Sauye-sauyen rayuwa ta yau da kullum sun bayyana a tsakanin al’ummar Hausawa. Irin waɗannan sauye-sauyen sun wanzar da wasu munayen halaye da ɗabi’u, har sun kane-kane a akasarin rayuwar Bahaushe, waɗanda a da can babu alamunsu. Misali, rashin rikon amana da rashin cika alƙawali da ganin ƙyashi da haɗama da rowa da son kai da dogon guri da kwaɗayin tara abin duniya ta kowace irin hanya da yaudara da rashin tausayin na ƙasa ga kuma rashin gaski a cikin zukata. Irin waɗannan munayen halaye su ne suka taru suka zubar da mutuncin al’umma a idon duniya. Kuma aikata su shi ya haifar da lalacewar ƙasarmu tare da al’ummarta. Su kuwa kyawawan ɗabi’unmu da muka gada kaka da kakanni su ma sun fara gushewa, sai labarinsu kawai ake yi. Shin me ya kawo haka? Kuma me ke faruwa ne?Dangane da haka ne, wannan maƙala ta ƙuduri aniyar kawo bayanai game da dalilan taɓarɓarewar tarbiyya a tsakanin al’ummar Hausawa. Da farko maƙalar za ta fayyace ma’anar tarbiyya da abubuwan da suka haifar da taɓarɓarewar tarbiyya a ƙasar Hausa. Abubuwan suna da yawa, sai dai ni a nan zan karkata ne a kan waɗannan dalilai:
·
Cuɗanyar Hausawa da Wasu al’ummomi
·
Yi wa tarbiyyar Gargajiya Rikon sakainar Kashi
·
Kauce wa tarbiyyar
musulunci
·
Gina tarbiyyar ‘ya’ya a kan tsarin Nasara
Daga ƙarshe za a yi tsokaci ne a kan dalilan da suka sa ‘yan bokon farko ke da nagartattun halaye da ɗabi’u nagari, duk da kasancewar Turawa ne suka koyar da su.
Musabbabin Taɓarɓarewar Tarbiyya A Ƙasar Hausa
Dr.
Adamu rabi’u bakura
08064893336
Gabatarwa
Matsalolin rayuwar duniya sai ƙara bayyana suke yi
kullun garin Allah yaw aye a farfajiyar ƙasar Hausa, sakamakon
bayyanar fasahohi da ƙirƙire-ƙirƙiren zamani da ke ƙaruwa. Hanyoyinmu na
tarbiyya da ladabtarwa waɗanda muka gada, sai
daɗa sukurkucewa su ke,
ko ma a ce sun gushe gaba ɗaya. An kuma rungumi wasu baƙin al’adu da ɗabi’un al’ummomin yammacin ƙas ashen Turai, ba
don komai ba sai don da’awar wayewar kai da buɗe ido.
Daga cikin abubuwan da aka watsar
akwai kyawawan hanyoyin tarbiyyarmu da
ladabtarwa, waɗanda bai kamata a ce
an ƙaurace
musu ba. Kamata ya yi a kyautata su tare da inganta su domin su dace da ci
gaban rayuwar zamani, ta yadda za a yaƙI munanan halaye da ɗabi’un al’ummomin
yammacin Turai. Al’adun da Hausawa ke kwaikwaya kuwa, da waɗanda suke ƙirƙira wa kansu, su ma a
tsaya a kale su da idon basira, masu kyau daga ciki a yi amfani da su. Maras
kyau kuma a ɗauki makin kau da su
cikin hanzari.
Ma’anar Tarbiyya
Tarbiyya kalma ce ta larabci, mai
kushe da ma’anar koyar da hali na gari da kyautata rayuwar al’umma da shiryar
da su zuwa ga halaye da ɗabi’u masu kyau da
nagarta. Duk al’ummar da ta kasance haka, za ta zama mai kima da kwarjini da ganin
mutuncin abokan zama. Kazalika za ta ding aba kowa haƙƙinsa kamar yadda ya
dace. Tarbiyya ta kunshi renon jikin ɗan Adam da ruhinsa da kyawawan abubuwa masu
kamala (Mafara, 1989), da (Yahaya da wasu, 1992), da (Tanko, 1993), da
(Sa’id,2001).
Amfanin Tarbiyya
Tarbiyya ta haɗa da kyautata
hankalin ɗan Adam domin ya sami
nagartrtar rayuwa da yadda za ta dace da yanayin al’ummarsa. Haka kuma tana
kyautata al’adun al’umma su kasance kyawawa, ta kuma inganta su. Ta hanyar
tarbiyya ne ake koyar da ladabi da biyayya da sanin ya kamata, da gargaɗI a kan tsare halayen
kirki da kunya da haƙuri da yin gaskiya da kiyaye mutuncin al’umma da kiyaye
ladabin Magana da kyautata sutura da muhalli don su dace da ɗabi’un al’ummar ƙasar (Yahaya da wasu,
1992:78).
Cuɗanyar Hausawa Da wasu
Al’ummomi
Duk inda aka sami baƙuwar al’umma ta zo ta
cuɗanya da wata al’umma
ta daban, dole ne a sami ɗaya ta yi tasiri a
kan ɗaya. Musamman idan cuɗanyar ta ɗauki dogon lokaci, ta
hanyar saye da sayarwa ko ta hanyar mamaya ko yaudara da fifikon ƙarfin makaman zamani,
tamkar yadda ‘yan mulkin mallaka suka yi a wasu sassan ƙasar Hausa. Irin haka
kan sa a wayi gari al’adun al’ummar da ta yi mamaya su yi tasiri a kan na waɗanda aka mamaye. In
aka yi rashin sa’a sai a wayi gari sannu a hankali kyawawan al’adu da ɗabi’un al’ummar da
aka mamaye suna gushewa ɗaya bayan ɗaya.
Ƙasar Hausa ta sha
gwagwarmaya da al’ummomi daban-daban na kusa da na nesa. Irin wannan cuɗanya da ta auku
tsakanin ƙasar Hausa da ƙas ashen Turai ta
haifar da sauye-sauyen al’adu da ɗabi’un Hausawa. Sakamakonsa ya wanzar da taɓarɓarewar tarbiyya a
tsakanin al’ummar ƙasar Hausa.
Duk ƙasar da Turawa suka
yi kaka-kaka gida, har suka kafa mulkin mallaka, sukan yi ƙoƙarin cusa wa al’ummar
ƙasar
wasu ra’ayoyi cikin zukatansu, don su rungumin hanyoyin tsarin rayuwarsu da
tsarin iliminsu. Turawa kan yi ƙoƙarin gabatar da
tsarin iliminsu ne ta hanyar buɗa makarantu don koyar da nau’in iliminsu. Wannan shi zai
taimaka har a koyi karatu da rubutunsu, har a iya karanta littattafansu da ke
kunshe da dangogin adabinsu da falsafar yanayin tsarin zaman rayuwarsu ta yau
da kullum. Ta haka ne akan karanci al’adunsu da ɗabi’o’insu, sai a wayi gari su zama
sun yi tasiri a cikin zukatan al’umma, musamman samari. Sannu a hankali sai su
yaɗu a cikin zukatan
sauran al’ummar ƙasar.
Gina Tarbiyyar ‘Ya’ya
a Kan Tsarin Ilimin Boko Da babu Addini
Babbar manufar kafa makaratun boko a
ƙasar
Hausa ba ta wuce ƙudurin wargaza tarbiyyar al’ummar ƙasar Hausa ba, wadda
Turawa suka same su da ita. Wannan ne ya sa suka shata tsarin bayar da ilimin
da ba su yi wani tanadi na koyar da ilimin addinin musulunci a cikin
makarantunsu ba. Duk da kasancewar sun san cewa, koyar da addinin musulunci
yana kyautata halayen yara har su kasance masu kyan hali. Shi kansa jagoran
Turawan Mulkin Mallaka Lugga ya san da haka har ga abin da y ace:
“Dole ne gwamnati ta
tsaya tsayin daka ta ga an samo wa addini
Gindin zama ta yadda su
yaran da suka yi karatu za su zama masu
Kyan hali. Domin abin da
addininsu ya koya musu, ko da kuwa
Kowane irin addini ne
(Abdullahi, (b.kw) :92).”
Haka kuma Gwamna Lugga ya nuna munin
da ke tattare da bayar da ilimin boko ba tare da an gauraya shi da ilimin
addini ba. Domin yin haka ya na haifar da matsalar tabarbarewar tarbiyya a
tsakanin al’umma. Hasali sun ga abin da ya faru a wasu ƙasashen da aka tsara
bayar da ilimin bokon da ba a surka da addini ba. Ga kaɗan daga cikin abin da
ya ce:
“ Mai hankali hattara
yake yi da abin da ya sami waninsa, domin ya
Wa’azantu da shi.
Karatun boko ya jawo tsiya, bala’i da tajarifi a
ƙasashe kamar Hindu
(Indiya) da Sin (China) da kuma Afirika. A
Sanadin yin bokon da ba
a gauraya shi da addini ba. Duk wanda ya
yi bokon da babu addini
to shi kam ya shiga uku. Domin kuwa ba zai
girmama iyayensa ba. Ba
zai ga girman magabatansa ba. Sannan shi
kansa ma ba zai iya yi
wa kansa wani abu na alheri ba (Abdullah (b.kw:92).
Ke nan, za a iya
tabbatar da cewa a sane ne suka yi wannan tsarin domin a ɓata al’ummar ƙasar Hausa, don ƙasar ta lalace. Ku
lura fa wanda yay i wannan Magana shi ne jagoran ‘yan mulkin mallakar ƙasar Hausa. Shi ne fa
da kansa ya jagoranci mutanen da suka shata mana tsarin ilimin bokon da aka ƙaddamar a farfajiyar
Hausa. Hasali ma shi ne da Kansa ya naɗa Hanns Vischer daraktan ilimi a ƙasar Hausa. Shi ya
umurci Hanns ɗin, ya ziyarci ƙas ashen Sudan da
Masar domin ya duba yadda suke tafiyar da nasu tsarin makarantun. Amma saboda
manufar da ke cikin zukatansu, sai aka ƙi bin bayanin aka
aiwatar da wani abu na daban. A ka kuma ƙI gauraya bokon da
ilimin addinin.
Wani muhimmin lamari da ke ƙara tabbatar da
wannan da’awa shi ne, duk da kasancewar Ɗan Hausa (Hanns) ya
yi amfani da Malaman Arabiyya ta hanyar ba su horo a matsayin malaman
makarantar boko na farko, da suka yi aikin koyarwa, amma ba wani tsari da ya
tanadar a cikin manhajar ta Elimantare wadda ta nuna ana koyar da wani fanni da
ya danganci addinin musulunci, tamkar yadda ya tarar ana aiwatarwa a Sudan da
Masar. Abin da kawai suka yi shi ne ƙyale ɗaliban su halarci
masallacin juma’a da makarantar Muhammadiyya, domin sallar juma’a da kuma ɗaukar darussan
addinin musulunci a wuraren malaman azure (Graham, 1966:87). Ƙarawa da ƙarau, albashin da ake
biyan malaman Arabiyyar bai taka kara ya karya ba. Haka malamin Arabiyyar da ya
tafi ƙasashen Larabawa wajen ƙaro ilimi, albashinsa
bai kai na wanda ya je ƙasar Turai ba ( Mahmud, 1988:6-9).
Me Aka Fa’idantu Da shi A Shirin Nasu?
Dun tsawon lokacin da ‘yan mulkin
mallaka suka yi suna gudanar da makarantun bokon ƙasar Hausa, har zuwa
watan Satumba na shekarar 1913, lokacin da suka ɗaga darajar Makarantar Elimantare ta
Katsina zuwa Makarantar Lardi, wadda ke ƙarƙashin kulawarsu, ba
wata fa’ida da ɗaliban suka samu in
aka cire wasannin motsa jiki, waɗanda suka ƙaddamar irin na ƙas ashen Turai.
Wasannin sun haɗa da: rawar soja, da ƙwallon ƙafa, da ƙwallon gora da sauran
su (Graham,1966:95). Sun yi hakan ne domin su kawar da hankalin ɗaliban daga karatun
Muhammadiyya, su karkata ga wasannin. Domin a daidai lokacin da ake wasannin ne
suke zuwa ɗaukar karatun na
muhammadiyya. Ke nan a kaikaice an cin ye lokacin ɗaukar karatun. Kuma
ba a fito fili ƙarara aka ce an hana su ba.
Katsina Kwalej, wadda aka buɗe a shekarar 1921, an
sake tsarin bayar da iliminta daga falsafar ilimin Islama zuwa falsafar ƙasar Turai da al’adun
yammacin Turai. Don haka aka mayar da darasin Ingilishi mafi muhimmanci a
makarantar. Kuma ya zama harshen sadarwa a tsakanin ɗalibai, wanda suke
amfani da shi a sauran lamurran rubuce-rubucen yau da kullum (Director,
1913:50). Amma fa duk tsawon lokacin da aka yi ana karatun boko ba wasu darussa
na kimiyya da ake koyarwa. Sai daga baya, lokacin da aka fara gudanar da
makarantu tamkar yadda ake tafiyar da su a Kudu. A lokacin ne aka soma horar da
ɗaliban Katsina Kwalej
yadda za su zauna jarabawa da ake shiryawa daga waje. Aka kuma fara koyar da su
darussa kamar Physic da Biology da Chemistry. A shekarar 1949 ɗaliban makarantar
suka soma zauna jarawar samun takardar shaida ta Cambridge, bayan shekaru 28 da
kafuwar makarantar (Ozigi & Ocho, 1981:52). Me ya haifar da haka? An yi ƙanfar ɗaliban ne ko yaya? Ko
malaman da za su koyar da irin waɗanca darussan ne babu? To me aka karantar da
su a makarantar tun wanca tsawon lokacin? Tambayar da ke buƙatar mai karatu ya
natsu yay i tunani a kan amsarta cikin natsuwa da basira.
Duk lokacin da aka shata horar da
mutun a kan wata sana’a to lallai ne akwai matakai da akan bi don cimma manufar
da aka sa a gaba. Haka ko lokacin da Turawa suka zo sun tarar da mu da namu
tsarin ilmantarwa. Kuma abin mataki-mataki ne, har ɗalibi ya kai wani
matsayi da zai zama malami. Amma a tsarin nasu, ba haka suka soma shi ba.
Dalili kuwa shi ne, sai da aka ɗau tsawon shekaru 40 ana karatun bokon a ƙasar Hausa kafin
Turawa su ba da sukolashif ga ɗalibai don su zurfafa karatun nasu. Anya kuwa sun so mu
ci gaba ke nan. Domin sai a 1945 suka soma tura ɗalibai Jami’ar London , don ƙaro karatu. Rukunin
farko su ne: Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, da Mamman
Kano, da Shatima Kashim Ibrahim, da Salisu Hayi Ilorin, da Abdurrahman Okene,
da kuma Yahaya Bauchi. A shekarar 1946 aka tura rukuni na biyu waɗanda suka haɗa da: Malam Aminu
Kano, da Shatima Ajiram, da Salihu Ilorin, da kuma Mr. Dimka ( Kano,
1989:13-14).
Fahimtar da wasu masu kishi yankin,
wato ‘yan bokon farko suka yi, na makircin da ake shiryawa yankin ya sa su yin
yunƙurin
tura ‘ya’yan yankin waje karatu a ƙasar waje ta hanyar
karo-karo da suke yi daga cikin albashinsu.
A shekarar 1949, ‘yan bokon Nijeriya ta Arewa suka fara ɗibar ‘yan makaranta
mutun 7 suka kai su Ingila don su yi karatun sakandare har zuwa Jami’a a
fannoni daban-daban da suka haɗa da ilimin injiniya da lauya da likitanci. Wannan ya
tilasta wa ‘yan mulkin mallaka ba ‘yan Arewa damar zuwa Kwalejin Yaba (Yaba
College) da ke Legas don zurfafa karatunsu. Kafin lokacin , Alhaji Sa’adu
Zungur ne kaɗai aka tura
makarantar, inda ya karanci fannin haɗa magani (Chemist). Amma aikin da suka ba shi
bai da nasaba da abin da ya karanta (Kano, 1987:17). Mai karatu na iya cewa, me
ya sa ‘yan bokon farko na ƙasar Hausa, waɗanda Turawa ne suka
koyar da su, suka kasance masu gaskiya da rikon amana ga kwarjini a idon
jama’a? Amsar wannan tambaya mai sauƙi ce. Domin kuwa
alheri ya riga ya zauna cikin zukatansu tun suna ƙanan. Hasali ma akasarin
su sun mallaki ilimin addinin musulunci,
wasu har sun zama malamai, sun yi aure har da ‘ya’yansu ko da suka soma ɗalibta a makarantun
bokon (Ɗalhatu,2002:161).
Kauce Wa Tsarin
Tarbiyyar Gargajiya (al’ada)
Tun kafin bayyanar musulunci a ƙasar Hausa, tun iyaye
da kakanni al’ummar Hausawa suka mallaki wasu kyawawan ɗabi’u da suka ɗabi’antu da su.
Yayin da addin musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa, sai ya ƙara ƙarfafa su, har suka
tabbata a cikin zukatan al’umma. Suka yi amanna tare da ɗaukar wa kansu cewa,
aikin kowa da kowa ne ya kula da gyaran tarbiyyar yara, a duk inda ya ci karo da buƙatar haka. Ba sai ‘ya’yansa ba. Wannan shi ya sa kowa ke
bayar da tasa gudummawa wajen gina kyakkyawar tarbiyya ta gari a tsakanin
al’umma, musamman lamarin tarbiyyar yara maza da mata. A sakamakon haka ne tsofaffi mata kan tara yara da dare
suna yi musu tatsuniyoyi da ke ƙunshe da wasu darussa da ke cusa
tarbiyya a cikin zukatan al’umma. Amare mat aba a bar su bay aba, wajen gudanar
da irin waɗannan darussa da ke ɗauke da hannunka mai
sanda game da lamurran rayuwar duniya. Yayin da manya maza kan halarci
matattarar ilimi da wa’azi, inda ake fassara nassoshin Alƙur’ani da Hadisai
tare da hikayoyi masu ɗauke da muhimman
darussa da suka danganci rayuwar duniya da lahira. Tasirin wannan lamari ba ƙarami ne a rayuwar
Hausawa. Kuma shi ya sa idan Bahaushe ya kai mizanin wasu shekaru ko da yana
ashararanci, zai yi ƙoƙarin kama kansa ta hanyar ƙaurace musu. In ma
bai daina ba akwai matakan ladabtarwa da al’umma kan ɗaukar masa.
Yayin da Turawa suka zo ƙasar Hausa kuwa, sai
suka kawo tsarin karatunsu , suka ƙaƙaba wa al’umma shi,
son su da ƙin su, dole aka koye shi. Suka tsara ba wanda zai wasu mƙamai, sai wanda ya
koyi karatunsu. Karatun kuma a kullum safiya ƙoƙarin tabbatar da
tsarin danniya da mulkin mallaka yake yi. Sun yi ƙoƙarin karkatar da
matasanmu zuwa ga addininsu, tare da kawar da tsarin ilimin addinin musulunci
da salon rubutun da suka tarar muna amfani da shi, wato Larabci da ajami. Sun
maye hanyoyin tarbiyyarmu ta gargajiya da irin tasu, mai yaɗa alfasha da fajirci
a tsakanin al’umma. A ɓangaren adabi kuwa,
sun gabatar da fasalin nau’o’in adabinsu
da ke ƙunshe a cikin littattafai da jaridu da mujallu masu koyar
da ayyukan assha. Haka sun yi amfani da gidajen sinima da akwtunan talabijin da
na bidyo da na’urorin tauraron ɗan Adam da suke watsa fina-finai da ke koyar da ayyukan
assha da zare tausayi da kunya a tsakanin matasa maza da mata. Da irin waɗannan abubuwa ne suka
maye gurabun ɗakunan tsofaffi da na
amare, har ma da matattarar ilimin addini. Ai dole ne tarbiyya ta taɓarɓare ƙasa ta lalace
al’ummar ƙasa su auka cikin masifu da fitini iri-iri.
Tasirin da waɗannan abubuwa suka yi
a cikin zukatan matsa ba ƙaramar illa ba ce a sha’anin tarbiyyar al’ummar ƙasar Hausa. Sakamakon
haka ne, wasu magidanta kan yi husuma, ko su garzaya gaban hukuma don an
ladabtar da ‘ya’yansu a waje. Wasu ma har sukan yi tashin hankali a tsakaninsu
da ƙannansu
ko yayyinsu, don an kwaɓi ‘ya’yansu a kan
aikata ba daidai ba. Irin wannan lamarin har ya kai inda ɗa kan zargi mahaifisa
da cewa wai ya ɗora ɗansa karan tsana. A
wasu lokutan har akan sami canza yawu a tsakanin uba da ɗansa. Wannan rashin
tarbiyya ya kai matuƙa, har kunya ta fice daga idanun al’umma. Ina mafita take?
Hausawa kan ce: “ in ka so naka, ka
so shi kai kaɗai. Idan ka ƙi shi duniya ta so
shi. Wannan zance haka yake. Duk lokacin da mutun ya nuna ba ya so abin da zai ɓata wa ɗansa rai, to shi wata
rana sai ya ga ɓacin rai da baƙin ciki iri-iri da
zai fito daga wajen ɗan nan nasa. Kafin
bayyanar wannan yanayi, iyaye ba su cika nuna wa ‘ya’yansu jin daɗi ba kama yanzu ba.
Amma karance-karance adabin Turawa da yawan kalle-kallen fina-finansu yay i
mummunan tasiri a zukatan al’umma. Sakamakon haka ɗin ne ya sa iyaye
mata suka taka muhimmiyar rawa wajen taɓarɓarewar tarbiyya. Sau da yawa yaro tun yana
goye wasu iyayen ke ɓata shi, ta hanyar
saya masa duk wani abu da ya gani , ya nuna yana so. Irin haka kan kai ga sa yaro kuka, idan ya ga wani abin da yake buƙata. Wani zubin in ya ga wani abu ko ba nasa ba ne, zai nemi
a bas hi. Har akan sami waɗanda kan yi faɗa don su mallaki abin. Daga irin haka ne birbishin sata kan yi naso
a cikin zukatan yara, har su kai ga ɗauke kuɗin iyaye don su biya buƙatunsu.
Ta fuskar matasa da ke karatu a
makarantun sakandare kuwa, wasu iyaye ne kan ɓata tarbiyyar yaransu. Wannan kan faru
ta hanyar ba su maƙudan kuɗi in za su koma makaranta. Da isar su makarantar, sai su
watsar da karatun su shiga yawace-yawacen shashanci tare da abokai maza da ‘yan
mata, ba su wannan gida disko ba su wancan. Daga haka sai aga yaro ya faɗa ciki wasu munanan ɗabi’u, kamar caca da
shan giya da neman mata da sauran su. Duk lokacin da babu kuɗin, mai ba shi kuma
ya kau, sai ya fantsa fagen ‘yan sace-sacen kayan hukuma in ya sami aikin ko na
al’umma.
Rashin Ba Da
Kyakkyawar kulawa Ga Samari
A bisa al’adar ƙasar Hausa, yayin da
yaro ya kai matakin samartaka, akan jawo
shi a jiki na jan hankalinsa ana lurar da shi abubuwa nagari masu amfani ga
rayuwa ta yau da kullim. Ana kuma bas hi damar yin walwala gwargwadon hali,
tare da yi masa gargaɗI akai-akai. Haka
akan tanadar masa matsugunni a gidansu, don a sami damar kula da irin
take-takensa.
Saboda wayewar zamani, iyaye sun yi
sakaci sun yi watsi da nauyi da mahalicci ya ɗora
musu. Irin wannan wayewa ta haddasa taɓarɓarewar tarbiyya a duk faɗin ƙasar Hausa. Domin an ɗauki cewa yana da
‘yancin walwala, don haka yana iya zama duk inda ya so. Wani lokacin saurayi
kan yi sati ko fiye da haka bai leƙa gidansu ba, ba tare
da iyayen sun damu ba.
Waɗanda ma suka tanadar da matsgunni ga
saurayi, sai ka tarar an keɓe shi can inda babu wanda ya damu da abin da yake
aikatawa, balle a rinƙa taka masa birki, hasali ma an yi masa tanadin akwatin
talbijin da bidiyo da makamantan su, da ke iya zama sinadarin taɓarɓarewar tarbiyyarsa.
Domin ta irin waɗannan kafofi ne ake
kallo yadda ake aikata miyagun ɗabi’u, kamar fashi da makami da fyaɗe da sata kisan kai
shaye-shayen maye da sauran lamurran ta’addanci.
Kammalawa
Duk da kasancewar tsarin mulkin ƙasar nan ya amince
gwamnati ta sa baki tare da kyautata lamurran addini da al’adaun gargajiya,
amma waɗanda ke da alhakin
yin sun yi wa lamarin riƙon sakainar Kashi. Sakamakon haka ne, ya haifar da rashi
yi wa ilimin addini kyakkyawan tanadi a cikin manhajar makarantun ƙasar nan tun lokacin
da aka soma kafa su. Wannan ba ƙaramar illa ya yi ba wajen haddasa taɓarɓarewar tarbiyyar
al’ummar ƙasa. Domin bayar da ingantaccen ilimin addinin musulumci
shi babbar madogara wajen shimfiɗa harsashen ginin sahihiyar tarbiyya. Domin
shi ke koyar da nagartattun halaye da ke ɗauke da mutunci da gaskiya da riƙon amana da alkunya
da girmama kai da ƙaunar juna ga kuma tsoron Allah a ɓoye da bayyane. Irin
waɗannan halaye ne suka
yi tasiri a rayuwar magabatanmu, a sakamakon samun kyakkyawar tarbiyyar addinin
musulunci da suka yi, shi ya sa Turawa ke ganin kwarjininsu, har suka yabi
addinin musulunci. Ga abin da Sir. Herry Johnston y ace:
“Addinin
Musulunci wata babbar rahama ce ga duk ɗan Afirika da ya
Rungume shi. Domin yana
sa shi ya zama mai tsoron Allah, mai jaruntaka
Da ƙarfin zuciya, mai
mutunta kansa, kuma mutum mai kazar-kazar don
Tabbatar da kansa”
(Abdullahi,(b.kwt):25).
Abubuwan da suka yi ƙamfa a rayuwar mafi
yawan jagororin ƙasar nan. Saboda rashin ingantacciyar tarbiyyar addinin
musulunci. Sakamakon haka ne ya haifar da rashin tsoron Allah a cikin
zukatansu. Aka wayi gari suka auka cikin ɓarna iri-iri tare da wawure dukiyar, wanda ya
jefa al’ummar ƙasa cikin wani hali na ni-‘yasu.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.