda tsayuwarsu ne ga neman ilimin addini aka samu jihadin daukaka addinin musulunci da yaɗa shi a ƙasar Hausa. Musulunci a wannan lokaci ya yi ƙarfi don haka duk waƙoƙin da aka rubuta a zamanin suna Magana ne a kan addinin musulunci tsantsa.Kuma duk wata waƙa da ba ta addinin musulunci ba ce ana daukar ta a matsayin "Hululu".Waƙoƙin da aka rubuta a ƙarni na goma sha tara sun shafi wa'azi da gargaɗi da furu'a da tauhidi da sauransu.

Rubutattun waƙoƙin Hausa sun bunƙasa sosai a ƙarin na sha tara,kuma da yake manufar rubuce-rubucen ita ce ,su yi wa'azi da yabon Ubangiji da begen Annabi (s a w) da tauhidi da fikihu,babau mamaki idan marubutan sun yi amfani da dukkan abubuwan da suka shafi addini a cikin rubuce-rubucensu.

2.7 WAƘOƘIN  SIYASA

A ma'anar kalmar Siyasa ta kurkusa tana nufin hanya ko dabara da ake amfani da ita don a cimma wani mataki na shugabancin al'uma.

A tsarin siyasa akwai siyasar addini da siyasar kishin kai da siyasar kishin ƙasa da siyasar jam'iyya. (M.Garba Gusau IJMB Note).

A ƙarƙashin siyasar jam'iyya za a sami shuwagabannin jam'iyya da 'yan takara,akwai muƙamai da gurabu na mulkin jama'a daban-daban. Sannan za a yi zaɓe a rantsar da waɗanda suka sami nasara su cigaba da gudanar da mulki.

Makadan Hausa sukan shirya waƙoƙi a kan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa da aka bayyana a baya da suka shafi al'amuran siyasa. Irin waɗannan waƙoƙin suna ƙarƙashin jigon siyasa ne.Waƙoƙi ne da ake yin su da nufin bayyana manyan saƙoni na siyasa. Kamar; bayyana manufofin jam'iyya ko yi wa jam'iyya kamfen ko wayar da kai kan zaɓe ko yabon 'yan siyasa da sauransu.

Alhaji Aminu Ibrahim ɗan Dago ya yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko waƙa a shekara ta dubu biyu da bakwai (2007), wanda wannan waƙa ita ce ta tallata Aliyu har Allah ya kai shi ga cin nasara.Waƙar ita ce:

" Sakkwatawa suna bayanka

Sarkin yamma Alla saka ma"

( Dan dago waƙa magatakarda)

Bayan waɗannan akwai, Dauda Adamu Kahutu rarara, wanda shi ma mawaƙin siyasa ne ya yi waƙoƙi da dama.daga cikin wakonsa akwai:

"Zuwan mai malfa kano"

"Mai malfa ya karaya,

Yace maganar zaɓe a ɗaga,

A ɗaga ko kar a ɗaga,

P.D.P sai mun kai ta ƙasa"

ƊRarara wakar mai malfaƙ

"Masu gudu su gudu,

Bana dai janaral shi ne a sama,

Mun hallaka P.D.P,

Bana A.P.C ita ce da ƙasa,

Mai malfa fara shiri,

Bana za ka fice Bila,

Da gudun gaggawa".

Rarara (Waƙar murnar cin zaɓen Buhari)

" Ga Buhari ya dawo"

 

"Cuta ba mutuwa ba

(Waƙoƙin Dauda rarara)

Haka shi ma Alhaji Kabiru Yahaya Kilasik a matsayinsa na mawaƙin siyasa, ya yi waƙoƙi masu ɗimbin yawa na siyasa.Daga cikin waƙoƙinsa akwai:

"Walin Kurya na Gwabna samunka da moriya,

Mamuda mijin Saratu ma nai maka godiya,

Angon Mariya da Aisha barka da ɗawainiya"

(Kabiru Kilasik waƙar Walin Kurya)

 

"Baba dawo baba dawo.

Dallatu ɗan Aliyu kazo,

Mamuda ka dawo muna jiran ka,

Ka cincinta da mulki Zamfara,

Dan ba ka saba da yaudara ba."

( Kabiru Kilasik wakar MAS)

                       

" Ubangiji shi yay yi Nijeriya,

Yay yi Zamfara tare da mu,

Ubanginmu ka yarda da mu,

Da Shehinmu Gwabna tare da mu,

Jarma Uranti yake maka murna,

Shatima kayi mulikinka da lafiya."

(Kabiru Kilasik wakar Shehi A.A.Yari)

 

"Sakkwato masha Allahu,

Kilasik barakallahu,

Albishirin da najji,

Shi  zanI Sanar wa da masu kaunarmu,

Sarikin yamma zai koma,

Da yarda Ubangiji Allah."

(Kabiru Kilasik waƙar sarkin yamma)

 

"A.N.P.P ba ni da kuwa,

Kuma kun sa ba ku da niya,

Kar muka kallon juna,

Kabiru nai maku kallon mai bisa ruwa"

( Kabiru Kilasik waƙar Ciki da gaskiya)

 

"Nijeriya ku yi mani murna,

Dan gaba ta samu garan,

Nijeriya muna da rabo,

Kuma Nijar mun samu rabo,

Shugaban ƙasa gare muna Nijar,

S.S.G yah haɗa mu da shi,

Mahammadu Yusuf madoga,

Na Aliyu magatakarda uba."

( Kabiru Kilasik wakar Shugaban Kasar Nijar Muhammadu Yusuf)

 

"Zamfara mun yarda da Tantabara uwar alkawari,

Saratu fes ledi innar-wuro madalla da ke,

Kin wuce matan Gwabnonin Arewa,

Ko sun ƙi su bi"

(Kilasik wakar uwar-gidan mamuda Saratu)

Waɗannan waƙoƙi da aka kawo a matsayin misalai, duk waƙoƙi ne na siyasa. Kuma ana yin su ne domin yabon 'yan takara da masoya da kuma yin zambo da habaici da gugar-zana ga abokan adawa.

2.8  MAWAƘAN  HAUSA  A ZAMFARA

A duk faɗin ƙasar Hausa, babu wani yanki da Allah ya albarkata da haziƙan makaɗa kuma da shahararrun, mawaƙa waɗanda suka bunƙasa adabin Hausa a duniya kamar yankin Zamfara.

Maƙadan su ne:

Alhaji Kabiru Yahaya Kilasik

  • Ɗan Ƙwairo
  • Salihu jan Kiɗi
  • Inka Bakura
  • Sani Sabulu
  • Gurso
  • Musa Ɗanbiri Bakura
  • Makaɗa Dungum Bakura
  • Abdun Rini
  • Amadu Mailauni Bakura
  • Amadu Mainakada Bakura
  • Siddi Bakura
  • Yahaya Sahunu
  • Ɗandodo Alu
  • Sa'idu Faru
  • Malamin Waƙa
  • Bawa Gabci
  • Daɗi Dolen Moriki
  • Hassan Wayam
  • Muhammad Sarkin Taushin Katsina
  • Ɗangiwa Zuru
  • Ɗanzaki Maradun
  • Ɗanbawa kaura
  • Ɗankurma Maru
  • Salihu Jankiɗi Rawayya
  • Mani mai kiɗa
  • Amali sububu
  • Kassu Zurmi
  • Mamman Nata ukka
  • Sagalo mawaɗin kokuwa
  • Sani Kaka Dawa
  • Ɗankurji
  • Ɗanwasa Gummi
  • Yahuza Ɗangiwa
  • Kabiru Birni Magaji
  • Sani Maikuntugi na Gusau

Wanda an yi amanna cewa marigayi Mamman Shata yakan sa a zo masa da shi su yi fira domin ya samu kalmomin da zai yi amfani da su a tasa waƙar.

Wasu daga cikin wamaƙan Zamfara kenan.Akwai wasu makaɗan da dama wadanda ba a ambaci sunayensu ba.

2.9 KAMMALAWA

Dangane da bita ko waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, wannan waiye ya zama shi ne tubalin ginin wannan aiki nawa, domin ya yi mani ƙarin haske wajen fahimtar yadda wannan aiki nawa zai kasance. Wannan ne ma ya sa na dawo cikin hayyacina tare da fahimtar inda wannan bincike ya sanya gaba,duk da dai cewa wasu manazartan sun gudanar da nasu binciken ne a kan tasirin waƙoƙin baka na Hausa wasu kuma sun kalli salon sarrafa harshe ya yin da wasu suka yi tsokaci kan jigon wasu waƙoƙi, wanda hakan ya nuna cewa duk suna da alaƙa da nawa aikin.

Haka kuma wasu sun yi nazari ne kan rubutattun waƙoƙin wasu mawaƙa.

Bugu da ƙari,wannan aiki zai gudana ne a kan nazarin wasu kalmomin Zamfarci a cikin wasu waƙoƙin Kabiru Yahaya Kilasik.

Post a Comment

0 Comments