Ilimin walwalar harshe, wani ɓangare ne da ya keɓanta da nazarin ilimin harshe, da al’ada da tsarin zamantakewa a tsakanin al’umma. Hasali ma yana bin diddigin halayyar zaman jama’a da harshe wanda ya danganta da kimiyyar zamantakewar ɗan-Adam musamman halayyar zaman ɗan Adam da ilimin halayyar al’adunsa da kuma ilimin halayyar zaman jama’a. Don haka ne wannan muƙala ta yi ƙudurin bayyana irin rawar da harshe kan taka wajen gudanar da rayuwar ɗan-adam. Da farko an kawo ma’anar harshe da muhimmancin sa ga ɗan-Adam da kuma irin abubuwan da yake aiwatarwa ga al’umma, har ya sarrafa ɗan-Adam cikin hulɗa ko mu’amalarsa ta yau da kullum. A daidai shekarar 1930 ne aka sami wasu masana biyu, Sapir da Whorf da suka bayar da muhimmiyar gudummawa da ke ƙarfafa hujjar yadda harshe ke sarrafa ɗan Adam tamkar yadda ɗan Adam ke sarrafa harshen. A muhawarar da suka gabatar, sun bayar da misali da harshen Indiyawa mazauna Amurka ne, waɗanda aka nuna harshensu ne ya haifar da kasancewar ra’ayoyinsu game da halittun duniya suka sha bamban da na sauran jinsin da ke amfani da harshen ƙasar Turai. Whorf ya yi da’awar cewa, ‘yan ƙabilar Hopi Idian da ke zaune a yankin Arizona, ya sa sun fahimci halittun duniya akasin da yadda sauran ƙabilun da ke magana da harshen Ingilishi suka fahimce su. Saboda a tsarin sigar ginin nahawun harshen ‘yan ƙabilar Hopi an bambanta abu mai rai da maras rai. Har ma sun ɗauka girgije (cloud) da dutsi (stone) duk abubuwa ne masu rayuwa (living thing), wanda harshensu ne ya sa suka yi amanna da haka. Yayin da tsarin sigar ginin nahawun Ingilishi bai alamta haka ba. Wannan shi ya sa ɗan asalin harshen Ingilishi bai ɗauki halittun duniya tamkar yadda ‘yan ƙabilar Hopi ke kallon su ba. A ƙarshen hasashen Whorf ya kamala da cewa, “ Mun karkasa halittu a bisa ga tsarin da harshenmu na asali ya tanadar mana (Yule, 1998:247). Wannan wata manuniya ce da ke tabbatar da yadda harshe kan sarrafa ɗan Adam.
Yadda Harshe Ke Sarrafa Ɗan-Adam
Dr.
Adamu rabi’u bakura
08064893336
2.0 Ma’anar
Harshe
Masana harshe sun bayyana
ra’ayoyinsu dangane da ma’anar harshe. Daga cikin ra’ayoyin akwai: Crystal ( 2008
) ya bayyana cewa, “ Harshe wani tsari ne na furici wanda ɗan Adam yake amfani
da shi don sadarwa tsakaninsa da wani ɗan Adam ɗin”. shi kuma Garba, (1984) cewa ya yi : “
Harshe wani tafarki ne na isar da saƙwanni dangane da
tunani da motsin rai da bukatu, ta hanyar amfani da saututtuka ta fasalin da
wata al’umma ta ƙayyade, wanda kuma tilas mai amfani da shi ya koya ne, ba
an haife shi da fasalin ba ne”.
Daga waɗannan ma’anoni za a
iya fahimtar ma’anar harshe da cewa: Wani tsari ne na sauti da ɗan Adam ke furtawa
wajen isar da saƙo tsakanin su, a kan wani ƙayyadadden fasali da
aka amince da shi.
3.0 Muhimmancin Harshe Ga Ɗan Adam
Sanin kowa ne cewa, harshe ya yi ruwa
da tsaki a kusan dukkan al’amurran harkokin rayuwar ɗan Adam. Saboda irin
rawar da yake takawa a al’amurran rayuwa ta yau da kullum, ya kasance mai
muhimmanci fiye da kima. Misali, za a tarar cewa da harshe ne ɗan- Adam ke saƙe-saƙensa a cikin zuciya, wannan
ne ya haifar da kasancewar harshe da tunani tamkar jini ne da tsoka kuma da shi
ake ƙaddamar da tunani. Hasali ma za a tarar cewa ta amfani da
harshe ne ɗan Adam yake bi ya
tuno da wani lamarin da ya faru.
Wani muhimmin abu kuma shi ne, za a
ga cewa, da harshe ne ake ƙaryata ko gaskata wani abu. Kuma shi
ne makamin ɗan Adam na furuci. Ta
amfani da harshe ake samun fahimtar juna a tsakanin al’umma.
Har ila yau za a ga cewa da harshe
ne ake gabatar da ra’ayoyi da shawarwarin da suka danganci ci-baya ko ci-gaban
al’umma. Kuma da shi ake isar da kowane irin saƙo. Waɗannan kaɗan ne daga cikin irin
ayyukan da ɗan Adam ke aiwatarwa
da harshe.
4.0 Abubuwan Da Harshe ke Aiwatarwa Ga
Al’umma:
Idan aka tsaya cikin natsuwa aka yi
amfani da idon basira za a tarar cewa, ba ɗan Adam ne kaɗai ke sarrafa harshe ba, har shi ma
harshen kansa yana sarrafa ɗan Adam. Akwai hanyoyi da dama waɗanda harshe ke
sarrafa ɗan Adam, daga cikin
su akwai:
4.1 Bambanta Mutun Da Dabba
Harshe ne ya bambanta mutun da
dabba. Wato ya sa mutun ya kasance wata halitta ta musamman daga cikin halittun
Ubangiji. Wannan ya faru ne a sakamakon magana da mutun ke yi da harshe.
4.1.1 Samar Da Sunaye
Babban abu na farko da harshe ya yi
wa mutane baya ga fifita su da dabbobi, shi ne ya samar musu da sunaye
daban-daban domin kiran abu guda a tsakanin al’ummomi. Misali a harshen Hausa
muna da kalmar gyaɗa a nan gida Nijeriya
inda za a tarar cewa, a wasu harsuna ba haka ake kiran ta ba. Misali:
Harshe Yadda suke kira
Filatanci biriji
Jukunanci fikyin
Tibi (Tiv) ahi
Yarbanci epa ( Garba,1984:2).
4.1.2 Kasa Al’umma Ƙabila Ƙabila
Harshe ne ya karkasa mutane zuwa ƙabilu daban-daban. Za
a iya tantance
Wannan a tsakanin al’ummomin duniya masu siffa
iri ɗaya, abin da ya
bambanta su shi ne harshe. Misali a tsakanin fararen fata, akwai Turawa da
Jamusawa da Amurkawa da dai sauransu. Haka kuma idan muka dawo gida Nijeriya za
mu tarar cewa akwai al’ummomi da dama waɗanda harshe ne ya bambanta su. Misali Hausawa
da Fulani da Yarbawa da Ibo da Igala da Nupawa da Gwari da Idoma da Jukun da
Angas da Katab da dai sauransu.
4.1.3 Bayyana Nahiyar Da Mutun Ya Fito:
Baya ga bambanta ƙabila, za a tarar
cewa ko da a cikin ƙabila guda harshe ne ke bayyana ɓangaren da mai magana
ya ya fito. Misali, idan mutumin Kanada ya yi magana, da jin lafazinsa za a iya
tantance cewa ai ga daga nahiyar da ya fito. Wannan yakan faru ne ta hanyar
la’akari da Karin harshen mai magana. Wannan lamarin haka yake ko a tsakanin
al’ummar Hausawa. Domin kuwa da zarar ka ji mutum ya ce: “Bara na rubuta.” Ka
san mutumin Kano ne, a daidaitacciyar Hausa cewa za a yi “ Bari in rubut.” Ko
kuma ka ji an ce:” Wanda ab Bakura”. Kai
da ji ka san mutumin Sakkwato ne ke magana ba ma sai ka tambaye shi ba Karin
harshensa ne zai bayyana maka daga shiyar ƙasar Hausar da ya
fito.
4.1.4 Bayyana Jinsin Mai Magana:
Daga cikin aikin da harshe ke yi wa
mutane shi ne, bayyana musu jinsin mai magana ko da kuwa ba su yi ido biyu da
mai maganar ba. Da zarar sun ji sautin za su iya tantancewa da lafazin mai
maganar mace ce ko namiji. Misali an tabbatar da cewa, muryar ( sautin ) namiji
babba ne, yayin da na mace ya kasance mai zaƙi da kuma ɗaukar hankalin mai
sauraro. Haka kuma abu ne tabbatacce cewa, harshen mata ya bambanta da na maza
domin akwai wasu kalmomi ko lafuzza da mata kaɗai suka keɓanta da amfani da su.
Irin waɗannan lafuzza ne ake
kira da kalmomin ɓoye ko kuma a kira su
da lafuzzan da ake sakayawa. Misali, abubuwa kamar: kunama sukan kira ta da
“maiƙari” maciji kuwa sukan ce “ yagiyar ƙasa ko maja-ciki”da
dai sauran su. Hasali ma mata sun fi keɓanta da Karin Magana da habaici da salon
Magana. Namijin da akan ji ya yawaita amfani da irin waɗannan kalmomi akan ɗauke shi tamkar ɗan –daudu.
4.1.5 Ƙarfafa Danƙon Dangantaka Da
Fahimtar Juna:
Wani aiki da harshe ke yi wa al’umma
shi ne yana ƙarfafa dangantaka a tsakanin masu amfani da shi, ta
wannan ne har za su fahimci juna. Hasali ma ta yadda jama’a kan fahimci harshen
junansu ke haddasa su zama tamkar ‘yan uwan juna, har a samu wata ƙwaƙƙwarar hulɗa mai ƙarfi a tsakanin
al’ummar.
4.1.6 Yaɗa Al’adu Da Adana Su:
Wani aiki da harshe ke
aiwatarwa ga al’umma shi ne yaɗa al’adunsu da suka shafi rayuwa ta gaba ɗaya. haka kuma da shi
ne ake adana su don kada su salwanta. Wannan yana faruwa ta cikin tatsuniya da
almara da hikaya da dai duk wani nau’i na adabin baka.
4.1.7 Bayyana Halayya:
Harshe wani abu ne da ke bayyana
yanayi da halayen al’umma. Domin sau da yawa akan fahimci nagarta ko rashin
nagartar mutum ta hanyar lafuzzansa.
4.1.8 Fayyace Nau’in Ilimi:
Wani aiki da harshe ke yi a tsakanin
al’umma shi ne bayyana musu nau’in ilimin da ya yi tasiri a tsakanin al’umma.
Misali, mutumin da yake da ilimin Larabci har kuma ya yi tasiri a rayuwarsa za
a ji a duk lokacin da yake magana yana amfani da kalmomin larabci fiye da kima,
hakan kan wakana ga mutumin da ke da ilimin Turanci ko Faransanci.
4.1.9 Siffanta Hoton Rayuwa:
Wani aiki da harshe ke yi wa
al’umma, shi ne bayyana al’adunsu da hikimominsu da basirarsu ta fuskar
siyasarsu da iliminsu da mu’amalarsu da juna. Babu wani abu da za a iya amfani da shi wurin cimma irin wannan nasara
in ba da taimakon harshe ba.
4.1.10 Bayyana Rukunin Jama’a:
Harshe na aiwatar da wani muhimmin
aiki a tsakanin al’umma, wannan aiki kuwa shi ne, ta hanyar ba da bayani game
da rukunin da mai magana yake ciki. Misali, idan mai magana Basarake ne ko mai
mulki, za a tarar cewa harshen da yake amfani da shi yana nuna hakan. Hasali ma
lafazin zai nuna isa da mulki wato za a ji yana Magana ɗaya bayan ɗaya. Misali sarki ko mai
mulki zai dinga amfani da lafuzzan da ke nuna yana waƙiltar al’umma ne.
Irin waɗannan kalmomi sun haɗa da:
Kamar yadda muka tanada
Za mu bayar da tallafi.
Idan kuwa likita ne
ko injiniya za a ji yana saka irin kalmomin da suka shafi aikin da yake
gudanarwa.
4.1.11 Nuna
Dangantaka:
Wani muhimmin aiki da harshe ke yi
wa al’umma shi ne ya fayyace dangantakar da ke akwai a tsakanin al’umma. Akan
gane haka ta hanyar magana. Misali, a ƙasar Hausa da zarar
mutun ya ce wa wani “ Ranka ya daɗe”, to wannan ya nuna wanda ake gayarwa yana
sama da wanda ke gaida shi. Haka idan an ji an ce “ Baba” wato wannan ya nuna
wanda ake ambata mahaifi ne ko kuma a matsayin mahaifi yake. Yayin da “ Kawu”
ke nuna “Wa” ko “ƙanin” mahaifiya ko wani daga cikin dagin mahaifiya a
nasaba.
Idan muka juyo ta la’akari da
wayewar kan ɗan Adam kuma, a nan
ma za a fahimci cewa, harshe ne yake sarrafa shi ta yadda za a iya bambance
mutumin birni da na ƙauye. Wato daga lafuzzan da kowane ya furta za a iya
fahimtar wayewar kansa. Misali, za tarar ɗan birni yana hautsuna harshensa da ƙirƙirarrun kalmomi da
suka wanzu a sakamakon ɓulluwar wani yananin
rayuwar al’mma wanda ya haifar da gudanar da wata haramtacciyar safar don samun
na sakawa a bakin salati. Hasali irin waɗannan lafuzza an ƙirƙire su ne don kauce
wa jami’an hukuma. Yayin da mutumin ƙauye harshensa bai
gurɓata ba.
Ta fuskar girma ko ƙanƙanta ma, harshe yana
yi wa ɗan Adam jagoranci ko
ma ya sarrafa shi, domin idan aka lura da yadda rukunin al’umma ya kasu gida
biyu ( yara da manya), za a fahimci cewa kowane rukuni yana magana ne ta irin
tanadin da harshe ya yi masa, misali ko da a rubuce ne, a sauƙaƙe za a iya fahimtar
waɗannan lafuzzan na
yara ne ko kuwa na manya ne.
5.0 Jawabin
Kammalawa:
A taƙaice dai, wannan muƙala, ta yi ƙoƙarin duba irin tasirin
da keg a harshe a kan ɗan Adam. Nazarin da
muka yi ya tabbatar muna da cewa harshe shi ke sarrafa ɗan Adam ya bambanta
shi da wani, ko ma ya yi masa jagoranci wurin gudanar da duk wani lamari na
rayuwar duniya. Yanke muna iya cewa, harshe ne ginshiƙin da ke ɗauke da rayuwar
al’umma domin da shi ne ake sadarwa da fahimtar juna; da shi ake bambanta
abubuwa; da shi ake samar da ci gaban rayuwa, da dai sauransu. Wato dai rayuwar
ɗan Adam gabaɗaya ya dogara ne ga
irin rawar da harshe yake takawa wurin yi masa jagoranci.
MANAZARTA
Tuntuɓi mai takarda
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.