Mafita
ga wanda yake aiki a babban ma'aikatar katako ita ce: Me zai hana shi yin É—an wani...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 19: Da Kayan Kai Ake na Rataya
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Akwai hikima mai girman
gaske mutum ya fara tunanin yin wani abu a gefe nasa na kansa wanda zai taimake
shi, in likita ne yana da kyamis, in babban malamin makaranta ne yana da wata
'yar makaranta a gefe koda kuwa ta lesson ce, in kanikanci kake yi a wurin wani
maigidanka na tsawon lokaci ka sami wani É—an wuri
a ƙofar gidanka kana gyara wa maƙwabta mashinansu, in kafinta ne ka fara
gyara wa mata 'yan kujerunsu a cikin gida lokacin da ba za ka je wurin aiki ba,
wannan shi ne wayewa, a duk lokacin da ka gama ƙwarewa
ko ba a sallame ka ba za ka yi naka na kanka.
.
Akwai hikima mai girman
gaske mutum ya fara tunanin cewa zai iya yin wani abu nasa na kansa, koda kuwa
talaka ne kamar yadda muka lissafo bare wani babban ma'aikacin gwamnati mai
aiki a wata babbar ma'aikatar tatse 'ya'yan bishiya, in mutum na samun kudi ya
gane cewa in fa ya sauka daga muƙaminsa
kuÉ—innan
da yake samu sun gama shigowa kenan sai dai kuma shigewa, yanzu sai ya fara
tunanin riƙe su ta yadda ba za
su ƙare ba, hakan kuma ba zai taba yuwuwa ba
sai in ana ƙara yawansu, kenan ya
fara tunanin yuwuwar yin wani abu da zai kawo kuÉ—in
shiga.
.
Mafita ga wanda yake aiki a
babban ma'aikatar katako ita ce: Me zai hana shi yin É—an wani
shago ya sami wanda zai riƙa
taimaka masa wajen tsarewa? Yanzu rashin aiki ya yi yawa, mutane na zaune ne
babu aikin yi, kana fara neman mai taimako nan da nan za ka samu, sai ka koya
masa aikin kamar yadda kake so ya yi, ka kawo kayan aiki masu kyau da nagarta,
nan da nan za ka ga kana buƙatar
sama da mutum guda matuƙar
dai ka sami kayan aiki na zamani, ka inganta aikinka kuma ka ƙimanta shi a idonka, kana aiki a wani
wuri kana fadada naka a hankali da abin da kake samu acan, kafin ka kai ga
yadda za a ce ba a buƙatarka
a wurin aikinka kai kanka ka fara tunanin ya dace a ce ka yi ritaya don daukaka
wurinka da habbaka shi.
.
A daya hannun kuma matuƙar mutum zai yi wani ɗan wurin
sana'a komai ƙanƙantarsa ba zai yuwu a ce shi ne komai
ba, misali ka yi wani ɗan kamfani da kake nuƙa zoborodo kana zuba shi a 'yar jaka
kamar shayi, ba zai yuwu a ce komai kai kake yinsa kai kaÉ—ai
ba, misali a ce kai ne shugaba, masinja, mai gadi, mai fita talla da sauransu,
dole ka sami ma'aikata, su ma ka hana su yawon banza kenan, suna samu daga
jikinka, wannan ne abin da ya dace, don aikin da ka yi a baya ya ba ka damar da
za ka yi naka ne, ba wai kuma in ka gama ka dawo ka tanƙwashe ƙafa
sai dai in an yi a diba maka ba, in ka yi haka duk ilimin da ka samo ya zama na
banza kenan.
.
Masu bincike na ƙasashen Turai sun gano cewa tsabar kudi
da za a saka jari duk da cewa shi ne ginshiƙi na
habbaka sana'a ko kasuwanci ba shi ne komai ba, kudi na da nasa gudummuwar da
yake badawa na masamman amma yawaitar mutane a bangarori daban-daban na
ma'aikata ko wuraren sana'a ita ce babban sanadi na habbakar wuri, misali kana
da kudi kuma ka zuba su a harkokin koyarwa akwai tambayar da za a yi maka wato
a wani bangare? Kana da buƙatar
lafiyayyen gini na zamani da aka cike shi da furanni, ka ƙayata dakunan karatu da ofisoshin
ma'aikata, ga azuzuwa gyararru da kujeru rantsattsu, 'yan abubuwan sauƙaƙe
rayuwa duk ka yi su.
.
A gefe guda kuma ka samo
ingantattun malamai waÉ—anda suka san abin da suke
yi, ka tanadi albashin da za a riƙa ba
su su da sauran ma'aikatan dake wurin, ka ga ai ka gama komai, yi ƙoƙari
ka gina dakin cin abinci da dalibai za su riƙa
ganin ya fi musu sauƙi da
a ce suna dafawa da kansu, a gyara abincin da ake yi ka ɗan sauƙaƙe kuɗinsa,
anan ma ka dawo da kudadensu aljihunka kenan, kuma ka samar wa jama'a da aikin
yi, daga gefe kuma ga wani É—an shagonan ka gina na
kasuwanci, anan ne za a riƙa
kwafe wa dalibai takardunsu, ana sayar da katin waya kuma ga na'urar canjin
kudi in akwai mai buƙata.
.
Sannan kuma in kana da dama
hatta É—an shagon
da za a riƙa sayen ƙananan kayayyaki duk ka samar a cikin
makarantar, ƙarshe dai kuɗin
duka aljihunka zai dawo, in ka ga ba za ka iya ba, to gina dakunan waÉ—annan
abubuwan ka bayar a matsayin haya ana biyanka kuÉ—insu,
shi ma ka samar wa wasu da damar kasuwanci kai ma ka sami wata hanyar da za ka ƙara kuɗin
shiga, wannan kam dabara ce duk wanda yake da idon kallo, a kowani fanni ka
shiga za ka ga muna da waÉ—annan damammakin amma
natsuwa da kai hankali nesa shi yake damummu, ba ma iya tantance abubuwan da
muke buƙata, da waɗanda
rayukammu suke so, akwai hanyoyin cin nasara da dama ba ma kallonsu, bai yuwuwa
ka ce komai kai daya za ka yi.
.
Yi
tsari mai kyau, hau kan hanya, duk wata 'yar dama da ka samu janyo wani ku tafi
tare, shi zai sami nasa, kai ma za ka dada daukaka ba tare da ka yi asarar komai
ba, mu dubi filin wasan ƙafa
kowa da irin aikin da yake yi, ƙarewa
ma an rubuta sunansa a bayan rigarsa da lambarsa dake nuna irin aikin da zai yi
da iya hurumin da zai tsaya, haka tsarin mutum a cikin lamarinsa yake, duk
aikin da mutane za su yi a ma'aikatanka su ma a ƙarshe
manufar dai kenan, a tabbatar ma'aikatar na sarrafa abubuwan da ake buƙata, kuma kayan na karbuwa ta wurin saye su a
duk lokacin da aka yi, wannan kuwa ba tunanin mutum guda ba ne ba aikinsa ne
shi kaÉ—ai
ba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.