Ticker

6/recent/ticker-posts

Tanade-Tanaden Tsafin Maguzawa A Al’adunsu Na Aure Da Haihuwa

Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2015) “Tanade-Tanaden Tsafe-Tsafen Maguzawa a Al’adunsu na Aure da Haihuwa.” Kadaura Journal of Hausa Multi-Disciplinary Studies Maiden Edition Vol. 1 No. 1 Department of Nigerian Languages & Linguistics, Kaduna State University, Pages 131 – 140

Tanade-Tanaden Tsafin Maguzawa A Al’adunsu Na Aure Da Haihuwa

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan Ph. D

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe
Jami’ar Jihar Kaduna.
e-mail: ibrasskg@gmail.com
Tel: 0803 6153 050

1.0 GABATARWA

Rayuwar Maguzawa da tsafi kamar dangantakar tsoka da jini ce. Wannan ne ma ya sa ake ganin sunan da ake kiran su ya bambanta da na sauran ’yan’uwansu Musulmi waɗanda suka Ƙaurace wa wannan rayuwa ta tsafi. Kasancewar tsafin da suke aiwatarwa yana da alaƘa da rayuwarsu gaba-ɗaya, Maguzawa sun yi tanadin tsafe-tsafe iri-iri waɗanda ke yi musu jagoranci a hanyar neman abinci da magani da sana’o’i da wasanni da tsaro da dai duk wani abu da ya shafi rayuwa ta yau da kullum.

MaƘasudin wannan nazari, shi ne ƘoƘarin gano irin tanadin da Maguzawa suka yi wa tsafi a wasu daga cikin matakan rayuwarsu na aure da haihuwa. An yi tunanin keɓe nazarin ga aure da haihuwa saboda a tabbatar da dugadugan nazarin wurin duban irin yadda tsafi yake da tasiri a lamurran da suka shafi murna da jin daɗi a rayuwar tasu. A taƘaice, nazarin zai yi ƘoƘarin tabbatar da hasashen da ke nuna cewa tsafi wani ginshiƘi ne da ke ɗauke da rayuwar Maguzawa. Wato bai keɓanta ga bauta kawai ba.

2.0 TSAFI

Manazarta yanayin tunani da imanin Hausawa sun karkasa addinin gargajiya na Bahaushe zuwa gida uku (Ibrahim 1982, Bunza 1990 da 1995). Waɗannan kuwa, su ne Bori da Camfi da kuma Tsafi. Daga cikin waɗannan rassan, kusan a ce tsafi ya fi sauran jagorancin rayuwar Bamaguje. A ra’ayin Bunza (2006:35), tsafi na nufin bin wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi wa iskoki hidima, da yanka, da bauta domin biyan wata bukata ko samun wani amfani ko tunkuɗe wata cuta.

Nau’o’in tsafi ga Maguzawa ba su da iyaka musamman da yake iskokin da suke bauta wa sun bambanta. Kowane rukuni na Maguzawa da irin hanyoyin da suke bi wurin aiwatar da tsafe-tsafensu ta la’akari da abin da suka gada daga iyaye da kakanni ko tasirin wurin zama ko wata fahimta ta musamman. A wajen bautar tsafe-tsaten Maguzawa ne iskokin da ake bauta wa suke bayar da laƘanin magungunan da za a harhaɗa, a sarrafa don a sami biyan bukata. Wannan yakan zama wani abin sirri ga jagoran wannan tsafin ko mutanen gidan da ke aiwatar da tsafin. Ga sauran zuri’ar gida ko mabuƘata, sai dai kawai a ba su magani a lokacin da buƘata ta taso.

3.0    TSAFE-TSAFEN DA SUKA SHAFI AURE

A rayuwa ta yau da kullum, samun ma’anar kalmar aure abu ne mai sauƘi ga duk mai hankali da aka tuntuɓa, ba masana kaɗai ba. Wannan ya kasance haka ne domin mu’amala da ake yi ta abin da kalmar ta Ƙunsa a kowace rana ko kowane lokaci. Ko da baligi bai sami kaiwa ga yin aure ba, to yana da makusanciyar alaƘa da ita ko masu aiwatar da rayuwarta ko ma abin da take ɗauke da shi. To amma a nazari irin wannan, akwai bukatar samar da abin da zai iya karɓuwa a ilmance. A taƘaice muna iya cewa, aure hanya ce ta rayuwar da ake so ta zamo mai ɗorewa tsakanin mace da namiji wadda ake ginawa ta hanyar shimfiɗaɗɗun Ƙa’idoji da al’umma ta tanada waɗanda kan haifar da nishaɗi tsakanin ma’auratan da taimakon juna da samar wa ’ya’yansu asali da kyakkyawan reno.

A al’adar Maguzawa, akwai matakai daban-daban da ake aiwatar da tsafe-tsafen da suka danganci aure tun daga neman aure har zaman auren. Wasu daga cikin su ana aiwatar da su ne saboda biyan bukatar rayuwa ko don a nuna buwaya ko don kariya ko kuma don a tabbatar da abin da al’ada ta tanadar wanda ya shafi kare zuri’a daga gurɓacewa.

3.1 Magungunan Tsafe- tsafen Farin Jini da Neman Aure

Magani muhimmin abu ne a rayuwar ɗan Adam. Rayuwa ba ta taɓa gudana ba tare da magani ba (Abdullahi 2000). Idan ba a nemi magani don warkar da cuta ba, za a nema don kariya, ko cutarwa, ko kuma biyan bukatar rayuwa. Magungunan farin jini na neman aure sun faɗo a ƘarƘashin rukunin magungunan biyan bukatun rayuwa.

Hausawa na cewa, “Idan kana da kyau ka Ƙara da wanka.” Maguzawa mutan ne da suka ba irin wannan magani na farin jini muhimmanci a rayuwarsu. Ko ba komai, sun yarda da akwai miyagun mutane ko maƘiya da ke sha’awar ganin rayuwar wani ta wulaƘanta. Tsoron shiga tarkon irin waɗannan miyagu ko abokan hamayya yakan sa su samar wa ’ya’yansu maza da mata magungunan farin jini dangane da lamarin aure. Haka kuma, abin takaici ne musamman ga budurwa a al’umar Maguzawa ta wuce munzalin aure ba tare da ta samu mai sonta ba.

Gano ainihin tushen magani ko mahaɗin magani na mutane irin Maguzawa abu ne mai wuyar gaske, musamman da yake lamarin ya Ƙunshi sihiri da tsafe-tsafe iri-iri. Duk da haka an gano cewa, samari suna neman magungunan farin jinin ’yanmata ne daga tsoffi ko kakanninsu. Saurayin Bamaguje ba ya jin kunyar gaya wa kakansa labarin budurwar da yake so da Ƙalubalen da yake fuskanta na gwagwarmaya da sauran samari wajen nemanta. Maganin da samari suka fi yi na jan hankalin budurwa ko farin jini ya shafi yin hayaƘi kafin a fita dandali.[1] Haka kuma wasu na shafa wani magani da aka haɗa da mai a ce su yi ƘoƘarin taɓa budurwar da suke so da maganin. Da zarar an yi haka, ta so shi ke nan har abada. A wannan ranar ma tana iya bin shi su kwana tare.[2] Wasu nau’o’in magungunan kuma garin magani ne za a kaɗa cikin ruwa, saurayi ya wanke fuska da ruwan. Idan ya fita dandali shi ’yanmata za su yi ta sha’awa a wannan ranar har sai ya darje ya zaɓa.

Su kuma ’yanmata sun fi samun irin nasu magungunan farin jini ne daga wurin iyayensu mata ko kakanni mata. A sakamakon ba lamarin muhimmanci da Maguzawa suka yi, tun yarinya tana goye ake sa mata maganin farin jini a cikin abinci ko abin sha, don kawai ta tashi samari suna son ta. Haka kuma idan iyaye mata da kakanni suka ga alamar sa’o’in budurwa suna ta fito da maza ita ba ta kawo kowa ba, to akan tashi tsaye wajen neman magani. Ire-iren waɗannan magungunan sukan shafi tsafe-tsafe ne na gargajiya wanda su ke bayar da saƘesaƘi da sayyun da za a yi amfani da su. Maguzawa sukan yi wa budurwa hayaƘi in za ta tafi dandali wurin wasa ko in za a halarci hidimar wani buki na Ƙawaye ko dangi. Idan waɗannan magunguna suka ci, to za a ga samari suna ta karakaina a kanta. Wani lokaci ma har da faɗace-faɗace, musamman a lokacin da wani daga cikinsu ya kasa sauran.

3.2 Karfa

Karfa a al’adar Maguzawa yana nufin yin magani ta hanyar tsafi don kowane iri don Ƙuntata wa abokin hamayya a wurin neman aure. Samari sukan daɗe suna neman budurwa, sai lokaci ɗaya wani ya zo ya kasa su. Idan irin haka ta kasance, ba kowa ke haƘura ba. Dole akan ɗan ratse ta yadda za a ɓata lamarin. Sakamakon irin waɗannan magunguna sukan bambanta dangane da Ƙarfin tsafin da aka yi amfani da shi wurin haɗa maganin, ko kuma irin sakamakon da ake bukata. Wasu sai bayan an yi aure mace ta kasa zama gidan miji. Wasu kuma ko auren ba za a yi ba, matsaloli su shigo, a rabu baram-baram. Ga misali, Maguzawan Batsari (ta jihar Katsina) suna da wani nau’i na karfa wanda ake raba saurayi da budurwa in suna son junansu. Daga cikin samarinta wani yakan kasa yin haƘurin kasa shi da aka yi. Irin wannan karfa garin magani ne mabukaci zai tauna da jar kanwa, sai an zo dandali ya fesa wannan yawun maganin ga wanda ya kasa shi. Wannan saurayin da budurwar ke so (wanda aka fesa wa maganin) ba shi ba ita har abada. Ya rinƘa ganin wulaƘanci ke nan daga gare ta, da rashin Ƙauna har sai ya gaji ya nemi wata. Haka kuma idan budurwar ta yi wa wani wulaƘanci saboda son wani saurayi na daban da take yi, to wannan saurayin da ta yi wa wulaƘanci yana iya fesa mata wannan magani, in ya kasa haƘuri. Ita da auren saurayi har abada. Sai dai ta sami wani tsoho ta aura don gudun kada ta mutu ba ta yi aure ba. Wato ba a sake samun wani saurayi da zai so ta, sai kuwa in an sami laƘanin karya maganin.

Su kuma Maguzawan ƘwanƘi (a Ƙasar Bakori ta jihar Katsina)sai bayan an fara bukin aure suke fara yin nasu karfan. Duk da yake abu ne mai wuya su ambaci sirrin maganin nasu, an gano cewa baƘar kaza mai rai ake ɗaurewa cikin baƘin Ƙyalle a yi tsafin da ita a kai kan suri (gidan gara ko jiɓa) a ajiye. Ana kai amarya gidan miji, ta bar wannan gidan ke nan har abada, an bar ango da takaici. Idan shi ma namiji ne, ko tsafin gidansu ya fi na abokan hamayyar to ana ƘoƘari a karya maganin ko ma ya Ƙi ci. Gudun cin karo da irin waɗannan mishkiloli shi kan sa Maguzawan Kainafara (da ke zaune a Birci ta Ƙasar Kurfi a jihar Katsina) suke yin nasu dabarun in za a kai amarya, kamar yadda za a gani nan gaba.

3.3 Tsafe-tsafen da Suka Danganci Bukin Aure

Baya ga tsafe-tsafen da Maguzawa ke aiwatarwa don samar da soyayya ko kare ta, ko lalata ta a lokutan da ake aiwatar da ainihin bukin aure, akan sami wasu Maguzawan da suke gudanar da tsafe-tsafe don neman amincewar abin da ake bauta wa ko don tabbatar da ɗiyaucin mace, ko magance matsalar wabi ko don a zaunar da amarya a cikin ɗaki, da karya duk wasu tsafe-tsafe da abokan gaba suka yi.

A al’adar Maguzawan Kainafara, a safiyar ranar da za a ɗaura aure, za a kai baƘin ɗan akuyar da iyayen ango suka kawo cikin dutsen Ɗantalle a garin Birci inda a nan ne tsafin nasu yake. Sarkin noma (shugaban tsafin) zai yanka wa iskokin Kainafara wannan ɗan akuyar kafin a ci gaba da sauran al’adun ɗaurin auren. Haka ma lokacin da aka zo da amarya Ƙofar ɗakinta aka sauko da ita daga kan goɗiya, jama’a za su yi dafifi a Ƙofar ɗakin. Za a sami wani namiji a ba shi baƘar kaza da jan zakaran ya riƘe a hannu. Zai kama hannun amarya su shiga ɗakin tare. Sai su fito, su Ƙara shiga, su fito. Sai sun yi haka har sau huɗu. Sai ya kewaya mata waɗannan kajin a kai. Idan ya Ƙare sai ya saki kajin. Daga nan sai ta shiga ɗakin, sannan sauran jama’a su shiga ɗakin. Waɗannan Maguzawan sun yi imani da cewa, duk amaryar da aka yi wa haka, to ita da ango mutu ka raba.

Su kuma Maguzawan Kaibaki da ke Ƙasar Fago ta jihar Katsina, idan an Ƙare wankan amarya, za a fito a ɗunguma tare da dangin ango zuwa wajen garin inda tsafin garin yake. Idan an isa za a yanka ɗan akuya a babbaka shi a daddatsa. Wanda ke jagorancin wannan tsafin zai fara ci. Sai a ba sauran jama’a su ci. Daga can za a ji Ƙarar iskar wu-wu-wu-wu…. Da zarar an ji haka za a fara tafiya ana waƘa zuwa gida. A kan hanyar dawowa in aka zo daidai gidan da wata mace ta yi lalata tana da aure, ta haifi shege ba a sani ba, za a ga tsafin ya kware mata rufin ɗakinta kamar dai yadda guguwa ko iskar damana ke ɓarna, wato tsafin ya tona mata asiri ke nan.

Maguzawan Gidan Gwarzo (Ƙasar Matazu ta Jihar Katsina) daga wurin ɗaurin auren dangin ango za su nufi wurin da tsafinsu yake tare da ɗan akuya da zakara. Ana isa, babba a cikinsu ko wanda ke jagorancin tsafin zai hau Ƙololuwar itacen tsamiya tare da zakara a hannunsa. Daga can saman itacen zai sa bakinsa ya tsinke kan zakaran, ya ɗaure Ƙafafun a jikin wani reshen itacen tsamiyar, zakaran na reto, jinin na ɗigowa. Ba zai sauko ba sai jinin ya gama ɗiga.

Yana saukowa za a kamo ɗan akuyar nan a yanka, a babbake shi da wutar da aka hura da kara. A nan ba a yarda a sa itace ba. Karan zai Ƙone ba tare da naman ya gasu sosai ba. Haka za a rarraba wa jama’a su ci naman. Sai a koma gida ko gidan amarya a ci gaba da shagali. Wannan shi ake kira rawar gunki. Haka kuma idan an zo ɗaukar amarya bayan an fito da ita, (an ba da ɗauka) za a yanka ɗan akuya. Ga maƘunshiya, ga mawanki, sai a kira amaryar ta Ƙetare jinin sau uku. A na huɗun sai a turo ta. Daga cikin abokan ango wani zai ɗauke ta ya ɗora kan goɗiya a kama hanya. Naman ɗan akuyar kuma za a raba wa dangin uwa da na uba su ci.

3.4 Kai Bante

Kai bante a al’adar aure yana nufin amarya ta yi aure ba tare da wani namiji ya taɓa tarawa da ita ba sai wannan mijin da ya fara aurenta. A Maguzance abin farin ciki ne ga ’ya mace da ma iyayenta a ga yarinya ta kai ɗiyaucinta. Haka kuma, abin baƘin-ciki ne ga iyaye da dangi da ma ita kanta amarya a wayi gari ranar aurenta a gane cewa, ta taɓa yin lalata. Wannan yakan rage kimarta da kimar iyayenta a idon jama’a. Tsoron sakamakon irin wannan ranar kan sa ’ya’ya mata ba su taɓa yarda su sadu da namiji sai fa bayan an yi aure. Akwai hanyoyi da dama da Maguzawa suke amfani da shi wajen gano ɗiyaucin mace a daidai lokacin da ake bukin aurenta kafin a kai ɗakin miji.

Ga misali, Maguzawan Kaibaki an nuna cewa, kafin a ba da ɗaukar amarya akan tafi wurin tsafin garin a yanka ɗan akuya a babbake, a ba mutane su ci. A wannan lokacin ne tsafin ke yin wani kuka wu-wu-wu… Waɗannan Maguzawa sun nuna cewa, wannan kuka da tsafin yake yi kamar alama ce ta nuna ya yarda da wannan aure kuma amaryar ta kai bante, watau ba ta taɓa yin lalata da namiji ba. Idan har tsafin ya Ƙi yin kuka to ba ta kai bante ke nan ba. Wannan na iya zama sanadiyyar mutuwarta. Ga amaryar da ta san ta taɓa sanin ɗa namiji, za ta yi ƘoƘarin gaya wa iyayenta. Su kuma su yi ta ’yan dabaru a Ƙi zuwa wurin tsafin. Sai dai kawai a ba da ɗaukan amarya. Da zarar an ga haka sai a fara tsegumi, a gane cewa, amaryar ba ta kai bante ba.

Su kuma Maguzawan ƘwanƘi, ɗan akuya ake yankawa a daidai Ƙofar gidan bayan an Ƙare wankan amarya an fito da ita. Baya ga wannan jini na ɗan akuyar, za a gitta taɓarya, amaryar ta zo ta Ƙetare sau uku. Idan har ba ta taɓa sanin namiji ba, to ba abin da zai same ta. Sai a ɗauke ta a ɗora kan doki ana ta murnar ta kai bante. Idan kuwa ta taɓa sanin namiji, kuma ta Ƙetare wannan taɓaryar da jinin ɗan akuyar, to za ta faɗi a nan. In ma ba ta yi sa’a ba yana iya zama ajalinta. Gudun haka kan sa su ma iyeye su yi ta ’yan dabaru a Ƙi yin duk wasu al’adu, a fito da amarya ta wata Ƙofar a ba da ɗauka. Da an ga haka an san abin da ya faru ke nan, sai bukin ya rage armashi.

A al’adar Maguzawan Gidan Bakwai (Ƙasar Faskari), idan za a kai amarya dangin amarya sukan yi sihirce-sihircensu na kiran tsafin da suke bauta wa. Sun nuna cewa, idan dangin amaryar ’yan Magiro ne sukan kira shi ya yi wa amarya rakiya. Za a riƘa jin Ƙuginsa a lokacin da ake tafiya kai amarya. Idan aka kira shi ya Ƙi zuwa to, wannan ya nuna amarya ba ta kai ɗiyaucinta ba. Wannan shi kowace uwa, da ’ya mace ke gudu a lamarin aure. Wato ya ishe su abin kunya a al’umma. Ya ishi uwa da ’ya abin gori idan ana magana. Da zarar haka ta faru za a ga ba su yawan shiga jama’a ana hira, gudun kada su sami saɓani da wani ya yi musu gori.

A wasu al’ummu na Maguzawa, al’adar kai bante ba ta tsaya ga ‘ya mace kawai ba. Wato har da ango akan yi tsafin da ke nuna cewa ya taɓa saduwa da ‘ya mace kafin aure ko bai taɓa ba. Misali a al’adar Maguzawan Gidan Gwarzo, a ranar da aka ɗaura aure bayan an dawo gida da dare, idan tsafin Bagiro iyayen angon suke bauta wa, za a ji tsafin yana kuka a bayan gida. Wannan kuka alama ce da ke nuna tsafin ya amince da auren. In kuwa har gari ya waye ba a ji kukan tsafin ba, to angon ya taɓa yin lalata da mace. Daga nan zumunci ya yanke tsakaninsa da abokansa. Haka kuma ba za a ci gaba da sauran hidimomin auren ba, ya rasa wannan matar ke nan sai dai a ba wani. Don tsananin kasancewar wannan abin kunya, hakan na iya sa ya bar wannan garin ko Ƙauyen har abada. Idan kuma mace aka gano ta taɓa sanin ɗa namiji, to sai dai a ba wani tsoho ita ya yi haƘuri amma ba dai ta auri saurayi ba.

4.0 AL’ADUN TSAFI A HAIHUWAR MAGUZAWA

Haihuwa dai Ƙaruwa ce ta hanyar fitowar wani abu mai rai daga jikin wata halitta jinsin mace. Wannan abu yakan ɓoyu a wani wuri na musamman na wani Ƙayyadadden lokaci don samun kamanni ko siffa kwatankwacin na zuriyarsu, wanda ke aukuwa a sakamakon saduwa da jinsin namiji na wannan halittar.

A fasalin da ya gabata an dubi tasirin da ke ga tsafe-tsafen Maguzawa a sha’anin su na aure. Wannan lamari bai tsaya ga aure kawai ba. Akwai wasu ’yan tanade-tanade da suka yi dangane da haihuwa. Maguzawan da suka yi fice wurin gudanar da irin waɗannan al’adun su ne Maguzawan Kainafara.

 

4.1 Ɓacewar Jinjiri

Idan mace tana da ciki, aka ga alamar cikin nan ya kusa kai wata tara, za a ja kunnenta da cewa, da zarar ta haihu kada ta kuskura ta gaya wa kowa, in kuwa ta bari mutane suka sani, za ta mutu. A al’adarsu, mace tana haihuwa ne ita kaɗai a ɗaki. Ana cin nasarar haka ne saboda yawan magungunan da ake sha na sauƘin gwiwa. Duk da haka a wasu lokuta akan ci karo da matsalolin da za su sa a nemi taimakon wasu na kusa, ko su ma a asirce. Su ma ɗin da zarar an sauka lafiya za su kulle bakinsu. Ana haihuwar, wannan jinjirin zai ɓace. Ba za a sake ganin shi ba sai bayan makonni biyu cur. Za a wayi gari a gan shi cikin ɗakin. A wani ra’ayin kuma, za a dawo da shi ne a daren rana ta sha bakwai da haihuwar. Akan ba mai jegon maganin firgita. In ba haka ba sai ta taɓu ko ma ta haukace saboda tsoron ɓacewar jinjirin. Maguzawan sun yarda da cewa, Iskokinsu ne ke ɗauke yaron su riƘe a wurinsu don ladabtar da shi na tsawon waɗannan kwanakin.

4.2 Tabbatar da Iyayen Jinjiri

A ranar da jinjirin zai dawo, ranar za a yi suna. A wannan ranar kuma za a yi al’adar tsafin da zai tabbatar da cewa, wannan jinjirin Kainafara ne. Idan ba Kainafara ba ne, wato uwarsa ta tara da wani can daban to ranar zai mutu. Abin da ake yi shi ne, za a sami kundon karan dawa (gaɓan kara) a koma gabas da ɗakin da yaron yake ciki. Sai a ɗaga jinkar ɗakin daga waje da karan nan, a tokare da Ƙasa ta yadda za a sami Ƙofa tsakanin ginin ɗakin da jinkar dakin. Sai wani ya shiga cikin ɗakin, wani ya tsaya waje daidai inda aka tokare jinkar. Sai na cikin ya ɗauki jinjirin ya miƘo wa na waje ta wannan kafar. Bayan ya karɓa zai mayar da shi ta wannan kafar ga wanda ke cikin ɗakin. Za su yi haka har sau huɗu. Idan wannan jinjiri ba nasu ba ne, ko kuma uwar ta bi maza ta sami cikin, wato ba na mijinta ba ne, to da an miƘo jinjirin, karan nan zai goce ko ya karye, jinkar ta faɗo ta danne jinjirin da jikin gini ya mutu. Idan kuwa jinjirin jinin Kainafara ne, to wannan kara ba zai goce ko ya kare ba.

4.3 Tsagar Gado

A wata al’adar mai dangantaka da tsafi ga su waɗannan Maguzawa na Kainafara, ba a tsaga su. Idan aka kuskura ana yi wa jinjirin Kainafara tsaga ko da cikin rashin sani ne, to wannan wanzami zai mutu. Haka shi ma jinjirin zai mutu. Idan ma ba a yi sa’a ba, hatta da uwar ɗan za ta bar duniya saboda sakacinta na barin a tsaga jinjirin Kainafara. A fahimtarsu, Iskokinsu ba su amince a tsaga musu shi ba.

5.0  NAƊEWA

A wannan nazarin, an waiwayi wasu abubuwa da suka danganci tsafi a al’umar Maguzawa. Waɗannan tsafe-tsafe sun shafi aure da haihuwa kawai. Tunanin da aka yi a baya, shi ne, ba a sa ran rayuwar Maguzawa kacokan ta karkata ga tsafi har a harkokin da suke da alaƘa da jin daɗi ko Ƙaruwa ko annashuwa kamar na aure da haihuwa. To da yake an kwatanta dangantakar Maguzawa da tsafi da irin alakar da ke tsakanin tsoka da jini, sai ga shi nazarin ya tabbatar da kusan kowane sha’ani na aure da haihuwa tsafin ya kutsa a ciki. Mun ga yadda tsafi ya yi tasiri a harkar aure kamar a wujen gwagwarmayar neman aure da na tabbatar da ɗiyaucin amarya da dai makamantan su. Haka ma a sha’anin haihuwa, nazarin ya gano hanyoyin da Maguzawa ke amfani da su wajen tabbatar da halaccin ’ya’yansu da gabatar da jinjiri ga Iskoki ta hanyar tsafi na wasu kwanaki bayan haihuwa. Don haka, ba zai zama wani abin gardama ba idan aka ce tsafi shi ke jagorancin rayuwar Maguzawa.

6.0 MANAZARTA

Abdullahi, I. S.S. (2000) “Magani Da Siddabaru Cikin Rubutattun Ƙagaggun Labarun Hausa.” Sakkwato, Kundin digiri na biyu, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Abdullahi, I. S. S. 2008, ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan

Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Sakkwato, Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Abu, M. (1985) “Al’adun Aure da Canje-canjensu a Katsina” Sakkwato. Kundin Digirin farko, Jami’ar Sakkwato.

Adamu, M. T. (1997) Asalin Hausawa da Harshensu, Kano, Ɗan Sarkin Kura Publishers.

Alhassan, H. da Sauransu (1982), Zaman Hausawa

 

Bunza, A. M. (1995) “Magungunan Hausa a Rubuce: (Nanzari Ayyukan Malaman Tsibbu),” Kano, Kundin digiri na uku, Jami’ar Bayero.

Bunza, A. M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada, Lagos Tiwal Nig. Ltd.

Bunza, A.M. (1990), “HayaƘi Fid Da Na Kogo: (Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa)”, Kano, Kundin Digiri na Biyu, Jami’ar Bayero.

Charanchi, R. (1999), Katsina Dakin Kara: Tarihin Katsina Da Garuruwanta, Zariya, Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Elias, T. O. (1957) “Hausa Marriage” In Nigeria , A Quarterly Magazine of General Interest No 53, Marina, Lagos, published by the Federal Government of Nigeria, Exhibition Centre.

Gwarjo, Y. T. da wasu (2005) Aure a Jihar Katsina Hukumar BincikenTarihi Da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina,

Ibrahim, M. S. (1982), “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”, Kano, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero.

Ibrahim, M. S. (1985), Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci, Zaria Cyclostyled Edition – Hausa Publications Centre.

Kado, A. A. (1987), “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

Safana, Y.B. (2001), “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar Safana”, Sakkwato, Kundin Digiri na farko, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.



[1] Don Ƙarin bayani a kan yadda ake sarrafa magani ta hanyar hayaƘi, dubi kundin Aliyu Muhammad

 Bunza na digiri na biyu mai take, “HayaƘi Fid Da Na Kogo: (Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa) Jami’ar Bayero, Kano, 1995, shafi na 144.

[2] A nan kwana tare ba yana nufin ya yi lalata da ita ba. Wannan al’ada da ake kira Tsarance ita ke tabbatar da cewa, budurwa tana son saurayin.

Post a Comment

0 Comments