Ƙoƙarin ƙara ƙauna a zuciyar maigida: Wannan kam yana da rassa da yawa amma mata sun fi kula da taƙaitattun kamar kwalliya da gyarar shimfiɗa. Shi ya sa kuɗaɗensu suke ƙarewa a nan. Mata da matan aure duk sun zama hawainiya. Na ga wata kwalliya da aka yi wa wata sai zufa take yi. Na ce: "Yanzu haka in ka bincika wannan ya kai Naira 7,000." Suka ce Naira 40,000 ne!” Na ce "Zai goge?" Suka ce "I, amma ba nan da nan ba." In ma ka...


Kunɗin Ma’aurata // 34: Ɗan Saurara

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

In kina son ki zama ta ƙwarai sosai to ki yi ƙoƙarin kiyaye waɗannan:-

1) Yi ƙoƙari ki gwanance a duk abin da za ki yi a cikin gida, kuma ya kasance don Allah ba don a yaba miki ba, don in dai za ki yi abu don yabo to a kullum yabon kike nema, in har ba ki same shi ba to hankalinki ba zai taɓa natsuwa ba, kuma za ki riƙa jin cewa aikin banza kika yi.
.
Haka kuma kar ki yi don tsoron bakin jama'a ko fushin maigida, ki yi don Allah sannan don kin fahimci cewa maigidan zai ji daɗi koda bai yi magana ba, kamar tsaftace dakinki, gidanki, ban-daki da kicin, ki gyara abincinki, dole dai ki ci abinci a wani wuri, in kika ji ya fi naki daɗi yi ƙoƙari ki san dalili, shin yanayin hadi ne ko dafawa ko cefanen ne ya bambanta yadda kike sanya abin da bai dace ba ko ba ki sanya abin da ya kamata ba? Bangaren abinci abu ne mai matuƙar mahimmanci yana da sashinsa na masamman a zuciyar maigida, kar ki yarda da cewa ke kin iya abinci don haka ba za ki koyi komai a wurin wata ba, don sau tari in ka ce wa mace ta yi kaza sai ta ce ita ba yadda take yi kenan ba.
.
2) Abin da Annabi SAW ya ce game da soyayya shi ne "Kau da kai ka bar duniya sai Allah ya so ka, nesanci abin hannun mutane  sai su so ka" wannan kar ki yi zaton maigidanki daban ne, yawan ba ni-ba ni ɗinnan bai da amfani, in za ki iya yin wani abu ba sai kin tambaye shi ba daure ki yi, in kuma abin da ya ba da ya zarce to ki rage ki adana, sai nan gaba in ya bayar ki gaya masa akwai sauran na baya, za a ƙara kadan ne ko kuma ya isa, namiji yana son ya ga mace tana tausaya masa, duk da cewa ya fi ƙarfin abu, don ya ba da wanda ya fi haka a nan gaba ba wani abu ba ne, in dai aka nuna masa ana jin tausayinsa ba ƙaramin daɗi zai ji ba.
.
3) Kasala da son jiki ba na mace ba ne. Ko kina da shi kar ki yarda maigidanki ya fahimci haka, duk abin da yake so tashi ki yi masa a lokacin, wasu mazan in aka yi musu jinkiri sun dauki fushin da ba ya yankewa kenan, ƙila ma su ce ba sa son abin da za a yi musu ɗin ma gaba daya, su tashi su yi da kansu, kasala da gardama ba abu ne mai kyau ga mace ba, don in ba ta yi sa'a ba duk lokacin da ta yi kuskure ba za a yi mata hanzari ba, wata macen gardama ta zama mata jiki, komai aka gaya mata sai ta sami abin da za ta fada, in har saba da haka ita ma da wahala ta riƙa sauraron maigidanta, ko fada zai yi mata kan wani abu da ta yi masa maras kyau za ka ji harshenta sama, kafin ya fadi 2 ta fadi 4 zuwa sama, irin waɗannan matan aurensu yakan fi na kowa tangadi, in ya zo da tsautsayi nan da nan yake kifewa.
.
4) Ƙoƙarin ƙara ƙauna a zuciyar maigida: Wannan kam yana da rassa da yawa amma mata sun fi kula da taƙaitattun kamar kwalliya da gyarar shimfiɗa. Shi ya sa kuɗaɗensu suke ƙarewa a nan. Mata da matan aure duk sun zama hawainiya. Na ga wata kwalliya da aka yi wa wata sai zufa take yi. Na ce: "Yanzu haka in ka bincika wannan ya kai Naira 7,000." Suka ce Naira 40,000 ne!” Na ce "Zai goge?" Suka ce "I, amma ba nan da nan ba." In ma ka ɗauko maganin mata za ka ga yadda ake cinikinsa. Ko da kuwa a zahiri mace ba ta jin komai, in dai aka kuzuzanta shi sai ta yarda cewa tabbas yana aiki, kuma da shi za ta farauci ran maigida. Tabbas akwai wasu abubuwa ban da waɗannan.
.
i) Na farko dai ibada da kusantar mace ga Allah. Dalili shi ne, idan Allah SW ya yarda da mutum dole mutane su yarda da shi ko suna so ko ba sa so, bare kuma mace da take mai tarbiyya, ita ce makarantar farko, a wurinta yaro ko yarinya za su fara daukar darasi, idan za ta yi wa maigida abu don Allah, ko ya kushe a ƙarshe dai babu wata gaskiya sai wannan, dole zai dawo ya yaba, ya kuma fadi cewa tabbas an nuna masa gaskiya shi ne bai dauka ba.
.
ii) Wannan ya yi kama da maganar Annabi SAW inda yake cewa "An halacci zuciya da son mai kyautata mata, da ƙin mai munana mata" ki dage kawai wajen kyautatawar ki manta da zancen baka, koda namiji bai fito ya tallata abin da yake ciki ba na ƙauna, shi ma zai yi wani abin da zuciyarki za ta natsu sosai da shi kan cewa yana ƙauna, kin ga kuwa kyautatawa ba ta da alaƙa da kwalliyar fuska ko adon tufafi ko maganin mata, ba cewa nake yi wadancan ba su da amfani ba, maganata ita ce ba su kadai ne ba.
.
iii) Nuna ƙauna da yin hidima ga makusantan maigida, da zabinsu a kan kowa, ba a jima ba wani abokina yake ba ni labarin cewa wani dan uwansa ya ciro kudi zai ba ƙanin matarsa sai matar ta ce "Mun gode wallahi, amma ka fara ba wanda ya zama wajibi a kanka tukun, mu kyautatawa ce" a ganinka wannan matar ba za ta canza masa tunani ba? Ka dubi dai yadda Ƙur'ani ya sifanta mutanen Maɗina lokacin da Allah SW yake ambatonsu yake cewa "Sukan yi zabi a ba wasu koda kuwa suna da matuƙar buƙatar abin" wannan a matakin kowa kenan to bare makusantan maigida, in har mijinki ya gano wannan ɗabi'ar zai so ki.
.
iv) Bin hanyoyin mallakar zuciya na halas, akwai wasu hanyoyin da ake mallake miji da su amma ba su da kyau, kamar hassada da ƙarairayi da shiga bokaye da mallaman tsibbu da sunan neman taimako, koda mace ta yi nasara zai kasance na dan ƙaramin lokaci ne kawai kuma ba za ta taɓa jin daɗin abin da ta yi ba, mallakar ba za ta ba ta kwantar mata da hankalin da take tsammani ba, sannan in asiri ya tonu to za ta yi asarar komai, ga haduwa da fushin Allah SW, wannan kuma yakan kunyata mutum ne duniya da lahiri, mata a yau sun yarda da bokaye sosai da malaman tsibbu don neman ƙaunar maigida.