Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Yaudara Da Makirci A Cikin Neman Auren Hausawa A Yau


Mun sadaukar da wannan bincike ga iyayenmu bisa ga kyakkyawar tarbiya da suka ba mu tun daga farkon rayuwa zuwa yau. Iyayen namu sun haɗa da: Alhaji Shehu Mustapha Ƙaura da Brr. Armiya’u Iliyasu Bukkuyum da Mal. Muhammad Umar Allah ya saka masu da mafificin alheri amin.


Nazarin Yaudara Da Makirci A Cikin Neman Auren Hausawa A Yau

A’ISHA MUHAMMAD UMAR
SAFIYA SHEHU
HAUWA’U ARMIYA’U B

Jinjina


Muna masu jinjinawa babban malaminmu kuma jagoran wannan bincike wanda ya kula da mu wato malam Ibrahim Ahmad ‘Dan’amarya na tsangayar harsuna sashen Hausa. Saboda nuna ƙwazonsa wajen duba wannan kundi tare da mayar da hankalinsa wajen wannan aiki tun farkon lokacin da aka fara har Allah ya kawo mu a wannan lokaci. Allah ya saka masa da mafificin alheri. Amin.

Godiya.


Muna godiya ga tabbataccen Sarkin wanda bai haifa ba, ba a haife Shi ba. Kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halittu annabi Muhammad (SAW).

Haka kuma muna miƙa kyakkyawar godiyarmu zuwa ga iyayenmu wato Alhaji Shehu Mustapha Ƙaura da Brr. Armiya’u Iliyasu Bukkuyum da Mal. Muhammad Umar, da duk waɗanda suka ɗauki nauyi da ɗawainiyar karatunmu har zuwa ƙarshensa, Allah ya saka masu da mafificiyar sakayya amin.

Ba za mu manta da miƙa kyakkyawar godiyarmu zuwa ga jagoran duba wannan aiki wato malam Ibrahim Ahmadu ‘Dan’amarya, wanda ya kula da dubawa da kuma gyare-gyare, Allah ya saka masa da alheri. Haka kuma muna miƙa kyakkyawar godiyarmu zuwa ga Dr. Haruna Umar Bunguɗu( H.O.D) na sashen Hausa a Tsangayar Harsuna Kwalejin Ilimi Da Ƙere-Ƙere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau Jihar Zamfara, kuma muna miƙa godiyarmu ga dukkan malaman wannan sashe, kamar su Mal. Salisu Sadi Tsafe da Mal. Sani Aliyu Soba da Mal. Aminu Saleh, da Mal. Bashir Aliyu Tsafe da Mal. Habibu Lawal Ƙaura da Mal. ‘Dahuru Hussaini Sankalawa da Mal. Muhammad Shu’aibu da Mal. Haruna Umar Maikwari, mun gode ga baki ɗaya Allah ya bar zumunci ya sa ma karatun da muka yi albarka ya sa abin da za mu taimaki wannan jiha da ƙasa baki ɗaya.


Babi Na ‘Daya

Gabatarwa


Wannan bincike mai taken “Nazarin Yaudara da Makirci a Cikin Neman Auren Hausawa a Yau”. Za mu gudanar da shi ne domin cika sharuɗɗan ƙare wannan kartu namu da kuma samu damar karɓar takardarmu ta ƙare karatu a wannan makaranta wato N.C.E.

Domin samar da sauƙi ga masu nazari mun tsara aikinmu bisa ga tsari na babi-babi har babi biyar.

Babi na farko za mu kawo bayani ne a kan Gabatarwa, Yanayin Bincike da Manufar Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin Da Suka Taso da kuma Matsalolin Da Aka Fuskanta.

A babi na biyu kuwa nan ne za mu yi tsokaci dangane da Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata da kuma Salon Nazari Da Tsarinsa.

A babi na uku kuwa nan ne za mu yi bayani a kan Ma’anar Aure, da kashe-kashensa da yadda ake neman aure da kuma yadda ake gudanar da biki a ƙasar Hausa.

A babi na huɗu za mu biyo da bayani da zai ƙunshi yaudara da makirci, kuma za mu ta’allaƙa su ga neman aure na Hausawa, da makirci a cikin aure da hanyoyin da za a bi wajen magance wannan matsala ta makirci a cikin aure.

Shi kuwa wannan babi na biyar a nan ne za mu naɗe tabarmar wannan bincike namu ta hanyar yin Jawabin Kammalawa da Shawarwari.

Yanayin Bincike


Wannan bincike na da yanayi na dubawa, saboda matsayinsa na ilimi, kuma wannan aiki na bincike ya sha bam-bam da sauran bincike da ake yi. Dalili shi ne, wannan fanni na al’ada an gudanar da ayyuka a cikinsa sai dai bai samu wasu ayyuka masu yawa da suka haɗa da yaudara da makirci ba.

Wannan ma ya sa a yunƙurinmu na gudanar da wannan aikin Binciken mun sha wahala sosai saboda rashin samun wasu litattafai da suka yi Magana a kan wannan aiki namu. Haka kuma yawace-yawacen da muka yi wajen samun wasu bayanai ya sa mun wahala matuƙa.

Muhallin Bincike


Da yake aikin yana da alaƙa da abin da ya shafi al’ada duk da cewa yaudara da makirci ba su cikin al’adun Hausawa, amma kuma wasu daga cikin Hausawa sukan iya aiwatar da su a cikin neman aure ko a zama na aure. Wannan ya sa muka keɓance wannan aiki namu ga abin da ya shafi yaudara da makirci waɗanda Hausawa ke yi ba wai wasu ƙabilu ba.

Hanyoyin Gudanar da Bincike


Wannan ya rataya ne a kan wasu hanyoyin tattara bayanai daban –daban na marubucin littafin ko mai aikin bincike na wasu ayyuka waɗanda suka gabata domin yin nazari a kan binciken da ake gudanarwa domin samun ra’ayoyi daban-daban.

Bayan wannan akwai wata hanya wadda mai bincike ke bi domin samun ra’ayoyi daban-daban don ƙarin haske ga aikinsa na bincike da yake gudanarwa, wato ta hanyar tambayoyi ga ma’abuta wannan ilimi.

Kamar yadda bayani ya gabata mun  lura da cewa, dukkan mai aikin bincike dole ne ya yi amfani da littafai daban-daban domin samun ingantu da kuma cikakkun bayanai masu gamsarwa. Haka kuma mun mayar da hankali a wurin gudanar da wannan bincike namu domin kuwa mun ziyarci mutane da dama da suka danganci tsofaffi masu masanniya a kan yadda ake yin yaudara a cikin neman aure da kuma yadda makirci yake gudana a tsakanin ma’aurata.

Manufar Bincike


Binciken yana da muhimmamcin gaske domin ta fuskar bincike ne a kan gano cikakkiyar ƙwarewar ɗalibai da fahimtarsu da hazaƙarsu. Ta wannan hanyar karance-karace za a ci karo da wani sabon al’amari domin ya ƙara tabbatar da abin da aka riga aka sani a fagen ilimi.

Binciken yana fitar da bayanai domin amfani al’umma, wani babban muhimancin bincike shi ne a duk lokacin da mai bincike ya tsunduma a fagen aikinsa yakan yi karo da wasu ra’ayoyi daban-daban wanda yana iya zama sabon darasi gareshi.

Manufar wannan binciken ita ce, domin mu ga irin yadda wasu Hausawa suke saka yaudara a cikin neman aure da kuma irin makircin da ke ƙunshe ga zaman auren Hausawa.


Matsalolin Da Suka Taso


Wannan bincike namu mun gudanar da shi ne a kan hanyoyin da suka dace, na irin hanyoyin da ake bi wajen samun bayanan da suka dace ta hanyoyi da dama. Mun ci karo da matsaloli da dama wajen binciken mu kamar haka.

Rashin isassun kuɗin mota, da matsalar iske waɗansu masana ko waɗanda za a tattauna da su, da muke son mu tuntuɓa wajen gudanar da wannan bincike namu, haka ma wani lokaci za mu kashe kuɗin mota domin zuwa wajen  waɗansu mutane da abin ya shafa, sai mu iske ba su nan. Haka ma kowa ya san irin halin da ake ciki a ƙasar nan na rashin tsaro, a inda ba ko ina za mu iya shiga ba dole sai da taka tsantsan.

Aikin bincike aiki ne mai wahalar gaske, musamman ma ga irin mu ɗalibai mata masu rauni da kuma karancin ilimi. Saboda haka lokacin da muke gudanar da wannan aiki na bincike wasu matsaloli da dama  sun sha kanmu. Daga cikinsu akwai:

Matsalar karɓar lacca da aikin aji da na jinga da kuma karatun jarabawar gwaji da ta ƙarshen zangon karatu.

Akwai kuma matsalolin gida kasancewar mu mata da suka haɗa da girke-girken abinci kula da tarbiyar yara, akwai rashin lafiyarmu da ta ‘ya’yanmu. Duk waɗannan matsaloli ne da mu ka yi ta cin karo  da su .

Akwai matsalar tuntuɓar magabata da masana, saboda wasu daga cikinsu suna ganin kamar za mu raina masu da al’adu ne saboda mu ‘yan boko ne su kuma ba su yi bokon ba..

Haka ma akwai matsalar yawan ɗaukewar wutar lantarki, domin sai mun tattaro bayanan mu na cikin aikin kwatsam sai wuta ta ɗauke. Kaɗan kenan  daga irin matsalolin da muka ci karo da su.

Matsalolin da aka Fuskanta


Kamar yadda aka sani a dukkan bincike za a iya samun nasarori da akasin haka, wato matsaloli a wajen gabatar da aikin. To don haka wajen bincike nan mun fuskanci matsaloli da dama kamar rashin kuɗi da za mu buga wannan aiki namu. Haka kuma akwai matsalar haɗuwarmu idan mun yi alƙawali, kuma idan za mu tafi wajen  ganawa da waɗanda za mu yi hira da su, saboda lokacin ba lallai ne a same su ba.

Haka akwai sha’anin rashin lafiya yakan kama magidanci , ko kuma halin tafiya wajen ƙaro ilimi wato a bangaren su masana.

Ba nan kaɗai muka samu matsala ba kuma mun fuskanci matsalar karamcin lokaci. Domin wannan aiki na bincike aiki ne da ya kamata a ce an gudanar da shi a cikin shekara ɗaya.


 Babi Na Biyu


2.01. Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.


Babu shakka ga duk wanda ya ke son ya aiwatar da aikin bincike dole ne a gare shi ya waiwayi baya domin ganin irin ayyukan da magabata suka yi masu dangantaka da nashi daga nan shima sai ya san inda suka tsaya ga bincike, ya kuma san inda zai ɗora nasa aikin.

Hausawa kan ce “waiwaye adon tafiya” wannan ko shakka bau gaskiya ne domin ta hanyar waiwaye ne kaɗai mutum zai iya gane irin ayyukan da magabata suka yi sannan ya san ta wace hanya zai bi wajen gudanar da nashi aikin na bincike. A cikin wannan binciken ne manazarci zai samu wasu ayyuka da dama waɗanda zai ɗauki wasu, kuma ya watsar da wasu.

A wannan bincike mun aiwatar da haka domin kuwa mun nemi inda za mu samu ayyukan magabata da za mu yi waiwaye mu ga abin da suka nazarta da kuma yadda za mu gudanar da namu. Ga dai wasu daga cikin ayyukan da muka samu yayin da muke nazarin wannan bincike.

CNHN, Jami’ar Bayero Kano (1981) sun buga wani littafi mai taken “Rayuwar Hausawa” an tsara wannan littafi bisa ga tsari na kashi-kashi inda suka fito da kashi shidda. Kashe na ɗaya dai ya ƙunshi tarihin ƙasar Hausawa, kashi na biyu kuwa yana bayani a kan aure, a kashi na uku bayanai ne game da haihuwa, yayin da kashi na huɗu yake ƙunshe da bayanai a kan mutuwa. Kashi na biyar kuwa bayanai ne a kan tasirin bukin al’adu a kan al’adun Hausawa, sai kashi na shida wanda yake shi ne na ƙarshe kuma a cikinsa ne suka kammala littafin.

Wannan littafi yana da alaƙa da aikinmu ta wani ɓangare saboda ya yi tsokaci a kan aure duk da cewa ba nan kaɗai ya tsaya ba. Wannan bayani a kan aure shi ne kaɗai yake da alaƙa da aikinmu, kuma zai taimaka ainun wajen gudanar da namu aikin. Inda gizo ke saƙa kuma shi ne aikin yana da bambanci mai yawa tsakanin namu da nasu. Dalili kuwa shi ne ba su ce komai ba game da yaudara da makirci.

Alhassan da wasu (1982), sun rubuta wani littafi a kan Al’adun Hausawa, waɗanda suka haɗa da aure haihuwa da mutuwa, a cikin wannan littafin na su Alhassan sun yi bayanin auren Hausawa kuma sun kawo ire-iren auren Hausawa da kuma yadda ake yin aure da lokacin da ake yin aure na Hausawa.

Wannan littafi na su Alhassan yana da alaƙa da namu aikin saboda sun taɓo al’adun Hausawa daga ciki kuwa har da aure. Wannan shi ne muke ganin aikin su yana da alaƙa da namu, sai dai inda gizo ke saƙa shi ne duk da cewa, aikinsu yana da alaƙa da namu kuma akwai inda muka sha bamban da su. Saboda su suna magana ne a kan al’adun Hausawa gaba ɗaya mu kuma muna magana ne a kan yaudara da makirci a cikin neman auren Hausawa.

Yahaya I.Y. da wani, (1986) sun rubuta littafi mai suna, “Jagoran Nazarin Hausa” sun yi taƙaitaccen bayani a kan adabin Hausa, kana sun kuma yi bayani a cikin shafi na 171, a kan Al’adun Hausawa inda har suka yi tsokaci a kan aure. A wannan littafi sun yi bayani a kan aure a ciki da wannan bayani ne muke ganin cewa, wannan aiki nasu yana da alaƙa da namu saboda sun yi magana a kan auren Hausawa. yayin da mu ma namu aikin yana da dangantaka da auren Hausawa. inda kuma muka samu bambanci da su kuwa shi ne, su sun taɓo har da adabi mu kuma al’ada ce kawai muka keɓance aikinmu a ciki.

Zarruk da wasu (1986) sun rubuta wani littafi mai taken “Sihili Uku” a cikin wannan littafi an yi bayani a kan al’adun Hausawa da yadda suke aure da yadda suke bukukuwan aure. Wannan aiki nasu yana da alaƙa da namu aikin saboda sun yi bayani a kan al’adun Hausawa da yadda suke gudanar da bukukuwan aurensu, mu kuma muna magana a kan auren Hausawa ne kuma yaudara da makirci a cikin neman auren.   Wannan ya nuna cewa, ayyukan suna da alaƙa da juna. Inda kuwa muka samu bambanci da su shi ne su sun yi bayanin auren Hausawa kuma sun bayar da ƙarfin aikin nasu ne a wajen al’ummar Hausa kacal, yayin da mu kuma har da wasu abubuwa da ba su cikin al’ada kamar yaudara da makirci mun taɓo.

Adamu M. I. (1998), “Aure a Ƙasar Hausa” adamu ya tsara aikin nasa ne a kan tsarin babi-babi har zuwa babi huɗu. Yayin da a babi na ɗaya ya yi bayani a kan aure a ƙasar Hausa. A babi na biyu kuwa bayanai ne da suka danganci neman aure a ƙasar Hausa. Sai a babi na uku inda marubucin ya yi tsokaci a kan baiko da ɗaurin aure. A babi na huɗu ya kawo bayanai a kan biƙi.

Duk da cewa wannan aiki na Adamu yana ɗauke da bayanai masu yawa bai hana a ga inda aikinmu yake da alaƙa da nasa, kamar yadda aka ga ya yi magana a kan neman aure. Wannan ko shakka babu a namu aikin za a ga cewa akwai neman aure. Sai dai inda bambanci yake shi Adamu bai yi magana a kan yaudara da makirci ba a cikin neman aure

Yahaya I.Y da wasu (1992) sun rubuta wani littafi mai taken “Darussan Hausa” a littafi na uku inda suka tsara littafin a kan darasi-darasi yayin da a darasi na goma sha biyu suka yi bayani a kan bukukuwan Hausawa daga ciki kuwa har da bukin auren Hausawa. wannan littafi yana da alaƙa da aikinmu saboda wannan bukin na Hausawa da aka yi bayaninsa a ciki. Idan aka lura za a ga cewa, mu ma namu aikin yana da dangantaka da buki irin na Hausawa musamman abin da ya shafi aure kuma za mu zo da su ne a cikin aikinmu domin kowa ya ga yadda yake gudana, kuma daga cikinsa za mu zo da wanda aka taɓa yin yaudara a cikinsa.

Garba U.G (2012) ya rubuta littafi mai suna “Bukukuwan Hausawa” a cikin wannan littafin Garba ya kawo bukin naɗin sarauta da bukin salla da bukin aure da na haihuwa. Wannan aiki na Garba yana da alaƙa da namu aikin saboda ya taɓo bukin aure, a namu aikin kuwa, ya zama wajibi mu yi magana a kan bukin aure. Wannan ne ya sa ayyukan suke da alaƙa da juna. Inda kuma suka bambanta shi ne aikin Garba yana bayani ne a kan bukukuwa daga cikin kuma har ya kawo bukin aure, amma mu namu aikin ba wai a bukin auren ne kawai ya keɓanta ba hatta da gano yadda yaudara take da makirci duk a cikin lamarin na aure.

Shi kuwa Musa I (2013) ya rubuta kundinsa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya domin samun digiri na farko a sashen Hausa, a cikin kundinsa mai taken “Nazarin Aure A Jahiliyya” ya yi bayanin a kan aure a zamanin jahiliyya da kuma aure a wannan zamani na ilimi, ya kawo irin yadda ake gudanar da auren a wancan zamani na jahiliyya ya kuma kawo yadda ake gudanar da shi a wannan zamani. Musa ya kalli aure a addinance kana ya kalle shi a zamanin dauri. Wannan aiki na Musa yana da alaƙa da aikinmu saboda shi Musa yana bayanin ne a kan aure, yayin da muma muna nazarin da ya shafi auren. Inda kuma muka sha bamban da shi shi ne, shi ya kalli abin a jiya da yau, mu kuma aikinmu ya ta’allaƙa ne a kan gano yaudara da makirci a cikin neman aure.

Ubaidu Y (2013) ya rubuta kundin mai taken “Nazarin Auren Jiya Da Yau” a Jami’a Ahmadu Bello da ke Zariya, domin samun digiri na farko. A cikin wannan kundin Ubaidu ya yi bayani a kan auren zamani da na zamanin da, wato tun kaka da kakanni. Ubaidu ya yi bayanin auren Hausawa da yadda ake gudanar da shi, ya kuma kawo bayani tun kafin zuwan musulunci.

Wannan aiki na Ubaidu yana da alaƙa da namu aikin saboda shi Ubaidun ya yi bayani a kan aure wanda yake muma namu aikin abin da ya ƙunsa kenan, da wannan ne ma muke ganin cewa, ayyukan suna da alaƙa, sai kuma inda suka bambanta shi ne Ubaidu ya mayar da hankalinsa a kan zamanin dauri da na yanzu, mu kuma muna kallon yaudara da makirci a cikin neman auren Hausawa.

2.0.2 Salo, Zubi Da Tsarin Bincike


Salo da zubi suna nufin irin dabarun da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike. Tsarinsa na nufin yadda aka tsara wannan bincike.

Salo shi ne hanyar da marubuci ke bi domin samun nasarar isar da saƙonsa ga masu karatu ko sauraro.

Idan aka ce salo to, ana nufin duk wata dubara da marubuci ko mai magana ya bi wajen isar da saƙonsa a cikin sauƙi.

Gusau (1993: 5), cewa ya yi. “salo shi ne hanyar da ake bi a nuna gwaninta da dubara a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da zaɓar abubuwan da suka dace game da abin da yake son bayyanawa.

A duk lokacin da aka yi maganar salo ana magana ne a kan irin ƙwarewar manazarci, wajen aikin bincike da kuma yadda yake jawo hankalin mai karatu a kan aikin da marubucin ya yi a kowane lokaci.

A wannan kundin dai za mu yi amfani da salo mai burgewa wajen aiwatar da wannan kundin ta yadda duk wani ya ɗaga shi sai ya amfana matuƙa. Wannan ba ya rasa nasaba da irin yawo da za mu riƙa yi a kasuwa-kasuwa saboda tattara bayanai da suka shafi wannan kundin. Don haka muka yarda cewa dukkanmu za mu ziyarci masu ilimi a kan wannan lamari na aure don samun ingantacciyar hujja.


Babi Na Uku


3.0.1 Taƙaitaccen Tarihin Hausawa


Masana da manazarta da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da ya shafi Mazaunan Ƙasar Hausa. Ga dai wasu daga cikinsu.

Dangane da mazaunan ƙasar Hausa kuwa shaihin malami Sa’idu Muhammad Gusau (2008), cewa ya yi:

Rubuce-rubuce da dama da ake yi domin ƙoƙarin gano asalin Hausawa suna nan jibge, ba tare da an haɗu a kan wani abu ɗaya ba. Ya ci gaba da cewa Abdullahi Smith da Ajayi Crowder, suna ganin ya fi dacewa a tafi kan cewa al’ummun da suke magana da harshen Hausa suna zaune ne a wata farfajiya, wadda take a zagaye bisa layin da ya taso daga Azbin zuwa ƙarshen mahaɗar gulbin Kaduna, daga nan ta doshi Arewa maso Yamma, ta dumfari gulbin Kabbi ta nufi fuskar Arewa maso gabas har ta sake haɗuwa da Azbin. Wannan marubuci ya daɗa ƙarfafa cewa, mazauna wannan wurin suna magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa.

Ya kuma bayyana cewa, a cikin ƙabilu mazauna yankin Savannah wato ƙasa mai ƙarancin itatuwa, ko mai itatuwa jefi-jefi. Hausawa su ne suka fi mamayen wurin zama mai faɗin gaske. Wannan wuri shi aka sani da ƙasar Hausa.

Dangane da abin da ya gudana daga masana za mu iya cewa, mafi yawan al’ummar da suke cikin wannan yanki na Savannah Hausawa ne. Kuma idan muka yi la’akari da yanayin da aka bayyana a wannan yanki za mu ga cewa al’ummar Hausawa su ke da irin wannan yanayi.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/




3.0.2 Al’adun Hausawa


Abin da ake nufi da al’ada shi ne, hanyoyin gudanar da rayuwar ɗan Adam ta yau da kullun. Al’ada abu ce, da ta shafi rayuwa tun ranar gini, tun ranar zane. A cewar Bunza, M. A. (2006:7) ‘’Al’ada tana nufin duk kanin rayuwar ɗan’Adam ce tun daga haifuwarsa har zuwa kabarinsa.” Shi kuwa ‘Dangambo, A. (1987:5) cewa ya yi, “ Al’ada ita ce, sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.” A taƙaice, al’ada wata abu ce wadda ta shafi abin da rai ya riga ya saba da aiwatar da shi har ya zamar masa jiki.

Aure da lamari ne da ya ƙumshi al’adu da ɗabi’un Hausawa tsintsarsu. Kama da zaman iyali na namiji ya auri macce fiye da ɗaya. A falsafar dangantakar iyali tsakanin magidanci da iyalinsa, idan aka ce iyali, a iya cewa kawai ma’ana iri biyu a nan. Ma’ana ta fako ita ce, wadda wasu suka ɗauka cewa, iyali sun haɗa mutum da matarsa ko matansa da ‘ya’yansa kurun. Ma’ana ta biyu kuwa, wasu sun ɗaukai cewa, abin da ake cewa iyali shi ne, magidanci da matarsa ko matansa da ‘ya’yansa da duk wanda yake ƙarƙashin kulawar wannan mai gidan. Wannan yana iya haɗa mahaifiyarsa da mahaifinsa da ƙannansa da barori, in dai shi ke kulawa da cin su da tufafinsu da wurin kwanciyarsu.

Ga al’ada a ƙasar Hausa, tsarin zamantakewar iyali a gidan Bahaushe miji ko maigida shi ne shugaba a gidansa. Matarsa ko matansa da ‘ya’yansa, har ma da yaran gida masu yi masu hidima suna a ƙarƙashinsa a matsayin mabiya. Mai gida ne zai ɗauki nauyin ciyar da mazauna a gidan. Shi ne kuma zai yi wa kowa tufafiin saka wa, ya kuma ba su makwanci. Haka kuma shi ne, wanda zai shirya masu irin ayyukan da kowane za yi, ya kuma tabbatar da kowa ya yi aikin da aka ba shi. wannan shi ne,tsarin zama na Bahaushe na asali, inda yake zaune a cikin babban gida tare da magidanta fiye da goma kowane magidanci da nasa yanki a gidan, inda yake tare da nasa iyalin, duk dai a ƙarƙashin “Uban-gandu”.

Uban gandu shi ne, dattijon gida da ya haifi magidantan wannan gidan nasa da yake da shiya-shiya, inda kowane magidanci yake da tashi shiyar, duk a ƙarƙashi kulawarsa. Ga al’ada, kowane magidanci zai zo shiyar wannan mai gidan nasu (Uban-gandu) da safe, don ya yi masa “ina kwana?” har matansu da jikokinsa, suma zasu zo, domin yi masa ‘ina kwana?’tare da nasa iyalin. Haka irin wannan tsari na iyali ya gada a wajen Bahaushe a ƙasar Hausa.

Wannan bayani ya nuna yadda Bahaushe yake zaune da iyalinsa, da kuma yadda al’amurra suke gudana na shawara tsakaninsa da iyalinsa.

Shi aure wajibi ne ga ɗiya macce, muddin dai ta kai minzalin shekarun aure, ta kuma samu masoyi mai nufin ya aure ta.

3.0.3 Ma’anar Aure.


Aure alaƙa ce ta halaccin zama tsakanin miji da mata, ana yinsa ne domin shi aure sunna ce ta Annabi Muhammada Rasulullahi (S.A.W) domin tsarkaka zuri’a. aure muhimmin abu ne ga al’umma saboda haka akwai hanyoyi da matakai na tabbatar da shi. Mataki na farko shi ne neman aure.

Aure wata yarjejeniya ce a tsakanin namiji da mace da kuma bin wasu ƙa’idoji da dokoki da wannan al’umma ta tanada domin samun zuri’a ta gari. (Magaji, A. 1999).

3.0.3.1 Neman Aure


Neman aure yakan fara ne daga lokacin samartaka, samartaka wani matsayi ne a rayuwar kowane ɗan Adam da yake farawa bayan ƙurciya. Ga ‘yan mata kuwa samartaka ana kiranta budurci. Neman aure yakan fara ne a lokacin da saurayi ya ga budurwar da yake so da kansa ko aka ganar masa ko ya ji labarinta, sai dai akwai wurare na musamman da saurayi ke iya ganin budurwar da yake so. Kamar, gidan ‘yan uwa da kasuwa da warin talla da hanya da makaranta da wurin buki da cikin mota da ta wayar salula da dai makamantansu.

A irin wannan lamari na neman aure a ƙasar Hausa, akan tanadi manyan abubuwa guda uku. Na farko dai waliyai, na biyu kuma sadaki sai na uku shaidun jama’a.

3.0.3.2 Toshi


Toshi dai wata kyauta ce da saurayi ke yi wa budurwa kuma wannan kyautar ka iya zama wani abun sakawa a jiki ko kuɗi ko abinci ko saye sana’arta da dai sauransu. A lokacin da can idan iyayen yaro suna son su haɗa shi da wata yarinya sukan fara toshin ta wato su riƙa kai kayan alheri ga iyayen yarinya su ce sun ɗaura ragga. Wato sun yi wa yaronsu kame. A wannan lokaci toshi yana iya zama kayan nagani ina so, ko kayan azumi da ake yi ko kayan salla da dai makamantansu.

3.0.3.3 Baiko.


Baiko dai shi ne alƙawarin da iyayen yarinya ke yi wa iyayen mai nema su ce sun ba shi ɗiayarsu ya aura sun aminta kuma sun yarda ya kasance mai tafiyar da lamurranta har ya zuwa lokacin aure. A wannan yanayi iyayen yaro ne suke zuwa gidan su yariya sai su nemi auren yarinyar ga ɗansu. Sukan je gidan su yi sallama sai a amsa masu su kuma ce sun zo neman iri, su kuma iyayen yarinyar sun sani cewa ga wadda suka zo nema sai duk da haka su kada baki su ce, “wa kuka zo nema?” sai iyayen yaro su ce “wance muke so ku bamu mu haɗa ta da wane su yi aure” nan take sai iyayen yarinya su ce, “mun baku bisa ga amana Allah ya nuna mana an yi da mu” sai iyayen yaron su bayar da abin da suka zo da shi kamar Tabarma, ɗan akuya, garin gero ko dawa, gishiri da goro a raba sai a yi addu’a sannan su tashi suna murna abin da suka je nema sun samu.

3.0.3.4 Tsarance


Tsarancev na nufin hirar tsakar dare tsakanin saurayi da budurwa. Bisa ga al’adar ƙasar Hausa da zarar an saka ranar aure to saurayi ko budurwa wani yakan gayyaci wani daga cikinsu. Wanda aka gayyata yakan je gidan wanda ya yi gayyata sai a kwana ana hira, kuma hirar ce kawai ake yi ba wani abu da zai biyo baya na lalata ko wata wasa. Ana yin haka ne domin samar da dangantaka da sabo da ƙarin ƙauna a tsakaninsu. Da musulunci ya zo sai aka yi watsi da wannan al’ada saboda tsarin musulunci da kuma ƙarancin gaskiya da riƙon amana tsakanin samari da ‘yan mata. Amma bayan zuwan turawa sai wannan al’adar ta sake dawowa kamar yanda aka santa.

https://www.amsoshi.com/contact-us/


3.0.3.5 Lehe


Lehe wasu tulin kaya ne da namiji ke yi wa matarsa da zai aura, wanda ke nuni da yanda zai riƙe ta bayan ta je gidansa. Ango kan nuna bajintarsa tare da gudummuwar wasu daga cikin danginsa da kuma iyayensa. Angi kan yi daidai ƙarfinsa kama daga atamfa da leshi da shadda da takalmi da jikkuna da sarƙoƙi da kayar shafe-shasfe da kayan kwalliya da turaruka da kayan gyaran jiki iri da sauransu. Ana zuba waɗannan kayan a cikin kwalla a wancan lokaci ko fantimoti. A yanzu kuwa ana saka kayan ne a cikin akwati mai tsada ta zamani. Sai dangin ango su ɗauka a riƙa bi gida-gida duk inda dangi suke ana nuna masu, a ce ga kayan wance na lehe. Sannan idan an gama gwada ma ‘yan uwa sai a kai a gidan su amarya su kuma su nuna ma nasu’yan uwan.

3.0.3.6 Sadaki


Sadaki dai shi ne  wani abu da aka iya bayarwa a matsayin wani rukuni na auren. Wasu sukan bayar da sadaki tun kafin a kai ranar aure wasu kuma sai a ranar aure suke bayar da sadaki. Sadaki wani babban rukuni ne daga cikin rukunan aure wanda ake bayarwa ga waliyan amarya. Sadaki ya danganta daga wasu, saboda wasu sukan karɓi kuɗi wasu kuma dabbobi suke karɓa, wasu kuma sukan nemi duk abin da Allah ya hore ma iyayen ango. Shi sadaki wasu sukan bayar da shi kafin aure wasu kuma sukan bi bashi bayan an yi aure in ango ya samu sai ya biya.

3.0.3.7 Sa Rana


Sa rana dai ana kai kayan sa rana a gidan su amarya daga nan sai iyayen su faɗi lokacin da suka tsayar na auren ‘yarsu. Galibi wannan iyayen ango su ne suke zuwa su tambayo lokaci wato su buƙaci a faɗa masu lokaci (a saka lokaci), wani lokaci iyayen sukan ce su iyayen ango su tafiya sai su aika masu da lokaci wani lokaci kuma a nan ake faɗa masu lokacin. Iyayen ango sukan kai kaya da suka haɗa da: goro dabino da alewa daga nan kuma sai ranar buki inda za a sha shagali.

3.0.4 Waɗanne Sharuɗɗa ne Ake Bi A Ƙulla Aure A Al’adar Hausawa.


Da farko dai ba wasu sharuɗɗa da ake bi waɗanda suka wuce amincewar iyayen ma’aurata domin a al’adance iyaye ne ke ganin dacewar auren ‘ya’yansu kuma sai su haɗa auren a tsakaninsu kuma su zauna lafiya da juna ba da wata matsala ba.

Daga baya ne aka sami sharuɗɗan amincewar ma’aurata kafin a yi masu aure a nan ne saurayi kan nemi amincewar budurwa da ta aure shi har iyaye su shigo kuma a yi aure a kan hakan.

Idan iyaye ba su aminta ba ko ma’auratan ba su aminta ba to auren ba zai yiwu ba ko kuma wani ɓangare bai aminta ba sai a sami wata matsala. . (Bunguɗu H.U. 2013).

3.0.5 Kashe – Kashen Aure


Masana da manazarta da dama sun karkasa aure na al’ummar Hausawa zuwa kashi-kashi daidai da yadda suka ga abin yana gudana. Ga dai wasu daga cikinsu.

3.0.5.1 Auren Soyayya


Ita dai soyayya wata bau ce da Allah (SWA) yake halittawa a cikin zukatan mutane. Wasu daga cikin al’ummar Hausawa suna yi mata kirari da cewa, “Soyayya gamon jini”. Wannan kirarin dai bai ƙayyade waɗanda jininsu zai gamu ba, kuma ita soyayya ba dole sai tsakanin saurayi da budurwa ba tana iya faruwa tsakanin ɗa da uwa ko uba, ko tsakanin wa da ƙane ko aboki da aboki ko ɗau’uwa da ɗan’uwa. Amma dai a wannan yanayi an fi danganta wannan soyayya da saurayi da budurwa.

Auren soyayya dai aure ne da ake gina shi a kan tafarki na masoya, tare da yardar miji da da mace. Wannan ya danganci ƙaunar da ke tsakanin ma’auratan, wato kowa yana muradin abokin tarayyarsa.

3.0.5.2 Auren Zumunta


Wannan nau’in aure ana gina shi ne tsakanin mutane biyu da suke da zumunci na ‘yan’uwantaka a tsakaninsu. Irin wannan auren iyayen ma’aratan ne ke haɗa shi, su za su yanke shawarar su haɗa wane da wance. A nasu tunani wannan auren zai kara danƙon zumuncin da ke tsakanin su iyayen har abin ya ɗore zuwa ga ‘ya’ya. Wannan nau’in auren dai bai cika daɗewa musamman idan ba a haɗa auren saboda Allah ba, kuma in aka yi shi saboda wata manufa sai ka ga an samu ɓaraka har ta kai ga zumuncin ya lalace.

3.0.5.3 Auren Tilas


Auren tilas wani nau’in aure ne akasin na soyayya da wasu iyaye ke haɗawa don son rai ko wani abin duniya, ta hanyar haɗa wani da wata aure ba tare da suna buƙata ba. Takan yuwu macen da za a haɗa da wani tana da wanda take muradi sai a hana ta ɗaura mata aure da wani. Ko kuma shi namijin da za a yi wa aure yana da wata da yake muradi sai a hana shi a tauye shi ya auri wata da ake buƙata shi ya aura ba don yana son ta ba, sai dai don ba yadda zai yi.

Irin wannan nau’in auren yana hardasa ɓarna, domin kuwa wani na iya aikata abin da ba daidai ba ko ma lamarin ya kai ga kashi (salwantar rayuwa).

3.0.5.4 Auren Sadaka


Wannan auren an fi yinsa a ƙauye kuma a wancan zamani na dauri. Ana ɗaura wa yarinya aure a kai ta gidan miji ba tare da ya sani ba ko ya nemi warin zamanta.

Irin wannan aure wanda yake da ɗiya kuma yake da ƙudurin yin sadaka da ita, sai ya zauna da iyayenta da duk wani mai haƙƙi ya gaya masu cewa zai yi sadaka da wance, cewa da ɗiyarsa za su amsa masa, sai ya yi shawarar wanda zai ba. Yana iya barin abin a zuciyarsa kuma yana iya kallon hankalin yariyar da kuma kiyon hankalinta tare da duba hankalin wanda yake neman ya haɗa su da shi.

A wancan lokaci idan za a yi sadaka da mace, akan duba a gani cikin masu hulɗa ta nema da ita wa ta fi so? Ko a nemi wani almajiri wato mai neman ilimi wanda aka san cewa, zai iya zama da mata cikin koyarwa ta shari’a tare da bin dokokin al’adun Hausawa, sai a ɗaura aure uban yarinya ya biya sadaki ya yi komai ya kaita gidan mijin da zai ba sadaka ba tare da wanda za a ba matar ya san cewa shi za a kai ma ba.

3.0.5.5 Auren Dangana Sanda


Auren dangana sanda aure ne da ya ta’allaƙa ga manya ba samari da budurwa ba. Irin wannan aure wasu da suka taɓa yin aure suke yinsa, kuma idan aka ɗaura babu zancen yin bukukuwa ko kai amarya. Inda matar take nan za a barta sai da shi mijin yazo duk ranar kwananta ya kwana nan in safiya ta waye ya kama hanyarsa ta komawa a gidansa na asali.

Ana kiran wannan nau’in aure ne da dangana sanda saboda shi mijin da zai zo galibi yaka zo da sandarsa kuma idan zai shiga ɗaki yakan dangane ta a waje ga ginin ɗakin. Idan Allah ya gwada masa safiya ta waye sai ya ɗauki sandarsa ya kama hanyarsa.

3.0.5.6 Auren ‘Dibar Wuta


Wannan aure shi ma aure ne na muatanen da suka saba da yin aure. Kuma shi ma ba saurayi da budurwa ke yinsa ba. Wani sanadi ke haifar da shi. Idan mata da miji suka samu matsala har ta kai ga saki to akan duba adadin yawan sakin da mijin ya yi, idan sakin ya kai uku, to dole ne matar ta fita bayan ta cika idda sai ta auri wani. Duk yadda suke son juna ita da mijin ba za su koma zama sai har ta auri wani, in auren ya ƙare tsakaninta da shi sai ta fito ta koma auren mijinta.

Akwai sharaɗi a wannan auren na ba za a gaya wa wanda zai aura ba, kuma ba za a je a yi wani abu marar kyau ba don ya saketa ta koma wa wancan mijin nata ba. Sai dai a jira ranar da wani abu ya aukuhar ta kai ga maganar saki sai ta cika idda ta sake auren mijinta da take so yana son ta.

3.0.5.7 Auren Jeka –da-kwarinka


Irin wannan aure manyan mata ne yinsa masu abin hannunsu suka fi yinsa. Saboda haka ba za su iya tarewa a gidan sabon mijinsu ba. Don haka sai su yi yarjejeniya shi zai riƙa binta a gidanta a duk ranar aikinta. Haka kuma tana iya zamowa mijin ya nema mata gida nata na kanta, wato dai ya ware ta da sauran iyalinsa, gudun kada wata matsala ta auku ko a ga wani fifiko da zai bata, kuma shi ne zai riƙa zuwa ba ita ba. Wannan shi ne ake kira auren jeka da kwarinka.

A wancan lokaci na dauri da yake akwai namun daji kewaye da garuruwa a ƙasar Hausa, idan wani ya yi auren jeka da kwarinka, yakan tanadi makami domin kare kansa daga namun daji masu cutarwa. Don haka irin wannan matar da zai aura za ta kasance tana wani ƙauye, kuma ya zama wajibi ya je wurinta duk lokacin da yake ranar kwananta ne. yakan tanadi kwari da baka domin samun sauƙi ga harin wasu namun daji da zai haɗu da su a hanyarsa ta zuwa garin da matar take.

3.0.5.8 Auren Buta


Auren buta dai nau’in auren Hausawa ne da ake yinsa tsakanin tsofaffin mutane waɗanda ba su da sauran ƙarfi. Wannan ana yinsa ne ba don komai ba sai don a ribanta da ladar zamantakewa ta aure. A wannan aure ba a tsammanin za a samu haihuwa a cikinsa. Kamar dai yadda aka kira shi ba wata moriya ta ma’aurata in banda ban buta in yi alwala ko tsarki ko wata buƙata da za a yi ta da butar.


Babi Na huɗu


4.0.1 Tsokaci A Kan Auren Hausawa.


A tarihi babu wani ƙayyadajjen lokaci da yaro zai kai a yi masa aure a al’adar Hausawa wto yawan shekarunsa ko girmansa. A ƙasar Sakkwato akwai bayanin yiwa yara aure tun suna datsa wato ƙasa da shekaru bakwai. A lokacin sai dai uwar yaro ta yi masu wanka ta kai su ɗakinsu kuma ta riƙa kula da sasanta rigingimmunsu na yau da kullum. Har dai su girma su san cewa aure ne ke tsakaninsu. Amma dai wannan ba koyaushe ne ake yinsa ba. Kuma ba wasu shukaru da mutum zai kai har ya yi yawa ga aure. Idan ba a yi masa wannan ba sai ya nema da kansa daga baya.

Tun kafin zuwan musulunci al’adar Hausawa ba ta ƙayyade ba wato ba a iyakance yawan matan da mutum zai aura ba, amma dai ya fi farawa da ɗaya. Bincike ya nuna cewa wasu masu zarafi sukan fara da biyu, amma ba su cika yawa ba. Bahaushe yana iya auren mata ko nawa yake iyawa daidai da ƙarfin arikinsa ko lafiyarsa ko sha’awarsa.

A al’adar Hausawa maigida shi ne shugaba kuma kowa da kowa dole ne ya yi byayya gareshi. Mata kan yi biyayya ne ɗari bisa ɗaari ga duk abin da maigida ya shimfiɗa a gidansa, haka ‘ya’ya da jikoki da barori da sauransu. Matansa kan bishi zuwa gonarsa don su taya shi noma da dai duk wani aiki da ya basu. Komai na gidan wanda aka samu mallakar maigida ne, kuma shi ne mai ikon kansa.

Hausawa suna da nau’o’in aure daban-daban da suka haɗa da auren soyayya, auren gayya, auren ɗibar wuta, auren dangana sanda, auren isa, auren buta, auren sadaka, auren tilas, auren jeka da kwarinka, auren zumunci da sauransu. Waɗannan nau’o’in aure duk ana yinsu a cikin Al’ummar Hausawa.

Wasu al’adu da suka haɗa da: neman aure da toshi da baiko da da lehe da tsarance da sa rana da dai sauransu duk suna gudana a cikin lamarin auren Hausawa.

4.0.2 Yaudara


Yaudara dai kamar yadda muka sani tana nufin cin amana. A taƙaice dai yaudara na nufin dafe ko taushe haƙƙi na wani ko wata na abin da ya shafi kuɗi ko wani abu da ake iya gani da daraja ko yashe farin ciki ko muzguna wa ɗarsashin rayuwa.

Ana samun yaudara tsakanin mutane biyu ko fiye, takan iya aukuwa tsakani namiji da mace ko namiji da wani namiji ko aboki ko ɗan’uwa haka ma ana samun ta tsakanin mace da mace ko ƙawa da ƙawa ko abokiyar zama. Lamari yana faruwa da kowa musamman idan wata harƙalla ta haɗa wani da wani ko wata.

4.0.2.1 Yaudara a cikin Neman Aure


Yaudara dai wata abu ce da aka samun ta a tsakanin ‘yammata da samari a cikin neman aure. A yau masoyi zai yaudari masoyiyarsa da sunan yana son ta kuma yana son ya aureta, amma ba haka ba ne shi ba aurenta a zuciyarsa yana son ta ne saboda tunanin zai samu wani abu daga ɓangarenta, ko dai iyayenta masu kuɗi ne yana son samun wani abu daga ɓangarensu daga ya samu ya gudu, ko kuma ita ce mai kuɗin yana buƙatar kuɗin sai ya nuna mata soyayya, da zarar ya samu sai ya ƙara gaba. Ko kuma yana da wata buƙata ta shi ta daban da ya samu biyan buƙatar sai ya gudu. Ya riga ya yi mata illa ko dai son sa ya yi mata yawa, ko kuma ya karɓe mata dukiya, ko ya lalata mata rayuwa.

Haka kuma su ma a ɓangaren mata su ma yaudara takan shiga sai ka ga mace ta samu wani wanda zai yi ta yi mata hidima, shi yana da ƙudurin ya aureta, ita kuma ba shi ne manufarta ba. Ma’ana kamar dai yadda Hausawa ke cewa, “Ana riƙa mugu kafin na ƙwarai ya samu” wato ta yarda da shi ne kuma za ta ci kayansa, amma ba shi take so ba. Kuma ba za ta aure shi ba sai dai ta yi ta amfani da son da yake yi mata ta ci dukiyarsa (kuɗi).

Wasu matan sukan ɗaura dukkan nauyi na wata lalura ga wanda ke son su kuma alhali sun san ba shi ne ke cikin zuciyar su ba. Kuma daga ƙarshe za su ƙirƙiri wani abu da zai hardasa rabuwarsu.

4.0.3 Makirci


Kamar yadda muka samo ga wani malami mai suna Balarabe Sani a nan garin Gusau, ya bayyana muna cewa, “ Makirci na nufin ƙulla wani sharri da zai bayyana wani mummunan aikin zuwa ga wani wanda bai ma san hawa ba bai san shiɗa ba, sai a danganta wannan aiki da shi domin shafa masa wani fenti da zai kawo kyama ko ƙiyayya tsakaninsa da wani ko wasu”.

Haka kuma a tamu fahimta “Makirci yana nufin tsara wani mumunan zance a ta’allaƙa shi ga wani wanda bai da alhaki ga wannan zance, ma’ana bai faɗa ba a ce, shi ne ya faɗa, domin a ɓata sunansa ga wani ko wasu”.

Irin wannan zance na makirci da ake tsarawa a danganta shi ga wani yana faruwa ga kowace al’umma ta duniya, ba wai Hausa kaɗai ba. Amma a nan wanda za mu taɓo wanda ake yi ne a cikin neman aure kawai.

4.0.4 Yaudara Da Makirci a Cikin Neman Aure.


Neman aure wani al’amari ne wanda yake faruwa tsakanin namiji da mace, wanda ya ƙunshi wasu sharuɗɗa waɗanda a cikinsu akwai sanin haƙƙin abokin zama da sana’arsa da asalinsa da halayensa na gari da miyagu da tarbiyarsa da iliminsa da kwazonsa da dai sauran wasu abubuwa makamantan waɗannan.

Mai neman aure ana sa ran zai iya sani asalin wadda yake nema da iliminta da tarbiyarta da ƙwazonta da halayenta na gari da akasinsu da dai wasu abubuwa da suke tattare da ita. Haka kuma shi ma namijin da yake neman aure, ana duban waɗannan abubuwa wato asali da ilimi da addini da sana’a da kwazonsa da halayensa na gari da akasinsu da dai sauran abubuwa makamantan waɗannan.

Waɗannan abubuwa da neman aure ya ƙunsa sun yi daidai da shari’a, kuma a yayin nemansu ne duk wata matsala take aukuwa. Ana iya samun yaudara a tattare da nemansu kuma ana iya samun makirci duk a cikin saninsu.

A wannan yanayi ne a yau, yaudara da makirce-makirce suka dabaibaye neman aure a wannan yanki na Hausawa. a wannan lokaci wanda bai rasa nasaba ba da son abin duniya da mutanen wannan zamani suka sa a gaba, ya sa ba su iya ko neman asali da halaye da dai duk abin da shari’a ta tanada, su dai idonsu a rufe ‘ya’yansu su samu miji mai kuɗi ko kuma in namiji ne shi dai ya auri ‘yar mai kuɗi. Wannan ke sa yaudara ta shiga. Idan kuma yaudara ta shiga to neman yana iya lalacewa.

4.0.5 Abubuwan Da Ke Kawo Yaudara a Neman Aure.


Akwai wasu abubuwa da suke taimakawa ga samun galaba na yaudara a yayin da ake neman aure. Waɗannan abubuwa sun haɗa da:

1.     Ƙarya: A halin yanzu kusan ita ce mafi kusan abin da ‘yammata da samari ke yin amfani da ita domin neman wani matsayi wanda ba su kai shi ba. Suna yin wannan ne ba don komai ba sai don su samu shiga a wurin wanda suke son su mallaki zuciyarsa. Ƙarya a cikin neman aure ta kasu kashi-kashi kamar haka:

1.     Yin ƙaryar gida

2.     Yin ƙaryar Mota


  • Yin ƙaryar dangi


1.     Yin ƙaryar wurin aiki

2.     Yin ƙaryar sutura


1.     Yin ƙaryar gida: wannan ya ƙunshi abin da muka faɗi a baya yaro zai yi ƙaryar cewa, ai yana da gidaje, saboda ya san sai wanda ya mallaki gida ne zai zo da maganar aure. Yana kuma iya dubin yanayin yadda yarinyar ke buƙatar gida ya gaya mata fiye da tunaninta. Haka zai tsara wa yarinya yawan gidajensa domin kawai ya mallake zuciyarta da ta iyayenta.

2.     Yin ƙaryar Mota: wannan ma kamar wancan ne, zai iya aron motoci kala-kala yana zuwa wurin yarinyar da yake nema da su, ba zai yarda ya zo wurinta da irin motar da yazo da ita ba jiya. Kullum sai ya aro wata kala domin kawai ya samu yarinyar ta amince da shi a zuciyarta.


  • Yin ƙaryar dangi: Saurayi kan yi ƙaryar dangi idan yana son ya mallaki zuciyar budurwa, haka kuma itama takan yi ƙaryar dangi domin ta samu galaba ga zuciyar saurayi. Amma an fi samun ƙaryar dangi a wurin maza. Za su ce ai su ‘yan dangin wani mai kuɗi ko mai mulki ne saboda su samu karɓuwa ga zuciyar wadda suke nema aure da iyayenta.


1.     Ƙaryar Wurin Aiki: Ita wannan ƙaryar samari ne suka fi yinta, sukan yi ta ne don su samu shiga ga budurwa, zai nemi wurin aikin da yasan ‘yan’uwan yarinyar ba su da alaƙa da wurin kuma ya san wurin babbar ma’aikata ce, sai ya yi ƙaryar cewa, shi a can yake aiki. Kuma ya gaya masu cewa, yana da babban muƙami a ma’aikatar.

2.     Yin Ƙaryar sutura: Wannan ma shi ne mafi sauƙin ƙarya daga cikin ƙaryaryakin da samari da ‘yanmata ke yi a yau. ‘Yanmata sukan yi aron sutura a wurin ‘yan wanki da ƙawayensu da yayyensu da dai sauran wurare. Haka kuma suna iya yin tariyar kuɗi su ɗunka kaya masu tsada duk don samarinta su ɗauka cewa ita wata ce, ko ɗiyar wani ce. Haka kuma su ma samari sukan yi ƙaryar kaya kamar su matan sai su je neman auren matan don dai su mallake zuciyar ‘yanmatan.

3.     Gasa: Gasa yanayi ne mutum zai sa kansa cewa sai ya yi duk irin abin da ya ga wani ya yi ko ta halin ƙaƙa, ko da bai kai matsayin wancan ba. Haka kuma ana kallon gasa a matsayin wata hanya da take kawo yaudara ga neman aure. Domin wasu iyaye suna buga misali da abin da aka yiwa wasu, domin a yi wa nasu yayan ko kuma su maza su dauki cewa yadda wani ya yi sai sunyi hakan ko fiye da hakanan ko da ba su kai ƙarfi wancan ba ko kuma ba su yi halin da za su yi abun ba, amma sun ɗauki abin ya zama masu dole sai sunyi kuma su shiga hanyar da zasu samu abin da za su yi wanda daga ƙarshe kan jefa su cikin abind a bai dace ba domin samun galabar macen ko namiji.

4.     Kwaɗayi: Bahaushe ya ce “kwadayi maduɗin wahala” kuma haka zancen yake duk wanda ya shiga motar kwaɗayi to za ta ajiye shi tashar walaƙanci ko wahala”. Haka kuma duk makirce-makircen da ke faruwa a lokacin neman aure tsakanin mace da namiji kwadayi ne sila. Haka kuma kwaɗayi ke kawo duk wata yaudara a cikin neman aure. Wannan yana samuwa daga yarinya ko yaron ko dangi na yaron ko na yarinyar.

5.     Son girma: Wannan wani yanayi ne wanda mutane kan sa kansu yayin neman aure, sai ka ga yaro ko yarinya, suna nuna cewa, su ‘yan babban gida ne ko kuma su nuna cewa, suna da wani matsayi wanda ba haka ba ne, ko kuma matsayin da bai kai hakan ba, domin su cimma gurinsu na samun aure ko kuma wata manufa ta daban. Wannan zai sa yaro ya ɗauka cewa shi wani ne, haka ita ma yarinyar wannan na sa ta ji cewa ita wata ce.

4.0.6 Illolin Makirci Da Yaudara a Cikin Auratayyar Hausawa


Duk abin da ba a yi shi a kan gaskiya ba kuma ba don Allah ba to babu shakka za a samu matsaloli tare da illoli masu tarin yawa, kuma al’umma kanta ba za ta zauna lafiya ba. Kuma komai daɗewar wannan al’amarin to sai ya samu matsala.

Yin yaudara da makirci a cikin neman auren Bahaushe yana da illoli kamar haka:

1.     yawan mutuwar aure

2.     rashin ganin mutunci

3.     gaba

4.     rashin yarda da sauransu.

Waɗannan su ne manyan illolin da yaudara da makirci suke yi wa al’ummar Hausawa. kuma waɗannan illolin sun yawaita ga al’umma.






Babi Na Biyar


5.0.1 Jawabin Kammalawa.


Alhamdulillahi godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki Mai Kowa Mai komai, Mahaliccin sammai da ƙassai da ya bamu ikon kammala wannan aikin Bincike. Yabo da jinjina ga AnnabinSa Muhammadu (SAW) Imamin Manzanni Cika makin Annabawa Muhammadu ɗan Abdullah, da iyalan gidansa da Sahabbansa da magoya bayansa tun daga farko har ƙarshe.

Saboda a nan ne za mu naɗe tabarmar wannan bincike. Kamar yadda aka gani a baya mun raba aikin nan namu gida biyar bisa ga tsarin babi-babi har babi biyar.

Babi na farko ya ƙunshi, Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallin Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike, Matsalolin da Suka Taso da Matsalolin da aka fuskanta.

A babi na biyu kuwa kamar yadda doka ta tanadar mun kawo Waiwaye A Kan Ayyukan da Suka Gabata kana muka yi bayanin Salon Nazari da Tsarinsa.

A babi na uku kuwa a nan ne muka yi bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Hausawa, da wasu al’adun Hausawa na aure, inda har muka faɗa cewa auren Hausawa ana gudanar da shi ta hanyar bin wasu matakai da suka haɗa da: neman aure da toshi da baiko da tsarance da kai lehe da sadaki da sa rana da tarewa. Duk kafin wannan mun kawo ma’anar aure daga masana.

A babi na huɗu kuma nan ne muka yi Tsokaci A Kan Auren Hausawa, inda har muka ce Bahaushe shi ne wanda yake gudanar da komai a gidansa. Kuma kowa a gidan yakan ba shi girma yana da ikon ya auri mata fiya da ɗaya. A wannan babi ne muka yi tsokaci dangane da yaudara da makirci da yadda suke faruwa, mun bayyana masu yinsa da. Bayani a kan yadda ake shirya yaudara a cikin neman auren Hausawa da makirci duk mun zayyano shi a wannan babi. Mun kawo wasu hanyoyi da ake bi wajen yin yaudara kuma mun faɗi illolin da yaudara da makirci ke kawowa ga neman aure.

Sai a wannan babi na biyar inda muka yi yunƙurin naɗe tabarmar wannan bincike namu, ga shi kamar yadda aka tanada muka yin jawabin kammalawa daga shi kuma sai shawarwari da za mu bayar ga mai karatu da waɗanda wannan sha’ani ya shafa.

5.0.2 Shawarwari


Muna son mu yi amfani da wannan damar mu ba ‘yan’uwanmu ɗalibai shawara su mayar da hankali wajen gudanar da sha’anin karatunsu tare da yin ƙoƙari gwargwadon hali, su kasance masu gwazo ga karatunsu. Idan kuwa Allah ya kai su ga lokacin da za su gudanar da bincike in suka ci karo da wannan aiki namu to su yi ƙoƙari su ɗora daga inda muka tsaya na wannan bincike.

Muna kira ga wasu waɗanda ba nazarin wannan kundi sukai ba da su yi ƙoƙari su koyi darussan da ke cikin wannan kundi kar su yi ƙasa a guiwa su kasance masu kyautatawa da neman ilimi da kauce wa abin duk da za ya sa a yi masu kallon da bai dace ba.

Haka kuma muna kira ga al’ummar da suke gudanar da aure da su kasance masu kula da haƙƙin addini a cikin sha’anin neman aurensu, kuma su kaucewa yaudara da kuma ƙulla makirci ga manema aure.

Manazarata




Post a Comment

0 Comments