Ticker

6/recent/ticker-posts

Dusashewar Wasannin Gargajiya A K’asar Yabo (2)

Wannan bincike zai bayyana irin tasirin zamani a kan wad’annan wasanni domin yara matasa su nuna sha’awarsu ga wasannin da, fiye da na zamani. Da haka ne za su gane alak’arsu.


Sufiyanu Abubakar
Hassan Ladan
Hassana Mustapha Ibrahim

BABI NA D’AYA

GABATARWA

Gabatarwa


Wannan bincike ya k’udiri aniyar yin bayani ne a kan dusashewar wasu wasanin gargajiya na yara a k’asar Yabo. “Dusashewar wasu wasanin gargajiya na yara a k’asar Yabo”, wanan zai ba, mai karatu damar sanin ire-iren wasannin gargajiya, da yadda ake aiwatar da su, da kuma lokacin aiwatar da su, da kuma tasirin zamani a kansu, sannan da sanadiyyar dursashewarsu.

Haka kuma wannan zai ba yara matasa sanin yadda wad’annan wasanni ke gudana, tare da sanin sunayen wasannin. Masana da dama sun yi bayani a kan ma’anar wasa. Wannan aikin ya yi tsokaci a kan wasu daga ma’anonin da suka ba wasa.

An tsara wannan aiki, babi-babi har zuwa babi biyar, domin samun sauk’in karantawa ga mai nazari. Har-ila-yau aikin ya yi nazarin wad’ansu littattafai, da kuma wasu ayukkan da suka gabata domin k’arin samun haske dangane da wannan aiki.

Dalilin yin wannan bincike shi ne, domin duba ko binciko wani ‘bangare na irin wannan tsarin wasannin.Wannan zai ba da damar ganin irin dusashewar da wasannin gargajiya ke samu. Saboda ganin muhimmancin wasanni, aikin binciken nan ya k’udiri aniyar d’aukar k’aramar hukumar domin yin bayanin wasannin na Hausawa da suka gudanar tun daga k’uruciyarsu har zuwa tasowarsu. Wanda kuwa, wasannin su ne ke k’ulla zumunta har zuwa tsufa. Ganin irin wannan muhimmancin da ke tattare da wasanni ya kyautu a gudanar da aikin bincike a kansu.

Wannan aiki na sa ran ya kasance mai amfani ga k’ananan makarantu (primary) har zuwa manyan makarantu (secondary). Ba su kad’ai ba ma, har da manyan yara na garin Yabo da kewaye. Amin.

Dalilin Bincike

Manyan dalilai na yin wannan bincike su ne:

  1. Muhimmanci nishad’i ga tarbiya

  2. Ba a yi irin wannan bincike ba
  • Saboda ajiye bayani don masu bincike
  1. Dusashewar wasannin sakamakon tasirin zamani

  2. Bunk’asa al’adar Hausawa

Muhimmancin nishad’i ga tarbiya: A nan ana nuna wa jama’a cewa, duk da kasancewar ta wasa, to aba ce mai muhimmanci ga koya wa yara tarbiya dangane da irin yadda wannan wasa take gudana. Domin kowace wasa akwai wani darasi da take koyarwa, domin a gani, a gane kyawunsa ko muninsa.

Ba a yi irin wannan bincike ba: A sakamakon binciken da wannan aiki ya yi, a d’akin karatu na wannan jami’a, da Jami’ar Usmanu Danfodiyo da C.O.E., aikin ya sami wasu littattafai da suka yi bayani a kan wasannin yara. Amma dai babu wasu ayyuka wad’anda suka yi bayani a kan dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo. Hakan ne ya k’arfafa wa wannan aikin bincike guiwa na yin bincike a kan wannan batu.

Saboda ajiye bayani don masu bincike: A k’ashin gaskiya abin bak’in ciki ne, ga d’alibai manya da k’anana, a rasa ajiye wani littafi a fannin adabi wanda ya yi magana a kan tsofaffin wasannin gargajiya na Hausa a garin Yabo. Samun  wannan littai shi ne zai k’ara bunk’asa al’adun Hausawa musamman a garin Yabo. Don haka samun wannan littafi, zai ba masu bincike sauk’in gano ire-iren wasannin gargajiya na da a garin Yabo.

Dusashewar  wasanni sakamakon tasirin zamani: Haka kuma, wani dalilinmu na yin wannan bincike shi ne, domin ganin cewa wad’annan ire-iren wasanni na gargajiya suna neman dusashewa, saboda tasirin zamani, idan ba wani aiki da aka gudanar da zai killace su wuri d’aya ba, lallai za su iya salwanta kafin wani lokaci.
  • Manufar Bincike

Wannan bincike a kan dusashewar wasannin gargajiya a garin Yabo, na da manufar nuna wa jama’a irin k’ullin zumuncin da yake k’ullawa a tsakanin yara har zuwa manyancinsu. Haka kuma da wannan ne binciken ke nufin nuna wa jama’a ire-iren wasannin gargajiya na da, wad’anda yara maza da mata ke aiwatarwa, na shirin ‘bacewa a k’asar Hausa.

Wannan bincike zai bayyana irin tasirin zamani a kan wad’annan wasanni domin yara matasa su nuna sha’awarsu ga wasannin da, fiye da na zamani. Da haka ne za su gane alak’arsu.

Haka kuma wannan bincike zai bayyana kyawawan wasannin gargajiya na da a k’asar Yabo, domin amfanin na baya wad’anda za su karanta, su san ire-iren al’adun yara maza da mata, wad’anda suka gabace su, don su koyi ire-iren al’adu musamman wasannin.

Haka kuma domin nuna sha’awar mai binciken ga duk mai nazarin harshen Hausa, musamman adabi. Hak’ik’a duk wanda ya nuna sha’awa a kan al’adun Hausawa ta wasanni, muddin ya sami kwafin wannan kundi, to zai iya tsintar wani abu domin karantawa.
  • Bitar Ayyukan da Suka Gabata


Wannan ‘bangare yana d’auke da sharhi a kan ayyukan da suka gabata, wad’anda suke da dangantaka da wannan bincike. Yin bitar ayyukan da suka gabata na da matuk’ar amfani ga duk wani aikin bincike da aka sanya a gaba. Dalili kuwa shi ne, bitar za ta ci karo da ayyuka daban daban masu alak’a ta kusa ko ta nesa da aikin binciken da aka sanya a gaba. Irin wad’annan ayyuka masu dangantaka da wanda aka k’udurta yi, za su kasance masu amfani matuk’a ga marubuci.

1.3.1 Littattafai

Umar, (1977) ya wallafa littafi mai taken Wasannin Tashe. A cikin wannan littafin ya kawo ire-iren wasannin tashe da dama da ake da su a k’asar Hausa. Wad’annan wasanni akan gudanar da su ne a lokutan azumi. Wannan aiki na Umar ba zai hana ci gaba da wannan bincike ba. Domin shi ya dubi wasannin tashe ne kawai. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

Isa da Daura (1982), sun rubuta littafi cikin harshen Ingilishi mai take: “Hausa Customs.” A cikin wannan littafi sun yi bayani game da wasu wasanni. Sai dai a iya cewa, wad’annan wasanni sun ta’allak’a ne a kan wasannin manya, wato maza. Don kuwa ya yi d’an tsokaci ne a kan, kokuwa, dambe, ‘yan hoto da kuma bori. Marubuta wannan littafi sun yi irin nasu k’ok’ari kuma sun burge k’warai. Sai dai littafin bai zo da wani bayani a kan wasannin gargajiya ba, musamman na matasa, don haka muke ganin ya dace a k’ara fito da su a sarari domin k’arin haske., domin k’arin samun haske.

Dembo, (2007), a nazarinmu, wannan littafi ya yi bayani a kan wasu wasanni misali, “langa” “d’an na kangal-kangal” da sauransu. Kuma hak’ik’ar marubucin wannan littafi ya yi matuk’ar k’ok’ari, kuma aikinsa yana da matuk’ar burgewa. Dambo ya yi wannan littafi ne a sigar wasan kwaikwayo. Cikin hikima ya sanyo irin wad’annan wasanni na yara. Amma wannan littafi nasa ba zai tsayar da wannan aikin bincike ba. Dalili kuwa shi ne, ya yi bayaninsa musamman a kan “Langa”, ya yi shi ne a tak’aice. Dalili kuwa shi ne, ga wanda bai san wanan wasa ba, to ba zai iya fahimtar yadda ake gudanar da ita a kan bayaninsa ba. Da haka ne wannan aikin bincike ya k’uduri aniyar fad’ad’a bayani sosai, ta yadda wanda bai san wasannin ba, zai fahimci yadda suke gudana. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

1.3.2 Kundaye

K’auran Namoda, (1982) ya gudanar da bincike na digiri na farko mai taken: “Wasannin Tashe.” Ya gabatar da wannan aiki a Sashen Harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato. Wannan kundi nasa ya k’unshi wasanni ne iri-iri na tashe, wad’anda ake gudanarwa a lokacin azumi. Kundin nasa ba zai hana ci gaba da wannan aiki ba, domin shi ya dubi wasannin tashe ne kawai, bai dubi yadda wasanni suke dusashewa ba a k’asar Hausa (musamman k’asar Yabo). Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

Sakkwato, (1982) ya gabatar da kundin digirinsa na farko mai a Jami’ar Usmanu Danfodiyo mai taken: “Wasannin da Wak’e-wak’en Yara a Sakkwato.” A cikin wannan aiki nasa, ya kawo wasu wasanni wad’anda ke d’auke da wak’e-wak’e a cikinsu. Sannan ya karkata akalar binciken nasa ne zuwa garin Sakkwato. Aikin nasa yana da dangantaka da wannan aikin, domin kuwa dukkaninsu suna magana ne game da wasanni. Sai dai sun sha bamban, saboda, shi yana magana ne kan wasanni da wak’e-wak’e na yara a garin Sakkwato. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

K’aura, (1986) ya gudanar da kundinsa na NCE mai taken: “Wasannin Yara.” Wannan kundi ya yi shi ne Sashen Hausa na Kwalejin Ilimi da ke Sakkwato. A cikin kundin ya kawo wasannin yara iri-iri wad’anda ake da su a k’asar Hausa. Wasannin sun had’a da na maza da kuma na mata. Sai dai bai yi magana game da dusashewar wad’annan wasanni ba, musamman a k’asar Yabo. Saboda haka, aikin na K’aura ba zai dakatar da wannan bincike ba, domin kuwa shi K’aura ya karkata ne zuwa ga wasannin yara bai d’aya. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

Bunza da Koko, (1988) sun gudanar da bincike wanda ya kai su ga rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Kundin yana da take: Wasannin Yara a K’asar Gwandu.” A cikin wannan kundin nasu, sun cakud’a wasannin maza da na mata ne, sannan sun fi mayar da hankali kan wasannin maza. Lallai kundin nasu yana da dangantaka da wannan aikin bincike, saboda sun kawo wasannin gargajiya da dama a ciki, musamman wad’anda ake samu a k’asar Gwandu. Sai dai duk da haka kundin nasu ba zai hana ci gaba da wannan bincike ba. Dalili kuwa shi ne, Bunza da Koko sun karkata ne zuwa ga k’asar Gwandu. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

Kaduna, (1988) ya rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, mai taken: “Tasirin Zamani a Kan Wasannin Yara a K’asar Hausa.” A cikin wannan kundi nasa, ya fi mayar da hankali ne kan yadda zamani ya yi tasiri a kan wasannin yaran Hausawa na gargajiya. Zamanin ya zo da wasu wasanni na daban wad’anda suke tattare da zamananci, sannan wad’annan wasannin zamani su ne suke dusar da wasannin yara na gargajiya. Aikin nasa yana da dangantaka da wannan bincike, dalili kuwa shi ne, dukkanninsu biyu za su yi tsokaci game da dusashewar wasanni musamman na yara. Sai dai kuma aikin na Kaduna ba zai tsayar da wannan bincike ba, domin shi ya yi bincike ne game da tasirin zamani a kan wasannin yara a k’asar Hausa. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

Yusuf, (1988) ta rubuta kundin digiri na farko a Sashen Harsunan Nijeriya da ke Jami’ar Bayero, Kano. Kundin yana da taken: “Wak’ok’in ‘Yanmata a Dandali.” A cikin wannan kundi, ta mayar da hankali kan ire-iren wak’e-wak’en da ‘yanmata kan yi a lokutan wasanninsu na dandali. Aikin nata yana da dangantaka da wannan bincike kasancewar ire-iren wad’annan wak’ok’in mata akan same su ne cikin wasanninsu na dandali. Sai dai kuma, aikin nata ba zai dakatar da wannan aikin bincike ba, domin ita ta mai da hankali ne zuwa ga wak’ok’in mata a dandali. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

Idris, (1989) ya gudanar da bincike mai taken: “Wasannain Yara na Wasan Kwaikwayo.” A cikin wannan bincike ya yi nazarin wasannin yara masu alak’a ko sigar wasan kwaikwayo. Wad’annan wasanni sun had’a da ‘yar tsana, inda yara ke kwaikwayon zaman aure da sauran wasannin yara masu irin wannan siga. Aikin na Idris ba zai hana ci gaba da wannan aikin ba, domin shi ya dubi wasan yara ne na wasan kwaikwayo. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

Mairukubta, (1994) ta rubuta kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato mai taken: “Tawai a Matsayin Dabarun Raino a K’asar Hausa.” A wannan kundin nata ta fitar da wak’ok’i kala-kala wad’anda mata musamman ‘yammata ke yi wa yara lokacin reno. Irin wad’annan wak’ok’i suna d’auke da zambo da ba’a da habaici da kuma kurarawa da gwarzontawa. Dangantakar aikin na Mairukubta da kuma wannan shi ne, kasancewar wasannin Hausa da dama suna d’auke da wak’ok’i, sannan yayin rainon yaran kansu, wasa ake musu. Sai dai aikin na Mairukubta ba zai hana wannan bincike ba. Dalili kuwa shi ne, yayin da Mairukubta ke duban taiwa a matsayin dabarun raino a k’asar Hausa, wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

Ibrahim, (Mrs) (2000) ta gabatar da gudanar da binciken kundin digiri na biyu a jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato mai taken: “Wasanni da Wak’ok’in Yara Mata a Sakkwato.” A cikin wannan kundi ta kawo wasannin mata iri-iri wad’anda suka had’a da; Carman Dudu da Wak’ar Basha da Wasan Gora-gora da Wasan Laula Amarya da makamantansu. Saboda haka aikin nata yana da dangantaka da wannan aiki, domin kuwa dukkaninsu biyu sun ta’bo magana game da wasanni. Sai dai aikin nata ba zai hana gudanar da wannan aikin bincike ba. Dalili kuwa shi ne, ita ta gudanar da aiki ne game da wasanni da kuma wak’ok’in mata a garin sakkwato. Wannan aiki kuwa zai yi nazari ne game da dusashewar wasannin gargajiya a k’asar Yabo.

A tak’aice za a iya cewa, a dukkanin ayyukan da wannan aikin bincike ya dora hannu a kai, babu wanda ya yi magana dangane da dak’ushewar wasannin Hausa na gargajiya a k’asar Yabo. Wannan ne ya sa, ayyukan wad’anda aka yi kan wasanni ba za su hana wanzuwar wannan aikin bincike ba.
  • Hujjar Ci Gaba da Bincike

Masana da manazarta harshe da al’adun Hausa sun yi rubutu daban daban game da wasannin yara a k’asar Hausa. Wad’annan rubuce-rubuce sun had’a da littattafai da kundayen digiri da kuma mujallu da makamantansu. Amma duk da haka, idan aka yi la’akari da nazarin da wannan aikin bincike ya yi a wurin bitar ayyukan da suka gabata, za a fahimci cewa ba a gudanar da wannan aiki ba a game da abin da wannan aikin bincike yake son tattaunawa. Watau wasannin gargajiya a k’aramar hukumar Yabo ta jihar Sakkwato. Domin duk wuraren da namu aikin ya bincika, ba a gudanar da shi ba.

Saboda haka ne wannan aikin bincike zai yi k’ok’ari domin yin bincike a kan wannan batu na wasannin gargajiya a wannan k’aramar hukumar, da irin muhimmancinsu ga wannan bincike. Aikin zai yi k’ok’arin fito da yadda wasannin gargajiya a k’asar Yabo suke dusashewa.
  • Iyakacin Bincike


Da yake wannan bincike ya tak’aita ne a kan dusashewar wasannin gargajiya na k’asar Yabo ba na wani gari ba, don haka dukan bincike a kan littattafai wad’anda aikin ya gudanar, da kuma hirar da aka yi da wasu masana, an yi su ne a kan dusashewar wasanni na yara maza da mata na gargajiya a k’asar Yabo. An yi wannan karance-karance da kuma hira da masana ne, domin k’arin samun haske da kuma samun wasu bambance-bambance da ke tsakanin wasannin gargajiya na garin Yabo da kuma wasu garuruwan na daban. Wannan binciken zai ba da damar samun k’warin guiwa don zurfafa tunanin masu binciken, da kuma k’ara musu himma a kan aikin binciken suka sanya a gaba.

Aikin ya ci karo da wasu wasanni a bincikenu a binciken da muka gudanar a wasu garuruwa, wad’anda sun (wasannin wasu garuruwa) yi kusan kama da na garin Yabo. Sai dai wasu bambance-bambance dangane da suna ko kuma yanayin aiwatar da su. Amma aikin ya gano cewa, an sami mafi yawancin wasannin sun yi kama da na k’asar Yabo ne ta fuskar aiwatar wa dangane da muhalli da kuma lokaci.
  • Hanyoyin Bincike

Da yake wannan aiki ya ta’allak’a ne a kan dusashewr wasannin da, na gargajiya, don haka hanyoyin da za a bi na wannan bincike sun had’a da:

Hira da mutanen da ake tunanin za a sami wasu bayanai wurinsu. A nan aikin zai sa ran ya samu wasu bayanai daga wurin wasu malamai na wannan jami’a, da Jami’ar Usumanu Danfodiyo, Sakkwato da kuma wasu masana na waje, har da wasu malamai na kwalejin ilmi ta Shehu Shagari Sakkwato. Haka ma, har wa yau mai yiyuwa ne aikin ya sami wasu bayanai daga abokan karatun masu gudanar da binciken na cikin jami’a da kuma na waje, da kuma wasu dattawa da ake tsammani wani bayani daga gare su.

Baya ga wannan, wata hanya da aikin zai bi a wajen bincikenmu ita ce; karance-karancen littattafai. A nan da yake akwai hanyoyi da dama na karance-karance, don haka aikin zai karanta wasu littattafai a d’akin karatu na Sashen Nazarin Harsunanan Nijeriya, Jami’ar Jahar Sakkwato da d’akin karatu na Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato. Haka ma aikin zai sa ran gudanar da karance-karancena a d’akin karatu na kwalejin ilimi ta Shehu Shagari, Sakkwato.

Bugu da k’ari, wata hanya da aikin zai bi domin gudanar da bincike ita ce: sauraren kafofin labarai, wad’anda sun had’a da; gidajen radiyon Rima Sakkwato da gidan talabijin Sakkwato da kafafen watsa labarai na BBC da muryar Amurka da Faransa. A wad’annan kafofin labarai aikin zai sa ran sauraren wasu shirye-shirye kamar irin su, Dad’in Zuciya da Zauren Mai Unguwa da Yau Da Gobe da Yara Manyan Gobe. Wad’annan su ne hanyoyin da za mu bi domin cim ma manufarmu yayin gudanar da wannan bincike. Musamman Rima da rediyo Faransa da ke gabatar da shirin al’adunmu na gado.


Post a Comment

0 Comments