Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Ganuwar Gusau Da Kofofinta (2)
NA
UMAR YAHAYA DOGARA
BABI NA ƊAYA
1.0
Shimfiɗa
Wannnan Bincike zai
yi magana akan ɗaya daga cikin
nau’oin al’adu al’umomi da rayuwarsu, har ma da tarihinsu.
Tarihi abu ne wanda yake sanar da
ama’a rayuwar al’umomi da suka wuce dangane da halin zamansu, da tattalin
arzikinsu, da sana’ar su, da al’adunsu, da ilimin su, da suaran abubuwan da
tarihi yake dubawa.
Duk da cewa rubutu a
kan tarihin kowane gari abu ne mai wahala da neman dogon binickie, domin gudun
rikitarwa da kuma buyar diddigin littattafan da aka, rubuta, domin kokarin
tabbatar da hakikanin gaskiyarsu da kawar da shakku ga al’umma.
Wannan bincike da za
a gabatar an laƙaba masa sun “Ganuwar
Gusau da Ƙofofinta” kuma an
rubuta shi da nufin ya ba yarda tarihin ganuwar garin
da bunkasar da mutane garin na farko, da kuma Ƙofofin
ganuwar Gusau.
1.1 MA’ANAR GANUWA
Sa’idu Muhammad Gusau
(2012) da Bello Muhammad (2012) cikin littafin “Gusau ta Malam Sambo” Sun bayyana
cewa; Ganuwa wata babbar kariya ce, mai muhimmanci a
gari. Sun ƙara da cewa; Ganuwa
da ɗaɗɗiyar
al’ada ce da aka daɗe ana ginawa tun
zamani mai nisa. Ta hanyar ganuwa ake gane faɗin gari da kuma yalwarsa da tattalin arzikinsa da
zamantakewa mai nagarta.
Haka zalika, wadannan
masana (2012) sun ƙara da cewa; Ganuwa tana taimakawa wajen bunkasar gari,
tare da bashi kariya da kuma tsaro. Domin gujewa farmaki ko hare-hare da yaƙe-yaƙe.
Gina ganuwa yana ɗaya
daga cikin tsarin mulkin manyan daulolin sarakuna kasar Hausa, kamar su: Kano
da Katsina da Zazzau da Sakkwato da Zamfara da Sauransu. Duk suna gina ganuwa
ne domin samun kariya ta musamman. Daulolin ƙasar Hausa sun jima
suna gina ganuwa tu zamanin kaka – da kakakanni.
Munir M. (2017) ya
bayyana cewa “ganuwa na nufin kare kowane irin gari ko birni daga cin zarafin
was, kuma tana taimakawa wajen samam masu ‘yanci da barrenta daga abokan gaba.
Ishak. M. (2017)
Ganuwa na nufin gina wani gin ko alama a gari don samun kariya da hare-haren ko
farmaki daga abokan gaba, da kuma gina kofofin cikin ganuwar.
Hashim Gumel M.
(1998) ya bayyana cewa, birane a ƙasar Hausa waɗanda aka kafa bayan kahuwar dauloli
da bayan jihadi suna da ganuwa. Tsofaffin Birane kamar su: Kwatarkwashi da
Birnin ‘yandoto
Birnin Daura da Birnin Katsina da Birnin
Zazzau da Birnin Kano da Birnin Wudil, duk suna da ganuwa. A kan
gina ganuwar gari ne kuwa domin a kare gari daga har-hare da suka yi yawa a
wuncan zamani.
Haka zalika,
Hashim Gumel (1998) ya bayyana cewa Birinin Kano ko a ce
Daular Kano ta sha Karawa da daular katsina da ta Zamfara da ta Zazzau, kai har
ma da su
Damagaram, da dai sauransu, ya ƙara da cewa; a na gina ganuwa ne domin a kare
Birni da jama’arsa, kuma hasashe ya nuna cewa a cikin ƙarni
na sha biyu (12) (kusan shekara 800 da suka wuce) aka fara gina ganuwar Birnin Kano tun a wannan karnin zamanain sarkin kano. Gajimusu
wanda ya yi zamani a tsakanin shekara 1095 zuwa 1134. An kammalata a zamanin
sarkin kano Jusa.
Har ila yau, Hashim
Gumel (1998) ya ci gaba da cewa; inda za’a iya nuna muna majigin yadda
ganuwowin birane suke a ƙasar Hausa kafin zuwan turawa da an burge mu
da kuma mun fahimci cewa kakanninmu wayayyu ne, kuma basira da fasaha ne kudu ba yadda turawa mulki mallaka suka dauki bakar fata a
matsayin koma bayan halitta, amma da suka zo ci Kano da yaki sai da
suka sarawa kakanninmu tare da girma mawa a gare su.
Bisa
dalilan da suka gabata zamu iya fahimtar dalilin gina ganuwar gari, kuma kamar
yadda aka fada a baya ba. Birnin Kano ne kawai ke da ganuwa ba. Manyan
Biranen ƙasar Hausa kamarsu; Katsina da Zazzau da Sakkwato da
Daura da Zamfara duk suna da ganuwa, to amman in anje yau kila sai dai a tara
da ƙofofi kawar, babu ganuwa. Kananan garuruwa ne
kamar su, Ƙausani da Wudil da ‘Yandoto da Kwatarakwashi sune da
ganuwa. Ana kyautata zaton cewa kafin zuwan turawa akwai garuruwa fiye da dari
masu ganuwa a ƙasar Hausa, amma yanzu duk sun zama tarihi saboda sakaci
da rashin kishin tushen da mutun ya fito.
Haka zalika, akwai
wani babban abin lura anan. Wannan abun kuwa shine, duk lokacin da ake yi
maganar ganuwa to dole ayi maganar ƙofofinta, domin kowace irin
ganuwa a duniya tana da ƙofofi kamar ganuwar Kano tana da Ƙofofi
kamar haka; Ƙofar Mazugal da Ƙofar Wambai da Ƙofar
Ruwa da Ƙofar Dukawuya da ƙofar Adama da Ƙofar
Dan Agundi da Ƙafar Mata da Ƙofar Na’isa da Ƙofar Kansakali da Ƙofar
Famfo da sauran su.
Har ila yau (Isma’il
Abbas) ya bayyana cewa ganuwar a Zazzau ita ma tana
da Ƙofofi kamar haka; Ƙofar Gayan da Ƙofar
Kuyan Bana, da Ƙofar Tukur – Tukur da Ƙofar Doka da Kuma Ƙofar
Galadima da Ƙofar Kibau da sauran su. Husau (Leadership 2017)
Haka kuma. Farfesa
Munir Mamman (2011) ya Bayyana kofofin Katsina da anguwoyinta kuma ya kawo su kamar haka; Ƙofar Doka da Ƙofar Kwa, da Ƙofar
Ƙaura
da Ƙofar Sauri da Ƙofar Durbi da Ƙofar Marusa da suaran
su.
Bisa ga
bayanan da suka gabata, mun fahimci cewa tabbas duk wata ganuwa da take a Ƙasar
Hausa dama duniya baki – daya tana da Ƙofofi, domin haka ne,
wannan binciken zai yi bayanin ganuwar Gusau da Ƙofofinta
1.2
Dalilin Bincike
Kamar kowa ne irin
bincike da a kan gudanar, akan yi shine domin zakulo wasu muhimman abubuwa da
ta yiwu ba a sani bad a farko ko kuma an sani, amma ba’a tara da shiba, ko kuma
ba a tsara shi ba, domin masu nazari, hausawa na cewa “Banza bata kai
zomo kasuwa” Wannan Magana ta yi dai-dai da nufinta na yin wannan bincike. Shi
ya sa naja damara na kuma zage damtse da nufin nazari a kan wannan batu mai
taken “Ganuwar
Gusau da Ƙofofinta”
Masana da manazarta
kamar su; Ferfesa Sa’idu Muhammad Gusau (2012) da kuma Bello Muhammad (2012) da
Ferfesa Munir Mamman (2011) da Isma’ila Abba (2017) da Garba Nadama (1972) da
Sauran su. Wadannan Masana sun nazarci ganuwa da Ƙofofinta, ta fuskar
daban-daban amman basu nazarci ganuwar gusau Da Ƙofofinta ba kaitsaye
a matsayin Ƙundin binciken suba. Amma Farfesa Sa’idu Muhammad da Bello (2012) Sun dan tofa albarkacin bakinsu game da
ganuwar Gusau da Ƙofofinta. Dalilin da yasa aka yi wannan nazarin shine
domin a dora daga gudummuwar da wadannan manazarta, a gano yadda tarihi ya
fayyace ganuwar Gusau da Ƙofofinta.
1.3
Manufa Bincike
A kowani lokaci mutum
yayi nufin yin wani abu, to! Lallai babu shakka
yana da manufarsa ta yin wannan abu. Kamar yadda Hausawa suke cewa” Kowanne
allazi da nasa Amanu” haka ne domin komai baya faruwa sai dai manufa ta yinsa.
Saboda haka babu wani bincike da zai faru ba tare da wata manufa ba.
Babbar manufar wannan
bincke shine a bayyana ganuwar Gusau da Ƙofofinta, tare da yin
tsokaci daga a,l’ada da adabi. Bincike ya Ƙudurin aniya nazartar
ganuwar da tasirinta a Ƙasar Hausa, da kuma yadda Bahaushe da
adabinsa ke kallon ganuwa a rayuwar Zaman duniya.
1.4
Harshen Bincike
Hausawa sun san me
ake kira ganuwa, kuma sun rarrabe tsakani nau’oin ganuwa da muhimmancinta, tare
da tasirinta. Domin haka shi yasa wannan bincike yake
hasashe abu ne mai yi yuwa a sami, kundi ko mukala ko littafi ko jarida, da
suka yi bayani a kan ganuwar Gusau da Ƙofofinta da
yanayinta.
1.5
Farfajiyar Bincike
Tarinin garin
Gusau da Ƙasar Hausa, shi ne farfajiyar wannan bincike, aikin ya taƙaita,
a kan Ƙofofin Gusau. Ganuwar Gusau tana cikin farfajiyar wannan
binciken, saboda haka nazarin ya taƙaita a kan Gusau da kuma Ƙofofinta.
Bugu da kari,
binciken zai yi tsokaci a kan tarihin ganuwar Gusau, da Ƙofofinta
cikin garin Gusau, da tsarin sarakunan Gusau, da wasu unguwanin Gusau, da Gusau
a ma tsayin babban Birnin Jahar Zamfara da sauran su. Saboda haka ganuwar tana
da tasiri mai yawa a cikin gari.
1.6
Muhimmancin Bincike
Ana saran wannan
bincike ya zama mai muhimmanci wajen fayyace ganuwa ga al’ummar Hausa ta fuskar
nazarin ganuwa. Haka kuma, aikin ya zamo mai muhimmanci saboda zai Ƙara
fito da alaƙar da ke tsakanin Ƙofa da ganuwa, da
kuma al’ada da adabin Hausawa, haka kuma ana saran binciken zai taimaka wa
Hausawa su zurfafa tunanin su da ke Ƙunshe a cikin adabin su. Haka zalika wannan
bincike zai kara fito da martabar ganuwar hausawa a duniya da ma kasa baki ɗaya.
Daɗin da ɗawa, wannan aiki zai
zama hanyata taimako ga wadan da suke son ganin ilimin al’ummar su ya haЪaka ta fannin karatu da rubutu sanna kuma
bincike zai zaburar da manazarta al’adun da adabin wajen zurfafa bincike a kan sa
wato a fahimci muhimmancin al’ada da kuma adabi harma da falsafar Bahaushe.
1.7
Hanyoyin Bincike
Kowane bincike na
ilimi na bukatar ingantattun hanyoyin gudanar da shi, a wannan bincike
an yi amfani da amintattun hanyoyin gudanar da bincike. Wato hanyoyin tara
bayanai, da kuma hanyoyin ƙwanƙwance bayanai;
hanyoyin da aka bi wajen tara bayanai sun hada da; shiga ɗakin karatu inda aka
karanta littafai da Maƙalu da ƙundayen bincike da
kuma jarida. An tattauna da mutane domin ƙkara samun haske
wajen tattara bayanai na wannan bincike. A dunkule wannan ita ce
yadda aka ƙwanƙwance bayanai.
1.8
Naɗewa
Wannan babi na ɗaya, babi na ɗaya kunshi da shimfiɗar wannan bincike
baki ɗaya,
inda aka kawo muhimman abubuwa waɗanda
suka haɗa
da; gabatarwa da dalilin bincike da farfajiyon bincike da muhimmanci bincike da
hanyoyon gudanar da bincike. Haka kuma, a cikin manufar bincike, an nuna cewa
manufar wannan bincike it ace zakulo tarihin ganuwar Gusau da kuma ƙofofinta.
Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar
Tarayya Gusau.
Ganuwar Gusau Da Kofofinta (3)
NA
UMAR YAHAYA DOGARA
BABI NA BIYU
WAIWAYEN AYYUKAN DA
SUKA GABATA
2.0 Gabatarwa
Masu iya Magana na cewa “waiwaye
adon tafiya” wasu kuma kance “daga na gaba ake gane Zurfin ruwa” Dangane da
wannan zance na hikima daya gabata, yana da matukar muhimmaci kwarai da gaske a
dubi wasu ayyukan da masana da manazarta suka gabatar, waɗan da suke da alaƙa
da wannan bincike nawa kuma alaƙar zai iya kasancewa ta kusa ko ta nesa.
Wannan babi a dunƙule
ya waiwaya littafai da ƙundaye da muƙalu da sauran
bangarorin da suke da alaƙa da wannna bincike mai suna binciken, na
ayyukan da suka gabata, shine a fayyace ganuwa da ƙofofinta, tare da
tasirinta, kuma binciken ya ƙudiri aniyar nazarin ganuwa da ƙofofinta
bakin gwargwado, domin haka wannan binciken zai yi ƙoƙarin
zaƙulo
waɗansu abubuwa na
tarihin garin Gusau da suka shafi ganuwar garin da ƙofofinta, wannan
shine makasudin wannan babi.
2.1 Gumel H. (1998)
ya bayyana cewa; duk Tsofaffin birane a kasar Hausa waɗanda aka kafa bayan
kafuwar dauloli; ko bayan jihadin shaihu Usman Ɗanfodiyo suna da
ganuwa. Tsofaffin birane kamar su, Kwatarkwashi da Birnin ‘Yandoto da Birnin
Katsina da Kogo da Zazzau da kuma Birnin Kano da Gobir da kuma Birnin Daura,
duk suna da ganuwa. Akan gina ganuwar gari ne domin a kare gari daga har-hare
da yake-yake da suka yi yawa a zamanin da.
Gumel H. (1980) ya
bayyana: Birnin Kano ko a ce daular Birnin Kano ta sha karawa da daular
Katsina, da ta Zamfara da ta Zazzau kai har ma dasu Damagaran. A na gina ganuwa
domin a kare Birni da Jama’arsa; A cikin ƙarni na sha biyu (12)
a shekar 1202 miladiya, kusan shekar dari tara (900) da suka wuce aka fara gina
ganuwar Birnin Kano (Gajimasu). Kamar yadda: Tanko (1996) na sashe labaran ƙasa
na jami’ar Bayero ya yi bayani, katangar ganuwa kano a zamanin ta kewaye bangaren
Dala da Gwauron – dutse ne, har yanzu in aka je wurin ƙofar
Mazugal za’a ga Burbushin ta. Daga nan sai ganuwar ta yi arewa tabi ta wajen
masallacin juma’a na Birnin, sannan ta yi ta wajen asibitin murtala ta mike ta ƙofar
wambai an zagaye Birnin lokacin kenan.
Haka zalika, Gumel H.
(1998) ya ƙara da cewa; ƙarni na goma sha biyar, sabida yawan jama’a
da habakar harkokin kasuwanci. Birnin Kano ya ƙara haЪaka. A sakamakon haka ne sarkin Kano
Muhammadu Runfa, wanda ya ƙara faɗaɗa
ganuwar kano. Tanko, (1996) ya ƙara bayyana cewa Sarkin Kano Muhammadu Runfa
ya ƙara da’irar ganuwar da kusan kasha hamsin daya (51), kuma
ya tayar da gidan masarautar kano ya matso da ita dai-dai inda take a halin
yanzu ta yadda ya shiga sabon birnin. Tunda kafin a yi hakan, inda gindan sarki
yake a halin yanzu a lokacin wajen badalane.
A wanan karo ne ake sami ƙofofi kamar su, ƙofar Gadon ƙaya
da ƙofar Dan Agundi da kuma ƙofa Na’isa har
ganuwar ta tarar da ƙofar ƙansakali.
Har ila yau Gumel, H.
(1998) ya ci gaba da cewa; lokaci na ƙarshe da aka ƙara
faɗaɗa ganuwar Birnin Kano
shine, a ƙarni na goma sha bakwai (17) a zamanin Sarkin Kano
Muhammad Nazaki Sarkin na Ashirin da takwas (28) Gumel H. (1998) ya ƙara da cewa; Wambai giwa shine ya’ yi wannan
gagarumin aiki a lokacin sarki ya tafi yaki da ƙasar Katsina. Garin
cewa shi Wambai giwa bashi da lafiya a lokacin da aka tafi yakin, sai ya yi
tunanin mai zai yi ya burge Sarki in ya dawo, An ce a lokacin da aka yi wannan
aiki sai da a ka yanka shanu ɗari
to ganuwar Birnin Kano da muke gani yanzu, a wannan lokaci ne a ka ginata. Ba za a ce ba’a ƙara yi mata komai ba,
tun daga lokacin har zuwa lokacin jihadi. Babu ko shakka ana yi mata yaЪe sana kuma kyautata. Wannan daliline ya sa
harta kawo yau muke ganin sauranta.
Har ila yau Gumel
H. (1998) ya ƙara da cewa; a taron
cikar Kano shekara dubu (1000) soma mulki, Tanko, (1996) ya yi tambayar cewa da
an ci gaba da faɗaɗa ganuwar Birnin Kano
in da ta kai a halin yanzun har yana cewa; ƙila yanzu da ta kai
kura.
Haka zalika, Hashim
gumel (1998) ya ci gaba da cewa; inda za a iya nuna muna majigin yadda ganuwowi
birane suke a ƙasar Hausa kafin zuwan turawa da an burge mu da kuma mun
fahimci cew Kakanninmu wayayyune, kuma masu basira da fasaha ne, ku duba yadda
Turawan mulkin mallaka suka ɗauki
baƙar-fata
a matsayin kom-bayan halitta, amma da suka zo cin Birnin kano da yaƙi
sai da suka sara wa kakaninmu. Lord Lugard a (1903) da su ka gane da badalar
Birnin Kano. “lokacin da dakarun mu suka iso Kano sun iske wata babbar katanga
mai matuƙar ƙwari wadda ta kewaye Birnin, Wannan Katagar
ta ganuwa, ta kai mil goma shatara da ƙofofi oma sha uku
(13) waɗanda
take dasu “Wannan daliline na ganuwar Birnin Kano ya hana Turawa mulkin mallaka
suka suka shiga cikin garin kano balle har suci daular su da yaƙi.
Sai dai suka haɗa
kai da ɗiyan
sarakuna suka ci kano da yaƙi, da ma wasu garuruwan na ƙasar
Hausa.
Bisa dalilin da suka
gabata; kowa zia iya fahimtar dalilin gina ganuwar gari, kuma kamar yadda aka
faɗa a baya, ba Birnin
Kano ne kawai ke da ganuwar ba. Manyan Biranen ƙkasar Hasau Kamar su,
Katsina da Zazzau da Sakkwato duk suna da ita, to amman in anje yau ƙila
sai dai a tatar da ƙofofi kwai ba ganuwa. ƙanana garuruwa ne
kamar su, ƙausani da Wudil da Daura da ‘Yandoto da Kwatarkwashi sune
da ganuwa. Ana kyautata zaton cewa kafin zuwanTurawan mulkin Mallak akwai
garuruwa fiye da dari (100) masu Ganuwa a ƙasar Hausa, amman
yanzu duk sun zama tarihi, saboda sakaci da rashin kishi tushen da mutum ya
fito.
Wannan aiki na Hashim
Gumel (1998) na da alaƙa ta kusa da wannan aiki da ake gudanarwa ta
la’akari da duka ayyukan sun fuskanci gari da ganuwa, har ma da ƙofofin.
Domin binciken Gumel
(1998) ya tabbatar da samuwar ganuwa a Kano, da kuma kasar Hausa, ya fito da
yadda Hausawa suke kallon ganuwa a matsayin garkuwa ko kariya a gari sannan ya
ambaci ƙofofin Kano, da kuma sunayen su.
Tabbas! Wannan aiki
yana da dangantaka da alaƙa da kut da Kut da binciken da ake gudanarwa,
saboda dukkan su ayyuka ne da suka shafi gari da ganuwa da kuma ƙofofi
sai dai ƙofofinta’ Ake gabar dashi.
Abba, (2017) ya
gudanar da bincike mai suna “Dangantakar tarihi da waƙar
ƙofofin
Kano” Nazari daga bakin Ala” Domin haka a wannan binciken ya tofa albarkacin
bakinsa akan ganuwa da kuma ƙofofin Kano, ya ce, a cikin sarakunana gidan
bagauda ba za a manta da gijemasu ba, domin shi ya halacci jama’ar Kano masu
bautawa Tsumbubura har suka yarda suka taimaka masa ya fara gina ganuwar gari.
Ya fara daga rariya (A tsakanin ƙofar ɗan gundi da ƙofar Na’isa)yayi yamma zuwa ƙofar
adama da ƙofar kansakali. wanda a yanzu ƙofar Adama da ƙofarTuji
Babu su duk da dai bincike ya gano cewa ba a gama ginin ba sai a cikin zamanin
Usman zamne gawa, wato a cikin ƙarni na sha huɗu 1343 – 1349m.
Lokacin da yake-yake
suka fara yawaita sai aka dinga haka kududdufai da fa ganuwa. Dalilin yin haka
kuwa domin hana abokan gaba shi ga gari, da Birnin Kano ya faɗaɗa to sai jama’a suka
mai da gindin ganuwar wajen ɗibar
ƙasar
gini. Ta haka aka din ga rushe wannan ganuwar mai daɗaɗɗen
tarihi, sai da hukumar kiyaye kayan tarihi wato (National Council for Antiƙuities) ta tsawata
kuma ta kawo wadan su gyara daga cikin waɗansu ƙofofin gari.
Haka zalika, Abba
(2017) ya jara da cewa; akwai wani abin lura, domin kowa ganuwa da ƙofofinta
a koda yaushe a tare suke tamakar ɗan
jumma ne da ɗan
jummai, dole ne duk lokacin da ake maganar ganuwa a yi maganar ƙofofinta.
Haka kuma idan a na maganar ƙofofi a yi maganar ganuwar su.
Bugu da ƙari,
Abbas, (2017) ya kawo sunayen ƙofofin Kano na tarihi a bakin Ala, Kamar
haka:
1. Ƙofar
Mazugal
2. Ƙofar
Wamabi
3. Ƙofar
Ruwa
4. Ƙofar
Dukawuya
5. Ƙofar
Adama
6. Ƙofar
Ɗan Agundi
7. Sabuwar Ƙafa
8. Ƙofar
Waika
9. Ƙofar
Mata
10. Ƙofar Na’isa
11. Ƙofar Dawanau
12. Kofar Nasarwa
13. Ƙofar Gadon-Ƙaya
14. Ƙafar Kabuga
15. Ƙofar kansakali
16. Ƙofar Famfo
Shine Wanna bincike
yana da alaƙa da aikin na alaƙar juna ta kut da kut
domin kanun aikinsa shine “Dangan taka da waƙar kofofin Kano
nazari daga bakin Ala” Domin haka Wannan binciken yana da alaƙa
da nawa binciken mai suna “Ganuwar Gusau da ƙofofinta”
Sai’du Gusau (2012)
da Bello Muhammad (2012) sun Bayyan cewa; ganuwa wata babbar kariya ce mai
muhimmanci a gari da take da matukar tasiri da kuma amfani ga al’ummar gari.
Bugu da kari, masana
(2012) sun ƙara da cewa Ganuwa daɗɗar al’ada ce da aka daɗe ana ginawa tun zamani mai nisa. Ta hanyar ganuwa ake
gane fadin gari da kuma yalwarsa da tattalin arzikinsa da zamanta kewa mai
nagarta.
Haka zalika, waɗannan masana (2012)
sun ƙara da cewa; ganuwa tana taimakawa wajen bunkasar gari,
tana da bashi kariya da tsaro. Domin gujewa farmaki ko hare-hare da yaƙe-yaƙe.
Gina ganuwa yana ɗaya
daga cikin tsarin mulkin manyan dauloli Sarakunan ƙasar Hausa, Kamar su,
Kano da Katsina da Zazzau da Sakkwato da Zamfara da sauran su. Duk suna gina
ganuwa ne domin samun kariya ta musamman daga abokan gaba. Daulolin ƙasar
Hausa sun jima suna gina ganuwa tun zamanin kaka da kakakanni.
Wannan littafi na
masan, yana da dangantaka ta kusa da binciken da ake gudanarwa, saboda sun yi
Magana a kan Gusau, da cewa shi wannan binciken ya karkata ne a kan “Ganuwar
Gusau da ƙofofi”
Mamman M. (2011) yayi
tsokaci akan ƙofofi katsina da a guwanninta, kuma ya kawo su kamar
haka:-
1. Ƙofar
Yan Doka
2. Ƙofar
Ƙwaya
3. Ƙofar
Ƙaura
4. Ƙofar
Sauri
5. Ƙofar
Durbi
6. Ƙofar
Marusa da sauran su.
Haka zalika, Munir
(2011) ya ƙara da cewa kasan cewar dole ne duk lokacin da aka yi
magan akan ƙofofi dole ne, a yi maganr ganuwar su, kuma ya nuna cewa
ganuwar katsina ta samu tun zamanin mai nisa, ko tun lokacin kaka – da kakanni
kasancewar har yanzu babu takamammen lokacin da ganuwar daular katsina ta samo
ko an ka yi ta, sai dai hasashe.
Idan aka duba bayanan wannan masani,
za a fahimci wannan aiki ne da dangantaka da aikin bincike da ake gabatarwa,
shi dai wannan an taƙaita akan ƙofofi da ganuwa ne,
shi kuma aikin da ake gudanarwa zai yi bayani ne a kan “Ganuwar Gusau da ƙofofinta”
A Jaridar Hausa (Leadership 2017)
sun bayyana cewa; Ganuwar Zazzau ita ma tana da nata ƙofofi
na tarihi tu ƙarnukan da suka gabata.
Haka zalika Jaridar
Hausa (leadership 2017) sun kawo jerin sunayen ƙofofin Zazzau Kamar
Haka:-
1. Ƙofar
gayen
2. Ƙofar
Tukur – Tukur
3. Ƙofar
Kuyan Bana
4. Ƙofar
Doka
5. Ƙofar
Kibau
6. Ƙofar
Kone
7. Ƙofar
Bai
8. Ƙofar Jatau
9. Ƙofar
Galadima
Muhammad,
(2017) ya yi aiki mai suna “Jiya a yau ƙofofin Zazzau a bakin
Ala” kuma a cikin nasa ya waiwayi tarihin Zazzau da ganuwarta da kuma ƙofofinta,
kuma cikin binciken nasa, ya bada tarihin kowace ƙofa da ke cikin garin
Zazzau, da kuma dalilin yiwa kowace kofa sunan da ake kiranta da shi jiya da
yau.
Haka zalika Muhammad I. (2017) ya
zayyano sunayen ƙofofin Zazzau tare da cikakken tarihin su da dalilin gina
kowace ƙofa da ke cikin garin Zazzau ga sunayen ƙofofin
kamar yadda ya bayyana:
1. Ƙofar
doka
2. Ƙofat
kuyan bana
3. Ƙofar
bai
4. Ƙofar
gayan
5. Ƙofar
galadima
6. Ƙofar
jatau
7. Ƙofar
Tukur – Tukur ko ƙofar kibo
Bugu da
ƙari
Ishak (2017) ya bada tarihin tun daga lokacin gina waɗannan ƙofofin
zuwa yau.
Waɗannan ayyuka na
musamman da aka na zarata kan gari da ƙofofin ganuwa na da
alaƙa ta kusa da aikin da za a aiwatar, domin sun bada
ma’anar ƙofofin da kuma ganuwar su, amma wannan bincike nawa ya ta
allaka ne kan “Ganuwar Gusau da ƙofofinta.
Bello Gusau da Sa’idu Gusau (2012) a
cikin littafinsu mai suna “Gusau ta Malam Sambo” sun tofa alabarkacin bakin su,
akan garin gusau, kuma sun yi bayani Akan ganuwar Gusau da ƙofofinta
da kuma tarihin garin Gusau da ƙofofinta Gusau da wasu unguwoyin Gusau da
kuma Gidajen Sarautar Gusau da tsarin
Sarakunan Gusau da a matsayin babban Birnin jahar Zamfara.
Haka zalika, waɗannan masana (2012)
sun bayyana cewa; ganuwar Birnin Gusau ta sake samun bunkasa da haЪaka a zamani Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu
Murtala (1900-1916). ƙarin ya auku ne ta wajen yamma masu arewa
wanda yasa ta hada da makabarta da kuma gandun sarki. (Hararar mu da M. U. A. G
Gusau ta samu bunƙasa lokacin ganuwar Gusau ta sami ƙofofi
har gusau tara (9) ga sunayen su kamar haka:-
1. Ƙofar
kwatarkwashi
2. Ƙofar
dogo
3. Ƙofar goje
4. Ƙofar
tubani
5. Ƙofar
jange
6. Ƙofar
matsattsa
7. Ƙofar
rawayya
8. Ƙofar
Katsaura
Domin
Haka, wanna littafi yana da dangantaka da aikin da ake gudanarwa, saboda
dukkansu ayyuka ne da suka shafi Gusau, domin haka suna da alaƙa
da kuma danganataka ta kusa da wannan bincike mai suna “Ganuwar Gusau da ƙofofinta”.
Bisa ga
bayanna da suka gabata, daga ayyuka ne musamman da aka nazarta a kan gari da
ganuwa da ƙofofi, na da alaƙa da binciken da ake
aiwatarwa mai taken “Ganuwar Gusau da ƙofofinta”.
2.2 Naɗewa
Wannan babi ya yi bitar ayyukan da
suka gabata a akan ganuwa da ƙofofi, har mada garuruwan ƙasar
Hausa masu ganuwa. Babin ya waiwayi wasu ayyukan da suka gudana a kan Gusau da
ganuwarta harma da ƙofofinta a dunkule, bitar waɗannan ayyuka ya jagoranci wannan bincike da bayanai masu
yawa game da abin da manazarta suka gano a al’adun Hausawa, da kuma ƙasar
Hausa, wanda ya nuna akwai alaƙa tsakanin al’umar Hausawa da al’adunsa da
kuma tunanain su game da ganuwa da ƙofofinta.
0 Comments
Post your comment or ask a question.