Irin wannan mutumin zuciyarsa ba ta taimaka masa da tunani mai kyau, saɓanin wanda ya taso maraya ya sami jarin galam ɗin kalanzir ya fara sayarwa, ta kai ga yana ɗaukar jarka. A hankali ya shiga ɗaukar durom. Sai ga shi...


Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 4: Saƙar Zuci

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

A wani Hadisi Annabi SAW ya ce a cikin jiki akwai wata tsoka in ta gyaru to mutum ya gyaru, in ta baci shi ma ya baci gaba dayansa, a ƙarshe ya nuna cewa zuciya ce, kenan zuciyannan yadda za ta iya taimakon mutum ya ci nasara a rayuwa za ta iya wargaza shi gaba daya, mun dai sani cewa ita ce za ta taimaka masa wajen gano sabbin abubuwan da za su taimake shi a rayuwarsa, kuma ita ce dai take taskace masa hanyoyin da wasu suka bi kafin a ƙarshe suka isa matakin da suke a yau, misali; na ga wani bawan Allah da mahaifinsa ya bar masa gadon miliyoyin kudi.
.
Nan da nan ya sami sabbin abokai, wasu ma ba sa'o'insa ba ne su ma binsa suke yi sau da ƙafa, ya bar gida ma ya koma hotel, sai abin da yake so zai ci, sai wanda yake so zai gani, a irin kudin da ya samu dinnan zai iya gina irin wannan hotel din a wani wuri, ya zuba duk abin da ke ciki, amma haka ya yi ta kashe musu kudin, ogan wurin ma girmama shi yake yi bare sauran ma'aikata, kudin da ya samu raguwa suke yi tsakanin abin da zai ci, inda zai kwana, suturar jikinsa, tafiye-tafiyen da yake yi, daukar nauyin masu taka masa baya, da kuma 'yammatan da yake nema, ma'ana kudin ba ya ƙaruwa sai raguwa kullum, a ƙarshe dai ya dawo kamar sauran jama'a, shi ma dole ya nema tunda wanda aka taskace an yi masa illa.
.
Irin wannan mutumin zuciyarsa ba ta taimaka masa da tunani mai kyau, saɓanin wanda ya taso maraya ya sami jarin galam ɗin kalanzir ya fara sayarwa, ta kai ga yana ɗaukar jarka. A hankali ya shiga ɗaukar durom. Sai ga shi yana da tankuna ma ba tanki ba, a maganannan yana da gidajen mai a ƙarƙashinsa kamar ba shi ne wancan ba, tabbas Allah ya shige masa gaba, sannan zuciyarsa ta riƙa bugawa ga abubuwan da za su yi masa amfani, akwai kansiloli da suka sami kudi tun lokacin ba a bincike, wasu sun yi abin da suka ga dama da kudin, wasu kuma sun tunano halin da suka shiga kafin suka taka wannan matsayin, sai suka fara tunanin yadda rayuwar za ta kasance bayan sun sauka don duk dadewarsu ba za su wuce shekara hudu ba.
.
Duk mutumin da ka ga yana taka-tsantsan wurin kashe kudi ko yana cire su kamar yana yankar naman jikinsa, kar ka taba tsammanin bai son jin dadi kamar yadda kake ji ne, tunaninku ne ya sha bamban, shi yana tuna yadda ya tara su ne, kai kuma kana tuna yadda za ka kashe ne, duk wanda ka ji yana cewa "Kudi Allah ke ba da su a kashe su kawai" to ka duba yadda yake kashe su, shin ta yadda Allan yake so ne? In ba haka ba ne ai bai da sakankancewar in sun ƙare za a sake ba shi wasu, Allah SW ya yi maganar zakka ne sai sadaka da sauran wuraren ibada, in ba haka ba kuma to da walakin wai goro a miya.
.
Za ka sami mutum yana burin kama sana'a, bai shiga ba amma ya fara tunanin in kuma kayan suka yi kwantai ko aka ƙi siya ya zai yi? Ko yana son ya shiga soja amma kuma ya ce "In aka tura ni Bama ko Sambisa ko Zamfara fa?" Ko zai gina makarantar Furamare a Kaduna ya ce "In kuma L-Rufa'i ya ci gaba da inganta makarantun gwamnati ai ba zan sami dalibai ba, dame zan biya malamai albashinsu? Ya za a yi makarantar ta dore? Ba wanda zai kawo wannan tunanin zuciyarsa sai ka ga jikinsa ya yi sanyi, in ba a yi sa'a ba komai daganan zai tsaya, ba wani abu ya ja masa ba sai irin tunanin da ya sako cikin zuciyarsa kafin ya fara.
.
Da yawa za ka taras ana son a yi wata harka ta hadaka amma wasu suna dan jajja da baya, ka ga kamar ba sa so ne, ko kuma wani abu na rashin natsuwa yana musu ƙaiƙayi a zuciya, gaskiya ba komai ne ba sai irin saƙe-saƙen da suke yi a zukatansu na yuwuwar rashin nasarar tafiyar, in sauran abokan za su zama haka to an gama, ba abin alkhairi da za a iya tsinanawa, har a koma zargin juna cewa wane ne ya ja, shi kuma ya fara ƙoƙarin kare kansa.
.
Mu dauki addinin muslunci a matsayin misali, mahaddata Ƙur'ani a lokacin su ne sojojin muslunci kuma su ne malamai, su din ne dai suka riƙa fita jihadi, ba su ce in aka kashe su ya za a yi Ƙur'ani ya zo gare mu ba, haka suka riƙa fita ko a mutu ko a yi rai, Allah ya kalli zuciyarsu ya ba su kariya ga shi muna amfani da ƙoƙarinsu, haka a yau mutum zai narka miliyoyin kudi ya gina makaranta, ko kamfani ko wata ma'aikata, ba tare da ya yi tunanin in kuma bai dawo da kudin ba fa? A koda yaushe yana tunanin cin nasara ne, tabbas zai ci din da izinin Allah, kowa da ka gani a cikimmu ya san da cin nasara ko faduwa, amma masu cin nasarar kau da kansu suke yi ba sa tunanin faduwar kokadan.