Wannan takarda mai taken “GUDUNMAWAR RUBUTUN WAƘOƘIN SIYASA WAJEN SAMAR DA KYAKKYAWAR DIMOKURAƊIYYA A NIJERIYA”, ta zama ruwan dare wajen kawo hanyoyi masu gamsarwa a kan yadda rubutattun waƙoƙin hausa na siyasa ke kawoo canji da ci gaban dimokuraɗiyya. A takardar an kawo tarihin samuwar rubutattun waƙoƙi a takaice da ma’anar waƙa da rabe-rabenta, sannan an kawo taƙaitaccen tarihin samuwar jama’iyyu tare da fito da misalai na baitoci daban-daban daga cikin rubutattun waƙoƙin hausa mabambanta dake ganin zasu zama gudunmawa wajen samar da kyakkyawar dimokuraɗiyya, da ga ƙarshe kuma a kawo jawabin kammalawa.
Gudummawar Marubuta
Waƙoƙin Hausa Na Siyasa
Wajen Ilmantar Da Al’umma Ga Samar Da Kyakkyawan Mulkin Dimokuraɗiyya A Nijeriya
ALIYU RABI’U ƊANGULBI
GSM NO. 07032567689
E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim
GABATARWA
Haƙiƙa waƙa tana da mutuƙar mahimmancii da
amfani wajen ci gaba da bunƙasar siyasa, kuma a ba ce mai koyar da
darasi da kuma sa a kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban ƙasa.
Annabi Muhammad (SAW) ya ce: “A
cikin waƙa akwaii hikima”, sannan kuma ya sake cewa “hikima adon
mumini”.
Wannan takarda za ta kawo irin salo
da dabaru da marubuta waƙoƙin siyasa suke amfani da su wajen cimma nasarar samar da
kyakyawar dimokuraɗiyya taer da kawo hiɗin kai da ƙaunar juna a tsakanin
al’umma.
Takardar ta kawo tarihin samuwa rubutattun
waƙoƙi a ƙasar Hausa a taƙaice, sannan kuma ta
dubi ra’ayoyin masana dangane da ma’anar waƙa da rabe-rabenta da
ma’anar dimokuraɗiyya tare da kawo
takaitaccen tarihin jam’iyyu. Haka kuma takardar ta fito da wasu misalai na waɗannan waƙoƙin domin nuna
tabbacin marubutan sun taka gagarumar rawa wajen sa jama’a da su shiga siyasa.
TARIHI SAMUWAR
RUBUTATTUN WAƘOƘI A ƘASAR HAUSA A TAƘAICE.
Yahaya (2002:8) ya
bayyana cewa, kafin musulunci ya iso ƙasar Hausa sai da ya
fara biyowa ta wasu sassa na ƙasashen Afrika ta yamma tukunna, kamar
Senegal da Mali a wajen ƙarni na 11. Sai dai ya kawo ra’ayin wasu malamai irin su
limamin Bauchi Ahmad Muhammad da Alhaji Nasiru Kabaro Kano, inda suka nuna cewa
musulunci ya iso Afrika ta yamma, musamman Agadas da Barno tun a ƙarni na 7, zamanin
Sayyadina Mu’awiya Ɗan Safiyanu.
To, ko ma dai yaya tarihin yake, an
tabbatar da cewa addinin Musulunci ya sami ƙarfafuwa a ƙarni na 15, lokacin
da Shehu Musa Jakollo da tawagarsa suka shigo ƙasar Hausa da
littattafan addini a kan Fiƙihu da Shari’a da Lugga a zamanin Sarkin Kano Yakubu (1452-1463)
(Yahaa 2002:10), bayan nan kuma zuwan wasu ƙungiyoyi na wangarawa
a ƙarƙashin jagorancin
Abdurrahman Zagaiti (1463-1499) da almaghili (1484) sun taimaka wajen bunƙasa addinin musulunci
da littattafan addinin waɗanda yawancinsu aka
wallafa su a waƙe.
Har’ila yau ayyukan Wali Ɗan Marina a ƙarni na 17 da Wali Ɗan Masani ya tabbatar
da samuwar rubutattun waƙoƙi a ƙasar Hausa (Auta: 2007:108).
A ƙarni na 18, an ci
gaba da samun Malamai masu yin wallafe-wallafe a waƙe. An samu ayyukan
Muhammad Al-Katsinawi da Muhammad na Birnin Gwari da Malam Shitu ɗan Abdurra’uf wadda
ya rubuta waƙoƙi masu yawa. Daga ciki akwai waƙar Tuba da Wawiya
(Sarɓi 2007:2).
A ƙarni na 19, an sami
ingantaccen tsarin rubuta waƙaƙi da kuma haɓakarsu. A wannan ƙarni ne aka sami
zuwan Shehu Usman Danfodiyo (1804) wanda ya ƙaddamar da jihadi
Sakamakon taɓarɓarewa da kuma gurɓacewar ɗabi’un musulmai a
wancan lokaci. Shehu Usman da tawagarsa sun ƙaddamar da yake-yake
domin kyautata tarbiyar musulmai da ta gurɓata da camfe-camfen waƙoƙin a kan ɓangarorin addini
daban-daban kamar wa’azi da tauhidi da yabon Ubangiji da sauransu (Sarɓi: 2007:3).
A ƙarni na 20 kuwa, an
sami ci gaba da wayewar kai na zamani. An sami hanyar rubutun ajami wadda aka
yi amfani da ita a ƙarni na 19, da kuma hanyar rubutun boko. A wannan ƙarni an sami bunƙasar rubuce-rubucen
waƙoƙi da dalilan rubuta
su suka sami bunƙasa. Bayan jigon addini sai aka rubuta waƙoƙi a kan soyayya da
siyasar jam’iyyu da talla da yabo baduniye da gasa da sauransu.
BAYANIN WASU MUHIMMAN
KALMOMI
Ma’anar Waƙa da Rabe-Rabenta.
Masana sun karkasa waƙoƙin Hausa zuwa gida biyu kamar haka:
i.
Waƙar baka: Ita ce wadda ake rerata da ka, kuma ake adana ta da ka.
ii.
Rubutcciyar waƙa: Waƙa ce da ake rubutata bisa wani tsari na musmaman,
sanan a rereta.
Yahaya (1997) ya bayyana ma’anar waƙa da cewa “Waƙa maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani sako da ke kunshe cikin
wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu”
Mukhtar (2005) ya ce
“Rubutacciyar waƙa wata hanya ce ta gabatar da wani saƙo a cikin ƙayyadaddun kalmomi da aka zaɓa waɗanda ake rerawa a kan kari da ƙafiya a cikin baitoci”.
Sa’id (2002) ya bayyana cewa “Waƙar baka ita ce wadda ake rerawa don jin daɗi, a ajiye ta a ka a kuma yaɗa ta da baka. Rubutacciyar waƙa kuma ita ce wadda aka tsara
aka rubuta ta a takarda don karantawa”.
Dangambo (2007) ya na cewa “Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararryar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙa’idoji da suka shafi daidaita
kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin
sigogi da ba lallai ne hakan su ke a maganar baka ba”.
Sarɓi (2007) ya ce “rubutacciyar waƙa hanya ce ta isarwa ko gabatar
da wani saƙo cikin ƙayyadaddun kuma daidaitattun kalmomi da akan rubuta kuma a rera lokacin
buƙata”.
MA’ANAR DIMOKURAƊIYYA
Skinner (1965) ya bayyana ma’anar dimokuraɗiyya inda ya ce “Dimokuraɗiyya hanyar mulkin ƙasa wadda kowa ke da hannu a cikinta”.
Ƙamusun Hausa (2006:104) ya
bayyan dimokuraɗiyya da cewa “tafarkin mulkin
da mutanen ƙasa ke zaɓar shugabanninsu ta hanyar jefa
ƙuri’a”.
Siyasa wani tsari ne na
tafiyar da mulkin jama’a ta yadda ake ba su damar faɗar ra’ayoyinsu da zaɓen mutanen da zasu wakilcesu, Hassan (2005).
Kamusun Hausa (2006:
397) ya bayyana siyasa da cewar “tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman
ra’ayoyinsu da shawarwari da su”.
TAKAITACCEN TARIHIN SAMUWAR JAM’IYYU
Kafin shigowar ilimin boko Hausawa ba su da tsarin mulkin siyasa, sai dai
tsarin tafiyar da mulki na addini, domin kafin Turawa su zo Hausawa suna da
tsarin mulkinsu na addini kuma suna tafiyar da mulkinsu kan hakan.
Akwai wani littafi na
tsarin gudanar da mulki na Al’magili mai suna Taj al-ɗin Fima Yajibu Ala
Al-muluk a cikin wannan littafi ya yi bayani yadda tsarin mulkin
musulunci yake.
Ilimin boko ya zo ƙasar hausa a (1909) inda a
wannan shekara ya yan musulmai suka fara koyar ilimin boko a makarantar Ɗan Hausa ta farko a Arewa,
Yahaya (2002).
Bayan an sami ilimin
boko aka sami yan boko, tafiya tai tafiya aka sami ‘yan boko suka fara kafa ƙungiyoyin tattaunawa irinsu
Dandalin Tattaunawa (disscussion circle) a Bauchi, sai kuma ƙungiyoyin Al’adun Gargajiya
(Cultural Association) as Sakkwato, saii kuma ƙungiyar Taron Masu Zumunta a Kano, sai ƙungiyar Jam’iyyar Mutanen Arewa
a Zariya, Shafa’u (2010:5).
Daga ranar 25 – 27 ga
watan Dicamba a (1949) a kai gagarumin taron wannan ƙungiya a cikin birnin Kano da
niyyar ta koma jam’iyyar siyasa. A (1950) kuma sai Turawa suka ƙi amincewa da ta zama jam’iyyar
siyasa ta zauna a yadda ta ke sai ta zauna a haka.
Jam’iyyun siyasa sun
fara samuwa a shekara ta (1950) wasu
mtuane su takwas ne suka kafa jam’iyyar ‘NEPU’ a ƙarƙashin jagorancin Malam Abba mai Ƙwaru (Shafa’u 2010:6)
Jam’iyyar NEPU ta tsara manufofinta kamar haka:
1.
Rushe zalunci
2.
Tabbatar da gaskuya
3.
Neman a bawa jama’ar ƙasa abubuwan da ya wajaba su samu
Jam’iyyar NEPU ta yi taron ta na farko a El-Duniya Cinima a (1951) a
Kano, a wannan taron ne aka zabi Alhaji Mudi Spikin ya zama sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, a nan ne ya karanta waƙarsa ta zalunci masu mulki
Sarakuna da Turawa.
A ranar 01/01/1951 ne
aka kafa jam’iyar N.P.C a cikin garin zariya a ƙarƙashin jagorancin muƙaddashinta Alhaji Sanda, sannan kuma sai aka samii manyan ‘yan boko guda
biyu suka shiga cikinta, daga cikinsu akwai alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa da Amadu Raɓe (Sardaunan Sakkwato). Shahararren mawaƙinnan Malam Sa’adu Zungur shi
ne ya faɗawa jam’iyyar NPC suna. (Baban
Zara 2006).
Jam’iyyar NPC wacce aka
kafa ta da goyon bayan Turawa da sarakuna ita ma ta na ta da manufofi kamar
haka:
1.
Girmama sarakuna da sarauta
2.
Jingine siyasa da addini
3.
Duk ‘yan NEPU jahilai ne
Bayan da Nigeriya ta sami ‘yan cin kai a (1960) jam’iyar NPC ita ce ta
kafa gwamnati a Arewa da tarayyar Najeriya, inda sir Abubakar Tafawa Ɓalewa ya zama shugaban ƙasa na farko a mulkin farar
hula, inda Sir, Ahmad Bello ya zama firimiyan Jihar Arewa (B. Hassan, 2006).
JAMHURIYYA TA BIYU
A Jamhuriyya ta biyu (1979- 1983) akwai jam’iyyun siyasa da suka taka
rawar gano. Hukumar zaɓe ta wancen lokacin mai suna (FEDECO)
ta yiwa ƙungiyoyin siyasa guda biyar rigista akwai N.P.U, U.P.N, N.P.P, G.N.P.P.
(Nigeria at 50).
Jam’iyyar N.P.N ita ce ta kafa gwamnatin tarayya da wasu johohi a ƙarƙashin jagorancin Chief M.a
Akinloye, sai jam’iyar P.R.P ta kafa gwamnati a Kano da Kaduna a ƙarƙashin jagorancin Malam Aminu
Kano, har ila yau jam’iyyar PRP itace ce jam’iyyar hamayya a Arewa a tarayya
kuma UPN kuma gyaran jam’iyar NEPU ce, ita kuma UPN gyaran jam’iyyar AD ce,
sannan jam’iyyar NPP, gyauran jam’iyyar NCNC ce.
Da yawa daga cikin mawaƙa da Allah ya raya na Jam’yyar
NEPU da NPC sun canja shekara sun dawo yiwa sababbin jam’iyyu waƙoƙi.
Daga cikin Mawaƙan PRP da suka yi fice akwai
Alhaji Aƙilu Aliyu, sai Abubakar Ladan Zariya, sai Malam Auwalu Isa Bunguɗu, sai Malam Shehu Taura, kowanne ɗaya daga cikin waɗannan mawaƙa yayi waƙoƙi masu daɗi da tarin hikima kuma sun
bayyana manufofin jam’iyyar da alamominta, sannan kuma sun kaɗa shugabancin jam’iyyar da nuna cewa duk waɗanda suka tsaya takarr shugabanci da Malam Aminu
Kano shi ne ya fisu cancanta ya zama shugaba fiye da kowa. (B. Hassan 2006).
GUDUNMAWAR WAƘOƘIN
SIYASA WAJEN SAMAR DA KYAKKYAWAR DEMOKURAƊIYYA A NIJERIYA.
Wannan takarda zata kalli irin gudumawar da marubuta waƙoƙin siyasa ke bayarwa don kawo ingantacciyar siyasa a
ƙasa, saboda
marubuta waƙoƙin siyasa Malamai ne masu hazaƙa da zalaka da fahimta. Su kan rubuta waƙoƙinsu don ilimantar da al’umma ta yadda za su fahimci
irin sakon da suke buƙata su sanar da jama’a domin samun amfanuwa.
Haka kuma marubuta waƙoƙin siyasa su na taka muhimmiyar rawa wajen amfani da
ɓangarori daban-daban ta inda
suke ƙoƙari a cikin waƙoƙin su cusawa al’umma manufofin jam’iyyu ko kuma su nuna wa al’umma
mahimmancin shiga wannan jam’iyyar, sannan kuma su kan cusa adawa ga sauran
jam’iyyum haka nan kuma su kan nasihantar da al’umma a kan jan hankalin mutane
cikin lumana don nuna musu abubuwan daya kamata su aikata da wannan bai kamata
su aikata ba.
1. Nasiha
Misali: Alhaji Mudi
Spikin a waƙarsa mai suna nasiha ga ‘yan siyasa yana cewa:
‘Yan siyasar
gari – gari
Duk ku zo kan batun
shiri
Cikin nasiha da hanƙuri
Inda dai babu tunzuri
Sai batun
masu gaskiya
Wannan baiti ya na fito da lallai ‘yan siyasa su riƙa yin sulhu da juna (saboda
bambancin siyasa) domin kar ya kawo rarrabuwar kai da gaba.
Daga nan kuma, sai ya ƙara yin wata nasihar da cewa,
Allah ya umarci musulmi su zama tsintsiya maɗaurinki daya duk da cewa kowa da ra’ayinsa, amma wannan ba zai hana kawo
zaman lafiya ba. Ga abinda ya ce kamar haka:-
Mai ya sa za
a ƙin shiri
‘yan gari ko da ‘yan
gari
Duk cikin babu ja’iri
Kuma ga faɗar Rabbi Ƙadiri
Muminai duk
su zam ɗaya
Haka nan kuma, a cikin waƙarsa ta nisiha za a fahimci cewa nasiha yake yiwa ‘yan siyasa da su zauna
da juna lafiya tare da bayyana gaskiya a dukkanin al’amurransu. Inda yake cewa:
‘yan uwa
kunga duniya
Duk ciki sai hatsaniya
An ƙi yarda da gaskiya
Ana ta faman hatsaniya
An ƙi gane wa gaskiya
Shi kuwa Auwalu Isa Bunguɗu a waƙarsa ta ‘yan santsi yana cewa:
Domin waƙar nisiha ce
Kuma ka riƙe nafsi ce
Ta zame hujja cikin
zance
Ka tunawa wanda ya mance
In bai yi riƙon nasiha ba
Shaiɗan ma bai biyayya ba
To amma bai ci riba ba
Bai sha daɗin butulci ba
Fahrijminha ka dudduba
Ayar ba za
ta shafe ba
A waɗannan baituka Malam Auwalu Isa
Bungudu yana nasiha da kada ayi butulci, domin ya ƙarfafa batun har ayar Al-Ƙur’ani ya kawo da nuna ƙarshen mai yin butulci.
KAMMALAWA
A wannan takarda, anyi ƙoƙarin bayyana irin gudunmawar da rubutattun waƙoƙin siyasa suke bayarwa don kawo chigaban dimokuraɗiyya a Nijeriya. Takardar ta fito da ɓangarori da ake ganin marubuta waƙoƙin siyasa suna amfani da su wajen cimma manufofin ga
al’umma.
A takaice, takardar ta
gano hanyoyi da marubuta waƙoƙin siyasa suke bi don yaɗa manufar jam’iyyarsu, ko ta hanyar nuna adawa, ko kuma ta hanyar yin
nasiha ga al’umma. Sannan kuma takardar ta fito da misalai na wasu baitoci daga
rubutattun waƙoƙin siyasa mabambanta domin tabbatar da cigaban dimokuraɗiyya a ƙasar Nijeriya. Saboda Marubuta waƙoƙi Malamai ne masu fasaha da hikima da hankali da
tunani sukan ƙulla magana kamar yadda masu sana’ar goro suke ɗaure shi domin siyarwa.
MANAZARTA
Tuntuɓi mai takarda.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.