Bege, soyayya da ƙaunar da ke tsakanin abokina Albani da sahibarsa Ruƙayya su ne suka ja hankalina zuwa ga tsara waɗannan baituka. 
Hirata da Albani

1. Da sallama na sami aboki sama.
2. Da na gai da shi ya amsa min sama-sama.
3. Tuni ni ko sai na ce malam mi na ma?
4. Ya za ka dinga zancenka da taƙama.
5. Da ganin ka kanka girma ka kinkima.
6. Ko ya kulani ga matashi ya runguma.
7. A kishingiɗe ƙafa harɗe ya ɗan zuma.
8. Na cane da shi tsaya Albani na ma-
9. Wata tambaya ka amsan ba gardama.
10. Daga ka ƙi za ni ce ma sai anjima.


11. Ya yi wuf ya ce da ni malam barka.
12. Mahamudu ɗan uwa yaushe zuwanka?
13. Yanzun nake shiri za ni wajenka.
14. Dan nai gamo, gamo fa irin naka.
15. Tuni zullumi nake yanzu na farka.
16. Wata ƙorama ta bege na afka.
17. A cikinta na ga sida mai suka.
18. Da itaciya kamar an shusshuka.
19. Kayan marmari suna nan a gabanka.
20. In ka shige ta ba mutum mai kallonka.

21. Ka ɗan dakata a nan Albani haba.
22. Kana yin batu kamar wani mai tsatsuba.
23. Cikin zullumi ka sa ni nake laluba.
24. Misalin batunka shi ne igiyar kaba.
25. Ga mai jan ruwa a tulu ya zuzzuba.
26. Sannan sai kadangare ya haye ka ji ba.
27. In ka bar shi to ruwa ya zamto guba.
28. In ka hare shi ka ga jifa bai kyautu ba.
29. Ina ma a ce kamar yau ne Laraba.
30. To da sai na ce rabon tuni an rarraba.


31. Wayyo ni farin Bahaushe mai sa gumi.
32. Zancen naka dinga zai sa a yi tagumi.
33. In da ka bi sannu-sannu cikin lalumi.
34. Da zan ba ka fira kanta ka bar tsegumi.
35. Ruƙayya nake bayani 'yar Malami.
36. Kaga Ruƙayya kaf a mata ba na gami.
37. Dan ita ce guda ganinta yake sa tsumi.
38. Ran da na gan ta farko na faɗa zullumi.
39. Ka ga Ruƙayya rayuwarta akwai illimi.
40. In ka ji wane to mutum ne gagarumi.

41. Malam Nasiri abokin alheri.
42. Yanzu kake batu batunka a kan jeri.
43. In zancen Ruƙayya ne zan ma gori.
44. Ka ce son Ruƙayya gun ka ya zam jari.
45. Wacece Ruƙayyatun da kake buri?


46. Ka ga Ruƙayya farko ga ta da annuri.
47. Kyawun Ruƙnas gareta ya zam jari.
48. 'Yanmata irin salonta suke sari.
49. Kyawun Ruƙƙi ba mutum mai inkari.
50. Kyan fiska da kyan halinta a labari,
51. In ka ji za ka san sifofinta da tsari.
52. Ruƙayya jikinta babu tabon mari.
53. Dukka mijin Ruƙayya shi ya rike jari.
54. Wanda cikinsa ya ci riba ya yiyi dori.
55. Tun da na san ta ko guda ba ta da sharri.

56. Iko sai Ilahu ka sa na wartsake.
57. Dan na gano Ruƙayya dole na yo fiffike.
58. Kai ka tsaya aboki Albani ina kake?
59. Wanga ɗiya Ruƙayya wanne gida ne take?
60. Shin dangin Ruƙayya kam a ina ne suke?

61. Farko Ruƙayya nan Arewa a birni take.
62. Can a Kaduna Kinkinau gefen 'yan tike.
63. Ka ga fa tarbiya gidan su Ruƙayya yake.
64. Dattaku Ruƙayya gun su mutunci yake.
65. Ka ga halinsu tuntuni na gari sun cike.
66. In ka ce karamci wannan gado suke.
67. Ka ga gidansu duk mutum son fa shiga yake.
68. Dan kakan Ruƙayya ai Baƙuraishe yake.
69. 'Yar dangi Ruƙayya aurenki biɗa ake.
70. Taka sannu-sannu 'yanmata da ke nake.

71. Albani cikin batu na Ruƙayya ka ce,
72. Siffofi ka nuna ta ɗara duk 'ya mace.
73. In ka rasa ta babu shakka sai ka mace.
74. To kafin na ce abin da ya dace na ce,
75. Addinin Ruƙayya Nasir me za ka ce?

76. 'Yar baiwa Ruƙayya mai kunya tawa ce.
77. Yin ladabi Ruƙayya wannan siffarki ce.
78. Gun kyauta da saddaka Ruƙnas tai fice.
79. Halayen Ruƙayya ba wani ce-ce-ku-ce,
80. Addinin Ruƙayya in ka gani za ka ce,
81. Wata ce can cikin sahabu aka killace.
82. Sunnoni Ruƙayya ta yi su a aikace.
83. Ƙurani ka gane tuntuni ta haddace.
84. Ruƙƙi fara cikarki ta kai ya cikar mace.
85. In na rasa ki Ruƙƙi tabbas zan haukace.
86. Cikin dukkaninsu mata da za a ce-
87. Na zaɓo guda gwanata ita za na ce.
88. A bar ma batu na zancen wata 'ya mace.
89. Idan har da Ruƙƙi ba wani ce-ce-ku-ce.
90. Domin ni a zuci kowa ma ta wuce.

91. Albani gareni ka amsan tambaya.
92. Na gane Ruƙayya ta kai ta yi mamaya.
93. 'Ya ce wanda sonta ke mamaye zuciya.
94. Domin ta ƙure a kyau da salon tarbiya.
95. Ni kin burge ni ɗiya Ruƙƙi Baturiya.
96. A tun farko har da ƙarshen duka ƙafiya.
97. Albani Ruƙayya ce ka kira mun jiya.
98. Tun da ka sami Ruƙƙi kai sai ka yi fatiya.
99. Ni Mamuda nan wajen dai haka zan tsaya.
100. Sai wata ran Ruƙayya kyakkyawar duniya

Mahmud Ahmad Musa
09020194569, 08147909719
madakinwaka@gmail.com