Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zababbun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (2)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Nazari Kan Jawabin Kama Aiki Na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara Daga Shekara Ta 2007 Zuwa 2019 (2)

NA

NASIRU HASSAN

jawabi

BABI NA ƊAYA

1.0 GABATARWA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikkai, mai kowa mai komai, wanda ya sanar da mutum rubutu da karatu da Alƙur’ani ya kuma sanar da shi abin da bai sani ba.

A cikin wannan bincike za a yi nazari ne a kan “Nazarin Jawabin Kama Aiki na Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Zamfara daga Shekara ta 2007 zuwa 2019”

Shugabanci shi ne yi wa mutane jagora da jan ragama a harkokinsu na zaman tare. Yawan jama’ar da mutum ya shugabanta da yaɗuwarsu ko girman muhallin da suke zaune a cikinsa da ƙarfin jagorancin da yake yi masu, su ake kira mulki. Kuma sauƙin bayar da umurni da hani da tsaro shi ne iko. Waɗannan abubuwa wato shugabanci da mulki da iko su suka taru suka yi sarauta. A taƙaice, shugabanci shi ne haɗa kan mutane da kare marasa ƙarfi daga mai ƙarfi da kuma kiyaye martabar ɗan Adam.

 

Wannan aiki zai gudana kan babi-babi. A babi na ɗaya za a yi bayani kan dalilan gudanar da bincike, muhallin bincike, manufar bincike, hanyoyin gudanar da bincike, farfajiyar bincike, matsalolin bincike da kammalawa.

 

A babi na biyu za a yi bayani kan sake duba ayukkan da suka gabata, bugaggun littafai, maƙalu da kundayen bincike, yanar gizo da kammalawa.

 

A babi na uku za a yi bayani ne kan taƙaitaccen tarihin jihar Zamfara, yawan jama’arta, albarkatun ƙasarta, sana’o’inta, yanayinta, ma’anar harshe, ma’anar siyasa, kafuwar jam’iyyun siyasa, lafuzzan siyasa da manufarta a siyasance da kuma kammalawa.

 

A babi na huɗu za a duba ma’anar salo, salo da siyasa, salo da lafuzzan siyasa, salo da sarrafa harshe da kuma nazarin jawabin kama aiki na zaɓaɓɓun gwamnonin Jihar Zamfara a shekarun 2007 da 2011 da 2019. Sai kammalawa.

 

A babi na biyar za a yi bayanin gabatarwa, taƙaitawa, shawarwari, jawabin kammalawa, rataye da manazarta.

 

1.1 DALILIN GUDANAR DA BINCIKE

Kamar yadda rayuwa take babu wani abu da ɗan’adam zai yi ba tare da manufa ko dalilin yinsa ba. Wannan aiki za a yi shi ne kan waɗannan dalilai kamar haka:

i.                    Babu shakka an daɗe ana sauraren jawaban kama aiki na gwamnoni daban-daban musamman jihar Zamfara da yadda kowane gwamna kan shirya tare da gudanar da jawabinsa zuwa ga al’ummar Zamfara.

ii.                  Wani dalili na wannan bincike shi ne, domin nazarin waɗannan jawabai da shuwagabanni ke yi domin fito da manufofinsu a fili domin amfanin al’umma baki ɗaya.

iii.                ‘Yan siyasa kan yi amfani da wasu kalamai irin nasu, wanda ta hanyar nazari ne kawai za a iya warware waɗannan kalaman. Misalinsu a nan kamar Karin magana, habaici, salon magana, baƙar magana da dai sauran kalamai da suka shafi adon magana.

iv.                Wani dalili mai ƙarfi shi ne, ƙoƙarin ɗora jawaban a ma’aunin harshe da salo da sarrafa harshe.

 

1.2 MUHALLIN BINCIKE

Kafin shiga bayani kan muhallin bincike, yana da kyau a dubi ma’anar muhalli ta ra’ayin masana kamar haka:

 

Sabo, (2015) ya ce, “Muhalli shi ne mazaunin da ke kewaye da mutum da dukkan abubuwan da ke taimakawa rayuwarsa ta yau da kullum. Muhalli ya samu ne ta hanyar hikima da basira da Allah Ubangiji ya yi wa ɗan’adam”.

 

Sa’ad (1981) “Yana kallon muhalli a matsayin tsare-tsaren da magina ke yi a ƙasar Hausa da kuma irin ƙyalle-ƙyallen da suke amfani da shi don nuna ƙwarewa fagen samun muhalli da kuma amfani da wasu al’adu.

Begery (1993:797 a ƙamusunsa mai suna “Hausa English Dictionary” ya kawo ma’anar muhalli da cewa “Muhalli shi ne muhallinka”.

 

Don haka, muhalli shi ne wani abu da ke kewaye da mutum, kuma wanda ya shafi rayuwarsa. Muhalli kan iya zama wurin zamanka da al’ummar da ke tare da kai da dukkan abin da ya shafeka.

 

Wannan bincike an gudanar da shi ne a cikin jihar Zamfara musamman a Gusau Babban Birnin jiha, kasancewar a nan ne ake gudanar da ko gabatar da jawaban da Gwamnoni kan yi ranar rantsar da su, kuma a nan ne dukkan ma’aikatun Gwamnati suke, kuma a garin Gusau ne na samu dukkanin bayanan da na buƙata.

 

1.8 MANUFAR BINCIKE

Manufar wannan bincike ita ce a rubuta wannan kundi, domin ya zama cigaba a kan wasu ayukka da suka gabaci wannan. An yi rubuce-rubuce da yawa a kan fannoni daban-daban, masu dangantaka da harshe da adabi da kuma al’adu, a wannan sashe na nazarin Hausa.

 

Sani, S. (2011) a littafinsa mai suna “Political Language and Hausa Leɗical Eɗpansion” ya bayyana jawaban ‘yan siyasa da ire-iren harshen da suke amfani da shi wajen tafiyar da harkokinsu na siyasa a cikin al’umma.

 

Manufar wannan bincike shi ne zai taimaka wajen fahimtar harshe da tasirinsa, musamman ta fuskar yin amfani da jawaban da Gwamnoni kan gabatar. Yin nazari irin wannan a cikin al’ummar da ke fama da siyasa zai taimaka wa ɗalibai da masu sha’awa har ma da Malamai wajen bunƙasa tunanensu, ta hanyar kawo ayyuka irin wannan, wajen fahimtar siyasa ta hanyar manufa da salo da ‘yan siyasa ke yi don samun biyan buƙatunsu, tare da fatar ya zama jagora ga masu buƙatar gudanar da bincike irin wannan.

 

1.4 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

An bi hanyoyi daban-daban domin samun nasarar gudanar da wannan bincike ta hanyoyi daban-daban kamar haka:

Waɗanda suka yi aiki da ya yi shige da wannan domin fahimtar yadda za a tsara aikin.

 

Bayan wannan kuma sai kundayen bincike kama daga digiri na farko da na biyu har zuwa na uku. Haka ma, maƙalu da mujallu da jaridu duk suna cikin hanyoyin da aka tsara bi domin samun nasarar binciken.

 

Haka ma, an tsara duba kundayen da suka ƙunshi jawaban gwamnonin cikin abin da za a duba, domin su ne suka ƙunshi jawaban da za a yi nazari a wannan binciken.

 

Wata muhimmiyar hanyar ita ce, ta bin ma’aikatun gwamnati da hukumominta waɗanda ke da alaƙa da wannan bincike tare da bin ɗaiɗaikun mutane domin cimma nasarar aikin.

 

1.5 MUHIMMANCIN BINCIKE

Kasancewar duk wani aiki ko wani abu da mutum zai yi ko zai gabatar to yana da muhimmanci. Kafin nan bari a duba ma’anar Kalmar muhimmanci kamar yadda ya zo a ƙamusun Hausa.

 

A cikin ƙamusun Hausa (2005), sun bayyana ma’anar muhimmanci da cewa “Abu mai daraja wanda yake da amfani ƙwarai da gaske ko abin farko – farko da mutum ya yi.

Daga cikin muhimmancin bincike a nan akwai:

i. Kasancewar bincike ne na farko da aka fara gudanarwa a kan “Nazarin Jawabin Kama aiki na Zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara a shekarun 2007 zuwa 2019”

ii. Muhimmanci na biyu da wannan bincike ke ƙunshe da shi, shi ne: Kasancewarsa bincike ne da ya shafi harshe da siyasa, wannan zai taimaka wajen fito da matsayin harshe ga jawabin kama aiki na Gwamnoni a ma’aunin nazari.

 

iii. Wannan aiki zai taimaka wajen ƙara fahimtar da ɗalibai masu nazarin harshe da su mai da hankali wajen nazartar jawaban ‘yan siyasa domin fito da abin da jawaban suka ƙunsa ta hanyar nazari.

1.6 FARFAJIYAR BINCIKE

Wannan aiki ya taƙaita ne a kan dangantakar harshe da siyasa. Saboda haka, akan jawabin kama aiki na zaɓaɓɓun Gwamnonin Jihar Zamfara ne a shekarun 2007 zuwa 2019. Wannan farfajiya ta taɓo nazarin harshe ta fuskar yin amfani da shi a ɓangaren siyasa, da salon jawabin siyasa, haka ma an nazarci sana’o’in al’umma, wannan ya nuna cewa waɗannan fannoni uku kan taimakawa juna. An taƙaita nazarin ga jawabin kama aiki na zaɓaɓɓun Gwamnonin jihar Zamfara  daga 2007 zuwa 2019.

 

1.7 MATSALOLIN BINCIKE

Babu shakka bincike kowane iri ne yana tattare da ɗimbin matsaloli; matsalolin sun fara tun lokacin da aka fara tunanen wannan aiki har zuwa kammala shi.

 

Matsala na nufin duk wani ko wata ƙuntatawa da rayuwa kan shiga ta sarrari ko ta ɓoye, wadda ake gani da wadda ba’a gani da rayuwa ta ci karo da ita.

 

An fuskanci matsaloli daban-daban dangane da wannan aiki daga cikin matsalolin akwai:

Na farko, shi ne ƙarancin lokaci, wannan babbar matsala ce domin bincike irin wannan yana buƙatar lokaci sosai, amma ya zo a taƙaitaccen lokaci.

Na biyu shi ne rashin kayan aiki, wato manazarta, wannan ya kawo matsala wajen jeka-ka-dawo don neman abubuwa da za su taimaka da suka shafi gudanar da binciken.

 

Babba matsalar da aka fuskanta ita ce rashin samun damar hira da waɗannan gwamnonin kai tsaye domin jin ta bakinsu, da kuma samun ƙarin haske ga jawabin nasu.

 

1.8 KAMMALAWA

A taƙaice, wannan babi ya yi magana ne kan dalilin gudanar da bincike da muhallin bincike da manufar bincike da hanyoyin gudanar da bincike da muhimmancin bincike da farfajiyar bincike da kuma matsalolin bincike. Waɗannan matakai ne sahihai dangane da bincike domin su ne ginshiƙai da ke kafa hujjoji; cewa an yi wa bincike shiri na musamman. Bayanan da ke cikin waɗannan ɓangarori sun tabbatar da cewa binciken ya yi amfani da dabaru masu gamsuwa domin samun karɓuwa.

Post a Comment

0 Comments