Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambance-Bambance Tsakanin “Bukin Buɗar Daji” da “Bukin Shan Kabewa”


Tun ana gobe za a yi bukin jama’an da aka gayyata na nesa da na kusa za su hallara a garin da za a yi bukin. Haka idan ana gobe za a yi bukin yau da la’asar sai manyan bokaye da mafarauta a ƙarƙashin jagorancin babbansu su fito su kewaye dajin da za a fita farauta a cikinsa idan gari ya waye. A ranar da za a yi bukin da safe sai ‘yan bukin da sauran jama’a tare da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe su yi harman fita daji domin yin farauta...


Bambance-Bambance Tsakanin “Bukin Buɗar Daji” da “Bukin Shan Kabewa”

Ibrahim Mohammed
(08060287141)
Lauwali Aliyu
Bello Umar Dargaza
Gabatarwa
Bisa lura da wannan aiki ya shafi bukukuwan Hausawa ne na gargajiya wanda suke gudanarwa tun kafin zuwan addinin Musulunci har zuwa yau, bukin “Buɗar Daji da Bukin Shan Kabewa” lallai ya kamata kafin mu shiga cikin aikin za mu yi tsokaci game da su wane ne Hausa domin zai ba da haske dangane da wanan al’ada ta budan daɗi da shan kabewa da za a aiwatar a yanzu. Haka ma akwai buƙatar tsakuro bayani dangane da ko su wane ne Maguzawa a idon Hausawa.
Hausawa mutane ne da ke magana da harshen Hausa a matsayin harshen farko, kazalika addinin Hausawa da al’adunsu ya yi tasiri a kansu. Dangane da ko su wane ne Maguzawa kuwa, binciken masana ya tabbatar da cewa ba kowa ne Maguzawa ba face Hausawa waɗanda ba su karɓi addinin Musulunci ba, haka kuma addininsu na gargajiya ke jagorancin raywuarsu. Dan haka ne kuwa, muna iya cewa dukkan Hausawa Maguzawa ne kafin shigowar addinin Musulunci. Bayan shigowar addinin Musulunci ne fasalin ya sauya zuwa Hausawa a matsayin waɗanda suka karɓi addinin Musulunci da kuma Maguzawa waɗanda suka ƙi karɓar addinin na Musulunci.
Hausawa kamar sauran al’ummu na duniya ne, domin suna da al’adu iri daban-daban da suke amafani da su a rayuwarsu ta yau da kullum. Haka kuma sun kasance ma’abota addinin gargajiya kafin haɗuwa da baƙin Larabawa da Turawa. Wannan ne ya sa ba su damar samar da hanyoyin bauta da kuma yin biyan wasu buƙatunsu na rayuwa. Kamar yadda aka ambata a baya.
Hausawa suna da al’adu da yawa da suke gudanarwa a rayuwarsu wanda suka shafi al’adar Aure, suna da waɗansu masu tarin yawa. Haka kuma sun kasance ma’abota dogaro da kai ta hanyar noma, kasuwanci, kiwo, farauta, ƙira da sauransu. Bayan abubuwa da suke aiwatarwa a rayuwa.
Saboda haka ne Hausawa ke da bukukuwan gargajiya iri daban-daban da suka haɗa da bikin buɗar daji da bikin shan kabewa da wasunsu, sannan a yanzu Hausawa na da bukukuwa da yawa wanda suka samu sanaɗiyar karɓar addinin Musulunci wanda suka haɗa da, bukin sallar takutaha, bukin sallar idi, bukin sallar maulidi da sauransu.
Dalilin wannan aiki ko nazari shi ne bayyana wasu nau’o’i daga cikin nau’o’in bukukuwan Hausawa na gargajiya wajen nuna bambanci da ke tsakanin bukin buɗin daji da kuma “bukin shan kabewa.” Akwai abubuwan da za mu bayyana dangane da waɗannan bukukuwa. Abubuwan su ne kamar haka:
a.      Ma’anar buki
b.     Ma’anar kalmar buɗar daji
c.      Ma’anar kalmar shankabewa
d.     Dalilan yin bukin buɗar daji da na shankabewa
e.      Yadda ake gudanar da su
f.       Bambancin da ke tsakaninsu
g.     Matsayin bukukuwan a raywuar Hausawa a yau
h.     Naɗewa

Dalilin Yin Bukin Buɗar Daji da na Shan Kabewa
Dalilin Bukin Buɗin Daji
Duk wani abu na duniya da ake gudanarwa ba zai rasa dalili ko hujjan aiwatar da shi ba. Saboda haka, shi ma bukin buɗin daji bai kauce wa wannan bayani ba, domin kuwa akwai dalilin aiwatar da shi a ƙasar Hausa.
Hausawa na gudanar da wannan buki ne domin a fayyace ko tantance abubuwan da za su faru a shekara mai zuwa. Daga cikin abubuwan da aka duba za su faru akan yi sa’a duk su kasance masu kyawu ko a samu gauraye wato masu kyawu da marasa kyawu. Saobda haka idan aka yi sa’a da duk abubuwan da za su auku masu kyawu ne akan taya juna murna da samun kyakkyawar shekara. Idan kuwa akwai munana a cikin abubuwan, to akan yi ƙoƙari ta hanyar tsafe-tsafe da siddabaru domin kaucewa wannan abin koko sauƙaƙa shi idan dole sai ya faru.

Dalilan Yin Bukin Shankabewa
A tsarin rayuwar al’umma babu wani abu da za a gudanar ba tare da wani ƙwaƙwaran dalili ko hujjar yin sa ba, saboda haka bukin shankabewa buki ne da ya samo asali tun kaka da kakanni, wanda ake aiwatarwa bisa tsarin bautar iskoki a gargajiyance wanda ke ƙunshe da wasu muhimman dalilai da suka shafi harkokin raywua na yau da kullum. Waɗannan dalilai sun haɗa da:
1.     Kariya daga miyagun cututtuka. Sarakuna kan sa ‘yan bori da bokaye su nema masu kariya a kan cututtukan da ke damun al’ummar ƙasar ko da kuwa ciwon daga aljanu ne kamar hauka, shan Innan da sauransu.
2.     Neman amfanin gona mai yawa: Ana aiwatar da wannan buki ne domin neman taimako ga ikoki da ake bautawa don su kare su daga sharrin fari ko bushewar ƙasa idan an yi shuka ko fara ko tsutsa ko sauran ƙwari da za su iya kawo cikas ga noma.
3.     Neman tsari daga annoba da kuma gano abin da zai auku a shekara mai zuwa: Sarakuna da talakawa suna ba da gudummuwa a bokaye da ‘yan bori domin su yi musu duba a kan wani abu da zai faru a wata shekara mai zuwa.

Yadda Ake Gudanar da Bukukuwan Buɗar Daji da na Shan Kabewa
Yadda Ake Gudanar da Bukin Buɗar Daji
Tun ana gobe za a yi bukin jama’an da aka gayyata na nesa da na kusa za su hallara a garin da za a yi bukin. Haka idan ana gobe za a yi bukin yau da la’asar sai manyan bokaye da mafarauta a ƙarƙashin jagorancin babbansu su fito su kewaye dajin da za a fita farauta a cikinsa idan gari ya waye. A ranar da za a yi bukin da safe sai ‘yan bukin da sauran jama’a tare da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe su yi harman fita daji domin yin farauta. Idan an fita farauta duk dabbar da aka ci karo da ita, ita za a kaso da ƙarfi da yaji ba tare da an yi amfani da kare ba a kawo gaban shugaba ko sarkin dawa ko sarkin bokaye a ajiye. Amma kafin a shiga dajin da za a yi dole sai sarkin bokaye ya ɗaure dajin ta yadda babu wani naman daji da zai iya cutar da wani.
Abin lura a nan shi ne, kowace irin dabba aka fara cin karo da ita aka farauto ta akwai fatawa na musamman da akan bayar dangane da ita kafin a feɗe ta a ciro kayan cikinta domin nazarinsu. Alal misali, idan aka kama zaki ko damisa, za a ce ‘ya’yan da za a haifa shekara mai zuwa za su kasance jarumai. Idan aka kama zomo za a samu ‘ya’ya masu wayo. Idan aka kama kura, za a samu matsorata. Idan bodari ne za a samu wawaye.
Haka kuma dai abin yake, kowace dabba da irin fatawar da ake ba ta. Haka kuma dabbar da za a kamo dole ta kasance mai rai ba matatta ba mai lafiya ba marar lafiya ba bayan an yi wannan, sai a feɗe a ciro kayan cikinta gaba ɗaya domin fatawa na ƙwaƙƙwafi. Daga nan shugaban tsafi zai natsu sosai ya ci gaba da nazarin kayan cikin da kyau domin gano aubuwan da za su auku a shekara mai zuwa. Abin nufi a nan shi ne kayan cikin dabbar su ne alamomin abuuwan da za su auku a shekara misali, idan aka ga yayi a cikin tumbi, sai a ba da labarin cewa shekara mai zuwa za a yi iska. Idan aka ga ruwa da yawa a cikinta, za a ce za a sami ruwa da yawa da damina mai albarka. Dan kuwa ruwan kaɗan ne, sai a ce za a yi fari, sai a ce za a samu albarkar noma da yawa. Idan kuwa aka sami ƙwari ko tsutsa a cikin tumbin, za a duba a gani idan ƙwarin ko tsutsotsin masu rai sun fi yawa za a ce babu mutuwa da yawa idan kuwa ƙwarin matattun sun fi yawa, za a yi mace-mace. Idan kuma ƙwarin masu rai ne amma aka ga ba su da kuzari kamar marasa lafiya sai a ce za a yi fama da cutuka amma babu mutuwa da yawa.
Bayan an gama wannan fatawa sai kuma a shiga raba naman da kayan cikin zuwa ƙungiyoyin jama’ar da suka halarci bukin. Kowa zai yi ƙoƙarin samun naman ko mai ƙanƙantarsa ya kai gida a sa a cikin girkin abincin gidan. Irin wannan abincin da aka yi idan an gama akan raba wa dangi ne kowa ya samu ya ci. An ce wai cin irin wannan abincin da aka yi da wannan nama zai kare duk wanda ya ci daga sharrin cututuka da masifun wannan shekara. Idan an gama raba nama kowa ya samu, za a kuma ɗebo icce ɗari a dajin da aka gudanar da bukin sai a dake su wuri ɗaya a ba kowa ya ci. Shi ma wannan kariya ne daga cututtukan da za su faru a shekara mai zuwa. Haka kuma idan aka koma gida za a yi yanke-yanken dabbobi a bai wa abubuwan bauta domin samun sauƙi ga illoli da masifun da aka bayyana za su faru.

Yadda Ake Gudanar da Bikin Shan Kabewa
A ranar da aka ba da shelar cewa za gudanar da bikin shan kabewa tun a cikin daren yinin ‘yan bori da bokaye za su fara haɗuwa a wani dandali na birni ko ƙauye da aka ce za a haɗu tare da masu garaya da gurmi ko kuntugi. Idan za a fara bikin, za a yanka tauren baƙin bunsuru. A yayyanka namansa guntu-guntu, a haɗa shi da ganyen lawashin albasa da yalo da gauta da soɓorodo da kuɓewa ko kabushi mai yawa a saɓe su cikin turmi, a dafe su tare a cikin wata babbar tukunya, wadda aka tanada don yin wannan hidima duk shekara.
Idan komai ya dafu an sauke tukunyar, za a rarraba wa kowa ya sha. Duk wanda ya sha kuɓewar to babu abin da zai same shi a wannan shekarar. A Zamfara har gumba suna sha a wannan bikin. Daga nan sai a hau bori da tsafe-tsafe a yi ta yi har tsawon mako ɗaya da wuni.
A rana ta ƙarshe ranar Lahadi sai kowa da kowa ya ɗunguma a yi yamma wajen nakiyar damina. Wasu riƙe da kaza ja wadda suke cewa kudukku kazar ‘yan bori. Wasu kuma jaye da akuya baƙa ko bunsuru baƙi waɗanda za su sakar wa iskokinsu da sunan sun raki damina.

Bambancin da ke Tsakanin Bikin Buɗar Daji da na Shan Kabewa
Idan muka lura za mu ga cewa akwai bambanci a tsakain bukin buɗar daji da na shan kabewa bisa la’akari da bayanin yadda ake gudanar da bikin buɗar daji da na shan kabewa za mu ga akwai bambanci mai tarin yawa ko da ma a nan, kawai aka dakata, to amma yana da kyau a fito da bambance-bambancen a fili domin ƙarin haskaka aikin ta hanyar da zai sake sa wa a samu ƙarfin guiwa tare da samun nutsuwa.
Bukin buɗar daji ana aiwatar da shi ne bayan ruwan damina ya ɗauke da wata huɗu (4). Idan wannan wata na huɗu ya kama, ranar sha huɗu gare shi ranar ake yin wannan biki. Kuma tun kafin loakcin ya yi akan sanar da jama’a na nesa da na kusa ranar da kuma lokacin da za a yi bukin.
Shi kuwa bikin shan kabewa a na yin taronsa ne a cikin watan goma na Bature wanda ya yi daidai da ƙarshen watan malamai wato watan Zulƙida na Musulunci. Haka kuma ga al’ada ba a fara wannan biki sai ranar asabar da rana tsakiya kuma ana yin mako guda ana gudanar da wanann buki. Kuma ba a gama shi sai ranar Lahadi.
Bukin buɗar daji ana aiwatar da shi ne a daji wajen da ake aiwatar da farauta duk dabbar da aka ci karo da ita, za a kaso da ƙarfi da yaji ba tare da an yi amfani da kare ba, a kawo gaban shugaban ko sarkin dawa a ajiye don a gudanar da bukin ta hanyar yin sharhi a kan dabbar bayan an yanka ta, wajen fahintar me zai faru a shekarar kamar yadda aka ambata.
Amma shi kuma bukin shan kabewa ana gudanar da shi ne a wani dandali ko ƙauye da aka ce za a haɗu tare da masu garaya da gurmi, kuma shi bukin shan kabewa idan za a fara bukin za a yanka taure wato baƙin bunsuru a yayyanka namansa guntu-guntu a haɗa shi da ganyen lawashin albasa da yalo da gauta da kuɓewa mai yawa a soɓe su a turmi a dafe su tare a cikin wata babbar tukunya.
Bukin buɗar daji ana aiwatar da shi ne a daji kuma akasari masu aiwatar da shi mafarauta ne don neman sanin abin da zai faru a wannan shekara ta hanyar yin tsafe-tsafensu a gano abin da shekarar take tafe da shi na alheri ko na sharri, shin za a samu ruwan sama mai yawa ko ƙarancinsa za a samu, kakar hatsi ko fari za a yi haka kuma mai zai biyo baya a cikin shekarar.
Amma shi bukin shan kabewa masu aiwatar da shi ‘yan bori ne da kuma bokaye ga al’ada shi wanan buki ana yin sa ne a lokacin da aka cim ma kakar hatsi musamman lokacin da aka gama girbin dawa ana roron wake a wannan lokacin ‘ya’yan kabushe ka nuna a ko’ina.
Shi kuma bukin shan kabewa ana aiwatar da shi ne bisa wani dalili kamar haka:
Neman tsari daga miyagun cutuka da kuma neman tsari daga annoba ta hanayr amfani da ‘yan bori da bokaye wajen neman kariya ga dukkan annoba. Wajen da ake yin amfani da naman baƙin bunsuru a haɗa shi da kabushi da kuɓewa da lawashin albasa a sa a turmi a dake a dafa su a tukunya a ba wa kowa ya sha don neman kariya daga cutuka na wannan shekarar.
Daga cikin bambancin da ke tsakanin bukin buɗar daji shi ne shi buɗar daji tun kamar gobe za a yi bukin to tun da la’asar manyan bokaye da mafarauta a ƙarƙashin jagorancin babbansu sukan fito su kewaye dajin da za a fita farauta a cikinsa. Idan mun lura a nan za mu ga cewa shi bukin buɗar daji a daji ne ake aiwatar da shi wato ba a gari ba.
A ta fuskar bukin shankabewa kuwa, shi ana aiwatar da shi ne a gari wato ƙofar sarkin bori ko kuma wani dandali da aka keɓe shi na musamman, haka kuma shi bukin shankabewa ‘yan bori ne ke jagorantarsa.
Baya ga haka, daga cikin bambancin da ke tsakaninsu shi bukin buɗar daji bokaye ne ‘yan bori ke shugabantar su, daga cikin aikin bokayen, dole ne sai sarkin bokaye ya ɗaure jeji da zai iya cutar da wani. Haka kuma a bukin buɗar daji ake neman albarkar noma.
Shi kuwa bukin shankabewa tun cikin daren yinin ‘yan bori da bokaye za su fara haɗuwa a wani dandali na birni ko ƙauye da aka ce za a taru da masu garaya da gurmi ko kuntugi.
Bukin buɗar daji dabbar da aka fara kamawa a daji ana yanka ta ne a ɗauki tumbinta a yi amfani da shi wajen gwada abubuwan da za su faru a wanan shekara, wajen duba irin jinyar da ke da akwai a wannan shekarar, ko kuma mace-macen da za a yi.
Bayan an gama wanann fatawa sai kuma a shiga raba wannan naman da aka kama da kayan cikin dabbar ga waɗanda suka halarci bikin. Kowa a ba shi naman komai ƙanƙantarsa ya tafi da shi gida domin a ci. Da nufin duk wanda ya ci wannan naman zai shekara cikin ƙoshin lafiya ba tare da wata jinya ta kama shi ba.
A ta fuskar bukin shan kabewa kuwa, baƙin bunsuru ake yanakwa a haɗa shi da ganyen lawashin albasa da yalo da kuɓewa ko kabushi mai yawa a dafa shi a tukunya don yin wanan hidimar, sai a bai wa kowa da ya zo ya sha don kaicewa daga dukkan wata jinya a wannan shekara.
Saboda haka, idan muka yi la’akari za mu ga cewa lallai akwai bambanci a tsakanin waɗannan bukukuwa wato bukin shan kabewa da na buɗar daji, dabbar da aka kama a dajin ita ake yankawa a yi gwaji da ita kuma araba ta ga waɗanda suka halarci bukin. Amma a shi bukin shan kabewa, ba haka ba ne, ana amfani ne da baƙin bunsuru (taure) da wasu abubuwa irin su kabusi, yalo da kuɓewa.

Matsayin Bukukuwan Guda Biyu a Rayuwar Bahaushe a Yau
Bukukuwan Hausawa bukukuwa ne da akan aiwatar da su a da da kuma wasu a yanzu. Alal haƙiƙa idan muka duba za mu ga cewa bukukuwan da Hausawa suke aiwatarwa a jiya suna da wata manufa da ya sa suke gudanarwa irin wannan manufa kuwa ta shafi irin su neman kariya ko tsari daga cutukan shekara da kuma sanin abin da shekarar za ta auku.
Hausawa a baya suna yin buki ne dan bauta wa iskoki da nufin neman kariya da kuma samun biyan buƙatunsu na yau da kullum. Wannan ne ma ya sa suke yi musu hidima game da abin da suke buƙata.
Amma a yau idan muka lura z amu ga cewa alal haƙiƙa shigowar addinin Musulunci a ƙasar Hausa ba ƙaramar rawa ya taka ba wajen kawar da wasu miyagun al’adu ko raunana su ba. Tarihi ya nuna addini ya samu karɓuwa a ƙasar Hausa kamar yadda ya kamata. Haƙiƙa malamai sun yi wa’azi ta hanyoyi daban-daban domin kyautata rayuwar Hausawa zuwa ga tafarkin addinin gaskiya wannan ne ya sa Hausawa suka yi watsi da al’adar bukin shan kabewa da na buɗar daji kai har ma da sauran al’adun gargajiya da suka saɓa ma koyarwan addinin Musulunci.
Duk da yake Musulunci ya ratsa zukatan Hausawa da ma rayuwarsu gaba ɗaya, amma har yanzu akwai ɓirɓishin wannan al’ada na bukin shan kabewa da na buɗan daji a wasu ƙasashen Hausawa kamar birnin Kwanni da wasu ƙauyuka na Sakkwato. Wannan ba abin mamaki ba ne domin kuwa har yanzu akwai Hausawan da ba su ba da gaskiya ga addinin Musulunci ba, ko kuma sun bayar amma babu haƙiƙanin yaƙini na gaskiya da shi. Haka kuma a yau Musulunci ya taka rawa wajen kawar da wasu bukukuwan gargajiya musamman da yake shi ma ya zo da irin nasa bukukuwan da yake tafiya da su.
Alal haƙiƙa bukukuwan buɗar daji da na shan kabewa a yanzu ba kasafai ake yin su ba domin wayewan kai da Musulunci ya yi wa al’ummar Hausawa mafi yawa a cikin ƙasar in dai har mutane sun karɓi Musulunci to sukan yi watsi da shi domin akwai wanda Musulunci ya zo da shi kuma ya tanada musu irinsu bukin sallah, bukin aure, maulidi da sauransu masu tarin yawa.
Saboda haka bukukuwan a yau ba su da wani tasiri mai ƙarfi wajen aiwatar da su domin samun wayewar kayi da kuma tasirin zamananci da kuma na addini.

Naɗewa
Wannan nazari ya cimma manufar na ƙoƙarin bayyana yadda ake gudanar da al’adun bukin buɗar daji da na shan kabewa wajen yadda ake aiwatar da su da kuma dalilin yin su, da kuma nuna bambancinsu ta wata fuskar. Haka kuma, mun ji su waye ke aiwatar da bukukuwan da kuma loakcin da ake aiwatar da bukukuwan da kuma ranar da ake aiwatar da bukukuwan da dai sauran muhimman abubuwan da dama da aka ji.
Alal haƙiƙa waɗanann al’adu za su yi wuyar mutuwa matuƙar masu yin ta ba su karɓi addinin Musulunci ba. Haka kuma akwai buƙatar malamai masana addinin Musulunci su yi himma su kuma ƙara ƙwazo a kan wanda suke yi wajen yin kira da kuma faɗakarwa tare da tsoratarwa ga masu aikata wannan al’ada da makamantansu, wajen daƙilewan aiwatar da waɗannan al’adu a doron ƙasa.

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.