Wannan bincike mai taken “Tauri Ko Barazanar
Siddabaru: Nazarin Siddabarun Cikin Wasan
Tauri,” an gina wannnan binciken ne a bisa la’akarin da yadda ‘yan wasan tauri
ke yin siddabaru a wajen wasan.
Binciken ya fayyace yadda ‘yan wasan tauri ke gudanar da siddabaru a filin
wasan da yadda suke harhaɗa kayan yin siddabaru kafin su shiga filin
wasa. An keɓe wannan bincike ne a ƙasar Kabi wato gundumar Argungu. An yi amfani
da hanyoyin hira da ‘yan tauri da ‘yan tauri masu aiwatar da wannana siddabaru
a wajen wasar tauri. Wannan bincike ya sami nasarar tattaro wasu abubuwa daga
cikin siddabarun ‘yan tauri. Bincike ya fito da nau’o’in siddabarun da ake
gudanarwa a cikin wasan tauri, tare da abubuwan da ake amfani da su a wajen
nuna barazana da nuna gwaninta har ma da burgewa a idon ‘yan kallo
Tauri ko Bazaranar Siddabaru: Nazarin Siddabaru A Cikin
Wasar Tauri A Ƙasar Kabi
Lauwali Aliyu
Gabatarwa
Ƙasaar Hausa tana ɗauke da ɗinbim
jarumai masu nuna jaruntaka a duk inda suka sami kan su ta fannonin rayuwa
daban-daban, haka ma, ta ɓangare
tauri ba a bar su a baya ba, domin wannan fannin ne da suke nuna waibuwa ta
amfani da ƙarfe
da abubuwan da suka shafi kaifi ko tsini. Waɗanda suka shahara a wannan ɓangaren suna cikin shirin ko-ta-kwana, sai dai Allah ya
kau da ɓacin rana. Saboda muhimmancin wannan ɓangaren shi ya haifar da yin bincike a kan barazanar
siddabaru da ‘yan tauri ke amfani da ita a wajen wasa, domin nuna burgewa da
kuma ɓatar da hankalin ‘yan kallo.
Kadadar Bincike
Ba burin wannan bincike, binciko siddabaru a
al’ada ba. Binciken ba ya da ƙudirin taɓo
komai na siddabaru a al’adun Hausawa balle sanin yadda ake aiwatar da siddabaru
a wasu sana’o’in Hausawa ba. Kadadar bincikena ita ce: Tauri Ko Barazanar
Siddabaru: Nazarin Siddabaru Cikin Wasan Tauri Kabi. Yaya ‘yan tauri ke aiwatar
da siddabaru a wajen wasan tauri? Binciken ya taƙaita ga abin da ya shafi siddabaru a cikin
wasan tauri kawai. Fatana wannan takarda ta zama mabuɗi ga yin wasu bincike masu amfani a kan siddabaru a wasu
al’adun Hausawa. Muhalin wannan bincike shi ne ƙasar Kabi wadda ta shfi Argungu da Augi da
Arewa da kuma Dandi
Dabarun Bincike
Daga cikin matakan da na hango za su kai ga
nasarar wannan aiki akwai bitar ayukkan da suka gabata. An dai ci karo da wasu
ayukka da aka yi a kan tauri da siddabaru, amman ba a taɓi abin da ya shafi siddabarun ‘yan tauri ba. Zuciya ƙudirin wannan aiki ban ga wurin da wani ya
ambaci siddabarun ‘yan tauri ba. Don haka tilas in dogara ga yawon rangadi
tsakanin ‘Yan tauri da Maƙera har ma Gardawa, domin samun ingantattun bayanai.
Ra’in Bincike
A
‘yan karance-karencen da bincike na ci karo da ayukkan Bunza (2018 da 2019),
inda ya jajirce a kan amfani tare da ɗora
ayukkan bincikenmu a kan Bahaushen ra’i mai taken “ Gwanin abu mai yin sa”.
Wannan karin yana magana ne a kan nuna gwaninta da ƙwarewa a cikin aikin da mutum ya saka kansa.
Manufa ita ce a ba bincike dama ya yanke hukunci akan abubuwan da aka gano. Da
mai ganin haka ne gwanin abu mai yin sa da mai musantawa duk maganin su a
aikata a gani.
Ma’anar Tauri
Bunza ya bayyana tauri da cewa
“ Tauri dai maganai ne da ya samo asali daga
taurin jiki, watau mai irin maganin jikinsa zai yi wa ƙarfe tauri, ba ya fasa shi”.
A wani bayani yana cewa:
“Asalin
Kalmar tauri daga “Tauri” take mai nufin abu ya ƙi fasuwa. Ko ya ƙi bari a sarrafa shi ta yadda yake so. Ko
mutum ya faye ƙin
karɓar shawara, akan ce wane taurin kai gare shi.
Mai irin wannan asiri na maganin ƙarfe ana kyautata zaton wuƙa, da takobi da mashi da duk wani makami na ƙarfe ba su fasa jikinsa. Haka kuma, yana iya
sarrafa ƙarfe
yadda yake buƙata,
ba tare da wata wahala ba.
A hirar da na yi da wasu’yan tauri sun
bayyana ma’anar tauri kamar haka:
Tauri,
ma’anar tauri, wani abu ne na tsaron jiki, maganin ƙarfe ya zamana ko a bakin ka kana tafiya ka
haye masa ko ya haye maka, ko a ishe ka, ko kuma kai da kan ka ka yi niyyar faɗa da wani tau duk abin da sara ma ko ya soka maka ba
za ya kama ka ba.
Ma’anar Siddabaru
A
ɓangaren lugga, Kalmar siddabaru, kamar Bargery (1934:938
da 946) ya nuna a kats, sakki: siddabaru, kn: suddabaru, a daidaitacciyar
Hausa: siddabaru, tana nufin dabo. Shi kuma ƙamusun Hausa (CNHN, 2006:395) ya nuna kalmar siddabaru
ita ce wasu dubaru na sihiri da suka wuce fahimtar hankalin ɗan adam, sannan kuma Kalmar siddabaru tana iya zama dabo
ko rufa-ido.
Idan
aka kalli Kalmar siddabaru ta fannin ilmi kuwa, masana al’ada da rayuwar ɗan adam sun bayyana ta ta fuskoki daban-daban. A wata
ma’ana ta isɗilahi kalmar siddabaru tana nufin dubaru
cukurkuɗa abubuwa da rikirkita su tare da ɓatar da bakin zare har a kasa gane lissafi. Wani lokaci
tana nuni a kan wayo da dabara wajen kare kai ko kuɓatar da kai tare da yin layar zana. Wasu kuma suna ganin,
siddabaru ya ƙunshi
yin surkulle da ɓatar da sau da kau da gani a samar da abubuwa
ko a gudanar da wasu ayyuka na ban mamaki.
Domin
haka, siddabaru yana nufin sanin yadda za a yi wasa da hankalin mutum har ya yi
mamakin yadda abubuwa ko ayyuka suka faru. A wannan madosa za a daɗa faɗaɗa ilimin siddabaru ya haɗa da fasaha da azanci da dibilwa da rufa-ido da srukulle
da dabo da sihiri da saɓa-al’ada da makamantan waɗannan abubuwa. Ta waɗanan hanyoyi ne ake yin siddabaru da cakuɗe-cakuɗen
abubuwa domin a gigitar da hankalin mutane ta yadda duk mutum ya kai ga wayo ko
ganewa sai an shigar da shi duhu.
Siddabarun Yanke Kwalba Da Kuɗi
Wannan
wani siddabaru ne da ‘yan tauri ke aiwatarwa a wajen wasa a yi amfani da kuɗi a yanka kwalba. ‘Yan tauri suna amfani da wani turare
ne da kaɗa, wato auduga, sai a lauya kaɗar a tsakiyar kwalbar, sai a sa zare a lauye yadda kaɗar ba za ta fita ba, a zuba turaren ya kewayo kaɗar ba da yawa ba, duk yada kaɗar ta sami turaren to ya wadatar, sai a sami kalanzir
wato barahuni ko fetur, shi ma za a zuba wa kaɗar ya zagayo, daga nan za a kunna wuta, idan ta kama da
wuta, za a bari sai kaɗar ta cinye, sai a goge baƙin da kwalbar ta yi da an goge za a ga
kwalbar ta tsaye a daidai inda aka lauye kaɗar. Daga nan za a riƙa kula da kwalbar saboda koyaushe tana iya
fashewa ta rabu biyu.
Idan
ɗan tauri zai shigo filin wasa, to zai aje kwalbar tsaye a
ƙasa, sai ya zuba mata ruwa sai ta cika, idan
zai zube ruwan sai ya riƙe tsakiya ya karkata kwalbar a hankali ya zube ruwan,
idan ya zube sai ya kira wani ya ce ya riƙe kwalbar, sai ɗan
tauri ya ɗauko naira biyar ko naira goma, ya ce zai
yanka kwalbar da kuɗin, to ɗan
taurin zai shirya da kuɗin sun kai ga kwalbar to zai ɗan tanƙwara kwalba ƙasa saboda ƙasan ya fi nauyi kuma mutane ba za su gane ya tanƙwara kwalbar ba.
Haka
kuma a hirar da na yi da Kabiru Aliyu (Ƙaro), wanda aka fi sani da Uban Dawakin Augie ya ce: Siddabarun yankan kwalba da kuɗi wata dabara ce da ‘yan tauri ke amfani da ita wajen
aiwatar da siddabarun, idan ɗan
tauri yana son ya saka kuɗi
ya yanke kwalba da su, to zai sami wani haki a ranar Lahadi kowane lokaci, duk
gutsun da ya riƙa
zai karanta masa tahiya, sai ya cire, sai ya sami gutsu bakwai, sai a saɓa shi a shanya da ya bushe a dake shi a ɗebe garin, za a sami zaren ɓartake, (Zaren kaɗa),
sai a lauya wa kwalbar zaren sau uku, za a sami barahuni wato kalanzir a zuba
shi ga wannan zaren da aka lauya wa kwalbar, amma kaɗan ba da yawa ba, sai a kunna wa zaren wuta.
Idan
wutar ta gama ci sai ya saka wa yatsansa yawu ya taɓo maganin sai ya aza maganin saman kwalbar daidai inda ka
kunna wa wuta, da zarar maganin ya taɓi
inda zafin yake to za ka ji kwalbar ta yi ƙara, idan ta yi ƙarar to da zarar ka duba za ka ga kwalbar ta
tsage daidai wurin da ka aza wannan zaren da ka ƙona.
Za
a sami ƙyalle
a goge wannan dattin na wuta, idan ya zo wajen wasa za ya baiwa wani ya riƙe kwalbar da zarar ya riƙe kwalbar shi da yasan abin da ke faruwa, za
ya aza kuɗin daidai inda kwalbar ta tsage, amma shi zai
ɗan tanƙwara kwalbar kaɗan
to lokacin za ta yanke.
Siddabarun Rawa Kan Kwalba
Wannan
wani siddabaru ne da ‘yan tauri ke amfani da shafi, wato shafa wani magani
saboda kada kaifin kwalbar da za su yi
rawa saman ta ya kama su. Ana haɗa
wannan maganin da ban wata itaciya, wato ɓawan
jikin itaciyar da jar kanwa, sai a haɗa
su waje ɗaya a dake, a sami mankaɗe a kwaɓa
garin maganin da mankaɗe, idan ɗan tauri zai je wajen wasa, sai ya safa wa ƙafafunsa ko hannuwansa ko kuma duk inda yake
buƙata a jikinsa. Idan ya gama shafa wa, to zai
sami kwalabe kamar guda ashirin ya farfasa su, ya je da su wajen wasa da zarar
an tayar da shi to zai fito da kwalaben a filin wasa ya zuba su a kan jikar da
ya zo da kwalaben, sai ya hau kan kwalaben yana rawa akai ko ya kwanta a kan
su, zai dai yi duk yanda yake buƙata, in sha Allahu ba kwalbar da za ta yanka shi.
Haka
kuma ana samun ‘yan taurin da ke amfani da ƙayar aduwa, za a saro ƙayar aduwa mai yawa ya zo da ita a filin wasa
a aje ta, to ɗan taurin da zai yi wasa da ita zai cire
tufafinsa ya hau ƙayar
ya yi rawa ko ya kwanta a kan ƙayar ko ya jawo ta wannan gefe da wannan gefen ya rufa ta
a jikinsa ya kama mulmula a cikin ƙayar, har ya gama wasa, ba za a sami ƙayar da ta shiga jikinsa ba da ikon Allah.
Siddabarun Kallar Adda
‘Yan
tauri suna da siddabarun da suke yi a lokacin wasa idan za su ƙalle adda. Za a kai adda maƙera inda wanda ya saba da yi musu aiki, ya ƙona addar ba tare da lambar addar ta ƙone ba, saboda ana zuba ƙasa mai sanyi ko busassa a kan lanbar , za a
bar addar cikin wuta sai tayi ja, sannan a fitar da ita a saka ta cikin ruwa masu wani garin maganai, sai ta sha ruwa
sosai, to idan addar ta ƙonu tun nan wata za ta kare wata kuma za ta tsage. Idan
an gama za a sami sanfefa mai garje da mai sulbi, a zauna a goge su duka, za su
koma farare kamar ba a taɓa ƙunar su ba, saboda a gusar da tunanin ‘yan
kallo.
To
ɗan tauri da zarar ya zo wajen wasa, aka fara kirarinsa
zai fito da addunan ya riƙa karya su, kuma ba wata gaddama duk yanda yake buƙata, to haka zai karya waɗannan addunan da ikon Allah.
Siddabarun Kallar Yuƙa
‘Yan
tauri suna yin siddabarun na ƙalle yuka a wajen wasa, wanda wasu mutane suna ganin abin
nan kamar gaskiya ne, amma ana bin waɗansu
hanyoyi ne domin a ɓatar hankalin jama’a ko ‘yan kallo.
Ana
gudanar da wannan siddabaru ne, ta hanyar samun guntayen addar da aka karya
wajen wasar tauri, sai a kai wa maƙeri ya yi amfani da su, ya sarrafa su ya mayar da su yuƙaƙe, bayan ya gama sai ya yi musa ɓotoci na itace da an gama yi musu ɓotoci, za a dawo a koma ƙonasu cikin wuta sai sun yi ja, sannan a
fitar a saka su cikin ruwan magani da sun huce, za a sami sanfefa mai garje da
mai sulɓi a zauna a goge su, su koma kamar sababbin
yuƙaƙe, idan an ƙare ɗan
taurin zai zo ya karɓa, ya je da su wajen wasa, da zarar an tayar
da shi wato in an fara yi masa kirari, to zai fito filin wasa da wuƙaƙe aƙalla guda huɗu
ko biyar ya karya su lokaci ɗaya
ba tare da an sami wata matsala ba.
Siddabarun Kallar Kwasa (Hauya)
‘Yan
tauri suna yin siddabaru a wajen wasa na ƙalle kwasa, domin gusar da hankalin masu kallo. A wannan
siddabaru ana yin tsabar kwasa da sifirin na mota, wato ɗan tauri zai samo sifirin na mota ya kai wa maƙera su ƙona shi a wuta sai ya yi ja, a mayar da shi tsabar kwasa,
sai a saka mata ɓota ta icce, bayan an gama kwasar, za a bata
wuta sai tsabar ta yi ja, sai a ɗauko
tsabar a saka cikin ruwan magani da ta sha iska sai a mayar da ita a ɓotar ta. To da an gama ɗan tauri zai zo ya karɓa ya je wajen wasa to duk yanda yake so zai yi da ita, da
zarar ya buge ta da hannu to za ta karye ko ya buga ta ga wani abu duk za ta
karye, da yaddar Allah.
Siddabarun Kallar Karfe Sifirin
A
wajen ƙallar ƙarfen sifirin ‘yan tauri suna yin siddabaru, domin gusar
da tunanin ‘yan kallo. Ana amfani da wani haki ne, za a shanya shi ko bai bushe
duka ba ayi amfani da shi ba matsala,
sai a daka shi a sami ruwa a zuba shi da ya yi kamar minti biyar, sai a sami
sifirin a saka shi cikin wuta sai ya yi ja, a ɗauko shi da sauri a kaɗa cikin ruwan nan na hakin da aka daka, idan ya huce, sai
a fitar da shi, to da zarar ɗan
tauri ya je wajen wasa yadda duk yake so ya yi amfani da shi zai yi, idan ya ga
dama zai buga ƙarfen
a, jikinsa ya karye ko ya ja sa, to duk zai kare, kuma ba guntu ɗaya zai yi ba, sannan idan ɗan kallo ya ɗauka
ba zai gane komai ba, saboda duk guntun da ya kare to ba za a sake iya kare shi
ba, kuma ba zai gane komai ba.
Siddabarun Ƙallar Adda Ba Tare Da An Ƙona Ta Ba
Akwai
siddabarun da ‘yan tauri ke yi na ƙallar adda, ba tare da an ƙona addar da wuta ba. Suna amfani da maganin
kaji ne, a wajen gudanar da wannan siddabaru, idan ɗan tauri zai yi wasa yau ko gobe to zai shafa wa adda
wanan maganin, ya shanya ta, ya bayar da kamar minti biyar, sai ya ɗauko addar ya shafe, saboda yakan yi ja a jikin addar sai ya sami sanfefa ya goge
addar yanda ba wanda zai gane ya shafa wani abu, to idan ya je wajen wasa zai
yi wa wannan addar ƙallar
da yake buƙata,
kuma ba abin da zai faru.
Siddabarun Yi Wa Adda Magana
‘Yan
tauri suna yin siddabaru na yi wa adda magana kuma mutane ko ‘yan kallo suna
ganin kamar abin gaskiya ne, saboda za a ce adda ta gaida mutum, kuma ta lanƙwasa wajen wanda ake da buƙatar ta gaida, idan an ka ce ta taso kuma za
ka ga ta lanƙwaso
ta tashi, tamkar tana karɓar
umurnin da ake bata ne.
Hasali
wannan addar akwai abubuwan da ake shafa mata, domin gudanar wannan wasar, idan
ɗan tauri yana buƙatar amfani da wannan
addar to zai sami waɗannan magunguna, a shafa mata, yadda ba za a
gane an shafa mata wani abu ba, idan an ƙare shafa mata abubuwan da ake buƙata, to za a sami shanfefa mai sulɓI a goge duk abin da aka shafa, saboda kada ana gane.
Idan
ɗan tauri zai yi wasa da adda a filin wasa, zai ɗauko ta ya tayar da ita, to zai saka yatsun sa ya tare
addar ko ya tura addar ko yana yi yana lanƙwasa hannunsa, to a wannan lokacin duk abin
da ya ce addar ta yi mutane za su yi tunanin tana karɓa umurnin da ake bata ne, saboda ba addar an riga an yi
mata wasu siddabaru, duk yadda yake so zai yi da ita. Saboda haka da ya ce adda
je ki gaida Sarki to zai saka yatse ya tura addar gefen da Sarki yake, kuma za
ta tafi da zarar ya ce adda tsaya, kuma za ta tsaya saboda zai saka ɗan yatsa ya tare ta. Idan an gama wasa da addar to za a
barta haka nan ba tare da an sake tada ta
ba.
Haka
kuma duk ɗan taurin da ke wasa da adda to ɗaya ce yake amfani da ita, idan ta sami matsala sai ya
sake wata irin ta. Wannan siddabaru yana bai wa ‘yan kallo sha’awa da ban
mamaki.
Siddabarun Fitar Da Ruwa A Lauje
‘Yan
tauri suna yin siddabarun fitar da ruwa a lauje a wajen wasa, domin nuna
barazana da burgewa a idon ‘yan kallo, wannan yana gusar da tunanin ‘yan kallo.
Ana
amfani da wasu hakukuwa ne a wajen yin wanann siddabarun fitar da ruwa a lauje,
‘yan tauri suna nemo waɗannan hakukuwa, za a jiƙa su a cikin ruwa sai sun ɗauki lokaci mai tsawo, ta hanyar sarrafa wannan laujen,
domin ya fitar da ruwa a lokacin da ake gudanar da wasar, idan an sami za a yi
amfani da susun katifa a wajen yin wannan laujen, ana shimfiɗa wannan susun katifa a cikin darmar sai a game, amma maƙerin ba zai bugi inda susun katifar yake ba,
sai dai gefe-gefe za a gyara shi yadda ba za a gane yadda aka sarrafa darmar
ba, ana yi wa laujen belar wuta, domin ya yi baƙi yadda ba za a gane darma ce aka sarrafa aka
mayar da ita lauje ba.
Haka
kuma ba za a bige ƙarshen
laujen ba, saboda ana yin wata kussuwa da
ruwa za su shiga a cikin laujen, wannan kussuwar ita ce ruwan za su kama
fita a lokacin da yake cewa laujen ya fitar da ruwa. Ana saka laujen a cikin
ruwa sai ya sami kamar minti biyar, sai a ɗauko laujen, idan mutum ya ga dama zai sa salatib, domin
rufe kussuwar kada ruwan su fita. Idan aka fara kirarin ɗan taurin sai ya ɗauko
laujen ya shigo fili da shi yana faɗar
lauje ka fitar da ruwa, to a wannan lokaci za a ga ruwa suna fita a lauje,
kamar lauje yana karɓa umurnin da ake ba shi ne.
Haka
kuma a firar da nayi da Bello Musa Maƙeri Argungu, ya ce: A wajen yin wannan laujen za a samu ƙarfe mai kwararo a yi wa laujen ɓota da shi, kuma za a sami (pibe) na firjin a saka a
tsakiyar darmar a wajen yin laujen, amma ba za a bugi tsakiyar ba saboda kada
kussuwar da aka yi ta rufe, saboda a sami wajen zuba ruwa a laujen da kuma
wajen fitar ruwan. Idan an tayar da ɗan
tauri zai fito da laujen yana kirari, amma kan laujen yana sama, domin idan ya
dubi ƙasa ko bai yi magana ba ruwan za su fito,
amma da ya buƙaci ruwan su fito zai yi magana ya kuma mayar
da kan laujen ƙasa
yana faɗar lauje ka fitar da ruwa ko ruwa ku tsaya;
to duk wannan siddabaru ne.
Siddabarun Na Cin Kwalba
‘Yan
tauri suna da siddabaru na cin kwalba a filin wasa da ‘yan tauri ke yi abu ne
mai matuƙar
burgewa, idan an tayar da su, ko an fara kirarin mutum, wannan cin kwalbar da
suke yi, akwai abubuwan da suke amfani da su, domin su gusar da tunanin mutune
da kuma jawo hankali masu kallo.
A
wannan siddabaru ana amfani da wani turare ne a shafa wa jikin kwalbar duka da
an gama, za a sami muhun Buzaye mai suna mangal, wanda suke shayi da shi, sai a
zuba gawayi a kunna wuta da zarar gawayin ya zama garwashi sai a aza kwalbar a
saman wutar a ci gaba da fitara da kwalbar ta yi minti ɗaya sai a juya, domin idan an barta ta ɗauki wuta sosai to za ta waste, to da zarar an ɗauko kwalbar za goge dattin da ke gare ta na wutar, za a
ga kwalbar duk ta tsage ko’ina.
Idan
ɗan tauri zai yi wasa da wannan kwalbar zai ci kwalbar a
cikin jama’a da bakinsa, amma sai ya sami ban kurna da jar kanwa da kuma wani
gari magani ko lungwaɓin zogala da jar kanwa da wani garin magani,
zai saka su a baki yana ci ba tare da ya
haɗe ko zubar da yawun da ke cikin baƙinsa ba, zai bar yawun a bakinsa, saboda sune
maganin da za su hana kwalbar ta yanka shi. Idan ya yi wannan to zai ɗauko kwalbar ya kama ɓulgutar ta kamar mai ƙallar goro, har sai ta ƙare.
Siddabarun Fitar Da Jini A Farcen Mutum
Wannan
wani siddabaru ne da ‘yan tauri ke yi domin nuna barazana da gwaninta ga ‘yan
kallo, ta hanyar fitar da jinni a yatsan mutum, amma ba tare da an yanka yatsan
ba.
A
wajen haɗa wannan maganin za a sami algasa da leda santana a zuba algasa a cikin cibiyar
ledar, za a saka algasar kaɗan
ba da yawa ba, sai a saka zaren tela a ɗaure
ledar, ɗan taurin zai saka ta a baki, idan ya saka ta
a baki za ya kai ta a gefen haƙora, wato saman dasashi ko ƙasan dasashi ya aje ta. Idan ɗan tauri yana son ya razana wani ko ya bashi tsoro to,
zai mayar da ledar a cikin baki ya taune ta, da ya saka farcen mutum a bakinsa
ya tsotsa, da ya fitar ya zubar da yawu za ka jini, amman ba jinni ba ne,
algasar da ya saka a bakinsa ce.
Siddabarun Saka Bunsuru Kwana
Akwai
siddabarun da ‘yan tauri ke yi na saka bunsuru kwana a wajen wasar tauri, domin
nuna barazana ko gwaninta har ma da ƙwarewa ga idon ‘yan kallo.
A
wajen haɗa wannan siddabaru, ana rubuta ayar wal’asar,
amman ba za a fara ba sai an fara kiran sallar la’asar, a lokacin da duk ladan
ya hau masallaci wajen kiran salla, to za a fara rubuta ayar kamin ya ƙare kiran salla ake son a rubuta ayar a gama,
kuma idan kana rubutun ba za ka sheɗa
ba, idan ka gama rubutun da ya bushe sai
ka haɗa layar da wani haki.
Idan
ɗan tauri zai yi wasa, to zai sa a kawo masa Bunsuru da
bargo wanda ke iya rufe Bunsurun duka ba za a ga jikin Bunsurun a fili ba, to a
wajen rufe Bunsurun ɗan taurin zai yi ƙoƙarin aza wa Bunsurun nan laya, ba tare da kowa ya gani
ba, to da an rufe Bunsurun da bargo ko da layar ta faɗi ƙasa ba matsala Bunsurun zai yi kwana, idan ma yana son ka
ɓadda mutane zai ɗaura
layar a bargon sai a lulluba wa Bunsurun sai ka kewaya Bunsurun, kana magana a
ciki, kamar kana wani siddabaru ne, amma ba sun laya ce ka ɗaura wa bargon ba, amma da an ɗauke layar to Bunsurun zai tashi.
Siddabarun Hawan Kwarya Ayi Tsaye a Samanta
Akwai
‘yan taurin da ke yin siddabaru na hawan ƙwarya da faifai, kuma ba tare da mutum ya faɗa cikin ƙwaryar ba ko kwarya ta mutu, domin ƙara jawo hankalin ‘yan kallo da kuma burge
su.
A
wannan siddabaru za a sami ƙwarya da faifan Fulani, sai a aza ƙwaryar inda babu faƙo bi ma’ana inda ke da yashi, domin ƙwaryar ta sami wajen zama mai kyau. To a
wannan siddabaru za a ayi amfani da layar nan da aka yi amfani da ita wajen
saka Bunsuru kwana, za a ɗauko
layar a goga wa ƙwarya
da faifan nan na Fulani, ba tare da ka bari kowa ya ga abin da kayi ba, za ka
nuna kamar kana wata addu’a ce ko ka saka hannu a aljifu kamar kana wani abu, a
wajen aje su sai ka shafa wa kowa ne layar, sai ka sake layar a aljifu.
Idan
ka gama wannan sai ka dubi mutum majiyi ƙarfi mai girma ka kira shi, da ya zo sai ka kira wani ko
da ƙaramin mutum ne, ya dafa shi ya hau saman
faifan ya yi tsaye a kan ƙwaryar nan, kuma ba za ta yi komai ba amma ya kasance duk
faifain da za a aza saman ƙwaryar ya zamo ya fi ƙwaryar faɗi ko da kaɗan
ne.
Siddabarun Cin Yuƙa
Wannan
siddabaru wata hanya ce da ‘yan tauri ke amfani da ita domin nuna barazana da
burgewa ga idon ‘yan kallo.
Wannan
yuƙar da ‘yan tauri ke amfani da ita ba, ba yuƙa ce
da ƙarfe ba, sunan samun darma ta batur na mota
ne su kai wa maƙera
baƙin ƙarfe, su yi musu yuƙa da wannan darma ne. maƙera suna zana yuƙa ne, sai su narka darmar su zuba, idan sun
yi haka za a gyara ta kamar yuƙar ƙarfe, amma su, da ke amfani da ita sun san yanda take, to
da zaran an tayar da ɗan tauri zai fito da ita yana kirari daga nan
zai saka yuƙar
a bakinsa yana ci, kasancewar darma ce da ya fito daga filin wasa zai fitar da
ita a bakinsa.
Siddabarun Fitar da Wuta a Hula
Wannan
siddabaru yana cikin manyan siddabarun da ‘yan tauri ke barazana ko nuna
gwaninta tare da burge ‘yan kallo, ta hanyar fitar da wuta a hular da ke saman
kansu.
A
wajen haɗa wannan ɗan tauri zai sami wani abu da ake kira mai kwalli, wato
(Fatashiya) za a haɗa shi da wani turare, idan an sami waɗannan sai a zuba mai kwalli daga a saman takarda, sai a ɗan zuba turaren nan kaɗan a cibiyar leda, sai a lauye ledar yada ba zai fita ba.
Daga nan za a ɗauko mai kwalli nan da aka zuba kan takarda
sai a ɗauko turaren nan da aka kulla, sai a aza kan
takardar sai a naɗe shi kamar laya. Idan ana son ya kama da
wuta to sai lokacin da ake buƙata ya kama, amma za a kula da shi sosai saboda da zarar
ya fashe to zai kama da wuta, saboda ba ya son matsuwa.
Idan
ɗan tauri zai yi amfani da shi wajen wasa to zai sami
hular saƙi
ta Yarabawa, za a yanka hular daga ciki inda ba wanda zai gane an yanke hular,
sai a tura layun guda biyu, idan ba za a gansu ba. To da zarar ɗan tauri zai yi wasa zai aza hular a kansa, da an fara
yin wasa kirari da ya fito a filin wasa to da ya sa hannu ya. Matse hular bayan saƙon daga zuwa biyu za ka ga hayaƙi ya fara tashi, sai hular ta kama da wuta. Haka kuma
idan yana son abin ya ƙara
almushi, za a saka tokar Bindiga a cikin haɗin, idan ta kama da wuta to abin zai fi rigima da nuna
barazana.
Fitar Da Wuta Ga Adda
Wannan
ma wani siddabaru ne da ‘yan tauri ke yi domin nuna barazana da gwaninta a
wajen wasar tauri.
Kamar
yadda muka yi bayanin layar da aka haɗa
a wajen fitar da wuta a hula, to a nan
ma ana amfani da waɗannan abubuwa da muka faɗi ana amfanin da su. Idan ɗan tauri zai yi wasar fitar da wuta a adda za a ɗaura waɗannan
layoyin guda biyu a sannan addar kasa ga ɓotar
adda ya saka ledar addar ya rufe, idan ya fito a filin wasa zai sa hannunsa ya
danne waɗannan layoyin da zarar ya yi sun fara zafi
sai ya ɗauke hanunsa, ba da jimawa ba za ka ga addar
ta kama da wuta. Idan ɗan tauri yana buƙatar karya addar to da zarar ya buga ta ga ƙasa ko wani abu, zai karya ta.
Sakamakon Bincike
Wannan bincike mai taken: Tauri ko Barazanar
Siddabaru: Nazarin Siddabarun ‘Yan tauri a a Ƙasar Kabi, ya gano cewa da yawa daga cikin
‘yan tauri suna amfani ne da siddabaru, watau dabaru da hikima domin burge masu
kallo, ba tauri ne na haƙiƙanin
gaskiya ba. Haka wannan bincike ya gano cewa akasarinsu sai sun shiryo abin da
za su aikata a dandali daga gida. Haka ma, binciken ya gano ‘yan taurin suna
amfani ‘yan kore, domin su riƙa musu kayan da za su yi amfani da su a dandali ba tare
da sun masu wata matsala ba. Haka kuma, binciken ya gano wannan siddabaru da
‘yan tauri ke aiwatarwa ba zai yiyu ba, ba tare da maƙera ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.