Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Nazarin Jumla a Nahawun Hausa

Zai fito da  tsarin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa fili ta yadda mahimancinsa zai bayyana don samun sauƙin fahinta...


HAMISU YUSUF
08036384676


BABI NA ƊAYA

GABATARWA


1.0 Shimfiɗa


Nahawu harshen Hausa fage ne da manazarta suka gudanar da zuzzurfan bincike a kansa. Duk da cewa harshen Hausa ya na da wadatattun kalmomi da kowane harshen duniya yake da su. Nahawun harshen Hausa ya na da rassan nazari guda biyar manya Akwai fanni nazarin gundarin sauti da na nazarin tsarin sauti, har-ila-yau akwai fannoni ginin kalma da na ginin jumla da kuma na ilimin ma’ana. Masana da mazarta ba fannin da ba su gudanar da nazari a kansa ba, sai dai idan aka yi la’akari da karin maganar harshen Hausa da ake cewa “ilimi gulbi ne mai zurfi wanda ba a kure shi”. Kenan duk da irin gudummawar da aka bayar, har yanzu akwai sauran abin dubawa. Sanin haka shi ya sa nazarin ya fara da bitar ayyukan da suka gabata a babi na ɗaya, sannan a ciki an bayyana dalilin da ya sa ake son gudanar  da wannan nazarin .

Bayan bitar ayyukan da masana da manazarta, suka gudanar, da shi an ƙebe wa nazarin hujjar gudanuwa. Don haka aka ƙebe wa nazarin farfajiya a fannin ilimin ginin jumla. Aikin zai sanmi nasarar gudunuwa ne ta bin hanyoyin gudanar da bincike kamar yadda aka bayyana a nan gaba. Da irin muhimmancin da binciken yake da shi in an kammala, naɗewa ita ce marfin babin.

A babi na biyu mai suna “Azuzzuwan kalmomi a taskar masana nahawu”. Sauran fannonin nazari na ilimi shi ne ake ganin ya dace a gudunar da bincike a fannin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Da fatar Allah ya sa a sami nasarar gudanar da binciken bisa ƙa’ida domin amfanin masu bincike da manazarta harshen Hausa.

1.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


Masana da dama sun gudanar da ayyuka a kan nahawun Hausa, tun daga Turawan mulkin mallaka da suka yi aikin rarraba ɓangarorin nazarin nahawun Hausa, bisa tsarin harshe Ingilishi har zuwa ga masana ‘yan gida da suka gaji Turawan, duk abun guda ne. Ire-iren waɗannan ayyukan masanan zamani musamman waɗanda suka gudunar da aikinsu kan yankin suna da ajin sifa da kuma ajin kalmomi masu aikin irin na nahawun harshen Hausa. Inda wannan aikin zai baje hajarsa a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Da farko kafin a shiga ka’in-da-na’in cikin aikin za a yi waiwayen  ayyukan da aka gudanar waɗanda suka shafi nazarin ginin jumla a nahawun Hausa.

Galadanci, 1976. Ya rubuta littafin mai suna “An introduction to Hausa Grammar”. A cikin wannan littafin an yi zancen kan nahawun ginin jumla, inda aka nazarci wasu mahimman abubuwa ɗangane da ginin jumlar Hausa. Amma a cikin wannan nazarin za a  fito da hanyoyin nazarin jumla ne a nahawun Hausa, ba tare da keɓe wasu ɓangarori ba wannan nazarin za a fito da Hanyoyin nazarin jumla  ne a nahawun Hausa.

Galadanci da Wasu, 1980. Sun wallafa wani littafi mai suna “Hausa a Textbook of Methodology.” Littafin ya yi bayanin jumloli masu ƙunshe da fi’ili a cikin nahawun Hausa. Bayaninsu ya taƙaita ne kan jumla mai ɗauke da fi’ili da lokaci a cikinsa, a nan bayaninsu ya taƙaita. Wannan binciken zai zayyano ire-iren Hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, kamar  yadda suke a sauran harsunan duniya.

Skinner da Wasu, 1976. Sun wallafa littafi mai suna “Hausa a sauƙaƙe: jagoran nahawun Hausa”. A cikin wannan littafin an kawo bayani akan azuzuwan kalmomin Hausa da ƙa’idojin rubutun Hausa. Wannan littafin yana da alaka da da wannan nazarin Sai dai wannan aikin zai bi sawun hanyoyin nazarin jumla ne a nahawaun Hausa, maimakon sanin azuzuwan kalmomi kawai.

Calvin, Y.G. 1985.  Ya rubuta wanni littafinsa mai suna “Nazarin Hausa a ƙananan makarantun sakandare na ɗaya’’. A nan ya yi bayani kan Sasauƙar jumlar Hausa sai dai ya tsaya ne kan cike gurabe, ba tare da an gudanar da gamsashen bayani game da jumlar Hausa ba. Shi kuwa wannan aikin zai yi tsokaci ne a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Zaria, A.B. 1981. Ya rubuta littafi mai suna “Nahawun Hausa”. A cikin wannan littafin ya takaita bayanin wasu matakan nazarin jumla irin su; suna, aikatau, lokaci, amsa-kama, tare da misalan jumloli nahawun Hausa a nan aikin ya tsaya. Bai ci karo  da wannan nazarin ba,  domin shi wannan nazarin ya dubi hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Umar, 1985. Ya gudanar da aikinsa na kundinn digiri na farko a Sashen Harsunan Nijeriya, Jamia’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, kan “Bishiyar li’irabi a cikin nahawunn Hausa”.  Wannan aikin na Umar Cike yake da matsaloli dangane da rabo ko bayanan wasu  daga cikin azuzuwan kalmomin harshen Hausa. Ya dubi ƙwayoyin harshen Hausa  ta fuskar ajin nasaba da mallaka, amma a daidailiyar Hausa. Don haka ba zai ci karo da wannan aikin ba, saboda shi wannan aikin ya yi tsokaci da bibiyar hanyoyin nazarin jumla ne a nahawun Hausa.

Lawal, 1985. ya gudanar da nasa bincike a kan ajin Sifa, mai taken “Gurbin Sifa a cikin jumlolin Hausa” a sashen harsunan Nijeriya na jami’ar Usmanu Danfodiyo sasakkwato. Inda ya dubi yanayin zuwan ajin sifa tare da suna. Sannan ya dubi yadda kwayoyin ma’anar –n da -r ta fuskar zaman takewar sifa da suna, tsarin daidaiciyyar Hausa. Sai dai wannan aikin zai yi bayani ne game da hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, tare da waiwayar azuzuwan kalmomin nahawun Hausa.

Umar, S. 2012. Ya gudanar da aikinsa na kundinn digiri na biyu a sashenn harsunan Nijeriya, jami’ar Usmanu Danfodiyo sakkwato, kan “Matsayin ’yan Rakiya a Yankin Suna: Tsokaci a kan ƙirgau”. Inda aikinsa ya dubi wasu sassa na nahawu. Don haka ba zai ci karo da wannan aikin ba, saboda shi wannan aikin zai yi bayanin hanyoyin nazarin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Amfani, A.H. 1995. Ya yi zuzzufar nazari a kan “giredin aikatau na Hausa” domin ya sama masa matsuguni sosai a rabe-raben kalmomin Hausa, shi giredi kwayar ma’ana ce mai aiki irin na nahawu (functional categoriy) a cikin jumla. A nan ya yi bayani aikatau Hausa da aka nazarce su bisa tsarin nazarin na ci gaba zamani. Nazarin zai tsaya ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Amfani, A.H. 1996. Ya gudanar da nazari a kan ”Aspect of Agreement Relations in Hausa Clause Structure”. A nan ya yi bayanin Mafayyaciya wato (agreement element (AGR) ) da lokataƙ (tense aspect) da ajin sifa kuma ya bayyani gamsashe bisa tsarin nazari na  zamani. Amma wannan aikin zai yi bayani daki-daki a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Amfani, 2004. Ya gabatar da mukala mai suna “waiwaye adon tafiya”. A nan ya yi bayanin wasu ƙwayoyin ma’anar tare da kawo rabe-rabensu a fannin nahawun Hausa, bisa tsarin nazari. Wannan nazarin zai tsaya ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Rabi’u, da wasu, 1988. Sun gudanar da wani aiki a kan nahawun Hausa, cikin wanin littafi da suka buga mai sunan “sabuwar hanyar nazarin Hausa: Ɗon kananan makarantun sakadare”. A nan ma sun yi bayani kan azuzuwan kalmomin da tsarin jumlar Hausa, ba tare da an gudanar da bayani kan zamantakewan azuzuwan kalmomi a cikin jumlar ba. Amma wannan aikin zai yi tsokaci ne daki-daki a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Sani, 1981. ya rubuta littafi mai suna “Nahawun Hausa”. A ciki ya bayyana ƙwayoyin ma’ana ta fuskar ajin sifa da adadi a jinsi. Shi ma ya yi aikin nasa ne ta la’akarin da matsayinsu a daidaitaciyyar Hausa. Wannan nazarin ya tsaya ne a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Safiyanu, B. K. 2013. Ya gudanar da aikinsa na kundinn digiri na biyu a sashenn harsunan Afirika da al’adu Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, kan “Kwatancin Wasun Bayanau (Rukunan Nahawu Dangin

Suna) A Hausa Da Fulfulde” binciken a nan ya tsaya, kuma bai cikaro da wannan nazarin ba, na hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Bagari, D.M. 1987. A cikin littafin sa mai suna “Hausa Subordinate, Adverbial Clauses, Syntax and Semantics” ya kawo mahimman sassan nazarin jumlar Hausa, irinsu; aikatau (Adverb) lokaci (Tense Aspect) yankin Suna wato (Noun Phrase). Ya yi bayani gamsasshe game da wasu sassan jumlar Hausa. Wannan binciken ya tsaya ne a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Jinju, 1988. A cikin littafin sa mai suna “Rayayen Nahawun Hausa”. Ya yi Magana a kan azuzuwan kalmomi nahawun Hausa tare da nau’o’in jumlar harshen Hausa. Amma bai fito da hanyoyin nazarin jumla ba, wannan nazarin zai yi bayanin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa ta yadda mai nazari zai fahimce su daki-daki, domin kwalliya ta bi ya kudin sabulu.

Hassan, 1999. Ya yi magana ne kan suna a cikin littafinsa mai suna “Hausa Language”. Wanda aikin nasa ya danaganci tsarin yakin suna a cikin jumlolin Hausa. An buga aikin da ingantattun bayanai. Wannan aikin zai tsaya ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Sani, M.A..Z. 1999. Ya kawo a cikin littafinsa mai suna “Tsarin sauti da na nahawun Hausa”. Inda ya kawo kasha-kashen azuzuwan kalmomi tare da bayani kan suna. Binciken zai tsaya ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

‘Yar’aduwa, T.M da wasu. 2007. Sun wallafa littafi mai suna “harshe da adabin Hausa a kammale don Manyan makarantun sakandare”. A cikin littafin ya kawo suna da sifa da bayanau da nasaba da adadi da jinsi. Ya bayana yadda suke daki-daki tare da misalansu a cikin jumla. Wannan nazarin ya tsaya ne a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Ibrahim, da Wasu, 1989. Ya bayyana wasu kalmomin da jumloli da sassan jumloli da karin sauti da kuma irinsu, Suna da wakilin suna da aikatau da sifa da mahadi da kuma harafi a cikin littafin sa mai taken “Darussan Hausa na ɗaya”. Waɗannan duk bayanan da suka gabata cikin wannan nazarin, mai ɗauke da hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa zai tsaya.

1.2 HUJJAR  CI GABA DA BINCIKE


Bisa la’akari da zuzzzurfan nazari da bincike da ka yi a kan bitar ayyukan da suka gabata a kaso na 1.1 ba a samin wanda ya yi nazari a kan  hanyoyin nazarin jumla a nahawun harshen Hausa ba, sai dai wasu sun taba ne kan wasu rassa kuma zai ba da guɗunmmawa wajen nazarin jumlolin a harshen Hausa kuma ya zame masu hasken da zai haska masu hanyar samin yadda a ke nazarin jumla ne ko gefe wannan shi ne ya ba da damar ci gaba da yin aikin ko bincike da a ke yin a hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Binciken bai ci karo da wani aiki ba da ya gabata wannan shi ya sa a ka ci gaba da wannan binciken don a samin abin dubawa ga ɗalibai ‘yan’uwan masu neman ilimi.

1.3 MUHIMMANCIN BINCIKE


Bincike kowane iri ne ya na da muhimmanci ga rayuwar al’umma, da yake zai iya ilmantarwa a kan wani abu da ba a sani ba, ko ya fito da muhimmancin wani abu don mutane su yi koyi da shi amfana, ko kuma ya fito da illar wani abu don mutane su gaju masa. Saboda haka shi ma wannan bincike ya na da nasa muhimmancin. Wannan binciken ya shafi hanyoyin nazarin jumla  a nahawun Hausa. Saboda haka zai zama a matsayin cike gurbi a kan abin da aka bari a baya wajen bayyana jerin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Wannan nazarin yana da mahimmanci domin zai taimakawa ɗalibai ta fuskar samun damar sanin irin yadda ake gudunarar da nazari jumlolin harshen Hausa ta yadda zai zamo abin sauƙin karatu kuma ya taimaka wa manazarta.

Kammala wannan bincike zai fito da  tsarin hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, fili ta yadda mahimancinsa zai bayyana don samun saukin fahinta. Kundin zai taimaka wa sauran ɗalibai su ma, su mayar da hankali wurin bincike fannin Nahawun Hausa domin su samar da abin karantawa musamman irin hanyoyin nazarin ilmin ma’ana a nahawun Hausa, da ya taimka wa wajen bayar da ingantacciyar ma’ana a cikin jumlolin harshen Hausa.


1.4 FARFAJIYAR BINCIKE


Wannan binciken ya shafi nahawun harshen Hausa ne. Nahawun Hausa ya karkasu zuwa gida biyar,  kamar yadda masana fannin suka  nuna. Watau akwai abin da ya shafi ilimin gundarin sauti (Phonetics) da ilimin tsarin furuci (Phonology) da ilimin ginin kalma (morphology) da ilimin ginin jumla (syntax) da kuma ilimin ma’ana (semantics). wannan bincinken  an gudanar da shi a fannin ilimin ginin jumla, inda aka yi tsokaci kan ɗaya daga cikin fannonin nahawun  wato fannin ilimin gargajiya inda aka zaɓI ɓangaren nazarin jumla. A nan ne aka keɓe Hanyoyin da aka bi wajen nazarin jumla, don ya zauna wajen da za a gudanar da nazarin.

1.5 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE


Wananan bincike za a yi akan da wasu mahimman hanyoyi wajen gudanar da shi Hanya ta farko ita ce duba ayyukan da masana suka yi ta fuskar rubutu da wallafa mujallu da littafai da kuma kundaye da maƙalu a fagen ilimi. Hanya ta biyu ita ce binciken cibiyoyin nazarin harsunan Nijeriya da daƙunan karatu da shi ga yanar gizo, (internet), domin fito da ayyukan da za su taimaka wajen kammalar  wannan nazarin.

Wata hanya kuma ita ce neman shawarwarin daga manyan malaman nahawun harshen Hausa, musamman waɗanda suka ƙware a fagen ilimin ginin jumlar Hausa, da nahawun Hausa gaba ɗaya. Hanya ta ƙarshe ita ce, ziyartar  ɗaƙunan karatu na manyan makarantu da jami’o’i domin samun nasarar kammaluwar nazarin.

1.6 Naɗewa


A ƙarshe wannan babi, babi ne dake ɗauke da shimfiɗa a farkonsa, sai kuma aka yi bayani a kan abubuwan da suka shafi wannan nazarin, kamar littfi hujjar ci gaba da bincike da mahimmancin bincike tare da matakan da aka bi domin  gudanar da binciken. Har-wa-yau an yi bitar ayyukkan da suka gabata, a fagen ilimin nahawun harshe Hausa, domin samun ƙarin bayani game da aikin. Farfajiya bincike da hanyoyin gudanar da bincike tare da duba iyakar binciken su, suka biyo bayan ƙunshiyar babin. Daga ƙarshe sai aka rufe babin da jawabin kammalawa, watau naɗewa a taƙaice.


BABI NA BIYU

AZUZUWAN KALMOMI  A TASKAR MASANA NAHAWU


2.0 Shimfiɗa


A ƙalla akwai fannoni guda biyar manya da ake nazari game da nahawun  harshe (grammar). Waɗanda suka ƙunshi; Nazarin gundarin sauti (Phonetics) da  nazari akan fannin tsarin ilimin furuci (Phonology) da nazarin ginin kalma (Morphology) da nazarin ginin jumla (Syntax), sai kuma nazarin fannin ilimin ma’ana (Semantics). A fahimta ta zamani (Radford, 1981), nazari a kan nahawun kowane harshe ba ya kammaluwa sai ya ƙunshi nazarin tsararre a kan waɗannan fannoni.

An daɗe ana gudanar da bincike da nazarce-nazarce kan nahawun Hausa, amma duk da haka a kullum ba a rasa samun waɗansu matsaloli na fahimta waɗanda kan tilasta yin sabon nazarin mai kyau bisa tsari na zamani. A wannan bincike an nazarci hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, wanda ya ƙunshi, sanin azuzuwan kalmomi, da fasalin su. Sannan a nuna yadda suke kasancewa a cikin jumla, da guraben da ya kamata kowanne ajin kalma ya zauna a cikin jumla.  Za a bayyana yadda dokokin ginin jumla suke tare da gabatar da fasalin nazarin jumla, sannan a kawo yadda tsarin bishiyar li’irabin nahawu take a harshen Hausa.

Ilimin ginin jumla fannin ne da ake bin dokokin nahawun harshe domin amfani da azuzuwan kalmomi (word classes ) a matsayin tubalan da za a yi amfani da su a jeranta su domin a gina zance bisa ƙa’idar nahawu. A wannan fannin ne ake bayanin yadda ake sarrafa kalmomi a haɗa su da juna don su samar da jumla gamsasshiya.

2.1 WAIWAYEN AZUZUWAN KALMOMIN NA HARSHEN HAUSA CIKIN TASKAR MASANA


Azuzuwan kalmomi su ne mahimman tubalan da ake harhaɗawa Don gudanar da ginin jumla. Kusan kowanne ajin kalma ya na da nasa muhalli a fagen tsarin nazarin jumla. Wato abin nufi a nan shi ne, kowanne ajin kalma ya na cin gashin kansa ne a fannin nazarin ginin jumla.

Bisa la’aƙari da lokaci mai yawa da ake yin nazarin kashi-kashi, azuzuwan kalmomi na harshen Hausa ana kuma ba kowa ne kashi nasa suna. Akwai ajin sunaye (Nouns) da ajin aikatau (verbs) da ajin sifa (adjectives) da ajin bayyanau (adverbs), da makamantan su.

Masana da dama sun ba da tasu  gudunmawa wajen fito da yadda azuzuwan kalmomin suke, abin lura a nan shi ne masana suna da tsari na musamman da suke bi na ba da sunaye ga azuzuwan kalmomi. An yi wani zamani a farko inda aka rika tilastawa harsuna su bi tsarin rabe-raben kalmomi na wani harshe a da an yi lokacin da harshen latin, (greek), ya gawurta shi ne ma’aunin ga sauran harsunan turai wajen raba kalmomin su. Abin nufi shi ne duk ajin kalma da latin ke da shi, to tilas ne a ce harshen Ingilishi da Faransanci da Jamusanci suna da wannan aji. Ko ba shi, sai an ƙirƙiro shi!

Rabe-raben kalmomin wani tsari ne da masana ilimin kimiyyar harshe na zamani (Moden Linguistics) suka samar da dama ƙwarai, dammar kuma ta karfafa gudanar da bincike mai cin gashinkai na kowane harshe. Masana sun lura cewa ta hanyar bincikar kowane harshe shi kaɗai, za a gano arzikin harshen dangane da ire-iren kalmominsa da kuma keɓaɓɓen tsarinsa na nahawu. Masana irin su Chomsky, sun bayar da guɗunmawa sosai wajen sake fahimtar yanayin tsarin harshe da kuma kawo hanya mafi dacewa ta aiwatar da nazarin nahawun harshe. Alal misali; Chomsky ya na nuna cewa akwai wani tsari na bai-ɗaya da yake ɓoye a halin yanzu na tsarin nahawun harshen duniya baki ɗayansu (Universal Grammar). Ya nuna cewa wata rana za a cimmma wannan tsari na bai ɗaya. Ya ce, ta hanya mafi dacewa ta kaiwa ga wannan tsari, ita ce ta yin nazarin zuzzurfa a keɓance na tsarin nahawun kowane harshe, sannan daga baya a tace abubuwan masu kama da juna, ya ce su ne gama-gari (Universal), waɗanda suka kasa shiga cikin wannan rukuni na ‘yan gama-gari, to sai a ajiye su a mala, har sai ilimi ya ƙaru, wanda zai ba da dama a sa su a wannan ajin na ‘yan gama-gari.

Bisa la’aƙari da ajin kalmomi (Lexical Categories). Chomsky (1986:p2) ya bayyana cewa ana iya raba dukkan kalmomin harshe gida huɗu bisa wata daraja mai baki biyu, wato kasancewa (+) ko rashin kasancewa (-). Ga yadda ya yi rabon.

1.     suna (S) = +S, - A
2.     Aikatau (A) = +A, - S

iii. Sifa (SF)       = +S, + A
1.     Harafi (H) = S, - A


abin nufi a nan  shi ne suna, suna ne (+S) ba shi da alaƙa da aikatau (-A).  Aikatau, aikatau ne (+A) kuma ba da alaƙa da suna (-S), sifa ta shafi suna (+S) ta kuma shafi aikatau (+A), harafi bai shafi suna ba (-S), haka kuma bai shafi aikatau ba (-A).

Bayan haka Amfani, 1996. A cikin maƙarlar da ya gabata a Sashen Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, ya bayyana rabe-raben kalmomin Hausa, bayan haka ya bayyana ra’ayoyin rukunin mutanen farko da suka yi aikin raba kalmomin.    Abney (1987:P62) ya ƙalubalanci rabon da Chomsky, inda ya ce lalle akwai wasu kalmomin harshe waɗanda ba su samu shiga ba, waɗanda kuma tilas ne a sa su cikin rabon. Shawarar ta abney (1983) ita ce abu mafi ƙyau shi ne a ce kalmomin harshe sun kasu kasha biyu: masu yin aikin irin na nahawu a cikin jumla da waɗanda kalmomi ne kawai waɗanda an san gurabun da suke cikewa a cikin jumla. Don haka kalmomi irin su ƙwayar ma’ana mai nuna mallaƙa (possessive) ko nasaba (genetive) ko lokaci (tense) ko taƙi (aspect) da makamantansu, kalmomi ne masu yin aiki na nahawu (functional categories) a cikin jumla. Kalmomin irin su suna (noun) da aikatau (verb) da sifa (adjective) kalmomi masu gurabe na ɗindindin (non functional categories) a cikin jumla. A nan wannan nazarin zai ɗauki kowane aji na kalmomin Nahawun  harshen Hausa ya yi cikakken bayani a kansa kamar haka:


 Suna da Rabe - rabensa

Suna kalma ce  ta nahawu wadda ke bayanin lafazin da ake amfani da shi wajen ambatawa kowane abu na rayuwa, mai rai ne, ko maras rai, yana motsi ko ba ya motsi, mutum ne ko dabba ko wani abu wanda ke kasantuwa a tsarin rayuwar yau da kullum. Duk a na ambata masa wannan kalma ta suna. Kusan ba wani abu da ɗan’Adam ya bar shi ba tare da ya ambata masa kalmar suna ba. Misali:

Mutane               Wurare      Dabbobi        Ƙwari                         Sauran abubuwa

Shehu                Makaranta     Doki           Gwano                            Itace

Musa                  Zariya           Akuya         Gara                               Kogi

Citumu                Katsina         Raƙumi       Cinnaka                        Ciyawa

Ɗanladi                Masallaci      Giwa          Tururuwa                       Ƙarya

Rabi                      Kasuwa         Zomo        Kiyashi                          Yashi

2.1.1.1 RABE – RABEN SUNA


Suna ya kasu zuwa rukunoni daban – daban na nazari, gwargwado yadda tsarin da suna ya ƙunsa.

1- Sunan yanka.   2- Suna gama – gari    3- Suna gagara - ƙirga.

4- Suna tattarau.   5- Suna harɗadƊ’e         6- Suna ɗan’aikatau.

Waɗannan su ne rabe - raben ajin suna, bisa la’akari da rukunin da kowanne suna ya fito. Yanzu za a ɗauke su ɗaya bayan ɗaya a yi bayanin su domin samun haske a game da su.

 2.1.1.1.1 Sunan Yanka

Sunan yanka suna ne da al’umma suka amince da shi don su riƙa ambaton sunayen abubuwa da shi ciki har da sunayen mutane da sauran halittu. Ana amfani da sunan yanka ne wajen bambance ɗaiɗaikun halittu da abubuwa da shi ta fuskar jinsi da adadi. Sunan yanka yana iya kasancewa sunan mutane ko dabbobi ko tsuntsaye ko tsirrai ko duwatsu ko muhalli da makamantan su. Misali: Musa, Tururuwa, Zaki, Akuya, Makaranta, Nijeriya d.s.





2.1.1.1.2 Suna Gama - Gari

Wannan  nau’in na suna ana amfani da shi, wajen ambaton abubuwa na tarayya. Wato ana kiran wasu sunaye da suka cancanci a haɗe su wuri guda don su samar da sunayen rukuni na tarayya wajen ambato, ba tare da an bambanta sunayen abubuwan ba zuwa ɗaiɗaikun suna. A taƙaice suna ne da al’umma suka zaɓa wajen ambata wa wasu rukunonin halittu da suka cancanci ambato a cikin adadi na tilo. Misali: Mutum, Dabba, Tsuntsu, Ƙwaro, Littafi d.s.

A nan ba sai an ware wani daga cikin rukunin ba, an ambaci wani laƙabi da ya shafe shi, shi kaɗai ba. Wato dai ana iya kiran sa da cewa suna ne na bai-ɗaya.



2.1.1.1..3 Suna Gagara – Ƙirga

Wannan nau’in na suna, suna ne na abin da ba a iya ƙirga shi da ɗai- ɗai da ɗai-ɗai. Ire-iren waɗannan abubuwan sun haɗa da: Madara, Nono, Yashi, Ƙasa, Gishiri, Gari.  d.s.

Abin lura a nan shi ne, kowane ɗaya daga cikin misalan da aka bayar, ba wanda zai iya ɗaukar kowane kaso ya ce zai iya ƙirga shi ɗaya bayan ɗaya don gane yawan adadinsa. Don haka ake kiran kason da suna gagara - ƙirga.



2.1.1.1.4 Suna Tattarau

Shi kuma wannan kashin na sunatattarau, yana ƙunshe da sunayen abubuwa ne waɗanda galibi ana samun su ne a cikin rukuni ɗaya. Kuma sunan kan zo a adadi mai alaƙa da jam’i. Abin nufi sunan yakan tattaro sunayen abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da jinsin tamata da na namiji a matsayin suna guda. Kuma ya haɗa da sunayen abubuwa da na halittu, kamar irin su: Garke , Ayari, Runduna, Bataliya, Gungu  d.s.

Waɗannan sunayen ana iya samun kowane jinsi a cikin kowane suna na tattarau.



  2.1.1.1.5 HarɗadƊ’en Suna

Shi kuma wannan nau’in na harɗadƊ’en suna ana haɗa kalmomi biyu ko fiye ne, masu zaman kansu ta hanyar liƙa su da karan-ɗori ko ƙwayoyin ma’ana ta –n ko –r don su ba da sunan wuri ko wani abun amfanin yau da kullum.Misali: Bayangida, Gidanwaya, Gidanrediyo, Bakinkogi, Tuma-ƙasa, Malam-buɗe-littafi, Cika-ciki, Ƙato-da-lage, Ciki-da-alako, Rub-da-ciki, Kau-da-bara

Da makamantarsu.



 2.1.1.1.6 Suna Ɗan’aikatau

Shi kuma wannan nau’in na suna ɗan’aikatau ya sha bamban da sauran nau’o’in sunayen da aka ambata a baya. Domin suna ɗan’aikatau ya fito ne daga kalmomin aikatau. Wato suna ne mai ɗauke da kalmar aikatau wadda aka yi wa ɗafi  ta koma suna. Misali:

Kalmar Aikatau Cikakka   Ɗafi da Kalmar Aikatau  Kalmar Suna Ɗan’aikatau

Tafiya                                      ma- + tafiya                              Matafiya

Noma                                       ma- + noma                              Manoma

Su                                            ma-  + su + -nta                        Masunta

Wannan shi ne yanayin ajin suna da rabe-rabensa a nahawun harshen Hausa.



 2.1.2 Wakilin Suna

Wakilin Suna yana ɗaya daga cikin ginshiƙan rukunnan nahawun Hausa. Wakilin suna wata kalma ce da ake amfani da ita wajen tsarin ginin jumla a nahawun harshe don ta wakilci kalmar suna a muhallin da kalmar suna ya kamata ta fito, amma saboda wani sharaɗin nahawu ya zama kalmar sunan ba ta fito a wannan muhallin ba. Ma’ana, amfani ake yi da ajin kalmomin wakilin suna a madadin kalmar suna a fagen nazarin jumla. Misali:

1-shi maimakon Audu

2-Ita maimakon Binta

3-Su maimakon Ɗalibai

Misalin wakilin suna a cikin jumla shi ne;

4-Musa ya a mare ta

5-Shi ne ya kama akuya.

Wakilin suna shi ma ya rarrabu zuwa rukunonin nazari kamar haka:

i- Wakilin suna katsattse.

ii- Wakilin suna  nunau.

iii- Wakilin suna tambayau.

iv- Wakilin suna madubi.



  2.1.2.1 Wakilin Suna Katsattse

Wannan nau’in na wakilin suna katsattse, ya na iya cin gashin kansa a ƙa’idar rubutun nahawun harshen Hausa. Abin nufi a nan shi ne ya na iya zama shi kaɗai a matsayin kalma mai cikakken aiki, ba tare da ya haɗu da wata  kalma ta nahawu ba wajen wakiltar suna a cikin jumla. Kuma ana amfani da shi wajen fayyace sunan mutum na ɗaya da na biyu da na uku. Haka kuma ana iya nuna adadin sunan da yake wakilta, wato a san sunan tilo ne ko jam’i. A na iya sanin jinsin da sunan ya fito, wato sunan namiji ne ko tamata. Misali:

Mutum na ɗaya (Mai Magana) Tilo                  Jam’i

      Namiji:                        Ni                    

Tamata:                       Ni                    

      ---------------                  -----                  Mu

Mutum na biyu (Abokin Magana)     Tilo                  Jam’i



      Namiji                                 Kai                                  

      Tamata                                Ke                   

      ------                                   --------                       Ku              

Mutum na uku (wanda ake magana a kansa/Sha Magana)       Tilo                          Jam’i

      Namiji                                                         Shi                                  

      Tamata                                                        Ita                   

      ---------                                                        -----                  Su

  2.1.2.2 Wakilin Suna Nunau

Shi wannan nau’in na wakilin suna, yana wakiltar suna ne ta hanyar nuni zuwa ga sunan da yake wakilta. Ana amfani da shi ne wajen nuna wani abu da shi, abin na kusa ne ko na nesa. Kalmomin wakilin suna nunau iri biyu ne; akwai dogo sannan akwai gajere.

2.1.2.2.1 Wakilin Suna Nunau Dogo

Wakilin suna nunau dogo ya na iya zama da kansa wajen wakilci. Sannan kuma yana zuwa a cikin jumla don ya wakilci suna. Kuma yana fayyace jinsi da adadi na sunan da ya wakilta. Sannan yana nuni kan wani abu da yake a kusa ko na nesa. Misali:

Kusa                                 Nesa                     Jinsi

wannan                             wancan                 Namiji

wancan                             waccan                             Tamacce

waɗannan                        waɗancan            Jam’i

2.1.2.2.2 Wakilin Suna Nunau Gajere

Wannan nau’in na gajeren wakilin suna nunau, gajeren zubi gare shi in aka kwatanta shi da dogon wakilin suna nunau. Haka kuma ba ya iya zaman kansa har sai an jingina shi da wata kalma. Dole sai ya sami abin da zai jingina da shi kafin wakilcin nasa ya inganta. Ana amfani da ƙwayoyin ma’ana na –n da –r tare da kalmomin wakilin suna nunau. Misali:

Kusa                                 Nesa

-n  nan (gidan nan)   -n  can (gidacan)

-r  nan (rigar  nan              -r  can (rigar  can)

-n nan (yaranan)    -n can (yaracan)



   2.1.2.3 Wakilin Suna Tambayau  

Wannan nau’in kuma kamar yadda sunan ke nuni, ya jiɓanci yanayin tambaya ce. Duk lokacin da aka yi amfani da shi, to tabbata tambaya ce ake yi. Haka kuma shi wannan wakilin suna tambayau iri biyu ne: Akwai na gaba ɗaya (wanda ya haɗa da mutum da abubuwa) da kuma na fayyatacce abu (wanda yake rarrabe mace da namiji). Misali:

Gaba Ɗaya

Wa? Mutum                      Su wa?

Me? Abu                           Su me da me?

Fayyatacce

       TILO                      JAM’I

Wanene?                 Su wanene?

 WAKILIN SUNA MADUBI

Wakilin suna ‘madubi’, shi kuma inuwa ce ta ‘suna’ ko wakilin suna katsattse. Shi ba ya zaman kansa. Duk inda aka faxe shi, to tabbata an riga an ambaci sunan nan ko wakilin suna katsattse da ya zo a farkon jumla. Misali:

Mai Magana          Tilo                Jam’i

      Namiji           kaina              

      Tamata          kaina              

      -------            ------               kanmu      

Abokin Magana     Tilo                Jam’i

      Namiji           kanka             

      Tamata          kanki              

      ---------          --------             kanku       

Sha Magana          Tilo                Jam’i

      Namiji           kansa             

      Tamata          kanta              

      ---------          ---------            kansu

Kowane misali aka ɗauka a nan, ba zai iya zaman kansa ba. Misali:

Ni kaina

Audu kansa

Shi kansa

Binta kanta

Ita kanta

2.1.3 Ajin  Sifa.

Sifa kalma ce ta nahawu wadda takan zo gabanin suna ko bayansa a harshen Hausa, don ta fayyace suna ta fuskar launi ko tsarin jiki da ya shafi girma ko ƙanƙanta da makamantan su. Tana bayyana jinsi da adadin suna a tsarin Nahawun Hausa Misali:
  • Binta ta sayi farar
  • Jaka faraa Binta taa sayaa.
  • Farin gida ya ƙone.
  • Gida farii ya ƙone.

A wannan misalin na (a) da yake a sama an nuna cewa, sifa takan zauna kafin kalmar suna (Sn.), tare da harafin –n ko –r  a liƙe da ita don ta nuna cewa ta zo kafin suna. Haka abin yake a misalin na (c). A gurbin misali na biyu (b) da yake a sama kuwa, sifar tana bayan suna ne, kuma babu harafi a tare da ita, watau a ƙarshenta. Maimakon haka sai wasalinta na ƙarshe ya zama dogo don ya nuna cewa ajin sifar ya biyo bayan ajin suna ne. Haka kuma abin yake a misali na (d) ƙwayoyin ma’ana na –n da –r suke nuna jinsin da ajin sifar ya kasanta. Dole ne idan ƙwayar ma’ana ta –n ta zo tare da sifa ya kasance sunan namiji ne sifar ke fayyace wa, idan kuwa ƙwayar ma’ana ta –r ta zo tare da sifa to dole ne kalmar sunan da sifar ke fayyace wa ta zamana tamata. Misali:

1.     ƙaramin gidaa              gidaa ƙaramii
2.     b) ƙaramar goonaa          goonaa ƙarama
3.     c) kooren ganyee ganyee kooree
4.     d) kooriyar  ciyawaa          ciyaawaa kooriyaa
5.     e) doogon riimii riimii doogoo
6.     f) dooguwar giginyaa           giginyaa dooguwaa


Ajin sifa shi ma yana da nasa nau’o’in kamar haka:

1.     Sifa Sassauƙa
2.     Sifa Nanatau
3.     Sifa ‘Yar aikatau

2.1.3.1 Sifa Sassauƙa

Wannan nau’i na sifa an san shi da tsari ne a sauƙaƙe. Sifar ta ƙunshi saiwar kalma da ɗafa-ƙeya. Misali:

baƙi                baƙa       baƙaƙe

shuɗi              shuɗiya    shuɗaye

dogo                doguwa    dogaye  d.s

Idan an lura za a fahimci saiwar kowace kalma da ɗafa-ƙeyarta. A kalmar baƙ, tushen kalmar shi ne ɓaƙ’ da ɗafin wasalin ‘i’ ko na ‘a’ sunan namiji ko ‘a’, a sunan tamata ko ‘aƙe’ a jam’i. kalmar shuɗi, tushen kalmar shi ne ‘shuɗ’ da ɗafin wasalin ‘-i’, ko ‘a’ sunan namiji ko wasalin ‘-iya’, a sunan tamace ko wasalin ‘–aye’ a suna jam’i. Kalmar dogo mai tushen kalma Ɗog’ da ɗafin wasalin ‘-o’, a sunan namiji ko ɗafin wasalin ‘-uwa’, a sunan tamace ko ɗafin wasalin ‘–aye’, a suna jam’i.



2.1.3.2 Sifa Nanatau

Nau’in wannan sifa shi ne wanda ke da tsari irin na maimaicin kalmomi. Waɗanda ba su la’akari da jinsi, ko adadi balle jam’i.  Misali:

ƙungiya-ƙungiya                 tsibi-tsibi

kashi-kashi                              buhu – buhu

launi-launi                    ganga- ganga d.s

2.1.3.3 Sifa ‘Yar Aikatau

Ita kuma wannan sifar kalmar aikatau ke samar da ita. Wato kowace sifa ‘yar aikatau ta samo asali ne daga kalmar aikatau. Misali:

Kalmar Aikatau Ajin sifa (namiji)       Ajin sifa (tamacce)  Ajin sifa (Jam’i)

Wanke -wankakke   -wankakkiya         -wankakku

Gina – ginanne –ginanniya -ginannu

Rubuta  -rubatacce - rubutacciya-  rubutattu d.s



2.1.4 Aikatau

Aikatau shi ma ya na ɗaya daga cikin rukunan nahuwun harshen Hausa. Aikatau kalma ce da ke ƙunshe da aikin da ke aukuwa a cikin jumla. Misali:

Wanke, dafa, ji, ci, d.s

Aikatan harshen Hausa ya kasu kashi biyu kamar haka:-

Aikatau so-karɓau

Aikatau ƙi-karɓau

2.1.4.1 Aikatau So-Karɓau

Aikatau so-karɓau shi ne kalmar aikatau da suna karɓau ke biyo bayanta a cikin jumla. Aikatau so-karɓau kalmar aikatau ce da take buƙatar wani abu ya biyo bayanta a cikin jumla. Abin da take son ya biyo bayan nata shi ne kalmar suna ko kalmar wakilin suna da kan zo a ƙarshen jumla don karɓar aikin da suna aikau ya aikata a cikin jumla. Misalan kalmomin aikatau so-karɓau su ne: kaama, maari, yanka, ɗeeboo, da duk wata kalmar aikatau da suna ko wakilin suna zai iya biyo bayanta. Misalin su a cikin jumla:

Bala yaa kaamakaaza.

Kande taa maari Audu.

Rabi taa yanka naama.

Yara sun ɗeeboo ruwa


2.1.4.2 Aikatau Ƙi-Karɓau

Shi kuma wannan nau’in akasin aikatau so-karɓau ne. Aikatau ƙi-karɓau, shi ba ya buƙatar zuwan suna karɓau a bayansa.  Misalan kalmomin aikatau ƙi-karɓau su ne kamar haka: gudu, dahu, bugu da makamantan kalmomin aikatau waɗanda in aka faɗe su a cikin jumla basa buƙatar wata kalma ta biyo bayansu. Ga Misalin kalmomin a cikin jumla.

Audu yaa gudu.

Abincin yaa dahu.

Shinkafa taa bugu.

2.1.5 Bayanau

Bayanau kalma ce da ake amfani da ita cikin jumla don ta ƙara bayani kan kalmar aikatau. Saboda a san lokaci ko wuri ko yanayin da suna aikau ya aikata aikin a cikin jumla. Misali:

  • Baƙii sun iso ɗaazu
  • Matasaa Baƙii sun iso ɗaazu.
  • sunaa zaune a kan dakali.
  • Malam ya a shigo aji d gaggawaa.
  • Akuu yana magana a
  • Hakimii ya a ziyarci ɗalibai da safe.

Dangane da haka kuma a iya raba bayanau zuwa gida uku ta ɓangaren nazarinsa.

Bayanau na yanayi

Bayanau na wuri

Bayanau na lokaci

2.1.5.1 Bayanau Lokaci:-

Shi wannan kashi yana da nasa rassa guda uku (3) kamar haka:-

HaɗadƊ’en Bayanau

Nanatau/ruɓayyen Bayanau

ƙosasshen/tsanantau Bayanau

2.1.5.1.1HaɗadƊ’en Bayanau:-

Shi ne mai nuna lokaci na ranakun da aka gudanar da aiki a cikin jumla. Misalan kalmomin wannan nau’in na bayanau su ne: Shekaranjiya, Bana, Jibi, Bara, Yau, Ban da gobe, Baɗi, Gobe: da dai makamantan waɗannan kalmomi masu nuna lokacin ranaku da yake ƙarin bayani kan kalmomin aikatau. Misalin su a cikin jumla:

(a) Musa yaa kaama kifi jiya.

                          (b) Rabi taa dafa naama shekaranjiya.

2.1.5.1.2 Nanatau/ruɓanyayyen bayanau

Irin wannan nau’in na riɓanyayye ko bayanau na nanatau yana ɗauke ne da wasu kalmomi na bayanau da ake iya maimaita su don a samar da shi. Ire-iren waɗannan kalmomin su ne; Jiya-jiya, Yanzu-yanzu, ɗazu-ɗazu, Gobe-gobe, ƙasa-ƙasa. Misalin su a cikin jumla:

  • Lawal yaa tafi kasuwa ɗazu-ɗazu.
  • Shehu yaa maari Hauwa yanzu-yanzu.

2.1.5.1.3 Tsanantau / ƙosasshen bayanau

Shi kuma wannan kashi yana tabbatar da aukuwar aikin da aka aikata a cikin jumla. Misalin kalmominsa  su ne: ainun, sarai, ƙwarai, sosai, garau da sauran kalmomi masu aikin ƙarin bayani kan kalmar aikatau masu nuna tabbatuwar aiki a cikin jumla.

Misalin su a cikin jumla.

  • Hafsa taa sari ƙafarta sosai.
  • Abdulmalik yaa sami kuɗi ƙwarai.
  • Ibrahim yaa warke garau.

2.1.5.2  Bayanau Na Yanayi.

Bayanau na yanayi ana amfani da kalmominsa ne a cikin jumla don nuna yanayin da aiki ya gudana a cikin jumla. Ire-iren kalmomin da ake amfani da su waɗanda suke ƙarin bayani kan kalmomin aikatau don nuna yanayin da aiki ya gudana a cikin jumla sun haɗa da: da Sauri, a firgice, a fusace, da gaugawa. Misalin su a cikin jumla:
  • Musa yaa shigo aji da sauri.
  • Ayuba yaa tafi makaranta a firgice.
  • Jafar yaa zo a fusace.

2.1.5.3 Bayanau Na Wuri

Bayanau na wuri yana nuni ne da wurin da aikin cikin jumla ya faru. Ire-iren kalmomin da ake amfani da su, a irin wannan bayanau ɗin su ne; waje, ko’ina ƙasa, sama, a kan, ciki, kusa da sauran kalmomin da suke nuni da muhallin aukuwar aiki. Misalin su a cikin jumla:
  • Audu yaa faɗƙasa.
  • Adamu ya shiga cikin aji

2.2  TAƘAITACCEN TARIHIN SAMUWAR HANYAR  NAZARIN NAHAWUN HARSHE


Nazarin ilimin harsuna abu ne Wanda tun farkon bayyanarsa yake tafe da ra’ayoyin malamai da masana, Wanda kuma a cikin ra’ayoyin nan, kowane na ganin ga yadda ya kamata a bi a yi nazarin harshe. Da farko tun wajen ƙarni na biyar kafin bayyanar Annabi Isa (A.S), Wato (5th C.B.C.) ɓayan nan an sami ra’ayoyi da dama daga malamai manazarta harsuna. Daga cikin su akwai ra’ayoyi daga malamai masu nazarin harsunan Girkanci da Latinanci da makamantarsu. Malamai na wannan lokaci duk sun nazarci harshe ne a tafarkin  nahawun gargajiya Wanda shi nahawun gargajiya ya ta’alaka ne kan wasu dokoki ko ƙa’idoji inda suke da mabiya wannan ra’ayin na nahawun gargajiya, kuma suna umurta jama’a a kan yadda za su raba ajin kalma, kuma a harsunansu, kada ka fadi wani abu (prescriptive grammar). A bisa wannan hujjar mabiya wannan hanya kuma sun fi bai wa harshen rubutu (written language) duk wani mahimmanci maimakon harshen baka (spoken language).

Ganin wannan hanya ta nazarin harshe sai aka sake bin sawun wasu manazarta waɗanda suka fito suna sha’awa ga nazarin wasu harsuna waɗanda ba nasu ba. Hanyar da suka bi don wannan nazarin ita ce hanyar da ake kira ilimin nazarin kwatanci da bin salsalar harsuna (comparative and historical linguistics). Wannan hanya ta kara fito da Wata sabuwar hanyar nazarí harsuna fili don samun daukaka. A cikin wannan hanya an sami malamai da dama irinsu, Sir Willian Jone, da Rusmus Rask, da Franz Bopp, da Jacob Grimm, da makammantarsu. Waɗannan malaman sun taimaka sosai ga wannan fanni. Nazarin harshe ta kan wannan hanya ya faro tun wajen shekarar 1787 zuwa 1833. A wannan tsakanin, malamai sun wallafa littattafai da maƙaloli da dama dangane da wasu harsuna.  Ganin yadda mabiya ra’ayoyin nahawun gargajiya suka yi nazarin harshe, ta kai ma an sake samun bayyanuwar wata hanya ko wani ra’ayi Wanda ake kira “Nahawun ƙwanƙwancewa”, (structural grammar). Wannan ra’ayi, ‘structuralistic’  wato ‘yan ƙwanƙwancewa, a ganinsu ya kamata a nazarci harshe kansa ɗungurugum, a maimakon nazarin wasu ‘yan tsirarun harsuna (Jibril, 1985:p62). Ya kara da cewa sun karfafa tunaninsu ne a cikin ƙasidu da littattafai masu yawa da suka wallafa. Bayan haka sun danganta nazarin harshe da kimiyya,  ma’ana nazarin harshe ya shafi daidai da irin ci gaban da aka samu a halin yanzu. Waɗanda suka taimaka wa wannan fanni  akwai malamai irin su; De-saussue da Leonard Bloomfield da Franz Boaa da Edwan Sapir da Fries. O.G da Zelling S. Harris da dai makammantarsu bayan haka (Jibril, 1985:p62), ya bayyana cewa ƙwazo da bincike na waɗannan mutane ya kai ga samun nasarar komawa kan abin da ake furtawa a maimakon tsohuwar hanyar nan da aka fi rinjaya na a maida hankali a kan duk wani abu da aka rubuta mahimmanci. Wannan gagarumin canjin ya auku ne a farkon ƙarni na ashirin (ƙn 20th C).

Hr-ila-yau  a na cikn wannan halin sai wasu malamai suka fito da wani ra’ayinsu akan nazarin harshe can kwatsam! Sai wani Ba’amerike (Bature), mai suna Noam Chomsky. Chomsky ya fito da sabon ra’ayi game da nazarin harshe,  inda ya nuna bai kamata ba a riƙa nazarin harshe ta hanyar nahawun gargajiya ko nahawun ƙwanƙwancewa ba. Wanna bayani da Chomsky ya yi cikin fagen nazarin harsuna ya samu ɗaukaka fiye da sauran malamai manazarta harsuna na wannan lokacin. Hasali ma ta kai kowa ya fito ƙokri ya ke ya kwatanta kansa da Chomsky, ko kuma ya samo wani abin kushewa daga gares hi (Chomsky). Chomsky ya bayyana ne a shekarar 1950, kuma a 1957, ya wallafa wani littafi mai suna “styntactic structure”Wannan littafin ya kara fitowa da Chomsky fili a idon duniya musamman a wajen ɗalibai da malamai manazarta harsuna. A cikin wannan littafin ne aka samu wani sabon ra’ayi  da ya kira, “Nahawun bai-daya” (Universal Grammar).  Bayan haka bisa la’akari da irin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da nazarin harshe ya shiga a shekara 1950.  A wannan tsakanin sai da ta kai an sami kusan shekaru ashirin babu wani canji na ku-zo-a-gani  da aka samu dangane da nazarin harshe. Malaman da suka cancanci su kawo wani sabon abu cikin nazarin ilimin harsuna, sai kuma kowanne daga cikinsu ya kasance ya na da ra’ayinsa game da hanyar nazarin harshen, wanda kan haifar da jayayya a tsakanin jama’a.  ɓullowar  Chomsky ya sa an samu gagarumin canji wanda ake kira “juyin-juya-hali” a cikin hanyar nazarin ilimin harsuna. Bayan haka nahawun taciya ba wani ra’ayi ba ne da Chomsky ya ƙirƙiro don ya kushe hanyoyin da ake bi wajen nazarin nahawun ƙwanƙwancewa. Nahawun taciya hanya ce da Chomsky ya zo da ita don daidaita hanyar nazarin harshe da ya zai zama na bai ɗaya kuma daidai da zamani. Chomsky ya bayyana wasu hanyoyi da yake ganin za a samu gyara ga wasu ra’ayoyi na malamai waɗanda suka gabaci nasa, kuma waɗanda a ganinsa waɗannan hanyoyin masu rauni ne wasu daga cikinsu marasa makama ne.

Dalilan da suka ƙara ƙarfafa wa Chomsky  ƙwarin guiwa har ya fito da wanna ra’ayi, Wanda ya kira “Generative Grammar”  wato Nahawun taciya ana iya ganinsu  a cikin nazarce-nazarcen malamai na wannan ƙarnin da na wasu malaman da suka shuɗe. Daga cikin rubuce-rubucen da Zelling, S.  Harris  ya  yi, sun ƙarfafa wa Chomsky tunaninsa. Haka kuma ayyukan  Jacobson  a koda yaushe  yakan yi tunanin tsarin sauti na bai ɗaya, ko kuma na gama duniya (phonological universal). Ya  yarda cewa bambanci da ke akwai na tsarin furuci a cikin harsuna na duniya bambanci ne wanda malamai suka karkata a kan ra’ayinsu. Shi ma, De-saussue ya na cikin waɗanda suka ƙarfafa tunanin Chomsky. De–saussure kuma shi ma ya nuna cewa gina jumla ba ya cikin wani yanki na tsarin harshe kamar yadda ya bayyana inda yake cewa harhaɗa kalmomi zuwa jumloli  abu ne wanda  kowanne ɗan asali mai magana da harshe kan yi a lokaci na musamman, ba abu wanda harshe kan yi gaban ɗaya ba.” Saboda haka irin wannan rashin yarda da wasu abubuwa game da harshe da wasu malamai suka nuna, shi ya ƙara ƙarfafa tunanin Chomsky wanda ya kai shi ga fitowa da wannan ra’ayi nasa wanda ya yi wa suna da “Nahawun taciya”.


2.3 MATSAYIN AZUZUWAN KALMOMI A CIKIN JUMLAR  HAUSA


A nan an dubi jumlar Hausa ne, da nufin fito da ire – irenta, don sanin yadda fasalolinta suke a fagen nazari. A nahawun harshen Hausa a na da ire-iren jumla guda huɗu ta fuskar zamantakewar azuzuwan kalmomin cikinta, waɗanda masanan zamani suka tantance su a fagen nazari. Waɗannan jumlolin sun bambanta da rabon farko da a ka sani, wato waɗanda masana suka samar da su ta fuskar yanayin zubinsu. Wato kaso uku da masanan farko suka aiwatar, kason na masanan farko da suka gudanar ya na da ire-iren jumla guda uku waɗanda suka haɗa da: sassauƙar jumla da sarƙaƙƙiya da harɗadƊ’iya. Su kuma, masanan na ilimin ginin jumlar harshen Hausa na zamani sai suka sake duba wannan rabon suka fito da ire-iren jumloli har guda huɗu kamar haka:

(i) Sassauƙar Jumla.

(ii) Jumlar Tambaya.

(iii) Jumlar Umarni.

(iv) Jumlar Korewa.

Waɗannan jumlolin su masanan zamani suka tantance don sama wa ɗalibai da manazarta ilimin ginin jumla sauƙin nazarin jumla da sassanta.Yanzu za a ɗauki kowace jumla domin a nuna yadda tsarinta yake a fagen nazari.

Sassauƙar Jumlar Hausa

Sassauƙar jumla ta ƙunshi yankuna biyu manya. Bisa ra’ayin masanan farko, sassauƙar jumlar Hausa tana da  yankin suna (YSn) da yankin aiki (YA). Amma a ra’ayoyin masanan zamani an sami bambancin ra’ayi dangane da yankin aiki. Bisa fahimtar masanan zamani suna ganin cewa yankin da masanan farko suka kira yankin aiki, sunan bai dace da shi ba, saboda yankin ya na iya kasancewa ya ɗauki wasu zmahimman azuzuwan kalmomi na daban bayan ajin kalmar aikatau. Sanin haka sai suka kira shi da yankin  abin da aka faɗi a game da suna (YAfgSn) maimakon yankin aiki (YA). Wannan batu a na iya taƙaita shi kamar haka:

J                    Suna aikau    +  Abin da aka faɗi a game da suna

Wannan yanki na abin da aka faɗi a game da suna (YAfgSn) ya ƙunshi kalmar aikatau da kalmar karɓau (Aikatau + Karɓau) sannan ana iya samun wasu azuzuwan kalmomin su fito a yankin. Ana iya samun kalmar bayanau da sifa da harafi.

Babban abin da ake son sassauƙar jumla ta ƙunsa a matsayin ginshiƙan tubalan gina ta su ne, kalmar suna aikau ta zo a farkon jumlar, sai kalmar aikatau ta fito a tsakiyar jumlar sannan kalmar suna karɓau ta zo a ƙarshen jumlar. Wannan tsarin shi zai ba da fasalin nan na S.A.K a matsayin tsarin gudanar da sassan sassauƙar jumla. Irin wannan gundarin tsarin na S.A.K shi ne ake samu a harshen Ingilishi da wasu harsunan masu ɗimbin yawa. Wannan tsarin na S.A.K. shi ake kira da S.V.O a harshen Ingilishi.

Ga Misali:

Hausa                                                                             Ingilishi

(a)    Bala     ci   abinci.                                          (b)     John       eat     food.

SnAikau  Aik   Snkaɓ                                                  Subject noun   Verb   Object noun

1.     A.     K.                                                               S.         V.       O.


Jumlar Hausa tana buƙatar mafayyaciya (Maf) bayyananne, wanda zai fayyace suna aikau ta fuskar jinsi da adadi. Wannan ƙwayar ma’anar ita ce, “ya” a wannan misalin na (a).

Aikatau na jumlar “ci” ya na buƙatar a fayyace shi ta fuskar lokaci da taƙi (Lokt). Ƙwayar ma’ana da ke gudanar da wannan aikin ita  ce, “a”. Ƙwayar ma’ana  “a” ana kiranta da lokataƙ (Lokt) domin tana fayyace aikatau ne dangane da lokacin da aka aikata aiki a cikin jumla da kuma kammaluwar aiki ko rashin kammaluwar aikin.Shi ya sa jumlar ta koma kamar haka:

Sassauƙar Jumlar Hausa:

  • Bala      ya      a                  ci
SnAikau Maf.  Lokt       Aik      SnKarɓa

S                                 A           K



Ga hanyar nazarin li’irabi a zamanance. Jumlar Hausa tana ƙunshe da waɗannan azuzuwan kalmomin kamar haka:

J                                  YSn + YAfgSn

YAfgSn                         KN + YA

YA                                                 Aik, YSn

KN                                    Maf, Lokat

YSn                                   Sn

Sn                                        Bala

Maf                                    ya

Lokat                                            -a

Aikatau                                ci

Sn                                        abinci


J


YSn         YAfgSn

Sn         KN            YA



Maf   Lokat    Aik              Sn



Bala     ya        -a          ci           abinci



Sassauƙar jumlar Hausa tana ɗauke da ginshiƙai guda uku ne ƙwarara. Ginshiƙan su ne: Suna aikau (Snaik), da aikatau (Aik), sai suna karɓau (Kƙb).



Jumlar Korewa

Jumlar Hausa ta korewa tana ɗauke da wasu kalmomi na musamman da harshen ya tanada domin yin sharaɗi da su, kafin a gina ita wannan jumla ta amsu. Sannan da waɗannan kalmomin ne za a iya nuna irin korewar zance da aka samu a cikin jumlar. Kalmomin ana amfani da su ne wajen nuna korewar zance a cikin jumla ta hanyar bin wasu ƙa’idoji da aka gindiya na amfani da su don nuna yadda korewar ta auku. Shin korewar ta jumlar ce gaba ɗaya, ko korewar wani ɓangare ne na zance a cikin jumlar. Misalin sassan jumlar korewa shi ne:

Rabi baa ta tafi kasuwa ba.

Masana sun fito da tsarin kalmomin korewa da fasalin da ake amfani da su a cikin jumla, domin nuna irin korewar da aka samu. Ra’ayi ya bambanta a wajen bayani dangane da korewa. Masana irin su Kraft C. H. da Kirk – Greene (1973:37-40 da 61- 64) da Galadanci (1976:77- 83) da Skinner (1977:77 – 78), da Zaria (1981:82 - 84) da Bagari (1986), duk sun bayyana korewa kaɗai ba tare da sun nuna korewar yanki ce ko ta jumla baki-ɗaya ba. Yalwa (1995) da Newman (2000) da  Amfani (2006) da Muhammad (2010) da kuma Sani (2010)  da Umar (2012) duk sun yi bayani kan cewa ana samun korewa iri biyu, da ta yankin jumla da ta jumla gaba ɗaya. Masana sun yi tarayya dangane da tsarin kalmomin korewar. Ga yadda suke tare da misalan su :-



(i) Ba (bàà-----bá)     =   Bàà Ali ya sayaa bá.

(ii) Ba (bà-----bá)        =    Rabi bà ta tafi makaranta bá.

(iii) Ba (báá----)          =   Báá kuɗi a banki.

(iv) Ba (bâ….)            = agwagwa bâ ta tashi sama sosai.

(v) Ba (báábù----)      =   Báábù ruwa a randa.

(vi) Ba-i (bà-i… bà)    = bài dace a hana bara bá.

(vii) Káádà/Kâr------       = Káádà ka a tafi. Ko kâr ka a tafi.

Abin lura a nan shi ne, fasalin ginin jumlar korewa yana ƙunshe da wasu mahimman kalmomi da aka tanada don amfani da su wajen nuna korewa a jumlar Hausa.

Jumlar Tambaya

Jumlar tambaya ita ce jumlar da ake ginawa don a yi tambaya. A Hausa ana da jumlar tambaya  kamar haka:

(a) Yàushéé Rabi za ta tafi?

(b) Wàà Isaa ya a mààráá?

(c)  Mèè Musa ya káamaà?

Hausa tana da tsarin da take bi wajen ginin jumlar tambaya. Hanyar da Hausa take bi wajen ginin jumlar tambaya ita ce, dole ne “kalmar tambaya,” ta zo a farkon jumla. Haka kuma dole ne alamar tambaya ta zo a ƙarshen jumla. Amma ana iya samun wani tsarin da Hausa take amfani da shi a maganganun yau da kullum. Wasu daga cikin kalmomin tambaya da Hausa take amfani da su wajen ginin jumlar tambaya su ne;

(i) Iná?  = Ina Maryam ta a tafi?

(ii) Wàà?     = Wàà za a aika?

(iii) Yàushéé?  = Yàushéé za a dawo aiki?

(iv)  Ƙàƙáá?    =   Ƙàƙáá za a yi?

(v)  Yáyáá?  = Yáyáá Audu ya a faɗi jarabawa?

(vi)   Mèè?     =   Mèè Ali ya a saya?

Masanan da suka aminta da wannan tsarin sun haɗa da; Kraft C. H. da Kirk – Greene (1973) da Skinner (1977) da Zaria (1981) da Jinju (1986) da Bagari (1986) da Yalwa (1995) da Amfani (2005) Muhammad (2010) Umar (2012). Duk sun yi bayani game da wannan tsarin na jumlar tambaya.



Jumlar Umarni

Jumlar umarni tana ɗauke da wani tsari da ya bambanta ta da sauran jumloli da ake da su a Hausa. Jumlar umarni takan zo da kalma ɗaya rak, a matsayin jumla cikakkiya, mai ma’ana. Kuma kalmar da take zuwa da ita, ita ce kalmar aikatau (Aik).  Ga misalin jumlar umurni;

(a) Tashi!

(b) Rubuta!

Abin lura a nan shi ne jumlar umarni koyaushe takan ƙare da alamar motsin rai. Kamar  yadda aka nuna, jumlar umarni cikakkiyar jumla ce, sai dai kuma ta ƙunshi kalma ɗaya rak.

Masana irin su, Kraft da Kirk – Greene (1973) da Skinner (1977) da Zaria (1981) da Bagari (1986) da Jinju (1986) da Yalwa (1995) da Newman (2000) da Jaggar (2001) da Amfani (2006) da kuma Umar (2012) duk sun yarda da cewa wannan bayanin da aka gabatar shi ne tsarin samar da jumlar umarni a Hausa


2.4 NAƊEWA


A babi na biyu shimfiɗa ce ta zo a matsayin gabatarwa, bayan nan sai bincike ya yi waiwayen azuzuwan kalmomi na harshen Hausa. Inda ya bayyanansu tare da kawo su daki-daki, wanda daga bisani nahawun taciya ya biyo baya tare da ra’ayin masana ilimin taciya da nahawun harshen Hausa. Matsayin azuzuwan kalmomi a cikin jumla ta zo a gaba wanda a nan ne a ka yi bayanan gamsassahe game dajumlar Hausa. Wanda da ma nazarin shi ne hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.


BABI NAUKU

HANYOYIN NAZARIN JUMLA A TAKAICE


3.0 Shimfiɗa


Babi na uku ya na dauke da muhimman abubuwa waɗanda suka shafi jumla ta hanyar azuzuwan kalmomin Hausa.  Wanda da ma taken  binciken shi ne hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa, nazarin zai kawo kasha-kashen azuzuwan kalmomi da ra’ayin masana game da nahawun taciya har wa yau nazarin zai yi bayanin jumla ta hanyar yanki, Bayan nan sai nazarin jumla ta hanyar li’irabi inda za a kawo misalan bishiyoyin bisa ra’ayin masana sai nadewa ta biyo baya.


3.1 NAZARIN JUMLA TA HANYARAZUZUWAN KALMOMI


Bisa ga abin da Masana suka nuna cikin nazarin jumla ta hanyar azuzuwan kalmomi, wannan al’amari ya na da matukar mahimmanci ga mai nazarin harshe musamman harshen Hausa wajen gano azuzuwan kalmomi da kuma matsayi kowannensu a cikin jumla, domin masu nazari ko ɗalibai ma’abota neman ilimin nahawun harshen Hausa domin ya zamo musu  ido wajen neman ƙarin haske game da karatunsu, bayan haka a kawai wasu hanyoyi guda uku da Lamidi, (2000). A cikin wani littafi mai suna “Aspects of Chomskyan grammer”. Ya fito da wasu dokoki guda uku da ake amfani da su wajen nazarin jumla kamar haka:

i- Dokar Tsarin Yankin Suna (Phrase Structure Rules).

ii- Dokar Tsarin bar ɗai (Lebelled Brackets).

iii- Dokar Tsarin bishiyar li’irabi (Phrase Markers).

Duk waɗannan hanyoyin da masanin ya ambata a na amfani da su ne wajen nazarin jumla bisa ƙa’ida.

3.1.1 Dokar Tsarin Yankin Suna (Phrase structure).  Wata hanya ce ta lura da yadda tsarin yankin jumlar ko sasan jumla ke zuwa bisa ƙa’ida, da kuma lura da wasu abubuwa da suka ketowa cikin jumlar irinsu, S----NP, VP (verb phrase), wanda ya yi daidai da YSn, YAikt, BYnau, YHrf, YSf.

3.1.2 Dokar Tsarin bai ɗaya (Leblled Brackets), wannan wata hanya ce ta bin tsari na musamman domin fito da jumla a cikin tsari da ya da ce,  a duk lokocin da aka buɗe ta tom dole sai an rufeta. Masali: “Ɗysn Ado/yaa na noma da karamar  fartanya hrfɗ,” bayan haka yawancin jumlolim da ke zuwa da yankin suna da yankin bayanau (ybyn) da ko kuma yankin abin da aka yi Magana game da suna (YAkgsn).

3.1.3 Dokar Tsarin bishiyar li’irabi (Phrase markers) hanya ta uku da masanin ya bayyana da za a yi amfani da su wajen nazarin jumla watau bishiyar li’irabi. Li’irabi wata hanya ce ta yin amfani da zane bishiya li’irabi (diagram), wajen fito ma’anar jumla domin gane abubuwan da jumlar ta kunsa. Bayan haka wannan fannin yana bayyana yadda bishiyar li’irabin ya kamata ta zo bisa kan ƙa’ida.

     3.2 NAZARIN JUMLA TA HANYAR YANKI


Bisa la’akari da yankunan jumla da kuma aikinnsu a cikin jumla, ba karamin al’’amari ba ne domin kuwa, da taimakonsu ne jumla ke ginuwa saboda yankunan ne ke kara fitowa da ma’anar abinda jumla ta kunsa. Bayan haka Akwai yankuna da Masana suka bayyana a wajen nazarin yankuna Kaman haka;

Masana da dama sun bayar da guɗammuwa wajen fito da yanayin tsarin yankin  jumlar Hausa. A nan za a kawo guɗummawar masana don nuna irin yadda suka fito da tsarin yankin suna na jumlar Hausa. Ga yadda suka yi bayani game da yankin suna:

1.     Amfani (1996:p80) ya bayyana mafayyaciya a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo sauyi a yankin suna na jumlar Hausa. Kuma ya yi bayanin cewa manyan azuzuwan kalmomin mafayyaciya a bayyane suke. Amfani ya yi bayani kan ɗanyatau koma baya (PRM), wanda yake nuna jinsi (gender) da kuma adadi (number) a lokacin rakiyarsa.
A lura cewa ita wannan Kalmar ta ɗanyatau koma baya, (PRM), wadda kuma mafayyaciya ce tana zuwa ne kawai bayan suna. Ga yadda ya yi bayanin zuwan nasu:

wannan nazarin zai bayyana yadda tsarin yankin suna da sauran yakuna yake kasancewa a jumlar Hausa. Yankin suna yana ƙunshe da wasu muhimman kalmomi da ake kira ‘yan rakiya. ‘yan rakiyar  da kan zo tare da suna da dama, kaɗan daga cikinsu sun haɗa da: mafayyaciya da ajin sifa da ƙirgau da manuni da wasu da dama.

‘Yan rakiyar da kan zo tare da suna, a yankin suna na jumlar Hausa, don nuna yadda fasalin tsarin suna yake kasancewa a jumlar Hausa.

A ciki an nuna yanayin rakiyar kowane ɗan rakiya a lokacin da suke raka suna. Daya daga cikin abubuwan da aka maida hankali a kansu shi ne fasalin rakiyar mafayyaci da ajin sifa kan fito a bagire biyu a lokacin rakiyar da take yi wa suna. Abin da yake nuna fasalin rakiyar shi ne, manunin bagire. Nazarin ya fito da bayanin yadda manunin bagire kan kasance a lokutan rakiyar, idan ajin sifa ya zo kafin suna shi manunin bagire ya kasance na ƙwayoyin ma’anar su -n da -r. idan kuma ta zo ne bayan suna sai ƙwayoyin ma’anar su ɗauki sigar wasalin ƙarshe na ajin sifar da suka zo tare.


Yaaro                     n

N                         PRM 

Haka kuma mafayyaciya da adadi suna zuwa bayan suna kamar yadda misali na (ii) da (iii) za su nuna:

  Yaro                   n                 nan


N                          Agr             Jinsi

iii.   Mutane                    kaɗan


Suna                     Adadi

Wasu ayukkan da masana suka yi kan yankin suna na jumlar Hausa su ne na Tuller (1986) da Yusuf (1991). Nazarin Tuller ya bada muhimmiyar gudummawa wajen warware matsalar fahimta game da matsayin ƙwayar ma’anar manunin bagire da Galadanci (1976) ya kira tada mahaɗi (linker element).


Yankin Suna

A wannan ɓangare za a yi nazarin yankin suna  (YSn). Yankin suna (YSn) shi ma wani mahimmin yanki ne a cikin jumla. Kowace jumla tilas ne ta ƙunshi suna aikau wanda yake a ko da yaushe yakan zo ne a matsayin yankin suna a cikin jumla. Wani abin lura kuma shi ne, yankin suna yakan zo  a matsayin karɓau (Ƙb).  Ga misali:



(i) ƊYSnAikauAuduɗ  ya  a  sayi  ƊYSnƙbgidaɗ.

(ii) ƊYSnAikauAudu fariiɗ ya a sayi ƊYSnƙbƙaramin gidaɗ.

Ga yadda abin yake a bisa bishiyar li’irabi:



J
YSn                                YAfgSn

KN                       YA

Sn              maf        Lokt   Aik          YSn



Sn

Audu              ya           -a     sayi          gida

A wannan misalin yankin suna yana ɗauke da wasu kalmomi, wato ‘Audu’ da ‘gida’. Ana kiran inda suna ‘Audu’ ya fito da yankin suna aikau. sannan kuma yankin da sunan ‘gida’ ya fito shi ne yankin suna karɓau. Kalmar aikatau a  cikin jumlar ita ce ‘sayi’. Zuwan kalmar aikatau da kalmar suna karɓau a yanki ɗaya shi ya hana a kira yankin da yankin aiki ko yankin aikatau. Saboda kowanne ɗaya daga cikin su yana cin gashin kansa ne.

Masana irinsu, Kraft da Kirk–Greene (1973) da Galadanci (1976), da Skinner (1977) da Bagari (1986) da Jinju (1986) da Yusuf (1991) da Yalwa (1995) da Amfani (1996) da Sani (1999) da Newman (2000) da Jaggar (2001), duk sun yarda da wannan bayani da a ka yi game da tsarin yankin suna (YSn) da abin da ya kunsa.

Yankin Harafi

Yankin harafi (YHrf), yana tafiya tare da yankin suna (YSn) kafaɗa – da - kafaɗa (wani lokaci ma har ‘yan rakiya kan shigo cikin yankin). Wato yankin ya ƙunshi harafi (Hrf) da kuma yankin suna (YSn). Haka kuma ana samun zuwan yankin harafi (YHrf) ya zo tare da bayanau (YByn). Ga Misali:

YHrf     Hrf    +                   YSn + YByn

YH
Hrf                                            YSn

Sn

a                                                                  ƙasa

Ga misali: Yankin harafi a cikin jumla, domin fito da bayanin fili.



Adamu / ya       na         noma   Ɗ da babbar fartanyaɗYHrfɗ.



Hrf            Sf          Sn

YSn                        YAfgSn



Yankin harafi a cikin wannan jumla shi ne:

da / babbar fartanya.



Hrf             Ysn


Yankin Sifa

Yankin sifa (YSf) ya ƙunshi sifa ita kaɗai, ko tare da ɗanrakiya. Ga yadda abin yake kasancewa.



(a)     YSf                  (b)                              YS





Sf                                             YSf             YSn

Sn



Ga misalin yankin sifa a cikin jumla:-

(a)  Yakubu / ya a sayoo sabuwar mootaa.



YSn            YAfgSn

Yankin sifa a cikin wannan jumla shi ne;

sabuwa  r          mootaa.



Sf       Mb   Sn

Ga yadda yankin sifa yake a bishiyar li’irabi:



YSf



Sf                              YSn



Mb                                    Sn



Sàbùwá      r                      Mótà



Yankin Bayanau

Yankin bayanau (YByn), yanki ne da yake fitowa a cikin yankin aikatau na jumla. Yana yin ƙarin bayani ne ga aikatau, domin a fahimce shi da kyau. Kamar sauran sassan jumla, shi ma yankin bayanau (YByn), kalmar bayanau ke jagorantar yankin. Misali:

Musa  ya  a wuce ɗazu
ɓangaren bayanau a cikin wannan jumlar shi ne, Ɗɗazuɗ.


Yankin Aikatau

Yankin aikatau (YA) wani mahimmin yanki ne a jumlar Hausa. Aikatau (Aik) shi ne ginshiƙi a yankin aikatau (YA). A ƙalla akwai aikatau iri biyu a Hausa. Akwai aikatau so – karɓau (Aik. SK), da kuma aikatau ƙi – karɓau (Aik. Ƙk). Idan yankin aikatau ya ƙunshi aikatau so – karɓau (Aik. SK), to yankin kan ɗauki yankin suna (YSn), a matsayin karɓau (Sn Ƙb). Misali:

Ali /  ya   a  ƊYAƊAik.SKsayiɗƊ YSn Ɗ  gidaɗSnƙbɗ.

YSn     YAfgSn

A wannan jumlar yankin aikatau (YA), shi ne “sayi gida”. Yankin aikatau  ya ƙunshi aikatau so - karɓau “sayi” da yankin suna “gida”. Idan kuma jumla ta ƙunshi aikatau ƙi - karɓau ne, yankin aikatau zai kasance da aikatau ne kawai, ba tare da wani ɗanrakiya ba. Misali:

Ali  /   ya   a ƊYAƊ  tafiɗAikƘKɗ.

YSn     YAfgSn

A wannan jumlar yankin aikatau shi ne, “tafi”. A nan yankin aikatau ya ƙunshi kalmar aikatau “tafi” kaɗai. Tafi aikatau ne ƙi - karɓau. Don haka a jumlar ba suna karɓau.

YA


YA

AikSk                                                    YSn

AikƘk                                                                                                                Sn



tafi                                                        Sayi                                                         gida










3.3 NAZARIN JUMLA TA HANYAR BISHIYAR LI’IRABI


Nazarin jumla ta hanyar bishiyar li’irabi ta la’akari da abin da ke faruwa a li’irabin da kuma yadda ake fasalta bishiyar li’irabi tare da nuna kowane kalma da ke tattare a cikin jumla da irin yankunan da suka keto a cikin li’irabi, bayan haka anan kawo su  daga kowane bangare na azuzuwan kalmomin hausa da ake dasu da kuma misali daga kowane bangare xa ya zo a cikin azuzuwan kalmomin domin a ga yadda suke a cikin jumla da li’irabi.



YANKIN HARAFI:                  YHrf        Hrf + YSA + YByn

A sama

YHrf            Hrf +   Ysn

YSn                      Sn

Sn                         Sama

Hrf                         a

YHrf

Hrf         Ysn

a             sn

Sama

Da ƙaramar fartanya

YHrf            Hrf + Ysn

Ysn            Sf + Sn

Sf             ƙarama

Sn             fartanya

Hrf             da

YHrf

Hrf             Ysn

Sf     Dik      Sn

da     ƙarama    (r)   fartanya



YANKIN SIFA: Ysf                Sf +Ysn                          sabuwar huulaa

Ysn             Sn

Sn             hula

Sf           sabuwa

Ysf                                                                       Ysf

Sf                     Ysn                                                                        Sf        Ysn

Sabuwa  mb         sn                                                                                       sn

r    huulaa                                            Sabuwar    Huulaa





YANKIN BAYANAU: YByN          BYN

Kande ta a wuce xazu.

YByn              Byn

Byn             ɗazu





YByn



Byn

ɗazu

Ladidi ta na daka a hankali

YByn              Byn

Byn             a hankali

Ybyn

Byn

A hankali

Aisha ta a je makaranta jiya

YByn              Byn

Byn             jiya

YByn

Byn

Jiya

YANKIN AIKATAU  YA           AK + Ysn

Ya a sayi gida

Ya         aik + Ysn

Ysn           sn

Sn           gida

Aik            sayi



YA

Aik sƙ                  Ysn

sn

Sayi          gida



Buba ya a tafi

YA           AIK

AIK         tafi

Ya

AIK kq

Tafi

Yasir ya a wanke kaya

YA             Aik+Ysn

Ysn            SN

Sn             kaya

Aik             wanke

Ya

Aik       Ysn

Sn

Wanke      Kaya


YANKIN SUNA

Tanko ya a sayi gida                                                       J

Ysn              YAfgsn                                                               Ysn     Yafgsn

YAfgsn          KN+YA                                                              Sn         KN            YA

KN           mal+Lokt                                                                         maf   Lokt  Aik     Ysn2

Maf            ya                                                          Audu        ya      -a      Sayi             gida

Lokt            a

YA            Aik +Ysn

Aik             Sayi

Ysn2         Sn

Sn             gida

Ysn2           Sn

Sn             Audu

Audu ya a sayi babban gida

YSN             TAfgsn

YAfgsn             KN+YA

KN              maf + Lokt

Maf            ya

Lokt            a

Aik            Aik + Ysn2

Aik            sayi

Ysn2           Sf + Sn

Sf           babbba

Sn             gida

J

Ysn      YAfgsn

Sn          KN             YA

maf       Lokt   Aik     Ysn2

Sf      Sn

Audu   ya        -a       sayi    Babba     gida



Audu ya a nome wata ‘yar gona

Ysn              YAfgsn

YAfgsn-KN+YA
KN              maf + lokt

Maf            ya

Lokt             a

YA            Aik+YSn

AIK            Nome

YSn            KN +Sn

Kn             maf +isgl

Maf            wata

Tsgl            ’yar                               J

Sn            gona

Ysn              sn              Ysn                  YAfgs

Sn                    KN                   YA

maf          Lokt   Aik                    YSn

KN            sn

maf                   Tsgl

Audu   ya    -a    nome   wata         ‘yar        gona

Sn           Audu

Audu ya na wanke kaayaa

Ysn           YAfgsn

YAfgsn            KN + YA

KN              maf + lokt

Ysn            Sn

Sn             Audu


J

Ysn                  YAfgsn

sn              KN                               YA

maf                 Lokt  Aik                    Ysn

Ysf     Dkb       sn

Audu         ya                   -a       sayi          babba    (n)        gida

Wannan katangan ta a rushe

YSN             YAfgsn

YAfgsn              KN+YA

KN            maf+Lokt

Maf            ta

Lokt             a

Ya             Aik

Aik              rushe

Ysn             mafmn +Sn

Maf            wannan                           J

Sn             Katanga

Ysn                                             YAfgsn

Maf mn                        Sn           Dkb              Kn                      Ya

maf                   Lokt        Aik

Wannan               Katanga      -n      ta                             -a         rushe


3.4 Naɗewa


Wannan babin na uku, ya fara ne da shimfaɗa a mtsayin gabatarwa daga baya sai kuma nazarin jumla ta hanyar azuzuwan kalmomi ya biyu baya. Sai kuma nazarin jumla ta hanyar yanki  da kuma nazarin jumla ta hanyar bishiyar li’irabi suka zo a jere wanda daga nan naɗewa ta zo a matsayin marufin babin.


BABI NA HUƊU

TAƘAITAWA DA KAMMALAWA

4.1 Taƙaitawa


Wannan kudin ya ƙunshi babi huɗu, kuma kowane babi ya na da abubuwan da ya ƙunsa game da nazarin. A babin na farko an nuna yadda tsarin binciken ya gudana. A farkon babin an fara da shimfiɗa, sannan aka kawo bitar ayyuka, a ciki an yi bayyanin ayyukan da aka gudanar na wani sashen aikin nan, haka kuma sai aka kawo dalilin bincike, a ciki an bayyana dalilan da suka sa aka gudanar da binciken sai kuma hujjar ci gaba da bincike ya biyo baya, wannan binciken bai cin karo da wani aika ba, wanda dama shi wannan aikin ya shafi hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Bayan haka sai muhimmancin bincike, inda a nan ne a kawo amfanin wannan bincike ga masu nazari da matakan da aka bi wajen gudanar da bincike. Haka kuma an bayyana farfajiyar wannan bincike, wato faɗi inda binciken ya tsaya ta la’aƙari da yadda tsarin yaƙe inda binciken ya gudana a cikin nahawu a fanin ilimi ginin jumla. Nazarin ya tsaya a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Daga nan sai kuma hanyoyin gudanar da bincike da aka bi don samun haske wajen gudanar da wannan bincike. Inda aka bi hanyoyin gudanar da binciken da kuma makamantansu, hanya ta farko shine kundaye da kuma hanya ta biyu shine littafai sai kuma hanyar ƙarshe shine shawarwari masana ilimin nahawun Hausa musamman waɗanda suka san ilimin kimmiyar sashen ɗausa. Babi na biyu yana ɗauke ne da shimfiɗa wannan take amatsayin gabatarwa. A nan ne aka fito da azuzuwan kalmomi nahawun harshen Hausa. Inda a nan ne aka fito da nahawun taciya tare da nuna muhimmancinsa a harshe, an kuma bayyana matsayin azuzuwan kalmomi a cikin jumla daga nan kuma sai naɗewa ya biyo baya.

A babi na uku an gudanar da aiki ne akan hanyoyin nazarin jumla a taƙaice kuma aka kawo dabarun nazarin jumla ta  hanyar azuzuwan kalmomi daga nan sai nazarin jumla ta hanyar azuzuwan kalmomi daga nan sai nazarin jumla ta hanyar yanki a nan ne inda aka bayyana su daki-daki, daga nan kuma sai aka kuma nazarin jumla ta hnayar bishiyar li’irabi, inda kuma daga baya naɗewa ta zama murfin babin. Babi na hudu ya zo da taƙaitawa da kammalawa.

4.2 Kammalawa


A babi na ɗaya an nuna yadda tsarin binciken, ya gudana. Babin ya fara ne da shimfiɗa sannan aka kawo bitar ayyukan da suka gabaci wannan aikin waɗanda suke da nasaba da shi ko wasu sassa daga cikin aikin musamman ma na masana ilimin nahawun Hausa. Daga nan sai aka zo da dalilin bincike. An bayyana cewa a lokacin da ake koƙarin karance-karancen don samar wa binciken gurbin zama, ba a ci karo da wani aiki ba da aka yi irin wannan binciken ba. Bayan haka hujjar ci gaba da bincike ya biyo bayan dalili daga nan an kuma bayyana mahimmancin wannan binciken da cewa an aiwatar da shi ne domin a magance ire-iren matsalolin da ake cin karo dasu a wajen fahimtar nahawun Hausa. Aikin ya gudana ne ta hanyoyin tattaro bayyanai daga ayyukan da aka gabatar waɗanda suka shafi nahawun harshen Hausa, daga kundaye da littafai da aka wallafa; babi na biyu yana dauƙe ne da waiwayen azuzuwan kalmomin na harshen Hausa. Sannan kuma an gudanar da aikin akan nahawun taciya bisa ra’ayin masana. An kuma gudanar da aikin a kan matsayin azuzuwan kalmomin a cikin jumla.

Babi na uku, bayan shimfiɗa aikin ya yi bayyani da ire-iren jumla ta hanyar yanki da kuma ta hanyar bishiyar li’irabi da kuma har wa yau ya yi bayyaninsu daki-daki ta yarda mai nazari zai fahimci abin cikin sauki tare da fito da tsarin da matakan gina jumlar Hausa kuma yadda suke zuwa a cikin tsari na musamman “suna” da “aikatau” da “ƙarbau” ( S. A. K). Aikin ya gabatar da sassan jumlar inda aka kawo wasu manyan sassa guda shiɗa da aka nazarce su. Sun haɗa da; yankin suna (Ysn) da yankin harafi. (YHrf) da yankin bayyanau (Byn) da kuma yankin yadda fasalin wadannan sassan suke, an bayyana cewa dukkan sassan suna amsa sunan kalmomin da suke  jagorantar kowane yanki. A babin an gabatar da yankin suna (Ysn) wanda idan jumla ta zo ba suna tom wakilin suna zai wakilce ta. Wanda da ma nashi aikin wakilta suna yake yi a cikin jumla wanda dama shi wannan binciken ya fada ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Babi na huɗu, bayan shimfiɗa aikin ya taƙaitawa ne inda ya yi bayyanin abubuwan da suka gudana a cikin nazarin tare da yin sharhinsu a taƙaice, amma bayan taƙaitawa sai kuma kammalawa ita ta biyo baya, inda aka yi bayani tare da yin sharhin abubuwan da binciken ya kunsa kuma ya samo a taƙaice, daga nan sai shawarwari.

4.3 Shawarwari


Dangane da binciken da aka gudanar a lokcin da ake ƙoƙarin kamala wannan aikin, an fahimci cewa akwai wasu mahimman abubuwa daya kamata masana su mai da hankali game dasu. Kamar haka: ya kamata masana nahawun harshen Hausa, su ƙara ƙoƙari don a samar da ƙarin ƙamusun ingilishi zuwa ƙausa. Saboda ba wani ƙamus mai irin wannan tsarin baya ga na Rozana da Newman, wanda ta wallafa a shekarar 1997. Samar da ƙamus irin wannan zai taimaka wa masu nazari don samun sauƙin fassara wasu kalmomi na ilimin kimiyyar harshe a lokacin da suke gudanar da nazarin wani fanni na nahawu daga littafan ingilishi.

A fannin nazarin gini jumla, ya kamata masana ilimin ginin jumla su samar da wasu ƙarin littafatn da aka gina su bisa sabuwar fahimta ta zamani. Yin haka zai taimaka wajen bunƙusa harshen Hausa ta bangaren littafan nahawu. Waiwayar ayyukan da suka daɗe da gudana zai taimaka wirin warware matsalar da wasu gurabe ke dasu don sauƙaƙa fahimtar ga masu nazarin nahawun Hausa. Misali sake waiwayar bngarorin nahawu, irin ilimin tsarin furuci da sauran sassan shi, kamar tsarin gaba. zai haska wa masu nazarta wannan fannin wajen fahimta.

Masana ilimin kimiyyar harshe da suke gudanar da ayukkansu a kan harshen Hausa ya kamata su lura da ire-iren sababbin kalomomi da suke shigowa na zamani zuwa cikin harshen Hausa. Ko dai an aro daga wani harshe ko kuma an ƙirƙire su ne. rashin lura da ire-iren sabbabin kalmomi da suke shigowa na zamani zuwa cikin harshen Hausa. Ko dai an aro daga wani harshe ko kuma an ƙirƙire su ne. rashin  lura da ire-iren waɗanna kalmomi na iya haifar da matsala na samun bacewar kalmomi na asali. Gudanar da nazarin waɗannan kalmomi zai taimaka wajen adana kalmomin Hausa na asali ba tare sun bace ba. Sannan kuma za a sami ƙarin wasu kalomimin da za su dace da zamanin da ake ciki.

Post a Comment

0 Comments