Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudunmawar Makadan Hausa Ga Al’ummar Najeriya; Misalai Daga Waƙar Hada Kan Najeriya Ta Musa Ɗan Ba’u

 Takardar Da Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Ƙasa Na Farko A Kan Harshen Hausa, Adabi Da Al’adu, A Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya A Jami’ar Bayero Da Ke Kano, Litinin 14-16 Ga Janairu, 2013.

Gudunmawar Makadan Hausa Ga Al’ummar Najeriya; Misalai Daga Waƙar Hada Kan Najeriya Ta Musa Ɗan Ba’u

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

GSM NO. 07032567689

E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim

1.0       GABATARWA

Hakiƙa irin rawar da mawaƙan baka na Hausa ke takawa wajen fadakar da al’umma game da halin da ƙasa take ciki ba ƙarama ba ce, kuma sun cancanci yabo.

A duk lokacin da wata matsala ta tusgo, shugabanni ko Gwamnatin Tarayya da Jihohi da kuma Ƙananan Hukumomi sukan rika tuntuɓar mawaƙan baka na Hausa da su rera waƙa don su faɗakar da jama’a a kan wannan buƙata. Dangane da irin wannan kira da Gwamnati kan yi wa mawaƙa ya sa su mawaƙan kan tsaya su kalli matsala, sannan su shirya mata waƙa da za ta wayar ma da mutane kawunansu da kuma ilmantar da su ga wani sabon abu da yake gudana a Ƙasa.

Najeriya ƙasa ce mai faɗi da yawan ƙabilu daban-daban da babbancin addinai da al’adu. Ana hasashen cewa akwai aƙalla kimanin ƙabilu ɗari ukku da casa’in da huɗu – (Source: K. Hansford and J.B Samuel: Studies in Nigerian Languages, No. 5 1976, pp 33-366). Don haka duk ƙasar da ke da yawan ƙabilu da addinai daban-daban kamar Nijeriya yana da wuya a sami ingantaccen haɗin kai da zaman lafiya da tsaro.

Ganin irin yadda waɗannan matsaloli na rashin zaman lafiya da hadin kai da tsaro ke aukuwa a ƙasar nan ya sa wannan takarda ta yi tsokaci a kan waƙar da Musa Ɗanba’u gidan Buwai ya rera, mai taken “Hadin kai a NIjeriya”, domin jawo hankalin yan Nijeriya da su zauna lafiya da junansu, don a sami bunƙasar tattalin arziki da haɗin kai da tsaro; misali:-

 

G/Waƙa:        ‘Yan Nijeriya, yan uwa mu yi ƙoƙari,

Amshi:            Mu zan haɗa kanmu mu kama hanyar gaskiya“

 

2.0       MUSA ƊANBA’U

Yana da kyau kafin a yi nazarin waƙar Musa Ɗanba’u a kawo taƙautaccen tarihin rayuwar Musa Ɗan Ba’u. Musa shi ne sunansa na yanka, Ɗanba’u kuwa laƙabi ne da mahaifiyarsa ta sa masa, saboda al’adar Bahaushe ta alkunya, wannan suna na Ɗanba’u da shi aka fi saninsa, kuma ake kiransa tun yana yaro ƙarami. Da ya manyata aka cigaba da kiran sa Musa Ɗanba’u Gidan Buwai wato ana kiran sa da sunansa na yanka da laƙabi da kuma sunan garinsu.

An haifi Musa a garin gidan Buwai a ƙaramar hukumar mulki ta Illela, a Jihar Sakkwato a Shekarar 1955, kuma mahaifansa su ne, Malam Abdullahi Maigwangwa da Malama Aminatu, ya yi karatun Allo a makarantar Malam Mai Littafai. Musa ya yi gadon waƙa ne daga Mahaifinsa Audu Gwangwa wanda shi makaɗin goge ne, amma kuma idan lokacin damina ya zo sai ya koma gona don noma abinci. Shi dai Musa ya yi Sha’awar waƙa daga sana’ar babansa. Ya tashi yana sha’awar waƙa, kuma yakan tara yara yan uwansa ya riƙa rera masu waƙa a dandalin wasannin dambe da kokuwa. Musa Ɗanba’u shi ka ɗai yake yin waƙarsa a wancan lokaci, watau bai da mai yi masa amshi. Ya kuma soma waƙa a lokacin da ya fahimci hazaƙa da basira sun zauna masa a kai, ya tanadi kayan kiɗa da masu taimaka masa da kiɗa da amshi da dan ma’abba (Kwando). Ya yi fice a fagen waƙar kokuwa a kowane lungu na jihar Sakkwato da jamhuriyar Nijer da Sauran jihohin Arewacin Nijeriya daban-daban.

Da siyasa ta shigo a shekarar 1979 sai “ya’yan jami’yyar NPN; ɗaya daga cikin jam’iyyu guda biyar da muke da su a wancan lokaci suka buƙaci Ɗanba’u ya yi wa jam’iyyarsu waƙa. Mawaƙin na kokuwa ya shirya wa jamiyyar NPN waƙa, wadda ta zama sanadiyar karɓuwar jam’iyyar ga mutanen Sakkwato da sauran masu sha’awar siyasa. Sauran jam’iyyu hudu na ƙasa su ne, (N.P.P, U.P.N, G.N.P.P  DA P.R.P). Daga wannan lokaci sai Musa ya bar waƙar kokawa ya koma mawaƙin siyasa da sauran jama’a daban daban. A halin yanzu Musa Ɗanba’u yana cikin shahararrun mawaƙan Hausa da suka yi fice a fagen waƙoƙin siyasa. Musa yana zaune a Illela da iyalansa, yana da matan aure da yaya da dama.

Alhaji Musa Danba’u ya shiga baje kolin hajar tunanensu wajen faɗakarwa da kuma wayar da kan jama’a game da amfanin haɗin kai da zaman lafiya.

Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai ya rera waƙarsa, mai gindi,

 

Ɗan Ba’u:                  ’Yan Nijeriya yanuwa mu yi kokari,

Amshi             Mu zam hada kanmu

mun kama hanyar gaskiya”

 

Ɗanba’u ya tsara wakar ne ta yin la’akari da yadda Nijeriya take mai fadi da yawan ƙabilu da banbancin addinai da al’adu inda ya danganta haɗin kai da zaman lafiya da cewa su ne ginshikan cigaban kowace kasa da bunƙasar tattalin arzikinta, ba wai Nijeriya kaɗai ba.

 

3.0       MATAKAN DAƊA HAƊA NAJIRIYA A TUNANEN WAƘA

Haɗin kai shi ne, haɗuwar mutane masu ra’ayi ɗaya, ko daban-daban a wuri ɗaya tare da fahimtar juna, domin su aiwatar da ayukkan cigaba ba tare da nuna wariya ko banbancin addini ba (Danmaraya Jos). Inda duk al’umma ta haɗa kanta wuri ɗaya, to babu shakka yana da wuya a raba su balantana a jefa su cikin rikici da kiyayya da junansu. Rashin hadin kan al’umma yana haddasa fitina da faɗace-faɗace da ka iya rushe cigaban ƙasa ta kowane fanni.

 

3.1       GARGAƊIN ’YAN BARANDA 

Mutane ne masu kai kawo, suna sayen haja daga hannun waɗanda suka sarrafa ta na asali suna kaiwa wata kasuwa ko kamfani suna sayarwa domin su sami riba. A nan Musa ya kamata America da Ingila da Faransa a matsayin yan barandar Siyasa da ke shiga a cikin wata ƙasa su sami labari su tafi su watsa a duniya ta kafafen watsa labaransu. Irin waɗannan ƙasashe, su ne Ɗanba’u ke kira da suna yan baranda, sannan yana kiransu da su daina yimana shisshigi ga ƙasarmu domin kada su roshe haɗin kanmu; ga abinda yake cewa.

 

Ɗanba’u:        Ƙasashen da ka shisshigi haɗin kan mu ya wargaje  

                        To Najeriya ta yi sayyu ta kafu

Amshi:            Munafuccin nasu ba za ya gurguntamu ba

 

3.2       GARGAƊIN YAN ZAMBAR CIKI

            Yan zambar ciki, su ne mutanen cikin gida/ƙasa waɗanda aka amince masu, amma da haɗin kansu ne yan baranda ke yiwa ƙasarsu zagon ƙasa, watau suna sayar da labaraii ko kwashe asirin ƙasa, suna sayarwa ga yan baranda domin su sami wata biyan buƙata taƙashin kansu, saboda haka ne, mawaƙin ya gargaɗi jama’a da su kaucewa yin hulɗa kowace iri da su domin kada su jefasu cikin rikicin siyasa da addini da ƙabilanci da ka iya ruguje haɗin kai da zaman lafiya a Najeriya. Ga dai abinda yake cewa:

Ɗanba’u         Kam mu yarda da yan baranda da yan zambar ciki

                        Masu son su haɗamu barna su koma tsallake

Amshi:            Idan ta rikice su buƙata ta biya

 

Haka zai iya kawo munafukai da marasa kishin ƙasa da ‘yan  barandar siyasa su kutso kai su rika watsa jita-jita da ƙirƙiren karya domin su watse haɗin kan al’umma da rushe tattalin arzikin ƙasa.

Alhaji Musa Ɗanba’u ya rera waƙa don ya gargaɗi masu irin waɗannan  dabiu su daina, haka kuma ya kira yan Nijeriya masu yi wa Nijeriya zagon ƙasa da su yi wa Allah su daina kaiwa da komawa ga abin da zai ruguje hadin kan ƙasa. Musa Ɗanba’u yana cewa.

Musa ya bayyana siffar munafukan Nijeriya a matsayin “Yan baranda da kuma yan zambar ciki” a sigar mutane biyu, watau yan baranda su ne wadanda ke sayen haja daga hannun wasu su tafi su sayar don su ci riba. Su kuwa yan zambar ciki mutane ne yan ƙasa da aka amince masu, amma suna amfani da damar da aka ba su, suna yi wa ƙasarsu zagon ƙasa. saboda haka ne mawaƙin ya yi gargadi ga jama’a da su kaucewa hulɗa da su don ka da su jefa su cikin rikice-rikicen addini da ƙabilancin siyasa.

 

3.3       KIRA KAN ZAMAN LAFIYA

Hausawa suna cewa; “Zaman lafiya ya fi zama dan Sarki, amma masu iya magana sunce, “Ko Sarkin ma ya fi". Zaman lafiya shi ne ginshikin cigaban ƙasa da haɗin kan al’umma. Idan babu zaman lafiya, yana da wuya a sami haɗin kai da fahimtar juna, Danba’u yana cewa:

 

Ɗanba’u:                    “Na ɗai haɗin kayin ƙasa, ka ga ba zai samu ba,

Amshi:                        Sai da zama lafiya muy yi fahimta yan uwa.

 

Idan aka yi maganar haɗin kai to dole ne a yi tunanen kauda ƙabilanci a cikin al’umma. Domin nuna ƙabilanci da banbancin addini suna taimakawa ga ragujewar zaman lafiya da fahimtar juna a ƙasa; Misali.

 

Ɗanba’u:        Kun gani Najeriya mai yawan faɗin ƙasa

                        Al’adunmu daban-daban, addinan mu daban daban

                        Allah mai ƙaddaroƙa a kowane al’amar

Amshi:            Shi ya ƙaddaro mun ka zauni wuri ɗaya

                        Kuma gidan mu yana ɗaya.

 

Ƙabilanci shi ne, nuna banbancin launin fata, ko yare ko addini ko al’ada. Ƙabilanci yana faruwa ne a ƙasa da ke da yawan ƙabilu daban-daban, inda kowace ƙabila take nuna jin kanta da ganin fifiko bisa ga wata ƙabila ko nuna bangaranci, ga wasu rukunin jama’ar ƙasa ko yanki. Misali:-

 

Ɗanba’u:        Kifi da kada da ƙwado, da tsari, dorina,

                        Halittarsu daban- daban, amma in mun tuna,

Amshi:            Duk gidansuu yana ruwa

 

Ɗanba’u:        Ina Yarbawa, Nufawa, ina jama’ar Ibo,

                        Harda ku jama’ar Tibi

Amshi:            duk mu taru muje gaba ɗai mu koma ‘yan uwa

 

Duk ƙasar da ke da yawan ƙabilu irin Nijeriya, babu shakka ba za a sami cikakken haɗin kai ba, sai idan shugabanni sun tsayar da adalci wajen raba mukaman gwamnati da arzikin kasa dai-dai. Saboda haka idan har ana son a sami zaman lafiya da haɗin kai ya ɗore, to dole ne a tabbatar da tsarin raba dai-dai ya yi tasiri a Nijeriya. Yin haka zai sa a kawar da ƙabilanci da bangaranci da ke haifar da faɗace-faɗacen addini da siyasa a kowane lungu na ƙasar nan.

Mawaƙin ya siffanta ƙabilun Najeriya da halittun da ke cikin ruwa wadanda ke da dangantaka ta wurin zama, misali kifi da kwaɗo, da kada da tsari dukkansu yan uwan juna ne, watau yan kwai ne, sannan kuma dukkansu cikin ruwa suke zaune. Haka ita ma dorina cikin ruwa take zaune duk da kasancewa ita ba yar kwai ba ce. Don haka a ganinsa waɗannan halittu masu asali ɗaya da mazauni wuri ɗaya bai kamata su ƙyamaci junansu ba. Haka kuma abin yake ko ga mutanen Nijeriya irin su Yarbawa da Nufawa da Ibo da Tibi da Hausawa da Fulani da sauran ƙabilun Nijeriya waɗanda ƙaddarar Allah (SWA) ta haɗa su wurin zama ɗaya, watau ƙasa ɗaya. Wannan magana ta Danba’u gaskiya ce domin idan“yan Nijeriya suka fahimci haka dole ne su kasance masu hakuri da juna, su haɗa kai don a sami cigaba da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa. Malamin yana fatar alhairi da yi wa ƙasar adu’a kamar haka:

 

Ɗanba’u:        Ni ɗan Najeriya kai ɗan Najeriya

                        Ke yar Najeriya ita yar Najeriya

Amshi:            Ku mu zauna da juna mu yi hankuri

 

3.4              TUNI KAN KYAWAWAN HANYOYIN SHUGABANCI

Kyakkyawan shugabanci ya dogara ne ga irin mutanen da aka baiwa jagoranci; idan ana son a sami kyakkyawan shugabanci na gaskiya da riƙon amana da adalci a ƙasa, dole ne a zaɓi mutane masu amana da mutunci da dattako da kishin ƙasa. Ka da a zabi masu tunanen tara abin duniya don ɗai su ji daɗi da su da iyalansu. Shugabanci na gari shi ne a yi rikon talakkawa da adalci watau a bai wa kowa hakkinsa da ya dace, ba tare da ha’inci da son zuciya ba, ko nuna ƙabilanci ko bangaranci ba. Musa Danba’u ya ba da misalai na wasu shugabannin ƙasa, masu adalci da rikon amana da kishin ƙasa waɗanda suka taka rawar gani wajen bunƙasa haɗin kan ƙasa da samar da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziki. Waɗannan dattawa sun haɗa da, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato (firimiyan Jihar Arewa) da Sir Abubakar Tafawa Balewa (firayiministan Nijeriya), da Dr. Nnamdi Azikuwe, da Sir Muhammadu Ribaɗo Yola da Sir Kashim Ibrahim da sauransu. Manufar waɗannan shugabanni ita ce su haɗa kan Najeriya da bunƙasa tattalin arzikinta. Hausawa sun ce “yabon gwani ya zama dole“, saboda haka ne Musa Danba’u yake tunatar da masu riƙe da mulkin ƙasa da talakawa game da irin ƙwazo da waɗannan shugabanni suka nuna wajen samar da haɗin kai da zaman lafiya a Nijeriya ya zama abin yabo, wanda har abada ba za a manta da su ba a tarihin Nijeriya. Don haka Danba’u yake kira da ayi koyi da su, yana cewa:

 

 

Ɗanba’u:        “Sir Ahmadu Bello shi da Tafawa

Sannan Ribaɗo Muhammadu

Amshi:            Sun dage ƙwarai namu yanci ya fito.

 

Ɗanba’u:        In Sir Kashim na Sardauna Ahmad Bello

Dattijo Baba Mazan Jiya

Amshi:            Irin hikimakku ba za mu mancikke ta ba.

 

Ɗanba’u:        “In ga dokta Namandi, Sannan da Awolawo ciki

Janaral Murtala ga Aminu garin Kano

Amshi:            Sun hada kammu ba za mu mancikke su ba.

 

Har wa yau Musa ya yi ƙoƙari ya nuna wa jama’a irin namijin ƙoƙarin da shugabannin Sojoji da yan siyasa suka yi irin su Obasanjo da sani Abacha da Ibrahim Babangida da Buhari suka yi wajen samar da haɗin kai abin a yaba ne. Ya cigaba da cewa;

 

Ɗanba’u:        “Obasanjo da Shehu Shagari,

Sa da Buhari Dattijo sai Babangida,

Da Sani Abacha Dattijo mai son gaskiya

Manufarsu guda haɗin kan ƙasar Nijeriya

In sunka hada ta tat tashi lebur tayyi tsaf

Amshi                         Ɗan Nijeriya ba ya shawar wata ƙasa.

 

Mawaƙin ya yi kira ga yan Nijeriya, musamman ma shugabanni da su yi koyi da shugabannin da suka taka rawa wajen hada kan yan Nijeriya da kawo cigaban ƙasa. Rashin kyakkyawan shugabanci yana haddasa taɓarɓarewar haɗin kai da zaman lafiya da rashin aikin yi da tsaro a cikin ƙasa.

Don haka Ɗanba’u ya ƙara da kiran yan Nijeriya baki ɗaya, musamman yan siyasa da sauran jama’a waɗanda aka zaɓa domin su sake gyara kundin tsarin mulki da cewa suyi koyi da su Sardauna. Yana cewa:

 

Ɗanba’u:        Wakilanmu da ke Abuja ku dage dai ƙwarai

Tsarin mulkin ƙasa, wanda shi muka sa gaba

Amshi:            Ku ɗauki halinsu don kam mu faɗa gargada.

 

3.5       BUNƘASA TATALIN ARZIKI

Kowace ƙasa ta duniya tana alfahari da tinƙaho da albarkatun ƙasa da take da su. Nijeriya tana daga cikin ƙasashen duniya da Allah (SWA) ya albarkata da nau’ukan ma’adinai da albarkatun ƙasa irin su manfetur, zinari, azurfa, tantalayi da sauran albarkatun gona da suka haɗa da auduga, da gyaɗa, da koko da sauransu. Idan ƙasa tana bukatar arzikinta ya bunƙasa, dole ne ta tanadi hanyoyi da zata haƙo ma’adinanta da bunƙasa harkokin noma. Dalilin haka ne Musa Danba’u ya yi kira da kuma gargadi ga hukumar Nijeriya da ta lura da irin albarkatun ƙasa da take da su don ta kafa  kamfuna da za su sarrafasu, tattalin arzikin ƙasa ya bunƙasa. Musa ya kawo sunayen ma’adinai da albarkar gona da muke da su kamar haka:

 

Ɗanba’u:        “Albarkar ƙasa ba kamar Nijeriya

Akwai zinari da fetur cikin Najeriya

Amshi:            Akwai koko, gyaɗa, auduga na nan ciki.

 

Haka kuma Ɗanba’u ya ƙara da fadakar da al’umma game da masanantunmu inda yake cewa:

 

Ɗanba’u:        In kamfuna da dama cikin Nijeriya

Masana’antu da dama cikin Nijeriya,

Amshi:            Saboda hakan ga mu ba mu kyashin wasu.

 

Ɗanba’u:        “In kamfunan da muke da su, masana’antun mu,

Amshi:            Duk mu adda abinmu mun daina bayarwa aro“

 

Ɗanba’u:        In kaya na aro idan sun zame ba naka ba

Amshi:            Da ka gama moriya sai ka maida mai gida

 

Duka abubuwan da Musa ya ambata game da tattalin arzikin ƙasa ba za a amfana da su ba irin yadda ya kamata sai fa idan an sami kyakkyawan shugabanci a ƙasa.

 

 


4.0       KAMMALAWA

Kamar yadda wannan takarda ta nuna makaɗan hausa sun taka rawa wajen haɓɓaka siyasa a Najeriya, Musa Ɗanba’u na ɗai daga cikin su, wanda ya duƙufa ga faɗakar da yan Najeriya da kuma yi masu gargaɗi ga me da amfanin haɗin kai, musamman wajen samar da zaman lafiya, bunƙasar tattalin arziki, kyawawan shugabanci da sauransu, wannan maƙala ta kawo takaitaccen tarihin Musa Ɗanba’u da irin rawar da waƙar sa ta haɗa kan Najeriya ta taka wajen fito da matakai daban daban da za’a yi amfani da su domin a gina ƙasa da samar da haɗin kai.

            Harwa yau maƙalar ta taɓo hanyoyin da waƙar take gani sune mafita da warware rickicin siyasar Najeriya domin a samu kyakyawan shugabanci, hanyoyin kuwa su ne; zaɓen mutane dattijai masu gaskiya da riƙon amana, irin su Sa Ahmad Bello Sardauna, da Abubakar Taɓawaɓalewa da Malam Aninu Kano, da Dakta Namandi Azukuwai da sauransu.

            Zaɓen irin waɗannan mutane, a tunanen waƙar shi zai kai Najeriya ta samu cigaba ta fusar bunƙasa tattalin arziki da haɗa kai da zaman lafiya.

Najeriya ƙasa ce mai albarka da yawan ƙabilu da addinai daban-daban wadanda ke buƙatar ingantaccen haɗin kai da shugabanci na gari. Irin wannan matsayi da Allah (SWA) ya yi wa Najeriya ya sa ƙasashen duniya sun sa mata ido da yi mata barazana da maƙarƙashiyar rugujeta ta hanyar haddasa rigingimun siyasa da ƙabilanci da addini.

Danba’u ya wayar wa jama’a da kawunansu ta hanyar waƙar hada kan Nijeriya da ya yi a shekarar 1993 lokacin da rikicin siyasar 1993 ta yi kamari (Watau rikicin Jun 12), ya gargadi yan Nijeriya da su kula da irin kisisina da makirci da Yahuɗawa, watau Amerika da Ingila da Faransa suke kullawa don su hassasa fitina da za ta rosa haɗa kan yan Nijeriya. Idan “yan Nijeriya ba su haɗa kai ba, suka zama tsintsiya maɗaurinki guda, babu shakka munafukai na cikin gida da yan barandar siyasa za su cimma burinsu na wargaza hadin kan al’umma da rushe tattalin arzikin ƙasa. Saboda haka ya kamata a farka a natsu domin a sami ingantaccen haɗin kai, a kauce ma rigingimun ƙabilanci da rikicin addini da siyasa da ka iya kawo hassarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Tabbatuwar haka ba zai samu ba sai da samun kyakkyawan shugabanci na mutane masu dattako da adalci da rikon amana. Don haka samun kyakkyawan mulkin dimokuraɗiya a ƙasa ya dogara kacokam ga zaɓen shugabanni na gari masu kishin ƙasa, adilai da za su kawo haɗin kai da zama lafiya da zai sa ƙasa ta cigaba.

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments