Sana’a ita ce samuwar hanya ta neman abinci da ɗan Adam zai yi domin neman halaliyarsa. Fatima Bagudo na ruwaito a cikin kundinta na MA cewa, Gusau da Yahaya (1991) sun bayyana sana’a da “Amfani da azanci da hikinma ne don sarrafa albarkatu da ni’imomi da ɗan Adam ya mallaka da niyyar biyan buƙatun yau da kullum. Shi muka Rabi’u (200) yana bayyana sana’a da “duk wani aiki da za a yi don gudanar da wani abu da za a musaya a tsakanin wani da wani don samun masarufi...


Matsayin Sana’o’in Hausawa a Yau

Haruna Umar Maikwari
07031280554

Gabatarwa
          Al’ada ta kasance abu ce mai rai, tana samuwa ta rayu, ta yaɗu ta kuma bunƙasa a wasu lokuta tana kuma iya mutuwa. Sana’o’in Hausawa sun samu kansu a cikin wannan tsari. Idan muka duba za mu ga cewa sana’o’in Hausawa sun ɗauki irin wannan salo, sun samu kuma sun yaɗu sun samu bunƙasa wasu kuma sun sauya, yayin da wasu kuma fara mutuwa (salwanta). A wannan jingar za a kalli sana’o’in Hausawa na gargajiya da na zamani, a kuma fito da sana’o’in da suka kwanta dama da waɗanda suka suma da waɗanda ake damawa da su, kana mu zo da waɗanda suka tsira. Amma dai kafin nan za a zo da ma’anar al’ada da kasuwanci kamar haka.

Al’ada
          Abin da ake nufi da al’ada shi ne, hanyoyin gudanar da rayuwar ɗan Adam ta yau da kullun. Al’ada abu ce, da ta shafi rayuwa tun ranar gini, tun ranar zane. A cewar Bunza, (2006:7) ‘’Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan’Adam ce tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa.” Shi kuwa Ɗangambo, (1987:5) cewa ya yi: “Al’ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.” Gusau (2010:2) ya bayyana al’ada a matsayin “Tafarki wanda wata al’umma take rayuwa a cikinsa dangane da yanayin abinci da tufafi da muhalli da rayuwar aure da haihuwa da mutuwa da wasu hulɗoɗin rayuwa kamar maƙwabta da sana’o’i da kasuwanci da shugabanci da bukukuwa da sauran abubuwa waɗanda suke da alaƙa da haka”. Wani masani mai suna Ibrahim (1982:iii) yana ganin “al’ada” tana nufin: “abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya”. Ta haka al’ada ta shafi yanayin rayuwar al’umma da harkokin da take gudanarwa na yau da kullum. A taƙaice, al’ada wata abu ce wadda ta shafi abin da rai ya riga ya saba da aiwatar da shi har ya zamar masa jiki.
       
Ma’anar Sana’a
          Sana’a ita ce samuwar hanya ta neman abinci da ɗan Adam zai yi domin neman halaliyarsa. Fatima Bagudo na ruwaito a cikin kundinta na MA cewa, Gusau da Yahaya (1991) sun bayyana sana’a da “Amfani da azanci da hikinma ne don sarrafa albarkatu da ni’imomi da ɗan Adam ya mallaka da niyyar biyan buƙatun yau da kullum. Shi muka Rabi’u (200) yana bayyana sana’a da “duk wani aiki da za a yi don gudanar da wani abu da za a musaya a tsakanin wani da wani don samun masarufi. Haka nan a ganinsa sana’a na iya shafuwar harkar kasuwanci wato saye da sayarwa”. A ra’ayin Garba C (1900) “sana’an ginshiƙin rayuwa ce, da kumu tattalin arzikin yau da kullum na Hausawa. tana daga cikin hanyoyin gane martabar mutum da ƙasaitarsa”.
                   Shi kuwa Abdulƙadir D (2004) yana ganin sana’a da “hanya ce ta sarrafa ɗimbin albarkatun ƙasa da dabbobi da ke kewaye da ɗan Adam da nufin biyan buƙata.
           Sana’a kan iya zama ta aikin ƙarfi, wato neman halaliya ta yin aikin mai wahala kamar su noma, gini, ƙira, jima, kaɗi, ɗinki da sauran su. Ta kan iya zama ta hanyar jiya, wato biyar ta koma goma wato aikin gwamnati a taƙaice dai duk wani aikin da ɗan Adam zai yi ta zama sanaɗiyar samuwar kuɗi a gare shi. Duk abin da mutum zai yi ya samu wani abin da zai gudanar da rayuwarsa da ta iyalinsa kuma jama’a suka san shi da ita wannan shi ake kira sana’a.
          Sana’a dai ita ce saye da sayarwa ko aikata wani akin da zai samar wa mutum riba da zai iya ya kore wa bakinsa ƙuda. Idan mutum ya samu wata hanya ta samun kuɗi ko samun abinci ko biyan wasu buƙatu kuma jama’ar da ke kusa da shi suka sani cewa wannan abu da wane yake yi yana samar masa da abin da zai iya yin lalurorinsa wannan shi ne sana’a.


Nau’o’in Sana’a
          Nau’o’in sana’a wani abu ne mai mahimmanci domin yakan fitar da irin ressan da sana’a take ɗauke da su. Bisa ga irin abubuwan da ake amfani da su a lokacin da ake aiwatar da ita, muna iya cewa, sana’a tana da ressa masu tarin yawa da suka haɗa da: Noma, ƙira, Jima, kaɗi, ɗinki, saƙa, sassaƙa, fawa, sarkanci, wanzanci, da dai sauransu. Ba za a iya cewa ga iya adadin nau’o’in sana’a ba. Wasu suna saye da sayarwa, wasu bankwai suke yi wasu tireda, wasu dako, wasu lodi da saukale, wasu lebaranci sukai wasu kanikanci suke yi kai abin da yawa mutuwa ta shiga kasuwa.
          Wannan jinga ba bayanin su za a yi gaba ɗaya ba sai da za a ɗauki wasu daga ciki kaɗan domin a ɗan yi bayani ya kuma zama misali wanda zai gamsar.
Sana’ar Gini
          Ita wannnan sana’a, sana’a ce wadda Hausawa ke yi. A da can lokacin da ba a san salon a yi gina da siminti ba a ƙasar Hausawa, Hausawa suna yin gini da yunɓu (laka) suna samun yunɓu su kwaɓa shi su yi tubali su bari ya bushe ya yi ƙarfi sai su yi gina da shi. Idan kana buƙatar yin gini na gida ko ɗaki ko rumbu (ruhewa) ko dai wani abu da ya ƙunshi gini, sai ka nemo magina. Su dai magina wannan sana’ar galibi ita ce sana’arsu. Suna yin gini da yunɓun da aka kwaɓa shi tare da hakin shuci (ramno) wannan hakin ana saka shi a cikin gini domin ginar ta ƙara ƙwari.
Sana’ar Kaɗi
        Ita wannan sana’a, sana’a ce da Hausawa suke yi ta hanyar sarrafa auduga (kaɗa) su mayar da ita zare don yin ɗinki. Hausawa kan samu auduga su gyara ta su nemi wani abu da ake kira “mazari” shi mazari kamar karen tsintsiya yake, amma ya fi karen tsintsiya ƙwari, daga ƙasa gare shi akwai wani ɗan ƙololo da ake sakawa mai nauyi wanda zai taimakawa mazarin juyawa idan aka murza shi. Shi dai mazarin nan ana saka masa auduga a ɗan lauya ta kaɗan gare shi sai a ɗebi ɗan habɗi kaɗan a murza a ƙafa sai a aza wannan mazarin wanda aka saka ma auduga sai a murza sosai, idan aka murza sai ya riƙa juyawa yana jan audugar yana naɗe ta tana komawa kamar zare. Wasu daga cikin Hausawa sun ɗauki wannan a matsayin sana’a kuma sukan je su ɗebo auduga su yi zare da ita masu ɗinki su kuma su zo su saya su yi aikin ɗinki da shi.
Sana’ar Fawa
          Sana’ar Fawa dai sana’a ce ta mahauta, wadda mafi yawan masu yin ta sun gada ne, waɗansu kuma ba su gada ba. (Calɓic Y. Garba 1991)
          Sana’ar fawa wata sana’a ce ta Hausawa, ta gargajiya wadda ake sayen dabba a yanka ta a sayar da namanta, domin miya ko wata buƙata. Ana sarrafa naman ne ta yin balangu, ko a soya ko a yi kilishi ko a dafa ko a yi tsirai ko langaɓu ga jama’a masu buƙata.
          Don haka fawa sana’a ce ta rundanci, wadda ake yanka dabba don a sayar da namanta ga jama’a, haka kuma sana’ar fawa ta ƙunshi tun daga kawo dabba zuwa mahauta, kayar da ita, yankawa da feɗewa da rarrabawar ƙashi da tsoka da sayar da naman ɗanye ko balangu don sayarwa tare da zimmar cin riba.
 Sana’o’in Da Suka Shafi Jinsin Mata
          Akwai sana’o’i da dama da suka shafi jinsin mata waɗanda mata ne kawai ke yinsu ba da maza ba. Wasu kuma idan ka ga maza na yinsu to lallai sai dai ‘yan daudu ko kuma wasu ɗai-ɗaiku. Waɗannan sana’o’in sun haɗa da: Sana’ar Kitso, Sana’ar Koda, Sana’ar Dafe-Dafe, Sana’ar Dawo da dai makamantansu.
          Yanzu bari mu ɗauki ɗaya daga ciki mu ɗan yi tsokaci saboda mu kafa hujja. Misali, Sana’ar Kitso
Wannan sana’a ce da mata ke yi suna samun wani abu. Sukan tanadi wasu kayan aikin sana’ar su kamar mashaci, da  tsinke wanda suke yi tsagar gashi da shi yayin da suke yin kitso.(Tcinke). Matar da take buƙatar a yi mata kitso takan kwance/banye gashin kanta ta wanke ta saka mai irin wanda ta fi son ta yi buƙata da shi sai ta sa a kanta sai ta nufi inda wadda take yin kitso take domin a yi mata wannan kitson irin wanda take buƙata, wasu suka ce a yi masu zanen yawo, wasu kuma sukan yi wibin ko kalaba ko shuku ko kwando, ko dai wani nau’in na daban.
Sana’o’in Da Suka Shafi Jinsin Maza
          Kamar dai abin da muka ambata cewa, akwai sana’o’in da suka shafi jinsin mata to, haka kuma akwai wasu sana’o’in jinsin maza ne suka fi aiwatar da su. Ba wai lallai sai maza ne kawai ke yin su ba, amma mafi yawan sana’o’in maza ne suka fi yin su. Irin waɗannan sana’o’i sun haɗa da: Ƙira, Rini, Jima, Farauta, Noma, Dukanci, Tauri, Dambe, Kokawa, Wanzanci, Sarkanci, Ƙwadago, Sassaƙa, Sodori, Bashirwanci, da dai makamantansu.
          Dukkan waɗannan sana’o’i maza ne suka fi yins u, mata ba su cika yin su ba. Domin samun kafa hujja bari mu ɗan yi bayani taƙaitacce a kan sana’a ɗaya daga cikin waɗannan.
Sana’ar Fawa: Sana’ar Fawa dai sana’a ce ta mahauta, wadda mafi yawan masu yin ta sun gada ne, waɗansu kuma ba su gada ba. (Calɓic Y. Garba 1991)
          Sana’ar fawa wata sana’a ce ta Hausawa, ta gargajiya wadda ake sayen dabba a yanka ta a sayar da namanta, domin miya ko wata buƙata. Ana sarrafa naman ne ta yin balangu, ko a soya ko a yi kilishi ko a dafa ko a yi tsirai ko langaɓu ga jama’a masu buƙata.
          Don haka fawa sana’a ce ta rundanci, wadda ake yanka dabba don a sayar da namanta ga jama’a, haka kuma sana’ar fawa ta ƙunshi tun daga kawo dabbab zuwa mahauta, kayar da ita, yankawa da feɗewa da rarrabawar ƙashi da tsoka da sayar da naman ɗanye ko balangu don sayarwa tare da zimmar cin riba.
Sana’o’in Da Aka Yi Tarayya Tsakanin Maza Da Mata.
          Su waɗannan sana’o’i dai kamar yadda aka ce na tarayya ne to dukkan jinsin biyu suna iya yin su, kuma ba ya zama wani abu. A al’adar Hausawa wasu sana’o’i da suke na mata ne idan aka ga namiji ya shiga yin su, to sai a kama kallonsa da wani abu daban marar kyau, saboda a ganin su ya saɓawa al’adun su. A wasu lokuta kuma har da tsarguwa tana shiga a ciki har ta kai a la’anci mai yin sana’ar ba don sana’ar ba ta yiwuwa ba. Haka abin yake ga sana’o’in da suke na maza ne idan mace ta shiga dumu-dumu a ciki sai ka ga mutane suna kyamarta ko ma su la’ance ta.
          Duk da cewa sana’a da ake yi tana da gurbin da ya dace ta faɗa dangane da jinsin al’umma. Wato kamar sana’o’in da suka danganci jinsin maza da kuma waɗanda suka danganci jinsin mata. Akwai kuma wasu sana’o’in da suke an yi tarayya a wajen yinsu wato maza na yi kuma mata na yi. Irin waɗannan sana’o’in sun haɗa da: Malanta, Kaɗi, Ɗinki, Saƙa, Kiyo, Dillanci da dai sauransu.
          Domin mu samun ɗaure akuyarmu a kan magarya za mu ɗauki ɗaya daga cikin waɗannan mu ɗan yi tsokaci a kai.
Ma’anar Sana’ar Tela.
          Wasu daga cikin masana adabin Hausa sun yi tsokaci dangane da ma’anar sana’ar tela. Ga dai abin da wasu daga cikin su da muka ci karo da yadda suka bayar da ma’anar.
          Alhassan da wasu (1982) ya bayyana ma’anar sana’ar tela a cikin littafinsu mai suna “Zaman Hausawa” cewa suka yi, “Haɗa sawaye da wani abu saƙaƙƙe a mayar da shi tufa ko wani abin sawa a jiki da taimakon zare da allura shi ne ɗinki”. A zamanin yanzu ne muke kira da suna tela.
Muhimmanci Sana’a Ga Al’umma.
        Sana’a dai kamar yadda aka sani tana da matuƙar muhimmanci ga al’umma amma yanzu bari mu kawo wasu bayanai da za su tabbatar da haka.
·        Sana’a tana samar da aikin yi ga al’umma. Idan kana da sana’a to lallai ya zama wajibi kai ka ƙaru su kuma al’ummar da suka saya su samu biyan buƙatarsu.
·        Sana’a tana rage sace-sace ga al’umma.
·        Sana’a tana rage zaman Banza ga al’umma.
·        Sana’a tana rage dogaro ga gwamnati, da wasu ‘yan siyasa.
·        Sana’a tana tare da albaka saboda annabi Muhammad (SAW) ya bayyana cewa, albarka tana cikin sana’a.
·        Sana’a tana samar wa mai ita kuɗi da suna da girma.
          Idan muka yi la’akari da waɗannan muhimman abubuwa da muka zayyana za mu ga cewa, suna daga cikin muhimman abubuwan da rayuwa ta ƙunsa. Kuma dukkansu sana’a ce take samar da su.
Tasirin Da Sana’o’in Zamani Suka Yi A Kan Na Gargajiya
          Shigowar zamani ya yi matuƙar tasiri ga sana’o’in gargajiya, tasirin da har ya sanya ana ganin sana’o’in gargajiya sun zama tsofaffin yayi. Daga cikin tasirin da sana’o’in gargajiya da na zamani suka yi tasiri a kansu sun haɗa da:
Sana’ar ƙira
          Wannan sana’a zamani ya yi tasiri a kanta, idan aka lura za a ga cewa irin ƙirar da ake yi a wancan zamani yanzu ba irin ta ake yi ba, kayan da ake aiki da su a wannan lokaci sun fi kayan da ake amfani da su a wancan lokaci na dauri sauƙin amfani. Misali masu walda suma maƙera ne saboda suna ƙera wani abin amfani kuma ba tare da sun sha wahalar zuga ba ko hura wuta. Haka kuma ƙaruffan da ake amfani da su ba sai a saka su a wuta za a sarrafa su ba. Sai a yi maka wani abin amfani ba tare da sun wahala ba kuma kai ba ka wahala ba.
Sana’ar Saƙa
        Sana’ar saƙa sana’a ce da ta daɗe ana yin ta a ƙasar Hausa, kuma ita wannan sana’a a wancan lokaci na dauri ana amfani da kaba ko auduga a saƙa wani abin amfani da ya haɗa da sutura ko wasu kayan amfanai da suka haɗa da jikkuna, tabarmi, fayafai, kayan ado da dai sauransu.
          A yau kuma zamani ya yi tasiri a kan kayan mu da muka sakawa irin waɗannan da muka lissafo kuma an wayi gari yau injimi ne ke yin duk waɗannan nau’ikan kayan amfani.
Sana’ar Ɗinki
          Wannan sana’a ita ma kamar saura ta jima ana yinta a ƙasar Hausa. Idan aka shiryar da wani abin amfani kamar sutura sai a ɗinka shi a yi kayan sakawa a jiki daidai girman da aka buƙata. Sai ga shi a yau masu wannan ɗinkin suna amfani da wasu teloli da wasu na’urori har da na yi wa sutura kwalliya ba wai ɗinkawa kaɗai ba.
Sana’ar Kiɗa
          Ita ma wannan daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa, kuma ta samu ne tun zamani mai nisa. Wanda a wancan lokaci sai a samu fatar wani dabba a sarrafa ta zuwa wasu kayan amfani a lokacin kiɗan kamar kalangu, katsagi, ganga, kotso, taushi, da dai makamantansu. Sai ga shi a yau zuwan zamani ya kawo canje-canje da yawa, da wasu kaya da suke latsawa kawai za a yi sai ka ji kiɗa ya tashi, kamar su fiyano, da abin busa da badujala da mandiri da dai sauransu. Da kayan tace murya da na tace kiɗa.
Kashe-Kashen Sana’o’in Hausawa
          An kasa sana’o’in Hausawa zuwa manya, da Matsalaita, da ƙanana da kuma salwantattu. Ba lallai ba ne mu ce ga adadin kowanne daga ciki. Sai dai za a kawo duk abin da ya sauwaƙa.
Sana’o’in da Ake Damawa da Su/Manyan Sana’o’i.
          Waɗannan nau’in sana’o’i suna daga cikin sana’o’in da har yau ana tu’ammali da su. waɗannan sana’o’in su ne suka fi kusanci ga al’umma kuma su ne suke taimaka wa tattalin arzikin ƙasar Hausa, a wancan zamani. A wannan zamani kuwa sana’o’in sun samu ci gaba sun canza salo, wasu an samu wasu injimuka/mashuna da ake gudanar da su. Wato dai abin nufi shi ne an zamanantar da su, domin kuwa ba a halin da muka sani ake yinsu ba a yau. Su dai waɗannan sana’o’i sun haɗa da:
·        Noma
·        Kiwo
·        Wanzanci
·        Ƙira
·        Ɗinki
·        Fawa
·        Gini
Sana’o’in da Suka Suma/Matsakaitan Sana’o’i
Matsakaitan sana’o’i dai kamar yadda aka sani su ne sana’o’in da galibi sun tsira ne daga wasu sana’o’i daga manyan sana’o’i. Duk da cewa ba kowace sana’a ce ta tsira daga manyan ba. amma zaman wata sana’a daga manyan yana hardasa ɗorewar wata sana’a. idan muka lura za mu fahimci cewa sana’ar noma ita ce ta haifar da sana’ar sakai. Ita kuma sana’ar fawa tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da sana’ar jima, ita kuma jima tana taikawa da Dukanci. In ka ɗauki ƙira za ka tarar tana taimaka wa Sassaƙa don tana taka rawa wajen amfani da kayan sassaƙa. haka dai abin yake zuwan wata sana’a yana taimaka wa wata sana’a. daga cikin sana’o’in gargajiya matsakaita sun haɗa da:
·        Sakai
·        Rini
·        Jima
·        Su/Kamun kifi
·        Sassaƙa
·        Dukanci
·        Kitso
Sana’o’in da Suke Ɗaukar  Sheɗa/Ƙananan Sana’o’i
          Ƙananan sana’o’in Hausawa sun haɗa da sana’o’in da suke da rauni a wannan zamani. Za ka tarar sun yi nisa, jama’a sun fara barinsu. Sai dai in buƙata ta nemansu ta taso ka tarar wanda zai yi maka su ma ya buwaya/yi wuya. Ba wai an bar su ba amma ba su da wani cikakken tasiri ga jama’a, sun fara tsufa domin an samu wayewa an bar su. wata gudummuwa da suke bayar wa masu yinsu sun tattara sun aje domin samun wasu sana’o’i da suka fi waɗanna bayar da kuɗi. Su dai Ƙananan sana’o’in sun haɗa da:
·        Tuggu
·        Taɗi
·        Bankwai
·        Koda
·        Surhe
·        Awo
·        Dako
·        Dillanci
·        Gyartai
Sana’o’in da Suka Tsira/Sana’o’in Zamani
          Sana’o’in da suka tsira a ƙasar Hausa a yau suna da yawa. Kuma sun samu ne a sakamakon zamani da sauyawarsa. A yau, biyan buƙatun al’umma yana daga cikin muhimmin abin da suka sa ma gaba. Kuma yau in ba ka da abin yi to wajibinka ne ka gani ga wani. Buƙatar abin yi ya sa al’ummar Hausawa suka shiga neman harkar yi har suka samu wasu sana’o’i suka riƙa yi domin su samu abin kore wa bakinsu ƙuda. Hausawa sun yi la’akari da abubuwan da suke cuɗanya da su a yau, kuma sun lura da cewa buƙatar waɗannan abubuwa na cikin ran wasu don haka suka riƙi wasu hanyoyi na koyon sana’o’in domin samun abin yi.
          Galibin sana’o’in da suka tsira ba gadonsu ake yi ba. Sai dai ana koyonsu kuma a iya. Da zamani ya zo yanzu har da wasu cibiyoyi aka buɗa domin koyon sana’o’in zamani. La’akari da irin ci gaban da aka samu ya sa Hausawa suke ganin samun wata sana’a da ta jiɓinci buƙatun al’umma yana da alfanu, don haka suka ɗauki sana’o’i daga cikin sana’o’in da suka tsira suka yi ta aiwatarwa suna samun amfani. Daga cikin sana’o’in da suka tsira akwai:
·        Ci-maka
·        Kwalliyar Hannu
·        Magungunan Mata
·        Cajin waya
·        Aikatau
·        Ɗinkunan Zamani
·        Lalle
·        Yanka salatib
·        Ƙwalama
·        Hakin maye
·        Saƙar zamani
·        Ƙulla suɓo
·        Kunun aya
·        Masu sayar da masa/waina
·        Tuwo-tuwo
·        Wanki da guga
·        Sayar da ruwan leda/pure water
·        Tireda
·        Hayar baro
·        Kabu-kabu
·        Hayar littattafain karatu na adabin kasuwar Kano
·        Hayar kasusuwan kallo
·        Sayar da sutura atamfa leshi da sauransu
·        Sayar da katin waya
·        Koyon sana’ar hannu ta zamani da ta haɗa da sabulu/man shafi
·        Man wanke-wanke/ car wash
·        Kanikanci
·        Kafinta
·        Walda
·        faci
·        Ɗinkin keke
·        Ginin bulo da siminti
·        Girke-girke
·        Soye-soye
          Ba waɗannan kaɗai ba ne domin ɗan binciken da na gudanar na jinga ne kuma zai yi wuya in iya tantance adadin yawan sana’o’in. Amma dai na san da waɗannan sana’o’in sababbi ne.
          A wasu jihohi da aka ci gaba har da cibiyoyi aka buɗe na koyon sana’o’i in da mutum zai je ya koyi wani abun amfanin al’umma kamar dai yadda ake girki, yadda ake ɗinkin zamani, da yadda ake yin man shafi, da yadda ake yin sabulun wanki, da yadda ake yin man wanke-wanke, da yadda ake yin soye-soye, da yadda ake yin wasu sana’o’in da suke da kusanci ga buƙatun al’umma.
Salwantattun Sana’o’in Hausawa/Sana’o’in da Suka Mutu
          Sana’a ta hau a misanin al’adun Hausawa, wanda yake ita ma tana yaɗuwa ta bunƙasa daga ƙarshe tana iya salwanta/mutuwa. Wasu sana’o’i sukan mutu ko su salwanta idan an samu wani abu ya wakilce su kuma idan an yi daidai da ya fi sana’o’in muhimmanci. Yadda muke gudanar da wasu sana’o’i a lokacin da ya gabata, ya sha bamban da yadda suke a yau. Yanzu mu dubi saƙa da kaɗi da farauta. Waɗannan sana’o’in sun kama hanyar salwanta/mutuwa. A wasu sassa na Hausa dai tuni sun mutu har an binne su. ba za ni iya cewa kowane yankin ƙasar Hausa ba, amma dai a ɗan inda bincike na ya shiga duk da cewa na jinga ne ban yi tsammanin sana’o’in suna nan kamar yadda suke a wancan lokaci ba. ga dai wasu sana’o’i da suka salwanta.
·        Saƙa
·        Farauta
·        Kaɗi
Kammalawa
          Maganin kada a yi, shi ne kada a fara. Wannan jingar ta kalli sana’o’in Hausawa na gargajiya da ma na zamani. Da yake buƙatar wannan jinga shi ne a fito da sana’o’in Hausawa da ake damawa da su wato manyan sana’o’i, da waɗanda suka suma wato Matsakaita, da masu ɗaukar rai da wato ƙanana da ma waɗanda suka mutu ko suke gangar mutuwa wato waɗanda suke hanyar salwanta. A wannan jinga zo da ma’anar al’ada inda aka ce ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa. Haka kuma an kawo ma’anar sana’a wadda aka ce ita ce hanyar da ɗan Adam yake amfani da ita domin samun abin dogaro. An kawo nau’o’in sana’a yayin da aka kalle su ta ta jinsi, kuma an kawo sana’o’in da suka danganci jinsin Maza da da na jinsin mata da ma waɗanda aka yi tarayya. Akwai wasu sana’o’i da suka tsira bayan waɗanda muke da su na ainihi. Wasu kuma sun bunƙasa sun haifar da wasu wato wasu sun tsira daga wasu sana’o’in. Wasu sana’o’in kuma sun samu ne sakamakon zamani da wasu cibiyoyin koyon sana’o’i da aka buɗa domin masu sha’awar koyon sana’a da kuma rage zaman banza.