Kishi kalma ce ta Hausa da ke cikin jerin jinsin kalmomin da masana harshe suka saka a ɓangaren sunaye na maza. Kalmar tana matsayin suna (noun).Takan ɗauki ɗafa-ƙeya. Irin waɗannan ƙare-ƙare ne suka wanzar da samuwar kashe-kashen kishi zuwa nau’i daban-daban. Amma da zaran an ce kishi kawai ba tare da an ambaci nau’in kishin kaza ba, to a kunnen mazauna ƙasar Hausa da sun ji, ba abin da zai faɗo musu a zuci, sai kishin da ke aukuwa a tsakanin mata da maza. Don haka, a wannan maƙala an ƙuduri aniyar gano yadda dangogin kishi suka yi fice da shige a wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Mamman Shata, don haka zai yi wuya a kawo misalai daga ilahirin waƙoƙin da ya yi, sai dai kawai a yi ƙoƙarin kawo misalai daga gwargwadon waƙoƙin da suka zo hannu. Haka an yi ƙoƙarin kawo bayanan masana daban-daban dangane da lamarin kishi da yadda ake tarbonsa da bambancinsa a tsakanin al’umma a sakamakon bambanci al’ada da muhalli. Duk an yi haka ne domin bayar da haske don saurin fahimtar inda aka dosa. Duk da haka maƙalar ta dubi yanayin kishi a waƙoƙin Shata wanda ya haɗa da kishin matan aure da kishin kansa da na zuriyarsa da kishin hani daga ƙarshe aka zo da  kishin amfani.

kishi

Nason Kishi a Waƙoƙin Alhaji (dr.) Mamman Shata Katsina

Dr. Adamu rabi’u bakura

arbakura62@gmail.com

08064893336

1.0 Gabatarwa

Kishi lamari ne dake gudana a rayuwa, kuma abu ne da ake samu a kowace irin halitta, ko kuma a tarbe shi bisa tsarin al’adu ko kuma a luggance, kamar yadda masana suka yi nazari, sai na ƙarshe a kawo bayaninsa kamar yadda yake a aikace, wato yadda masana da manazarta suka kalle shi.

            A bincike neman gano matsayin kishi, halitta ko al’ada da ake samu a kowace irin  halitta. Heiman  da Iyon,  (1998) sun yi nuni da cewa yadda ake kallon kishi a tsakanin kowace al’umma ta mabambantan fuskoki, shi ya sa suka so su amince da cewa kishi ba wani abu ne da ya wuce yadda kowace halitta ke tafiyar da shi, kuma kowace al’ada na iya sauya masa fasali. Tunanin da masana ke da shi, na cewa maza kamata ya yi kishinsu ya ɗokanta ( zaƙu) ga idon matansu na kwanciya da wani namiji na daban da su, bai kuma dace su ƙyale wannan hali ba, alhali su matan bai dace su damu ba idan namiji ya nemi wata a waje ba, domin wannan fagensa ne, bai kamata a ce ya janye ra’ayin masana ga fahimtar kishi ba. Domin  duk wani abu da ya shafi zaman tare, tsakanin mace da namiji, yana ginuwa ne bisa yadda suka tsinci kansu dangane da yanayi da addini da siyasa da sauran su.

            Sai dai duk da cewa ba a da wani tabbaci gurbin da za a dasa jijiyar kishi a tsakanin halitta  da al’ada, wasu masana, kamar yadda Heiman da Iyon, (1998) suka yi nuni, sun fi amincewa da cewa kishi yana tsakanin waɗannan sassa biyu ne na rayuwa, ba don komi ba sai ganin cewa, duk da cewa ana samun kishi a kowace irin al’umma, amma yadda ake gudanar da shi ya sha bamban, saboda canjin al’adu da yanayi. A waɗansu al’ummu, ana iya ba ka matar wani ka zauna da ita na wani lokaci, idan  ka biya waɗansu keɓaɓɓun kuɗaɗe, wasu kuma ana yi maka maraba da amarya ne a yayin da ka sauka a gidan, a matsayin baƙo, alhali a wata al’ummar ko kallon matar wani, kan sa a sare maka kai. Wannan ya sa masu wannan nazari ke ganin ba yadda za a yi a ce a tsayar da kishin ga halitta kurum, ba tare da an taɓo al’ada ko ɗabi’a ba, ba don komi ba , sai don ganin yadda  kishiin kan canza, saboda tsawon zamani ko canjin yanayi.

            Bisa irin wannan tunanin ne ya sa, wasu masana halitta da tunanin ɗan Adam ke ganin idan dai har akwai kishi a tsakanin ‘yan Adam, to ba za a rasa shi ba a tsakanin kowace irin halitta da ke doron ƙasa ba, abin da ba a da masaniya a kai shi ne, ko kishin dabbobi daidai yake da na mutane a bisa misali. Wannan tunani shi ya fito da fagen nazarin tunanin dabbobi, wato ETHOLOGY, kamar yadda Gale Encyclopedia of Psychology ya tabbatar. Masana wannan fage suna masu ra’ayin cewa, tun da ko an tabbatar da cewa kusan kashi 80 na ƙwayar halittar dabbobi, musamman gwaggwan biri, iri ɗaya ne da na mutun, to kishi yana nan tsire ke nan a rayuwar dabbobi su ma, sai dai ƙila yadda suke aiwatar da shi ya sha bamban da na mutane, saboda yanayi da ake rayuwa ya bambanta.

            Ganin haka ya sa masana suka shiga nazarin kishi bisa kowace fuska da suka ci karo da ita, ba kuma tsakanin mutun ba, har ma da dabbobi da kwari da tsuntsaye, domin a gane irin yanayin kowace halitta. A cikin littafinsa The Psychology of Jealousy and Envy, Peter ya kawo dukkan tambayoyin da mutun zai iya yi dangane da kishi da ƙyashi a tsakanin halitta, kamanci da yadda yake gudana, ire-irensa, nazarin tunanin ɗan Adam, da yadda yake a cikin ginuwar iyali da kuma addini, a taƙaice dai ba wani ɓangare na rayuwa da kishi bai shiga ba.

            Da yake ba ta tunanin ɗan Adam kawai masana suka dubi lamarin kishi ba, ya dace a nan a dube shi ta fuskar addini, ko ba komi yana daga cikin al’amurra da suka daɗe tattare da ɗan Adam tun farkon halitta. Ga ‘yan ɗariƙar Katolika, suna ganin kishi bai wuce ƙyashi ba, ko kuma ana iya cewa tare suke tafiya ɗan jimma da ɗan jimmai ne. Sun yi nuni da cewa, kishi bai wuce ɓacin rai ko  hassada da wani kan ji game da abin da wani ya samu na cigaba ba. To sai dai kamar yadda The Catholic Encyclopedia ya nuna, yawancin ƙyashi ya fi zuwa a tsakanin masoya, duk kuma da cewa bai dace ba a addinance, domin kamar yadda suka yi nuni, idan ƙyashi ya yi yawa, to yana iya zama zunubi a gurin Ubangiji.

            Haka wannan tunani ya kasance ko cikin Bayibul, inda aka nuna cewa, akwai kishi, akwai ƙyashi, Ubangiji mai kishi ne.

            Haka wannan fasali yake a addinin Musulinci, domin kuwa Allah ya kasance Ubangiji da bai da farko, bai da ƙarshe. Bai haihu ba ba a haife shi ba, bai da mata ko wani mataimaki. Haka kuma bai da abokin tarayya, a taƙaice dai ba shi da kishiya, balle kuma a yi tarayya da shi.

Zai fi dacewa a kawo ma’anonin tubulan ginin wannan maƙala. Tubulan kuwa sun haɗa da: naso, kishi da kuma waƙa.  

1.1 Ma’anar Naso:

            Kalma ce ta Hausa da ke cikin tsarin sunaye jinsin namiji da ke ɗauke da ma’anar: “shiga ko bazuwar wani abu cikin wani, ko yaɗuwar wani abu a kan wani abu. Wato wani abu ya shiga cikin wani abu kana ya watsu CNHN.JBK,( 2006:357).

1.2 MA’ANAR KISHI :

            Saboda haka duk wani nazari ko bayani da za ayi kan kishi, bisa matakan da masanan da suka gabata suka shata ya kamata a biyo, kuma a kan su ne sauran masana, masu nazarin lugga da al’ada suka dubi tasu ma’anar, suka kuma gabatar da ita. Bari mu soma da duba ma’anar kishi daga Ƙamus na THESAUSRUS, inda aka nuna cewa, kishi shi ne matuƙar damuwa, ko kuma ɓacin rai dangane da wata alaƙa tsakanin mutane, ko kuma rashin yarda da miji dangane da wata mata a waje, haka kuma nuna isa na iya zama kishi.

            Shi kuwa Bargery, (1934) a ƙamus ɗinsa, ya bayyana ma’anar kishi da cewa, “ shi ne ganin ƙyashi da ke tsakanin kishiyoyi”. A cigaba da bayanin kishi, ya kawo rabe-raben kishi kamar haka: kishin birni, kishin kai, kishin sauri da kuma kishin zuci.

            A Hamly, (1971:891)  an bayyana ma’anar kishi da cewa: “ Kishi wata hanya ce ta bayyana rashin jin daɗi a kan nasarar da abokin hamayya ya samu”.

            Har wa yau an kuma bayyana kishi da cewa:  “Rashin kwanciyar hankali da ke tattare da zargi da tuhuma ko tsoron hamayya a kan wanda ake ƙauna ko ake burin a ƙulla soyayya da shi” ( Fassarar marubuci da ƙamus  na Bargery).

            Cikin CNHN, (2006:247) a ƙamus ɗinsu, an bayyana ma’anar Kishi ta fuskoki uku kamar haka: i. Rashin jituwa da nuna ƙyashi irin wanda matan auren mutum ɗaya ke nuna wa juna. ii. Nuna gaba ga wani a kan wata mace. iii. Tsayawa da nuna ƙwazo a kan wani ra’ayi ko sana’a da sauransu. A ƙarin bayaninsu sun nuna cewa, ana iya cewa mai kishin ƙasa ko mai kishin zuriya ko mai kishin zuci. Wato dagewa da nuna ƙwazo a kan wani abu na kirki da mutum ya sa a gaba don cimma buri.

            Shi kuma Talata Mafara, (2002) ya fassara ma’anar Kalmar Larabci ta “ALGIRAH” wadda ke ɗauke da ma’anar kishi da cewa: “ Canzawar zuciya da motsawar jini domin nufin ramuwa, saboda dalilin tarayyar wani a kan wani abu da ba ya karɓar tarayya”. A cigaba da bayaninsa ya nuna cewa: “ mafi tsananin kishi shi ne wanda ake samu tsakanin ma’aurata”.

            A cikin littafin bayanin kalmomin harshen Larabci mai suna AL-MUJAMAL-WAT an fassara Kalmar Larabci ta kishi, ALGIRAH, da cewa: Namiji ya yi kishi ga mace ko mace ta yi kishi ga namiji, idan ransa ya motsa saboda macen ta bayyanar da adonta ga wani, ko kuma ta juya masa baya, tana mai sha’awar wani. Haka ita ma idan ranta ya motsa, za a ce ta yi kishi, idan mijinta ya karkata ga wata mata ta daban, kamar yaddaTalata Mafara, (2000:12) ya nuna.

            Shi kuma Malan Jarjani a littafinsa mai suna: ATTARIFAT ya bayyana ma’anar kishi da cewa : Ƙin karɓar tarewa da wani ga abin da yake haƙƙin mutun, kamar yadda  Talata Mafara, (2000:12) ya zo da shi.

            Yayin da Malam shankidi a cikin littafinsa mai suna ZADUL-MUSLIM ya bayyana ma’anar kishi da cewa: “ kishi ga taliki yana da ma’anar kariya da nuna ɗaukaka Talata Mafar, (2000:13). A cigaba da bayaninsa ya nuna cewa: Wannan shi ya sa ɗaya daga cikin malaman harshen Larabci mai suna Malam Nuhas, yake  cewa: “ kishi shi ne namiji ya zama ya kiyaye matansa da wani na daga ‘yan-uwan zumunta, ya zama ya hana wani shiga a wajensu ko kuma wani wanda ba muharrami ba ya zama ya gansu.

            Shi kuma Malam Mazin Alfuraih, a yayin da yake bayyana tasa ma’anar ta kishi cewa ya yi: “ Kishi halitta ce ta asali, kuma ɗabi’a ce mai tushe ga mace. Kuma kishi baya kasancewa, sai in akwai soyayya. A koyaushe mace ta zama mai son mijnta, to za ta yi kishinsa sosai. Sai dai kishin yana iya jan ta zuwa wuta ko kuma ya sanya ta aljanna, idan ta ji tsoron Allah Talata Mafara, (2000:14).

            Yayin da Abubakar Abbas ya bayyana ma’anar kishi da cewa: “ Kishi shi ne sosawar zuciya da ɓacin rai da suke jawo fushi, a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani, a kan abin da wani ya keɓanta da sonsa, ko mallakarsa(1418AH:3).

            Idan muka dubi waɗannan ra’ayoyi na malamai, za a iya ƙwanƙwancewa tare da tabbatar da cewa, kishi wata hanya ce ta gwagwarmaya da ke tattare da  zargi da tuhuma da saɓani da rashi jittuwa da husuma da mugun nufi, domin ƙoƙarin kare keɓantacciyar ƙauna ga abin so ba tare da yin tarayya da wani ba.

            Idan muka dawo a kan ma’anar kishi ta fili kuma wadda da zaran an faɗe ta kowa zai fahimta, ba tare da wani tunani ba. A wannan fagen ma manazarta da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ra’ayoyinsu dangane da ita wannan ma’anar Ingawa, (1994) ta bayyana ma’anar tana mai cewa: “ Kishi a Hausa na nufin wata hanya ta tsokana don nuna fifikon kariyar abin ƙauna dangane da irin matuƙar son da ake wa wannan abu”.

            Ita kuwa Gwandu, ( 1997) ta bayyana ma’anar kishi da cewa: “ Shi ne wani hali na ƙaƙa ni kan yi, wanda yake sakar wa mutun wani ƙololo na baƙin ciki a zuciyarsa na zafin cewa wani abu ya faru”.

            Abubakar A. Muhammad, shi kuwa bayyana ra’ayinsa ne game da kishi inda ya ce: Kishi wani nau’i ne na ƙiyayya wanda ya ƙunshi jiyewa, ƙyashi, hassada, da ake samu a tsakanin Hausawa musamman mata.

            A ra’ayin Yakubu Aliyu Gobir kuwa, yana ganin ma’anar kishi da cewa: Kishi shi ne samun damuwa a kan wata ni’ima ko baiwa da Allah ya yi ma wani mutun, tare da fatar ni’imar nan ta gushe (ƙare) ko kuma ta dawo gare shi, ko jin cewa, ni’imar ba ta dace da kowa ba sai shi.

            Ta la’akari da ma’anonin da waɗannan malamai suka bayar dangane da kishi, zan iya cewa, kishi shi ne tsananin son da mace ke yi wa mijinta ko neman keɓancewa zuwa ga mijinta ko wanda ta ke son ta aura, da take ƙauna, da kyakkyawar fata gare shi, tare kuma da nuna ƙiyayyarta ga duk wata da ke sonsa da aure ko kuma shi yake sonta da aure. Ina kyautata zaton cewa, shi wannan nau’i na kishi ya fi shahara ne saboda kasancewar an fi aiwatar da shi a tsakanin al’ummar Hausawa yau da kullum.

1.3 Ma’anar Waƙa:

            Waƙa a bisa ma’anarta a luggace tana nufin furta abin da ke cikin ƙwalwa Bargery, (1934:1075). Sau da yawa akan ji Bahaushe na cewa:

·         Na sha waƙa zuwa aikin Hajji.

·         Na waƙa yi masa dukan tsiya.

·         Na waƙa masa farashin kayan.

·         To, Allah Ya sa ba waƙa ba ce.

A wata ma’anar kuwa, waƙa takan kasance wata murya ko zaƙin murya mai shiga zuciya da faranta rayuwa. Misali Bahaushe kan ce:

·         Ai na zaci waƙa ce.

·         Ya matse sauti kamar mai waƙa.

·         Zaƙin murya sai ka ce zabiya.

Ta wata fuska kuwa, waƙa takan kasance wata Magana wadda akan rera da baki, aka tsara bisa wani zubi na musamman, Garba, (1990:152).

Idan aka dawo a ɓangaren adabi kuwa, masana da dama sun ba da ma’anar waƙa a wurare daban-daban gwargwadon fahimtarsu. Daga cikin masanan, Gusau, (1984) ya bayyana ma’anar waƙar baka da cewa:

Waƙar baka ita ce wani saƙo cikin zance na azanci

Da ake rerawa ba faɗa kurum ba, ta cikin hikima da

Fasaha da zaɓaɓɓun kalmomi, waɗanda suka dace da

Saƙon. Kuma tana zuwa gunduwa-gunduwa, dangane da

Sautin murya da kiɗa da amshi da gaɗa da taɓi ko zabiyanu

Mai saka zuciya jin daɗi.

            Haka kuma Umar, (1987) na cewa:

Waƙa ita ce nau’in sarrafaffen harshe da ake gabatarwa

Da sigar gunduwoyin zantukan da ake kira baitoci ko ɗiyoyi

Waɗanda ake ginawa a kan kari ƙayyadadde, kuma ake rerawa

Da wani irin sautin murya na musamman.

            Yayin da aka dubi waɗannan ma’anonin dam asana suka bayyana za a tarar sun yi ƙoƙarin fayyace mana cewa, waƙa wata tsararriyar Magana ce da ke ƙunshe da fasaha da hikima da ake rerawa gunduwa-gunduwa, cikin wani amo na musamman.

2.0 Yanayin Kishi a Waƙoƙin Alh. (Dr.) Mamman Shata

Kafin a ce wani abu game da wannan rukuni, zai fi dacewa, a yi ɗan taƙaitaccen bayani game da rukunin da mawaƙin yake. Domin yin haka zai ba mu damar fahimtar inda aka fuskanta.

Alh. (Dr.) Mamman Shata mawaƙin  jama’a ne,wanda ke rera wa jama’a waƙoƙi, ba tare da ƙebancewa ga wani rukuni na jama’a ba. Mai aiwatar da irin waɗannan waƙoƙin, shi ake yi wa laƙabi da makaɗin jama’a. Hasali ma bai ta’allaƙa ga kowa ba. yakan yi wa kowa da kowa kiɗa da waƙa, muddin dai aka yi masa hasafi ko kuma ya ga alamar zai sami abin masarufi. Don haka bai da takamaiman wani rukuni da yake yi wa waƙa, balle ya yi taka-tsantsan ko ya nuna jin kunya ko sanin ya kamata, domin kare martabar wani. Wannan shi ya sa ya bambanta da sauran rukunin mawaƙa, kuma shi ya haifar aka samu bambancin yadda yake gabatar da kishinsa a yayin da yake aiwatar da sana’arsa. Alhaji Mamman Shata na ɗaya daga cikin mawaƙan jama’a, idan ma an ce shi ne jigonsu, ba a yi ƙarya ba.

2.1 Kishin Matan Aure

Mawaƙan jama’a kan bayyana kishinsu ta hanyoyi da dama. Wasu kan bayyana kishin nan da ke tsakanin mata da miji, musamman inda aka samu rabuwar aure a  tsakanin ma’auratan. Idan kuwa an samu faruwar haka, mawaƙi ya samu labarin wani na neman matar da ya saki, to a cikin irin wannan hali mawaƙin kan fito fili ya bayyana kishinsa ta hanyar yi wa wancan zambo ko ma ya fito fili ya zage shi. Za a iya ganin irin wannan a cikin waƙar Alƙali Maɗanɗani ta Mamman Shata. Hasali ma bincike ya tabbatar mana da cewa ya gina tulabin wannan waƙar ne a sakamakon kishin matarsa mai suna Yelwa, wadda alƙali ya raba shi da ita. Daga baya kuma sai alƙalin ya koma yana nemanta tare da wani mai kuɗi, Bakura, (2003:129). Hasali ma Shatan ya yi wanka mai kamar jirwaye a cikin waƙar mai amshi kamar haka:

Ɗan Liman uban Ciroma, ɗan Shehu Garkuwa.

A cikin ɗaya daga baitin waƙar ne yake cewa:

Ni an fi ni,

An ƙwace man matata da na so

Wannan shi ya ƙwace

Matar shata ya tai ya ci.

Idan muka dubi wannan baitin za mu iya fahimtar cewa, an aiwatar da waƙar ne domin a huce haushi. Hasali ma Shata ba ya tsaya kawai a kan bayanin an yi masa ƙwacen mata ba, har ya kai ga zagin wanda ya ƙwace masa matar, a inda yake cewa:

Wai na ji kahurin kirari ranar yake mata

Ga ta baƙa gajeruwa.

Ya ga gajeruwa ‘yar baƙa

Shegen Tudun-Wada.

Shegen ya yi gida a Zariya,

Tudun-Wada.

 

Yau ga kafiri,

Marar kunya ɗan baƙar uwa,

Ku kore shi Zariya,

Nan dai zuwa ya yi.

 

Allah tsine ma,

Allah watse maka,

Ka kau ji sau biyu,

Tun da ka hau.

Ruwan cikin matata gajeruwa.

Rafukka, (1999:56-60).

Waɗannan ɗangaye sun nuna yadda tsananin kishi ya sa Shata fitowa ƙarara, ba tare da shakka ko tsoro ba, ya ambaci abokin hamayyarsa da cewa shi kafiri ne, a wani gun kuma ya ce masa shege, hasali ya yi wa jama’a hannunka mai sanda, domin a gane abokin hamayyar tasa ta hanyar nuna mazauninsa tare da bayyana wa jama’a cewa baƙo ne, don haka a kore shi. Daga ƙarshe dai ya tsine wa abokin hamayyar tasa, kuma ya ce ya yi haka ne a kan kishin ya sadu da matarsa.

Abin kula a nan shi ne Shata ya yi waƙoƙin ne domin ya huce haushinsa a kan yadda alƙalin ya kashe masa aure alhali ya son matarsa Yalwa. Sai dai ba yadda zai yi da alƙalin, ta hanyar zambo ne kawai zai kece rainin da ke tsakaninsa da shi. Kishin mata idan har ya tsira ba yakan gushe ba. Mutuwa kaɗai ce ke kawar da shi, shi ma sai in duk abokan hamayyar sun bar sararin duniya. Dalili ke nan da ya sa saɓanin da ke tsakanin Shata da alƙalin da ya kashe masa aure bai gushe ba har tsawon lokaci. Hakan ya haifar da ginuwar wasu ɗiyan waƙoƙinsa a inda yake cewa:

Mai cinikin jifa an  jefai,

Bana dai shegen ya karye

Yau ai asali nai da ɗan Nijar ne

In ka korai duk daidai ne

Yau ai asali nai da ɗan Nijar ne

In ka korai zan sha iska

Wai yau shi ku ji alƙali ne

            (maimaitawa)

Wawa yai shari’a ta ɓaci

Shegen tsoho miƙe kai tafiyar

Ɗan bori kyalla.

Ji yadda kishi ya taso wa Shata har yake kamanta alƙali da wani gurgun ɗan bori wanda in zai hau bori yakan jefa ƙafa, ‘yan kallo na dariya, Ƙanƙara,( 2013:285). 

2.2Shata A Fagen Kishin Kansa

Mawaƙan jama’a ba su tsaya a kan bayyana kishin da ke da alaƙa da mace ba, har ma akan sami lokuttan da suka nuna kushe ga junansa, saboda tsananin kishi. A irin wannan yanayi ne akan sami mawaƙi na nuna kishi kansa ta ƙoƙarin kare mutuncin da kuma irlinsa a tsakanin al’umma. Za a iya samu kyakkyawan misali a cikin waƙar Mamman Shata, Bakandamiya.

A cikin wannan waƙar, Shata ya nuna kishin kansa ta hanyar barazana domin ya jawo hankalin jama’a wajen sauraren waƙarsa, wanda hakan zai sa ya sami abin duniya, a inda yake cewa:

Matsoraci ba shi zama gwani ko wanene,

Ya zama kamar ni hilin waƙa,

Saranin waƙa ban san tsoro ba.

In na fito shata ne,

Kun sanni na sanku,

Sai ƙaƙa.

Bakura, (2003 : 131).

Kishin kai ya sa Shata koɗa kansa da kansa, a inda ya ke nuna cewa shi gwanin waƙa ne, wanda ba ya tsoro ko nuna fargaba a duk lokacin da aka nemi ya shirya waƙa nan take. Hasali ma saboda kishi, Shata yake ɗaukar wasu rukunin mawaƙa ba bakin komai ba, waɗanda ba su kai matsayin su yi jayayya da shi ba, don haka ne yake cewa a cikin waƙar:

Na ƙyale banjo da kukuma,

Wargin yara ne”.

Mawaƙan baka na jama’a sukan gina waƙoƙinsu ta amfani da tubalan kishin kai. Sukan yi haka ne domin kare martaba da zubewar mutunci a idon jama’a. Domin ba abu mai muni a ƙasar Hausa da ya wuce, a ce musulmi yana tsafi. Hasali ma ko da yana yi ba zai so a bayyana shi a matsayin matsafi ba. Don haka ne Shata ya fito yana ƙalubalantar masu zargin sa da cewa yana amfnai da iskoki wajen yin waƙoƙinsa, a inda yake cewa:

Ba malamai ba ne,

Ba bori, ba na tsafi,

Ni haka Allah yai ni,

Da yai ni kau ya tsare ni,

Bakura,(2003: 132).

Mawaƙin bai tsaya nan ba, sai da kishi ya sa ya fito fili ya faɗakar da masu wannan da’awar, ta hanyar nuna musu irin halayyar nan ta ɗan-Adam ta son kai da babakere ga duk wata harka da ta shafi mallakar abin duniya da kuma jin daɗi, inda koyaushe mutum zai fi son komai daga shi sai ‘ya’yansa, musamman abubuwa da suka shafi dukiya, kamar kuɗi da gidaje da motoci da kuma kyawawan mata. Misali Shata na cewa:

In malami ne ya fara shirya ‘ya’yanshi,

Su samo, su kawo mashi,

ko ko su ba sa son samu sai dai ni,

da tsohona, a’a, da sakal,

ku bincika dai, samu fa!

In bori ne, su fara girka ‘ya’yansu,

Su samo, su kawo masu,

Ko ko su ba sa son samu sai dai ni da tsohona,

Nairori, gidaje da motoci ga sutura,

Ga mata, zumdum-zumdum,

Kai ta nemo ma ɗan wani, kai ga naka,

Bakura, (2003: 133).

 

 

2.3 Kishin Ƙasa

Ta fuskar kishin ƙasa kuwa, za mu tarar cewa, mawaƙan baka sun yi ƙoƙarin cusa wa al’umma kishin ƙasarsu, ko kuma na wani ɓangaren da suka fito. Mawaƙan kan yi amfani da tubala daban-daban domin gina wannan yanayi. Ire-iren waɗannan tubalan sun haɗa da gargaɗi faɗakarwa, wayar da kai da dai sauran su. Misali Alhaji Mamman Shata ya rera wata waƙa mai suna ‘Yan Arewa ku bab bacci’, a inda yake ƙoƙarin cusa wa ‘yan uwansa al’ummar Arewacin kishin yankinsu da ma ƙasa baki ɗaya a kan su dage ban da zaman banza don su tono albarkacin da ke jibge a yanki, wanda hakan ba zai yiyu ba sai an falka daga shagalar da aka yi. Ga abin da yake cewa kamar haka:

‘Yan Arewa ku bab bacci,

Nijeriyarmu akwai daɗi,

Ƙasar Afirka baƙar fata,

In ka yi yawo ciki nata duk,

Ba kamar Nijeriya gidan daɗi,

Balle Arewa uwad daɗi.

Bakura, (2003:134).

2.4 Kishin Zuriya

            A wannan ɓangaren kuwa, za a tarar cewa, Shata ya yi ƙoƙarin nuna kishin kansa ne har ma da zuriyarsu, a sakamakon abin da wani basaraken yankinsu ya yi musu na nuna ƙarfin mulki, ta hanyar kwace musu gona da danne masa kuɗi tare da halaka masa shanu ba don komai ba sai don yana talakan ƙasarsa. Wannan lamarin ne ya ruruta wutar kishin mawaƙin har ya fito fili ido rufe ya yi masa zambo a cikin waƙoƙi da dama da ya sha sabuntawa tare da ƙarin wasu ɗiyan waƙar. Misali, Shata na cewa:

            Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa,

            Allah ya tsine ma tsohon mazinaci,

            Allah ya tsine ma da kai da iyalinka,

            Wallah alhamdu lillah hankalina ya kwanta,

            Wallahi alhamdu lillahi ba abin da ya dame ni,

            Yanzu babban ɗan bai gari,

            Babban jikanshi kuma yana kama agwaginmu,

            Gidan ya lalace.

            A nan za a fahimci tsabagen kishi ne ya sa Shata ya fito ido rufe ba tare da nuna tsoro ko kunya ya zagi wannan basaraken.

            Haka kuma kishin ya sa ya yi amfani da kalmomin wulaƙantawa wajen fito da siffofin abokin hamayyarsa wanda ya yi wa ƙazafi a cikin zambo don al’umma su ji su rena shi. Misali ya ce:

            Gaishe ka mahaukaci,

            Macuci mamugunci.

            Yana sanɗa ta da bindiga baba a harben,

            Yana nema na da gatari wai zai saran.

(Waƙar Gagara Badau).

Wannan babban wulaƙanci ne ga sarki, domin matsayinsa ya wuce haka a ƙasar Hausa.

2.4 Kishin Hani

            Shi ne inda wani kan yi tasiri wajen hana wani mutun ya yi wa wani alheri. Hakan kan faru ne yayin da ɗan Adam ya mallaki wani mutun ta hanyar bayar da shawara ko tilasta masa yin abu ko hana shi ya yi wa wani alheri ko da kuma murmushi ne. a sakamakon haka ne Shata ya yi wa wani masoyinsa zambo. Saboda ya roƙi Alh. Muhammadu Adamu Ɗankabo mota bambalista, amma sai wani ya hana Ɗankabon ya ba Shata motar. Haka kuma lokacin da mai kuɗin ke bukin auren ‘ya’yansa, Jarman ya gayyato Shata suka tafi Gusau, amma sai tajirin ya hana Shata yin waƙa. Wannan lamarin ya tabbatar masa attajirin bai ƙaunarsa. Don haka sai Shata ya ƙulla ɗiyan waƙarsa a inda yake cewa:

            Wata rana a Gusau aka yi buki,

            Bukin kuma yac cika ya batse,

            Na hangi uban buki a tafe,

            Na miƙe in kwashi nairori’

            Sai gas hi da ‘yar baza ta rawa,

            Na ce yaran Kanon Dabo ku taho ya fara hali nai,

            Yanda duk ka shirya ɗankama sai ya yi ma batun banza.

            (Waƙar Bala Gaye da Ɗankabo), 

Ƙanƙara, (2013:286).

Haka kuma akwai inda Shata ya yi masa zambo a ciki shekarar 1993 a wata waƙar da ya rera ta kamar haka:

            Wutsiyar akuya Bala kuturu,

            Ba ki gaji rufin asiri ba,

            Watarana a Gusau aka yi buki,

            An gasa nama na ‘yan birni,

            Kuturu yaj jefa hannu nai,

            Na ce ba na cin naman kuturu,

            Ya jefa hannu nai,

            Na ce masu ba na cin naman kutur,

            Ya jefa hannu nai ni ko ga ni da yatsuna,

            Idan kuma ya yi musun kuturta tai,

Riƙe shi ka duba yatsu nai,

            In ta tabbata sai ka kom nan,

            Baya sarkin rashin kunya,

            Kare baka san harara ba,

            In baicin rashin kunya,

            Mai gidansu ya ce aboki nai,

            Niko in na raɓa na cuci,

            Mutum ba na ce mai abokina.

Ƙanƙara, (2013:287).

Haka a cikin shekara ta 1996 Shata ya ƙara yi masa wani zambo duk a sakamakon abubuwan da ya yi masa. Ga abin da ya ce:

            Angulu gidan munafunci,

            Kasuwar ga da ke ake cinta,

            Ki komo nan kina kala,

                        (maimaitawa).

            Kara da kiyashi ɗan baba,

            Dibi duk sun ɗauke shi sun watsar,

            Babban attajirin Bauci na ji,

            Ya ɗauke shi ya watsar,

            Ka ji Isansi da ke cikin Katsina,

            Shi ma ya ɗauke shi ya watsar,

            Ka dubi kumya ga Kanon Dabo,

            Kunya ga Kanon Dabo,

            Su ma sun ɗauke shi sun watsar,

            Tsoho Amale da ke Ƙaura shi ma

            Ya ɗauke shi ya jefar,

            Ruwan zafi kake ɗan baba,

            Kowag gumtseka ya furzas.

                        (maimaitawa) 

Ƙanƙara, (2013:288).

Dubi irin yadda Shata ya yi wa attajirin zambo sakamakon kishin hani. Irin wannan nau’in kishin ne kan haifar da kishin uwar miji da na ƙanin miji da na masu hidimar gida.

2.5 Kishin Amfani

            Nau’in kishi ne da mutum zai nuna damuwa a kan wani da ya fi shi samun wani abin amfani, kamar kayan gona ko abokan ciniki ko shahara da sauransu. Mai irin wannan nau’in kishi ba ya damuwa da duk abin da wani ya samu matuƙar bai fi nasa ba. Sakamakonsa kan haifar da sihirce-sihirce domin ganin an fi kowa. Shata ya yi manuniya a cikin waƙarsa ta: “Hauwa mai tuwo Innar Dije” inda ya ce:

            Tsaya wata mai tuwo a cikin birni,

            Tuwo-tuwonta take birni,

            Takan tuwonta ta saida duk,

            ‘Yan birni suka ruɗa ta’

            Sun zuga ta sai taj ja Hauwa,

            Sai ga shi tai tuwon ba ta saida ba,

            Ta kai shi kasuwa ba ta saida ba,

            Ta yi talla ta gaza saidawa,

            Ta Kai shi gida ba ta saida ba,

            Sai tay yi tsugunne tana kuka af,

            Wayyo niya Allah!

            ‘Yan birni kun iza ni kun gaza fid da ni.

                         Gusau, (2009:336).

            A duk waɗannan misalan da suka gabata za a ga irin yadda kishi ya yi naso, musamman idan aka yi la’akari da salon da mawaƙin ya yi amfani da shi ta tsalma zambon waɗanda yake hamayya da su a cikin waƙoƙin masoyansa.

3.0 Kammalawa

            Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin gano cewa, lamarin kishi abu ne da ya zama ruwan dare game duniya, da ake iya samunsa a kowace halitta musamman bani Adam. Saboda haka ba abu ne da za a keɓance shi ga wani jinsi na daban ba. Kuma in ya yunƙuro ba sauran zaman lafiya, sai an haras da shi. Wannan ne ya sa Hausawa kan yi masa kirari da kumallon mata. Hasali in aka yi la’akar da jerin misalan kishin da aka kawo daga cikin ɗiyan waƙoƙin Alhaji Mamman Shata da sigoginsa da abubuwan da suka wanzar da shi a tsakaninsa da al’ummar da lamarin ya shafa. Daga waɗannan bayanai za a iya fahimtar cewa kishi ya yi fice da shige a kowace irin rayuwa ta al’umma, hasali ma shi ne ginshiƙin ɗorewar rayuwar al’umma, idan ta rasa shi kuwa ba za ta iya taɓuka komai na rayuwa. Kuma duk al’ummar da ta rasa shi, za ta ga taskun duniya.

Manazarta

Tuntuɓi mai takarda.