Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 18: Rashin Girman Kai

    WaÉ—anda suka sayi filaye, motoci da sauransu in ba sa'a aka yi ba nan da nan za su kadar da su su bi kan kuÉ—in su lashe. Da a ce kansilanmu malamin makaranta ne, lokacin da ya sami  kuÉ—innan kamar ana zubo su da bakin Æ™warya sai ya sayi wani...


    Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 18: Rashin Girman Kai

    Baban Manar Alƙasim
    Zauren Markazus Sunnah

    Na isa wata ƙasa a 2002 inda na kammala digirorina a 2015, idan muka lura da cewa na dan jima a can, kuma ko tun farko karatun ne dai ya kai ni, sannan a matakin digiri wanda ko kafin na tafi ina da diploma kuma na dan jima ina koyarwa waɗannan abubuwa za su iya ba ni damar da zan dan lura da wasu abubuwa waɗanda sun dan saba wa yadda na saba gani a ƙasata, ba ina cewa sun fi mu hikima ne da jajurcewa ba, amma akwai wasu abubuwan da in an koya za a iya magance zaman banza, bambadanci, ubangidanci, neman alfarma da ƙarfa-ƙarfa, a can ne na ga wanda yake aiki a gidan jarida da majalla ta ƙasa da rana, in dare ya yi ya koma wata jami'a a matsayin mai-kula da yara yana kwana da su, yana dan samun na cefane.
    .
    Na ga soja a matsayin major kuma malami ne a wata jami'a, na shiga ajinda da yake koyar da addinin kiristanci, tsakanina da Allah bayan na gabatar da wata ƙasida sai da ya nuna min cewa ban san komai a ƙasata ba, ni kaina na yarda da hakan, masamman irin hujjojin da ya bayar, na ji labarin wani babban sojan sama da yake koyar da konfuta a wata jami'ar, ni da kaina na taba ganinsa a cikin kaki ina ta mamaki, na ga wasu masu dafa abinci a wata jami'a ashe 'yan sanda ne, suna aikin ne idan sun cire kaki don su ƙara ƙarfin abin da suke samu a wata.
    .
    A lokacin da muke dalibai na ga wani ministan ilimi wanda shi ne shugaban tsangaya ta ilimi a wata jami'ar, akwai wani dan sanda da muka san shi, sai ga shi yana kamisho, ban sani ba in wannan yana da alaƙa da tsaro ko baida shi, ina kuma da masaniyar cewa ƙasata ba ta ba da hurumin da ma'aikacin gwamnati zai yi aiki biyu ba, amma kuma ba a hanaka ka nemi na rufin asiri a wani wurin ba, babban abin da yake ba ni sha'awa da su shi ne babban aikin da kake yi ba zai hana su su yi wani da ake ganin ƙasƙantacce ne ba, tabbas akwai masu yin haka anan amma ba su ne suka fi yawa ba.
    .
    Zai yi wahala mutumin da ya yi kansila a same shi ya koma ajinsa na furamare kamar yadda yake da, to bare kuma wanda ya hau matsayin shugaban ƙaramar hukuma, da ya koma aikinsa na baya ya gwammace ya riƙa bin 'yan uwansa 'yan siyasa su ba shi ko su hana, matsalar da muke fama da ita kenan, na ga kansiloli a baya da suka riƙa sayen filaye da gina gidaje suna wadaƙa da kudi yadda suke so, abin takaici ba sa iya aiki da damar da suka samu ta wurin gina ƙaramin kamfani ko wata ma'aikata ko shagon kayayyaki yadda in suka sauka za su koma can don rufin asiri, da sun sauka da dan ƙaramin lokaci sai ka ga sun lashe abin da suka tara.
    .
    WaÉ—anda suka sayi filaye, motoci da sauransu in ba sa'a aka yi ba nan da nan za su kadar da su su bi kan kuÉ—in su lashe. Da a ce kansilanmu malamin makaranta ne, lokacin da ya sami  kuÉ—innan kamar ana zubo su da bakin Æ™warya sai ya sayi wani fili ya gina makaranta tun da ya san kan abinnan, yana sauka ya Æ™ara fadada ta ya sami hanyar da zai riÆ™e rayuwarsa ya dauki wasu ma aiki, yau a ce mutum tela ne aka ciro shi aka nada shugaban Æ™aramar hukuma, da sai ya yi kamfacecen shagon teloli, ya zuba kekunan da ba ko'ina ake samunsu ba, ya dibi ma'aikata, sannan ya yi ofis dinsa na masamman saboda ko-ta-kwana, yana sauka ya san inda zai je.
    .
    Hana ƙarya na ga wani kansila wanda tun asali shi manomi ne, dan abin da yake samu a gwamnatance ya riƙa ƙara shi cikin abin da yake birnewa a ƙasa, ya ƙara zama babban manomi, koda ya sauka ba wani abu nasa da ya canja, don ko tun yana kai yakan dibi 'yan ƙwadago su shiga daji, nan ma ya taimaki wasu, duk da cewa rayuwa ta dan sauya da ya sauka din, amma bai wani shiga halin ni-'ya-su ba, wani tela da na sani ya sami aiki babba, kuma yana samun kudi ba shakka, a maimakon ya ƙawata sana'arsa ta farko ya habaka ta bai yi ba, a ƙarshe damar da yake da ita ta kubuce masa, har muka rabu shagonso ba a daina murza zare a cinya ba, bayan na ga wasu suna amfani da wani dan inji ƙarami.
    .
    Matuƙar babban matsayin da ka samu a yau na dan wani taƙaitaccen lokaci ne da yatsun hannunka za su iya ƙirgawa, me zai hana ka yi wani shiri da za ka dade kana jansa bayan saukarka ko bayan gushewar wannan damar? In ka yi hakan aikin da ka samu zai dada taimakonka ne zuwa ga nasarar da kake sa rai da ci a rayuwarka, tabbas wasu suna da tsari, sukan waiwayi halin da suke ciki kafin su sami kansu a irin wannan halin na yau, sukan yi tunanin cewa in fa suka sauka za su iya komawa gidan jiya, sai su yi wa kansu tsari.
    .
    In a baya mutum ya karanci likitanci ne amma bai fara aiki ba saboda halin da ake ciki na Æ™arancin gurabun aikin, sai Allah ya tarfa wa garinsa nono ya sami wani muÆ™addashin Æ™aramar hukuma na riÆ™o,  me zai hana ya ririta dan  kuÉ—in da yake samu wurin gina Æ™aramin asibiti, ya riÆ™a kawo kayan da ake buÆ™ata a hankali yadda kafin ya sauka ya gama tanadar duk abubuwan da ake buÆ™ata? Da farko dai in ya sauka zai ci gaba da aikin da ya karanto a wurin da shi ne shugaba, sannan kuma zai samar wa bayin Allah da aikin yi, ga riba ga lada.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.