Hausa is a name of
language by which a group of peoples who shared common beliefs and cultures are
known in Nigeria. The Hausa population resides mostly in the northern part of
Nigeria and the southern part of Niger, and they are predominantly Muslims. Whatsapp
is a social media platform that is shaping or affecting the lives of African
citizens. Today, most people’s attitudes, decisions, dress codes, communication
skills are in a way affected by WhatsApp messaging. They sleep very late and
put their body health at risk. In Hausa society, the young ones have been misusing
WhatsApp social media in such a way that affects their moral off-bring trained
by their parents. In this view, this article titled “Whatsapp Social Media: Its Negative Impact to the Morality of Young Ones in Hausa Society” attempts to
highlight some of the negative effects of misusing WhatsApp social media in
deteriorating good morality of young ones and Hausa society at large.
Shafin Zumunta Na Was’af (Whatsapp):
Tasirinsa Ga Lalacewar
Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa
Dr. Musa Shehu
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto,
Nigeria
07031319454
Dr. Rabi’u Aliyu Rambo
Department of Nigerian Languages
Usmanu Ɗanfodiyo University, Sakoto,
Nigeria
08140736435
1.0 Gabatarwa
A duniyar da muke ciki a
yau, tana ƙara tsukewa da dunƙulewa wuri ɗaya sakamakon kafar sadarwa na
intanet wadda ita ce ta samar da shafin zumunta na Was’af. A yau cikin ‘yan daƙiƙoƙi kaɗan ana gudanar da
hulɗa tsakanin mutane ko tsakanin ƙasashe a kowane yanki na duniya. To sai dai
kuma, duk da irin wannan ci gaba da shafin na Was’af ke bayarwa a rayuwarmu ta
yau, idan aka juya ta wani ɓangare za a ga ya yi tasiri ainun ga gurɓata
rayuwar Hausawa musamman matasa daga cikinsu. Manufar wannan takarda dai shi ne
fito da mawuyacin halin da matasan Sakkwato suka faɗa na lalacewar tarbiyya
sakamakon amfani da shafin zumunta na Was’af wajen gudanar da mu’amaloli ko
ayyukan assha. Wannan shafi ya yi tasiri ƙwarai wajen kawo ci baya da ƙoƙarin
ruguza tarbiyyar matasa wanda ke da haɗarin gaske, domin kuwa matasa su ne ƙashin
bayan kowace al’umma. idan matasa a
cikin al’umma suka lalace, al’umma na iya rushewa. Irin lalacin da ke gudana
tsakanin matasan Sakkwato maza da mata a shafin zumunta na Was’af sai dai
addu’a.
2.0 Ma’anar Tarbiyya
Tarbiyya
kalma ce ta Larabci da ke da fuska biyu. Fuska ta farko tana nufin reno kamar
wadda ake yi wa jarirai. Fuska ta biyu kuwa, za a iya ba da ma’anarta da cewa,
wata hanya ce ta kyautata rayuwar ɗan Adam da shiryar da shi ya zuwa halaye da ɗabi’u
masu kyau da nagarta. Ta yin haka zai sa ya tashi da ƙima da kwarjini da ganin
mutuncin abokan zamansa, ya riƙa ba kowa haƙƙinsa gwargwadon hali.[1]
A ma’ana ta ƙamusun Hausa (2006:428) kuwa, tarbiyya ita ce koyar da hali
nagari. Don haka ana iya cewa, tarbiyya ita ce aza wani mutum bisa wata hanya
da zai koyi wani abu wanda zai amfani rayuwarsa da sauran jama’ar da yake
rayuwa a cikinta. Saboda haka, ana iya kallon tarbiyya ta yadda za ta iya ƙunsar
waɗannan abubuwa:
● Koyar da ladabi
da biyayya da ɗa’a da sanin ya kamata.
● Faɗakarwa game
da abokan zaman tare.
● Gargaɗi ga riƙe
halayen kirki da gaskiya da kunya da haƙuri da sauransu.
● Koyar da ladabin
zance da kyautata sutura don ta kasance daidai da al’adar al’umma.
● Tsara rayuwar
mutum ta yadda zai sami damar amfanuwar al’ummarsa.
● Kyautata
kyawawan al’adun al’umma da inganta su tare kuma da bayyana munanan al’adu
domin a guje su.
● Kyautata hankalin
mutum don samun rayuwa tagari.
● Kawar da kai ga
abin mutane da kare ɗiyauci da riƙon amana.
3.0 Dabarun Tarbiyyar Hausawa
Hausawa
al’umma ce da suka sami kyakkyawar tsarin rayuwa dangane da tarbiyya tun kafin
saduwarsu da baƙin al’ummu. Haka kuma a koyaushe sukan yi ƙoƙarin kare
tarbiyyarsu ta kowane hali a yayin da baƙuwar
al’umma ta shigo su musamman idan tarbiyyar baƙin ta sha bamban da tasu.
Don haka ne ma sukan bi hanyoyi iri daban-daban domin ganin ‘ya’yansu sun tashi
da halaye abin koyi ga sauran jama’a. Daga cikin hanyoyin akwai tatsuniya wadda
ta kasance makaranta ta farko ta tarbiyyantar da yaran Hausawa. Sai kuma camfi
da wasannin kwaikwayo da makamantansu. Akan yi ƙoƙarin karantar da su abubuwa
da dama na gari da suka haɗa da gaskiya da riƙon amana da jarunta da tausayi da
ƙarfin hali da ladabi da biyayya da girmama na gaba da sanin ya kamata da
ire-irensu da dama. A taƙaice ana iya kallon tarbiyyar Hausawa ta gargajiya
dangane da waɗannan abubuwa da ta ƙunsa :
Ladabi Da
Biyayya: Ladabi da biyayya manyan qusoshi ne a cikin tarbiyyar
Hausawa.Wato muhimman halaye ne da Bahaushe yake so ya ga ana yi. Girmama na gaba
da kyautata wa na baya su ne halayen da ake kira ladabi da biyayya. (Alhassan
da wasu 1982). A kullum burin iyaye ba ta wuce ta ganin ‘ya’yansu sun girma
cikin halaye kyawawa masu nagarta, don haka suke koya musu yin ladabi da
biyayya ga iyaye da ma na gaba gare su. Sukan koya musu ladabin magana wanda ya
shafi koya musu tausasa murya lokacin magana da babba, kuma kar a tsura masa
ido da kallo kamar yadda tumaki suke yi. Haka ma ba a gai da iyaye ko magabata
a tsaye sai an duƙa musamman idan suna zaune. Ba a ƙetare umarnin iyaye ko ba
daɗi, sai dai a daure a aikata yadda suka buƙata.
Kunya: A magana,
kunya wata kalma ce ko kalmomi da ake furtawa masu nauyi ga al’adar rayuwa da
zamantakewa da mutuncin ɗan Adam, kasancewarsa mutum irin mutane. Ta fuskar
aiki kuwa, kunya wani aiki ne da ake aikatawa da gaɓoɓi wanda al’ada ke hange
da cikas da munin da zai ƙarasar ga ma’abota hankali ga mai aikata aikin domin
tsira da mutuncinsu. (Bunza 2006:249-250). Idan an ce ana jin nauyin mutum ko
ana jin kunyarsa, to ana girmama shi kenan. Wato idan mutum zai aikata wani abu
ya duba abin da zai je ya dawo ta ɓangaren kansa da tsakaninsa da jama’a. Kunya
na hana aikata ayyuka munana domin kare mutunci. Tun fil azal Bahaushe mutum ne
mai ɗabi’ar kunya a rayuwarsa, saboda haka yake ƙoƙarin cusa wannan al’ada ga
‘ya’yansa. Saboda kunya, Bahaushe bai iya kiran sunan ɗansa na fari musamman a ɓangaren
mata. Mace ba ta kiran sunan mijinta kai tsaye sai dai da wani sunan na daban.
Haka ma budurwa tana kunyar a ji saurayinta balle ta faɗi sunansa a gidansu, ko
ta kai wa iyayensa ziyara. Haka dai wannan kyakkyawar al’ada take tafiya a
rayuwar Hausawa.
Kare Ɗiyauci:
Bahaushe bai san karuwanci ba balle masu yin sa.’Ya’yan Hausawa mata tun
suna ƙanana akan yi ƙoƙarin cusa musu al’adar nisantar maza da kuma illar da ke
tattare da kusantar su. Don haka ne ko a wasannin dandali ƙungiyar mata daban
na maza ma daban. Wannan tarbiyyar ba ta tsaya a nan kawai ba, hatta idan aka
yi wa mace aure akan kai ta da wani farin ƙyalle da ake kira bante wanda za ta
fara kwanciya da shi. Ta wannan ƙyalle ne za a gane ta kare ɗiyaucinta ko
akasin haka. Idan aka yi nasara ta kai bante wato ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba
sai ga mijinta na aure, iyayenta kan yi murna da kasancewa masu alfahari da
ita. Idan kuwa aka sami akasin haka, to yarinyar ta bar abin faɗe da zubar da
mutuncin iyayenta. Wannan al’ada ya yi tasiri ainun ga ‘yan mata wajen ganin ba
su zubar da mutuncin gidansu ba, da kuma barin abin faɗe a baya.
Gaskiya Da
Riƙon Amana: Hausawa mutane ne da suke da kyakkyawar tarbiyya da
himmatuwa zuwa ga ɗaukar halaye nagari irin su gaskiya da riƙon amana. Babu
yaudara ko cin amana a rayuwar Hausawa. Wato mutane ne masu karimci da shimfiɗar
fuska wadda aka ce ta fi shimfiɗar tabarma. Duk wanda ya haɗa hulɗa ta
kasuwanci ko na zamantakewa da Hausawa zai tabbatar da cewa Hausawa mutane ne
masu gaskiya. Wannan ne ya samar wa Hausawa kyakkyawar dangantaka ta kasuwanci
tsakaninsu da al’ummomi daban-daban na cikin gida da ma sauran ƙasashen duniya.
Zumunta: Ƙoƙarin
kusantar ‘yan’uwa da abokan arziki da ziyartar su a kai a kai, ita ce zumunta
(Alhassan da wasu 1982). Tarbiyyar Hausawa tana jaddada ziyarce-ziyarce
tsakanin ‘yan’uwa da abokan arziki. A tsarin rayuwar Bahaushe, maƙwabci tamkar ɗan‘uwa
ne, domin idan aka wayi gari akan gaisa kafin kowa ya fita harkarsa. Don haka,
idan wani abin farin ciki ko akasinsa ya samu maƙwabcin mutum, za a zauna a
taya shi murna ko kuma juyayi idan na juyayi ne. Haka ma duk wani abu da ya
samu ‘yan’uwa na murna kamar haihuwa ko aure akan taru domin a sada zumunci
kuma a ƙarfafa shi. Har ta kai ga Bahaushe kan ɗauki ɗansa ya ba ɗan‘uwansa riƙo
domin ƙarfafa zumuntar da ke tsakaninsu.
Mallakar
Sana’a: Al’ummar Hausawa tun asali al’umma ce wadda ta dogara
da kanta wajen samar da hanyoyin tattalin arzikinta. Ta haka ne ya zama a
kowane gidan Bahaushe za ka tarar yana da sana’o’in da yake aiwatarwa. Don
haka, yakan yi ƙoƙarin gina yaransa bisa wannan sana’a domin su girma da ita,
su kuma kauce wa zaman kashe wando da sa ido da yawon gararamba a cikin unguwa.
4.0 Ma’anar Shafin Zumunta na Was’af
Deepa (2015) ya bayyana
ma’anar Was’af a matsayin hanya ta sada zumunta mafi sauƙi wadda ke ba masu
amfani da wayoyin Iphone, Blackberry, Android, Windows, Nokia, Smart Phone
damar tura saƙonnin hotuna da bidiyo da saƙonnin murya da saƙonnin rubutu a
cikin sauƙi kuma kyauta. Ina (2016) yana cewa, shafin Was’af hanya ce mafi sauƙi
na tura saƙo ga masu amfani da wayar Smart phones wadda ke amfani da Intanet don
tura rubutattun saƙonni da hotuna da bidiyo da saƙonnin murya zuwa ga sauran
masu amfani da ita.
5.0 Tarihin Samuwar Shafin Zumunta na Was’af
A cikin shekarar 2009 ne
wasu matasa biyu, Brain Acton da Jan Koun waɗanda tsafaffin ma’aikatan kamfanin
Yahoo ne suka ƙirƙira masarrafar da a halin yanzu ta rikiɗe zuwa Was’af don
aiwatar da sadarwar LAN (Local Area Network). A watan Nuwambar shekarar ne na
2009 Brain ya gayyaci wasu abokansa biyar, su ma tsofaffin ma’aikatan Yahoo su
saka jari don ciyar masarrafar gaba. Waɗannan abokan sun saka jarin dalar
Amurka 250,000. A cikin shekarar ne aka fitar da zubin farko na masarrafar
Was’af wadda ke aiki a wayar Iphone ta hanyar App Store na kamfanin Apple. Ana
shiga shekarar 2010 sai Jan Koun ya gayyaci wani abokinsa mai suna Chris
Peiffer, masani a kan masarrafar kwamfuta ya shigo cikinsu, kuma shi ne ya gina
manhajar Was’af da ke aiki a wayar Blackberry.
Daga nan aka ci gaba da samar da
nau’ukan manhajar Was’af a wasu wayoyi, irin su Nokia da Android da sauransu. A
cikin shekarar 2013, kamfanin yana ɗauke da ma’aikata hamsin da biyar, kuma a
cikin shekarar na 2013 ne kamfanin Facebook ya saye manhajar na Was’af da
kamfanin gaba ɗaya a kuɗi dalar Amurka Biliyan 19. Kamfanin na Was’af ya sanar
da cewa akwai mutane masu amfani da manhajar sama da mutum miliyan 400 a kowane
wata. Akwai manhajar Was’af nau’in wayar salula ta Android wadda ake samu a
cibiyar “Play Store” (Google Store) kaɗai. Akwai nau’in IOS da ake samu a
cibiyar “App Store” kawai. Akwai nau’in “Blackberry” da ake samu a cibiyar “App
World”. Sannan akwai nau’in Windows Phone da ake samu a cibiyar “Store”. Kowane
daga cikin waɗannan yana da nau’in babbar manhajar wayar da aka gina shi a kai,
idan an saka masa abin da ba nasa ba, wayar ba za ta iya lodawa ba.
6.0 Ire-Iren Saƙonnin da ake Turawa a Shafin Zumunta
na Was’af
Saƙonnin
da ake iya turawa a shafin Was’af suna da yawa, ga su kamar haka:
a)
Mashaƙatar
Rubutu (Text Messge): A wannan mashaƙata mutum yana da damar tura
rubutaccen saƙo ne kawai a shafin na Was’af, waɗanda suka haɗa da labarai da saƙonnin
gayyata da sanarwa da duk wani saƙo da ake so a isar amma a rubuce.
b)
Mashaƙatar Sautin Magana (Voice Note): A
wannan mashaƙata ana tura saƙonnin sautin magana ne a shafin na Was’af, kuma za
a iya ɗaukar saƙon da ake so a tura kai tsaye, ko kuma a ɗauko daga wata folda
(folder) a tura.
c) Mashaƙatar
Bidiyo (Video Message): Wannan mashaƙata ce da ke ba masu amfani da shafin
Was’af damar tura saƙonnin da ake iya kallo a cikin bidiyo kai tsaye domin isar
da wani saƙo. A cikin wannan bidiyo, mutum zai kalli yadda abu yake a aikace
tare da jin sautin maganar bidiyon.
d) Mashaƙatar
Hotuna (Picture Message): Wannan ma mashaƙata ce da ake iya amfani da shi a
shafin Was’af wanda ke ba da damar tura saƙonni a cikin hotuna waɗanda ke ɗauke
da wani saƙo, duk da cewa hotuna ba su magana, ba ya hana a fahimci saƙon da
suke ɗauke da shi.
e) Mashaƙatar
Kiran Was’af (Whatsapp Call): Wannan hanya ce da masu amfani da shafin
Was’af kaɗai ke iya amfani da wannan tsari don kiran ‘yan’uwa da abokan arziki
don a ji muryan juna don isar da saƙon da ake buƙata cikin sauƙi. Wannan kira
na Was’af ba ya amfani da katin waya, yana amfani ne da data kuma a cikin sauƙi.
Sai dai abin lura a irin waɗannan saƙonni
shi ne, saƙonnin da ake turawa a wannan shafi na Was’af akan samu masu kyau da
alfanu, akan kuma samu marasa kyau waɗanda ke kawo cikas ga tarbiyya musamman
ga matasa.
7.0 Dalilan Amfani da Shafin Zumunta na Was’af
ga Matasa
A bayyane yake cewa yawancin
matasa na amfanin da shafin zumunta na Was’af ne domin kasancewa kusa da
‘yan’uwa da abokan arziki. Wasu kuma na amfani da shafin ne don tallata
kasuwancinsu. To sai dai kuma, Hausawa na cewa, “kowane allazi da nasa amanu”,
wannan ya sa wasu matasa amfani da shafin ta gurɓatacciyar hanya na yaɗa fasadi
a shafin. Ga ra’ayoyin wasu matasa da aka tattauna da su game da shafin na
Was’af:
Kasuwanci:
Wasu matasa sun bayyana kasuwanci a matsayin dalilinsu na yawaita amfani da
shafin zumunta na Was’af.
Shaƙatawa:
Wasu matasan suna da ra’ayin yawaita amfani da shafin na Was’af saboda samun
natsuwa da ɗauke kewa.
Hulɗa da Jama’a:
Wasu matasa sun bayyana ra’ayinsu da cewa, suna amfani shafin Was’af ne saboda su
samu damar hulɗa da jama’a ‘yan’uwa da abokan arziki.
Karatu:
Wasu matasa na amfani da shafin Was’af ne domin domin su ƙirƙira rukunin da za
su riƙa tattaunawa a kan abin da ya shafi karatunsu da sauran saƙonni.
Soyayya:
Wasu matasa sun bayyana cewa, suna amfani da shafin Was’af ne don tattaunawa da
ƙarfafa soyayyarsu ga masoyansu a cikin sauƙi ba tare da wahala ba.
Rayuwa:
Dalilin wasu matasa na amfani da shafin zumunta na Was’af shi ne, don su riƙa
haɗuwa a ƙungiya ɗaya (group) domin tattaunawa da mahawara a kan kallon ƙwallon
ƙafa ko wani abu da suke son fayyacewa tsakaninsu musamman na masha’a.
Labarai:
Wasu matasa sun nuna cewa, suna amfani da shafin ne domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu
a kan abubuwan da ke faruwa a gida Nijeriya da ma duniya baki ɗaya. Haka ma
idan an samu labarin gurbin neman aiki akan yaɗa ga abokai da ‘yan’uwa domin su
kowa ya jaraba sa’arsa.
Samun Saƙo da Turawa
Cikin Gaggawa: Dalilin wasu matasa na mayar da hankali
ga amfani da shafin Was’af fiye da sauran shafuka shi ne, samun saƙo da tura saƙo
cikin sauri ba tare da ɓata lokaci ba.
Nishaɗi da ban Dariya:
Wasu matasan suna da ra’ayin yawaita amfani da shafin Was’af don nishaɗi da ban
dariya kawai, ta hanyar saƙonnin da ake turawa a cikin ƙungiya (group).
8.0 Abubuwan da ke Ɓata Tarbiyya a Shafin Zumunta
na Was’af
Ba shakka, shafin zumunta
na Was’af yana ba da gagarumar gudummawa ga ɓata tarbiyyar matasa a yau, domin shafi
ne mai matuƙar amfani idan za a yi amfani da shi ta hanyar da ta dace. To sai
dai kuma, a yau matasa sun mayar da shafin dandalin yaɗa fasadi domin rushe kyakkyawar
tarbiyyar da aka gina su a kanta. Wasu matasan suna amfani da mashaƙatar bidiyo
su riƙa tura bidiyon batsa da ke gudana tsakanin mace da namiji. Wasu kuma
hotunan batsa suke bajewa a shafin. Yayin da wasu ke aika saƙonnin rubutun
batsa, ko kuma batsar a cikin sautin murya. Ga dai bayanin illolin shafin na
Was’af daki-daki:
8.1 Mashaƙatar Bidiyo (Video Message)
A wannan mashaƙata na
bidiyo, ɓara-gurbin matasa kan saka bidiyon lalata da ke gudana tsakanin mace
da namiji, inda har sunaye na musamman suke yi wa irin waɗannan bidiyo waɗanda
ke zagayawa a shafin zumunta na Was’af daga lokaci zuwa lokaci. Idan aka ɗauki
lokaci ana kallon wani bidiyo, sai kuma a sake fitar da wani sabo, an gama da
wancan, ya zama tsohon yayi. Ga wasu nau’ukan bidiyon batsa da ke zagayawa a
shafin:
Ɗan Daudu: Saƙon
Ɗan Daudu da ke zagayawa a shafin zumunta na Was’af yana cikin bidiyo ne.
Tsawon lokacin da bidiyon kan ɗauka minti huɗu ne, wanda ke ɗauke da hoton wani
mutum da ake kira Nasiru. Nasiru yana sanye ne da tufafin mata, ɗankwali da
hijabi da dogon wando. Nasiru ya sha kwalliya na hoda da kwalli da jan baki. A
cikin hoton bidiyon, akwai jami’an tsaro na ‘Yansanda sun saka wa Nasiru Ankwa
a hannunsa biyu ana yi masa intabiyu kan yaushe ya shiga sana’ar Ɗan Daudu.
Jamai’an tsaron suna umurtar Nasiru da ya kwaɓe hijabin da ya saka don suga ƙirjinsa
da sauran sassan jikinsa, suna tona asirin tsiraicinsa suna ɗauka a wayoyinsu.
Wannan bidiyon ya ɗauki lokaci yana zagayawa a shafin was’af.
Malam Rabi’u Jaki: Saƙon
Malam Rabi’u yana cikin sigar bidiyo ne, kuma yana ɗaukar tsawon minti takwas
ana kallonsa. Wannan bidiyo yana ɗauke ne da hoton wani mutum mai suna Rabi’u
(ga alama malamin makarantar ‘yan mata ne). An nuna malam Rabi’u yana tafiya
bayan wata ɗaliba sun nufi hanyar makewayin makaranta, inda aka nuna malam Rabi’u
ya tuɓe wa ɗalibar hijabi da wandonta yana aikata masha’a ƙiri-ƙiri.
Taimaka mini Fanka: Wannan
ma wani bidiyo ne da ke zagayawa a shafin zumunta na Was’af da ke ɗaukar minti
biyu ana kallo. Hoto ne amma a cikin bidiyo ana nuna wani mutum a kwance tsirara.
A wurin da yake kwance akwai fanka irin ta tsakiyar ɗaki saman kansa tana
juyawa, matar da yake masha’a da ita a tsirara ta riƙe fankar suna aikata
fasadi, fankar na taimaka wa matar wajen fasadinsu.
Wada da Jesika: Wannan
wani bidiyo ne mai tsawon minti shida, wanda ke nuna yadda wata mata mai suna
Jesika ta duƙa ma wani Wada, shi kuma Wadan ya hau saman kujera yana fasadi da
ita.
Ka Fi Zuma Zaƙi:
Shi ma wannan bidiyo yana ɗaukar tsawon minti bakwai. A bidiyon an nuna wani
mutum tsirara tare da wata mace tana tsotsan kayansa, daga bisani ya kwantar da
ita ya ɗaga ƙafafuwanta sama suka ci gaba da fasadi.
8.2 Mashaƙatar Hotuna (Picture Message)
A wannan mashaƙatar ma
akwai hotuna iri-iri da ke yawo a shafin zumunta na Was’af tsakanin matasa da
aka yi wa suna iri-iri. Ga wasu daga cikinsu:
Musayar Al’aura a cikin
Hotuna: Wannan yana faruwa ne tskanin matasa maza
da mata a shafin zumunta na Was’af. Irin waɗannan saƙonni da matasa ke musaya
tsakaninsu yakan faru yayin da masoya suka shaƙu da juna sosai, sai namiji ya
buƙaci mace ta turo masa wani sashe na jikinta kamar mamanta ko al’auranta. Nan
take sai ta ɗauki hoton da wayarta ta tura masa, shi ma haka zai ɗauki hoton
nasa al’auran ya tura mata.
Allah Ya Kiyashe mu:
Wannan wani saƙo ne a cikin sigar hoto da matasa ke yawo da shi a shafin
zumunta na Was’af, wanda ke bayyana yadda wasu mutane ke ɓata ƙananan yara. A
cikin hoton za a ga wani ƙaton mutum ya kwantar da wata ‘yar jaririya yana ƙoƙarin
saka gabansa a al’auranta.
Mummunan Rabo (Night
Mare): Shi ma wannan hoto ne mai ɗauke da sharhi
a gefensa. Saƙon da aka liƙa a hoton yana bayyana wani mutum ne mai nakasa
wanda ya ƙware a soyayya amma ta fuskar fasadi. Abin da ya fi bayyana a wannan
hoto shi ne fasadi tsakanin mace da namiji.
A Riƙa yin Sitayal
Iri-iri: Wannan wani nau’in saƙo ne mai ɗauke da
hotuna kusan arba’in da tara, kuma kowane hoto yana ɗauke da mace da namiji tsirara
da sifar suna fasadi. Haka ma, kowane hoto da irin sitayal ɗin fasadi da aka yi
a cikinsa.
Karas ko wani Dodo:
Wannan hoto ne da ke zagayawa a shafin Was’af musamman na ‘yan mata suna
tsokanar juna kan yanayin mazakutar namiji. Mafi akasari idan aka aika wannan
saƙo ana raka shi da tambayar “shin ko wadda aka aika wa saƙon tana iya maneji
da namiji mai irin wannan yanayi”.
Madarar kawobel
(cowbell): Shi ma wannan hoton wata mace ce wadda
aka ce tana tallata kanta a Intanet da sunan tana neman abokin da za ta burge
domin ƙulla mugunyar hulɗa.
Manya:
Wannan hoton mazakutar namiji ne aka ɗauka. Hoton ya nuna an sanya wa mazakutar
ankwa tare da maƙulli an rufe. Bayanin da ya biyo hoton shi ne, wata mata ce ta
yi wa mazakutar maigidanta haka nan a dalilin ya gaya mata zai tafi wani taro
amma ba da ita zai tafi ba. Kan haka, sai ta nemi maƙulli ta ƙulle mazakutarsa
da nufin kar ya nemi mata a can sai ya dawo gida.
8.3 Mashaƙatar Sautin Murya (Voice Note)
Waɗansu nau’o’in saƙonni da ke
zagayawa a shafin zumunta na Was’af tsakanin matasa a cikin sigar murya kawai
suke. Ana aikawa da su ne domin a koyar da matasa wani mugun ilimi na fitsara
da lalaci. Irin waɗannan saƙonni ana samunsu a cikin waƙa, kuma suna ƙumshe da
kalmomin zagi da batsa masu gurɓata tarbiyya. Daga cikin irn waɗannan waƙoƙi
akwai waƙar “sa mata” da “kuɗin anko” da “matan aure” da “kazar mata” da
sauransu.
8.4 Mashaƙatar Rubutu (Text Message)
A cikin wannan mashaƙata
ta rubutu, ana samun saƙonni masu jigon ƙarya da batsa da koyar da fasadi a
shafin na Was’af. Daga cikin ire-iren waɗanna saƙonni sun haɗa da:
Daren Amarcin Saude:
Saƙo ne da ke zagayawa a shafin zumunta na Was’af tsakanin matasa maza da mata inda
ake bayanin wata amarya ce bayan daren amarci da ita da angonta, da safe ta
samo mai baro ta ɗauko talabijin da rediyo da DVD ta aika gidansu a ba mamanta.
Da yaro ya kai saƙo sai mamar ta yi mamaki ta ce “yarinya daga tarewa gidan
miji sai ki kwaso kayan mijinki ki kawo mini”. Daga nan ta aika aka kira ta don
ta ji abin da ke faruwa, sai ɗiyar (Saude) ta ce “Ai jiya ne cikin dare ya ce
ya ba ni talabijin, anjima kaɗan ya ce ya ba ni rediyo, anjima kaɗan ya sake ba
ni DVD, shi ya sa na ce bari in kawo muku ku ɗan more rayuwarku”, sai uwar ta
ce “zo ki kwashi kayan nan ki mayar, babanki sau shida yana ba ni gidan nan”.
Sauran ire-iren wannan saƙonni sun haɗa da Fatino
da Ustaz da Shan Ayabar Laure da ‘Yammata sai an haɗa da Ƙarya da Yaro da Mahaifiyarsa da sauransu waɗanda
matasa ke yawan aikawa a tsakaninsu, dukkan waɗannan saƙonni ne da suka shafi
koyar da fasadi da ɓata tarbiyya.
9.0 Illolin Shafin Zumunta na Was’af a Rayuwar
Hausawa a Yau
Da ma wasu mutane suna da
ra’ayin cewa, duk wani abu mai amfani ba zai rasa illa ba. Shafin zumunta na
Was’af shafi ne mai matuƙar amfani a rayuwar al’umma, to sai dai kuma a yau
shafin ya zama dandalin sheƙe ayar matasa wanda ke yi musu jagora ga lalata
tarbiyyarsu da ma rayuwarsu baki ɗaya. Daga cikin illolin da ake samu a wannan
shafi na Was’af sun haɗa da:
9.1 Koyar da Fasiƙanci
Daga cikin illolin da ake samu a
wannan shafi na Was’af akwai koyar da matasa maza da mata fasiƙanci a
tsakaninsu, musamman idan aka yi la’akari da irin saƙonnin bidiyo da hotuna da
rubutu da murya irin na batsa da ke yawo a tsakaninsu. Ta wannan hanya ne matasan
kan yi ƙoƙarin aiwatar da abin da suka ji ko suka gani na batsa a zahirin
rayuwa musamman a mashaƙatar biiyo da suke ganin yadda ake aiwatar da fasadin a
zahiri.
9.2 Ruguza Kyawawan Al’adun Hausawa
Wata illar da shafin zumunta na
Was’af ke ɗauke da ita shi ne, ruguza kyawawan al’au da ɗabi’un da aka sani ga
Hausawa kamar al’adar kunya, inda za ka iske ba kunya ba tsoron Allah yarinya
ko saurayi za su ɗauki hoton wani sashe na jikinsu musamman al’aura suna tura
wa junansu suna kallo a duk lokacin da suka buƙaci haka. Haka ma, akan riƙa
yawo da ƙaryayyaki da rashin girma ma iyaye da sauransu.
9.3 Haɗuwa da Abokan Banza
Yana daga cikin illar shafin zumunta
na Was’af haɗuwa da abokai barkatai marasa kyakkyawan tarbiyya, masu miyagun
halaye waɗanda za su iya gurɓata tarbiyyar mai tarbiyya da iyaye suka gina
‘ya’yansu a kai.
9.4 Ɓata Lokaci
Lokaci wani abu ne mai muhimmanci a
rayuwar ɗan Adam, omin wani abu ne mai tsada a rayuwarmu. Sau da yawa za ka
tarar idan mutum ya shi sashen shafin zumunta na Was’af ya yi zurfi a ciki sai
ya manta da duk wasu ayyuka nasa masu muhimmanci musamman ma ibadarsa (Sallah),
yana can wurin kallon batsa da soyayya mara amfani. Sau da yawa za ka iske yara
sun tafi makaranta malami na koyarwa a cikin aji amma wasu yaran na can sun
mayar da hankalinsu wajen waya ana ta catin (charting) a maimakon mayar da
hankali ga abin da ya kawo su.
10.0 Kammalawa
Duk al’ummar da ke buƙatar ci gaban
rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, kamata ya yi idan wasu baƙin al’adu da ɗabi’u
suka shigo cikinta, ta tsaya ta yi nazarinsu da ƙwaƙwalwar basira ta ɗauki waɗanda
suka dace da koyarwar al’ada da addininta, ta yi watsi da na watsarwa, ba ta yi
musu kwasan karan mahaukaciya ba. A tunanina, kamata ya yi mu sake bitar
dabarun tarbiyyar da muke amfani da su a can baya kamar su gaskiya da riƙon
amana da kunya da sauransu, a sake ƙarfafa su a zukatan al’ummarmu, sa’annan a ɗaura
ɗamara da faɗakarwa a kan amfanoninsu da illolin da ke tattare da yin watsi da
su da kuma rungumar al’adun da ba su dace da rayuwarmu ba. Don haka, tilas mu
tashi tsaye a kan waɗannan matsaloli don kauce wa ci gaba da lalacewar rayuwar
matasanmu wanda zai iya zama sanadiyyar rushewar al’ummarmu baki ɗaya. Saboda
haka ne aka shirya wannan takarda don ta falkar da al’ummar Hausawa a kan
mawuyacin halin da tarbiyyarsu ta faɗa da kuma hanyoyin da ake tunanin za su
iya shawo kan al’amarin ko rage masa kaifi ainun.
[1]
Gusau, S.M. (1999) “Tarbiyya a Idon Bahaushe”, a cikin Journal of
Hausa Studies, Jami’ar Bayero, Jano.
Na ji dadin takardan nan. Na gode.
ReplyDelete