Ticker

6/recent/ticker-posts

Hoton Shugaba Na Gari A Rubutattun Woƙoƙin Siyasa, Ta Jamhuriya Ta Huɗu: Nazarin Rubutattun Waƙoƙin Siyasar Zamani

 Kowace al’umma tana alfahari da samun ‘ya’ya na gari da za a yi bugun gaba da su. Kyakkyawar tarbiya ita ce sinadarin kafa shugabanni na gari masu gaskiya da amana da kuma haƙuri wajen tafiyar da shugabancin da aka ɗora masu. Haka kuma, a sami cikakken jagoranci cikin adalci da kwanciyar hankali. Tarbiya ta gari ita ce wadda iyaye na gari a cikin al’umma suke bayarwa ga ‘ya’yansu har su zama abin so a kowane lokaci suka sami kansu cikin al’ummar da ba tasu ba. Marubuta waƙoƙin siyasa suna ƙoƙarin tallata irin waɗannan mutane da suke da kyakkyawar tarbiya domin su nuna su a idon duniya har su sami karɓuwa, a kuma zaɓe su su jagoranci jama’a a muƙamai daban-daban na gwamnati. Zaɓen shugabanni masu tarbiya ta gari wani mataki ne ko gimshiƙin samar da shugabanni na gari a mulkin dimokuraɗiyya. Wannan takarda za ta yi nazarin halaye da ɗabi’u na gari da marubuta waƙoƙin siyasa ke kallo a cikin waƙoƙinsu suna faɗakar da al’umma mahimmancin zaɓen masu kyakyawar tarbiya domin a samu zaman lafiya da tsaro da cigaban tattalin arzikin ƙasa. Kauce wa zaɓen mutane masu tarbiya ta gari kan zama musabbabin taɓarɓarewar mulkin dimokuraɗiyya har a wayi gari a cikin mulkin zalunci da yawaitar ayyukan ta’addanci irin su fashi da makami, sara suka, bangar siyasa, sace-sacen dukiyoyi n al’umma, satar mutane a na garkuwa da su da cin hanci da rashawa, dukkansu ayukkan ne na rashin tarbiya da akan samu cikin al’umma. Waɗannan ayyukan rashin ɗa’a sukan zama tushen rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki wanda ke jefa ƙasa cikin halin masu gudu su gudu. Kyakkyawar tarbiya itace nuna halaye na gari, da kunya da kawaici da dangana waɗanda suke zama ginshiƙin kafa mulkin adalci a mulkin dimokuraɗiyya.

shugabanci

Hoton Shugaba Na Gari A Rubutattun Woƙoƙin Siyasa, Ta Jamhuriya Ta Huɗu: Nazarin Rubutattun Waƙoƙin Siyasar Zamani

 

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

GSM NO. 07032567689

E-mail: aliyurabiu83@gmail.cim

1.0       GABATARWA

Mutane ku taho ina buƙatar ku fahimta,

Ga Waƙata wadda za ni yi don mu riƙeta,

Ta gina mutanen da anka san sun cimcimta,

Su zo, su yi mulkin ƙasa a samo daidaita,

Da kwantarwar hankali a samu a yi aiki,

(Sambo Wali Sokotom Waƙar Muhimmancin mai da mulki hannun farar hula, 1997)

 

Sau da yawa akan zargi shugabanni da cewa su ne mafarin taɓarɓarewar tattalin arikin ƙasa, da rashin tsaro da duk wani halin rashin zaman lafiya da al’ummar da suke shugabanta kan sami kansu a ciki. Al’adar Bahaushe wata abu ce mai muhimmancin gaske musamman wajen zaƙulo da kuma tantance halaye da ɗabi’un ‘ya’yansu tun suna ƙanana har zuwa lokacin da suka isa su zama shugabanni. Al’adar koyar da tarbiya ga Bahaushe aba ce mai dogon tarihi tun kafin zuwan ilimin addinin musulunci da boko. Kyawawan halaye da ɗabi’u da Bahaushe ke koyar da ‘ya’yansa ba ƙaramin tasiri suke da shi ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda shugabanci yake a masarautun ƙasar Hausa. Halaye da ɗabi’u da Bahaushe ke koyar da ‘ya’yansa irinsu riƙon amana, da dogaro da kai da dangana da haƙuri da kuma juriya a lokacin da ake renon su. Dangane da haka ne mawaƙan siyasa na Hausa suke ɗora alƙalami a kan takarda su tsara tare da rera waƙa mai faɗakar da jama’a muhimmancin zaɓen mutane masu kyakkyawar tarbiya, wanda shi ne zai kai ƙasa ga samun cikakken tsaro da zaman lafiya da cigaban tattalin arzikinta.

 

Tarbiya ta gari daga sama take farowa, wato sai an sami manya na gari sannan a sami yara na gari.

 

2.0       MA’ANAR TARBIYA  

Kyawawan ɗabi’u da halaye na gari su ne abubuwan da masana suke cewa tarbiya. Kyakyawar tarbiya ta ƙunshi waɗannan halaye kamar Dangana, Haƙuri, Kunya, Riƙon Amana da sauransu. Kano (1982:6) ya bayyana tarbiya da cewa, kirki, wato girmama iyaye da yi wa na gaba gare su ɗa’a, ita ce tarbiya. Tarbiya ta fara daga magabata, wato iyaye waɗanda haƙƙin renon ‘ya’ya ya rataya a wuyansu. Akan kula da ba da umurni da hani ga ƙananan yara ta hanyar gabatar da labarai da tatsuniyoyi a al’adance kafin zuwan ilimin addini da na zamani a ƙasar Hausa. Wato da zarar yaro ya fara wayo sai salon reno ya sanya, iyaye da kakanni su riƙa tara ‘ya’yansu suna tarbiyantar da su yadda za su zauna da mutane masu kirki da biyayya ga al’ummar da suka tashi cikinta, da kuma wadda za su yi hulɗa da ita. Kafin zuwan addinin musulunci da boko iyaye na biyar hanyoyin gargajiya musamman tatsuniya da tarihi da karin magana suna koyar da yayansu dubarun zaman duniya. Da addini musulunci ya zo ƙasar Hausa, Hausawa suka karɓi addini kuma suka cigaba da koyar da ‘ya’yansu karatu da rubutu, da sana’a, da mu’amala da girmama na gaba kamar yadda addini ya tanada. Wannan kuwa ba domin komai ba, sai don ka da ‘ya’yansu su tashi a watse su zama abin ƙyama ga al’umma da kuma abin kunya da dariya a cikin jama’a.

 

Murad (1999:18-19) cewa ya yi, iyaye ke da haƙƙin tarbiyantar da ‘ya’yansu aƙidar bautar Mahalicci da koyar da su kyawawan ɗabi’u har sai sun kai munzalin sanin ciwon kansu. Wato su koyar da ‘ya’ya girmama Mahalicci da kuma mahaifansu, da yi masu hidima. Haka kuma, su koyar da su kyakkyawar ma’amala da wasu mutane da ‘yan uwansu na jini da na addini. (Alkur’ani Suratul Isra’i: 23 - 24).

 

Gurin kowaɗanne iyaye shi ne su ga cewa ‘ya’yansu sun zama na kirki har su zama manyan shugabannin al’umma. Don haka wajibi ne su hori ‘ya’yansu da su ƙaurace wa hulɗa da miyagun abokai da ba su da kyakkyawar tarbiya tun daga iyayensu.

 

Bakura da Aliya (2013:357), sun bayyana tarbiya da cewa kyawawan ɗabi’u da halaye na gari ne, wato tarbiya ita ce hanyar kyautata rayuwar ɗan Adam da shiryar da shi bisa ga halaye da ɗabi’u masu kyau da nagarta. Duk al’ummar da ke da kyakkyawar tarbiya babu shakka za ta zama mai kima da kwarjini da ganin mutuncin abokan zama, kuma ta riƙa ba kowa haƙinsa kamar yadda ya kamata.

 

Kyakkyawar tarbiya ita ce ginshiƙin da ake ɗora gini ko kange shi daga tuɗewa watau samun baya mai nagarta da za ta iya jagoranci na gari, wanda ke haifar da samuwar tabbacen zaman lafiya da tsaro da bunƙasa arzikin ƙasa. Shugabannin na gari su ne jagororin jama’a masu riƙon amana da haƙuri da gaskiya da Dattako da kuma baiwa abun duniya bayam. Malam Umar Kwaren Gwamba yana jan hankalin ‘yan siyasa da su sa ido su zaɓi mutum mai kirki wanda zai kai ƙasa ga cigaba da kuma kyautata rayuwar al’ummarta. Yana cewa:

“Ku zaɓi ɗan ƙwarai mai kirki guda ku tsai da shi,

Wanda ya fito don su kara sai ku mai da shi

Gami da ba shi amsar cewa ɗangida ne shi,

Yanzu in guda daga cikinku anka kada shi,

Za mu samu cikas jam’iyyarmu ya hulla.

(Umar Kwaren Gamba, waƙar maida mulki ga hannun farar hula 1997)

 

Tun da demokuraɗiyya wani salon mulki ne da ke buƙatar mutane su zaɓi mutane na kirki wajen jagorancinsu domin su sami damar walwala da faɗar albarkacin bakinsu, don haka mutumin kirki shi ne wanda masana daban daban suka bayyana shi kamar haka:

 

2.1 MUTUMIN KIRKI

Kirki na nufin kyawon ɗabi’a da halaye na gari waɗanda suka haɗa da biyayya ga iyaye da manya na gaba gare ka da haƙuri da kunya da sauransu. Daga cikin kyakkyawar tarbiya da Bahaushe yake da ita, kuma yake tunanen yi wa ‘ya’yansa tarbiya ta gari domin su zama abin so a cikin al’umma. Kirkgreene (1973), ya bayyana mutumin kirki da cewa shi ne wanda halayensa da ɗabi’unsa suka ƙunshi gaskiya, amana, karamci, haƙuri, hankali, kunya, mutunci da hikima da kuma adalci. Mutumin kirki shi ne mai kyawon ɗabi’u ko hali, wanda ba ya ƙarya idan ya yi magana, ba a jin zancen banza ko batsa a bakinsa, ba ya ashararanci ko mugun baki. Ba ya yi wa mutane shaƙiyanci, wato yana girmama mutane, ba ya zunɗe da ƙifce. Haka kuma ba ya ruba da fankama ko girman kai da sauransu. Koyaushe mutumin kirki yana kiyaye dokokin Allah tare da girmama na gaba da shi a shekaru da sadar da zumunci, da sauraro sau biyu kafin ya yi magana sau ɗaya. Kano (1982), ya ƙara da cewa mutumin kirki shi ne mai riƙe amana da tausayin gajiyayyu da alhairi ga yara, mata da tsofaffi, da rashin haɗama, wato son kai. Haka kuma ba ya zalunci ta kowane fanni. Ana ta’allaƙa mutumin kirki da son ƙasarsa, don haka ba za a haɗa kai da shi ba, a cuci ƙasarsa. Duk mutumin da ke da irin waɗannan ɗabi’u da halaye shi ne mutumin kirki kamar yadda Habib Alhassan da wasu (1982) suka siffanta mutumin kirki da kyakkyawar ma’amala da ladabi da biyayya. Haka kuma, ga son zumunta da kunya da kara. Ga kuma riƙon amana da addini da gaskiya da dattako da adalci da kuma kawaici, da rashin tsegumi da dogaro da kai da juriya da kuma jaruntaka.

 

Aliya (2013) ta bayyana mutumin kirki shi ne wanda ɗabi’unsa da halayensa suka dace da tarbiya da reno na al’ummar Hausawa da suke bai wa ‘ya’yansu domin shiryar da su bisa ga halaye masu kyau da nagarta. Duk mutumin da yake da irin waɗannan halaye da ɗabi’u shi ne mutumin kirki wanda marubuta waƙoƙin siyasa ke duƙufa ka-in-da-na-in wajen tallata shi ga jama’a domin su amince da shi. Misali Garba (Gwandu), a cikin waƙarsa ta mai da mulki a hannun farar hula a 1997, yana faɗakar da jama’a inda yake cewa.

                        Kowane ɗan siyasan ƙwarai mi an nufin shi,

Shi yoma ƙasarsu aiki da kowa zai yaba shi

Ba shi da hura hanci da hwaɗi ta naɗa shi

Mai dogon kwaɗai shi ka hanƙure amshi ta shi,

Mai rowa da ɗai ba shi murnar mai matsewa

(Garba Gwandu)

 

Sha’irin ya fito fili ƙarara ya bayyana wasu ɗabi’u da halaye na rashin tarbiya da mutumin kirki ba za ya zama yana nuna su a bayyane ba, balle har ya zama shugaba na gari ba. Ya bayyana cewa, hura hanci, wato ji da kai, da yin hwaɗi da kwaɗayi wasu ɗabi’u ne na rashin tarbiya.  

 

Waɗannan ɗabi’u wato hura hanci da girman kai da kwaɗai kalmomi ne da ke nuna rashin tarbiya da matsayin mutum maras kirki. Rashin tarbiya ita ke haifar da rashin adalci da riƙon amana da satar dukiyar al’umma, idan aka zaɓi mutum maras kirki a mulkin dimokuraɗiyya. Kuma a same shi da rashin haƙuri da kwaɗayin tara dukiyar da ba ta halas ba. Garba Gwandu na cewa:

 

Duk mai son a zaɓai shi fara cakin na kainai,

Mi yaw wa mutane da yas sa za su zaɓai,

Tare nai da fatan da yay yi suna rufa mai,

Sauran masu zaɓe suna shawar tsayi nai,

Amsa wagga ita za ta nuna mai tsayawa.

                        (Garba Gwandu, Waƙar Maida mulki ga hannun farar hula 1997)

 

Wato mutum mai kirki in ji shi, shi ne wanda tarbiyarsa ta dace da ya zama shugaban al’umma ta hanyar taimakon da yake yi wa jama’a. Sai dai in ji mawaƙin shi wannan mutum ya dace ya binciki kansa idan ya kasance mai tausayi ne da kuma taimakon jama’a kafin ya tsaya takarar kowane muƙami na siyasa, Saboda haka tausayi da taimako wasu halaye ne na tarbiya da ake sa ran shugaba na gari ya kasance yana da su, sannan a zaɓe shi a matsayin da yake takara. Don haka ga al’adar Bahaushe ana buƙatar mutum ya tabbatar da cewa shi mutum ne na kirki kafin har ya nemi wata buƙata ga jama’a. Wato mutum ya binciki irin kyakkyawar alaƙarsa da mutane da kuma irin taimakon da yake bai wa jama’a ta kowane hali. Idan halayensa da ɗabi’unsa sun tabbata bisa ga tarbiyar da Bahaushe ya aminta da ita, to shi zai tabbatar da tsayawarsa takara har ya sami nasarar karɓuwa ga jama’a su zaɓe shi, inji garba Gwandu.

“Mai son takara kowane na ba ba’a ba,

In dai takara zai yi don a kire shi babba,

A tabbata takaran nashi bai zama twakarar ba,

Hulɗatai da sauran mutane ba na ƙi ba,

Shi zo shi yi takara don zaton shi zai hayewa”

(Garba Gwandu)

 

2.2 KISHIN ƘASA

Kalmar “kishin ƙasa” kalma ce da ke ɗauke da kalmomi biyu masu banbancin ma’ana suka haɗe suka ba da kalma mai ma’ana ɗaya. Wato “kishi” da “ƙasa”. Masana suna ganin cewa kishi kalma ce da ke nuna gwagwarmaya wajen ayukkan dogaro da kai da wani zai yi lokacin da yaga wani ya yi wani abu na cigaba. Idan aka ɗauki wannan ma’ana a iya cewa kishi ya na nufin tserereniya, yi in yi ba a bini ba game da wani alkhairi da wani ya samu na cigaba, (Bakura (2014), Bergery (1934) sun bayyana kishi da cewa shi ne ganin ƙyashi da ke tsakanin kishiyoyi. Ita kuma ƙasa tana nufin muhalli ko bagire da wata halitta ke gudanar da rayuwarta. Thesaurus (Kamusna Turanci), an bayana ƙasa da cewa al’umma da ke zaune a muhalli ɗaya bisa ga wani tsarin rayuwa da al’adu na bai ɗaya a tsakaninsu, ko tarihi ko kuma al’umma da suka haɗu a ƙarkashin hukuma ɗaya suna gudanar da rayuwarsu.

 

To idan aka haɗa kishi da ƙasa bisa ga bayanan da suka gabata, sai a fahimta da cewa kishin ƙasa yana nufin gwagwarmaya da tserereniyar neman ma kai wani matsayi na ɗaukaka ko bunƙasar tattalin arziki fiye da wata ƙasa. Wannan zai ba mu ma’anar cewa kishin ƙasa shi ne damuwa da ci gaban al’umma ta fuskar abubuwa daban-daban na raya ƙasa. Misali Malam Sambo Waliyi yana siffanta ɗan ƙasa na gari da cewa zaɓen shi ya waƙilci jama’a shi zai samar da cigaban ƙasa ta fuskar bunƙasa tattalin arziki da ilimi da sauran harkokin rayuwa. Malamin yana cewa:

Muhimmancin ɗan ƙasa idan an zaɓe ka,

Ka zauna, ka yi tuntunin shirin gina ƙasar ka

Ka yo aiki wanda ‘yan uwa zasu yabon ka

Kai kassa kanka, in tunama uzurinka

Bawan yarda ga zuciya ba shi da surki.

(Sambo Wali, Waƙar muhimmancin mai da mulki hannun farar hula, 1997)

 

Kishin ƙasa al’ada ce da ta keɓanta ga ɗan Adam wadda ke tabbatar da zaman mutum mai hankali da ya bambanta da dabba. Wato hankali da tunani shi zai tabbatar da kasancewar ɗan Adam ya zama mai kishin farfaɗo da matsayin al’ummarsa fiye da sauran al’ummomi na duniya. A taƙaice wannan shi ne kishin ƙasa. Don haka yin biyayya ga dokoki da shirye-shiryen gwamnati wata “tarbiya ce da ke tabbatar da cikakken kishin ƙasa da sadaukar da kai wajen bunƙasa cigaban ƙasa ga kowane mutum mai kirki. Misali Shu’aibu Yar Medi yana cewa a cikin waƙarsa ta PDP kamar haka:

In Ɗa na da kunya shi da uwa ba za su saɓa ba

Ko sanda ta sa ta buge shi ba zai juyo ya rama ba

Mai ƙaunar ƙasa ba zai shiga layin ‘yan tazarce ba

Ko sun ce taho zai ce a a don kar a ɓata ƙasata

(Shu’aibu Yar Medi, Waƙar PDP 1998).

 

Haka kuma, dangane da kishin ƙasa, Shu’aibu ‘Yar Medi ya ƙara da cewa:

Kyakkyawar Aƙidar Cigaba ba mulkin riƙau ne ba

‘yan cin al’umma talakawa mu ba za mu manta ba

Tilas zamu karɓa har abada ba zamu kyale ba

Sai mun kai ga alkhairin da muke nema mazan mu da mata

Aminu Ibrahim Ɗandago a cikin waƙar sa ta APP ya na nuna irin alkhairin da kishin ƙasa yake kawowa a lokacin mulkin demokuraɗiyya. Malamin yana cewa:

APP na shirin ƙasa talaka yasan hali

Ya sami sukuni ya ɗebi daularsa da cokali

Ba mai dubansa ko gida ko ko a dandali

Yai masa kallon maras kwabo ko maras hankali

Daidai da ƙasarmu jam’iyyar ‘yan Nijeriya

(Aminu Ibrahim Ɗandago)

 

Saboda haka duk ɗan ƙasa na gari mai kishin ƙasa ya wajaba ya san cewa babban aikin da ke gabansa shi ne ya fito da hanyoyin cigaban ƙasarsa da iyalansa don samun walwala da kwanciyar hankali ga al’ummar ƙasarsa baki ɗaya. Mutumin da ya kasance haka to shi ne ɗan kishin ƙasa na gari (Ibrahim 2004).

 

Bisa ga wannan aƙida ta tarbiyar kishin ƙasa, marubuta waƙoƙin siyasa suke ɗora alkalami kan takarda su zayyana manufofinsu zuwa ga jama’a da nufin tallata ɗan takara na jam’iyyarsu a idon duniya. Haka kuma su yi kira ko faɗakar da mutane alfanun zaɓen mutum mai aƙidar kishin ƙasa ya shugabance su a lokacin mulkin dimokuraɗiyya. Wannan faɗakarwa tana taimakawa wajen zaɓen shugabanni na gari domin samun ɗorewar zaman lafiya da tsaro da cigaban arzikin ƙasa. Wanda shi ne aka sa a gaba, ba wai tarwatsa ƙasa da handame dukiyar jama’a ba. Malam Umar Kwaren Gamba Sakkwato ya yi gargaɗi ga “yan siyasa inda yake cewa:

 

“Kun ga ‘yan kwaɗan su yi mulki su cuci danginsu,

Irin su ɗan kuregen dutsi kar ku tsai da su,

Masu tattalin sui mulki don ƙashin kansu

Nufin su kai su hau mulki don cimma gurinsu,

Irin su kar ku tsai da su ga mulkin farar hula.  

(Umar Kwaren Gamba, Waƙar mai da mulki hannun farar hula 1997)

 

Mutane marasa kishin ƙasa koyaushe gurinsu shi ne su hau mulki ba don su ciyar da ƙasa gaba ba, a a sai dai don su tara dukiya su riƙa jin daɗi daga su sai iyalansu. Wato kamar yadda mawaƙin ya faɗa cewa gurin waɗannan mutane shi ne su handame dukiyar ƙasa su ɓoye a ƙasashen ƙetare saboda rashin kishin ƙasa. Ya ƙara jaddada niyarsa ta faɗakar da al’umma dangane da zaɓen irin wadannan mutane da ba su da tarbiya ta kishin ƙasa cewa kuskure ne a zaɓe su su shugabanci al’umma. Yana cewa.

“Akwai su ɓera sarkin sata kar ku tsaida shi,

Duk abin da an na hukuma za su kwashe shi,

Buja-buja da babbar riga ka gan shi koyaushi,

Duk abin da an na hukuma muka ikonshi,

Wanga kar ku ba shi muƙami cikin farar hula.

(Umar Kwaren Gamba)

 

Yin sama da faɗi ko handame dukiyar ƙasa suna daga cikin ayyukan rashin kishin ƙasa. Duk wani ɗan siyasa ko shugaba da ba shi da tarbiya da aƙidar kishin ƙasarsa bai dace da a ba shi amanar shugabanci ba a mulkin dimokuraɗiyya. Domin koyaushe ba shi da wani guri face na satar kuɗin al’umma ya gina kansa, al-Bashi sauran mutanen ƙasa su shiga wani halin la’ila ha ula’i. Irin wannan mutum ba ya cikin mutanen da ke da kyakkyawar tarbiya da ya dace ya zama shugaba na al’umma.

 

 

2.3 SHUGABANCI NA GARI

Shugabanci shi ne jagoranci na mutane da Allah yake zaɓar wasu ɗaiɗaiku daga cikin al’umma ya basu jagorancin mutanen da suke tare da su domin a samu rayuwa ta tafi bisa gat sari na adalci. Wato shugabanci yana nufin kula da tafiyar da al’amurran jama’a ko wasu rukuni na jama’a dangane da rayuwar yau da kullum, wannan bayani ya nuna cewa shugabanci abu ne da Allah yake zaɓen wani ya ba shi mulki lokacin da yake so ga wanda ya so kamar yadda ya fito a cikin Alƙur’ani mai tsarki, inda Allah yake cewa “Ka ce Ya Allah Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda kake so, Kana zare mulki daga wanda kake so, kuma kana buwayar da wanda kake so, kuma kana ƙasƙantar da wanda kake so, ga hannunKa alkhairi yake. Lallai ne kai a kan kowane abu, mai ikon yi ne. (Ƙ3:26).

 

Kamusun Hausa (2006: 415) ya bayyana kalmar shugabanci da cewa tana nufin jan ragamar jama’a ko wata ƙungiya, wato daidai da jagoranci. Al’adance a ƙasar Hausa, akwai rukuna daban-daban na shuabanci. Akwai shugabanci na mulki waɗanda kan haɗa da sarakuna, da hakimai, da dagatai, da masu unguwanni. Waɗannan su ne ke riƙe da ragamar jagorancin al’ummar da suke a ƙarƙashin gundumominsu ko yankinsu. Su ne ke da wuƙa da nama ga dukkan lamurra na mulki da suka shafi yankunansu.

 

Haka kuma, akwai shugabanni waɗanda ba na mulki ba, aikinsu shi ne jagorancin wani sashe na al’umma kawai suke yi, amma ba su da wuƙa da nama wajen abin da ya shafi dukkanin al’umma. Misali jagorori da shugabanni na kungiyoyi da sana’o’i da ake aiwatarwa a cikin al’umma. Haka shugabanni na siyasa suna cikin rukunin shugabannin mulki wanda siyasa ta zo da shi. Saboda haka ne mawaƙan Hausa suke baje hajar tunanensu wajen rubutawa da rera waƙoƙi domin su faɗakar da mutane da ‘yan siyasa mahimmancin zaɓen mutane masu mutunci da taimakon al’umma kamar yadda tarbiyar Hausawa ta nuna ta kuma yarda da shi. Shugaba mai rikon amana da kula da ba da haƙƙi ga kowane ɗan ƙasa ba tare da nuna bambancin addini ko kaɓilanci da bambancin jam’iya ba, shi ne cikakken shugaba na gari mai adalci. Shugaba adili shi ne wanda ba ya satar dukiyar al’umma, da nuna banbancin addini ko kabilanci ba. Rashin tarbiya ta riƙon amana ita ce ke haddasa mulkin zalunci da rashin tausayi ga waɗanda suke ƙarƙashin mulkinsa. Saboda haka idan ana son a kauce wa mulkin zalunci a kafa mulkin adalci da samun shugabanni na gari to dole ne a zaɓi mutane masu tarbiya ta gari da aƙidar ciyar da ƙasa gaba. Malam Shu’aibu Yar Medi ya faɗakar da jama’a dangane da haka, inda yake cewa:

Kyakkyawar aƙidar cigaba ba mulkin riƙau ne ba

‘Yancin al’umma talakawa mu ba za mu manta ba

Tilas za mu karɓa har abada ba za mu ƙyale ba.

Sai mun kai ga alherin da muke nema mazanmu da mata.

(Sha’aibu Yar Medi)

 


 

KAMMALAWA

Tarbiya ginshiƙin samar da shugabanni na gari. Wannan takarda ta yi nazarin irin alfanu da tarbiya take da shi ga samar da jagorori na gari a kowane mataki na shugabanci. Hausawa sun ce tarbiya daga gida takan somawa, don haka ne ya sa marubuta waƙoƙin Hausa musamman na siyasa sukan yi la’akari da mutane masu kyakkyawar tarbiya su riƙa garzaya su da kuma tallata su domin su sami karɓuwa a idon jama’a. Mulkin siyasa mulki ne da ke buƙatar mutane masu kirki waɗanda za su riƙe amanar talakawa da kuma bai wa kowa haƙƙinsa. Da wannan ne mawaƙa suke tsara waƙoƙinsu a rubuce suna yi wa jama’a nuni da kuma hannun-ka-mai-sanda ga zaɓen shugabanni masu aƙida ta ƙwarai waɗanda ba za su zalunci al’umma ba idan su riƙi ragamar mulki. Dalilin haka ya sa Garba Gwandu, yana faɗakarwa ga ‘yan siyasa, cewa:

            Dum mai son a tsai sai ga fate kowane na,

            Faten nashi su za su san mai martaba na,

            Mun tsai sai ku zaɓai, faɗar wannan kure na,

            Son ran shugabanni cikin fate dahi na,

            Shi ka hana ma ɗan takararsu wucewa. 

            (Garba Gwandu, Waƙar muhimmancin maida mulki hannun farar hula 1997)

 

MANAZARTA

 

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments