A Paper Presented At 1st
International Conference on The Hausa People, Language And History
(Kaduna, 2015) On 24th March,
2015.
Tasirin
Musulunci A Cikin
Kirarin ‘Yan Tauri
ABUBAKAR SANI SAYAYA.
SASHEN WATSA LABARAI DA ƊAB’I
MAJALISAR DOKOKI TA JIHAR KATSINA.
08022671839
Gabatarwa
Kafin Hausawa su ci karo
da wasu baƙin al’adu,
musamman irin waɗanda addinin
Musulunci, ya zo da su sun kasance
suna gudanar da dukan
harkokin rayuwarsu a
al’adance ne. Ta hanyar salon rayuwa wadda suka gada kaka da kakanni, ba
tare da
sun gauraya ta
da wata baƙuwar al’ada ba,
kamar yadda muka gani cewa kafin
zuwan Larabawa, Bahaushe ba ya da addinin da ya fi Tsafi da Bori. Wato bai san
Allah ba. Ba abin da ya ke bauta wa
sai tsafin gidansu. Aminu, N. (2013).
Irin
wannan salon rayuwa ya shafi har da irin kirarin da Hausawa ke yi,
wanda kuma
kirarin ‘yan tauri na daga ciki. Tauri wata hanya ce da Hausawa ke amfani
da wasu
sinadarai da ake samu daga waɗansu itace, ko tsirra, ko sassan jikin wasu halittu,
misali kwari ko dabbobi, ko kuma wasu ayoyi daga cikin Al’ƙur’ani mai tsarki, su
sarrafa su ta hanyoyi daban-daban
domin kare jikinsu daga rauni, ko
cutarwar da
ƙarfe ko
wani makami ka iya yi masu………… Waɗanda suka ci
maganin Tauri,
har ya kama jikinsu ana kiransu ‘yan
tauri, Sayaya, A. S. (2009). ‘Yan
tauri suna
gabatar da kirari ne domin su tsorata
abokanen adawarsu tare da zummar ƙara ma
kawunansu ƙaimi, da nufin kawar da tsoro, ko shakkun tunkarar duk wanda ka
iya
taso masu.
MA’ANAR KIRARI.
Kamar sauran fannonin adabi, an samu masana da dama da suka yi
tsokaci a kan
ma’anar kalmar kirari. Bunza, A. M. (2009), ya bayyana
ma’anar kirari da cewa,
Kalmar kirari asalinta daga “Kira”
take. A sa kalangu, ko ganga, ko murya a kira
wani da ƙarfi don ya fito a ɗebe tababan
abin da ake faɗa a kansa.
Janaidu da
‘Yar’aduwa (2007), cewa suka yi kirari, wani rukuni ne na salon sarrafa
harshe da
Hausawa kan yi amfani da shi
wajen nuna gwaninta da kimar harshe, ta hanyar
tsara kalmomi da suka dace da halayen abubuwa
a cikin lugga mai ban sha’awa.
A yayin da Dunfawa, (2002), ya ce,
Kirari shine jera jimlolin adabi masu amfani
da kalmomi waɗanda aka tsara
cikin salon siffantawa domin wasa, ko kumbura,
ko ingiza mutum ko wani abu. Hausawa
sun fara gabatar da kirarin ne tun gabanin
su fara cuɗanya da wasu baƙin al’adu, wato
tun lokacin da ake bautar iskoki kamar
yadda ya gabata. A wancan lokacin ‘yan tauri su kan yi amfani da wasu
lafuzza
da suka danganci na bautar iskoki, kuma sun ci gaba da gabatar da shi har
lokacin
da addinin Musulunci
ya shigo ƙasar Hausa, aka samu Hausawa suka karɓe shi
hannu biyu.
TASIRIN MUSULUNCI A CIKIN KIRARIN ‘YAN TAURI
Addinin Musulunci ya zo ƙasar Hausa a
wajen ƙarni na 14 daga Larabawa,
waɗanda suka shigo Ƙasar Hausa ta ɓangaren Afirka
ta Arewa Maishanu, (2007).
Nazarce-nazarce sun gabata
da cewa zuwan Musulunci a ƙasar Hausa ya kawo
sauyin al’adun Hausawa
da dama, yayin da ya zubar
da wani sashe, ya tsarkake
wasu al’adu, kamar yadda ya zo da wasu sababbi waɗanda Hausawa ba
su san su
ba kafin zuwan Musulunci. Muhammad, S. U. (2006). Ko da yake
‘yan tauri sun
ci gaba da yin kirari, sai dai a
sakamakon shigowar addinin da kuma irin tasirin
da ya yi a kan harshen Hausa ne ya sa aka riƙa samun canje-canje daga irin zaɓin
kalmomi da masu kirarin ke yi. Da haka suka riƙa gina kirarin nasu ta hanyar aron
kalmomin Larabci da addinin ya zo da su, ko wasu Jimloli daga cikin harshen
har
zuwa lokacin da karatun Ƙur’ani da
Hadissan Annabi Muhammadu (S.A.W), ya
yawaita tare da fahimtar ma’ana, sai suka riƙa ɗaukar wasu
sassa daga ciki, suna
amfani da su cikin kirarin. Irin wannan tasiri da addinin
ya yi a cikin kirarin ‘yan
tauri shine aka yi ƙoƙarin dubi a cikin wannan takarda. An kuma gina takardar
ne
tare da kawo
misalan kirarin da su ‘yan tauri
suke yi, tun kafin zuwan
addinin
Musuluncin, da irin yadda aka riƙa yin sa tun
farkon shigowarsa, da kuma yadda
kirarin ya kasance bayan sabon addinin ya kankama.
KIRARIN ‘YANTAURI KAFIN ZUWAN
ADDININ MUSULUNCI.
Kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa,
lokacin da Hausawa ba su san wasu
kalmomin Larabci waɗanda suka jiɓinci addinin ba,
sai suka riƙa yin amfani da
kalmomin Hausa tsagwaronsu suna gina kirarin. Wasu kuwa suna gina shi tare
da
ambaton hanyoyin bautarsu, wato tsafi ko kuma wuraren da suke bautar, da
kuma
ire-iren lafuzzan da suke yi yayin
ganawarsu da Iskokan da suke bauta wa
kamar
yadda za mu gani.
TSAFI A CIKIN KIRARIN
‘YAN TAURI.
Kamar yadda bayani ya gabata, cewa
tun kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar
Hausa, babu wata hanyar bauta sai ta Tsafi da Bori. (Wato bauta wa Iskoki),
yayin
da kowa irin tsafin da ya gada iyaye da kakanni shi yake
yi. Kuma sun yarda da
cewa daga cikin mazaunin Iskokai, akwai kango ko gidan Turwa, da wasu manyan
itatuwa irin su kuka da marke da tsamiya ko tsohuwar rijiya ko kogo da
sauransu.
Sallau, (2010) ya jaddada haka inda ya ke cewa bauta ta hanyar tsafi na
nufin bauta
wa wani aljani da aka ɗauka yana zaune a wani wuri na daban. Ire-iren waɗannan
aljannu, an ɗauka suna zaune ne a wata
kwankwamar dutse ko wata sarƙaƙƙiya ko
wurin wata tsohuwar
itaciya, misali kuka ko tsamiya ko marke da sauran su. Da
haka ya sa wasu suke ambaton ire-iren mazaunun nasu a cikin hulɗoɗinsu na yau
da kullun. Irin wannan hali ba wani baƙon abu ba ne ga ‘yan tauri, domin kuwa
ɓurɓushin hakan ya fito fili a cikin waƙar makaɗa Mamman ɗan ƙanen Kassu, a
yayin da ya kaɗo taken wani ɗan tauri da ake
kira Sule. Da tasowarsa sai ya
fara
da cewa:
“Ashe dai Mamman! Ashe dai
Mamman!!
Sai ni
mai Tururuwa mai Turba,
Mai
Gajimari, mai jam Marke,
Mai Tsamiya bakwai wurin yin tsahi.”
(Mamman ɗan ƙanen Kassu, kirarin Sule Birnin
Kuka).
A cikin kirarin da ya gabata Sule ya ambaci wasu daga cikin wuraren da
Bahaushe
ya fi zaton cewa mazaunin Iskoki ne. Wuraren kuwa sun haɗa da gidan Turwa, da
Turba (magamar hanya), da jan marke, da tsamiya, da ma
sunan wani Iskan, wato
Gajimari. Haka nan kalmar tsafin ta
bayyana a cikin kirarin wani shahararren ɗan
tauri, wato Mamman Dogo yayin da makaɗa Garba ɗan wasa Gumi ke yi
masa
take, yana cewa:
“Kai
Garba! Kai Garba!! Kai Garba!!!
Tuba ta
tashi malami ya ci biri,
Garba
kana hwaɗin in tuba,
Dan
Allah jinjina mani Kurya,
Kurya ta ce mu yi
Tsahi,
Mu yi Tsahi, mu yi
Tsahi,
Mu ci taurin baƙar tama har abada”
(Garba ɗan wasa, kirarin Mamman Dogo).
Waɗannan bayanai da
suka gabata sun gabbata
da cewa lallai
akwai ɓurɓushin
tsafi cikin ire-iren kirarin ‘yan tauri.
KIRARIN ‘YAN TAURI
MAI ƊAUKE DA FASALIN
BAUTAR ISKOKI:
Bayan tsafi wani nau’i
na addinin gargajiya
na Hausawa shi ne
bori, A wurin
Hausawa bori tsohuwar al’ada
ce, domin kuwa an daɗe ana
yin ta a matsayin
addini. Sallau, (2010). Kamar yadda
Bunza, A. M. (2009). Ya ke cewa, yayin da
ɗan bori ya
hau, zai Kasance yana ɗimauta, ko ya
yi mamunga, yana
wasu irin
maganganu na surkulle. Maganganun
surkulle da ake yi wajen kafin
gida da idan
za a ci sabon hatsi da idan ɗan Bori ya shiga
Boboniya, duk sun aminta da cewa,
Iska na ji kuma bukata na biya. Wannan ya
gwada ke nan duk lokacin da masu
bautar Iskoki suke mu’amula da Iskan
da suke bauta wa, su kan riƙa gabatar da
waɗansu sabbatu na daban da suka banbanta da kalmomin da
Hausawa ke magana
da su, wato su kan yi magana da iskan ne da wasu kalmomi na surkulle, waɗanda
dole sai mai hulɗa da Iskan ne kaɗai zai iya
fahimtar su. Ganin cewa ‘Yan
tauri
suna rungume da irin daɗaɗɗiyar al’adar
Hausawa wadda ta jiɓinci bautar
iskoki
shi ne ya sa suke gina kirarin ta hanyar amfani da irin waɗannan kalmomi waɗanda
da jin su, sun yi kama da kalmomin
surkulle, Bunza, (2009), ya ci
gaba da cewa,
yayin da ake yi ma ɗan tauri
take, ya kan
tashi tsaye yana kirari da nuna bajinta
da waibuwarsa ga
aikin da yake yi. Cikin
wannan lokacin ne
zai nuna ire-iren
surƙullensa ya
kuma nuna buwayarsa nan take a
gani, ido na ganin ido. Hakika
amfani da irin wannan salo na kawo kalmomin
surƙulle cikin kirari ga ‘yan tauri
ya zama ruwan dare.
Kamar yadda Mamman ke cewa a
cikin kirarinsa:
“Sakadamna, Lakadamna min dam,
Ka ce
bara, nara,
Ta kurum,
ba’adi kurum,
Kulle
kurum, kulle jigim.
Ku
kurumta maza,
Ku makanta maza.
Na tashi
kasau tambina,
Ba
kan da za kui da mu kam mu.”
(Dagajirau Garin
Malam, kirarin Mamman Zangina).
Haka nan lokacin da Lawan
S-kila ya kaɗa taken Ala na Butawa, a cikin
kirarin
nasa sai ya ke cewa:
“Bari
Lawan!
Na ji kira kai Lawan!
Ni
mai ƙala
bila, ni mai ƙala
babila,
Ni mai
arwa bila, ni mai arwa babila,
Ni mai
sadau bila, ni mai sadau babila,
Ni mai
asadau bila, ni mai asadau babila,
Ni abokin
tafiyar yaro, ba abokin dawowarsa ba.”
KIRARIN TAURI A CIKIN HAUSA TSAGWARO.
Baya ga ire-iren hanyoyin gabatar
da kirarin, ‘yan tauri guda biyu
da muka gani,
wata hanyar da suke gina kirarin kafin zuwan addinin Musulunci, ita ce ta
amfani
da kalmomin Hausa zunzurutunsu. A cikin irin
wannan fasalin kirari, ‘yan tauri
sukan yi amfani da kalmomin Hausa zalla ba tare da sun gauraya su da
kalmomin
da suka daganci na bauta ko tsafi
ba. Haka nan kuma babu wasu da aka aro daga
Larabci. Misalai a cikin wannan kirarin
“Kai! Shiru dakanta,
Na ji ka
kira maza kamar ta faɗi,
Ka bari
sai Gada ta faɗi,
Ko
ta faɗi, sai ka ji ta koka,
Sai ta kira maza sau uku,
Sai ta ce
Me ! Me !! Me !!! har sau uku,
Sannan
ka kira na Delu da Mamman,
Ni aƙ ƙodago
abun gogayya,
Abun
gogayyam maza na Delu da Mamman,
Ai gaya
ma arna gulbi,
Gulbi
nike babu jira sai ɗiba,
Ni
am Moɗa ko Kuwara sai an tausa“,
(
Mai hwara, kirarin Alhaji Goje Ƙofar Ƙaura).
KIRARIN ‘YAN TAURI
MAI NUNA MATSAYIN
MUSULUNCI.
A lokacin da addinin Musulunci ya fara kunno kai a cikin ƙasar Hausa, sai wasu
suke ganin ya kawo cikas ga al’adun Hausawa. Sallau, (2009). Ya jaddada
haka
inda yake cewa, wannan ya nuna ke nan shigowar addinin Musulunci ƙasar Hausa
da karɓarsa ga Hausawa ya sa addinin gargajiya ya yi rauni domin
Musulunci yana
da tasa alƙiblar ta
daban wajen bautar Allah. Shi ya
sa ya ke yin fito-na-fito da
harkokin addinin gargajiya
kamar bori da tsafi da camfi da sauransu. Irin wannan
fito-na- fito da addinin ya yi da al’adun Hausawa ya sa
wasu suke tunani cewa duk
wanda ke yin Sallah, to mawuyacin abu ne magani tauri ya zauna a jikinsa. Daga
bisani, sai wasu suka
fahimci cewa ba haka abun yake ba sai suka
riƙa ƙaryata
batun a cikin
kirari. Tabbacin irin wannan ya fito a cikin waƙar Mamman ɗan
ƙanan Kassu wurin
da wani wanda ake kira Yusuf Kunu ya ke
kirari kamar haka:
“Ashe dai
Mamman!
Sai ni
kunun kuɗi, kunun kukkuki,
Kunun da
ba a ba mai jego,
Ina masu
cewa ba su Sallah, ba su salati?
Wai ba su
shan huram mai Sallah,
Mamman
ni ka Sallah, ni ka salati,
Ni ka shan huram mai Sallah”
(Mamman ɗan
ƙanan Kassu, kirarin Yusufa Kunu).
KIRARIN ‘YAN TAURI DA KE TABBATAR DA AN KARƁI MUSULUNCI.
A irin wannan fasali ne a kan samu ɗan tauri ya gina kirarinsa tare
da nufin gabatar
da cewa, shi fa wannan sabon addin gadonsa ma ya yi ba haye ba. A nan zai
gwada
cewa har iyayensa ma duka
Musulmi ne. Irin wannan fasali ya fito a cikin wani
kirari na Zubairu wanda yake nuna cewa,
shi fa musulmi ne kuma bai taƙama da
wani abu banda Allah maɗaukakin sarki, kamar haka:
“Sai ni
goga, sai ni goga,
Sai ni baƙi ɗan Musulmin Allah,
Ni mai taƙama da ya Allahu, ya Allahu,
Ya sarkin
dare da rana Allah,
Ni mai sa
a sha ruwa da ƙauyen
baki,
Yanzu baƙat
Tama ta sauka a cinya”.
(Ummaru Jikan
Bagwariya, kirarin Zubairu magajin fama).
KIRARIN ‘YAN
TAURI BAYAN KANKAMAR
MUSULUNCI.
A yayin da Musulunci ya
kankama a ƙasar Hausa, aka samu harshen Larabci ya
fara yaɗuwa ta
musamman ta dalilan da suka haɗa
da koyar da addini. Wannan
lokaci ne Hausawa suka zurfafa wajen fahimtar ma’anar baƙin kalmomin waɗanda
sabon addinin ya zo da su har suka yi tasiri. A sakamakon tasirin
da kalmomin
suka yi a cikin harshen Hausa ya sa,
su ma ‘yan tauri suka fara amfani da
ire-iren
waɗannan baƙin kalmomi a cikin kirarinsu. Su kan yi la’akari
da ma’anar kalma ta
fuskar gwada ƙarfi, ko ban tsoro, da saka
fargaba, ko rantsuwa da makamantansu,
su gina kirarin kamar yadda za a gani.
AMFANI DA KALMOMIN LARABCI CIKIN
KIRARIN ‘YAN TAURI.
Daga bisani, wato bayan shigowar
addinin Musulunci sai aka fara samun gauraye
a cikin kirari, inda ake samun wasu ‘yan tauri da suka fara fahimtar
ma’anar wasu
daga cikin kalmomin da sabon addinin ya zo da su, sai suka riƙa gina kirarin nasu a
gargajiyance amma tare da gaurayawa
da wasu kalmomin da suka ara daga sabon
addini. Misali a cikin kirarin na Amadu, lokacin da Mai
hwara ya kaɗo taken nasa
da ya taso sai yake cewa:
“Ni ag
gagara dako magajin Mani,
Ni am mai
kutu-kutu uban na Hayatu,
Arna
masu cin na gobe ga sarki Allah.
Babbaƙun ruwa ni ke, na Malkatu,
Kowas
sha mu Lahira shika kwana.
Ni ak
Kura kahirin kare na Mani Dumba,
Ni
ag garo dama farauta,
Ƙabari nike wanda ba a yi ma shi taga,
Lisha’i
sallar kwana,
Dag
gareki sai rufe ɗaki.”
Shi kuwa sarki Audu da ke Bichi, lokacin da Lawan S- kila ya kaɗa nasa taken, da
ya fito a fage cewa ya
ke:
“Dakata
dai ka ji Lawan,
Bari in
ba ka addu’a ta karye ƙarafa,
Ka ce Bisimillahi
ƙaƙal,
Arahamanu ƙaƙal, Arahimu
ƙaƙal,
Ayatin
ƙal!
Miyya ƙit.
Ka ce Bismillahi
saye,
Arahamani
saye,
Saya mu Rasulullahi,
ko gida ko daji,
Wallahi
ko sun yi su dubu Lawan zan keta su”.
Daga misalan da suka gabata
mun ga yadda waɗannan ‘yan
tauri, na Amadu da
sarki Audu suka riƙa yin amfani da ire-iren kalmomin
da suka aro waɗanda sabon
addinin ya zo da su, suka riƙa saƙa su cikin
kirarin. Ire-iren waɗannan kalmomin
sun haɗa da Allah, da
Lahira, da Kabari, da Lisaha’i, da Bismillahi, da Wallahi, da
Arrahamani, da Rasulullahi, da
Aya, da Addu’a waɗanda a zahiri a
sakamakon
zuwan addinin Musuluncin ne
‘yan taurin suka same su, suka fahimci ma’anarsu,
suka kuma riƙa amfani da su yayin da suke gina
ire-iren kirare-kirarensu. Haka nan
a waɗansu lokutta a kan
samu wasu ’yan tauri da suke sako fasalin addu’a yayin
da suke kirarin. Misalin irin wannan ya fito a cikin kirarin wani da ake
kira Duna
inda yake cewa:
“Ni
dashira bawan jihadi,
Ya Allah,
ya ma’aikin Allah,
Ka
fissheni kunyar uwata,
Ya Allah,
ya ma’aikin Allah,
Ka
fissheni kunyar ubana,
Ya Allah,
ya ma’aikin Allah,
Ka
fissheni kunyar yayyena,
Ya Allah,
ya ma’akin Allah,
Ka
fissheni kunyar ƙannena,
Kiɗa
shiru, waƙa
shiru,
Hayaniyar
banza shiru.”
(Ummaru jikan Bagwariya,
kirarin Duna karan Jarman ‘Yan awaki).
Kamar yadda wasu ke sako addu’a a cikin
kirari, haka wasu kuma ke amfani
da
Kalmomin rantsuwa irin su
Wallahi. A cikin kirarin Galadima yana cewa:
“Ai tahe
nike ban hwasa ba,
Kirana
ka ke, zuwa ni ke cikin gaggawa,
Wallahi,
yaɗo nike mai ganin ƙurewar
icce,
Wallahi,
mu ka cin uban gida bara na kallo,
Mu ka sawa uba ya bar ‘ya’yan shi,
Wallahi
ba ni lambar ƙarhe,
Sai in
babu ayar Allah a cikin Ƙur’ani”.
(Lawal L. G. Jibiya, kirarin
Galadiman Tauri, Ƙofar Ƙaura, Katsina).
AMFANI DA JUMLAR LARABCI KO SASSANTA
WURIN GINA KIRARIN
‘YAN TAURI.
A sakamakon tasiri da Musulunci ya yi a cikin al’adar Hausawa ne da kuma irin
fahimtar da suka yi masa, ya sa ‘yan taurin ba su tsaya ga aron kalmomin kaɗai ba,
har sai da suka riƙa amfani da jimloli
ko sassan su waɗanda sakamakon zuwan
addinin ne suka same su, suƙa riƙa yin amfani da su, suna gina kirarin nasu. A irin
wannan fasali a kan samu ‘yan tauri su ari jimla wadda take ta Larabci ce
kai tsaye
su yi amfani da ita a cikin
kirarinsu. A nan su kan yi la’akari ne da ma’anar jimla
ko sashenta. Kwatankwacin irin wannan
ya fito a cikin kirarin Garba bayan da aka
kaɗa masa take, yana cewa:
“Kai!
Ummaru kai!!
Asalati
ya ibadal Lahi,
Sallah ta
zo malam ya zo,
Ummaru
ina matanbaya? Ina macigita?
Ga
itatuwa na Alhaji,
Itatuwa
na Jarman yanzu,
Ummaru
Jarma ya sako Karen kora tai,
Aradun
Allah komin sanin mutum muna ɓaci nai.”
(Ummaru Hassan ɗan Barunje, kirarin Garba Uban
Dawakin sababi).
A cikin wannan
kirarin Garba ya yi la’akari da matsayin
limami ne a gurin sallah,
wanda shi ne ja-gora duk lokacin da mamu suka taru za su gabatar da sallar.
Don
haka a nan Garban ya na gwada cewa fa shi jagora ne a
cikin ‘yan tauri, duk wata
harka ta tauri da za a yi sai da shi. Shi kuwa Iro a
cikin nasa kirarin cewa yake yi:
“Yanzu ka
ji ana Subahanal Lahi,
Masha
Allahu, ka ga abin da ake gudu,
Ga shi
nan ya auku,
Ni kau
abin ya yi kyau a gare ni,
Yanzu a
fadi ba daidai ba,
Yanzu a
yi ƙudundune
ba sanyi.”
(Shagari
Adahama, kirarin Iro Baban Kwari).
Kamar yadda
muka gani daga cikin waɗannan kirare
-kirare guda biyu, an kawo
wasu Jimloli da asalinsu ba na
Hausa ba ne. Wato addinin
Musulunci ne ya zo da
su. Jumlolin kuwa sun haɗa da Assalatu ya ibadallahi, da Subihanal Lahi, da kuma
Masha
Allahu da Aradun Allah.
AMFANI DA HADISI DA NASSI A CIKIN KIRARIN ‘YAN TAURI.
Bayan da addinin Musulunci ya kahu, ya samu wurin zama
ne, sai aka samu wasu
da suka karantu, suka kuma zurfafa a cikin nazarin Al’ƙur’ani da Hadissai, sannan
kuma suka fahimci
ma’anoninsu, sai suka riƙa tsakuro wasu
sassa daga ciki suna
gina kirarin kamar yadda za mu gani.
AMFANI DA HADISI CIKIN KIRARIN.
A irin wannan
fasali na kirari ne ake samun wasu ‘yan tauri da suke ɗaukar wani
Hadisi su gina kirari da shi ta fuskar ma’ana.
Misali a cikin kirarin Garba inda ya
kawo wani Hadisi da Abu Huraira ya ruwaito cewa Annabi
(SAW), ya ce “Karanta
La
haula wa la ƙuwata
illa bil Lah,-1 na
maganin cutuka casa’in da tara”. A nan ne
Garba ya yi
la’akari da ma’ana, da kuma mahimmancin
Hadisin ya gina kirarin
nasa inda yake cewa:
“Ummaru
kai!
Kai bari
in ba ka addu’ar fasa fage,
Ka ce
Bismillahi Gabas duhu, Yamma duhu,
Kudu
duhu, Arewa duhu,
Sama
duhu, ƙasa
duhu,
Idona
hasken rana,
Ummaru
kai!
Wa la
haula wa la ƙuwata
illa bil Lahi, Aliyun Azim,
---------------
1. Duba Bukhari: Hadisi na 393, littafi na 8 kashi na 75.
Ummaru mai kiɗa ma
arnan kawo”.
(Ummaru Hassan ɗan Barunje, kirarin Garba Uban
Dawakin Sababi).
GAMIN-GAMBIZAR NASSI DA HADISI.
Wannan ma
wata hanya ce da su ‘yan taurin suke bi suna gina
kirarin, inda suke
ɗauko wasu ayoyi
daga cikin Al ƙura’ani, su haɗa da Hadisi ta
hanyar la’akari da
ma’anoninsu,
kamar yadda ya bayyana a cikin kirarin
Iro, inda ya yi la’akari da
ma’anar suratul (Ikhlas) wadda ke nuna kaɗaitar ubangiji,
da (La haula----). Su ne
ya gina kirarin nasa kamar haka:
“Dakata ka
ji Adahama,
Ƙul huwallu, na tashi,
Da ikon
La haula wa la ƙuwati
illa billahi,
Ahadu
Allah, na tashi,
Da ikon
La haula wa la ƙuwati
illa billahi,
Assamadu,
na tashi,
Da ikon
La haula wa la ƙuwati
illa billahi,
Lam
yalidi, walam yulada, na tashi,
Da ikon
la haula wa la ƙuwati
illa billahi,
Walam
yakullahu, na tashi,
Da ikon la haula
wa la ƙuwati
illa billahi,
Ƙuhuwan, na tashi,
Da ikon
la haula wa la ƙuwati
illa billahi,
Ahadun,
na tashi,
Da ikon
la haula wa la ƙuwati
illa billahi,
(Shagari Adahama,
kirarin Iro baban kwari).
Shi kuwa Idi ya yi amfani da ayoyin Alƙur’ani guda biyu ne da ya ciro daga cikin
Suratul Ya’ sin da kumaSuratul Baƙara, ya haɗa su da wannan
Hadisin da ke cewa
(La malja’a wa la manja
minka illa ilaika),-2 wanda yake
nuna cewa: Babu wani
abun neman tsira
ko makoma daga gare shi banda Allah. Sannan ya haɗa da wasu
ayoyi daga cikin Al’ƙur’ani, yana cewa:
“Ya
Allahu! Ya Karimul lah!
Innama
amruhu Iza aradal lahu shai’an,
An yakunu
lahu kun fa yakun,
‘Yan
banawan tauri,
La munja
wa la munja’a illa ileka Allah,
Allahumma
haza karimus sharri,
Sanda!
Kullu nafsin za’ikatul mautu’-3
Duk mai
rai mamaci na,
Sai wanda
kwana nai bai ƙare
ba”.
(Ummar Hassan ɗan Barunje, kirarin Idi Garkuwa).
AMFANI DA AYOYIN AL’ƘURA’ANI ACIKIN KIRARIN ‘YAN TAURI.
A yayin da wasu ‘yan tauri ke amfani da Hadisi su gina kirarin, ko su haɗa hadisin
---------------
2. Duba
Bukahri: Hadisi na 327, littafi na 8,
kashi na 75.
3. Dubi Al ƙur’ani Mai
tsarki Suratul Ali Imran (3: 185).
da ayar Al ƙura’ani, wasu kuwa ayoyin ne kaɗai suke amfani da su, su gina irin
kirarin nasu. Irin wannan fasali ya fito a ciki kirarin
wani da ake kira Na Faranshi.
A ciki ya kawo suratul (Ikhlas) -4 ne gaba ɗayanta, inda ya
fara da (Bismala) kamar
haka:
“Na ce to
Bissimillahi Allah,
Na ce
Arrahamani Allah,
Na ce
Arrahimi Allah,
Na ce Ƙul huwallahu Allah,
Na ce
Ahadun Allah,
Na ce Assamadu Allah,
Na ce Lam
yalidi Allah,
Na ce Walam
yuladi Allah,
Na ce Wal
ya kullahu Allah,
Na ce
Kufuwan Allah,
Na ce
Ahadun Allah,
Na riga ku, n ace
Allah,
Ina da
mai hawa ga Doki,
Dokin da
ba hawa sai sharɓa”.
(Ummaru jikan Bagwariya, kirarin Ummaru na Faranshi).
Shi kuwa sarkin taurin sarkin Gwandu, sai ya yi amfani da
wasu ayoyi guda uku
da ya tsakuro daga cikin Al ƙur’ani, kamar haka:
---------------
4. Duba Al ƙur’ani Mai
tsarki Surat a 114.
Kai mai kasaken Tauri!
Bisimillahi wa makaru makaran,
Wa makarna
kairun makira,
Wallahu
kairun makirin,-5
Zuwa gare
ku mahassada da masu adawa.
Haka nan kuma ya kawo wata ayar a cikin wani ɓangaren kirarin
nasa inda yake
cewa:
“Bissimillahi, Falamma ra’aitahu,
Akabar lahu aƙadaina,
Waƙadana aidiyal lahu,
Waƙulna hadiyal Lahi,
Ma haza
bashara,
In haza
illa basharan,
In haza
illa malikul kairim,-6
Kai
mahassada ku je,
Ku je ku
bincika cikin Ƙura’ani,
Allah Shi
ka ɗaukaka ba ku ba”.
Daga nan sai ya ƙara kawo wata
ayar inda ya ce:
“Kai
mai kiɗin kasaken Tauri,
Bissimillahi
mai kiɗin kasaken Tauri,
---------------
5. Duba Al ƙur’ani Mai
tsarki Surat Ali-Imran ( 3: 54).
6. Duba Al ƙur’ani Mai
tsarki Suratul Yusuf (31:31).
Bissimillahi dikki, doka,
Marbuga
marbuga, mari girigi,
Ma
ilahira madaku,
Warafa’anahu makana aliyan,-7
Ai ka san
na ce ma ƙarhe,
Ko babu
lahiya shina katcewa”.
KAMMALAWA
‘Yan tauri sun
kasance daga cikin al’umar Hausawa,
da suke tsare daal’adarsu
da suka gada kaka da kakanni. Amma duk da haka shigowar Addinin Musulunci
ya sa an samu wasu
canje-canje a cikin hanyoyin
da suke gudanar da wannan
al’ada. Wannan kuwa
ya shafi har da yadda suke ginawa
da gabatar da kirarin. A
cikin wannan takarda an lalubo misalan ire-iren
kirare-kiraren da wasu ‘yan taurin
suka yi ta
hanyar la’akari da
yadda ake yin kirarin tun gabbani
zuwan Addinin
Musulunci ƙasar Hausa da
kuma yadda aka riƙa samun canje-canje
a ciki, ta
hanyar saƙo wasu baƙin kalmomi ko jimlolin daga harshen da sabon addinin ya
zo
da su. Kuma Waɗanda su ‘yan taurin suka fahimci ma’anarsu, suka yi amfani
da
su wurin gina kirarin nasu.
---------------
7 Duba Alƙur’ani Mai
tsarki Sratul Maryam (19:58).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.