Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Sana’ar Aruguma (Ƙwarya)

 Tattalin arzikin kowace al’umma ta duniya ya ta’allaƙa ne ga irin hanyoyin da take bi wajen samar da kuɗin shigarta, sana’ar ƙwarya tana ɗaya daga cikin hanyoyin da ke bunƙasa tattalin arzikin al’ummar Hausawa, musamman al’ummar Gummi da kewaye a jihar Zamfara. Wannan takarda mai taken, “Nazarin Sana’ar Ƙwarya” za ta yi bayani ne a kan sana’ar ƙwarya a karamar Hukumar Gumi da kewaye da yadda ta kasance hanyar bunƙasa tattalin arzikin al’ummar Gummi da kewaye da kuma wasu masu sana’ar ƙwarya a kowane lungu da saƙo na Nijeriya da ma wasu ƙasashen Afrika ta yamma. Wannan sana’a ta ƙara ɗaukaka darajar Gummi da kuma tattalin arzikinta.



Nazarin Sana’ar Aruguma (Ƙwarya)

 

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

GSM NO. 07032567689

E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim

1.0 GABATARWA

Sana’a tana nufin saye-da sayarwa da ɗan Adam yake yi domin neman abincin da zai ci, ya kuma sami rufin asiri ga wasu buƙatunsa na yau da kullum. Sana’ar ƙwarya tana ɗaya daga cikin manyan sana’o’in al’ummar Hausawa waɗanda suka samo asali daga yanayin zamantakewar da Hausawa suke yi a ƙasar Hausa ta hanyar noma.

 

Duk da kasancewar ƙasar Hausa tana da faɗi da kyakkyawan yanayi wanda ya tanadar wa al’ummar Hausawa da sana’o’i daban-daban da suke amfani da su wajen neman abinci, wannan ya nuna mana cewa sana’ar ƙwarya wadda asalinta daga noma ne, ya ba mu dammar gudanar da bincike a kan sana’ar da asalinta da rawar da take takawa ga bunƙasar al’adun gargajiya da haɓaka tattalin arzikin al’ummar Hausawa jiya da yau musamman a yankin Gummi da kewayenta.

 

1.1 MASU SANA’A ƘWARYA

Kowace irin sana’a da waɗanda ake danganta ta da su. Sana’ar ƙwarya tana da mutanen da suke aiwatar da ita kamar sauran sana’o’in gargajiya da suka haɗa da jima da rini da ƙira, da sassaka da sauransu. Bisa ga wannan dalili ne yasa wannan bincike ya yi tattaki har garin Gummi inda can ne cibiyar sana’ar ƙwarya ta yanke cibinta. Binciken ya zanta da masu sana’ar ƙwarya daban-daban domin jin ta bakinsu game da yadda sana’ar take da kuma irin gudummawar da take bayarwa wajen bunƙasa al’adu da tattalin arzikin ƙasa, wannan zamani da muke ciki da kuma can da da al’ummar Hausawa basu waye ba.

 

Na zanta da mutum na farko mai suna Alhaji Auwali Imam ɗan shekaru talatin da takwas (38) haifaffen garin Gummi, a karamar hukumar mulki ta Gummi, Alhaji Auwali Imam Bahaushe ne kuma mai biyar addinin musulunci, na farad a tambayarsa kamar haka.

1.      Wace sana’a ka fara yi a rayuwar ka?

Amsar da ya bani it ace “Na fara sana’ar ƙwarya da sayen Aruguma wato ƙwaryar da ta Lanƙwashe sai in kai rafi (Gulbi) in saka ta a ruwa ta kwana sannan in je in tayar da lanƙwasarta in kai kasuwa in sayar, da haka na cigaba da yi har na samu jarina ya girma sai na fara sayen ƙwarya mai kyawo ina sayarwa” Irin bayanin da na samu daga wannan Malami ya ƙara sa na yi masa sauran tambayoyi game da matsayin sana’ar, sai ya faɗa cewa, sana’ar kwarya tana da muhimmanci idan aka kwatanta ta da sauran sana’o’in gargajiya na al’ummar Hausawa. Ya ce sana’ar ƙwarya a da ba ta faɗaɗa sosai irin yanzu ba saboda ƙarancin abubuwan hawa da za a ɗauki ƙwarya a kai wurare masu nisa ba, saboda a da tafiyar ƙasa ake yi, mutum shi zai ɗauki ƙwarya a kansa ya tafi kasuwanne. Amma a yanzu motoci da sauran abubuwan hawa irin su mashin da kekuna su ake amfani das u wajen safarar ƙwarya zuwa gariruwa masu nisa.

 

1.2 KASUWAR DA TAFI CIKA DA ƘWARYA

Kasancewar Gummi ita ce cibiyar masana’antar ƙwarya a ƙasar Hausa da ma Nijeriya baki ɗaya, sai ta zama wata babbar kasuwa da ta fi kowace kasuwa cika da ƙwarya. Domin mutane daga kowane lungu na jahar Zamfara da sauran johohin Arewacin Nijeriya da Nijar da Ghana da Togo da sauransu suna zuwa kasuwar Gummi domin su sayi ƙwarya. Dalilin haka ya sa kasuwar Gummi tafi cika da ƙwarya, saboda yawan masu sana’ar da ke zuwa daga ko’ina domin sayen ƙwaryar.

 

 

 

1.3 WURAREN DA AKE KAI ƘWARYA DON KASUWANCI

Sana’ar ƙwarya ba a Gummi da kewayenta kawai ta tsaya ba, ana kai kwarya don sayarwa a wurare daban-daban na ƙasar don sayarwa a warare na ƙasar Afrika. A wata zantawa da na yi da Alhaji Tasi’u Sarkin Ƙwaryar Gummi, ɗan shekara 56, ya bayyana cewa yana kai ƙwarya don sayarwa a garin Kano, da Ɗanbatta, da Daura, da Maiaduwa da Kaduna, da Mina da Maiduguri, da Yola da kuma Gombe. Haka akwai Jalingo da Dutsi da Katsina da Potaskum a jihar Yobe duk a nan cikin Nijeriya. A ƙasashen waje kuma yana kai ƙwarya a Togo da Yamai da Libiya da sauran wasu garuruwa a cikin Afrika ta yamma.

 

Shi ma Alhaji Lawali Ɗanƙwarya mai shekaru 49 haifaffen garin Gyalenge, ya tabbatar da cewa sana’ar ƙwarya ba ta tsaya Gummi ba kawai, ana kai ƙwarya har jibiya da Sokoto da Illela da kuma Minna da Kontagora a Jihar Neja. Masu sana’ar ƙwarya daban-daban sukan shigo Gummi domin su sayi ƙwarya su kai garuruwa masu nisa kamar Jos da Bauchi da Ibadan ta Jihar Oyo. Waɗannan yan kasuwa na ƙwarya sun ɗaɗa faɗaɗa sana’ar ta hanyar karɓar kuɗaɗe daga masu zuwa sayn ƙwarya daga wasu wasu jahohi da kasashen waje domin su saya masu ƙwarya su tura masu a garuruwan su.

 

1.4 SAFARAR ƘARYA (TRANSPORTATION)

Mafi yawa masu sana’ar ƙwarya ba su ke da motocin da ke ɗaukar masu kaya ba zuwa wasu kasuwanni ko garuruwa. Akan sami waɗanda suka mallaki nasu motocin amma kaan ne daga cikin yan kasuwar. Wato ‘yan kasuwar suna ɗaukar hayar moticin da ke ɗaukar masu ƙorai zuwa kasuwannin da suke so su kai kaya, ko garuruwa. Misali masu fataucin ƙwarya sukan haɗu kamar su goma ko fiye da haka su haɗa ƙarfi su ɗauki hayar mota ta kai masu kyanasu kasuwanni ko garuruwan da suka fito, domin su sami sauƙin sufarin kayan su. Yan kasuwa daga jihohin Katsina da Kano masu kai kaya katsina da Kano sukan ɗauki motoci su yi masu dakon kayan (Ƙwarya) zuwa garuruwansu. Sukan ɗauki hayar mota/motoci dai dai ƙarfin jarinsu. Misali sukan ɗauki mota ɗaya a kan kuɗi Naira Dubu Saba’in da biyar (N75,000.00) ko abin da ya fi haka a lodi guda daga Gummi zuwa Dutsi da Jibiya a Jihar Katsina.

 

Su ma ‘yan kasuwar ƙwarya na Gummi, masu ƙarfi daga cikinsu sukan ɗauka irin wannan hayar mota wadda ke dakon kayansu. Wani direba da na zanta da shi; Alhaji Sani yace yakan karɓi kuɗin dakon kaya daga yan kasuwa kimanin Naira dubu ɗari (N100,000.00) a lodi ɗaya daga Gummi zuwa Malumfashi da Bakori jihar Katsina. Wani abin shaawa a nan shi ne, dalilin haɗa kai a ɗauki mota guda shi ne don a sami sauƙi, maimakon kowane ɗan kasuwa ya ɗauki tashi mota. Kuma yan kasuwar ƙwarya suna riƙe direba guda wannan kowane lokaci shi ne zai riƙa dakon ƙwaryarsu, sai fa idan wata matsala ta gitta sannan su nemi wani direba ya yi sufarin kayan su.

 

1.5 LODIN ƘWARYA A MOTOCI

Motocin da ke dakon ƙwarya zuwa wasu kasuwanni ko garuruwa suna ɗaukar kimanin kwarya da dama dangane da girman kowane ɗauri. Misali akan yi ɗaurin ƙwarya, wato ana shirya ta ɗauri ɗauri kamar haka:

a.      Doro – Shi ne ɗauri mai layi ɗaya da sanda  

b.      Falle  - Shi ne ɗauri mai layi biyu

c.       Kai – Shi ne ɗauri mai layi huɗu

d.     Bukka – shi ne ɗauri mai layi biyu sama, ukku ƙasa

Lodin babbar mota ya fi ɗaukar layuka da yawa, wato tana ɗaukar fiye da ashirin (20) wata kuma layi talatin da biyar (35). Su kuwa ƙananan motoci sukan ɗauki kimanin layi shidda ko bakwai (6-7). Wannan dakon ƙwarya da masu motoci daban-daban ke yi yana taimaka wa masu sana’ar ƙwarya wajen samun abin duniya cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Su kuwa direbobi suna samun abincin da suke ci da iyalansu ba tare da wata damuwa ba ɗauki tashi mota.

 

1.6 FARASHIN KWARYA JIYA DA YAU

Farashin ƙwarya abu ne wanda yake ba ya da tabbas domin akan sami howa da saukar farashin idan aka yi la’akari da yanayi da kuma darajar kowace ƙwarya. Ana iya kimanta /ƙiyasta farashin ta daidai da zuwan yanayin lokaci da ciniki ke gudana. Misali kowace ƙwarya ana sayenta dangane da darajarta. Ga dai yadda farashin yake kasancewa”

1.      Ƙwarya mai zane ana samunta N1,200.00 duma ɗaya (Argugumarta) (wato maras kyau) ana samunta N700.00

2.      Gidauniya ‘yar daka N500 – N600, Arugumarta N300 – N400

3.      Gidauniya yar jega N200 – N250

4.      Ƙoƙo N100 – N150

5.      Komo N200 – N250

6.      Ƙaƙe N80 - N100

7.      Ƙoƙon zoma (Karamin ƙoƙo N100 – N150)

8.      Goran hawan ruwa da kamun kifi N1,500 – N2,000

9.      Gorani hawan ruwa da kam????????

10.  Goran kuɗin Nono N600

11.  Ƙwarya mai ƙurzunai N250 – N300

12.  Marar kwasar tuwo N20 N30 N50

13.  Gyanɗamar sanya fura Nono da ruwa N250 – N300

14.  Masakin wankan jego N1,000 – N1,200

15.  Gago (Ludayi na shan hurar a gayya) N200

16.  Cilela/cilela (wadda dakarawa ke amfani da ita) N500 gumki

 

1.7 HASARAR DA AKE SAMU A SANA’AR ƘWARYA

Kowace sana’a da ɗan Adam ke gudanarwa akwai irin hasarar da ake fuskanta tattare da ita. Don haka Hausawa ke wata Karin magana inda suke cewa “Kasuwa ci mai tsoronki, haɗa da mai jin kunya” Wannan Karin magana tana da alaƙa da hasarar da ‘yan kasuwa suke samu a lokacin da suke gudanar da kasuwancinsu. Wato idan mutum yana jin tsoron kada ya faɗi ga sana’arsa, to ba zai yi kasuwanci ba. Kamar yadda Alhaji Muh’d Bello Gyalenge mai shekara 52 ya bayyana cewa ana samun hasara ga sana’ar ƙwarya idan aka sami.

a.      Dasun dasun ga ƙwarya (Ciwon Kwarya)

b.      Karancin ruwa a damana, kwarya za ta kasa yin kyau.

c.       Lodin ƙwarya a mota ya yi sama, ya bugi ice za a sami hasarar mutuwar ƙwarya

d.     Farashin ƙwarya ya faɗi ƙasa, ba za a mayar da kuɗin da aka sayi ƙwarya ba.

e.      Bashi ya yi yawa, za a sami hasarar karewar jari

 

1.8 RIBAR DA AKE SAMU A SANA’AR ƘWARYA

Riba garaɓasa ce da ɗan kasuwa yake samu lokacin da ya sayar da hajarsa da kuɗi masu yawa. Wato a lokacin da ya sayar da ƙwaryar da ya saya da kuɗi kaɗan ya kuma sayar da kuɗi masu yawa. Ita wannan riba tana samuwa ne lokacin da farashin kasuwar ƙwarya ya yi sama/ƙaru daga kuɗi ‘yan kaɗan zuwa kuɗi masu yawa. Misali mutum ya sayi ƙwarya dubu ɗaya ya sayar da ita dubu da ɗari biyu ko fiye da haka. Akan yi sa’a mai ƙaramin jari ya samu riba mai yawa har ya zama mai babban jari, idan farashin ƙwarya ya tashi sama. Haka shi ma mai babban jari yakan ci riba mai yawa ga hajarsa a lokacin da ya sayar da kayan da ya saye tun suna da sauƙi (da kaka), wato masu babban jari sukan sayi ƙwarya mai yawa a lokacin kaka, su ajiye har sai ta yi tsada kamar yadda sauran ‘yan kasuwa masu sayen kayan gona suke yi.

 

Tashin farashin ƙwarya yana ta’allaƙa ne da yawan masu buƙatar ƙwarya (Masaya daga ko’ina) masu zuwa (Gummi don su sayi ƙwarya su kai wurare daban-daban har da ƙasashen waje. A cikin bayaninsa, Alhaji Auwali Imam (Sakataren Kungiyar masu sana’ar ƙwarya Gummi) ya tabbatar da cewa, masu babban jari su suka fi kowane ɗan kasuwa cin riba mai yawa, saboda kayan da suke saye su a je har sai sun yi tsada. Misali idan mutum ya sayi ƙwarya ta kimanin naira dubu ɗari da kaka, idan farashi ya tashi yakan sayar da ita kimanin dubu ɗari uku zuwa huɗu. Ya ce yana sayen ƙwarya ta kimanin naira miliyan ukku ko fiye, lokacin da take da sauƙi, ya ajiye sai ta yi kuɗi sannan ya fito da ita ya sayar. Yana cin ribar aƙalla naira miliyan ukku ko biyu da rabi, idan ya sami saa farashi ya yi sama, wato a lokacin da masu sayen ƙwarya suka zo saye daga kowane lungu na ƙasar nan har da kasashen ƙetare. Wannan sana’a ta taimaka ma mutanen yankin Gummi ta samar masu aikin yi da hana matasansu zaman banza da shaye-shayen abubuwan sa maye barkatai. Alhaji Auwali Imam ya tabbatar da cewa wani lokacin yakan ɗauki ƙwarya ya kai wuraren kasuwancinsa kamar Gombe da Yola da Jalingo da Jos da kuma Bauchi. Haka kuma yakan kai ƙwarya Illela, da Yamai da Togo da Kwatano a cikin Afrika ta Yamma. Wannan zirga-zirga da yake yi ta kai ƙwarya a wurare daban-daban ta samar masa da cin riba mai yawa. Sanadiyar ribar da yake samu a sana’ar tasa ya sa ya mallaki dukiya da dama, ya tafi makka, ya sayi motocin zirga zirga ya kuma mallaki muhalin kansa. Da yake bayyana irin ribar da yake samu, ya misalta cewa idan farashi na tashi ƙwaryar da ya saya dubu goma (10,000) yakan sayar da ita dubu ashirin (N20,000) ko fiye da haka.

Shi ma da yake nasa bayani, Alhaji Tasi’u Sarkin Ƙwarya Gummi, ya ce yakan kai ƙwarya Kano da Ɗanbatta a jihar Kano da Daura da Maiaduwa a jihar Katsina. Haka kuma yana kai ƙwarya Kaduna, da Minna a Jihar Neja da Maiduguri da Yola da Gombe da Jalingo da Kuma Dutsi a Jihar Katsina. Har wa yau Alhaji Tasi’u Sarkin ƙwarya Gummi ya ce yakan kai ƙwarya Sokoto da Libiya, Yamai, Togo da Kuma Ghana. Saboda haka ya samu riba mai yawa, inda har takai akan kawo masa kuɗaɗe masu yawa ya sayi ƙwarya don kai wa abokan hulɗarsa ta sana’ar ƙwarya. A sanadiyar haka yake samun riba da ta sa ya zama babban ɗan kasuwa, kuma sananne a fagen cinikayyar ƙwarya. Yan kasuwa da dama suna amfana da sana’ar ƙwarya wanda ya haifar da cigaba da bunƙasar sana’ar ƙwarya ba a Gummi kawai ba har ma a faɗin arewacin Nijeriya da wasu ƙasashe na Afrika ta yamma. Da wannan hulɗa ta kasuwanci da mutane daban-daban suke yi tsakaninsu da mutanen Gummi, ƙaramar hukumar mulkin Gummi takan sami kuɗin shiga masu yawa da yake ba ta damar aiwatar da ayukan cigaba a duk faɗin yankin kamar ƙaramar hukumar, ba sai ta dogara ga kason da take samu daga gwamnatin tarayya ba.

 

1.9 MASU SAYEN ƘWARYA 

A dalilin amfani da ƙwarya da ake yi ya sa aka sami mutane da ƙabilu da dama suna sayen ƙwarya don yin wasu aikace-aikace da ita. Kafin zuwan wannan zamani da ake amfani da roba, ƙwarya ta kasance abu da ake amfani da ita wajen aikace-aikacen gida da sauransu. Saboda haka sai ƙabilu da dama suka riƙa sayen ƙwarya suna amfani da ita a harkokinsu na yau da kullum. Misali Fulani suna sayen ƙwarya domin su riƙa sa nono da suke zuwa kasuwa talla. Haka kuma suna amfani da ƙwarya da ɗaukar ruwan sha a rafi da makamantansu. Bayan ƙabilar Fulani, su ma Yarbawa suna sayen ƙwarya domin amfani da ita wajen bukatunsu na al’ada da kuma yin ado a gidajensu wurin adana kayan tarihi.

Haka kuma masu sayen ƙwarya don yin amfani da ita wajen ado da sauran abubuwa na yau da kullum sun haɗa da Inyamirai (Igbo) da Dakarkari (Dakkarawa) da Zabarmawa da sauran ƙabilu na arewa da kudancin Nijeriya.

 

1.10 ƘUNRIYAR MASU SANA’AR ƘWARYA

Kamar yadda kowace sana’a take da ƙungiya, ita ma sana’ar ƙwarya tana da tata ƙungiya wadda ke kula da masu sana’ar na cikin gida da kuma na waje. Aikin wannan ƙungiya shi ne ta kula da shige-da fice na masu sana’ar, domin hana wasu ɓata gari su gurbace manufar wannan sana’a. Haka kuma da hukunta masu laifi. Ƙungiyar sana’ar ƙwarya wato, (Calabash Sellers Association) tana da shugabanni da ke gudanar da al’amarinta domin kawo cigaban wannan sana’a. Shugabannin su ne:

1.      Alhaji Shehu Muhammad Shugaba          (Chairman)

2.      2. Alh. Auwali Imamu                                (Sakatare)

3.      3. Alhaji Tasi’u –                                           Sarkin Ƙwarya.

4.      Tukur Muhammad                          Ma’ajin Ƙungiya

5.      Garba Ƙusa –                                                 Alƙalin Ƙungiya

Wannan ƙungiya tana gudanar da tarurrukanta a offishinta da ke cikin babbar Kasuwar Gummi akai-akai domin tattauna matsalolin da ke tasowa. Haka ya sa an sami kwanciyar hankali da natsuwa a tsakanin masu sana’ar ƙwarya na gida da ma masu zuwa Gummi, daga wasu wurare don gudanar da sana’arsu.

 

Idan ɗan ƙungiya ya yi wani laifi akan kira taron gaggawa a ofishin ƙungiyar don a yanke shawarar ɗaukar matakin ladabtar da shi. Idan laifi mai tsanani ne akan yanke wa mai laifin hukuncin dakatar da shi daga kowace irin hulɗa da yan kasuwar ƙwarya har tsawon mako/sati uku ko wata guda. Yin haka zai sa wasu su koyi darasi su ƙaurace wa aikata duk wani laifi da zai kawo ɓatanci ga sana’ar ƙwarya. Ba akan yi hukunci da tarar kuɗi ba, sai dai a dakatar da mai laifi daga hulɗar ciniki da kowane mai sayen ƙwarya na ciki da na waje.

 

1.11 AMFANIN ƘWARYA

Ƙwarya tana da amfani da dama tun daga aikace-aikacen gida har zuwa ga bunƙasa tattalin arziki da haɓɓaka al’adun Hausawa na gargajiya; Misali:

1.      Aikace- Aikacen Gida: Ana sa hura/fura a cikin ƙwarya, da nono da ruwan sha.

2.      Ana sa tuwo da miya, musamman dakarkari, a aje a ɗaki don ka da ya lalace.

3.      Ana amfani da ƙwarya wurin yin dambu

4.      Ana amfani da ƙwarya wajen wankin kalwa

5.      Ana adon ɗaki da ƙwarya

6.      Ana wankan biƙi da ƙwarya

7.      Ana rufe masai da ita

8.      Ana wankin gumi/shinkafa da ƙwarya

9.      Ana tallar nono da ƙwarya

10.  Kambari na amfani da ita wajen aikin mankaɗe

11.  Ana yin mara da ita ta suyar gyaɗa da ƙwara da kwasar tuwo

12.  Ana kiɗa na aure da ita

13.  Ana kiɗan kaca-kaura da ita

14.  Ana kiɗan bori da ƙwarya

15.  Ana hawan ruwa (gora) da ita

16.  Ana fiton mutane a gulbi da ita

17.  Ana kamun kifi da ƙwarya

18.  Ana amfani da ita wajen tallar zuma

19.  Ana yin agushi da ɗiyanta

20.  Ana ƙuli da mai da ɗiyanta

21.  Ana bugun nono (Yarbaje/Fulani)

22.  Ana hude ta a ɗaura mata zare ana kamun kifi.

23.  Ana tankaɗe gari a cikinta

24.  Ana wankan magani da ita

25.  Ana yi mata ado a ajiye ta don tarihi da raya al’adu

 

1.12 MAGANIN GARGAJIYA DON BUNƘASA TATTALIN ARZIKI

Ta fuskar bunƙasa al’adu, da tattalin arziki ana yin magani da ƙwarya wajen warakar cututtuka na mutane da dabbobi da ƙwari da duk wani abu mai rai.

1.      Mutane: Ana amfani da toton ƙwarya idan aka jefeta za a ɗauki toton a haɗa magani a ajiye a gona idan ɓarawo ya saci ƙwarya ba zai iya fita cikin gonar ba. Wato idan ya saci ƙwarya zai yi tsaye wuri guda har sai mai gonar ya isko shi, sannan ya sallameshi ya tafi.

2.      Ana maganin fitsarin kwance ga yara maza da mata. Za a jika totonta maras kauri wanda ake kankarewa daga cikin ƙwaryar a riƙa ba yaro ko yarinya mai fitsarin kwance ya sha har sau uku, sai ya daina fitsarin.

3.      Idan mutum yana fama da masassara mai sa zafin jiki ana ɗauko ruwan gulbi da ita a kuma jiƙa wannan toton maras kauri a ba maras lafiya ya sha, sai ya sami waraka jikinsa ya bar yin zafi.

4.      Ana jiƙa toto maras ƙauri a bai wa dabba mai tari/tari ta sha sai ta warke.

5.      Ana ba shanu totonta su ci maganin ciwon ciki da tsutsotsin ciki.

6.      Ana yin dussa da gari da totonta a riƙa sayar ma Fulani ko masu kiwo su ba shanu suna ci maganin yunwa.

 

1.13 WURAREN DA AKE NOMAN ƘARYA

Mafi yawan wuraren da ake noman ƙwarya sun ƙunshi tudu da fadama. Waɗannan wurare ana samun su a garuruwa da suke gulabe sun kewaye su. Misali akwai garin Gummi da Gayari, da Gyalange, da Bardoki da Falale, da Unguwar Hassan da Turmi, da Girkau, da Birnin Magaji da Birnin Tudu duka a ƙaramar hukumar mulki ta Gummi jihar Zamfara. Waɗannan garuruwa da aka ambata sun amfana da noman ƙwarya domin tattalin arzikinsu ya bunƙasa sosai.

 

Haka kuma ana noman ƙwarya a Gombe da Dukku a Jihar Gombe, Akwai Romo da Margai da Sokoto a Jihar Sokoto. Sauran wuraren da ake noman ƙwarya a ƙasar Hausa asalinsu duk mutanen yankin Gummi suka tafi da irin can suna nomawa. Ga bincike da muka yi ya nuna cewa Gyalange da Bardoki da Gayari su ne cibiyoyin noman ƙwarya a ƙaramar hukumar mulkin Gummi (Bayan daga Uban ƙasar Gayari Alhaji Hassan Muhammad Gayari 24/4/2019.

 

1.14 JARIN DA AKE FARA SANA’AR ƘWARYA DA SHI

Jarin da ake fara sana’ar ƙwarya ya danganta da zarafin da mutum yake da shi. Kamar yadda Tasi’u Sarkin Ƙwaryar Gummi mai shekara 52 ya bayyana cewa, ya fara noma ƙwarya ne da hannunsa ya sayar jikka takwas kwatankwacin naira dubu da ɗari shidda (N1,600) sai ya fara sayen naƙasassun ƙorai da ƙoƙo yana tayarwa ya sayar har ya sami jarin da ya cigaba da sana’arsa. Da wannan ne jarinsa ya bunƙasa har ya zama babban dilan sana’ar ƙwarya a ƙaramar hukumar mulki ta Gummi.

 

Shi kuwa Alhaji Lawali Ɗanƙwarya mai shekaru 49, cewa ya yi sana’ar sakai, wato sayen hatsi yana sayarwa ya fara da ita, da ya sami jari sai ya koma sana’ar ƙwarya. Ya ce, ya fara da jarin N13,000.00 yana kai ƙwarya Illela da Jibiya har ya kai matsayin da yake a yanzu. Wasu kuma suna fara wa da Jarin N200,000.00 har abin da ya yi sama. Masu jarin miliyan suke da babban jari, suna sayen kwarya suna adanawa har sai ta yi tsada su fitar su sayar; (Jawabi daga Sarkin Ƙwaryar Gummi) 24/4/2019. Sauran farashin ƙwaryar ya danganta da ingancinta kamar yadda bincike ya gano.

 

1.15 NAU’O’IN ƘWARYA

Ƙwarya ta kasu kasha kasha kamar haka:

1.      Masaki – babbar ƙwarya ce da ake amfani da ita ga jego

2.      Argumarta

3.      Yar daka

4.      Gidauniya

5.      Yar Jega

6.      Ƙoƙon Yar Jega

7.      Ƙoƙon dan zoma

8.      Komo

9.      Ƙaƙe

10.  Gora

11.  Gyanɗama

12.  Zunguru

13.  Shantu

14.  Ludayi

15.  Gago

16.  Kumbu

17.  Bakabata

Kowace daga cikin waɗannan nau’o’in ƙwarya da ake das u akwai amfanin da ake yi da ita, musamman a ɓangaren al’adu da bunƙasa tattalin arzikin al’ummar Hausawa fannoni daban-daban.

1.6 SAKAMAKON BINCIKE

A sanadiyar cinikayyar ƙwarya da al’ummar Gummi da kewaye suke gudanarwa, an sami cigaba da bunƙasa tattalin arziki da ya haifar da:

a.      Samar da aikin yi ga matasan yankin

b.      Samar wa ƙaramar hukuma kuɗaɗen shiga da yabata dammar aiwatar da wasu ayyukan raya ƙasa a dukkanin yankin.

c.       Duk da canjin zamani da aka samu na kayan alatu da zamani ya zo da su, har yau ƙwarya tana da matsayi a fagen bunƙasa tattalin arikin yankin, saboda mutane da dama suna zuwa Gummi don kasuwancin ƙwarya, daga kowane lungu da saƙo na ciki da wajen Nijeriya.

 

1.7 KAMMALAWA

Da sana’ar ƙwarya ta bunƙasa a ƙaramar hukumar mulkin Gummi da ke waye, mutane sun sami yalwar arziki da samun ayyukan yi, wanda ya rage zaman banza da ayyukan ta’addanci tsakanin matasa da sauransu.

 

1.8 SHAWARWARI

Ina kira ga hukuma da masu ruwa da tsaki a cikin kasuwancin ƙwarya da su kafa wani kamfani da zai sarrafa ƙwarya don samar da magani ta hanyar zamani domin ƙara bunƙasa tattalin arziki a jihar Zamfara da ƙasa baki ɗaya. Idan haka ya samu babu shakka matasa za su sami ayyukan yi, a rage zaman kashe wando da ayyukan ta’addanci, da samar da tsaro a yankin Zamfara da ƙasa baki ɗaya.

 

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments