Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Kishi Kumullon Mata: Nazarin Kishi Cikin Fina-Finan Hausa

Takarda Wadda Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Sani, Na Jami'ar Jihar Kaduna, Daga Ranar 28th Zuwa 30th Ga Watan Maris, Shekarar 2019.

mata

Kishi Kumullon Mata: Nazarin Kishi Cikin Fina-Finan Hausa

Ibrahim Baba (Nayaya)

Ma'aikatar Ilimi ta Ƙananan Makarantun Sakandare, Ƙaramar Hukumar Nguru, Jihar Yobe.

Shugaban Ƙungiyar Nguru Writers' Association of Nigeria

07066366586, 08125351694.

Kibɗau: ibrahimba182@gmail.com

 

                            

Hassan Musa

Sashen Nazarin Harshen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Umar Suleiman dake Gashua, Jihar Yobe.

08064890499

hassanmusa170 @gmail.com

 

 

Saminu Sabo

Sashen Nazarin Harshen Hausa

Kwalejin Shari’a da Addinin Musulunci ta Atiku Abubakar, Nguru Jihar Yobe 08062563939

Kibɗau: saminusabo3467@yahoo.com

 

1.0    Gabatarwa

   Fina-finan Hausa wata tsararriyar hanya ce mafi sauƙi wadda ake bayyana halayya da ɗabi'u na al'umma cikin fasaha domin isar da saƙo ga wanda ya ji ya gani. Tun lokacin da fina-finan Hausa suka samu ɓulluwa a tsakanin Hausawa, wato ƙarshen ƙarni na ashirin 20, masu rubutawa da tsarawa da shiryawa suka ta ƙoƙarin bayyana al'adu iri daban-daban da halayyar zaman al'umma. Idan muka dubi fina-finan Hausa yan bana bakwai, za mu iske cike suke da al'adu daban-daban na al'umma, da kuma ɗabi'u na rukunonin mutane da halayyarsu. Misali, tun lokacin da finan-finan Hausa suka fara yawaita a tsakanin al'ummar Hausawa, masu tsarawa da shiryawa sun mayar da hankali ne wajen shirya fina-finan da suka shafi zamantakewar auratayya, tun daga kan neman aure, har kawo yin sa da kuma irin zaman da ake yi bayan aure, sawa'un mai daɗi ne ko akasin sa.A irin wannan shirye-shirye na fina-finai ne, sai ake shirya fina-finan da suka shafi kishi tsakanin ma'aurata, wato mata suna kishi tsakaninsu da junansu a matsayin matan mutum guda, ko kuma samari su rinƙa kishi tsakanin waɗanda suke neman budurwa ɗaya, ko kuma yan mata masu son saurayi guda.

   A cikin wannan takarda, an tattaro fina-finai guda goma sha biyu waɗanda aka naƙalto abubuwan kishi na tashe-tashen hankula da suka wakana tsakanin kishiyoyi, munin kuwa, ya afku ne tsakani kishiyoyin ko kuma tsakaninsu da mazajensu ko da 'yan'uwan miji ko uwar miji.

1.1   Ma'anar Fim

   Gidan Dabino da wani 2004:332sun bayyana fim da cewa, "Tantagayyar kimiyya da fasaha ce kuma rayuwar ɗan'adam ce ake nunawa. Fim yana ɗauke da tarihi da ɗabi'un jama'a da muhallinsu da abincinsu da kuma suturarsu musamman bisa harshensu da tsarin su na rayuwa da hanyoyin tunaninsu da kuma falsafar rayuwar mutanen da ake yin fim ɗin su. Har ila yau, fim hanya ce ta sanarwa da ilimantarwa da jan hankali da nishaɗantarwa da faɗakarwa da yaɗa manufa da tallatawa".

   'Yar'aduwa 2007:30ya yi na shi ta'arifin da cewa, "Fim wata hikima ce ta hoto mai motsi da take ɗauke da mutane, wato hotunansu maza da mata, yara ko manya, ko kuma ma wanin mutane, wanda aka ɗauka ta hanyar yin amfani da na'urar ɗaukar hoto ta musamman, tare da bai wa mutane kowannensudamar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwayo ko wanin sa, a wani ɗan lokaci da aka keɓe wanda shi wasan kwaikwayon fimyake ɗauke da wani saƙo na musamman kan nishaɗi da  gargaɗi da wa'azi da soyayya da tarihi ko wanin haka, zuwa ga al'ummar duniya".

   Idan muka yi la'akari da waɗannan ma'anoni guda biyu, za mu iya kallon ma'anar da fim a taƙaice da cewa, wata keɓantacciyar hanya ce tsararriya ta sarrafa hikima da fasaha a aikace; wanda ake amfani da na'urar ɗaukar hoto mai motsi da sautuka, domin isar da wani saƙo na musamman ga al'umma, ta hanyar zayyano matsaloli da hanyoyin magance su ko uƙubar wanda ya munana.

 

1.2   Asali da Samuwar Fina-finan Hausa

   'Yar'aduwa 2007:30 ya bayyana samuwar fina-finan Hausa, abu ne da ya faru a ƙarshen ƙarni na ashirin 20. Amma farkon abin da ya ɗora tubalin samuwar sa shi ne wasan kwaikwayo. Kuma shi kan sa wasan kwaikwayo ya samu ne bayan Turawa mulkin mallaka sun kafu, kuma har sun yi nisa wajen shimfiɗa tsare-tsare da suka shafi ilimi da tsarin mulki da sarauta.

   Binta (2008:11-16) ta bayyana tarihin samuwar fina-finan Hausa dubi da nazarce-nazarce daga mawallafe-wallafen masana, misali Bargery (1934), Chamo (2005:36), Inuwa (2009) da Garba (2009), inda yawancinsu bakunansu sun daidaita da na juna ta fuskar asalin fina-finan Hausa. Misali, majigi hoton farko da Hausawa suka fara cin karo da shi kafin sauran hotuna da ake nunawa. An fara nuna majigi ta hanyar sanya allon kallo a saman mota.

   Binta (2008:15 – 16), bayan tattara bayanan masanan da ta yi game da samuwar fina-finan Hausa, sai ta nuna cewa, a cikin shekarar 1998 ne masu shirya fina-finai suka yunƙuro suka kafa ƙungiya ta masu wannan harkar domin su yi magana da murya ɗaya. Tun daga wannan lokaci sana 'ar shirya fim ta bunƙasa, kuma ga shi ƙofar shiga wannan sana'ar a buɗe take, sai aka dinga tururuwa cikin ta maza da mata, saboda amfanin da ake ganin masu wannan sana'a sun fara samu. Gaskiya ne, wannan sana'a ta samar wa matasa da dama aiki, maza da mata sun zama 'yan wasa da masu shiryawa da masu ba da umarni da masu ɗaukan nauyi, masu waƙoƙi da masu kwalliya da masu ɗaukan hoto da 'yan kasuwa da sauransu. Wannan sana'a ta haɗa mutane iri-iri, kuma kowa yana da tasa wadda ta shigo da shi wannan sana'a. Da wannan sana'a suka yi mata rajista suka sa mata suna Kannywood Industry, wato masu shirya fina-finan Hausa. A ƙarƙashin wannan Industiri akwai kamfanoni da suke shirya fina-finai kuma cibiyar wannan ƙungiya Kano. Kamfanoni sun haɗa da Kaduna, Abuja, Sakkwato, Maiduguri da sauran wurare.

 

2.0    Ma'anar Kishi

   Kishi suna ya tara, domin a kan bayyana shi ta hanyoyi daban-daban, kamar yadda ake masa kallo ta fuskoki da dama, kuma kowa da irin yadda yake sarrafa na shi/ta a aikace.

   Kishi tsakanin kishiyoyi shi ne abu mafi muni kuma wanda ya zama ruwan dare a yau, wanda kuma a kan sa ne muhallin wannan takarda.

 

2.1    Ma'anar Kishi

   Masana da dama da masu nazari sun bayyana ma'anar kishi a cikin kundayensu. Misali, Rabi (1998) a cikin Binta (2009:92) ta bayyana cewa "Kishi wani hali ne da mutum yake tsananin son abu ba tare da tarayya da wani ba".

   Garba (1998:334) ya kawo ma'anar kishi da cewa, "Kishi cikin jikin mutum yake, sai dai kuma mata sun fi nuna shi da aiwatar da shi. Mata na da hanyoyin nuna kishi kanar ta magana, da habaici da karin magana da lugude da waƙa, ko ta shanti ko ta niƙa ko zungurar wani abu inda kishiya take, yadda za ta farga da ita ake, ko wata shewa, ko dai wani abu makamancin waɗannan".

   Shi kuwa Abbas (1999:1) cewa ya yi, "Kishi shi ne sosuwar zuciya da ɓacin ran da suke kawo fushi a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani a kan abin da wanin ya keɓanta da son sa, ko mallakarsa".

   A ta'arifin Bakura (2003:91) ya bayyana kishi da cewa "Wata hanya ce ta gwagwarmaya dake tattare da zargi da tuhuma da saɓani da rashin jituwa da husuma da mugun nufi, domin ƙoƙarin kare keɓantacciyar ƙauna ga abin so, ba tare da yin tarayya da wani ba".

   CNHN (2006:247) kuwa ta bayyana kishi da cewa, "Rashin jituwa ne da nuna ƙyashi irin wanda matan dake auren mutum ɗaya suke yi wa juna. Ko kuma nuna gaba ga wani a kan wani abu na kirki da mutum ya sa a gaba don cimma buri".

   Idan aka dunƙule waɗannan ma'anoni, za a ga kishi ya shafi tarayyar mutum biyu ne a wurin mutum guda kuma a matsayi guda, ta yadda kowa zai yi ƙoƙarin ganin shi ne a gaba, ko kuma a sama. Wanda hakan kuwa zai kawo rikice-rikice da hayaniya da musguna wa juna.

 

2.2   Abubuwan Dake Kawo Kishi

   Kishi ba abu ne da ke zuwa kai tsaye ba, dole ne yana da wasu sabuba dake janyo shi ƙarshe ya zaunar da shi a zuciyar mai yi. Ta la'akari da ma'anonin da suka zo a baya, za mu ga kishi na da sabuba kamar haka:

 

2.2.1  Tsananin So

   Wato ta yadda wani zai sallama zuciyarsa ga wani, har iya kasance ba ya ganin laifinsa, kuma ba ya buƙatar wani ya kusanci wannan abu ko da da wasa ne.

 

2.2.2  Tarayya A Kan Abu Guda

   A duk lokacin da wani ya haɗa soyayyar mata biyu a zuciyarsa, to waɗannan mata za su kasance cikin kishin juna sakamakon tarayyar da suka yi da juna a zuciya guda.

 

2.2.3  Rashin Jituwa da Ƙyashi

   Wannan ma na janyo kishi, musamman tsakanin matan mutum guda, domin kowacce za ta rinƙa bibiyar yar'uwarta sakamakon wannan rashin jituwar, sannan kuma ƙyashi da mugunta ko mugun nufi zai riƙa biyo baya, saboda wancan rashin jituwar.

2.3   Rabe-raben Kishi

   Masana sun bayyana kishi kan iya zama kyakkyawa ko mummuna, kuma dukkansu ana iya gane su ta irin yanayin da aka bayyanar da su.

   Mohammed (2011:105-106) ya bayyana cewa, kyakkyawan kishi ana aiwatar da shi ne domin amfanin kai ba tare da cutar da abokin kishi ba. A nan ne akan samu irin kishin da ake kira 'Kishin zuci'. Misali, ta fuskar neman ilimi a tsakanin masu ƙoƙarin neman sa, kowane daga cikinsu yakan yi ƙoƙarin ya ga ya fi kowa ƙoƙari, ba tare da cutar da kowa ba. Haka ko ta fuskar sana'a ne za a ga kamfanoni masu yin abubuwa iri ɗaya, kamar sabulu ko magi ko katifa ko gadaje da sauransu, za a ga kowane kamfani da irin ingancin abin da ya samar. Saboda haka sukan yi kishi a tsakanin su ta yadda za su samu karɓuwa ga jama'a, wanda duk ya fi kishi to za a ga kullum yana daɗa inganta sana'ar tasa ce ba tare da ya cutar da abokin hamayyarsa ba.

   Sannan akwai irin kishin daga jin sunan; ba abin so ba ne. Kishi ne da ake bayyana shi ta hanyar cutar da abokin yi, ko a nuna masa ba a ƙaunar sa. Irin wannan kishi, shi ne aka fi samun sa a tsakanin mata.

   Ana samun kishi a tsakanin mata biyi waɗanda suke mijinsu ɗaya. Sannan ana samun kishi a tsakanin matar wa da matar ƙani, wato faccala. Haka ma kuma ana samun kishi tsakanin uwar miji da matar ɗa. Akwai kuma kishin dake tsakanin yayye ko ƙannen miji da matar ɗan'uwansu.

   Binta (2009:94 – 118) ta yi bayani game da rabe-raben kishi, inda ta kasafta su zuwa gida uku, kuma kowanne ta yi bayanai da buga misalai gwargwadon iko. A dunƙule, ta kasa kishin kamar haka:

 

2.3.1 Kishi tsakanin kishiyoyi, wato irin kishin dake tsakanin matan mutum guda. Irin wannan kishin ya faru a fina-finai da dama kamar Rikicin Cikin Gida (2018) na kamfanin Ɗan Hajiya Film Production Kano.

 

2.3.2 Kishin uwar miji, irin kishin da uwar miji ke yi ga matar ɗanta. Irin wannan kishi ya faru a fim ɗin Uwar Miji da sauransu.

 

2.3.3 Kishin faccala, wato irin kishin dake tsakanin matan wa da ƙani a junan su.Irin wannan kishin ya faru a fim ɗin Ƙawayen Amarya 2018na kamfanin 2 Effect Empires Kano.

3.0  Yanaye-yanayen Kishi Tsakanin Mata a Cikin Fina-finan Hausa

   A rayuwar zahiri, kishi kan sanya mata aikata abubuwa daban-daban na halaka wanda a ƙarshe yake zama sababin jefa rayuwar kishiyoyi ko mazajensu ko kuma su ɗin a karan kansu cikin mawuyacin hali. Idan aka leƙa ga fina-finan Hausa ma za a iske cike suke da fina-finai masu ɗauke da irin waɗannan halaye na kishi tsakanin mata. A nan, za a kawo wasu fina-finai da kishi ya bayyana ƙarara da kuma irin abin da mace take aikatawa a sakamakon wannan kishi, sawa'un a kan kishiyarta ce, ko 'ya'yan kishiya, ko maigida ko kuma wani cikin dangin miji, musamman mahaifiyar miji.

3.1  Kishi kan sa mace ta kashe kishiyarta

   A rayuwar zahiri tsananin kishi kan sanya mace kashe kishiyarta ta hanyar amfani da makami ko asiri ko kuma duka kawai. Haka abin yake a cikin fina-finan Hausa. A cikin fim ɗin Akushi (2018) na kamfanin Oscar International an ga yadda Lami ta hallaka kishiyarta ta hanyar amfani da magani. Lami wadda suke auren Malam tare da kishiyarta, ta rasa haihuwa wanda kishi ya hana ta nutsuwa, a ƙarshe kuma ta halaka ta.

3.2   Kishi kan sa mace ta yi wa kishiyarya asiri, ta shiga duniya

   A cikin fim ɗin Matar Uba (2018) na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment Nigeria Limited, an ga yadda Asabe ta yi wa Mariya asiri ta shiga duniya. Malam Nasidi shi ne mijinsu, amma tsananin kishi ya sanya Asabe ta je wajen Malami domin neman maganin da za ta yi wa Mariya asiri ta halaka ta. Ga yadda suka yi da Malamin:

Malam: Ai ni ma ba cewa na yi zai rabu da ita ba, ita za ta rabu da shi, za mu kore ta ta bar gidan ta shiga duniya har abada ba wanda zai ƙara jin labarin inda take, kuma har abada ba za ta dawo ba.

Asabe: To ai ni Malam a daidai na, ai in wannan ita kenan sharaɗin, na amince. Mata ta shige min rayuwa, haka kawai ta same ni da mijina ta raba ni da shi.

   A nan, mun ji yadda aka yi, kuma ƙarshe hakan ta faru, inda ta yi asirin da ya sanya Mariya ta shiga duniya, ba a ƙara ganin ta ba sai labarin mutuwarta aka ji.

3.3   Kishi kan sa mace ta kashe uwar mijinta

   Kamar yadda aka sani, kishi kan sanya mace kisan uwar miji. Ya zo a cikin fim ɗin Dalal (2018) na kamfanin A. Y. I Uniɓersal Motion Pictures Kano inda hakan  ta faru. Hafsat matar Jamil ta haɗa kai da mahaifiyarta da ƙanin mahaifiyar Jamil, wato Alhaji Bala domin ganin bayan mahaifiyar Jamil ɗin. Mahaifiyar Jamil ta sanya ya ƙara aure sakamakon rashin mutunci da tsatsube-tsatsuben da Hafsat da mahaifiyarta Hajiya Mama suke yi don ganin sun mallake shi. Haka kuwa aka yi, amma bayan ya yi auren sai da suka rinƙa asirai, ƙarshe sai da kishi ya sanya ta kashe uwar Jamil ɗin da goyon bayan Hajiya Mama da Alhaji Bala.

3.4   Kishi kan sa mace ta kira danginta/ƙawayenta domin dukan kishiyarta

   Daga cikin abin da zuciyar mace ke raya mata, bayan mijinta ya ƙara aure, akwai dukan amarya, wannan kuwa ya faru a fim ɗin Dalal (2018) ɗin, bayan Jamil ya ƙara aure, sai da Hafsat ta kira ƙawayenta/'yan'uwanta domin dukan matar da ya auro. Ga yadda suka yi:

Ƙawa 1: Ai ni haushinki nake ji, ya za a yi a ce kina zaune duk kishin kin nan wai har mijinki ya yi aure ya shigar da amaryar gida kina zaune a falo ba ki ɗauki wani mataki ba, kin ban kunya wallahi.

Hafsat: To ya zan yi? Ai ba kwa nan ne, ko ba gaskiya ba?

Ƙawa 1: To ai yanzu ga mu mun zo.

Ƙawa 2: Ai wannan cin mutunci ne da cin amana.

Hafsat: Ai dama na sani, daman jira nake ku zo mu afka musu.........

Ƙawa 3: Ai ga mu mun zo, sai ki tashi yanzu mu afka musu.

Hafsat: Abin da nake ao, kirawo min su Falmata, kafin su zo mu je mu afka musu, duk abin da ta tafasa ta ƙone.

   Haka kuwa aka yi, domin daga nan sai suka nufi ɗakin Amaryar inda suka rufe ta da duka bayan ta fito daga ɗakin.

3.5    Kishi kan sanya mace ta daina yi wa mijinta biyayya da kyautatawa

   Mace idan ta kasance ma'abociyar kyautatawa da ladabi ce ga mijinta, to a sakamakon kishi zai sanya su samu saɓanin da za ta daina yi masa dukkanin biyayya da ladabi da kyautatawar da take masa a baya.

   Fim ɗin Lubna (2018) na kamfanin Ƙalarawi Enterprises ya nuna hakan, yayin da Ibrahim ke zaune lafiya da matarsa, amma sakamakon ya nuna mata zai ƙara aure sai da kishin ta ya bayyana, har ta canja masa a yanayin mu'amala da kyautatawa.

Ibrahim: Tun lokacin da na ce zan ƙara aure shi kenan kika bi kika canja.

Mata: Me ka gani? Ni ba komai.

Ibrahim: A'a da komai, walwala ta canja, clearing ya canja, akwai abubuwa da yawa da kike min a gidan nan kin daina su. Kai amma kina da zafin kishi!

Mata: Ai kishi dole ne, duk macen da ka ga ba ta da kishi to wallahi ba ta son mijinta. Amma kishi ya zama dole, abin da kake so dole ka yi kishi..

   A nan, mun ga yadda kishi ya janyo ta daina kyautata wa mijinta, walwala ta sauya, ladabi ya sauyu.

   Fim ɗin Matar Mijina (2018) na kamfanin Al-Rahuz Film Production Kano, an ga yadda Jalila ta sauya mu'amalarta da mijinta a sanadiyyar ya ce zai ƙara aure, inda suna zaune cikin zaman lafiya da walwala, amma da ya zo da maganar aure sai matsala ta nemi kunnowa.

Adam: Ya za ki ji idan aka ce miki zan ƙara aure? (Bayan abin da ya bayyana a fuskarta na damuwa da kiɗimewa). Ya ya na ga duk jikinki ya yi sanyi?

Jalila: Ka ga duk zaman lafiyar da muke, ka ga duk ƙaunar junan dake tsakan na da kai, da zarar ka ƙara aure za ka neme su ka rasa.

Adam: Ban gane me kike nufi ba!

Jalila: Ina nufin zan buɗe wani sashi na daga Jahannama! Wallahi da faɗuwar gaba za ka rinƙa shigowa gidanka.

   Wannan ya nuna a baya suna zaman lafiya, amma sakamakon maganar ƙarin aure da ya yi mata, sai ta furta waɗannan kalamai.

 

3.6   Kishi kan sa kishiyoyi rikici a cikin gidan su, su rinƙa faɗa a junansu

   Abu mafi sauƙi da matan da suke auren mutum guda suke yi shi ne faɗa a koyaushe. Fim ɗin Rikicin Cikin Gida (2018) na kamfanin Ɗan Hajiya Film Production ya nuna irin wannan kishi, inda A'isha da Maryam waɗanda matan Sadiƙ ne suke faɗa a junansu a koyaushe.

   Bayan Maryam ta ɗebo ruwa ta watsa wa A'isha wadda ke kwance a kan doguwar kujera a falo, sai A'ishan ta miƙe tsaye.

A'isha: Ni kika watsa wa ruwa?

Maryam: An watsa miki.

A'isha: Lalle kin yi kuskure, wallahi sai kin yi nadamar abin da kika aikata a jikinki.

Maryam: Ke da Allah dakata! Wacce take faɗa a baki ba za ta iya aikatawa ba, ke kin san tsohuwar kuka ta wuci runguma wallahi sai dai sara.

A'isha: Haka kika ce?

Maryam: Ƙwarai kuwa.

   Sai A'isha ta ɗauki kwalba ta kwaɗa wa Maryam a ka, nan take faɗa ya kaure a tsakaninsu. A taƙaice dai, kishi kan sanya irin wannan faɗa a kowanne lokaci, ta yadda ba wani sauran zaman lafiya a gidan.

 

3.7   Kishi kan sa mace ta rinƙa yi wa mijinta rashin kunya, ƙarshe ma ta iya lalata auren ta

   Sau da dama idan mace ta san mijinta yana shirin ƙara aure, to fitsara da rashin kunya ce suke fara biyowa baya, ƙarshe ma auren su ya lalace sakamakon irin rashin kunyar da take yi masa. Irin wannan al'amari ya faru a fim ɗin Mubeenah (2017) na kamfanin Mai Shadda Inɓestment, inda Mubeenah ta ɗauki aniyar cin zarafin mijinta a yayin da ya zo mata da maganar ƙarin aure.

Adnan: Bai kamata 'ya'yanmu su gane cewa akwai wata matsala tsakaninmu ba, ko kaɗan ba ni da niyyar na cutar da ke ko na wulaƙanta ki, ba wai na yi shi da niyya ba ne.

Mubeenah: Dan Allah ka dakata min! Kana so ka ce min yarinyar ce ta janyo ka ta ce lalle sai ka aure ta? Kana so ka ce min ba ka taɓa furta mata kana son ta ba kenan?

Adnan: Ni fa ban ce haka ba, amma ina so ki fahimce ni, kuma ina so ki yi min kyakkyawan zato.

Mubeenah: Ka ga dan Allah ka yi haƙuri kar ka min wata lakca ba abin da za ka faɗa min na fahimta. Don haka ka je ka yi duk abin da ka ga dama, amma ina so ka sani, ni ban isa na hana ka abin da ka ga dama ba, amma idan ka yi kuskuren  yin aure, wallahi tallahi za ka yi nadama, za ka ga kuma abin da zai biyo baya.

   Haka al'amarin ya faru, domin bayan auren ta yi ta fitina har sai da ta kai ta lalata rayuwar auren ta hanyar saki, inda suka rabu.

 

3.8   Kishi kan sanya kishiya ta kira kishiyarta da karuwa

   Bayan faɗa dake afkuwa tsakanin kishiyoyi, haka akwai faɗar baƙaƙen maganganu masu muni kamar ambatar kishiya da karuwa. Fim ɗin Rikicin Cikin Gida (2018) na kamfanin Ɗan Hajiya Film Production ya zo da hakan, wato yayin da Maryam ta gyara falo a ranar girkinta, sai A'isha ta zo ta kwanta.

Maryam: To tsohuwar kilaki! Sai ki tashi ki fita daga falon nan saboda yau ba ke kika gyara falon ba, ballantana ki zo ki wani kwanta ki baje, sai ki bari lokacin da kika yi sai ki zo ki kwanta.

3.9  Kishi kan sanya mace ta rinƙa zargin mijinta

   Sau da dama mace idan mijinta ya yi yunƙurin ƙara aure, to wannan mat za ta koma sae-sae da zargin mijin nata a kan munanan halaye. Ya zo a cikin fim ɗin Halin Kishi (2008) na kamfanin Global Time Moɓies yayin da Abdallah ya yi yunƙurin ƙarin aure, sai kishi ya sanya matarsa Zainab ta rinƙa zarginsa da fasiƙanci. A gefe guda kuma ta rinƙa yin barazanar kisa ga Zara'u (Budurwar mijinta) matuƙar ba ta rabu da mijin nata ba.

3.10   Kishi kan sanya mace ta rinƙa yi wa kishiyarta ƙage da sharri a gaban mijinsu

   A lokacin da mutum ke auren mace sama da ɗaya, kuma kishi ya sanya su rashin zaman lafiya, to kowacce za ta rinƙa ɓata kishiyarta a gaban mijinsu. Ya bayyana a cikin fim ɗin Matar Uba (2018) na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment Nigeria Limited, inda Malam Nasidi ya zauna yana jimamain rashin sanin inda Mariya ta shiga, sai Asabe take mata ƙage.

Malam Nasidi: Yau fa kwana uku ba mu ga Mariya ba, ba mu san halin da take ciki ba har yanzu.

Asabe: Kai kake ta da hankalinka, ni fa ina ganin Mariya gajiya ta yi da zaman gidan nan, tana so ta ga duniya, duniya ta ganta ta gogu, ta buɗe ido, idonta ya yi tar a duniya.

Malam Nasidi: Dakata, Mariya ba za ta yi haka ba, na san ta sarai.

Asabe: Ba a shaidar mutum, mutum ai shege ne, Malam mutum shege ne........

            A nan, duk da Mariya ba ta nan, ta ma ɓata, amma sai ga shi kishi ya sanya Asabe aibantata; ta hanyar yi mata ƙage.

3.11  Kishi kan sanya kishiya ta rinƙa azabtar da 'yar kishiyarta

    Sanin kowa ne, kishi kan haddasa ƙiyayya da gaba da kuma tsana. Haka zalika, kishi kan sanya mace ta rinƙa azabtar da ‘ya’yan kishiyarta. A cikin fim ɗin Matar Uba (2018) na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment, an ga yadda Asabe ta rinƙa azabtar da Amira 'yar gidan Mariya; bayan ta yi wa Mariya ɗin asiri. Ta rinƙa ɗaura mata talla, kuma idan ba ta sayar ba ta rinƙa jibgar ta, ba isasshen abinci, ba barci  wadatacce, wanda a ƙarshe sai da K.B saurayinta ya yi sanadiyyar tafiyar ta bariki.

 

3.12   Kishi kan sanya kishiya ta kashe mijinta

   A duk lokacin da kishi ya tunzura mace, to za ta rinƙa yin saƙe-saƙen hallaka mijin nasu, domin a nata tunanin shi ya jefa ta cikin wannan halin. Wata kuwa za ta yunƙuro domin kisa amma ba da gaske ba, sai dai idan akwai tsautsayi, sai kisan ya afku. Fim ɗin Mariya (2018) na kamfanin Mai Shadda Inɓestment Limited an ga yadda hakan ta faru. Mariya, wadda aka yi mata auren dole da Sarkin Noma Malam Sada ba tare da tana son sa ba. Shi kuma ya kasance mai auri saki ne, sannan yana da 'ya'ya. A haka aka yi auren, wanda bayan yin sa Mariya ba ta ba da kai ga Malam Sada ba.

   Wata rana ta aika a sayo mata maganin ɓera domin ta zuba masa a abinci ya ci ya mutu, a dalilin ba ta son shi sai bayan ta zuba, tausayi, da imani ya zo mata, sai ta ɗauka ta je za ta zubar. Ashe duk abin da yake faruwa a idanun Talatu (uwargidan Malam Sada) ake yi, inda ita kuma tuni ta faɗa kogon kishi da Mariya. Ganin Mariya za ta zubar da wannan abinci mai guba, sai ta zo ta karɓe abincin, ta aika masa, saboda kishi, alhali ta san da guba a ciki. Malam Sada bayan ya ci abinci, cikinsa ya murɗe har ya mutu, sai Talatu ta koma tana cewa ai Mariya ce ta kashe shi. Bayan Shari’a ta yi zurfi, gaskiya ta bayyana cewa Talatu ce ta kasha shi saboda kishi.

 

3.13 Kishi kan sa kishiya ta tayar da hankalin mijinta, ta haifar da rikici a gidan mijinta, a kasa zaune a kasa tsaye, kamar yadda hakan ya afku a fim ɗin Ɗakin Amarya (2016), inda Talatu ta rinƙa tayar da fitintunu wanda har a ƙarshe ta yi yunƙurin ƙona gidan gaba ɗaya. Sannan ta rinƙa ƙirawo ƙaninta tare da 'yan daba, suka rinƙa hautsina gidan da farfasa kayan kallo da kujerun gidan.

3.14   Kishi kan sanya mace ta rinƙa haukar ƙarya

   Mace takan yi haukar ƙarya da da'awar aljanu sun kama ta yayin da mijinta ya nemi ƙarin aure. Ya zo a fim ɗin Hawainiya (2014) inda Jamila ta rinƙa haukar ƙarya yayin da mijinta Shu'aibu ya zo mata da batun ƙarin aure.

3.15   Kishi kan sanya mace ta rinƙa tozarta mijinta da yi masa gori

   Kaɗan daga cikin aikin mace shi ne tozarta miji yayin da ta ba shi kuɗi ko suka haɗa jari domin yin kasuwanci ko kuma idan ta yi masa wata alfarma, muddin idan ya zo mata da batun ƙarin aure, to za ta rufe idanuwanta ta rinƙa cin zarafinsa da yi masa gori.

   Ya zo a fim ɗin Mu Zuba Mu Gani (2018) inda Sakina ta fara goranta wa mijinta Ahmad jarin da ta ba shi a dalilin ya zo ƙara aure. Bayan ta same shi a falo yana shirye-shiryen fita ɗaurin aurensa kamar yadda aka gaya mata, sai ya yi ta ƙoƙarin nuna mata ba wurin kowa zai je ba, ƙarshe ta nemi mintuna biyu a wurinsa. Bayan ta juya za ta shiga ɗakin girki, sai ya ce:

Ahmad: Wayyo uwargidana.....

Sakina: (Ta juyo da mamaki a fuskarta) Uwargida kuma?

Ahmad: Kuma Amaryata, ki bari na ƙarasa zance, ke an fara magana ba a ƙarasa ba sai ki shigo.

   Bayan ta tafi zuwa kicin, ta dawo hannunta a baya, ta nufo shi, sanna ta nemi ya rufe idanuwansa, sannan ta watsa matsa manja a babbar rigarsa. Daga cikin maganganun da suka yi akwai:

Ahmad: Ban gane ba, ya aka yi na yaudare ki? Me kike nufi da haka?

Sakina: Kar ka yi tsammanin Allah bai yoni asirinka ba, duk abin da kake Allah ya tona asirinka na sani. Wato an ɗaura auren ka yau kana sauri za ka tafi wajen dinner. To bari na faɗa maka, wallahi tallahi ba za ka cuce ni ka ce na ba ka kuɗi mu yi kasuwanci ka je ka yi aure da shi ba.

   Haka dai rikici ya ɓalle tsakaninsu, har bayan an yi auren ta ci gaba da goranta masa wannan kuɗi, ta hana amaryar zuwa wurinsa. Dukkanin tashe-tashen hankulan da suka faru, sun faru ne a dalilin ƙarin auren da ya yi, wanda kishi ya jagoranci aikata komai.

 

4.0  Kammalawa

   Bayan tattaro bayanai da aka yi yayin buɗe wannan takarda, waɗanda suka haɗa da ma'anar fim da samuwarsa, sannan aka yi bayani dangane da kishi da yadda yake auluwa. A cikin takardar, an bayyana sababin faruwar kishi a tsakanin al'umma, inda aka karkatar da bayanin kishin dake tsakanin kishiyoyi, wato matan da suke auren mutum ɗaya. Har wa yau, a cikin takardar, an ga yadda kishi yake a cikin fina-finan Hausa, ta yadda aka ciro misalan a cikin fina-finai daban-daban na Hausa wanda yawan su ya kai goma sha biyu. A ciki an nuna sakamakon dake afkuwa wanda yawancinsa rabuwa ce, domin a yayin da tashin hankali ya biyo baya, ba lalle a samu bakin zaren da za a haɗa domin ɗaure wannan matsala ba. A cikin takardar, an bayyana yadda mata a fina-finan Hausa ke aiwatar da kishinsu a aikace a yayin da suke kasance matan mutum guda. Hakan sai kishi ya yi tasirin da zai sanya su illata kishiyar tasu, ko mijin, ko ‘ya’yan kishiya, ko kuma su illata uwar miji kamar yadda misalai suka gabata a wasu fina-finai.

A mafi yawan waɗannan fina-finai kuwa, akan ga sakamakon da hakan yake haifarwa wadda ta aikata mugunta, ko dai ta harkace, ko ta gamu da wata cuta, ko ‘ya’yanta su kasance mutanen banza, ɓarayi, ko kuma ta rabu da mijinta ta koma rayuwar zawarci cikin ƙasƙanci. 

Manazarta

Tuntuɓi masu takarda.

Post a Comment

0 Comments