The Place of articulation also point of articulation of a consonant is the
point of contact where an obstruction occurs in the vocal tract between an
active articulator and a passive articulator…
ALH 203: Hausa Phonology 1
(Wurin/Gurbin Furuci (Place of Articulation))
Muhammad Arabi Umar
Department of Languages and
Cultures
Federal University
Gusau
Ma’anar Wurin
Furuci
“Wurin furuci shi ne
daidai inda mafurci mai motsi ya haɗu da marsa motsi wajen aiwata wani baƙi” Sani, (1999).
Translation:
The Place of
articulation also point of articulation of a consonant is the point of contact
where an obstruction occurs in the vocal tract between an active articulator
and a passive articulator.
Wuraren Furuci da
suka shafi baƙaƙen Hausa guda bakwai ne, kamar haka:
We have seven places
of articulation that concern Hausa consonants, namely:
i.
Baleɓe
(Bilabial)
ii.
Bahanƙe
(Alveolar)
iii.
Naɗe-harshe
(Retroflex)
iv.
Ɗan
Bayan Hanƙa (Post-alveolar)
v.
Baganɗe
(Palatal)
vi.
Bahanɗe
(Velar)
vii.
Hamza (Glottal)
Baleɓe : Inda leɓen ƙasa ya kusanci leɓen sama ko ya haɗe da
shi.
Bilabial: When the lower lip is in contact
with or approaches the upper lip.
/b/, /ɓ/,/m/ and
/ϕ/ as in “baka”, “ɓarawo”, “malam”, and “fata” respectively.
Bahanƙe: Inda tsinin
harshe ya kusanci tsinin hanƙa ko ya haɗe da shi
Alveolar: it
refers to a sound made by the tip
of the tongue in contact against or touches the alveolar ridge.
/d/ “dankali”
/t/ “talata”
/n/ “nama”
/r/ “bara”
/z/ “zakka”
/s/ “sani”
/l/ “lada”
/s’/
“tsawa”
Naɗe-harshe: Inda tsinin harshe da bayan tsinin
hanƙa suka haɗe.
Retroflex: It refers
to a sound made when the tip of the tongue is in contact with the back of the alveolar ridge.
/ɽ/
as in “ruwa”
/ɗ/ as in “ɗaki”
Ɗan Bayan Hanƙa: Inda
ƙirjin harshe da bayan tsinin hanƙa suka kusanci juna ko suka haɗe.
Post-alveolar: It
refers to a sound made when the blade of the tongue is near or touches the back
of the alveolar ridge.
/ʃ/
as in “shara”
/ʤ/
as in “jaki”
/ʧ/
as in “caca”
Baganɗe: Inda gaban
harshe da ganɗa tsattsaura suka kusanci juna ko suka haɗe.
Palatal: it
refers to a sound made when the front of the tongue is in contact with
or approaches the hard palate.
/ɲ/ as in “hanya”
/j/
as in “yara”
Bahanɗe: Inda doron
harshe ya kusanci hanɗa ko ya haɗe da ita.
Velar: it
refers to a sound made by the back of the tongue against the velum, or soft palate.
/g/ as in “gado”
/k/ as in “kaza”
/ŋ/ as in “can”
/ƙ/ as in “ƙasa”
/w/ as in “wasa”
Hamza: Inda tantanin
maƙwalloto ya ja ya rage faɗin maƙwallato ko ya ja ya rufe faɗin maƙwallaton baki ɗaya.
Glottal: it is a sound made in the larynx, due
to the closure or narrowing of the glottis.
/h/ as in “hannu”
/?/ as in “sa’a”
Baƙaƙe Masu Goyo
(Consonants with Secondary Articulation)Leɓantaccen bahanɗe (Labialized velar) Is a velar consont
that is labialized with /w/ in secondary articulation.
/kw/ as in “kwakwa”
/ƙw/ as in “ƙwallo”
/gw/ as in “gwanda”
Ganɗantaccen baleɓe (Palatalized bilabial) Is a bilabial
consonant that is palatalized with /j/ in secondary articulation. /ϕj/ as in “fyaɗe”
Ganɗantaccen bahanɗe (Palatalized
velar) Is a velar consonant
that is palatalized with /j/ in secondary articulation.
/kj/ as in “kyanwa”
/ƙj/ as in “ƙyama”
/gj/ as in “gyara”
Ganɗantacciyar
Hamza (Palatalized glottal) Is a
glottal consonant that is palatalized with /j/ in secondary articulation.
/?j/ as in “‘ya’ya”
5 Comments
Very interested in Arabic we have five main articulation and their categories
ReplyDelete1. Aljauf ( The empty space of the mouth and throat)
2. Alshafatain (The upper and lower lips)
3. Alkhaishum (The nasal cavity)
4. Alhalq (The throat)
5. Allisan (The tongue)
Cartego
That is great.
DeleteThanks for sharing.
Allah ya saka da alheri
ReplyDeleteMUNA godiya
ReplyDeleteMasha Allah mungode da wannan kokari naka. Zamu so acigaba da dauka topics daya bayan daya Ana mana bayani domin yaranmu sufahimci Hausa da turanci.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.