Ticker

6/recent/ticker-posts

Ganuwar Gusau Da Kofofinta (4)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Ganuwar Gusau Da Kofofinta (4)

NA

UMAR YAHAYA DOGARA

Ganuwa

BABI NA UKU

GANUWAR GUSAU

3.0 Shimfiɗa

A babin daya gabata, watau babi na biyu binciken ya duba ayyukan da suka gabata a wannan fanni, musamman waɗanda suke da ganuwa da ƙofofi. Ban samu wani kundin da ya yi bayani akan, ko nazari gane da ganuwar Gusau da ƙofofinta ba, wannan baba zai yi bayani akan, ganuwar Gusau, watau tarihin Gusau da kuma tarihin ganuwar Gusau da tasirin ganuwa a (gari) da nadewa, wato wanna shine maƙasudin wannan babi.

3.1 Tarihin Gusau

            Allah Ubangiji ya yi halitta ya halici jam’a daban-daban, ya kuma zaunar da halittunsa a ƙasashe daba-daban da kuma wurare, daban-daban, kuma ta haka ne Allah ke azurta bayinsa kuma ya ni’imtar dasu, da abubuwa da yawa, wanda za su yi amfani da su a rayuwarsu ta duniya.

            Gusau ƙasace mai tarin albarka kuma Allah ya ni’imta ƙasar da arziki, da jama’a hazikai, tun a zamanin da har zuwa wanna zamani. Gusau na da sunan da ake mata kiraru dashi “Gusau ta Malam Sambo Kwazo Gusau abinai ya Gusa” wannan kirarin ƙasar garin Gusau wanda yana da ɗaɗɗaɗen tarihi, tin kafin yaƙin kafa daualar Musulunci, wanda shaihu Usman ɗanfodiyo ya yi. Gusau dai tun a zamanin da ƙasace mai ɗinbin tarihi domin ƙasar ta yi fice wurin sha’anin tafiya da mulki da kasuwanci; da aikin noma da masana addini Musulunci.

            Gusau dai ta samo asalinta ne daga kalmar Hausa watau (Gusau) wanda Hausance ake nufin mutum ya matsa, ko kuma kamar a ce mutum ya dan ƙara tafiya gaba ko ya matsa a nan, dai ya danganta ga yadda mutum ya fahimci kalmar Gusau a hausance. (Gusau ta Malam Sambo 2012).

            A shekarar (1811) kimanin shekara (207) da suka gabata bayan tasow a daga garin “Yandoto” a shekar (1806). Garin Gusau yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan tsohowar jahar Sakkwato wato, kafin daga bisani ya zama babban Birnin Jahar Zamfara a shekara (1996). Garin Gusau yana kan titin Sakkwato zuwa zariya ne, kimanin kilomita (179) kilimita (2010) tsakanin su da Sakkwato. Daga gabas garin Gusau ya yi iyaka da kasar Katsina da kwatarkwashi, daga arewa kuma yayi iyaka da Ƙaura-Namoda, a ya yin da ya yi wata iyakar da garin Bungudu, daga Yamma a aЪan garen kudu kuma ya yi iyaka da Ɗansau.

            Almajirin Shaihu Usman Ɗanfodiyo ne, watau Malam Sambo ɗan Ashafa, ya kafa Birnin na garin Gusau wanda yake shi da jama arsa. Wajaje shekarar (1214H/1799M). Kafuwar wannan garin Gusau ta faru ne a Sakamakon umurnin da Shaihu Usman Ɗanfodiyo ya bai wa Malam Sambo da jama’ar su, bayan da “Yandotawa suka bi su da bakar yadiya, har sunka yi yunkurin kasha shi Malam Sambo inda aka kasha wani maharbi wanda ya bashi kariya. Malam Sambo Ɗan Ashafa da jama’rsa. Sun rike wanan sabon wurin nasu, matsayin wurin ribadi, wato cibiyar da zasu ci gaba da neman ilimi da bayar dashi, da kuma shirye-shiryen yaƙar ‘Yandotawa, domin kuwa hijirar da suka yo daga ‘Yandoto ba ta sa sun tsira daga makircin mutane garin na ‘Yandoto ba, na ƙoƙarin shafe hasken addini Musulunci a ƙarƙashin jagorancin Shaihu Usman Ɗanfodiyo. Malam Sambo Dan Ashafa da jama’ar sa sun sami nasarar kammala waɗannan  shirye-shirye  na yaƙi a cikin tsawon shekaru bakwai. A shekarar (1121H/1806M). Allah ya basu nasarar cinye ‘Yandoto da yaki a cikin dan kankanin lokaci, bayan yaƙin Alwasa (Gusau da Gusau:1984)

            Wannan nasara da Malam Sambo, da jama’ar sa suka samu kan ‘Yandotowa bata basu dammar mike kafa su zauna lafiya a sabon garin su na gusau ba, domin kuwa ‘Yandotawa da uwayen gidansu da magoya bayansu basu saki kariba, sai suka ci gaba da ƙoƙarin yi wasu Malam Sambo kumun kazar kuku, wanda a sakamako haka ta sa, suka zauna a garuruwa da dama, kamar, sabuwal 1806 zuwa 1807, sanan shekara  1807 suka koma ‘Yar Gusau da garin cideya 1807 zuwa 1811, bungudu 1818-1820 da kiyawa, da Banga 1820-1822, sai kuma suka koma Birnin Kamani, duk a cikin ƙasar Ƙaura Namoda suka shekara ɗaya daga, 1822 zuwa 1823. Daga nan kuwa Malam Sambo Dan Ashafa, ya kafa garin Wonaka inda ya shekara hudu a Wonaka, sannan Allah kuma ya karЪi rayuwar sa shekara 1827.

            Bayan rasuwar Malam Muhammadu Sambo, sai sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya nada babban ɗansa, Malam Abdulƙadir a shekara ta (1827), duk a Wonaka suka ci gaba da zama garin Wonaka har zuwa (1860) inda suka bar garin wonaka, suka koma garin Rawayya, suka shekara biyu 1860-11862 da jama’arsa a Birnin Rawayya, a shekara 1862, suka share wuri suka yi  tajadid ‘Yan bukko kinsu da Masallaci , daga wannan lokaci mutane Gusau suka mike kafa basu sake zuwa ko’ina ba, domin sun a iya kare kansu daga kowace irin barazana da kuma mugunta.

            Bayan kafa garin Gusau da Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa, shine Sarkin na farko, kuma shine ya sara garin Gusau, daga baya an yi ta yin sarakuna da dama tun daga wannan lokaci har yau. Bayan rasuwar Malam Sambo Ɗan Ashafa, Ɗan sa Malam Abdulkadir ya gaji wannan sarautar ta Sarkin Katsinan Gusau, garin Gusau yana ɗaya cikin sababbin garuruwan da aka kafa waɗanda suka maye tsofaffin garuruwan da aka samar shekaru da dama da suka shude, kafin jihadi, kamar Birnin Alkalawa da Kiyawa  da Birnin Samari da Birinin ‘yandoto da suaran su. Almajiran Shaihu Ɗanfodiyo suka kafa garin Gusau.

3.2 Tarihin Ganuwar Gusau

A lokacin da mutane Gusau suka sami zama a garin Rawayya, suka ga kuma sun yi ƙarfi sai suka shirya tsananta wa mutane garin Rawayya suka hana su sakat, harta kai idan Rashin hakimi Rawayya ya sa ake yi shela, sai su kuma su yi tasu shelar, su warware abin da mutanen garin Rawayya suka yi shawarar abin da Rashin ya umarta da aikata. Daga nan sai mutanen garin Rawayya ruka yi shawarar hanyar da za su bi don su fitar da su daga garin su, wani daga cikin su yace, tun da ba mu iya cin su da yaƙi, ba abin da zai sa su bar garin an sai gori, A bari sai Sarkin yakin su ya   fita kilisa bayan gari a rufe kofofi, in ya yi Magana a mayar masa dab aka. Suka shirya da haka, kowa ya yarda da wannan shawar (Hira da M.M.  da ƙungiyar mutane a 1976 da M.M.W da ƙungiyar mutane a 1978).

Bayan wannan shawarar rannan sai sarkin yaƙi Salihu Ɗan Kambo cikin mutanen Wonaka ya fita kilisa da marece. Ko daya dawo, sai ya tara da an rufe dukkan ƙofofin kowace ya zagaya, sai ya tarar da ita a kullace. Daga nan ya koma ƙofar da sarkin ƙofa yake zaune, ya nemi ya buɗe masa yaƙi, illa ya ce masa “kai ku gudu ku ba mu wuri na ki bude ma, ai ga kangon uwayenku can kun baro kun zo nan gari wasu kuna kaba” wannan jawabi na Sarkin ƙofa ya yi wa Salishu Ɗankambo zafi, sai ya cewa Sarkin ƙofa “ka gaya wa duk wanda ke cikin zuriyarmu ya isko ni kangon uwayen namu gobe da safe, ni na tafi” Sarkin yaki Salihu Ɗankabo ya kuma tafiya tar da zagin sa har suka isa tsohon wurin nan nasa na farko, suka kwana a nan (Hirar da M.A.D ya yi da kungiyar mutane 1976) kuma yana gabin sun yanke shawara su sanya mutane su dinga yi masu najasa a bakin ƙofofin bukko kinsu, kuma idan sallah karama ta zo su riga su zuwa idi, idan suka fita daga baya. A rufe masu ƙofofi haka kuwa ta faru, lokacin da Sallah karama tayi, sai mutanen garin Rawayya suka shirya tun da wuri, suka fita suka yo sallar idinsu. Da mutanen Gusau da na Wonaka suka ce masusu fita zuwa idi, sai suka mayar masu da cewa har sun gamo tasu sallah. Don haka, da jama’ar Sarkin Kastina Abdulkadir suka fita zuwa idi, sai mutanen garin Rawayya, su ka rufe kofofin su. Suka nemi a bude masu, aka kiya har ma dai suka yi masu gorin das u zarce zuwa garinsu na farko daga nas, sarkin yaki Salishu Dankabo ya daura kayaa sirdin dokinsa, ya jawo ta har zuwa tsahon wurinsu, wato y’ar Gusau,ya bude hanya ga mutane, amma sai ya gurgusa gaba kadan da ‘yar Gusau ya zabi wuri. Da mutane suka iso aka ci gaba da gyara wuri, aka kafa wa Sarkin Katsina Abdulƙadir bukkokin sa, sai kuma na Malam Muhammad Modibbo da Ɗangaladima Usamatu da shi kansa Salishu Ɗankaboda liman Muhammadu babba da sauransu. Haka dai mutane Gusau suka dinga tasowa daga zama har suka dawo wannan wuri sai suna kiran shi da Gusau. Wannan kuwa yafaru ne a shekara ta 1275 zuwa 1862. A lokacin da aka yi wata wuta wadda ake kira wutar A’isa a garin Rawayya a 1862 ya ƙara karfafa wa mutanen garin Gusau ƙwarin guiwar barin Rawayya domin mafi yawan garin wuta ta kone shi. Bayan komawar su Gusau a zama na biyu wato sabon zama ya farune a farkon sarautar Sarkin Musulmi Amadu Atiku a shekara (1859-1866) Bayan mutane garin Gusau sun koma wurin su na farko lokacin Sarkin Katsina Abdulƙadir shekara 1827 – 1867. A lokacin ne aka gina garin Gusau da ganuwa, samin kariya ga mazauna wannan gari domin taken ƙara jawo masa bunkasa da haЪaka ta hanyoyi da yawa.

            A lokacin da mutanen garin gusau suka dawo wurin tahanyar kewaye shi da shigen ƙaya. Wannan kuwa ya auku ne tun zamanin Malam Muhammadu Sambo ɗan Ashafa har zuwa farko da tsakiyar sarautar Sarkin Katsinan Gusau Abdulƙadir. A zamanin Sarkin Katsina Abdulƙadir, Sarkin Musulmi Amadu Atiku a shekarar (1859) ya yi wa Sarkin Katsinar a lokacin daya je yi masa muba’yi’a bayan nada shi Sarkin Musulmi. Alkawarin ya sa a gine garin Malam Muhammadu Sambo ɗan Ashafa da ganuwa.

            Don haka, ya umurci sarakunan garuruwan dake makwabtaka da garin Gusau dasu taima ka wajen gine garin na Gusau da ganuwa. Daga cikin waɗanda suka taimaka wurin gina ganuwar Gusau, suka turo mutanen su, akwai Sarkin kiyawa Jibri na Ƙauran Namoda, da Sarkin Fulani Bundgudu Muhammadu da mutanen Kwatarkwashi, da kuma mutanen Garin rawayya da suaran su, duk sun zo sun taimaka kwarai wajen wannan aikina gina ganuwa. Wanan shine lokacin na farko da garin Gusau ta fara samun ganuwa ginanna da ƙasar wato yambu mai ƙwari tare da yi ma ta ƙofofi guda tara. 

            Bayan haka, a zamanin Sarkin Katsinan Gusau, Muhammad modibbo shekarar (1867) aka sake faɗaɗa garin Gusau da ganuwa a sana diyyar zuwan wasu mutane. Shi wanna ƙari ya haɗa da unguwar da ake kira Rahaji wadda ta kunshi mutane Abarma da Janyau da wasu Rahazawa. A lokacin ne aka sami kofar Rahaji haka kuma an daɗa faɗaɗa ganuwar ta bangaren kudancin garin ya yi da haza da abokin shantali da dan’uwansa Malam Umaru suka zo Gusau.

            A zamani Sarkin Katsinan Gusau Muhamamdu Tuburi; (1876 – 1887) an ƙara samun bunƙasar, garin da suka haɗa da shiyar Birnin ruwa a zama cikin ganuwa. Amman a lokacin sarkin katsinan Gusau, Muhammadu giɗe (1887 – 1900) ne aka haɗa Birnin haza da Birnin ruwa suka zama shiyya ɗaya da sunan Birnin haza.

            Ganuwar Birnin Gusau ta sake samun bunkasa da haЪaka a zamanin Sarkin Katsinan Gusau, Muhammadu Murtala (1900-1916). Ƙarin ya auku ne ta wajen yamma maso arewa wanda ya sat a hada da makabarta da kuma gandun Sarki,  zuwan wanna lokacin ganuwar Birnin Gusau ta sami ƙofofi guda tara (9) sune; ƙofar Rawayya, ƙofar Katsaura, ƙofar Kwatarkwashi, ƙofar Goje, ƙofar Dogo/dokau, ƙofar Tubani, ƙofar Jange, ƙofar Mani da ƙofar Matsatstsa. Ginin ganuwa watau babbar kariya ce da samun ci gaban gari na son ya bunƙasa ya samu ci gaba sosai da haЪaka da yawaita  mai amfani, to ginin ganuwa yana daga cikin abubuwan da ke samar da leka. Kuma gina ganuwa yana daga cikin tsarin tafiya da har kofofin manya dauloli don kariya ta sosai. Kamar Kano da Katsina da Zazzau, duk sun samar da ganuwa har a yau wasu wurare akwai sauran burburshinta. 

            Ganuwar garin Gusau dai tun zamanin Sarkin Katsinan Gusau Malam Muratala bata ƙara samun wane bunkasa ko kum kari ko habaka daga lokacin ba’a ƙara faɗaɗa garin Gusau da ganuwa ba.

3.3 TASIRIN GANUWA (A GARI)

Ma’anar tasiri: Masana daban-daban sun tofa albarkacin bakin su akan wannan kalma ta tasiri, kamar haka; Ibrahim. M (1985) ya bayana Kalmar tasiri da cewa, al’adar da wani yakan yi wadda a da can ba’a san da ita ba. Inda ya ƙara da cewa, hakan na faruwa ne a sanadiyyar zamantakewa da cuɗanya da juna ta fuskar siyasa da addini.

Uwaisu. A (2007) ya fassara Kalmar Tasiri da cewa asalinta Kalmar larabci aka aro, wadda ke da sigar kamar haka “Ta’asiri” wadda kuma a larabci a ke nufin mamaye wani abu ko wata al’ada. A Hausan ce kuma, kalamar na nufin yadda wani abu yake mamaye ko canza sigar wani abu, ko kuma ya canza al’adar da wani yake yi wadda da can ba’a san shi da ita ba.

Bashir A. (2001) ya bayyana Kalmar tasiri da cewa, kalma ce ta larabci da. Hausawa suka yi mata kwaskwarima ta zama ta su. Basher yace, kalamar tasiri na nufin abu ya kama mutun har ma ta kasance ya yi ƙarfi a zuciyarsa, haka kuma ya fassara kalamar tasiri da cewa yadda wani abu daban yake canza ma wani abu yanayi, ko ya ƙara ma wannan abun kyau da bunƙasa, ko kuma ya haifar ma da abin naƙasu.

Babu wani abu da wata al’umma ko wani mutun zai aikata ba tare da makasudin aikata wannan abin ba. Haka kuma, akwai wata manufa ta musamman wajen aikata wannan abin, sai dai abin yana iya kasancewa mai kyau ko kuma mummuna, ya danganta yadda abin ya yi tasiri a zuciyarsa, ko kuma yadda abin ya yi tasiri a ala’adar al’umma ko ƙasa.

Domin haka, wannan babi zai ci gaba da bayyana irin tasirin ganuwa a gari. Hausawa basu da ganuwa ga al’adarsu ko adabin su, amma tasirin hulɗa da mutanen shingai na ƙasar mali, da Hausawa sun kayi a zamanin da sun ko yi yadda ake yin ganuwa, iri daban – daban da kuma sanin amfanin ganuwa da muhimmancinta. Wanna hulɗa ta faru ne, tun a karni na shida (6), daga lokacin Hausawa suka fara tunanin gina ganuwa a ƙasar Hausa, kuma sun samu nasarar gina ganuwa, daga bisani Hausawa sun ci gaba da amfani da ganuwa a kasashesu da daulolinsu, har zuwa ƙarni na goma sha tara, bayana rushewar daular Shaihu Usman Ɗanfodiyo.

Ana amfani da abubuwa da dama, wajen yin ganuwa a ƙasa, kamar dutse ko kuma ƙasar yumbu, ko kaya, ko kuma ayi rame a zagaye gari da s hi da sauransu. Samun ganuwa ga kowane irin gari alamace ta samun kariya ga mazauna wannan gari domin takan ƙara jawo masa bunkasa da haЪaka ta hanyoyi da yawa. Domin haka yana da kyau mufadi irin matsayin ganuwa da tasirinta.

Duk tsofaffin birane a ƙasar Hausa waɗanda aka kafa, kafin daulolin da waɗanda aka kafa bayan kafuwar dauloli ko bayan jihadin Shaihu Usman Ɗanfodiyo suna da ganuwa. Tsofaffin birane kamar su, Kwatarkwashi da Birnin ‘yadoto da Birnin Katsina da Zazzau da Daura da Gobir da Kabi da kuma Birnin Kano, da sauransu. Duk suna da ganuwa.

Tasirin ganuwa a gari shine, domin a kare gari, daga har-hare da yake-yake da suka yi yawa a zaminin saboda tarihi ya nuna cewa; Daular Birnin Kano tasha karawa da Daular Katsina da Zamafara da Zazzau kai har ma dasu Damagaram. Domin haka, sai a gina ganuwa saboda a kare birane da jama’arsu, daga hari ko yaƙi, ko wani farmaki da barazana.

A cikin ƙarni na sha biyu (12) kusan shekara ɗari tara (900) da suka gabata aka fara gine ganuwa a garuruwa ƙasar Hausa ya kasance tun kafin ƙarni na goma sha bakwai, har zuwa karnin na goma sha tara (19), bayan jihadin Shaihu Usman Ɗanfodiyo, kafin zuwan turawa mulkin mallaka ƙasar Hausa (1903), aka gina ganuwa kuma duk manyan dauloli sun mallaki ganuwa domin sanin irin tasirinta a zamanin da.

Saboda haka, dole ne kowani gari ya mallaki ganuwa, domin duk lokacin da ƙaasa bata da ganuwa a kowane lokaci za a iya shigowa a cisu da yaƙi, kuma a kama mutane ƙasar a maida su bayi, kuma a mallake masu dukiya, daga wannan lokacin ana ruguje wannan daula, kuma za a mallaka wannan ƙasa sakamakon an ci su da yaƙi.

Amma saboda irin tasirin da ganuwa take dashi, ba za a shigo ƙasa ba kai tsaye bare a kawoma mutanen gari farmaki ko yaƙi ba, ko a masu wata barazana ba, har a ci su da yaƙi ba. Sai dai in yaƙi ya haɗa wata ƙasa da wata kasa a lokacin sai a yi wasika da yarjejeniya za a haɗu domin yin wannan yaƙi, sai a saka rana da lokaci da za a haɗu domin karawa da gwabzawa a fagen yaƙi.

Har way au; cikin tasiin ganuwa a gari, dole ne duk wanda zai shiga ƙasa, sai an san shi, kuma an san ko daga, inda yake, da kuma makasusin baro ƙasar sa, ta haihuwa. Sabanin a yau da muke a ciki.

3.4 Naɗewa

            Waɗannan su ne, abubawa da suka samu a cikin wannan babi na uku, inda aka fara da shimfida kuma sai aka kawo, tarihin garin Gusau, sai kuma aka kawo takaitaccen tarihin ganuwar Gusau, sai kuma ƙarshe aka yi bayanin tasirin ganuwa a (gari) da kuma muhimmancinta.

Post a Comment

0 Comments