Maƙalar da aka Gabatar a Taron ƙara wa
juna sani na ƙasa da ƙasa a kan Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa A Yau Wanda
Hukumar Gidan Tarihi Da Al’adu ta Jihar Katsina ta Shirya Tare da Haɗin Guiwar
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua a ranar 25-26
ga watan Yuni 2013 a babban ɗakin taro na Jami’ar.
Zama da Maɗaukin Kanwa Shi Ke Sa Farin Kai:
Nason Baƙin Al’adu Cikin Al’adun Hausawa Ta Fuskar Aure
Dano Balarabe Bunza
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Phone No. 07035141980
E Mail. danobunza@yahoo.com
Tsakure
“Ka ba manya kashi yara na
ganin damarka’. Aure na cikin matakan rayuwar Hausawa guda uku kuma na farko.
Wannan maƙalar ta yi tsokaci kan al’adun auren Hausawa na gargajiya da kuma
nason da baƙin al’adu suka yi a cikinsu daga neman aure har zuwa kai garar
biki. Takardar na ɗauke da canje-canjen da suka kutso kai a cikin lamarin auren
Hausawa suka yi tasiri ta fuskar taɓarɓarewa. Takardar na tare da rakiyar
bayanai da misalai daga wasu makaɗan bakan Hausa gwargwadon hali.
1.0 GABATARWA
Aure na ɗaya daga cikin matakan
rayuwa guda uku da aka sani da suka haɗa da aure da haihuwa da kuma mutuwa da
masana suka yi wa bante daidai kwankwasonsa ta fuskar yin bayani mai gamsarwa.
Wannan bai tsaya ga al’ummar Hausawa kaɗai ba, ya haɗa da al’ummomin duniya
baki ɗaya. Wannan maƙala za ta yi tsokaci a kan nason baƙin al’adu ta fuskar
aure a cikin al’adun Hausawa. Baƙin da wannan maƙala za ta yi tsokaci kansu ta
fuskar nason al’adunsu na aure a cikin na Hausawa ba su zarce Turawa da
Indiyawa da Faransawa, da na cikin gida da suka haɗa da Yarbawa da Ibo da
sauran irinsu ba. Wannan maƙala za ta kalato baƙin al’adun da suka shigo cikin
na Hausawa suka yi kaka-gida a ɓangaren lamarin aure ta fuskar taɓarɓarewa. Ga
abubuwan da zan gabatar kamar haka:
2.0 MA’ANAR AL’ADA
Masana al’ada sun daɗa juna
sani a fagen ba da ma’anar kalmar al’ada inda wasu ma sun kawo asalin kalmar a
taƙaice inda aka ce kalmar al’ada ba Bahaushiyar kalma ba ce. Aro ta aka yi
daga Larabci. A Larabci tana nufin wani abin da aka saba yi ko ya saba wakana
ko aka riga aka san da shi. A harshen Hausa kuwa kalmomin da suka fi kusa da
al’ada su ne, sabo da gado da hali da sada da gargajiya. A ɓangaren ma’ana
kuwa, an ce “Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan adam tun daga haihuwarsa
har zuwa kabarinsa. A ko’ina mutum ya samu kansa duk ɗabi’a da ya tashi da ita
tun farkon rayuwa ya tarar da wurin da ya rayu ko yake rayuwa, ita ce al’adarsa
da za a yi masa hukunci a kai. Babu wata al’umma da za ta rayu a doron ƙasa
face tana da al’adar da take bi, kuma da ita ake iya rarrabe ta da wata da ba
ita ba”. Haka kuma al’ada “Wata tsararriyar kimiyyar rayuwa ce da ta shafi
rayuwar mutane tun daga haihuwarsu har zuwa kabarinsu”. Falsafar al’ada da
kimiyyarta ya ƙunshi fasahar mutane da aƙidojinsu da taskar ayukkan da suke
sarrafa gaɓoɓinsu da abubuwan da suka yi imani da su. Waɗannan abubuwa ko dai
an gaje su ne, ko ƙirƙiro su aka yi, ko an garwaya su da wasu baƙin al’adu, duk
suna cikin hurumin nazarin al’ada.
Akwai ƙanshin gaskiya a cikin
zancen da aka faɗa na cewa kalmomin sabo da gado da hali da sada da gargajiya
sun fi kusa da ma’anar al’ada domin kowane daga cikinsu akwai abin da Hausawa
suka faɗa a kansa. Da farko ana cewa sabo turken wawa da kwas saba kai gida sai
ya kai. Gado kuma ana yi masa kirari da cewa, ‘gadon gida alali ga raggo’ da
‘gado bai wofinta’. Shi kuma hali ana yi masa kirari da ‘hali zanen dutse’ da
‘halin mutum guzurinsa’. Sada kuma kalma ce da ake amfani da ita a cikin
maganganun yau da kullum da kuma waƙa. Misali akwai wurin da ake furta kalmar
sada idan ana son a nuna ko da yaushe. Ana ce wa yaro ‘Sada haka kake’. Ma’ana
ko da yaushe haka yaron yake. Wannan kalma na da kusancin ma’ana da sabo. Gambo
mai waƙar ɓarayi ya furta kalmar sada a cikin waƙar da ya yi wa Tudu Tsoho inda
ya ce:
Gambo:“ In nig ga Tsoho ya kula
min,
:Sai in yi wurin ‘yan koli
sada,
:Ina cinikin banza da wofi,
: Ko an bar min ban biyanai”.
Kalmar gargajiya kuma na fitowa
a bakin makaɗan Hausa domin nuni ga abin da aka gada tun kaka da kakanni. Ɗanƙwairo
da Sarkin Taushin Sarkin Katsina sun yi waƙa kan al’adun gargajiyar Hausawa
inda suka kawo kalmar a cikin waƙoƙinsu. Ga abin da Ɗanƙwairo ya ce:
Ɗanƙwairo:Kar mu sake mu mance,
:Mu bi al’adunmu na gargajiya
Shi kuma SarkinTaushin Katsina
ya kawo kalmar gargajiya a cikin waƙarsa kamar haka:
Gindin waƙa: Nufinta ne wasan
gargajiya,
:Da za ta sa mu ƙara fahintar
juna.
A wani wuri kuma an ba da
ma’anar al’ada da cewa, “Hanyar rayuwar al’umma da jinin haila da wani irin
hali daban na mutum da kuma magani ko tsafi”.
A wata mai kama da wannan kuma
cewa aka yi “Al’ada ita ce abar da aka saba yi yau da gobe”
Al’ada ita ce, sababbiyar
hanyar rayuwa wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.
Al’ada dai ita ce dukkan
hanyoyin rayuwa. Al’adar jama’a ta ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi zaman
al’umma. Don haka al’ada ta haɗa da addini da ɗabi’u da tsarin zaman iyali da
tsarin mulki da tsarin ilmi da dai sauransu. Hanyoyin shaƙatawa da nishaɗi
kamar su raye-raye da waƙe-waƙe da kiɗe-kiɗe da sassaƙe-sassaƙe ko ƙere-ƙere ba
su ne kawai al’ada ba.
Haka kuma, akwai wata ma’ana da
wani ya ba da inda ya ce “Al’ada ita ce dukkanin cikar jimillar gwaninta ko
fasahar waɗansu mutane, da kuma abubuwan da suka faru gare su ko abubuwan da
suka saba da su, da abubuwan da suka daraja (ba muhimmanci), da irin muradin da
suke son su cimma, da kuma matsayin da suka kamala bayan shekarun da suka yi
suna ƙoƙarin cimma nasara kan muhallinsu bisa ga matuƙar iyawarsu kuma domin
babban amfani da fa’ida gare su.
3.0 MENE NE AURE?
Masana da manazarta sun ba da
ma’anar aure gwargwadon fahimta kuma kowane aka ɗauki ma’anar da ya bayar za a
gamsu da ita. Ga wasu daga cikin ma’anonin aure daga masanan da manazartan
kamar haka:
Aure wata hanya ce ta ƙulla
zaman tare tsakanin namiji da mace ba tare da iyakancewa ba, sai in mutuwa ta
raba wanda ake tabbatarwa ta amincewar ma’aurata da waliyansu da kafa shaidu.
Aure alaƙa ce ta haliccin zama
tare tsakanin namiji da mace. Ana yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami
asali da mutunci da kiwon iyaye. Kuma shi ne maganin zina da samar ‘ya’ya
marasa iyaye.
4. DALILAN DA SUKA HADDASA NASON BAƙIN
AL’ADU CIKIN AL’ADUN HAUSAWA NA AURE
Babu shakka akwai dalilan da
suka haddasa nason baƙin al’adu a cikin al’adun Hausawa a ɓangaren aure. Wani
abin kula a nan shi ne, dalilan sun haɗa da na ciki dana waje. Na waje su ne da
suka fito daga ƙetare. Na ciki kuwa su ne na gida, wato na tsakanin Hausawa da
maƙwabtansu. Ba zan tsaro waɗannan dalilan tare da bayanai ba sai dai in kawo
su kara zube saboda abubuwa ne da aka sani ba waɗanda ke shige wa al’umma duhu
ba. Daga cikin dalilan akwai: Shigowar Turawa da mulkin mallaka da auratayya
cikin wasu ƙabilu da cinikayya da canjin lokaci da gwagwarmaya da baƙin da ba
Hausawa ba da sauransu.
5.NASON BAƙIN AL’ADU CIKIN AL’ADUN
HAUSAWA TA FUSKAR AURE
Hausawa mutane ne da ke da
al’adu na gudanar da matakan rayuwarsu guda uku da suka haɗa da aure da haihuwa
da kuma mutuwa. A lokacin aikata kowane ɗaya daga cikin waɗannan matakan rayuwa
nasu, sai aka ci karo da al’adun maƙwabtansu na nesa da na kusa suka fara naso
har suka nashe a cikinsu ta hanyar so da ƙi. A nan ina nufin sun ɗauki wasu da
saninsu wasu kuma ba da saninsu ba domin an ce ɗabi’a na satar ɗabi’a.
Zancen nason baƙin al’adu cikin
al’adun Hausawa na aure ba tatsuniya ba ne. Ko wanda ba Bahaushe ba aka
tambaya, ko wasu al’adu sun yi naso cikin al’adun Bahaushe na aure? Zai amsa da
‘E’. Hausawa na da al’adun da suke gudanarwa a cikin lamurran aurensu a gargajiyance.
Sai dai a kwana a tashi aka sami kutsowar baƙin al’adu har suka yi kaka-gida
cikin na Hausawa. Ko da yake an fi samun baƙin al’adu a lokacin shirye-shiryen ɗaurin
aure da kuma lokacin ɗaura shi. Ga bayanin wuraren da takardar ta hango naso a cikinsu
da yadda nason ya kasance:
5.1 NASON ZAMANANCI CIKIN AL’ADUN NEMAN
AURE
Hausawa na cewa “Zamani riga
ne”. Ba shakka zamani ya kawo canje-canje masu yawan gaske a cikin auren
Hausawa tun daga neman aure har zuwa ɗaurinsa. Dalilin shigowar zamani ya kawo
sababbin abubuwa cikin sha’anin auren Hausawa da kuma yin watsi da wasu
tsofaffin abubuwan da aka saba da su. Alal misali, a zamanin da iyaye ke nema
wa ‘ya’yansu aure ga iyayen yarinyar da suke son ya aura. Ba yara ke zaɓi da
kansu ba a da, iyaye ke yi musu zaɓin wadda za su aura domin yaro bai san abin
da ya fi cancanta gare shi ba bale ga waninsa. A kan wannan ne Hausawa suka ce
“Ta yaro kyau gare ta ba ta da ƙarko”. Ba a zancen neman aure kaɗai ba, akwai
nason zamananci a sauran matakan neman aure. Waɗannan sun haɗa da kayan toshi
da kayan zance da dukiyar aure har da sa rana. Zamananci ya yi tasiri sosai
domin ana sanya ranar ɗaurin aure, sai yaron da ke neman auren ya ce ranar da
aka saka domin ɗaura aurensa ba ta yi masa ba domin wata ‘yar matsalar da ba ta
kai ta kawo ba,ba tare da la’akari da yi wa iyayensa ɗa’a ba. Wannan na ƙara
tabbatar da nason zamananci a cikin matakan neman auren Hausawa. Ai shi ya sa
Ɗanmaraya Jos ya yi waƙar biyayya ga iyaye tare da barin saɓa musu. Ga abin da
ya ce:
“‘Yan yara ku bi ma iyaye,
Ku bi malaman makaranta,
Irin haka Allah ke so”.
Bayan wannan kuma, akwai wata
mawaƙiya, Fati Nijar a cikin waƙara mai suna Alan Gidigo da ta ƙara tabbatar da
zancen da ke sama, kan cewa zamani ya yi naso ƙwarai cikin matakan neman aure
na Hausawa. Ta goyi bayan ‘ya’ya mata da su yi tsaye su zaɓi wanda suke so ba
wanda aka so musu ba. Ke nan a nan tana horo ne ga ‘ya’ya mata da kada su
kuskura a yi musu zaɓen tumun dare. Ga abin da ta ce:
Jagora: Ke yarinya zaɓi dogo
‘Y/Amshi: Ke yarinya zaɓi dogo
Jagora: Zaɓi dogo na Ɗanwuro
dokin Iyani
‘Y/Amshi: Ala gidigo”.
Idan aka yi la’akari da abin da
Fati Nijar ke kira kansa za a fahimci tana yi ne domin ‘ya’ya mata su yi wa
iyaye bore kan cewa zaɓar musu mazan aure da ake yi ya ishe su don haka a bari
kowa ta zaɓa wa kanta mijin da take so da aure.
5.2 NASON SUTURA
Wannan ba abu ne da ke ɓoye ba
bale a yi dogon bayani kansa. Idan ba a samun sa gidan kowa da kowa, zan ce
mafi yawan gidaje ana samu. Daga cikin suturun, wasu na baƙi ne wasu kuma na
gida ne. Akwai nason tufafin Turawa da Larabawa da Indiyawa da Faransawa da
sauransu da yawa. Wannan kuma ya faru ne sanadiyar kalle-kallen fina-finan waɗannan
mutane a cikin talabijin da hotunan kalanda. Ai mafi yawa daga cikin mawaƙan
Hausa na fina-finai da ke wannan ƙasa tufafinsu na mutanen ƙetare ne musamman
mata. Akwai ɗinki kala-kala da Hausawa suka ɗauka matsayin baƙin al’adu a
lokacin bikin aure da suka haɗa da fitted da umbrella da pre-fitted da gown da
half gown da stella da show me your back da buba da wasila da fitted gown da
sauransu. Da jin waɗannan sunaye babu kokanto sunaye ne na wasu al’ummu da ba
Hausawa ba. A nan ne za a ga yarinya ta ci ado, idan aka gan ta a cikin bidiyo
za a zaci Ba’indiya ko Balaraba ko Baturiya idan aka yi la’akari da tufafin da
ta sanya. Idan aka bincika za a tarar Bahaushiya ce wata ƙila ma ta Kebbi ko
Kano ko Katsina. Mai son gane wa idonsa ya je wuraren da aka ambata a sama a
lokacin bikin aure zai tabbatar da cewa baƙin al’adu sun ƙara wa Borno dawaki ta
fuskar al’adun aure Hausawa.
Haka kuma, idan aka dubi gida
Nijeriya za a ga irin saka/sanya wannan sutura ta wasu ƙabilu ta yi naso a
cikin al’adun Hausawa na aure musamman Yarbawa da Inyamurai, duk da ba nasu kaɗai
suka yi nason ba. Hausawanmu sun ɗauki al’adar Yarbawa ta ɗinka tufafi iri ɗaya
ba tare da samun bambanci ba a lokacin bikin aure. Yarbawa na kiran wannan
Oshobe ko Anko. Bayan wannan ma abin haushi shi ne ɗunkin lalaci ban a mutunci
ba. Akwai wani ɗunki da ake yi wa yara mata budare mai suna sakaɗa-hannunka–masoyi
a inda za a iya ganin hamutar yarinya ko da daga nesa bale kusa. Akwai a matse ƙugu.
Akwai irin waɗannan ɗunkuna da yawa Ba wannan kaɗai ba. Zamani ya yi sanadiyar
canje-canje masu yawan gaske a cikin al’adun Hausawa na ta fuskar aure. Haka
kuma, al’adar ɓarnar kuɗi a ɓangaren ɗunka tufafi a lokacin bikin aure ya zan
yayi. Kai! Kitson da ‘yan mata ke yi ma ba na Hausawa ba ne a lokacin bukukuwan
aure. Ko dai ya kasance na Yarbawa ko na Ibo ko wasu ƙabilu na daban, kuma
kowane da nasa suna. Duk abin da aka faɗi a ɓangaren mata ana samun wani abu a
na maza sai dai, abubuwan sun fi naso a ɓangaren dangin Shaiɗan (mata). Haka
kuma a Katsina akwai wata fita da ake kira Arabian night inda ake yin fitar
Larabawa a lokacin bikin aure. A ɓangaren maza jallabiya fara suke sanyawa mata
kuwa baƙa suke sanyawa. Don gudun faruwar wannan ne Sarkin taushin Katsina ya
yi wata waƙa ta ‘FESTAC 77’ inda yake horon Hausawa yara da manya yana cewa:
Jagora:Yara-yara ‘yan
makaranta,
: Manya da ƙanƙananku ku ɗau
horona
‘Y/Amshi: Ku kama al’adu na
iyayenku
: Kar ku yarda da aikin banza
Jagora: Sai ku kama al’adu na
iyayenku,
‘Y/Amshi: Kar ku yarda da aikin
banza
Gindin Waƙa: Nufinta ne wasan
gargajiya,
:Ta sa mu ƙara fahintar juna.
Wannan mawaƙiya yi horo ga dukkan al’ummar Hausawa tare da jan hankalinsu domin
su riƙe al’adunsu da hannu biyu ba tare da sanya wasa ko abin da zai aibata
al’adun ba kuma, kar su aminta da wasu baƙin al’adu bale ma su fifita su a kan
nasu. Ga abin da ya ƙara faɗi dangane da wannan:
Jagora:Gwannati tana da yawa
jama’a,
: Gargaɗi ga babba da yaro,
‘Y/Amshi: Kowa ya kama
al’adunshi,
:Akwai waɗansu mutane,
:Sun yada nasu sun bi na ‘yan
cirani.
Tabbas gaskiya ce makaɗa ya faɗa
domin akwai waɗanda suka fifita al’adun wasu a kan nasu ba tare da yin la’akari
da aibin watsi da nasu ba, ta hanyar rungumar na wasu. Allah Ya sawwaƙa!
5.3 NASON AL’ADUN KIƊA DA WAƙA
Wannan ma ba abin musu ba ne
domin ya zama ruwan dare game duniya a ƙasar Hausa. A wannan zamani nason baƙin
al’adu na kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe sun yi naso sosai a cikin al’adun auren
Hausawa kuma ba mai tada hannu ya ce ba haka abin yake ba. A taƙaice, sanin
kowa ne cewa mafi yawan Hausawa sun yi watsi da kaɗe-kaɗen gargajiya da
raye-rayensu suka cirata zuwa ga na baƙi. Mafi yawan kayan kiɗan Hausawa an
fara watsi da su domin sun zama tsohon yayi, aka rungumi waɗanda ba su kai su
daraja ba kamar yadda Sarkin Taushin Sarkin Katsina ya yi bayani. A zamanin da
ake ciki an yi jana’izar mafi yawa daga cikin kayan kiɗan Hausawa da suka haɗa da
kalangu da ganga da duma da ƙaho da kuge da kurya da kotso da dundufa da taushi
da sauransu sai dai kaɗan da ba a rasa ba. Ko su ma domin kada a rasa wuta ne a
maƙera ko kada a rasa nono ruga. Ba shakka an koma ga kayan kiɗan zamani irin
jita da fiyano da gangunan bigala da sauran irinsu. Har ta kai ga ba a gayyatar
makaɗin da ke amfani da kayan kiɗan gargajiya zalla sai can ba a rasa ba ko shi
a ƙauyuka da kaɗan a cikin birane domin ƙauyawan da suka kwararo ciki. Mafi
yawa idan aka saurari makaɗan Hausa tare da yin la’akari da kayan kiɗansu za a
tarar sun saka kayan kiɗan zamani cikin kiɗan da suke yi. Misali, Ɗandago da
Mai Asharalle a Katsina da sarkin Ɗori a Sakkwato da wasu da dama. Mafi yawan
kaɗe-kaɗen da ake yi a cikin waƙoƙin bikin auren Hausawa sigar waƙoƙin baƙi
suke ɗauke da su.
Idan aka yi zancen waƙe-waƙe
kuwa, ba sai an yi dogon bayani ba domin abubuwa ne da aka shedar a wannan
zamani. Maimakon waƙar gargajiya da sautin gargajiya, sai aka musanya da na baƙi
inda za a ji muryar Turawa ko Indiyawa ko Larabawa da sauran ‘yan ƙasa maƙwabta
irin Yarbawa da Ibo da sauransu. Idan aka yi zancen rawa ma haka abin yake
kamar sauran bayanan da suka gabata a ɓangaren kiɗa da waƙa a cikin bikin auren
Hausawa.
5.4 NASON FATI DA FIKINIK
A da, ba fati ko fikinik
Hausawa ke yi ba. Abin da suke yi shi ne ‘Ajo’ domin taimaka wa ango domin
samun abin tarbon amaryarsa. Maimakon wannan sai aka sami nason baƙin al’adu na
yin fati da fikinik a lokacin bikin auren Hausawa. Fikinik ba komai ba ne sai
iskancin da ake yi a cikin daji da Hausawa suka ara suka yafa domin ganin an yi
da su ba tare da an bar su a baya ba, kuma ba tare da sanin manufarsa ba. Ba
komi ya haddasa wannan ba sai kalle-kallen fina-finan da ake yi na zamani. Wani
abin da ya kamata a sani a nan shi ne, babu ɓarnar da ba a yi a wajen fati da
fikinik. A daji ake yin fikinik. Fati kuwa, a cikin gari ake yin sa. Sai dai
saboda ci gaban mai gainar rijiya da ya Hausawa suka samu na ɓatar basira, an
fara barin garin da ake bikin aure a je wani gari a yi hayar otel domin a yi
fati can. A can ne mafi yawan samari da ‘yan mata ke kinkan da zina, abin da ke
sanadiyar gurɓatar tarbiyyar al’umma baki ɗaya. Za a fahimci cewa waɗannan
al’adu na waje ne ba na gida ba, sun yi nason gaske a cikin na Hausawa musamman
a bukukuwan aure.
5.5 NASON SHAYE-SHAYE
Shaye-shaye kala-kala ne. Akwai
na ruwa da kuma sandararre. Ban ce Hausawa ba su shaye-shaye ba sai dai baƙin
al’adun shaye-shayen wasu al’ummu sun yi naso sosai ga rayuwarsu a lokutan
bukukuwan aure. Ya dace a san da cewa, shaye-shayen da Hausawa ke yi ba domin
bukin aure ne ko wani abu da ya yi kama da haka nan ba. Suna sha ne saboda wata
buƙata ta daban musamman wani aiki da ya kai wa mai shi gaya. Su kuma baƙin na
yin shaye-shaye ne da nufin jin daɗin rayuwa da kuma nuna wayewa. Idan aka dubi
mawaƙan waje irin Bob Marley da Michael Jackson da sauransu, suna sha ne domin
jin daɗin gudanar da aikinsu na waƙa. Sai dai kayya! Ganin wannan a cikin
na’urorin kallo ya sanya wasu Hausawa rungumar sa ba tare da wata fargaba ba.
Sanin kowa ne cewa shaye-shaye aibi ne. Wasu na yin shaye-shaye ne domin samun
raguwar damuwar rayuwa, suka manta da naƙasar rayuwarsu da suka samu. Idan aka
yi la’akari da cikin gida Nijeriya za a ga cewa Hausawa sun sami nason al’adun
baƙin da ake tare da su kamar Yrbawa da Ibo da sauran ƙabilun da ake
gwagwarmayar rayuwa tare das u. Nason baƙin al’adu ya sa shahararren makaɗin
nan Marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina, a waƙarsa mai suna ‘A shs ruwa’ yake
nuna irin holewar da aka saba da ita sanadiyar mu’amala da baƙi. Ga kaɗan daga
cikin waƙar:
Jagora: Ya bisimil ilahi,
‘Y/amshi:Jalla ubangiji, sha
ruwa,
Jagora: Ka ji karatun masu
bugun ruwa,
Wa’anda ke zikiri a kuloniyal,
‘Y/Amshi: Sha ruwa ba lahani ba
ne,
Jagora: A nan muke sallarmu ta
jumma’a,
‘Y/Amshi: A sha ruwa ba lahani
ba ne
……………………………………..
Allah Ya jiƙan rai! Wannan ya
nuna ken an waɗannan abubuwa sun faru ne sanadiyar nason baƙin al’adu, kuma
yakan iya faruwa ga kowa domin tsaka mai wuyar sani ce.
5.6 NASON RASHIN TARBIYYA
Na yi ƙudurin bayyana irin alaƙar
da ke tsakanin miji da matarsa da kuma iyayen miji da matar. A da, ba yadda za
a yi a sami rashin kirki tsakanin surukai da sarukarsu, wato matar ɗansu, a
bayyane kuma da gangan said a aka fara samun nason baƙin al’adu. Idan aka yi
la’akari da wannan alaƙa a wannan zamani za a ga bambancin da ke akwai ba kaɗan
ba ne. Wulaƙanta iyaye al’adar mutanen banza ce. Haka kuma Turawa na daga cikin
waɗanda ke wulaƙanta iyayensu musamman idan sun cimma shekarun tsufa. Sai ga
shi wannan al’ada ta yi naso cikin al’adun Hausawa na aure inda za a sami matar
yaro ba ta san girman iyayen mijinta ba bale ta girmama su. Ko miji ya tarar da
matarsa ta ci mutuncin iyayensa, ba zai yi wani bincike ba, sai ya faɗa
iyayensa da faɗa wai su ke da laifi musamman wasu ‘yan boko da ke barin
iyayensu a ƙauyuka su koma birni suna kece raini da jin daɗi iri-iri. An sha
samun matsalar rashin ɗa’a da matar miji ke yi wa iyayensa, wani lokaci ma har
kotu matar ɗa ke kai iyayensa domin ganin sun kula mata kuma, suna damuwarta. A
fahimtata ɗan ne ya wulaƙantar da iyayensa ba matar ba. Ita kuma matar halin da
ta nuna a gidan surukai ya tabbatar wa al’umma cewa ba a koyar da ita tarbiyyar
kirki ba a gidansu. Duk waɗannan halaye da ake samu sun faru ne sanadiyar nason
baƙin al’adu a cikin al’adun Hausawa na aure. A taƙaice dai, duk zama ne da maɗauki
kanwa ya sa kai ya yi fari.
6. KAMMALAWA
Gaskiya dokin ƙarfe! Yadda
yanayin zamantakewa yake shi ne duk lokacin da mutum ya yi sake babu abin da za
a yi masa face sakiya. Riƙon kirki ga abin da yake naka na sa shakku a zuciyar
mai laɓaɓen ya canza maka naka tare da fargaba, duk da yake an san da cewa ɗabi’a
na satar ɗabi’a. Wasu baƙin al’adu sun zama tarnaƙi ga ɗorewar na Hausawa
saboda nason da suka yi mai muni a cikinsu. Da ma Hausawa sun ce “Bala’i
maganinka roƙon Allah”. Wannan ya yi daidai da maganar da Sani Sabulu na Kanoma
ke faɗi cewa:
Jagora: A zuba zuwa ya ishi mai
hankali
………………………………......
Ba shakka na gaba idon na baya
ne. Kuma in kunne ya ji, jiki ya tsira.
Baƙin al’adu sun yi wa Hausawa
babbar ɓarna saboda nason da suka yi a cikin al’adun aurensu har suka kai ga taɓarɓarewa.
Don haka a fahimtata baƙin al’adun da suka yi naso a cikin al’adun Hausawa na
aure sun kasance kamar abin da Sani Sabulu ya faɗa a cikin waƙarsa inda yake
cewa:
Jagora: Reza nike mai kaifin
baki,
: Kowa ya hau ni karkace ya faɗi,
:Kafin ya farga rainai ya ɓaci.
Dangane da haka ana iya cewa
nason baƙin al’adu cikin al’adun Hausawa na aure ya zama ma Hausawa reza yanke
baƙauye. Don haka ina mafita?
1 Comments
Muna godiya.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.