Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure 34: Makarantu Ma


Don tabbatar da wannan tsari wata makarantar Islamiyya da na taɓa karantarwa ta sanya dokar-ta-ɓaci a kan duk wani malami cewa kar ya taɓa yarda a kama shi da laifin soyayya da wata ɗaliba. Samun hakan zai iya kaiwa ga korar su gaba ɗaya. Ke nan ba wani...


Zan Ƙara Aure 34: Makarantu Ma

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunna

Galibi makarantu su aka fi sa rai da gyaran ɗabi'u  da halaye na ƙwarai, koda kuwa ba makarantun addini ba ne, sannan sukan shagaltar da yaran ta wurin debe lokutansu, yadda dalibi zai dawo gida a makare ga kuma tsabagen gajiya, a ƙarshe ba abinda yake buƙata sai hutu, malami hakkinsa ne ya kula da tarbiyyar yarinya matuƙar tana gabansa, matsalolin da zai iya daukar mataki na nan take ya dauka, waɗanda suka fi ƙarfinsa kuma uwayen su yi maza su gyara kayansu kafin ya baci.

Don tabbatar da wannan tsari wata makarantar Islamiyya da na taɓa karantarwa ta sanya dokar-ta-ɓaci a kan duk wani malami cewa kar ya taɓa yarda a kama shi da laifin soyayya da wata ɗaliba. Samun hakan zai iya kaiwa ga korar su gaba ɗaya. Ke nan ba wani malami da zai ce ya auri daliba a makarantarsa, in dai ta gama ta koma gida kai malami za ka iya binta can ka neme ta a wurin uwayenta, to gaskiya kusan ni kaina abinda ya faru kenan, ina tare da ita na tsawon shekaru kuma na yaba da laɗabinta a ƙarshe tana kammala karatunta na bi ta na dawo da ita gidana.
.
Makarantar dai ita ce dalili, akwai kuma wani da ya je kai wa ƙanwarsa ziyara ta fito wurinsu tare da wata ƙawarta, ashe kai yallaboi ya ƙyasa, nan take ya dan fara tuntuba, "Ke wance wai ƙawarnan taki ba ta magana ne?" Ka san mazan yanzu da son fararen mata, komai ya ji, ga kunya, ta sha jan lalle ni da ban gan ta ba na yi sha'awa, makarantar ta Islamiyya ce, an ce yarinyar ma mahaddaciya ce, yallaboi dai ya nace, har ƙanwarsa ta fahince shi ta yi dabarar da ta hada su kafin su fita, an ce har yarinyar ta kai shi gidansu, ga alama dai komai ya yi.
.
Akwai wani babban mutum da ya same ni yake ce min yana son mace mai sifa kaza da kaza don Allah na duba masa a Islamiyya, abinda ya fi maida hankali a kai shi ne mai tarbiyya da hankali, babba ne a ƙasa amma ya dawo makarantar Islamiya yana neman aure, banza dai ba ya kai zomo kasuwa, ai bai rasa ganin 'yammatan a gari ba, na tabbata har a kwanan gidansu akwai su, me ya sa ya bari ya zo Islamiyya? Yana zaton mace ta ƙwarai tana can ne, maganar da wasu ke cewa wai "Hatta matan da suka karanci addini in suka kantara maka tsiya sai ka yi fatar da ba su ka aura ba" na ce: To mai ilimi ma ta yi hakan ya kake tsammanin za ka sami jahila?
.
Na yarda cewa ba duk mace mai ilimi ce salaha ba, amma Ƙur'ani ma ya tabbatar da cewa ba za a hada wanda ya sani da wanda bai sani ba,vko kusa ba za su hadu ba, akwai lokacin da mace za ta aikata wani abin in ta tuna lahira sai ka ga ta dan ja da baya, kenan ba za a hada ba da wace tunanin lahirar ma ba shi a gabanta, ni dai da idona na ga wasu malaman da duk dalibansu suka aura, ciki har da wani dattijo da yauri yarinya danya fatau, wasu malaman da muke tuhumarsu da auren daliban suka ce "Ai gwara ka auri wace ka amince da tarbiyyarta da ka je ka auro wace samsam ba ka san yadda ta taso ba".
.
Akwai wani mutum da na ji ya ba da wasu sifofi na mace ya ce a je a nemo masa a Islamiyya, an samu ɗin amma 'yar gidan manya ce sai ya haƙura, makarantu dai ana samun dalilan da za su hada maza da mata, duk kuma dalilin da zai yi wannan tabbas zai bude ƙofa ta ƙarin aure, ziyarar da uwaye ke kai wa yarinya dalili ce, don da wannan idonka zai iya leƙo maka alkhairi, in kana da jarumta tun daganan za ka hada komai, to bare kuma ga bukukuwan saukar karutu wanda ake ƙure adaka a zo, ga zuwa daukar yara a maida su gida ko a biya musu kuɗin makaranta.
.
Tarurruka na uwayen yara duk dalilai ne, wasu shirye-shirye da makarantu ke yi kuma su gayyaci 'yan kallo duk sukan taimaka yadda wani bai komawa sai da abinda zuciyarsa ta ƙunsa, in aka yi sa'a sai ka ga aure ya datso, na ga wace nan da nan ta sami mijin aure a dalilin musabaƙa, dama ana ta yi mata tsiyar baƙi, gaskiya baƙar ce, sai dai Allah ya hore mata Ƙur'ani ga murya, na ji wai ta yi ta ɗaya a wurin musabaƙar Ƙur'ani kuma ta sami kujerar Maka da kayan daki, kan ta gama karatunta har ta yi aure ta bar masu tsokalanta.

Post a Comment

0 Comments