Ticker

6/recent/ticker-posts

Ci Da Ceto: Turawa Da Adabin Hausa

 Turawa na sane da haɗarin da ke tattare da kutsa kai a cikin baƙuwar al’ummar da ba a da masaniya game da adabinsu, a matsayin wani salon yunƙurin ƙunar baƙin wake ne ga wanda ya yi isgilin wanzar da hakan. Wannan ne ya sa su ƙoƙarin tattaro adabin Hausawa tare da nazarin harshen Hausa, don sanin ciki da wajen al’adun Hausawa. Sun san cewa sanin harshe ne ginshiƙin fahimtar al’adun al’ummar da aka naƙalci harshenta; kuma shi ne sinadarin gudanar da kowace irin hulɗar sadarwa cikin sauƙI a tsakanin al’ummomi mabambantan ra’ayoyi da aƙidoji dakuma al’adu, don cimma manufofin da aka sanya a gaba. Sun kuma san da cewa, adabi madubi ne ko hoton rayuwar al’umma ne da ya ƙunshi  yadda al’adu, da ɗabi’u, da harshe, da halayyar rayuwa, da abinci, da tufafi, da makwanci, da hulɗoɗi, da tunani da ra’ayoyin rayuwar zaman duniya ke gudana. Sun kuma tattara fannonin adabin al’ummar Hausawa don su nazarci ciki da wajen al’ummar, domin samun sararin cimma muradin da suka sanya a gaba. Fahimtar haka ne ya sa maƙalar ta yi ƙoƙari zaƙulo irin rawar da turawa suka taka a fagen raya adabin Hausa da manufofin da ke tattare da aikin tare da irin alfanun da al’ummar Hausawa suka girba daga aikin.

adabi

Ci Da Ceto: Turawa Da Adabin Hausa

Dr. Adamu rabi’u bakura

arbakura62@gmail.com

08064893336

1.0    GABATARWA

Hukumomi da ƙungiyoyi na da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen sarrafa adabin baka ta yadda suka fahimci zai amfani jama’a ta fuskar gudanar da muhimman lamurran da suka fuskanta. Wannan ya sa Turawa ‘yan leƙen asiri da ‘yan mishan da masu fataucin saye da sayarwa da masu neman tabbatar da kafuwar mulkin mallaka suka duƙufa wajen tattara adabin bakan al’ummar da suka ci karo da ita a sassa daban- daban na doron duniya, ciki kuwa har da Hausawa. Sun  yi haka ne a tsare, sun kuma adana  ne domin su sami damar cimma ƙudurorinsu na ƙoƙarin tatse albarkatun ƙasashen al’ummomin da suka kutsa cikin su.

            Turawan da suka zo ƙasar Hausa da kuma manazarta waɗanda da goyon bayansu ne abin  da ake kira adabin zamani ya bayyana a farfajiyar ƙasar Hausa, sun ɗauki adabin ne a kan tafarkin da suka san shi tun suna Turai, wato yana zuwa ne cikin harshen mawallafi. Haka ya sa suka dage wajen daidaita adabin da suka ci karo da shi bisa irin wannan mataki. Abin la’akari shi ne, kafin zuwan Turawa an fara rubuta Hausa, domin ba da Hausar boko aka fara amfani wajen rubutu a ƙasar Hausa ba. Akwai tabbacin cewa ko kafin  ƙarni na 19 an aiwatar da rubuce-rubuce da dama a kan fannoni mabambanta a cikin harshen Larabci da kuma Ajamin Hausa. Irin waɗannan ayyuka sun ƙunshi rubutattun waƙoƙin Hausa ɗauke da jigogin addinin Musulunci da wasu sauran al’amurra. Haka kuma an sami rubutaccen ƙagaggen labari da wasan kwaikwayon Hausa da rubuce-rubucen waƙoƙin baka da tatsuniyoyi da karin magana da sauran su duk a cikin sigar Ajamin Hausa. Abin da za a iya cewa a nan shi ne, Hausar boko ta sami karɓuwa a cikin ƙarni na 20 ɗin ne bayan zuwan Turawan Mulkin Mallaka.

            Wannan takarda ta yi ƙudurin rairaye aya daga tsakuwa don fito da irin rawar da Turawan Mulkin Mallaka suka taka game da adabin Hausa. An kuma ƙoƙarta fito da irin abubuwan da suka kawo su ƙasar Hausa da abubuwan da suka aiwatar da yadda suka sami adabin da irin taimakon da kuma alfanun da suka samu ta wannan fage.                                2.0Adabin Hausa A Zamanin Zuwan Turawa:

Ko da Turawa suka zo ƙasar Hausa, sun sami ƙasar Hausa an gina ta bisa kyakkyawan tsarin shugabanci irin na addinin Musulunci. Ga su da iliminsu na rubutu da karatu a cikin harshen Larabci da wata hanyar rubutu da suke amfani da haruffan Larabci wajen rubuta harshensu, wato ajamin Hausa. An daɗe ana amfani da wannan salon rubutu ta hanyar sadarwa da wajen tafiyar da lamurran mulki da na ilmantarwa. Ke nan al’ummar yankin ba kara zube suke ba. Suna da kyakkyawan tsari da wayewar kai irin nasu (Yahya, 1988:89-90), har ma sun taskace nau’o’in adabin bakansu gwargwadon buƙata, ta hanyar rubuta su cikin sigar rubutun Ajamin Hausa.

Turawa sun sami rubutaccen adabin Hausa a rubuce cikin harshen Larabci da kuma harshen Hausa a sigar rubutun ajami. Hasali ma sun same shi ne ta hannun malamai da almajirai da fatake ‘yan kasuwa da ke yawon fatauci a kusa da kuma nesa da ƙasar Hausa ( Robinson,1896:vii). Wanna ya nuna cewa, ba Turawa ne suka fara koyar da harshen Hausa ba, har ma an sami masana daga cikin Hausawa da suka yi ƙoƙarin koyar da darasin harshen Hausa ga wasu al’ummomi na daban (Baldi, 1977:26).

Akwai ayyuka da dama da ke iya tabbatar da yadda Turawa suka sami adabin Hausa a ƙasar Hausa. Misali, idan aka ɗauki littafin da Charles Henry Robinson  “Hausa Gramma” da aka buga a 1891 bugu na biyar, za a ga cewa tun daga shafi na 133 zuwa 144 ya kawo misalan adabin Hausa a fannin rubutattar waƙa, waƙar da ya yi amfani da ita, ita ce ta “ Murnar cin birnin Alƙalawa” ta Shekh Abdullahin Gwandu. Ya kawo ta a cikin sigar rubutun ajami kamar yadda ya same ta. Fagen rubutacciyar waƙa abu ne wanda aka yi ittifaƙin wanzuwarsa tun kafin ɓirɓishin zuwan Turawa. Har wa yau ya zo da tatsuniya guda ɗaya ta “Mujiya da tsuntsaye” wadda ya same ta a cikin sigar rubutun ajami. Akwai abubuwa masu yawa da aka samu a cikin sigar rubutun ajami da suka danganci adabin  Hausa da ya yi amfani da su cikin littafin, tamkar yadda ya samo su. Irin waɗannan ayyukan sun haɗa da:-

-          Wasiƙar da wani madugu ya rubuta wa Sarkin Zindar

-          Labarin garin shamuwa.

-          Adon maganar Hausa a babi na 15, da karin magana 124.

-          Maganganun hikimomin Hausa guda 16 da kacici- kacici guda 3.

-          Tun daga shafi na 83 zuwa na 89 ya ƙunshi gaishe- gaishen Hausawa, lokutan yini da sunayen ranakun mako da sunayen watanni ( yanayin lokutan shekara na gargajiya ) da sunayen kusurwoyin duniya, da hulɗar saye da sayarwa.

Wannan aiki ya ƙara nuna wa duniya cewa ko da Turawa suka zo ƙasar Hausa sun  sami Hausawa da iliminsu da fasahohinsu gwargwadon buƙata. Ba kara zube suke ba.

Ayyukan da Dokta Prietze ya tattaro da suka ƙunshi labaran Hausa, da wasan kwaikwayon, da waƙoƙin makaɗan baka, da karin magana, waɗanda ya same su  ne a rubuce cikin sigar rubutun ajamin Hausa, shi kuma ya juya su a cikin sigar rubutun Romawa, ya kuma fassara cikin harshen Jamusanci . Daga cikin irin waɗannan ayyuka da aka aiwatar cikin ajamin Hausa tun kafin Turawan mulkin mallaka an same su ne daga hannayen marubutansu ( Ahmed,2001:v- vi).

2.1Mene Ne Adabi?

     Kalmar adabi an samo ta daga kalmar Larabci wadda Larabawa ke kira “Adab”. Hausawa suka yi mata kwaskwarima ta koma “Adabi”. Kalmar Adab ta sami sauye-sauye tun kafin ta zo ga sananniyar ma’anarta ta yau. Ma’anonin da kalmar ta ɗauka sun haɗa da : “ kiran liyafa”. Idan kuma mutum yana da halaye nagari da ɗabi’u masu kyau, akan kira shi “Adibi”. An yi hasashen cewa, daga nan ne Hausawa suka aro Kalmar “ladabi”, domin idan mutun na da halaye da ɗabi’u kyawawa sukan ce, “ wane yana da ladabi”, ( Babikir, 2008:7). Ma’anar ta sauya zuwa ga wata ma’ana har aka rinƙa kiran mutumin da ke da ilimin kowane fanni da suna “ adibi”. A wata ma’anar kuma, sai aka dinga ambaton duk wanda ya iya tsara waƙa cikin hikima da basira, ko tsara maganar azanci ko zube da ke ƙunshe da hikima da basira “ADIBI”.

            A kunnen Larabawa, da zarar an ambaci kalmar “ adab” ba  abin da zai zo musu cikin zuciya, sai wasu zantuttukan fasaha da aka rubuta da ke ƙunshe da nishaɗi ga mai karatu ko mai saurare. Wannan na iya kasancewa a cikin sigar zube ko waƙa. Haka lamarin ya kasance a wajen Turawa da wasu marubutan zamani, kamar yadda ( Webster, 1990:698) da ( Encarta, 2008 ) suka bayyana.

            A wannan takarda, adabi ya haɗa da duk wani fannin ilimi da ya ƙunshi labarai da waƙoƙin baka da rubutattu da wasan kwaikwayo da al’adu da abubuwan fasaha da hikimomin al’umma.

2.2Adabi Na gama gari  

     Kalmar adabi a wannan fage kuwa, tana nufin: “ dukkan labarai, da waƙoƙi da wasanni da ke ƙushe da muhimman abubuwa na fasaha, waɗanda ba kawai sun ta’allaƙa a kan nishaɗantarwa ba. An nuna cewa, littattafai ko wasu abubuwa da aka wallafa game da wasu fannoni duk abubuwa ne na adabi. Wannan ya haɗa littattafan ilimi da ƙasidodin da aka wallafa game da wasu keɓantattun darussa, ( Macmillan, 2007:881).

            A wata makamanciyar ma’ana, an bayyana adabi gama-gari da cewa, duk wani nau’i na rubutu da aka gudanar a cikin sigar zube ko cikin tsarin baitocin waƙa da ke isar da wasu kyawawan saƙonni da ke cikin zuciyar marubucin da ke da alaƙa da dauwamammen tunani ko wasu lamurran da suka shafi duniya baki ɗaya. An ƙara da cewa duk wani aiki da aka rubuta a cikin wani ƙayyadadden harshe, ko da na kowace irin ƙasa ce a kuma cikin kowane irin lokaci aka yi shi, ana kallon sa a matsayin  adabi. Wannan ya haɗa da rubuce-rubucen da aka yi kan wani darasi ko da darasin na kimiyya ne, ana ɗaukarsa a matsayin adabi, ( Webster,1990:698).

            Daga waɗannan ma’anoni za a iya fahimtar cewa, adabi gama gari ya ƙunshi duk wani abu da aka rubuta a kan takarda ko da abin ya jiɓinci addini, ko siyasa ko falsafa ko kimiyya ko wani bincike da ‘yansanda suka gudanar a kan wani lamari da ya shafi al’umma. Don haka, duk wani rahoto da Turawa suka rubuta game da ƙasar Hausa da Hausawa yana daga cikin aikin adabi.

2.3Adabi Na Ilimi

     Idan aka dawo a kan ma’anar adabi ta fuskar ilimi, za a tarar cewa, wasu masana sun ɗauki adabi a matsayin wani fanni da ya ƙunshi waƙoƙi, da huɗubobi, da tarihin al’umma da sarsalarsu da yaƙe–yaƙensu, ( Mustapha, 2000:27). A wajen Ibn Mukaffa’a kuwa, adabi shi ne duk wani rubutu da aka aiwatar, da ke ƙunshe da siyasa da hikimomi da nasihohi da ke tsarkake halayen al’umma. Shi kuwa Abu Tamamu a littafinsa mai suna  DIWANIL HAMASA ya bayyana adabi da cewa , duk wani tsararren abu da ke koyar da kyawawan halaye da ɗabi’u, a cikin sigar waƙa ko zube.

            Bincike ya nuna cewa, tun daga ƙarni na biyu har zuwa ƙarnonan da suka biyo shi, Kalmar Adabi ta ɗauki matsayin nazarin waƙoƙin larabawa da labaransu, har masana sun kasance suna rubuce-rubucen littattafai da wannan ma’ana. Suka kuma kira su da suna littattafan adabi. Misali, littafin Jahiz mai suna: “ AL BAYANU WAT TABYANU”, malamin ya tara waƙoƙi da huɗubobi da labaran Larabawa tare da yin nazari da sharhin ciki da waje.

            Wani masani da ake kira Mubardir ya rubuta littafi mai take: “ KITABUL KAMIL FIL LUGA WAL ADAB”. A cikin littafin  ya kawo jerin waƙoƙi da rubutun zube da aka rubuta da ke ƙunshe da hikimomi da abubuwa masu sa nishaɗi. A nan kalmar adabi ta ɗauki ma’anar bin diddigin zubin  abin da aka rubuta cikin kyakkyawan tsari, wanda ke jan hankalin mai saurare da mai karatu, ya kuma ba su nishaɗi kamar yadda ake samu a cikin rubutun zube na adabin da ya ƙunshi huɗubobi da ƙissoshi da karin maganganu da wasan kwaikwayo da sauran su, ( Ibn Manzur, 2003:100).

            Baya ga masana na sassan duniya, masana na cikin gida ma sun yi bayani game da adabi a tsakanin Hausawa. Gusau (1984:7-9) ya bayyana adabi da sarrafaffen harshen Hausa ne wanda ya ƙunshi hanyoyin rayuwar Hausawa, musamman ta wajen fasaharsu da maganganun hikimominsu da waƙe-waƙensu da kaɗe-kaɗensu da bukukuwansu da wasanninsu da rubuce-rubucensu da halayyar zamansu da sauran abubuwan da suka shafi al’adun rayuwa da fasaha na al’umma.

            Shi kuwa Ɗangambo (1984: 1-4) ya nuna cewa adabi na nufin abubuwan da suka shafi al’adu da rayuwa baki ɗaya da fasaha da dai sauran abubuwan da suka danganci al’umma. A taƙaice, ya nuna cewa, adabi shi ne madubi ko hoton rayuwa na al’umma. Wannan ya haɗa da yadda al’adunsu da harshensu da halayyar rayuwarsu da abincinsu da tufafinsu da makwancinsu da hulɗoɗinsu da tunaninsu da ra’ayoyinsu da sauran abubuwa da suka shafi dabarun zaman duniya don cigaban rayuwa; kai har ma da abubuwan da suka shafi mutuwa.

            Daga waɗannan bayanai za a fahimci cewa, adabi a mahangar ilimi ya ƙunshi duk wani nau’in rubutu da aka yi cikin sigar zube ko tsarin baitocin waƙa da ke isar da wasu kyawawan saƙonnin  da ke cikin zuciyar marubucin da ya zayyana kan takarda , wanda ke da dangantaka da wasu darussa.

3.0Gudunmuwa Ce ko taimakon kai.

        Turawa sun bayar da gudummuwa wajen ɗora adabin Hausa a kan  wata sabuwar turba da ta taimaka masa wajen daidaituwarsa tare da inganta shi ba tare da samun tangarɗa ko kuma salwantarsa baki ɗaya ba. Ta wannan fuskar za a tarar  Turawa daban daban tun daga ‘yan mishan har zuwa ga ‘yan mulkin mallaka, sun bayar da gagarumar gudummuwa wajen ganin adabin baka na Hausa ya ci gaba da rayuwa. Sun sauya masa sabuwar riga da za ta dace da zamanin da aka shiga.

Tambayar da za a iya yi ita ce, shin wannan ya isa gudummuwa? Gudummuwar da Turawa suka bayar ta haɗa da tattara dangogin adabin bakan Hausa, suka taskace waje ɗaya, wanda haka ya hana shi salwanta a sakamakon rasuwar waɗannan da suka mallaki irin waɗannan hikimomin a cikin ƙwaƙwalwarsu. Misali idan aka ɗauki aikin James Frederich Schon, wanda ya yi ƙoƙarin taskace karin magana guda 117 da tarihin rayuwar Dorugu da tafiye-tafiyansa, za a iya cewa ya taimaka. Haka ya taimaka wajen ɗorewar tatsuniyoyin Hausa da suka danganci ɓangarori daban daban, da suka haɗa da  tatsuniya 10 da suka jiɓinci mutane, da guda 9 da suka shafi dabbobi, da guda 7 kuma sun danganci dabbobi da mutane, sai tatsuniya ɗaya da ta shafi mutane da aljannu. Ya kawo almarori guda 23 da tarihihi guda 14 da tarhi 10 da ƙissoshi 4 da waƙoƙi 2 duk ɗauke da fassararsu a cikin Ingilishi. Schon ya yi ƙoƙarin raya kacici-kacici guda 107 da tarin karin magana guda 6407 (Khajah da wasu), a cikin sigar rubutun Hausar boko. Sakamakon wannan aiki, adabin bakan Hausa da ke cikinsa ya kawo wannan lokaci.

            Wani ƙarin misali shi ne, aikin da Dokta Prietze ya tattaro daga hannayen mutane daban- daban da ke zaune a sassan ƙasar Hausa da ma nesa da ƙasar; shi ma gudummuwa ce mai tarin yawa. Ya dai sami ayyukan ne a cikin sigar rubutun ajami. Ayyukan sun ƙunshi dangogin adabin Hausa da suka haɗa da Rubutattun wasan kwaikwayo; wanda ya haɗa da:

 Turbar Ƙudus

Turbar Tarabulus

Tarihin Rabeh

‘Yan Matan Gaya

A ɓangaren labarai kuwa, littafin da aka samu a cikin kundin nasa shi ne : “ ‘Yan Matan Gaya”, kamar yadda ( Ahmad, 2001: i-V ) ya nuna, wanda daga bisani aka mayar da shi cikin sigar wasan Kwaikwayo. Duk waɗannan an same su ne daga hannun wani Bahaushe mai suna Amadu Kano da ke zaune a Tunusiya wanda ya rubuta su da hannunsa cikin ajamin Hausa.

            Haka Prietz ya yi namijin ƙoƙarin raya wasu jerin waƙoƙin baka da ya samu a rubuce cikin ajamin Hausa. Waƙoƙin guda huɗu ne da aka gina su bisa jigon yabo. Biyu daga cikinsu na mawaƙan baka ne, biyu kuwa na gardawa ne:

1-Waƙal Malam Takunta.

2-Waƙal Sarki Tanimu.

3-Waƙar Sarkin Makaɗa Ɗan Madugu da ya yi wa Sarki Tanimu.

4-Waƙar Ƙanen Kada da ya yi wa Sarki Tanimu.

Har ila yau an sami tarin waƙoƙin makaɗan baka da shi Prietze ya juyo daga ajamin Hausa. An gina waɗannan waƙoƙin ne  a kan jigon zambo, kamar waƙar Aku da aka wallafa a 1916, da waƙoƙin Sarkin Noma Gelbu, da ta Kiroro Sarkin Noma, da waƙoƙin Hausa Na Tattalin Arzikin Noma da aka wallafa 1917, da wasu waƙoƙin gardawa guda 4 da aka gina kan jigon yabon kai, waɗanda aka wallafa a 1919. Haka akwai waƙoƙi kimanin 23 da suka shafi al’ummar Hausawa da aka wallafa a 1927. Duk Prietze ya same su ne a rubuce cikin farfajiyar ƙasar Hausa, musamman a yankin Daura da Damagaran, ( Ahmed, 2001Vii).

            A zamanin mulkin mallaka ma an sami wasu Turawa da suka aiwatar da makamancin wannan aiki. Misali, Edgar za a tarar cewa, a littafinsa    “ Tatsuniyoyin Hausa”, ya ƙunshi tatsuniyoyi 162 daga shafi na 1-186. Shafi na 187 – 298 ya ƙunshi labarai 83 da suka jiɓinci ƙasar Hausa da ma sarakunan ƙasar, labaran na nuni ne dangane da yanayin halayyar hoton rayuwar al’ummar ke gudana a ƙasar Hausa, da yadda sarakuna ke yi wa talakawa kisan gilla ba gaira ba dalili. Daga shafi na 298 – 306 an taskace kacici-kacici 166 tare da amsarsu. Yayin da a shafi na 306 -315 ke ɗauke da karin magana 251.

            Idan aka yi la’akari da waɗannan bayanai  za a fahimci cewa, gudummuwar waɗannan Turawa ta haɗa da waɗannan abubuwa:-

·         Sauya wa adabin sabuwar riga, ta hanyar rubuta shi cikin sigar rubutun Romawa.

* Tattarawar da suka yi waje ɗaya, suka adana shi a ingantaccen muhalli, wanda hakan ya kare shi daga salwanta, a sakamakon rashin masanansa ko gobara da makamantan ta. Da ba su yi waɗannan ayyukan ba da tuni sun ɓace.

            Ƙila wata ƙarin tambayar ita ce shin wannan gudummuwa ce ko taimakon kai? Amsar ba za ta kasance ta farat ɗaya ba. Taimakon kai a nan na nufin da wace irin manufar Turawa suka gudanar da irin waɗannan ayyuka game da harshen Hausa da kuma adabin Hausawa? Hausawa dai na cewa ruwa ba ya tsami banza. Dole akwai wani dalili da ya haifar da gudummuwar da Turawa suka bayar. Daga cikin dalilan da ake jin su ne suka haifar da samuwar ayyukan sun haɗa da:-

            Domin ba Turawa (‘yan leƙen asiri da ‘yan mishan da ‘yan kasuwa da ‘yan mulkin mallaka) damar samun wasu takardun bayanai da za su taimaka musu yin nazari tare da koyon harshen Hausa ta yadda za su gudanar hulɗar sadarwa a cikin sauƙi a tsakaninsu da al’ummar Hausawa. Domin hakan zai ba su damar cimma manufofin da suka sa a gaba. Haka kuma suna sane da cewa, kusan al’ummomi da dama da ke nahiyar Afirka suna amfani da Hausa a wajen sadarwa fiye da sauran harsunan da ke nahiyar.

Domin su sami sukunin mallakar ilimin al’ummar Hausawa da yanayin yadda halayyar rayuwa ta kasance a ƙasar Hausa wanda ke tattare a adabin Hausa. Hakan zai agaza musu  wajen fahimtar al’ummomin da tsarin al’adunsu da ɗabi’unsu da yanayin tattalin arzikinsu da yanayin zamantakewarsu baki ɗaya.

            Ta wannan hanya ce suke  zaton za su iya bi su sami galaba wajen ɗauke hankalin al’ummar don samun sukunin cimma manufarsu ta bunƙasa tattalin arzikinsu.

4.0Wa ya ƙaru da wani tsakanin Turawa da Hausawa?

Idan aka yi la’akari da yadda yanayin ƙasar Hausa yake kafin bayyanar Turawa har bayan zuwan su ƙasar Hausa, musamman ta fuskar rashin kyakkywan wajen adana kayan tarihi da taskace su, za a iya cewa Hausawa ne suka ƙaru da Turawa ta wanna haujin. Ko ba komai, Turawa sun ɗauki ɗawainiyar tattaro wasu muhimman bayanai da aka rubuta  waɗanda suka danganci adabin Hausa a cikin sigar rubutun da suka taras a ƙasar Hausa , suka taskace a cikin littattafai da fayel-fayen , suka kuma adana su a ingantaccen wuri don amfanin na baya.

            Sun kuma yi ƙoƙarin aza adabin Hausa a kan sabuwar turbar da ta taimaka wajen daidaituwarsa tare da inganta shi, har ya wanzu a wannan lokaci da aka san shi cikin sigarsa a yau. Sun kuma raya adabin Hausa ta hanyar ba shi wani matsayi da ya kai har aka wayi gari wasu al’ummomin na kusa da na nesa da ƙasar Hausa, na ƙoƙarin gudanar da nazarce-nazarce game da harshen Hausa da kuma adabin.

            Haka yunƙurin da Turawan suka yi wajen tattaro wasu takardun rahotanni da yawa a rubuce na tun zamanin masu jihadi da ke ƙunshe da bayanai da suka kalato daga hannun mutane daban daban, suka haɗa su waje guda aka taskace, ita ma wata fa’ida ce ga Hausawa. Da ba su yi hakan ba,  da tuni rumbun tarihin fasahohin da ilimin hikimomin  Hausawa da al’adunsu na kaka da kakanni sun salwanta daga doron ƙasa, kamar yadda wasu muhimman takardun addininmu waɗanda magabatanmu suka juyo su da hannunsu suka salwanta a sakamakon ta’adin gobara da ambaliyar ruwa. Misali, a Magazawa da ke garin Bakura, ɗimbin irin waɗannan littattafai da zuriyar ta gada tun kafin masu jahadi, sun salwanta a sakamakon gobara da ta’adin ruwan sama da na gobara. Akwai kuma muhimman ayyukan muƙaraban Shehu da suka salwanta a sakamakon ɓarnar ruwa da gobara da rashin ingantaccen wuri taskacewa. Hasali ma duk mafi yawan kayan da ke taskace a gidajen tari, za a tarar na asali sun salwanta a hannayen zuriyar marubutan. Wanzuwarsu ya ƙara kare martabar Hausawa da harshen Hausa tare da nuna wa sauran al’ummomi matsayin ilimi da wayewar kai tun kafin cuɗanyarsu da Bature. Bayyanar irin waɗannan abubuwan a farfajiyar ƙasar Hausa, ya haifar da samuwar hukumomin adabi a ƙasar Hausa, waɗanda har gobe ana more musu.

4.1Tattara adabi, Domin Wa?

     Duk da irin ɗawainiyar da Turawa suka sha wajen tattara adabin Hausa , za a ga cewa, ba sun yi haka ɗin da nufin tallafa wa al’ummar Hausawa ba ne. Sun yi ne domin su gano ire-iren darussan da ke ƙunshe cikin adabin da yadda adabin ke ilmantar da al’ummar Hausawa ta fuskar tsarin ginin nahawun Hausa, ( Schon, 1885:iii-v ). Hasali ma, za a tarar wasu bayanan adabin Hausa suna ƙunshe da darussa da yawa, tun daga gishirin zancen Hausa da salon magana da ilimin hikimar al’ummar Hausawa, da tarihi, da al’adu, da labarin ƙasa. Ta amfani da adabin Turawa sun fahimci al’ummar Hausawa da ke da wannan adabin. Da irin waɗannan abubuwa ne Turawa suka yi amfani wajen fito da asiran rayuwar al’ummar Hausawa.

            Wasu ayyukan ma an yi amfani da su ne wajen koyar da harshen Hausa ga Turawan da ke sha’awar zuwa ƙasashen Hausa daga Turai, don su sami damar gudanar da mu’amala tsakaninsu da Hausawa cikin sauƙi don cimma manufar da aka sa a gaba, ( Edgar, 1911:v-vii).

4.2Sanya a rubuta labarai don me?

       Tun bayan da Turawa suka karɓe mulki daga hannun sarakunan ƙasar Hausa, sun yi ƙoƙarin kawo nasu tsarin ilmi. Don haka sai suka kafa makarantun zamani. Makarantun na buƙatar kayan koyo da koyarwa. Wannan ya jawo aka samar da littattafai domin koyo da koyarwa a makarantun. Duk da haka ba za a rasa wata ɓoyayyar manufa ba, ta ƙoƙarin cusa wa al’umma tunani irin na al’ummomin yammacin ƙasar Turai don ya maye gurbin na ruhin addinin musulunci a cikin zukatan ‘ya’yan Hausawa, ta yadda za a sami damar kai ga manufarsu ta mulkin mallaka. Bisa wannan tunani ne aka samar da ingantaccen harsashen ginin labaran Hausa. An kuma yi ƙoƙarin kafa hukumomi a cikin gida da ƙasashen Turai da aka ɗora wa alhakin kyautata adabi da haɓaka shi. Hukumomin sun haɗa da:-

·         Hukumar Ƙasa da Ƙasa Ta Nazarin Harsuna da Al’adun Afirka.

·         Hukumar Fassara.

·         Hukumar Talifi.

·         Hukumar Yaƙi da Jahilci

·         Kamfanin Gaskiya.

            Bayyanar ire-iren waɗannan hukumomi ya taimaka wajen ci gaba da bunƙasar adabin Hausa ta hanyoyi daban daban. Ta fuskar ƙaddamar da gasar rubutun ƙagaggun labaran Hausa an yi shi ne a kan wasu manufafi da suka haɗa da:-

·         Domin a samar da littattafan da za a yi amfani da su wajen koyar da ɗalibai a makarantun boko da aka buɗa a ƙasar Hausa.

·         Domin a zaɓo malamin makaranta ko ɗan boko mai hazaƙa da za a iya sarrafawa kamar yadda ake buƙata, a koya masa ayyukan wallafa littattafan  da za a yi amfani da su a makarantun Elemantare, ( Pwedden,1995: 88-110).

Kamar yadda bincike ya nuna ne tun daga farko, an samar da hukumomi na adabi a ƙasar Hausa  a sakamakon wasu muhimman buƙatu da suka tusgo bayan an sami yawaitar makarantun boko a ƙasar Hausa. Hakan ya haifar da matsalar ƙarancin kayan koyo da koyarwa, ta fuskar abin karantawa a makar antun. Don haka sai aka samar da hukumar domin ta tallafa wa ‘yan ƙasa su

samar da littattafan ƙagaggun labaru a cikin harshen Hausa, don a yi amfani da su a makarantu wajen koyar da ɗalibai, tare kuma da samar da abubuwan nishaɗantarwa ga al’umma, don a samar da littattafan da za a sayar, waɗanda aka rubuta a cikin harsuna daban-daban da ke faɗin ƙasar Hausa don samun riba.

5.0Kammalawa

            Tabbataccen al’amari ne a ƙasar Hausa, duk wani abu da Turawa suka zo da shi, sai sun  yi amfani da dabaru iri iri wani zubin ma sai an kai ruwa rana, wato sai an nuna ƙarfin mulki kafin su amince da abin da aka ƙaddamar. Wannan ne ya sa a zamanin da Turawa suka zo ƙasar Hausa sun yi matuƙar faɗi tashi wajen  ƙoƙarin kalato adabin Hausa nan da can daga hannun mutane a rubuce cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Wasu kuma daga cikin ayyukan na adabi sun samo su ne ta hanyar shifta suna rubutawa, har suka sami damar tattara ɗimbin hikimomin al’ummar Hausawa daga bakunan waɗanda Allah ya yi wa baiwa da su.

            Sakamakon rashin kulawa da nuna halin ko-oho na akasarin al’ummar ƙasar Hausa wajen tattara adabin Hausa da rubuta shi tun kafin bayyanar Turawan mulkin mallaka, shi ya janyo har ake da’awar cewa, Hausawa ba su da rubutaccen adabin Hausa in aka cire fagen rubutattar waƙa. Wannan ba zai rasa nasaba da irin tasirin da addinin Musulunci  ya yi a cikin zukatan al’ummar ba. Hasali ma dai a daidai lokacin sun fi mayar da hankalinsu wajen ƙoƙarin juya littattafan addanin Musulunci domin su sami damar mallakar nasu kwafi don neman yaye duhun jahilci, da sanin yadda za a bauta wa Mahalicci. Ga alama ƙarancin littattafan addinin Musulunci waɗanda sai mutun ya sami damar juyowa daga hannun wanda ya mallaka, yake samun damar ɗaukar darasinsu a gaban malami, ya janye hankullan almajirai da malaman. Adabin Hausa kuwa, ba abu ne da ake koyo da koyarwa a makarantu ba. An ma ɗauka cewa, abubuwa ne na hululu da mata tsofaffi ke amfani da su wajen kange ƙananan yara da samari daga gararanba cikin dare na ba gaira ba dalili. Ƙunshiyar adabin bai wuce tatsuniyoyi da waƙoƙin baka ba, don haka ba wani babban malamin da zai ɓata lokacinsa wajen rubutun abubuwa na hululu ko tattaro su.

            Turawa sun tattaro tatsuniyoyi da almarori da karin magana da sauran su, sun taskace su cikin littattafai ta hanyar amfani da rubutun  Romawa. Da farko sun samar da littattafan koyo da koyarwa a makarantun da ke faɗin ƙasar Hausa, sai dai irin waɗannan littattafai na ƙunshe da nau’o’in adabin Hausa ne. Daga baya suka shirya littattafan ƙagaggun labarai, sun kuma horar da ‘yan ƙasa dabarun talifi da yadda ake shirya ƙagaggunn labarai da wasan kwaikwayo. Haka sun yi namijin ƙoƙarin samar da hukumomin ilimi da na inganta adabi. Irin waɗannan hukumami har yanzu suna anfanar da al’umma.

            A wannan muƙalar an yi ƙoƙarin bitar irin rawar da Turawa suka taka a ɓangaren adabin Hausa da fa’idar da al’ummar Hausawa suka tsinta, duk kuwa da kasancewar ba an yi hakan ba ne don su, sai don wata manufa ta daban. Sai dai a cikin zuwa da komawa, ba za a rasa wata fa’ida da ke tattare a cikin ayyukan ba. Domin akwai masu ra’ayin cewa, duk wani abu da Turawa suka kawo a ƙasar Hausa, sun zo da shi ne domin wata garaɓasa da suke hangen za su girba a cikin lamarin. Muradina a nan bai wuce, wannan muƙala ta zama matashiya game da wasu sassa da ban taɓo ba.

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments