Being A Paper Presented at the National Conference, Theme “Kano: Politics, Economy and Society from the Earliest Times to the Present” Organized by Faculty of Humanities, Yusuf Maitama Sule Uniɓersity, Kano. On Monday 15th – Wednesday 17th April, 2019.
Nazari
Kan Kasuwancin Littattafan Hausa: Gudumawarsu Wajen Haɓaka Tattalin Arzikin Ƙasa
Ibrahim
Baba (Ibrahim Garba Nayaya)
Postgraduate
Student, Department of Nigerian Languages and Lisguistics, Bauchi State Universiry,
Gadau. (Masters in view).
07066366586,
08125351694
Email:
ibrahimba182@gmail.com
Da
Audu
Baba
School
of Postgraduate, Department of Nigerian Language, Bayero Uniɓersity Kano. (Masters
in view)
08069580413
Email:
abdullahibabanguru@gmail.com
Da
Saminu
Sabo
College
of Education and Legal Studies Nguru, Yobe State
1.0 Gabatarwa
Rubutu hanya ce sassauƙa ta isar da saƙo ga al’umma, wannan
rubutun kuwa ya shafi na zube ne, ko waƙa ko kuma na wasan
kwaikwayo. Wannan hanya ta rubutu ta zaburar da ‘yan ƙasa ta fuskoki da
dama tun daga lokacin da suka buɗe idanuwansu a kai.
Wannan rubutu ya kasu zuwa gida uku, wato zube (ƙagaggen labari), waƙa da kuma wasan kwaikwayo.
Waɗannan kashe – kashen
yana ƙunshe da ire – iren mutanen da suka ƙware wajen tsara su
da rubuta su. Ɓangare mafi girma cikin waɗannan nau’o’i shi ne ƙagaggen labari.
Marubuta ƙagaggun laraban Hausa
ba ya ga zaburar da ‘yan ƙasa da suke yi ga rubuce – rubuce, sun bayar da
muhimmiyar gudumawa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasa. Rubuta ƙagaggun labarai a
yau, ɗaya ce daga cikin
sana’o’in da suke tsakanin al’umma, musamman mata da matasa maza. Sana’ar,
wadda take ta ƙirƙirar labari ce da tsarawa bisa baiwa da hikimar da Allah
ya huwace wa bawa. Ta irin wannan hanya ce wasu rukunan al’umma rayuwarsu
kacokan ta ɗoru a kan wannan
sana’a. Baya ga nau’in mutanen da suke ƙirƙirar labarin, su
tsara, akwai wasu nau’o’in mutane da suka yi tarayya a kai wajen yaɗuwar waɗannan littattafai.
Cikin wannan takarda an yi ƙoƙarin bayyana ire –
iren mutanen da rayuwarsu ta jingunu zuwa ga wannan sana’a, wadda jingunuwar
rayuwar tasu ya shafi cinsu, shansu da tufafinsu. Sai ya kasance bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ne, domin su a
karan kansu suna samun biyan buƙatunsu na yau da gobe, sannan kuma
suna bayar da haraji ga hukuma, wanda haraji ga hukuma haɓaka tattalin arziki
ne ga asusun ƙasa.
1.1 Ma’anar Ƙagaggun Labarai
Masana sun tattauna wajen bayyana ma’anar
ƙagaggun
labarai. Misali: Yahaya (1992:65) ya bayyana shi da cewa, “Na ɗaya daga cikin
rukunin adabin Hausawa na zamani da masana adabin Hausa suka bayyana shi da
‘zube’, wanda shi ne na farko a cikin rukunin, kafin waƙa da wasan
kwaikwayo.”
Shi kuwa Mukhtar (2016:2) a wata
lakca da ya gabatar, ya ce, “Shi ƙagaggen labari cike
yake da zantukan hira da nishaɗi, wanda ba da gaske ya taɓa faruwa ba, saboda ana samar da shi
ne kawai don nishaɗantarwa.”
Duba da waɗannan ma’anoni da
suka gabata, ƙagaggun labarai na Hausa, su ne ire – iren labaran da ake
samu a rubuce ko da ka, domin samun abokin hira da ɗebe kewa ta hanyar
karantawa ko sauraro. Tun bayan da Hausawa ‘yan ƙasa suka koyi karatu
da rubutu, sai suka riƙi hanyar rubuta ƙagaggun labarai a matsayin
wata hanya ta sana’a, musamman ta la’akari da yadda ake ƙara samun yawaitar
masu karantawa, wanda hakan sai ya haifar da yawaitar marubuta waɗannan ƙagaggun labarai, ciki
kuwa maza da mata, matasa da manya.
1.2 Tarihin Rubutun Ƙagaggun Labarai Na Hausa
Yahaya (1988:77) ya bayyana tarihin
rubuce-rubuce na ƙagaggun littattafai bai daɗe sosai ba, domin an same su ne bayan
shigowar Turawa, musamman masu bincike da yaɗa addinin Kirista irin su J.F. Schon. Schon
ya yi rubuce-rubuce duk da kasancewar mafi yawan littattafan na shi sun fi kama
da na yaɗa addinin Kirista,
face littafinsa na Letafin Magana Hausa (1857) da ya yi kama da zube, sai na ƙarshe wato ‘African
Proɓerbs, Tales and
History (1886)’ da ya fi kama da ƙagaggun labarai. Yunƙurin haɓakarsu kuwa, ya biyo
bayan zuwan Turawa ‘yan mulkin mallaka a waɗannan rubuce-rubucen a cikin zube na Hausa.
Misali an samu Frank Edgar, Fletcher, Rattray R.S. da Whitting. Sai kuma
lokacin da aka kakkafa makarantun boko a Jihar Arewa. Misali a lardin Sakkwato
a 1905 ƙarƙashin shugabancin Mr. Burden, wadda aka rufe ta sakamakon
rashin kai yara. Sannan a 1909 Gwamna Lugard ya sa Mr. Harns Ɓischer wato (Ɗan Hausa) ya sake buɗe wata makarantar a
Kano.
2.0 Kafa Hukumomi da Ƙungiyoyin Rubuta Ƙagaggun Labarai
Baya ga samar da ɗaiɗaikun waɗancan rubuce –
rubuce, an yi ƙoƙarin haɓaka rubutattun ƙagaggun labarai na
Hausa ta hanyoyin kafa hukumomi waɗanda za su samar da sabbin littattafan ƙagaggun labarai, da
kuma fassara wasu rubuce – rubuce. Waɗannan hukumomi da ƙungiyoyi da aka kafa,
sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da sabbin littattafan ƙagaggun labarai. Don
haka a nan, dole mu kalli haɓakar waɗannan littattafai da fuskoki biyu, wato ta fuskar
hukumomi da kuma ƙungiyoyi.
2.1 Gudumawar Hukumomi/Kamfanoni Wajen Samar
da Litattafan Ƙagaggun Labarai
Ko shakka babu, hukumomi/kamfanoni
sun taka rawa wajen samar da sabbi da fassarawa na littattafan ƙagaggun labarai na
Hausa. Samuwar waɗannan hukumomi sun
yawaita littattafan zube waɗanda suke zama tsani na samar da wasu a yau. A taƙaice, ga jerin
hukumomi/kamfanoni da kuma wasu cikin littattafan da suka samar.
2.1.1 Hukumar Gudanarwa ta Makarantar Midil,
Katsina
An kafa wannan Hukuma a shekarar
1927, inda Hukumar ta yi nasarar samar da wasu littattafai waɗanda suka haɗa da:
i. Hausa Stories na Malam H.B.G. Nuhu
ii. Littafin Karatu na Hausa na Malam Bello
Kagara
iii. Takobin Gaskiya na Malam Nagwamatse
2.1.2 Hukumar Fassara (Translation Bureau)
An kafa wannan hukuma a shekarar
1927. Wannan hukuma ita ma ta samar da littattafai da dama, kamar yadda Maƙera (2009) da Lawan
(2011) suka bayyana a cikin Abu Sabe (2013: 1 – 5), irin littattafan da aka
samar a ƙarƙashin wannan hukuma ta fassara sun haɗa da:
i. Dare Dubu da ɗaya (1933) na Mamman
Kano da Frank Edger
ii. Littafin Hausawa da Maƙwabtansu
iii. Labaru Na Da da Na Yanzu (1931)
iɓ. Fassara littafin kiwon lafiya (1931)
(Muktar, 2004:18).
A cikin shekarar 1933 ne aka canja
sunan Hukumar Fassara ya koma Hukumar Talifi, wato Literature Bureau a Turance.
An yi hakan saboda la’akari da ayyukanta ba sun tsaya a fassara ba ne kawai,
har da sanya gasa da samar da ƙagaggun labarai. An naɗa Dr. R.M. East a
matsayin Shugaba, sannan an samar da wasu littattafai a yayin gasar farko da
Hukumar ta sa, musamman guda biyar da suka yi nasara waɗanda suka haɗa da:
i. Ruwan Bagaja (1933) na Malam Abubakar
Imam.
ii. Gandoki (1933) na Malam Bello Kagara.
iii. Shehu Umar (1933) na Malam Abubakar
Tafawa Balewa
iɓ. Idon Matambayi (1933) na Malam Muhammadu
Gwarzo.
ɓ. Jiki Magayi (1933) na John Tafida da
R.M. East.
2.1.3 Kamfanin Gaskiya Ta Fi Kwabo
An kafa wannan
kamfani a shekarar 1945, musamman la’akari da aka yi da yadda gwamnatin mulkin
mallaka ta Arewacin Nijeriya ta zaɓi ‘yan Arewa a shekarar 1939 domin su taimaka
a cikin yaƙin duniya na ɗaya, inda buƙatuwar a yawaita
labaran yaƙi ta taso. Wannan Hukuma, an naɗa Alhaji Abubakar
Imam ya zama Edita; yayin da Mr. Rupert M. East ya zama mataimakinsa. Daga
shekarar da aka kafa ta, wato 1945 zuwa ƙarshen 1949 ta samar
da littattafai irinsu:
i. Ikon Allah na Dr. R.M. East da Alhaji
Abubakar Imam,
ii. Kyaftin Makama na Abdulkadir Makama,
iii. Zamanin Nan Namu na E.M. Rimmer da Ahmadu
Ingawa,
iɓ. Bala Da Babiya na Nuhu Bamalli
ɓ. Mango Park Mabuɗin Kwara na Alhaji
Nuhu Bamalli
ɓi. Yawon Duniya Hajji Baba na Alhaji
Abubakar Tunau Mafara ya fassara (Abu Saber, 2013: 7, Mukhtar, 2010:19).
2.1.4 Hukumar NORLA (Northern Region Literature
Agency)
An kafa wannan
hukumar a shekarar 1953, kuma aka damƙa ta ga Alhaji
Abubakar Imam; domin ya gudanar da azuzuwan yaƙi da jahilci da kuma
samar da littattafai don waɗannan azuzuwan. Wannan Hukuma, ta ci gaba da gudanar da
ayyukanta har zuwa shekarar 1959, lokacin da aka rushe ta aka mayar da aikinta
zuwa Kamfanin Gaskiya. A tsakanin waɗannan shekaru, wato daga shekarar 1953 zuwa
1959, wannan Hukuma ta samar da littattafai guda shida (6), waɗanda suka haɗa da:
i. Hali Zanen Dutse na Sarkin Musulmi
Alhaji Abubakar na III
ii. Littafin Addini na Alhaji Halliru Binji
iii. Tarihin Fulani na Wazirin Sakkwato Alhaji
Junaidu
iɓ. Littafin Mamaki na Abdullahi Maƙarfi
ɓ. Littafin Mafarki na M.M. Kumasi
ɓi. Motsi Ya Fi Zama na Malam Aminu Kano, da
sauransu. (Mukhtar, 2010:20).
2.1.5 Hukumar Northern Nigerian Publishing Company
NNPC
Wannan Hukuma an kafa
ta a shekarar 1960. Ita ma ta yi hoɓɓasa wajen samar da littattafai. Cikin
littattafan da ta samar sun haɗa da:
i. Nagari Na Kowa (1959) na Jabiru
Abdullahi.
ii. Tauraruwa Mai Wutsiya (1969) na Umaru
Dembo da sauransu. (Yahaya, 1988:213)
Bayan haka, wannan Hukumar ta (NNPC)
ta sa gasar ƙagaggun littattafai a cikin shekara ta 1981 inda ta buga
uku daga cikin waɗanda suka yi nasara.
Cikinsu akwai:
i. So Aljannar Duniya (1980) na Hafsatu
Abdulwaheed
ii. Ahmadi Na Malam Amah (1980) na Magaji Ɗanbatta
iii. Mallakin Zuciyata (1980) na Sulaiman
Ibrahim Katsina.
Haka kuma baya ga waɗannan kamfanoni da
hukumomi an sami wallafe-wallafe da dama a cikin shekarun 1970 misali:
i. Littafin Abdullahi Ka’oje mai suna
‘Dare Ɗaya’ wanda aka buga a shekarar 1973.
ii. Littafin Abdulƙadir Ɗangambo mai suna
‘Kitsen Rogo’ wanda aka buga a shekarar 1978 da dai sauransu. (Mukhtar,
2010:20)
2.1.6 Hukumar Al’adu Ta Arewa (Federal Department
of Culture)
Wannan Hukuma an kafa
ta a shekarar 1982. Ita ma ta yi ƙoƙari wajen samar da
littattafan ƙagaggun labarai, cikinsu akwai:
i. Turmin Danya (1982) na Sulaiman
Ibrahim Katsina.
ii. Tsumagiyar Kan Hanya (1982) na Musa
Muhammad Bello.
iii. Ƙarshen Alewa Ƙasa (1982) na Bature
Gagare.
iɓ. Zaɓi Naka (1982) na Munir Mamman Katsina.
Baya ga waɗannan, a shekarar
1984 wata al’adar rubuce – rubuce na ƙaggagun littattafai
ta sake kunno kai wadda aka sa wa suna “Adabin Kasuwar Kano” wadda a Turance
ake kira “Kano Market Literature”. An sami wani jigo na soyayya inda ya yi
tasiri sosai da sosai a cikin wannan adabin. Daga cikin waɗanda suka share fage
akwai irin su littafin:
i. Rabin Raina (littafi na ɗaya) (1984) na Talatu
Wada Ahmed.
ii. Soyayya Gamon Jini (1986) na Ibrahim
Hamza Abdullahi.
iii. In Da Rai (1987) na Idris Imam.
iɓ. Budurwar Zuciya (1987) na Balaraba Ramat
Yakubu.
ɓ. Kogin Soyayya (1988) na A.M.
Zahraddeen.
ɓi. Idan So Cuta Ne (1989) na Yusuf M. Adamu
(Muktar, 2010: 21).
2.2 Kafa Ƙungiyoyin Marubuta Ƙagaggun Labarai Na
Hausa
Bayan ɓullowar Adabin Kasuwar Kano a 1984,
kamar yadda Malumfashi (1984) ya raɗa wa suna, sai ƙagaggun labarai suka
fara yawaita, musamman ma waɗanda suke da jigon soyayya. Wannan sai ya haifar da
kakkafa ƙungiyoyi na marubuta daban-daban. Mukhtar (2004:27), ya
jero ire-iren ƙungiyoyin da aka samar tun a wancan lokaci, cikinsu
akwai:
i. Ƙungiyar Raina Kama
ii. Ƙungiyar Marubuta ta
Himma
iii. Ƙungiyar Marubuta ta
Mikiya
iɓ. Ƙungiyar Marubuta ta Ɗan haƙin da ka Raina
ɓ. Ƙungiyar Marubuta ta
Soyayyar Zamani
ɓi. Ƙungiyar Marubuta ta
Kukan Kurciya
ɓii. Ƙungiyar Marubuta ta
Nijeriya (ANA) da sauransu.
Kafa
waɗannan ƙungiyoyi ya haddasa
samuwar tarin marubuta mata da yawan gaske waɗanda littattafansu suka mamaye
kasuwannin ƙasar Hausa.
2.3 Wasu Cikin Littattafan Ƙagaggun Labarai Na
Hausa da Marubutunsu a Yau
Baba da Nayaya (2017:6) sun haƙaito ire – iren
littattafan ƙagaggun labarai na Hausa a wani aki da suka gabatar.
Cikin waɗannan litattafan
akwai:
i. In da Alƙawari (1992) na Bala
Anas Babinlata
ii. Duniya Sai Sannu (1997) na Ado Ahmad
Gidan Dabino, MON.
iii. Mafarkin Khadija (2014) na Maimuna Idriss
Sani Beli
iɓ. Rayuwar Bilkisu (2016) na Ayuba Muhammad
Ɗanzaki.
ɓ. Launin So (2009) na Kabir Yusuf Anka
ɓi. Jininmu Ɗaya (2012) Abida
Muhammad
ɓii. Amon ‘Yanci (2013) Halima Ahmad Matazu
ɓiii. Jarrabi (2014) na Abubakar Auyo.
iɗ. Ɗan Musulmi (2014) na
Rahma Abdulmajid
ɗ. Me Zan Yi Da Ke (2016) na Maryam Rabi’u
Ado
ɗi. Marubuciya (2017) na Jiddah Haulat Nguru
ɗii. Bulaguron Wawa (2014) na Sa’adatu Baba
Ahmad
ɗiii. Rumaisa (2014) na Fauziyya D. Suleiman.
ɗiɓ. Adon Dawa (2011) na Jamila Umar Tanko
ɗɓ. Babban Dare (2014) na Amina Dauda
Abubakar.
Idan an dubi waɗannan littattafai, za
a ga mafi yawan jigonsu ya karkata ne a kan soyayya, wannan shi ya ƙara tabbatar da
sauyin jigo da aka samu tsakanin wallafe – wallafen baya, har kawo shekarar
1984, da kuma waɗanda ake haifa a
yanzu. Wannan kuwa na da alaƙa da yanayin da aka samu na sauyin
zamani da kuma wanzuwar baƙin al’adu a cikin al’adun Hausawa.
2.4 Marubuta Ƙagaggun Labaran Hausa
Tun lokacin da sana’ar rubuce –
rubucen ƙagaggun labarai na Hausa ta fara kankama a tsakanin
Hausawa, sai aka samu yawaitar marubutan a dukkanin sassanin ƙasashen Hausawa. Kawo
yanzu, ba za a iya ƙayyade adadin marubuta ƙagaggun labarai na
Hausa ba.
Nayaya da Baba (2018: 55) sun jero
wasu daga cikin marubutan ƙagaggun labarai na Hausa. Misali;
i. Bilkisu Ibrahim Nabature
ii. Zuwaira Isa
iii. Fauziyya D. Suleiman
iɓ. Hadiza Nuhu Gudaji
ɓ. Naja’atu Haruna Saleh
ɓi. Muhammad Lawal Barista
ɓii. Maryam Kabir Mashi
ɓiii. Abubakar Auyo
iɗ. Nura Sada Nasimat
ɗ. Zaidu Barmo Katsina da sauransu.
2.5 Wuraren da Ake Ɗab’in Ƙagaggun Larabci na
Hausa
Da yake marubuta ƙagaggun labarai suna
da yawa, kenan wuraren da ake bugawa a kwamfuta ma dole su yawaita. Masu ɗab’i su ne masu fitar
da shi a cikin fallayen takardu, a wuraren a kan samu, masu yin bango da sauran
dukkanin ayyukan da suka shafi ɗab’i. Kaɗan daga cikin wuraren akwai:
i. Gidan Dabino Publishers dake kusa da
Gidan Ƙanƙara, Sabon Titi Sani Mainagge, Kano.
ii. Anka Graphics Fagge, Kano.
iii. Iya Ruwa Publishers Kano.
iɓ. Gimbiya Publishers Fagge, Layin Wafa,
Fagge D2, Birnin Kano.
ɓ. Fancy Printing and Publishing Company,
Sabuwar Unguwa, Katsina.
2.6 Wuraren Da Ake Dillancin Ƙagaggun Labarai
Akwai wurare da dama da ake
dillancin littattafan ƙagaggun labarai na Hausa. Daga cikin wuraren akwai:
i. Sauƙi Bookshop, Ƙofar Maggi, Bayan
Banki Layina 2, Kasuwar Muhammad Abubakar Ilimi dake Sabon Gari Kano.
ii. Alhaji Muhammad Jega Bookshop, Kasuwar
Kurmi Kano.
iii. Nurullah Bookshop, bayan gadar ‘Yan Kura,
Kasuwar Sabon Gari Kano.
iɓ. Mace Mutum Bookshop, Kan Titin Dawaki,
daura da Titin Ahmadu Bello, G.R.A., Nasarawa Kano.
ɓ. Garba Mohammed Bookshop, Kasuwar Sabon
Gari Kano.
ɓi. Nazzy Bookshop, Kasuwar Gama, Brigade
daura da Gwagwarwa Police Station, Kano.
ɓii. Amintako Bookshop, No. 1 Shamaki Road,
Hadejia, Jihar Jigawa.
2.7 Wuraren da Ake Bayar da Hayar Littattafan
Ƙagaggun Labarai
Da yake harkar bayar da hayar
littafi, harka ce wadda ta saɓawa duk wasu marubuta, hakan ya sanya ba kowane
mamallakin littafi ba ne ke aminta da a bayar da hayar littafinsa. Wannan sai
ya sanya galibi a ɓoye ne mata a
gidajensu da kuma wasu ɗaiɗaikun shagunan sayar
da littattafan ke bayar da wannan haya. Wasu cikin wuraren da ake bayar da
wannan haya sun haɗa da:
i. Rakiya da ke unguwar Hotoro, Kano
ii. Hajiya Maryam mai Kunun Aya, Unguwar
Hausawa, Kano.
iii. Aisha mai sayar da takardu dake Tokarawa,
Kano
iɓ. Shagon Gimba mai littattafai, maina huɗu, Ƙaramar Hukumar Nguru,
Jihar Yobe.
ɓ. Isa Mai Kayan Bulawus, kan Titin Ahmadu
Bello, Ƙaramar Hukumar Nguru.
3.0 Gudumawar Ƙagaggun Labaran Hausa
Wajen Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasa
Haƙiƙa yaɗuwar ƙagaggun labaran Hausa
waɗanda aka buga a
matsayin littafin karantawa; sun bayar da gagarumar gudumawa wajen yaɗa tattalin arzikin ƙasa. Za a yarda da
hakan yayin da aka yi la’akari da yadda rayuwar dubban mutane ta dogara ga
wannan sana’a, wadda ta nan suke samun ci da sha, da kuma sauran buƙatunsu na rayuwa.
Kamar yadda aka faɗa, akwai nau’o’in
mutane mabambanta waɗanda rayuwarsu
kacokan ta dogara a kan wannan sana’a. Don a fahimci bayani na a fili, an kasafta
su kamar haka:
3.1 Masu Rubutawa (Marubuta)
Waɗannan su ne rukuni na farko wajen
samar da ƙagaggun labaran Hausa, domin su ne nau’o’’i na mutanen da
Allah ya huwacewa basirar tsara labarin da kuma baiwar rubuta shi. Rubuta ƙagaggun labarai baiwa
ce ba karantar ta ake ba, domin zurfin ilimin mutum ko matakin karatu ba za su
sanya ya zama marubuci ba. Marubuta litattafan Hausa, ta hanyar tsara basirar
da Allah Ya fuwace musu ce, suke samar da rubutattun littattafai, wanda daga
nan sai a samar da shi, har a kai kasuwa ga masaya. Da wannan abin za su
gudanar da al’amuran rayuwarsu na yau da gobe, wato wannan ce sana’arsu.
3.2 Masu Yin Faifan Littafi
Su ne waɗanda ke sanya
littafin a faifan CD, wato bayan an rubuta shi da keken rubutu ko na’urar rubutu,
sai su mayar da shi faifan domin saita shi. Ta wannan hanya ce suke samun abin
masarufinsu, bayan sun yi wa littafi wannan faifan na CD.
3.3 Masu Buga Littafi (Masu Ɗab’i)
Maɗaba’a nan ce wurin da ake buga
littattafan ƙagaggun labarai bayan marubuta sun rubuta, sannan an
sanya shi a kwamfuta har a yi masa faifai. To daga nan sai a sanya a na’urar ɗab’i wadda za ta
fitar da adadin da ake buƙata. Masu aiki a maɗaba’a, suna da ƙaiyadaddan farashi ga
dukkanin wani ɗab’i da za su yi
wanda ta nan suke samun nasu abin masarufin.
3.4 Masu Tsara Bango (Coɓer Design)
Waɗannan rukuni kuwa su ne suke tsara bangon
littafi kafin a kai ga buga shi, sawa’un wannan tsarawar suna yi ne da kwamfuta
ko kuma da hannu. Irin waɗannan mutane,
marubuta kan kawo musu aikin ne sai su bayyana musu tsarin bangon da suke so,
kuma su biya su. Ta nan su ma suke samun nasu abin masarufin.
3.5 Masu Yin Faifan Bango (Coɓer Plate)
Wannan wani muhimmin rukuni ne waɗanda ke dogaro da ƙagaggun labarai wajen
tafiyar da rayuwarsu. Aikin wannan jama’a shi ne yin faifan bangon littafi,
wato ‘plate’ a Turance. Domin za su ɗauki aikin da aka yi na bangon littafi da
kwamfuta sai su mayar da shi cikin faifan. Ta irin wannan hanyar, marubuta ke
biyan su kwatankwacin aikin da suka yi musu, to sai su samu ribarsu a ciki
bayan sun cire kuɗin kayan aiki.
3.6 Masu Buga Bango (Coɓer Printers)
Bayan an tsara bangon littafi, kuma an
sanya shi cikin faifai. To abu na gaba shi ne fitarwa, to wannan rukuni su ne
masu fitar da bangon littafi. Su kuwa za su yi amfani ne da tsarinas na cikin
faifai su fitar da adadin yadda suke so. Ta wannan hanya ce suke samun kuɗaɗen gudanar da
al’amuran rayuwarsu nay au da gobe.
3.7 Masu Sayarwa/Dillalai Ko Diloli
Bayan aikin littafi ya kammala, marubuci
kan sauƙi littafi domin sayarwa. To marubuci kan ɗauki littafin ne ya
kai wa masu samarwa, wato diloli waɗanda a gun su ne ƙananan ‘yan kasuwa za
su je su saya domin su ma su sayarwa makaranta. To marubucin littafi yakan
bayar da wani ayyanannen farashi na shi, su kuma sai su ɗora ribarsu, wadda da
ita suke riƙe wannan kasuwanci nasu.
3.8 Masu Sayar da Ɗai-Ɗai
Wannan rukuni kuwa, su ne ƙananan ‘yan kasuwar
da suke sayowa a wurin manyan diloli sannan su zo su kasa suna sayarwa masu
karantawa. Irin wannan nau’i, sukan sayowa a cikin farashi mai rahusa, sai su ƙara wani abu ta
la’akari da kuɗin dakon da za su
cire da ɗawainiyar da suka yi
da kuma abin da zai biyo baya na riba.
3.9 Masu Dako
Wannan rukuni kuwa, jingunuwarsu ga
wannan sana’a ita ce dako. Wato su ne masu jigilar littattafan ƙagaggun labarai tun
daga maɗaba’a zuwa gun
marubuci, ko diloli, ko ƙananan ‘yan kasu, ko kuma ma zuwa wani gari makusanci ko
mai nisa. A irin wannan jigilar ce suke samun abin masarufinsu wanda suke riƙe rayuwarsu da
shi.
3.10 Masu Bayar da Shi Haya
Wannan wani nau’i ne na mutanen da
ke bayar da hayar littattafan sawa’un a shagunansu ne ko kuma mata ne a
gidajensu. Amma mafi yawan masu bayar da wannan haya mata ne. Wato bayan sun
bayar kan wani farashi za a karanta a dawo musu da shi cikin ƙidaddigun kwanakin da
suke bayarwa.
Masu bayar da haya, sukan sayo duk
duga ɗaya a kan kuɗi N 150, N
200, N 250, ko kuma N 300. Idan sun kawo shagunansu ko
gidajensu, sukan bayar da shi haya a kan N
40 tsawon awa ashirin da huɗu (24 hrs), idan ba a samu matsalar riƙewa daga gurin wasu
ba, to a sati guda sukan fitar da kuɗinsu, har ma su samu riba, musamman waɗanda suke ƙasa da ɗari uku (N 300).
3.11 Masu Turawa a Wayoyi
Su kuwa waɗannan masu samun abin
masarufinsu ne ta hanyar tura wa mutane sautin murya na waɗannan littattafai a
wayoyinsu ko wani abin saurare kamar radiyo mai amfani da memory. Irin waɗannan ana karance
labaran ne tsaf, sannan a rinƙa turawa domin saurare maimakon
karantawa daga cikin littattafai. To a yayin da masu buƙata suka je domin a
tura musu, sukan bayar da wani kuɗi da aka ƙayyade da wannan suke
mayar da kuɗinsu har su ci riba.
3.12 Masu Shagunan Haya
Waɗannan kuwa su ne irin waɗanda ke gina shaguna
domin bayar da su haya, cikin waɗanda ke karɓar hayar kuwa akwai masu ɗab’i, dilolin
littattafai, masu sayar da ɗai-ɗai da masu haya, sai
kuma sauran waɗanda suka jiɓinci wannan sana’a,
kuma suka karɓi hayar wurin
sana’ar. Ta irin wannan hanyar ce masu hayar shaguna suke samun kuɗaɗen shiga yayin da
suka bai wa masu harkar littafi hayar shaguna.
4.0 Kammalawa
Kamar yadda ya gabata a wannan takarda
an bibiyi ɓangaren ma’ana da
kuma taƙaitaccen tarihin samuwar ƙagaggun labarai na
Hausa. A cikin takardar, an bayyana kamfanoni/hukumomi da gwamnati ta kafa a
matakai daban – daban domin samar da waɗannan littattafai, sannan aka bayyana irin
gudumawar da suka bayar wajen samar da littattafan. A cikin takardar dai, an
bayyana ƙungiyoyin da aka samar domin wallafa ƙagaggun labarai na
Hausa, haka zalika da irin rawar da suka taka. Sannan aka bayyana masu ƙagawa, da masu bugawa
da kuma masu dillancinsu. Takardar, ta bayyana nau’o’in mutane guda goma sha
biyu da rayuwarsu ta rataya a wannan sana’a, wanda ya kasance su suke cicciɓawa wajen samarwa da
yaɗa littattafan ƙagaggun labarai,
kamar yadda su ma da wannan sana’a suka dogara wajen gudanar da al’amuran
rayuwarsu na yau da gobe. Kenan, a takardar an fahimci lalle ƙaga labari da bugawa
sana’a ce da take da muhimmanci a wannan ƙasa, ta fuskar
gwamnati/hukumomi da ɗaiɗaikun mutane, domin
sana’a ce da ta kewaye wani sashe na rayuwar al’umma, kuma ta zama maɓuɓɓuga ta yaɗa aikin yi da arziki.
A shawarce, ya kamata gwamnati ta ƙara inganta wannan
sana’a ta hanyar kakkafa masana’antu da horas da masu wannan sana’a ilimummuka
da dama domin ƙara inganta wannan sana’a.
Manazarta
Tuntuɓi masu takarda.
Masha Allah. Naji dadin wannan rubutu matuƙa
ReplyDelete