Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsattsafin Adabin Zamani A Farfajiyar Ƙasar Hausa Kafin Zuwan Turawa

 A wata ƙwarya-ƙwaryar ma’ana da Yahaya da wasu (1992) suka bayar, sun bayyana cewa, rubutaccen adabi shi ne wanda  ake kira da adabin zamani. Wannan shi ne adabin da masu ilmi suka rubuta a littattafai don jama’a su karanta, su kuma amfana. Irin waɗannan rubutattun littattafan adabi ana yin nazarinsu a makarantu.

adabin zamani

Tsattsafin Adabin Zamani A  Farfajiyar Ƙasar Hausa Kafin Zuwan Turawa

Dr. Adamu rabi’u bakura

arbakura62@gmail.com

08064893336

1.0 Gabatarwa

            Kowace al’umma da ke sararin duniyar nan, ba za ta rasa adabin baka nata na kanta ba, komai rashin wayewar kanta. Irin wannan adabi kan kasance ta fuskar tarihi da labarai da kacici-kacici da Karin magana da habaici da zaurance da sauran su. Idan har al’ummar ta yi gamon katar ta ci gaba, ta hanyar samun damar mallakar fasahar karatu da rubutu, akan samu wasu ɗaiɗaikun mutane daga cikin  al’ummar da kan yi ƙoƙarin taskace dangogin adabin al’ummar a rubuce, domin na baya su riske shi. Daga wannan lokacin, adabin ya tashi daga na baka ya koma rubutaccen adabi ke nan. Wannan kan faru ne a sakamakon hikimar da Allah ya yi musu, ko ta hanyar cuɗanya da wata al’umma ta daban. Sau da yawa adabin baka kan inganta sigar rubutaccen adabi. Hasali ma da shi ne  akan aza harsashen ginin adabin zamani, wato rubutaccen adabi.

            Al’umma na da muhimmiyar rawa da take takawa wajen taskace adabin bakanta ta yadda ta fahimci zai amfani jama’a, musamman wajen gudanar da lamurran yau da kullum. A fafutukar cim ma wannan ƙuduri ne, aka sami wasu daga cikin Hausawa da suka zayyana adabin nasu na baka a kan takarda. Hakan ya sauya masa matsayi ya zama adabin zamani (rubutaccen adabi) na Hausa tun kafin bayyanar Turawan mulkin mallaka a ƙasar Hausa. Hausawa kan ce, “Da rashin kira Karen bebe ya ɓata”. Saboda haka ne wannan maƙala ta ƙuduri aniyar zaƙulo wasu ayyukan adabin Hausa da Hausawa suka rubuta a cikin sigar rubutun ajamin Hausa tun kafin zuwan Turawa. Irin waɗannan ayyukan Turawa ne suka samo su daga hannayen marubutansu na asali, wasu kuma an same su ne daga magadansu. Yayin da Turawan suka taskace su a cikin sifarsu ta asali aka kuma adana a ɗakunan ajiye kayan tarihi. Irin waɗannan takardu sun ƙara fito da martabar Hausawa da harshensu. Kuma sun nuna wa duniya zurfin ilimi da hikimomin al’ummar Hausawa. Hakan ya tabbatar da wayewar kan Hausawa ta kowace fuska tun kafin zuwan Turawa ƙasar Hausa. Sai dai kafin a tsunduma cikin wannan fage, zan ɗan waiwaya a kan ma’anonin tubalan ginin wannan takarda. Wato ma’anar kalmar “tsattsafi” da kuma “adabin zamani” sannan daga bisani a zo da bayanai game malaman farko na harshen Hausa da hujjojin da ke tabbatar da samuwar adabin zamani a farfajiyar ƙasar Hausa kafin mulkin mallakar, waɗanda suka haɗa da rubutattun wasan kwaikwayo da ƙagaggun labaran Hausa.

1.1 Tsattsafi :  Wannan kalma tana cikin rukunin jerin suna na jinsin maza. Tana ɗauke da ma’anar yayyafi, wato ruwan saman da bai da yawa, mai sauka jefi-jefi. Sai dai a wannan maƙala an yi amfani da kalmar ne domin a ayyana rashin wadatuwar rubutaccen adabin na Hausa. Domiun akan same shi ne nan ɗaya can ɗaya, saboda ba kowa da kowa kan rubuta shi ba. Waɗanda suka yi ƙoƙarin rubuta adabin Hausa sun aiwatar da shi ne cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Aikin ya kasance ne a sakamakon sha’awarsu ko kuma a kan buƙatar fatake ‘yan kasuwa aka rubuta shi, domin a sami abin karantawa a lokacin da aka yada zango domin su ɗebe kewa.

1.2 Adabin Zamani:  Tun da daɗewa masana sun sha bayyana ma’anar adabi. Don haka, a wannan takarda za a mayar da hankali ne a kan ma’anar adabin zamani. A wannan fanni ma masana sun rattaba ma’anar, sai dai wasu kan kira shi da laƙabin rubutaccen adabi kamar yadda za a gani.

            Ibrahim, (1979:iii) ya kira rubutaccen adabi da  adabin zamani, wato wanda aka rubuta a takarda dangane da yadda Hausawa ke sarrafa harshensu wajen bayyana tunaninsu da al’amurransu na aiki ko na nishaɗi. Adabin Zamani ya ƙunshi rubutattun waƙoƙi da rubutattun zube da wasannin kwaikwayo.

            Yayin da Ɗangambo (1984:3) ya ce, adabin zamani, adabi ne wanda zamani ya kawo, wato zuwan Larabawa da Turawa ne ya kawo shi. Ya kuma raba shi gida uku, rubutattun waƙoƙi da rubutun zube, da rubutaccen wasan kwaikwayo.

            Shi kuma Garba, (1984:25) cewa ya yi, rubutaccen adabi shi ne  abin da aka zauna aka tsara a rubuce da rubutun ajami ko boko. Rubutaccen adabi yana da rassa uku kamar yadda Ɗangambo ya jero su a sama.

            Su Muhammad da Yahaya (babu shekara : 19) sun bayyana shi da cewa, adabin zamani shi ne abin da aka zauna aka tsara shi a rubuce, kamar waƙoƙi da sauran rubuce-rubuce da aka yi da rubutun ajami ko da boko.

            A wata ƙwarya-ƙwaryar ma’ana da Yahaya da wasu (1992) suka bayar, sun bayyana cewa, rubutaccen adabi shi ne wanda  ake kira da adabin zamani. Wannan shi ne adabin da masu ilmi suka rubuta a littattafai don jama’a su karanta, su kuma amfana. Irin waɗannan rubutattun littattafan adabi ana yin nazarinsu a makarantu.

            Shi kuwa Malumfashi (2009) ya bayyana ma’anar rubutaccen adabi da cewa, duk wani adabi da aka ƙaga ba fassaro ko baddalo shi aka yi ba, amma aka mayar da shi ta hanyar rubutu, alal misali, ƙagaggun labarai, wasannin kwaikwayo ko rubutattun waƙoƙi.

            Daga waɗannan ma’anoni za a fahimci cewa, adabin zamani shi adabi ne wanda zamani ya kawo. Domin  a can da kafin bayyanar addinin musulunci da zuwan Turawa babu shi. Ana yi masa laƙabi da rubutaccen adabi. Saboda daga baya ne Hausawa suka mallake shi, bayan sun koyi rubutu da karatu na Larabci da boko. Wato bayan sun fara hulɗa da wasu al’ummomi kamar Larabawa da Turawa. Shi irin wannan adabi an kira shi rubutaccen adabi ne, saboda a rubuce ake shirya shi, a bayar da shi a rubuce, a kuma adana shi a rubuce. Don haka, duk wani lamari da ya danganci adabin gargajiya wanda aka rubuta shi a kan takarda ko wani abu mai bagire, kamar ƙagaggun labarai, waƙoƙi, wasanni da sauran su. Muddun an rubuta su rubuce, sun tashi daga siffar gargajiya sun faɗa cikin siffar zamani.

 

2.0 Malaman Harshen Hausa Na Farko 

            Ko da Turawa suka zo ƙasar Hausa, ba kara zube suka sami al’ummar Hausawa ba. Sun tarar da su da kyakkyawan tsarin rayuwa irin nasu. Suna da iliminsu na karatu da rubutu cikin harshen Larabci da ajamin Hausa, wanda ya daɗe suna sarrafawa wajen sadarwa da gudanar da mulki da harkokin addini da na ilimi (Yahaya,1988:90) Mallakar irin wannan wayewar kai ta ba Hausawa damar tsara ƙwarya-ƙwaryar darasin harshen Hausa a rubuce domin koya wa al’ummar da ke sha’awar koyon harshen Hausa. Akwai tabbacin cewa, hukumomin mishan sun tura ‘yan mishan Tarabulus don su koyi harshen Hausa a wajen Hausawan da ke zuwa wurin (Bakura,2012). ‘Yan mishan kamar  Robinson da Miller da Richardson da Ryder, duk a Turabulus (Tripoli) suka koyi harshen Hausa. Wannan ne ya ba su damar fahimtar harshen Hausa, har suka sami damar gina adabin mishan a ƙasar Hausa (Bakura, 2012:197).

            Mafi yawan ɗaliban da suka koyi harshen Hausa a ƙasar Turai sun yi amfani da aikin da Schon ya yi na nahawu (Baldin, 1977:9-10). Wannan aikin an yi masa take da: “Farawa Letafin Magana Hausa Ko Mu Koyi Magana Gaskiya Da Hanya Garau Hal Abbaba Wonda Goni Mallami Yakubu Ya Rubuta Ya Aike ga Hausawa Duka tare Da Gaisuwa”. Kamar yadda sunan aikin ya nuna ne, marubucin littafin ana kiran sa Malam Yakubu, ana kyautata zaton littafin an shirya shi ne domin koyo da koyarwa. An rubuta littafin ne a cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Ƙumshiyar littafin ta kasance kamar haka: Daga shafi na ɗaya (1) zuwa shafi na biyu (2) ya ƙunshi abjadin Hausa ne. shafi na uku (3) zuwa  shafi na hamsin da uku (53) yana ɗauke da jerin kalmomi da yankunan jumlolin Hausa, duk a cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Daga bisani ne Schon ya juya aikin cikin Hausar boko. Sai dai an sake tsarin  shafukan littafin da ke ɗauke da rubutun Romawa zalla, wato shafi na 1-46 (Baldin, 1977: 26).

            Ke nan wannan wata manuniya ce da ke tabbatar da cewa, Bahaushe ne farkon wanda ya fara koyar da harshen Hausa, ba Turawa ba. Kuma tana yiyuwa wajen kai da komowa ne na bayar da misalai ya haifar da yin amfani da sassan adabin Hausa, kamar tatsuniyoyi da karin Magana, wanda har Turawa suka ga amfanin irin waɗannan misalai, suka ci gaba da amfani da salon bayar da misali daga adabin Hausa. Hasali ma wannan manufa ce ta wanzar da samun littafin, wanda Schon ya juya tare da wallafa shi a shekarar 1857 a matsayin littafi (Bakura, 2012:308). Ashe zai yiyu kuwa, ace al’ummar da za ta iya tsara littafin da zai koyar da nahawunta, ta kasa samara da rubutaccen adabinta a cikin sigar zube da wasan kwaikwayo?

3.0 Adabin Zamani Kafin  Mulkin Mallaka A Ƙasar Hausa  

            Masana da dama kamar Ɗangambo (1984) da Yahaya (1988) sun nuna cewa, samuwar hanyar rubutun ajami a farfajiyar ƙasar Hausa bai sa aka samu rubutun zube na ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo ba, kafin zuwan Turawa ƙasar Hausa, tamkar yadda aka san su a yau. Masu wannan ra’ayi, sun nuna cewa, duk wani abu da aka ƙaga wanda ba gaskiya ba ne, bai sami gurbin zama ba, ballantana har a gina shi cikin sigar rubutun ajami. Tun da ajamin ɗa ne na tsatson harshen Larabci, wanda ya kasance harshen addinin musulunci. Saboda haka, duk wani aiki in ba na addini ba ne, to ba zai samu karɓuwa ba. Wannan shi ya haifar da rashin wanzuwar rubutaccen zube da wasan kwaikwayon Hausa.

            Watakila a daidai lokacin da masanan suka yi bincikensu Allah bai ƙaddara sun yi tozali da wasu ayyukan adabin Hausa da Turawa suka tattara ba, kana suka adana. Irin waɗannan ayyukan an samo su ne daga hannayen marubutansu na asali a cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Misali, ayyukan da James Fredierick Schon  ya aiwatar tun  a wajen ƙarni na18 da suka danganci adabin Hausa, waɗanda ya wallafa a kundaye goma sha biyar (15). Haka kuma da aikin da Rattray ya yi a kan adabin Hausa mai take: “Hausa folk-lore: Customs,Proverbs, E.T.C. Volumes I & II”  su ma wata madogara ce. Domin ayyukkan suna ƙunshe da tatsuniyoyi da bukukuwan aure da na zanen suna da kaciyar ‘ya’ya mata da maza da lamarin al’adun mutuwa, da saye da sayarwa da sana’o’in Hausawa, kamar rini da jima. An buga littafan a Oxford, At the Clarendon Press, a shekarar 1913.

            Wannan wata ƙwaƙƙwarar hujja ce mai tabbatar da samuwar adabin zamani a ƙasar Hausa kafin zuwan Turawa. Domin takardun da Rattray ya tattar ya haɗa waɗannan kundaye nasa, ya same su ne daga hannayen fatake ‘yan kasuwa a lokacin da yake riƙe da muƙamin mataimakin kwamishina a yankin Ashanti da ke ƙasar Gana (Rattary, 1913).

4.0 Wanzuwar Rubutaccen Wasan Kwaikwayon Hausa Kafin Mulkin Mallaka  

            Ɓangaren adabin da ya fi yawa kafin zuwan Turawa ƙasar Hausa, shi ne fannin rubutattun waƙoƙin Hausa. Sai dai bincike ya tabbatar da samuwar rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa, tun kafin mulkin mallakar ƙasar Hausa (Ahmad,2004:V-VIII) wanda Hausawa suka rubuta cikin sigar rubutun ajamin Hausa, kamar yadda za a gain nan gaba. Wannan ya kau da da’awar da East  (1936) ya yi, inda ya nuna rashin wanzuwar rubutaccen ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo a nahiyar ƙasar Hausa, ba don komai ba, sai don kawai hannayensa ba su sami dafa su ba. Kundayen binciken da Dokta Rudolf Prietze waɗanda aka wallafa a lokutta mabambanta na shekarar 1916, da 1917, da 1924, da kuma na 1927 su suka kasance alƙalai wajen yanke wannan hukuncin tabbatar da samuwar adabin zamani a ƙasar Hausa. Ba ma ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo ba, har ma da waƙoƙin baka na makaɗan Hausa, waɗannan kundaye sun tabbatar da samuwar su a rubuce cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Misalai daga cikin su sun haɗa da:

 

4.1       “Yan Matan Gaya” (Labarin 1900)

            Wannan wasan kwaikwayo, Ahmadu Kano ne da kansa ya ƙago labarin, ya kuma cusa labarin wasan magi (Ahmad, 2001:V). An tsara shi ne a cikin sigar ƙagaggen labari, daga baya aka mayar da shi a cikin sigar wasan kwaikwayo. Marubucin ya rubuta wasan ne ta amfani da rubutun ajamin Hausa.

4.2 “Turbar Ƙudus” (Labarin 1898)  

Prietze ya samo shi ne daga hannun Ahmadu Kano cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Shi kuma ya juya da rubutun Romawa. Ya sa masa suna “ Der Besuch des deutschen Kaisers 1898 In Jerusalam”. Ma’ana ziyarar Sarkin Jamus Zuwa Ƙudus a Shekarar 1898. wannan wasa ta ƙunshi ziyarar da Sarkin Jamus William II ya kai a Ƙudus, wanda ya yi hulɗa da Sarkin Istambul Abdulhamid II. Ahmadu Kano ya yi wa labarin na asali ‘yan sauye-sauye, domin wasan ya yi armashi (Ahmad, 2004:V-VI).

            Daga waɗannan misalai ana iya fahimtar cewa, Hausawa sun daɗe da mallakar fasahar gina adabin zamani ta amfani da adabinsu na gargajiya ta hanyar amfani da rubutun ajamin Hausa. Sai dai abin da kawai ba su yi ba , shi ne koyar da shi a makarantun allo da na zure kamar yadda ake yi a makarantun boko.

5.0 Samuwar Rubutun Zube Na Ƙagaggun Labaran Hausa

            A wannan fannin ma akwai ɗimbin misalai da ke tabbatar da wanzuwar rubutun zube na ƙagaggun labaran Hausa a farfajiyar ƙasar Hausa tun kafin zuwan Turawa. Irin waɗannan ayyuka suna nan jibge an taskace su cikin fayil-fayil da kundayen binciken da Turawa suka aiwatar game da ƙasar Hausa da harshen Hausa, waɗanda ake iya samu a gidajen ajiye kayan tarihi da ke Kaduna ko Jos. Hasali ma za a tarar ayyukan sun ƙunshi lbarai nau’i-nau’i da suka danganci Hausawa. Wasu labaran da aka samar dogaye ne, wasu kuma gajeru. Labaran sun ƙunshi na ban dariya da raha da abubuwan al’ajabi. Wasu kuma bayanai ne game da al’adu. Daga ciki akan samu labaran gaskiya na haƙiƙa da ƙagaggun labarai da labaran da suka danganci tarihi da al’amurran da suka jiɓinci sassan rayuwar Hausawa da ta haɗa da mulki da siyasa da saye da sayarwa da bukukuwan addini da al’ada. Misalai daga cikin irin waɗannan ayyukan sun haɗa da:

5.1 Aikin Malam A. Yusha’u

            Wani malami mai suna Malam A. Yusha’u ya rubuta labarai da hikayoyi a cikin sigar rubutun ajamin Hausa. Yayin da Frank Edgar ya juya da rubutun hannu a ckin sigar Hausar boko. Ya yi masa take da: “Hausa Fables”  a shekarar 1919 ( Kaduna, NAK/ Fil.No.78/1919). Wannan ya nuna cewa aikin ya samu ne tun kafin a ƙaddamar da gasar rubutattun ƙagaggun labaran Hausa. Ta ma yiyu samun irin waɗannan labarai ne ya sa lokacin da East ya fita rangadin neman waɗanda za su shiga gasar, ya haɗa da malaman Arabiyya, domin su shiga a fafata da su don a tsamo wanda za a koya wa aikin talifi.

5.2 Aikin H. Gana Bida

            Haka kuma littafin  da H. Gana Bida ya rubuta cikin sigar rubutun ajamin Hausa, wanda ke ƙunshe da wasu labarai da waƙoƙin Hausa. Shi kuma Frank Edgar  ya juya aikin da rubutun hannu cikin sigar Hausar boko a shekarar 1901. ya kuma yi wa aikin laƙabi da: “Books of Hausa Poems and Stories”  (Kaduna, NAK/Fil.No.2/1901). Shi ma wata madogara ce da ke tabbatar da wanzuwar adabin zamani a ƙasar Hausa. Saboda an sami aikin ne tun kafin kammaluwar yaƙe-yaƙen tabbatar da kafuwar mulkin mallakar ƙasar Hausa.

            Edgar (1911) a muƙaddamarsa ya fito fili ya fayyace mana sirrin da ke ɓoye game da adabin zamani a ƙasar Hausa. Jami’in mulkin cewa ya yi: “ A farkon shekarar 1910 na karɓI ɗimbin ayyukan adabin Hausa a cikin sigar rubutun ajami daga hannun Major Alder Burdon, waɗanda na juya su cikin sigar rubutun Romawa. Sakamakon wannan aiki ne ya haifar da wanzuwar aiknsa mai take ‘Littafi Na Tatsuniyoyi Na Hausa’. Ke nan wannan wata babbar matashiya ce da ke tabbatar da adabin zamani cikin sigar rubutun ajamin Hausa.

6.0 Kammalawa

            Duk da kasancewar lokacin da Turawa suka zo ƙasar Hausa, sun sami Hausawa da fasahar rubutu da karatu da ci gaban rayuwa da wayewar kai gwargwadon buƙata fiye da mutanen da ke bakin ruwa. Amma sun yi ƙoƙarin dakushe wayewar kanmu. Da gangan suka kushe ci gabanmu suka ɗauke mu ƙidahumai waɗanda ba su mallaki adabin zamani ba. Har ma sun yi iƙirarin cewa wai su suka koya mana fasahar samar da rubutaccan adabi. Sai dai akwai jerin takardun bayanai da tarin littattafan da su Turawan da kansu ne suka tattaro su a cikin sifar da suka same su ta asali, waɗanda daga bisani suka juya su da sigar rubutun Romawa. Irin waɗannan ayyukan sun taimaka matuƙa wajen kawar da da’awar da Turawa suka yi na cewa, wai su ne suka fara samar da adabin zamani a ƙasar Hausa, in aka cire rubutattun waƙoƙin Hausa.

            Daga ƙarshe, ina kira ga manazarta a kan su mayar da hankalinsu wajen nazarin ayyukan da Turawa suka tattara tare da adana su, musamman waɗanda suka danganci ƙasar Hausa, ba don komai ba sai domin a zaƙulo irin hikimomi da asiran da ke tattare a cikin su. Burina shi ne a samu wanda zai ɗora a kan wannan aiki domin samar da zuzzurfan biciken da zai amfani al’umma da kuma ƙasarmu baki ɗaya. Allah Ya taimake mu don alfarmar  Annabinsa. Wassalam.  

 Manazarta

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments