Ticker

6/recent/ticker-posts

Karin Magana A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Siyasar Zamani, Makamin Cin Nasarar Kafa Shugabancin Adalci Da Tsaro A Nijeriya

 Wannan takarda mai taken “Karim Magana a cikin Rubutattun waƙoƙin siyasar Zamani, Makamin cin Nasarar kafa shugabancin Adalci da tsaro a Nijeriya”, bayani ne na harshe da adabi a kan yadda ake amfani da karin magana a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa, domin faɗakarwa da wayar da kan al’umma da jawo hankalinsu, musamman masu jefa ƙuri’a da su kula da irin mutanen da suka dace su zaɓa. Karin magana na ɗaya daga cikin hanyoyin adabin Hausa da al’umma ke amfani da ita wajen sanar da al’umma abubuwan so ko ƙi, da kuma abin da zai kawo wa jama’a zaman lafiya. Dalilin haka ne ya sa marubuta waƙoƙin siyasa suke amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu, domin su faɗakar da al’umma su zaɓi jam’iyyu da shugabanni masu manufar tabbatar da adalci da zaman lafiya a ƙasa. Wannan takarda za ta yi tsokaci a kan gudummawar da karin magana ke bayarwa cikin rubutattun waƙoƙin siyasa wajen samar da shugabanci na adalci da tabbatar da tsaro a Nijeriya.


Karin Magana A Cikin Rubutattun Waƙoƙin Siyasar Zamani, Makamin Cin Nasarar Kafa Shugabancin Adalci Da Tsaro A Nijeriya


Aliyu Rabi’u Ɗangulbi

 

DA

MUSA ABDULLAHI 

GSM NO. 07032567689, 08037765415

Email: aliyurabiu83@yahoo.com

Email: abdullahialhaji707@gmail.com

 

1.0              GABATARWA

 

Kyakkyawar faɗakarwa da wayar da kai ga kowace irin al’umma ta duniya shi ne ginshiƙin samar da nasarar rayuwa da kafa shugabanci nagari a lokacin mulkin dimokuraɗiyya. Siyasa tana daga cikin al’amurran rayuwar ɗan adam da ke buƙatar samun kyakkyawar faɗakarwa musamman domin a wayar da kai da kuma jawo hankalin jama’a da su yarda da manufofin jam’iyyun siyasa daban daban, don cimma nasarar kafa mulkin adalci da zai zama makamin samar da zaman lafiya da tsaro a cikin ƙasa.

 

Da yake muna magana ne a kan gudummawar da karin magana a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa ke bayarwa. Ya dace mu yi tsokaci a kan ma’anar ita kanta karin magana da yadda take da mahimmancin gaske wajen umurni da hani da horo a cikin al’umma da ke da aƙidar samar da kyawawan halaye da ɗabi’u na gari. Ba wai ga ƙananan yara ba, har ma da manya baki ɗaya.

 

Saboda haka a siyasance, akwai buƙatar zaɓen mutane masu halaye da ɗabi’u na gari domin su ne za su iya riƙa amanar talakawa da tsare rayukkansu da dukiyoyinsu a duk lokacin da aka ba su jan ragamar mulkin al’umma. Bisa ga wannan dalilin ne marubuta waƙoƙin siyasa ke amfani da hikimominsu ta hanyar jefa karin maganganu cikin waƙoƙinsu don faɗakar da jama’a da ‘yan siyasa game da zaɓen shugabanni na gari. Yin haka zai sa a sami nasarar kafa mulkin adalci da samar da cikakken tsaro a cikin ƙasa.

 

1.1       MA’ANAR KARIN MAGANA

Karin magana wani gajeran zance ne mai bayyana gaskiya ko koyar da darasi na ɗa’a a cikin kalmomi ‘yan kaɗan, wanda ke buƙatar dogon bayani (Chambers 1998: 1,324). Wato zance ne ɗan gajere amma mai ƙunshe da dogon bayani idan aka warware shi. Wannan ya yi kama da abin da ya bayyana a cikin Webster’s (1987) da yake cewa, karin magana taƙaitaccen sababben zancen hikima ne da akasari ke zuwa a dunƙule da ya ƙunshi hoton abu a zahiri mai ɗauke da saƙon da ke zuwa kai tsaye daga ƙwaƙwalwa.

 

Shi ma Yunusa (1977:3) cewa ya yi, ‘karin magana Hausa ce a dunƙule”. Dunƙule a nan yana nufin abin da aka cure a wuri ɗaya ne. A nan za mu iya cewa maganar harshe ta fito wanda ke nuna haɗiyewar zance a wuri ɗaya. Amma akwai bayani mai tsawo, idan aka walware shi. Yin haka ba ƙaramar hikima ba ce kamar yadda Hadiza S. Koko (2011) ta gani, ko baya ga maganganun masana daban – daban game da ma’anar karin magana ana iya kiran karin magana da wani saƙo na baje kolin tunani da bahaushe kan yi ta hanyar hikima cikin yan kalmomi kaɗan. Ta kawo kalmar baje koli a nan domin idan aka faɗe ta za ta iya ba da ma’ana mai yawa kuma kala-kala har dai idan aka yi sharhinta.

 

A taƙaice dai, kamar yadda muka fahimta, kamar yadda ɗan Adam ya bambanta a siyasa da hali, to ko a tunani ya bambanta. Lokacin da wani ya fahimci abu cikin lokaci ƙanƙane, wani sai ya ɗauki dogon lokaci kafin ya fahimce shi. Tunaninsa da bayaninsa zai so ya zazzage shi duk da dagon lokaci da zai ɗauke shi. Saboda haka a tunaninmu, karin magana wata gajeruwar kalma ce ko dunƙulalliya mai ɗauke da hoton abu na zahiri mai isar da saƙon gaskiyar abin da ake son a isar ga al’umma cikin hikima, wanda ke ɗauke da dogon bayani idan aka warware shi. Da wannan ɗan takaitaccen bayanin ma’anar karin magana za mu gina bayaninmu dangane da rawar da karin magana ke takawa a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa wajen ilmantar da al’umma cikin hikima.

 

1.2       MA’ANAR WAƘ

A adabin Hausa, waƙa tana daga cikin hanyoyin isar da saƙo cikin sauƙi. Waƙa ita ce ta ƙunshi zaɓaɓɓun kalmomi da ake tsarawa cikin hikima da karin sauti da amsa amo da salon sarrafa harshe da ake don rerawa a isar da wani saƙo zuwa ga jama’a (Yahya 1997).

 

Sa’idu Gusau (1993) da Skinner (1980): sun yi mawafaƙa a kan cewa waƙa abu ce da ke cikin tsarin kalmomi na musamman da suka samo asali daga baitocin larabci masu ƙunshe da jigogin addini da al’amurran rayuwar ɗan adam ta yau da kullum. Kuma tana buƙatar laƙantar harshe da rera ta cikin murya mai rauji. Wato manyan tubalan waƙa kamar yadda suka bayyana su ne, rerawa da rauji waɗanda suka bambanta da maganar yau da kullum.

 

A takaice muna iya cewa tsari da kalmomi zaɓaɓɓu su ne ginshiƙin ginin waƙa domin su ne za su iya zama magana mai ma’ana da ake rerawa cikin sautin murya mai armashi da ƙafiya, domin a isar da saƙo muhimmi zuwa ga jama’a. A kan haka ne mawaƙa ke amfani da waƙa a matsayin makami na samun nasarar aiwatar da manufofi daban-daban ta hanyar yin amfani da hikimar da Allah ya ba su, musamman a ɓangaren siyasa.

 

1.3       MAWAƘAN SIYASA  

Mawaƙan siyasa su ne waɗan da ke shiryawa da kuma rera wa jam’iyyu da ‘yan siyasa waƙa domin su tallata su ga jama’a. Ana kyautata zaton an soma rubuta waƙoƙin siyasa tun lokaci mai tsawo da addinin musulunci ya bayyana a duniya. An yi rubuce-rubuce da dama game da sarakunan musulunci ciki har da waƙa a cikin littattafan adabin Larabci (Arabiya). A lokacin Sarkin Musulmi Halifa Al-Mansur (Ɗangulbi 2003), an sami wani mutum ɗan ƙasar Sin (China) da ya kawo labarin sarkinsu da Allah ya jarabce shi da kurumcewa, bai jin koke-koken jama’arsa. Ya nuna matuƙar damuwarsa a kan haka. Da sarkin Musulmi ya ji wannan labari sai shi Halifan (Al-Mansur) ya yi nadama saboda halin ko- in kula da yake nunawa ga talakawansa.

 

A ƙarshe ya yi alƙawarin gyara halayensa. Saboda haka yana da kyau idan an ga wani shugaba yana aikata wani abu maras kyau, a riƙa yi masa nasiha dangane da yadda yake tafiyar da sha’anin mulkinsa. Irin wannan nasiha ce da gargaɗi marubuta waƙoƙin siyasa ke amfani da hikimarsu suna faɗakar da shugabanni da talakawa a kan bin hanyar da ta dace wajen gudanar da mulki na gari.

 

A ƙasar Hausa an sami irin waɗannan labarai game da waƙoƙin da Hausawa musulmi suka rubuta domin su yi wa shugabannin ƙasar Haɓe nasiha da gargaɗi ga barin wasu munanan ɗabi’u da suka saɓa wa dokar musulunci a cikin mulkinsu. Wani marubucin waƙoƙi na Afrika ta Arewa da ake kira Ali bin Hussaini da Al-fazazi sun rubuta waƙoƙi a ƙarni na takwas miladiyya masu suka ga daular sarakunan labarawa na Afrika ta Arewa.

 

Haka kuma a ƙarni na goma sha tara (19th Century) miladiyya, an sami waƙoƙin siyasa da Shehu Usman Ɗanfodiyo da wasu daga cikin almajiransa da ƙanansa Abdullahi bin Fodiyo suka wallafa game da siyasa. Waɗannan mutanen sun rubuta waƙoƙi game da yadda sarakunan Haɓe suke gudanar da mulkinsu a ƙasar Hausa. Shehu Ɗanfodiyo da Abdullahi Bin Fodiyo, ƙanensa da Muhammadu Tukur sun rubuta waƙoƙi daban-daban game da tsarin mulki irin na addinin musulunci. Haka kuma sun yi bayani game da yadda ya kamata shugabanni su riƙa talakawansu da adalci. Shehu Ɗanfodiyo ya rubuta waƙarsa mai suna “Tabban Haƙiƙa” wadda a cikinta yake kira ga masu mulki da su riƙa talakawansu bisa ga amanar da Allah (SWA) ya ɗora masu. Su kuwa talakawa ya kire su da su zama masu biyayya ga shugabancinsu. Haka su kuma Abdullahi bin Fadiyo da Mamman Tukur duk sun rubuta waƙoƙi game da tsarin mulki irin na Musulunci da sauransu. Wannan gagarumin ƙoƙari da waɗannan bayin Allah suka yi ya nuna mana cewa waƙoƙin siyasa sun samo asali tun daga zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa.

 

Waƙoƙin siyasa da masu jihadi suka wallafa sun zama tushe ga salon rubutattun waƙoƙin siyasar zamani a yau. A ƙarni na 20 marubuta da dama sun rubuta waƙoƙi domin faɗakarwa da gargaɗi ga al’umma game da mahimmancin shiga harkokin siyasa da Turawa suka kawo. Salon Marubuta waƙoƙin siyasar zamani ya bambanta da salon waƙoƙin masu jihadi ta fuskar jigo da salo.

 

Jigon waƙoƙin siyasa kamar yadda addinin musulunci ya zo da shi, shi ne aiwatar da adalci bisa ga tsarin shari’ar Musulunci. Shi kuwa jigon waƙoƙin ƙarni na 20 ya fi mai da hankali a kan harkokin duniya da tsarin mulkin da yahudanci ya zo da shi.

 

Ta fuskar salon rubutu dukkan rubutattun waƙoƙin masu jihadi an yi shi ne a cikin haruffan larabci da kuma ajamin Hausa. Su kuwa waƙoƙin ƙarni na 20 bisa ga salon rubutun ajamin Hausa da kuma baƙaƙen bokon Hausa da ilimin zamani ya zo da shi aka tsara su. Daga cikin mawallafan waƙoƙin siyasar zamani akwai malam Sa’adu Zungur da Malam Gambo Hawaja da Malam Mudi Sipikin. Haka kuma akwai Malam Lawal Maiturare da Malam Aminu Kano da Lawal Isah Bunguɗu da Sauransu. Har wa yau akwai irin su Malam Garba Gwandu da Malam Haliru Wurno da Malam Aminu Ibrahim Ɗandago da Shu’aibu ‘Yar Medi Karaye da Malam Umar Kwaren Gamba da Sauransu.

 

Waƙoƙin da waɗannan marubuta waƙoƙin siyasa na zamani suka rubuta, sun yi amfani da hikimomi cikin harshen Hausa wajen isar da saƙonsu ga al’umma. Daga cikin hikimomin akwai yin amfani da karin magana cikin waƙoƙinsu, domin su yi gargaɗi da faɗakar da al’umma dangane da muhimmancin zaɓen shugaba na gari.

Shugabanci na gari shi ne zai kawo cigaban tattalin arzikin ƙasa da adalci da tabbatar da tsaron ƙasa da rayukka da dokiyoyin al’umma.

 

1.4       SHUGABANCI

Shugabanci na nufin jagoranci, wato jagoranci na mutane ko wasu halittu da za a sami, mutum ɗaya ya zama shi ne wanda zai kula da tafiyar da al’amurran jama’a na yau da kullum. Haka yake ko a cikin dabbobi akan sami babba guda ta shiga gaba tana yi wa sauran dabbobi jagaba. Wato dai shugabanci yana nufin kula da yadda abubuwa ke gudana a tsakanin al’umma ta hanyar bin dokoki da ƙa’idojin zamantakewa. Ɗangulbi (2003). Shugabanci abu ne mai wuya domin kamar rigar siliki yake, in nan ya gwabce an taro shi, sai can ya gwabce. Kowace al’umma ta duniya ba za ta taɓa tafiya ba tare da shugabanci ba. Akwai matsaloli da dama a wajen gudanar da shugabanci musamman ta fuskar zamantakewar mutane. Matsalolin kuwa su ne; Rashin Adalci da Rashin bin doka. Rashin Adalci yakan fito daga shugaba saboda jagorancin mutane daban-daban da yake yi. Akwai masu ilimi da marasa ilimi da masu hankali da akasin haka. Kuma akwai mawadata da faƙirai dukkansu suna ƙarƙashin jagorancin shugaba. Idan shugaba ya kasa bai wa mutanen da yake shugabanta haƙƙinsu yadda ya kamata, to babu shakka rashin adalci ya shiga kenan. Su kuwa waɗanda ake shugabanta za su kasance marasa biyayya ga shugaba idan bai yi adalci ba. Ta haka sai a sami wanzuwar fitintinu da ka iya yin barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa. Dalilin haka ya sa mawaƙan siyasa suke tsare waƙoƙi, inda suke jefa karin maganganu domin su yi wa mutane gargaɗi da wayar masu da kowanansu dangane da amfanin zaɓen shugaba mai dattako da riƙon amana. Idan aka sami shugaba mai dattako da gaskiya da riƙon amana, to ta nan ne ake sa ran a sami mulkin adalci wanda zai kawo zaman lafiya a ƙasa.

 

Shugaba adili shi ne mutumin da ba shi zalunci, kuma mai bai wa kowa haƙƙinsa. Ba shi nuna ƙabilanci ko ɓangaranci ko bambancin addini wajen tafiyar da mulkinsa.

 

1.5       ADILIN SHUGABA

Kamar yadda muka ce shugaba adili shi ne wanda ke da tsoron Allah da gaskiya da riƙon amana, shi ne idan an ba shi amanar dukiyar jama’a yana bai wa kowa haƙƙinsa ba tare da zalunci ko nuna ƙabilanci da wariyar yanki ba. Haka kuma bai nuna bambancin addini da sauransu. Wani mawaƙi mai suna Muhammadu Ɗan Baɗɗo Gwandu ya bayyana siffar adilin shugaba a cikin waƙarsa, ya na cewa:

Wanda ba shi nuna ƙabilanci

Wanda ba shi son a yi zalunci

Wanda ba shi ƙyamar mai yanci

Wanda ba shi son mai lalaci

Shi shina cikin dimokuraɗiyya

 

Wanda ba shi warewar jinsi

Kowane mutum shi an nashi

Kowane addini na nashi

Ko talakka yas so shi gane shi

Babu fargaba ko jin kunya

 

Babu shakka irin waɗannan siffofi da marubucin ya bayyana sun cancanta a duba su domin ya fito da hoton shugaba na gari mai ɗabi’u da al’umma ke so ya shugabance su a fili.

 

Kamar yadda muka gani a cikin baitocin da ke sama, mun fahimci cewa shugabanci da adalci shi ne wanda ke sa ɗan ƙasa ya sami haƙƙinsa ba cutarwa. A nan ana nufin jagorancin al’umma sai mai gaskiya da riƙon amana wanda zai bai wa kowa haƙƙinsa ya kuma kare ƙasarsa daga faɗawa cikin fitintinu da ayukkan ta’addanci. Hausawa suna wata karin magana inda suke cewa “Gaskiya dokin ƙarfe”. Wannan karin magana tana nufin idan ka tsayar da gaskiya ga al’amurranka to ko yaushe sai ka kwanta ka yi barci ba tare da tunanin wani cin mutunci ya same ka ba.

 

Mun san cewa doki wata dabba ce da sarakunan ƙasar Hausa ke hawa idan za su shiga cikin ƙasarsu don yin rangadi. To ita gaskiya an siffanta ta da doki domin ita ma ana hawa kanta, amma ba kamar yadda ake hawan doki ba. A nan ana nufin mai gaskiya yana iya tsayawa a gaban kowa ya faɗi abinda yake so ba tare da an tozarta shi ba, kamar yadda za a hau dokin karfe. Dalilin haka ya sa Hausawa suke danganta mai gaskiya da wanda ya hau dokin ƙarfe a matsayin mutumin da ba a walaƙantawa a cikin al’umma. Saboda haka a fagen siyasa marubuta waƙoƙin siyasa suna yi wa mutane gargaɗi da irin wannan karin magana domin su zaɓi irin mutumin da baitocin da suka gabata suka bayyana. Har wa yau su marubuta waƙoƙin siyasa suna yaba mutum mai gaskiya da riƙon amana ta fuskar ƙwazonsa da jajircewarsa da ganin ƙasarsa ta kasance cikin ƙasashen da suka ci gaba ta ɓangarori daban-daban. Domin haka a duk lokacin da mutum ya zamo dattijo mai gaskiya da mutunci, mawaƙan Hausa sukan ɗaga mutum sama kowa ya san shi. Misali Malam Muhammadu Bello Aliyu Zurmi a cikin waƙarsa ta mai da mulki a hannun farar hula ya na cewa:

Siyasa ka nuna mutum har a san shi

Cikin duniya ko ina a faɗe shi

Mutane su kau nuna ƙauna gare shi

Anai mashi murna irin ta arushi

Da kakkaɓe masu rashin gaskiya

 

Siyasa tana gargaɗii inda ɗanta

Nufina mutum in shina ra’ayinta

Takan sa a zaunad da shi a gabanta

Ta gargaɗi ɗanta ta hori abinta

Ta ce mai ahir da rashin gaskiya

 

Maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi zufa/jiɓi. Wannan karin magana tana nuna goyon baya ga maganar da baitocin sama suka yi na gargaɗi ga ‘yan siyasa. Domin ko yaushe maras gaskiya bai da amana, zalunci kawai ya sa a gaba, sannan ga saɓa alkawali, idan ya ɗauka. Saboda haka ne ma ya sa Malam Muhammadu Ɗanbaɗɗo Gwandu yake gargaɗin ‘yan siyasa da su zaɓi mutum mai gaskiya, da jam’iyyu suka tsayar ‘yan takarar don ciyar da ƙasa gaba ta hanyar zaman lafiya da tsaro. Misali; ya na cewa:

            Shin ina nufin dimokuraɗiyya?

            Bayyana mu san ka san hanya,

            Ba a yin tuwo babu tukunya

            Ba a gina huska ba ƙeya

                        Ba a tuƙa mota ba taya.

 

Za a ba farar hula mulki,

Ya kamata ko mu yi jan aiki

Wajibi ga aure da sadaki

Lafiyar kuɗi a aje banki

Shi ka sa ɓarayi sui kunya     

 

Wato Malamin yana nuna wa ‘yan siyasa cewa mai ilimi haziƙi gwarzo mai ƙwazo da riƙon amana shi ne ya fi cancanta jam’iyyun siyasa su tsayar ‘yan takara. Domin su za su tsai da adalci a cikin shugabancin jama’a, wanda shi zai zama makamin samar da tsaro a cikin ƙasa. Idan shugaba ya zama azzalumi to za a sami rashin zaman lafiya saboda zaluncin da yake yi a cikin mulkinsa.

 

1.6 MULKIN ZALUNCI

Zalunci yana nufin hana wa mai haƙƙi haƙƙinsa kamar yadda shari’a ta tanada. Zalunci yakan kama tun daga gudanar da harkokin cikin gida da mai gida har zuwa ga shugabancin ƙasa baki ɗaya. Cin hanci da rashawa, sama da faɗi da dukiyar al’umma da sata da sauransu, duk nau’o’i ne na zalunci waɗanda ke haddasa fitintinu a tsakanin mai mulki da waɗanda ake mulki. To wannan hauji marubuta waƙoƙin Hausa na siyasa sukan yi gargaɗi ga ‘yan siyasa da sauran jama’a dangane da zaɓen shugabanni azzalumai. Zalunci duhu ne a lahira inji Hausawa don haka ya sa marubuta waƙoƙin sukan jawo hankalin ‘yan siyasa da kauce wa zaɓen azzaluman mutane a lokacin zaɓe. Saboda haka ne Hausawa suke cewa “Zaɓi maƙwabci tun ba ka sayi gida ba”. Wato a nan shugaba maƙwabci ne da ke wakiltar jama’a wanda a tsarin zamantakewa. Don haka wannan karin magana tana da mahimmancin gaske wajen gargaɗin ‘yan siyasa ga zaɓen mutumin kirki mai amana. Azzalumin shugaba maƙwabci ne da mutane ke zaɓe ya wakilce su, don haka mawaƙa ke yin nuni da kira ga ‘yan siyasa da su ƙaurace wa zaɓen azzaluman shugabanni.

Malam Shu’aibu ‘Yar Medi yake wata karin magana a cikin waƙarsa inda yake cewa.

Hausawan garinmu suke cewa in za a sai ƙwarya

Sai an ƙwanwasa kaji ta ce ƙwarƙwar ƙwar a can baya

Jam’iyyun ƙasarmu ku tashi ku koma can kuja baya,

PDP kawai jama’ar ƙauye domin a gyara ƙasata

Hausawa suna cewa, “in za a sai ƙwarya sai an ƙwarƙwasa domin a ji mai ƙwari”. Dangane da wannan karin magana kamar yadda ta fito a bauti na sama shi ne; Lokacin da wannan mawaƙin ya garzaya jam’iyyarsa babu shakka ta sami ƙarɓuwa ga jama’ar ƙasa har ta kafa gwamnati, Jam’iyyar ta samu nasara ne saboda akwai mahimman mutane masu gaskiya da roƙon amana, irin su Farfesa, Jibril Aminu, Shehu Musa da Dallatun Adamawa Atiku da sauransu. Da wannan jam’iyya ta kafa mulki jama’a sun sanya idanu su ga yadda za ta gudanar da mulki to ashe daga cikin masu mulkin azzalumai ne.

 

Don haka ba su tsinana komai ba sai wasoson dukiyar hukuma, suka arzuta kansu, suka bar jama’a cikin ƙuncin rayuwa. Wannan yanayin a rayuwa da shugabannin wannan jam’iyya suka jefa ƙasa ya haddasa ayukkan ta’addanci da kasha-kashen rayukka da dama da kuma sace-sacen dukiyoyin al’umma. A dalilin haka, sai wani mawaƙi ya jawo hankalin ‘yan ƙasa da su marawa jam’iyyarsa baya saboda cika mulkin adalci da tabbatar da cikakken tsaro. Malam Aminu Ɗandago yana cewa a cikin karin magana kamar haka:-

Sawun giwa a yanzu ta take na raƙumi

Jam’iyyar can ku lura mun mata takunkumi

Dukkan ɗan jam’iyyarmu bana ba shi da zullumi

Mun hargitsa jam’iyyarsu na ji suna bambami

Da ma ku taho ku amsa sonta baki ɗaya

            Tallar turmi akwai wuya bana ba zan yi ba,

Ba zan yi abin da zuciyata ba ta gamsu ba,

Cutar da kare ya tashi, zancen ku biyo gaba,

Akuya in ta yi ku tabbata ba ta tashi ba,

Daɗa jan ɗamarar ka murƙushe ga baki ɗaya

 

Shi kunun zaƙi yai kaɗan ya wa koko barazana

Ɗan akuya bai kama da giwa ba ta ko’ina

Gorar ruwa ga buhun baƙin ƙarfe jinjina

Kowa yal lashi garwashi shi zai ɗanɗana

Ba a shara da yatsa sai dole da tsintsinya

 

Hausawa suna Karin magana da cewa, Sawun giwa ya take na raƙumi” idan suna gwama abubuwa biyu a lokaci ɗaya domin su fitar da wanda ya fi mahimmanci ko ƙarfi a garesu, saboda haka ne Aminu Ɗandago ya yi amfani da wannan karin magana a lokacin da yake son ya bayyana wa jama’a mahimmancin jam’iyyarsa da samar da shugabanni na gari. Ya nu na cewa dabbobi suna da matsayi da girma da kuma bambamci, ya yi amfani da salon kamancen fifiko dan ya nu na darajar giwa ta fi ta raƙumi, bag a girman jiki ba har ma da kwarjini. Don haka idan ana maganar giwa to ba a maganar raƙumi. Malamin bai ma ambanci bambanci na dukkan girman jikin giwa ba a a sawun kawai ma ya kwatanta da na raƙumi, idan ya ce babu shakka ya take na raƙumi, wannan karin magana idan an danganta ta ga ‘yan siyasa sai aga cewa har cikin su idan aka ambaci wasu muhimman mutanen jam’iyya, to sai wasu su ja baya. Dalilin haka ya sa shi kansa mawaƙin ya lura da irin matsalolin da ke tattare a cikin mulkin wata jam’iyya idan yake nuna wa jama’a cewa yanzu kam ga wata mafita an samu, idan ya nuna jam’iyyar sa ita ce ta fi mai mulki. Domin idan ana maganar jam’iyyar sa to ba a maganar jam’iyyar da aka ga irin takin rawar da take yi a lokacin da take gudanar da mulkinta. A nan mawaƙin ya faɗar ka da jama’a cewa jam’iyyar can da ke mulki a yanzu tasu jam’iyya ta yi wa waccan takunkumi, wato sun ɗaure mata baki babu wani abin da zasu ce domin bas u tsinana komi ba a cikin mulkinsu. Misali babu wadatar abinci, babu tsaro da zaman lafiya, don haka yan zu an sami mafita.

 

Yanzu ‘ya’yan jam’iyyar su bana basu da zullumi idan har aka zaɓeta. A ƙarshe ya nuna cewa ai sun hargitsa ‘ya’yan waccen jam’iyya mai mulki domin yaji suna ta bambami, wato suna ta faɗa na rashin dalili.

 

Domin ya ƙara nuna ‘ya’yan waccan jam’iyyar cewa sun kasa, sai ya ƙara kawo wata karin magana a baiti na biyu, idan ya ke cewa “Tallar Turmi akwai wuya ga maras hakuri, kamar yadda Hausawa ke cewa, sannan kuma cutar da kare ya yi ya tashi, idan akuya tayi irin tab a zata tashi ba, da sauran ire-iren karin maganar da ke cikin baitin.

 

Duka waɗannan karin maganganu da mawaƙin ya yi amfani da su a cikin baiti na ɗaya da na biyu ya nu na cewa, a sanadiyar da wasu suka yi a lokacin da suke kan karagar mulki ba zata yi tasiri ba idan jam’iyyarsa ta kafa mulki, kuma yana son ya bayyanama jama’a irin illar da zalunci yake da ita ga al’umma. Saboda haka duk wahalhalun da jama’a suka sha a lokacin mulkin waccan jam’iyya bana ba za su yadda su sake maimaita irin ta ba, domin ga jam’iyyar da zata kula da bada haƙƙin kowa da samar da tsaro da zaman lafiya.

 

Day a koma kan yan takara sai ya danganta ‘yan takara biyu na Jam’iyyar sa da ‘yan takarar waccan jam’iyya, inda yake karin magana kamar yadda Hausawa ke cewa “Kunun zaƙi ba warin koko ba ne” ya kawo wannan karin magana a cikin waƙa, domin ta dace da karin waƙarsa da mai karatu ko mai saurare zai fahimta da sakon. Shi ya sa ya ce “Kunun zaƙi yai kaɗan ya wa koko barazana” wato kunun zaƙi ba koko bane domin ba a shan shi don maganin yunwa, sai dai don maganin ƙishin ruwa. Don haka komi kyawan kunun zaƙi ba zai yi amfani a ciki ba kamar yadda kunu zai yi. Wannan karin magana ya dantanta ta ga ‘yan takara biyu waɗanda suke kusan matsayi ɗaya, ama fa darajar ɗaya ta zarce ɗayan inji mawaƙin, kamar yanda koko ya banbanta da kunun zaƙi, duk da kasancewar an yi su da garin gero ko na dawa, amma darajar ɗayan ta kasa ta ɗayan.

 

Harwa yau, ya kamanta darajar ɗan akuya da giwa, wanda a aikin hankali an san ba zasu taɓa haɗuwa ba domin akwai fifikon girma da ƙarfi.  Haka kuma ya danganta goran ruwa da buhun baƙin ƙarfe ta fuskar nauyi, mawaƙin ya yi amfani da salon kamancen fifiko a cikin karin magana daban - daban da suka fito a cikin waɗannan baitoci guda uku da ke jere da juna. Haka kuma a wajen zafi mawaƙin ya nuna cewa komi dauriyar mutum ba zai lashi garwashin wuta ba domin harshen sa zai ƙone. Ƙarshe yace ba’a shara da yatsa sai da tsintsiya.

 

Da waɗannan baitoci da ke ɗauke da karin magangu ya sa mawaƙin ya ƙara jawo hankalin talakawan Nijeriya suka aminta da jam’iyyar da ke jagorancin shugabancin ƙasar nan a wannan lokaci, mawaƙin ya kuma nuna wa ‘yan wacan jam’iyya cewa zaluncin da suka yi wanda ya jefa ƙasar nan cikin halin ƙaƙa-ni-kayi ba zai je ko’ina ba. Dalilin haka wasu jam’iyyu suka yi yarjejeniyar haɗin guiwa don su tsayar da ɗan takara ɗaya mai zimmar ceto halin da mutanen ƙasar suke ciki. Saboda haka ya nuna ma jama’a cewa duk abin da ‘ya’yan waccan jam’iyya suka tara aikin banza ne bai da wani amfani, matuƙar ba ta hanyar halal suka tara shi ba.  Domin Hausawa sukan ce, kashin kare bai taki, kamar yadda mawaƙin ya kawo. Misali yana cewa:

Ƙaryar kashin kare ya zama taki na gani

Ba a sayarwa a kasuwa ku sani tun tuni

Ba a jiƙawa a sha shi don neman magani

Ba wani mai tanadinsa don ajiya har da ni

Ku zo zam fasa ƙwai kuji ni in ba mu da gaskiya

 

Babu shakka ƙashin kare ba ya taki, wannan karin magana ta yi dai dai da irin abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan game da ƙwato dukiyoyin hukuma da shugabannin da suka gabata suka sace. Wannan yunƙurin da gwamnatin yanzu ke yin a ƙwato haƙƙin jama’ar ƙasa daga hannun azzalumai ya nuna mana; cewa shugabanci tafe yake da ma’umin shugabanni da ke nuna cikar moruwa da ƙwazon shugaba ta fuskar gudanar da adalci a cikin mulkinsa. Rashin samun shugaba mai adalci da riƙon amana shi ke kawo taɓarɓarewar tattalin arziki rashin aikin yi ga matasa. Saboda haka akan sami rashin zaman lafiya da cikakken tsaro a ƙasa.

 

1.7       TSARO

Tsaro shi ne samar da kulawa da kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma a kowane lungu na ƙasa baki ɗaya. Mutane na ta alaƙa samun kyakkawan tsaro a ƙasa ga shugabanci na adalci wanda akan same shi a sanadiyyar zaɓen shugabanni na gari. Shugabanni na gari su ne masu gaskiya da riƙon amana da kuma kishin ƙasa. Rashin adalci ga shugabanci shi ne umul-haba’isan kowace irin fitina a ƙasa. Domin idan aka sami shugabanni marasa adalci da kishin ƙasa, to su ne za su yi wa dukiyar ƙasa rubda ciki su kwashe su kai ƙasashen ƙetare.

 

A duk lokacin da haka ta faru a ƙasa, za a sami cewa wasu ‘yan tsiraru kawai ne ke jin daɗi sauran mutane da matasan ƙasa su rasa aikin yi. Idan haka ta faru sai ta’addanci da faɗace faɗacen ƙabilanci da na addini su yawaita a cikin ƙasa. Haka kuma akan sami yawaitar ɓarayi da fashi da makami da sauran rikice-rikicen siyasa da satar mutane ana yin garkuwa da su, sai an biya milyoyin naira sannan a saƙo su. Da zaran shugabanni sun kasa yin adalci a mulkinsu, da kula da ba da haƙƙi ga kowane ɗan ƙasa, to babu shakka wannan abu zai haifar da rashin zaman lafiya da rashin samun ingantaccen tsaro a ƙasa.

 

Hausawa na cewa, zama lafiya ya fi zama sarki. Domin a sami zaman lafiya da tsaro a ƙasa, dole ne a zaɓi mutane masu gaskiya da amana waɗanda za su bai wa talakkawa haƙƙinsu. Haka zai sa a sami ingantaccen tsaro ta hanyar zaɓen mutanen da suka dace. Marubuta waƙoƙin siyasa suna amfani da irin wannan karin magana da ta gabata domin su yi wa jama’a hannunka-mai-sanda wajen zaɓen shugaban da ya dace. Jam’iyyoyi sukan so su tsai da mutum mai kwarjini da ƙwazo da tausayin talakawa. Idan an tsai da ‘yan takara na wata jam’iyya, to marubuta waƙoƙi kan tsara waƙa domin su tallata shi a idon jama’a. Idan har mutumin an san shi da gaskiya, to babu shakka jama’a za su amince da shi, su kuma zaɓe shi a matsayin shugaba. Wannan ya sa mawaƙa irin su Aminu Ibrahim Ɗandago suka duƙufa wajen faɗakarwa da jawo hankalin jama’a ga zaɓen da ya gabata. Inda aka zaɓi Gen. Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC. Wannan jam’iyya haɗaka ce ta jam’iyyoyin siyasa da suke da manufar kawo sauyi na cigaba da bunƙasar arzikin ƙasa da zaman lafiya. Aminu Ibrahim Ɗandago yana ɗaya daga cikin marubutan da suka tallata jam’iyyar ANPP wadda tana daga cikin jam’iyyun da suka cure suka zama jam’iyya guda ta APC. Sanadiyar tsai da ɗan takara mai kwarjini da gaskiya da riƙon amana, wanda ake yi wa kirari da fiya-fiya kashe ƙwari”. Haka kuma ana yi masa take da “Gaskiya Dokin Ƙarfe” Dukkan waɗannan karin maganganu sun ƙara ɗaukaka martaba da kwarjinin wannan ɗan takara.

Ya mai bunu a gindi zai je kasha gobara.

Ya za ai ne a ce gara za ta ci marmara,

Ya kuma za ai a ce  agwagwata yi kyarkyara,

Mun yunkura za mu farmake su da ɗanyen kara,

Jiki magayi za mu murƙushe masu ƙiriniya

Da talakawa suka ji haka, kuma suka aminta, sai suka ɗaura ɗamara murƙushe jam’iyyar da ke mulki, wadda ta kasa shawo kan matsalar tsaro a ƙasa. Saboda ya tabbatar wa talakawa cewa jam’iyyarsa mai ɗan takara mai gaskiya za ta shawo kan matsalar tsaro ta hanyar hana fashi da makami da sauransu.

 

A taƙaice dai gyaran matsalar tsaron ƙasa sai masu adalci waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu ga kawo zaman lafiya da jin daɗin talakawansu da kuna walwarsu. Don haka duk mai wani laifi ko rashin gaskiya bai kamata ya shiga cikin masu gyara ƙasa ba. Wannan dalili ne ya sa marubucin ya kwatanta wasu halaye na mutane a cikin karin magana da kishiyoyinsu inda yake danganta wuta da bunu, da gara da marmara da kuma agwagwa da kyarkyara. Waɗanda duk abubuwan da ya danganta da su ba za su taɓa yiwuwa ba.

 

1.8       KAMMALAWA

Matsalar tsaro abu ce da ta addabi wasu sassa na ƙasar nan musamman arewacin Nijeriya. Don haka akwai buƙatar samun shugabanni masu gaskiya da riƙon amana, masu ƙwazo da ƙwarewa a harkokin mulki. Irin waɗannan shugabanni su kaɗai ba za su iya cin nasarar samar da zaman lafiya da ingantaccen tsaro a Nijeriya ba.

 

Haka kuma idan shugaba mai adalci ne, to ya dace ya sami mataimaka irinsa domin a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ragargaza maƙiya ci gaba. Bisa ga wannan buƙata ne, ya sa mawaƙan siyasa sukan yi kira da babbar murya a cikin waƙoƙinsu, domin su jawo hankalin ‘yan siyasa da jam’ar ƙasa. Su bai wa shugaba goyon baya a kau da ayukkan ta’addanci da rikicin addini da na ƙabilarci a cikin ƙasa. Misali Aminu Ɗandago ya yi kira da haka inda yake cewa.

Mai taya kishi ga kishiya shahashan gari

Mai ba da gudummawa ga ‘yan iska Shagiri

Anyi butulci a bara aka ɗau ɓatakarkari

Shashashan babu wanda yat tsira da ko ɗari

Bana a yi hattara a duba waina toyayyiya

A nan mawaƙin yana nuna wa jama’a cewa akwai mutane da ba su nufin alhairi domin ana haɗa kai da su domin a watse shirin zaman lafiya. Don haka duk wani ɗan iska, shashasha mai butulci bai kamata ya shigo cikin gyaran tsaron ƙasa ba. Saboda haka da shugabanni da jami’an tsaro da sauran al’umma suna da rawar da za su taka wajen shawo kan matsalar tsaro a Nijeriya, ta hanyar kai rahoton duk wani mutum da ba a aminta da shi ba ga hukumar tsaro da ke kusa. Zaman lafiya ya fi zaman ɗan sarki, Hausawa sun ce har sarkin ma ya fi. Don haka shugaba mai ci a yanzu ya dace ya samu cikakken goyon baya ga al’ummar ƙasa don kawar da ayukkan ta’addanci da matsalar boko haram, da ɓarayin shanu da kuma masu satar mutane suna yin garkuwa da su. Wannan kuma ba zai samu ba sai idan an tantance jami’an tsaro masu gaskiya, masu kishin ƙasa aka kuma ba su isassun kayan aiki.

 

MANAZARTA

Tuntubi masu takarda

Post a Comment

0 Comments