Babban saƙo wannan waƙar shi ne yabo, yabon kuwa wanda ke ƙunshe da ƙaunar wanda ake yabon tare da bayyana muhimmancinsa da girmansa da kuma fifikonsa a tsakanin al’umma. Sannan saƙon na tattare da razani ga wanda ya ƙi wannan da ake yabo a cikin waƙar; ta yadda maƙiyinsa zai iya gamuwa da wata fitina musamman a bayan rayuwa ta duniya. Wannan saƙo na waƙar ya fara ne tun daga ɗa na biyu har zuwa na huɗu, waɗanda ke nuna tsantsar yabo gare Shi.
Daga
Ibrahim Baba (Garba
Nayaya)[1]
Mamba, Ƙungiyar Matasan
Musulunci.
Shugaban Ƙungiyar Marubuta
ta NWAN, kuma Shugaban riƙo na Jihar Yobe
1.0 Gabatarwa a
Kan Salsalar Waƙa
Wannan waƙa an ƙirƙirin yin ta a sakamakon wani
taron ƙara wa juna sani wanda Ƙungiyar Matasan Musulunci[2] ta Ƙaramar Hukumar Nguru Jihar
Yobe suka shirya, taron kuma an shirya shi ne domin yin martani ga masu cin
zarafin Annabi Muhammad S.A.W, wanda an yi taron a ranar Lahadi 27 ga watan
Satumba, 2020, a babban ɗakin karatu na zamani Galadima
Maikyari da ke Kwalejin Koyon Aikin Shari’a da Addinin Musulunci, wanda aka
fara da misalin ƙarfe goma na safe zuwa ƙarfe ɗaya da arba’in na rana.
1.1 Shekarar
Haihuwar Waƙar
Kamar yadda aka faɗa, an gabatar da waƙar a wurin wani taro a ranar 27 ga watan Satumba,
2020, amma an fara rera waƙar a ranar 18 ga watan Satumba na 2020.
1.2 Wurin da Aka
Yi Waƙar
An fara rera waƙar a situdiyo ɗin Abu Raihan Multimedia da ke Kulegande, Tsohon
Nguru, Ƙaramar Hukumar ta Nguru.
1.3 Yawan Ɗiya a Waƙar
Waƙar na ɗauke da ɗiya guda goma sha ɗaya (11).
1.4 Tarihin Aliyu
Auta
An haifi Aliyu Auta a safiyar ranar Juma’a sha bakwai ga watan
Juli na shekarar 1993; a Ƙaramar Hukumar Nguru, Jihar Yobe. Aliyu ya yi makarantar firamare ta
Shuwarin, sannan ya shiga ƙaramar sakandare ta Hausari, kafin daga baya a mayar da shi Damaturu
International School da ke Ƙaramar Hukumar Damaturu, fadar Gwamnatin Jihar Yobe. A shekarar 2011 ya
kammala babbar sakandare ta Royal Academy Damaturu, sannan ya ci gaba a ɓangaren difloma, inda ya karanci ilimin Na’urar
Gwajin Ƙwaƙwalwa[3].
Tun a shekarar 2007, Aliyu Auta ya fara rubuta waƙa, wanda kawo yanzu ya rubuta waƙoƙi daban-daban a fannini
siyasa, addini, aure, tallace-tallace, sarakuna da waƙoƙin faɗakarwa ko wa’azantarwa.
1.5 Nasabar Wanda
Aka Yi Wa Waƙa
An haifi Manzon Allah[4] S.A.W[5] ranar
Litinin 8 ko 12[6]
ga watan Rabi’ul Auwal shekarar Giwa. SunanSa Muhammad ɗan Abdullahi, ɗan Abdul Muɗɗalib, ɗan Abdu Manaf, ɗan Kusayyu, ɗan Kilabu, ɗan Murratu, ɗan Ka’abu, ɗan Lu’ayyu, ɗan Galib, ɗan Fihr (Ƙurayshi), ɗan Malik, ɗan Nadhru (Ƙays), ɗan Kinanata, ɗan Khuzaimata, ɗan Mudrikata (Amir), ɗan Ilyas, ɗan Mudhar, ɗan Nizar, ɗan Ma’ad, ɗan Adnan; wanda shi ne Kaka
na ashirin ga Manzon Allah S.A.W kuma ƙarshen nasaba mafi inganci. Amma an tabbatar da
cewa, Adnan shi ne jika na 38 ga Annabi Isma’il A.S ɗan Annabi Ibrahim Ibn Ishaƙ A.S. MahaifiyarSa kuwa, ita
ce Aminatu ‘yar Wahbi ‘yar Abdi Manafi, ‘yar Zuhrata, ‘yar Kilaabi, ‘yar
Murrata, ‘yar Ka’abi, ‘yar Lu’ayyi, ‘yar Galibi, ‘yar Fihr.
Annabi S.A.W an haife Shi
bayan rasuwar MahaifinSa, sannan bayan an haife Shi ita ma bayan shekara biyu,
ta rasu a yayin da ta tafi ziyara kabarin MahaifinSa, inda ta rasu a wani wuri
a ake kira Abwa’i[7].
Daga cikin waɗanda suka shayar da Shi
akwai Ummu Aiman, Suwaibah, sannan Halimatus Sa’adiyyat. Yayin da Ya kai
shekaru takwas, sai KakanSa ya rasu, kafin rasuwar sai da ya damƙa amanarSa ga BaffanSa wato
Abu-Ɗalib. Abu-Ɗalib ya ci gaba da kula da Shi inda ya taso cikin garin Makka.
Manzon Allah S.A.W ya
kasance wanda bai cin amana ga gaskiya, wannan ya sanya a dukkanin sana’o’inSa
ake samun Sa da gaskiya da riƙon amana. Ta fuskar aure kuwa, ya auri mata goma sha ɗaya waɗanda suka haɗa da: Khadijatu ‘yar
Khuwaild, Saudatu ‘yar Zam’ah, Aishatu ‘yar Abubakar, Hafsat ‘yar Umar Alkhaɗɗab, Zainab ‘YAR Khuzaimah, Ummu Salamah Hindu ‘yar
Abi Umayyah, Zainab ‘yar Jahshin, Juwairiyyah ‘yar Harith, Ummu Habibah Ramlatu
‘yar Abi Safyan, Safiyyat ‘yar Huyayyi, Maimunatu ‘yar Harith. ‘YayanSa kuwa
akwai: Alƙasim, Abdullahi, Ibrahim, Zainab, Ruƙayya, Faɗima, da Ummu Khulsum. Allah ya karɓi rayuwar Manzon Allah S.A.W da hantsin ranar Litinin 12 ga watan Rabi’ul
Auwal na shekara ta goma sha biyu bayan Hijira, kuma an binne Shi a ɗakin MatarSa A’ishat ‘yar Abubukar kamar yadda ya
tabbata cewar ana binne annabawa ne a wurin da suka rasu.
1.6 Tasirin Waƙar a wurin al’umma
Kasancewar Manzon Allah
S.A.W mutum ne da dukkanin duniya ta taru kan amincinSa, soyayyarsa da kuma
kamalarSa, wannan ta sanya duk abin da aka jingina maSa yake samun tasiri a
wurin al’umma, musamman ma musulmai. Tare da haka, wannan waƙa ta sami tagomasi da sowa a
wurin ɗaruruwan al’ummar da suka
saurare tat un kafin a kai ga lokacin da za a rare ta a wurin wannan taro.
Sannan bayan an rera ta, ta sami karɓuwa da sambarka a wurin dubban jama’a, malaman addini da na boko da ɗalibai gaba ɗaya. Wannan ta sanya, Malam Khamisu Ya’u Bello[8] ya
ambata cewar, “Bai taɓa jin wata waƙa a wannan zamani da ta kai
wannan waƙar ba”. Kuma al’umma suka rinƙa tururuwa domin a tura musu ita a wayoyinsu don su
saurare ta.
2.0 Saƙo ko Turken Waƙar
Saƙonnin wannan waƙa sun karkasu kamar haka, wato bisa tsarin yadda ake
nazarin waƙar baka Bahaushiya.
2.1 Gundarin
Turken Waƙar
Babban saƙo wannan waƙar shi ne yabo, yabon kuwa
wanda ke ƙunshe da ƙaunar wanda ake yabon tare da bayyana muhimmancinsa da girmansa da kuma
fifikonsa a tsakanin al’umma. Sannan saƙon na tattare da razani ga wanda ya ƙi wannan da ake yabo a cikin
waƙar; ta yadda maƙiyinsa zai iya gamuwa da wata
fitina musamman a bayan rayuwa ta duniya. Wannan saƙo na waƙar ya fara ne tun daga ɗa na biyu har zuwa na huɗu, waɗanda ke nuna tsantsar yabo gare Shi.
2.2 Muhallin Turke
Domin tabbatar da abin da aka ambata
na saƙon waƙar, wato wanda yake shi ne yabo, ga
inda hakan ya bayyana a ɗa na biyu, uku da
huɗu.
Jagora: Ya Allah tsira aminci daɗa wa Rasulu abin
kwatance,
Annabi kyakkyawa a siffa da kyawun
hali tsaftatacce,
Kowaye ya
ƙi
Mustapha Annabin Allah shi ne ɓatacce,
Bare ya taho filin Ƙiyama a nan zai gane fushi na Rabba.
Jagora: Assalamu alaikum ikkiwani ga wata waƙa kan Annabina,
Mai taken
matsayin Ma’aiki mu kare mutumcin Annabina,
Marubucin
wagga farar ƙasida Aliyu Suleiman Ɗa ga Ghana,
Auta Masani a cikin mawaƙa da ba ya son ya ga masu zamba.
Jagora: Annabi ne mutuƙar ƙurewa a komai in
ka cire Maƙagi,
Miya ba ta daɗi a koyaushe in
aka bar gishiri da magi,
Matasan Addini
na Islamu kun burge ni a wagga ƙangi,
Da kun ka haɗo manyan mutane saboda
faɗar matsayin na Babba.
2.3 Warwara da
Tsettsefe Turke
Jagora: Ya Allah tsira aminci daɗa wa Rasulu abin
kwatance,
Annabi
kyakkyawa a siffa da kyawun hali tsaftatacce,
Kowaye ya ƙi Mustapha Annabin
Allah shi ne ɓatacce,
Bare ya taho filin Ƙiyama a nan zai gane fushi na Rabba.
Jagora: Assalamu alaikum ikkiwani ga wata waƙa kan Annabina,
Mai taken
matsayin Ma’aiki mu kare mutuncin Annabina,
Marubucin
wagga farar ƙasida Aliyu Suleiman Ɗa ga Ghana,
Auta Masani a cikin mawaƙa da ba ya son ya ga masu zamba.
Jagora: Annabi ne mutuƙar ƙurewa a komai in
ka cire Maƙagi,
Miya ba ta daɗi a koyaushe in
aka bar gishiri da magi,
Matasan Addini na Islamu
kun burge ni a wagga ƙangi,
Da kun ka haɗo manyan mutane
saboda faɗar matsayin na Babba.
Idan aka yi duba ga
turken nan na wannan waƙa, za ga ka ɗiyan da suka bayyana sun
nuna tsantsar yabo ga wanda ake so. Shi yabo ana yin sa bisa nau’i ga mutanen
da ake so, so irin na soyayya, da so irin na girmamawa, da kuma so na kusanci
da kuma so na yarda da wajibci haɗe da girmamawa. A nan, wannan yabon da ake yi, yabo ne na son tilas da
kuma girmama wanda ake so ɗin. A cikin ɗa na farko cikin waɗannan ɗiya da aka ambaci turken, za a ga yadda makaɗin ya bayyana kyawun siffar wanda ake son, sannan ya
bayyana wajibcin son, har ma ya nuna makomar wanda ya ƙi Shi.
Idan
aka yin irin wannan son, to yana tafiya ne tare da nuna matsayin wanda ake so ɗin. Shi ya sa a ɗa na gaba, sai makaɗin ya bayyana waƙar a matsayin ‘Matsayin
wanda ake so’. Sannan a ɗa na gaba, sai ya bayyana
matsayin na Shi, inda har ya nuna matuƙar muhimmancinSa ta hanyar kamantawa. Gishi ko magi wasu sinadarai ne na sanya
daddaɗan ɗanɗano a abinci; ta yadda duk daɗin abinci muddin ba a sanya masa gishiri ba, to waɗannan kayan da aka sanya sun tashi a banza, domin ɗanɗanonsu ba zai fito ba. A nan, sai makaɗin ya yi amfani da waɗannan kalmomi domin ya kamanta matsayin Annabi S.A.W a cikin alummar
duniya, ta yadda duk wani babba wanda yake ji da malamanta, dukiya, sarauta ko
wani matsayi, ƙasa suke ƙasan ma na sosai da Shi. Kai, ba ma wannan ba, idan ba Allah ba, babu
wanda ya kai Annabi S.A.W.
2.4 Taƙaita Turke
Saƙonnin da wannan waƙa ta ƙunsa a dunƙule sun ƙunshi abubuwa ne kamar haka:
Ɗa na farko: Ya yi yabon buɗewa ga Allah tare da roƙon Allah ya shige masa gaba, sannan ya
ɗan taɓo kalmar yabo ga Annabi S.A.W.
Ɗa na 2 - 4: Ya yi nemar wa sahhabbai amincin Allah,
sannan ya bayyana kyawawan halaye da
munin ƙinSa, da matsayinSa da kuma
muhimmancinsa ga al’ummar duniya gaba
ɗaya.
Ɗa na 5 - 6: Ya bayyana matsayin wanda ya ƙi Manzon Allah S.A.W a wurin
Allah ranar
Ƙiyama da kuma muhimmancin
bin Sa da son Sa, da kuma illar cin mutuncinSa.
Ɗa na 7 - 8: Ya bayyana sunayen malaman da suka gabatar
da nasiha a wurin taron son Annabi
S.A.W. Malaman
kuwa su ne: Sheikh Isa Madina[9], Malam
Musa Kallah[10],
Malam
Khamisu Ya’u[11],
Malam Munir Sheikh Ngibrima[12],
Malam Muhammad Baba[13] da
Dk. Abba Idris[14].
Ɗa na 9 - 11: A nan kuwa ya
kawo wasu munanan al’amura ne guda huɗu da Manzon Allah
S.A.W ya yi
hani a aikata su, waɗannan abubuwa kuwa su ne: ƙarya, shirka, cin
dukiyar marayu,
ƙin kyautata wa
iyaye alhali mutum yana da hali, ya fifita
matansa, ya bar
iyayensa cikin wahalhalu.
3.0 Awon Baka a Waƙar:
3.1 Yawan Layuka a
Ɗa
Wannan waƙa ta yabon Manzon Allah
S.A.W tana ɗauke da layuka hurhuɗu a kowane ɗiya.
3.2 Zubin Ɗiyan Waƙar
An buɗe waƙar ta fara bayyana gindin waƙar wanda yake a matsayin amshi, sannan an ƙarƙare ta da gargaɗi ga al’umma.
3.3 Tsarin Ɗiyan Waƙar
A tsarin ɗiyan wannan waƙa, makaɗin ya yi matuƙar ƙoƙarin jeranta tunaninsa ba tare da yin ƙwan-gaba-ƙwan-baya ba. A tsarin ɗiyan, ya yi ƙoƙarin fito da dukkanin abin da yake son a fahimta cikin sauƙaƙaƙƙen bayani. Har wa yau, a
wajen tsarin layukan waƙar, babu yawaitar saɓi-zarce face a ɗa na 9 har zuwa na 11.
Gangara kuwa, an same ta a ɗa na farko; a layi na uku zuwa na huɗu.
3.4 Tsarin Rerawa
Tsarin rera waƙar ya kasance ƙarƙashin jagora ne kawai, wato
babu masu amshi ko mai amshi, jagora kaɗai ke yin komai a waƙarsa. Sannan a tsarin rera waƙar babu kiɗa a ciki, kawai dai an rera ta a ɗakin situdiyo ba tare da sanya mata kiɗa ba; amma an yi amfani da na’urorin seta murya domin ta bayar da amo mai
daɗin saurare.
3.6 Amsa-amon Kari
Amsa-amon kari a wannan waƙar ya kasu guda biyu, wato
na ciki shi ne yake canjawa daga ɗa zuwa wani ɗa, amma na wajen yana ƙarewa ne da ‘ba’ tun daga
farko har ƙarshen waƙar.
4.0 Adon Harshe a
Waƙar
A nan an sami abubuwa
kamar haka:
4.1 Kamantawa
Matuƙa kalma ce da ke nuna isar
abu, ko cikar abu, kamar yadda ƙurewa ke da makamanciyar wannan ma’ana. A nan ke nan, ya haɗa kalmomin guda biyu domin su ƙarfafi juna. To a nan sai ya
nuna Annabi S.A.W ya fi kowa da komai a duniya, kai in da Allah ba ma, ba wanda
ya kai Shi. Makaɗin ya yi ƙoƙarin bayyana irin dubban muhimmancin da gishiri yake das hi a cikin
abinci ko miya, ta yadda idan babu shi, to wannan abincin bai amsa sunansa ba.
Sai ya ɗauko wannan muhimmanci na
gishiri da magi ya kamanta shi da muhimmancin Annabi S.A.W; ma’ana duk wata
rayuwa ta duniya in dai ba a tsarin Annabi S.A.W take ba, babu sonSa ga mutum,
to wannan rayuwa shirme ce, sannan lami ce kwatankwacin lamin da ake samu a
miya ko abincin da babu gishiri da magi. Wannan kuwa ya faru a ɗa na uku layi ɗaya da na biyu.
Idan aka duba ɗa na huɗu (4), layi na uku, za a gay a kamantasokwanci ga wanda yake ƙin Manzon Allah S.A.W.
4.2 Siffantawa
Gogagge kalma ce ta
siffantawa, to a nan, sai ya ɗauko kalmar ‘yaƙi’ wadda take aikatau ce ya ya haɗa su wuri guda, harɗaɗɗen suna, sannan ya jingina sunan ga Annabi S.A.W,
wato Annabi S.A.W Gwarzo ne, gwarzantakar da ta kai a siffanta Shi da ‘Gogaggen
mayaƙi’, wato gwani a yaƙi. A ɗa na ɗaya (1) siffantawa ta bayyana, inda ya nuna siffanta
ƙasidar ta shi da
‘fara’. A nan, idan an ce fara, ana nuna fari na kyau. Sannan a ɗa na goma (10) ya siffanta mai cin dukiyar marayu da
wawa, domin a wurin sa duk wanda zai ci dukiyar marayu, to fa wawa ne.
4.3 Abuntawa
A ɗa na tara (9) layi na uku (3), ya yi abuntarwa, inda
ya jero wasu siffofi munana, kuma ya nuna duk wanda ya sami kansa cikinsu, to
bai da bambanci da itacen da masu aikin biredi suke amfani da shi, amma a ranar
Ƙiyama. Abuntawa
a nan, shi ne mayar da mutum a matsayin itace.
5.0 Aiwatar da
Harshen Waƙar
A nan, za a duba tsarin da
aka bi wajen aiwatar da harshe a cikin wannan waƙar, ƙarƙashinsa akwai muhimman abubuwa da za a duba waɗanda suka haɗa da:
5.1 Zaɓen Kalmomi
An yi amfani da sauƙaƙan kalmomi wajen gin a
jimloli, irin kalmomin da ba za su bayar da wahalar fahimta ba.
5.2 Aron Kalmomi
Daga cikin kalmomin da aka samu na aro
a cikin wannan waƙar akwai irin su: Rabbi, Proɓost, Ƙasida, Rasulu, Ikhwani, Sheikh, Dr. (Doctor), Jahannama, Nabiyyu da
sauransu.
5.3 Karin Harshe a
waƙar
Kusan a wannan waƙar an yi amfani da
Daidaitaccen Kari, face ɗan tsarma karin Yamma da aka
yi domin daidaita ɗiya. Misali a kalmar
‘wagga’, ‘bare’, kac ci’
5.4 Ginin Jimla a
Waƙar
Idan aka yi duba ga ginin
jimla a cikin wannna waƙar, za a ga kusan dukkanin jimlolin da suka yi tarayya wajen ƙulla ɗiyan waƙar; sauƙaƙa ne. Wannan ya sanya waƙar ta yi sauƙin fahimtar saƙonta ga mai sauraro da kuma bayar da sauƙin hardace ta ba tare da an sha wata wahala ba.
6.0 Kammalawa
A wannan takarda, an ɗan yi ƙoƙarin bayyana taƙaitaccen tarihin makaɗin, sannan aka koro bayain kan asalin waƙar da shekarar yin ta. A cikin takardar, an yi ƙoƙarin yin fiɗar waƙar daidai gwargwado.
Manazarta
Abba, M & Zulyadaini, B. (2000). Nazarin
Waƙar Baka
ta Hausa. Zaria, Nigeria: Gaskiya
Corporattion Limited.
Baba (Nayaya), I. (2019). Nazarin
Salon Zuga a Waƙoƙin
Ibrahim Narambaɗa Tubali. A Paper
Presented at Internation Conference,
organized by C
Bunzu, A. M (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre Limited.
CNHN. (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria,
Nigeria: ABU Press Limited.
Dunfawa, A. A (2003). Ma’aunin Waƙa. Sokoto: Garkuwa Publishers.
Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon Tsari). Kano: K.D.G Publishers.
Gusau, S. M.
(2008). Dabarun Nazarin Adabin Hausa.
Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gamawa, A. M. S.
(2020). Tarihin Farin Jakada: Annabi Muhammad
S.A.W. Bauchi: Saga Press.
Gusau, S. M.
(2014). Waƙar Baka Bahaushiya
(The Hausa Oral Song). Kano: Bayero Uniɓersity.
Gusau, S. M.
(2005). Makaɗa Da Mawaƙa A Ƙasar
Hausa.
Kano: Benchmark Publishers LMT.
Gusau, S. M.
(2020). Feɗe Waƙar Jarumar Mata Ta Makaɗi Hamisu Yusuf Sa’id (Hamisu
Breaker)
Bisa Gadon Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya. (Unpublished).
Mukhtar, A. B.
(2017). Hausa Da Karorinta. Kano: Goɓernment Printing Press.
Sa’id, B. (1981). Bambancin Waƙar Baka Da
Rubutacciya.
A Cikin Yahaya, I.Y.; Rufa’I, A. &
Abu-Manga, A. (ed) Studies in Hausa Language, Literature and Culture:
The Second
Hausa International Conference.
Kano: Centre for Study of Nigerian Languages, B.U.K.
Salihi, T. M.
(2012). Sakace A Kan Karin Harshen Hausa.
Kano: Ɗorayi Babba Comm. Press.
Sarɓi, S. A (2009). Nazarin Waƙen Hausa. Kano: Samarib
Publishers.
Umar, M. B.
(1987). Dangantakar Adabin Baka Da
Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph
Publishing Company.
Umar, M.S. (2017).
Nabiyyur Rahmati: Siratu wa Durusu wa
Ibra. Kano: Alhikmah Printing.
Yahya, A. B.
(2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: Fisba
Media Serɓices
Yakasai, S. A.
(2012). Jagoran Ilimin Walwalar Harshe.
Sokoto: Garkuwa Media Serɓices
LMD.
Rataye
Matanin waƙar Yabon Manzon Allah S.A.W ta
Aliyu Auta Masani
Gindin Waƙa: Ku tashi mu kare hakin Ma’aiki;
Gaba ɗaya al-ummar musulmi;
Annabi ɗangata na Rabbi;
Kowa ya taɓa Shi ba ma bari ba.
Jagora: Almusawwiru Rabbi Allah Ta’ala Sarki mai
iyawa,
Wadataccen da Ya ƙagi Dakta Abba Proɓost ya ba shi baiwa,
Ka iya mini ya Sarkin iyawa a wagga ƙasidar nan da nai
wa,
Annabi gogaggen mayaƙi da Shi ya hane
mu mu daina gaba.
Jagora: Ya Allah tsira aminci daɗa wa Rasulu abin
kwatance,
Annabi
kyakkyawa a siffa da kyawun hali tsaftatacce,
Kowaye
ya ƙi
Mustapha Annabin Allah shi ne ɓatacce,
Bare taho
filin Ƙiyama a nan zai gane fushi na Rabba.
Jagora: Assalamu alaikum
ikkiwani ga wata waƙa kan Annabina,
Mai taken matsayin Ma’aiki mu kare mutuncin
Annabina,
Marubucin wagga farar ƙasida Aliyu
Suleiman Ɗa ga Ghana,
Auta Masani a cikin mawaƙa da ba ya son ya
ga masu zamba.
Jagora: Annabi ne mutuƙar ƙurewa a komai in
ka cire Maƙagi,
Miya ba ta
daɗi a koyaushe in
aka bar gishiri da magi,
Matasan
Addini na Islamu kun burge ni a wagga ƙangi,
Da kun ka haɗo manyan mutane
saboda faɗar matsayin na Babba.
Jagora: Idan ka ƙi Manzo Mahmudu
gun Allah ai sunanka fanko,
Ba kai ba
rahama ta Allahu koda ka yi bara da ƙoƙo,
Bare
ka taɓo darajar Ma’aiki
ka kushe ai ya zarce soko,
Idan ɗan wuta aka so a kalla kawai fuskarka a je
a duba.
Jagora: Cikar ka musulmi sai kana son shi fiye da ɗiya har ma iyaye,
Idan ka bi Manzo Ɗan Amina haƙiƙa ba kai ba hawaye,
Mutuncin Annabi ya wuce kac ci koda ranar ka
yi maye,
Ya ɗan’uwa ka tsaya ka gane halacci Annabi ya yi
duba.
Jagora: Sheikh Malam Isa
Madina a harkar Annabi bai da wasa,
Ina Malam
Musa Kallah yana koyin Angonsu Hafsa,
Akwai Malam Khamisu Ya’u Majalissa ta
malamai da kansa,
Mu sa Munir Sheikh Ngibrima, Muhammad
Baba ba zan bari ba.
Jagora: Idan a ka zo
lamari na Musbahu Dr. Abba hakan yake so,
Da an ce Annabi duk abin da yake a ƙwaƙwalwa ta yi naso,
Dakta Abba a kan Ma’aikinmu ya yi abin da Ilahu
ke so,
Yai koyi da Nabiyu Manzonmu bai hau
turbar mushirikai ba.
Jagora: Ga mutum huɗu cikinmu Annabi
ya ware:
Idan ka
mace kana ciki Allahu ya kare,
Da kai da itacen
da mai biredi ya sa zaure,
Bambancin
sai idan ba za ka lahira ba.
Jagora: Mai ƙarya ɗan wuta ne Allahu
ya kare,
Mai shirka ɗan wuta ne Allahu
ya kare,
Mai cin
dukiyar marayu wawa ne,
Lahira Jahannama
zai in bai bari ba.
Jagora: Mai halin da ya
bar iyayensa cikin yunwa,
Matarsa
tana cin ƙwai uwarsa tuwon dawa,
Suturarsa
na yalƙi Babansa kamar bawa,
Shawarar
da zana ba ka kar ka je ga rabba.
[1]
Yana
daga cikin waɗanda
suka fara zama domin assasa Ƙungiyar matasan, sannan shi ne ya fara
duba waƙar bayan mawaƙin ya rubuta; duk da kasancewar bai
sami wasu kurakurai ba. Yanzu haka ɗalibi
ne mai neman digiri na biyu a Jami’ar Jihar Bauchi da ke Gaɗau. Yana da
rubuce-rubuce da dama a Hausa musamman a tarukan ƙara wa juna
sani.
[2]
An kafa ƙungiyar a ranar Litinin 7 ga watan
Satumba, 2020, domin kare mutuncin Manzon Allah S.A.W da kuma nuna taƙaici kana bin da ake yin a cin
mutuncinSa. Inda aka fara zaman kafa ta a Kwalejin Koyon Aikin Shari’a da
Addinin Musulunci ta Nguru. Nan take aka naɗa
Dr. Jamilu Ibrahim Mukhtar Shugaba, Salihu Suleiman Ɗanjajimaji; Mataimaki, Idriss
Kabiru Ɗanyaro;
Sakatare, biyo bayan shawarar da Ibrahim Garba Nayaya ya bayar.
[3]
Yanzu haka Auta ma’aikaci ne
a Kwalejin Koyon Aikin Shari’a da Addinin Musulunci ta Nguru, sannan mawaƙi ne, kuma shi ya kafa Abu Raihan
Multimedia Limited.
[4] Ya sami wannan suna ne
kasancewarSa ɗan aiken Allah da Addinin Musulunci
zuwa ga al’ummar duniya gaba ɗaya. Har wa yau an ace masa
‘Annabi’ daga kalmar ‘Nabiyyu’. Shi ne Annabin ƙarshen zamani, bayan Shi babu wanda aka aiko da
annabta.
[5]
SallalLaahu Alaihi Wasallam,
wato amincin Allah ya (ƙara)
tabbata a gare Shi.
[6]
Takwas ga watan shi ya fi
inganta, amma sha-biyu ga watan ya fi shahara.
[7] Wani ƙauye ne da ke tsakanin Makka da Madina
kilomita 20.
[8]
Malam Khamis Ya’u Bello, shi
ne Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, reshen Nguru, kuma Mataimakin Shugaban
Zauren Limaman Juma’a na Nguru, sannan Malami ne a Sashen Tsangayar Ƙur’ani a Kwalejin Shari’a ta Nguru.
Yana karantarwa ga huɗubobi. Kuma shi ne babban Limamin
Idi na JIBWIS reshen Nguru.
[9]
Sunansa Sheikh Isa Garba
Nayaya, ana kiransa da Malam Isa Madina saboda a can Saudiyya ya yi digirinsa
na farko a Tsangayar Shari’a, Jami’ar Musulunci, ya kammala kusan shekaru
ashirin baya. Shi ne babban Limamin Masallacin Juma’a na Na-Malamai (FK),
sannan shi ne Shugaban Cibiyar Na-Malamai Centre for Islamic Nguru, kuma Malami
a Kwalejin Ilimi ta Gashua.
[10]
Shi ne Shugaban Kwamitin Kula
da Gudanar da Aiki da Shari’ar Musulunci ta Nguru.
[11] Bayani ya gabata a kansa.
[12] Ɗa ga babban Malami Sheikh Muhammad Ngibrima, sannan
Ma’aikaci ne a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Nguru.
[13] Yana koyarwa a Jami’ar Jihar Yobe,
sannna Malami ne a Ƙungiyar
Izala.
[14] Shi ne Shugaban Kwalejin Koyon
Aikin Shari’a ta Nguru, sannan Patron na Ƙungiyar
Marubuta ta NWAN, kuma Lakcara a Jami’ar Jihar Yobe, kuma shi ne Shugaba na huɗu a jerin shugabannin da suka jagoranci Kwalejin.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.