Mu kuma maza Muslunci ya
yi mana kadada. Ya yi ƙofa kan cewa ban da aibanta abinci. In ya yi maka, ka ci. In ba haka ba ka ja bakinka ka tsuke, duk da cewa hadisin yana
nuna ɗabi'un Manzon Allah ne ba cewa ya yi kowa haka zai yi ba. Sai dai
ai ba mu da wani abin koyi sama da dabi'un nasa. Kenan hanya mafi tsarki
da lafiya kowace uwa kar ta cutar da ɗiyarta! Bakin abin
da kika iya dafawa, ko kuke dafawa a gidanku, koyar da ɗiyarki. Sauran
kuma tura ta duk inda ake koyar da girki ta koyo. In kika yi haka kin buƙaci ta zauna da maigidanta
lafiya kenan....
Kundin Ma’aurata 29: Haƙuri Kawai Zan Ba Ka
Baban Manar Alƙasim
Zauren
Markazus Sunnah
Tilas ka yi haƙuri, domin gaskiya ba
laifinta ba ne, kusan zan ce laifin uwayenta ne, dole kowace uwa ta koyar da ɗiyarta komai, daga tsafta
zuwa kwalliya da yadda ake dafa nau'o'in abinci daban-daban, da wasu 'yan
tunatarwa game da sha'anin shimfida, wasu 'yan matan suna sane da rauninsu don
haka suke nema wa kansu mafita tun da wuri, masamman wadanda suka dan girma ba
su yi aure ba, wadannan sun san ciwon kansu, sabanin yara ƙanana wadanda sam ba su
san illar a ce mace ba ta iya girki ba, sau da yawa wasu uwayen sukan koya wa
diyoyinsu irin abincin da suke dafawa ne a gida, kamar dai tuwo da miya.
.
Miyar ma irin wace aka
saba ci tun zamani bai tsofe ba, yanzu komai ya canja, ya zama dole ɗiyarki ta fara koyon girki
a baki tun tana 'yar shekara 8, da zarar ta kai 10 kuwa ya kasance ta fara yin
wasu ƙananan
abubuwa, ba wai ƙyuya ba ce, koya mata yadda za ta fitar da kanta za ta yi, a yau
kuskuren da uwaye suke yi sai ka ji sun ce "Diyoyin yanzu in an saka su
yin wasu abubuwan ba sa so" daganan in uwar ta ga lahiyarta lau sai ta
tashi ta yi abinta da kanta, a ganinta ta huce takaici, sai dai ta riƙa cewa kawai a baki
"Allah ya gani ba ni da alhakinki, ke ce kika ƙi tsayawa ki koya".
.
To ai ba a fafe gora ranar
tafiya, kin yi sakaci ne har ta girma sannan kika fara ƙoƙarin sanya ta abin da ba
ta saba ba, wadanda suka fi kowa fadawa wannan matsalar su ne diyoyin masu
kudi, domin komai akan sakar wa ma'aikata ne, ita uwar tana ganin tunda akwai
wadata ai bai zama dole sai ɗiyarta
ta yi shara ko wanke-wanke ba, to bare kuma tsaftace daki, abinci ma ya wuce a
dafa ta ci, sai ma an kai mata daki a kuma gaya mata cewa abincinta fa yana
daki, tsakani da Allah ba a taimake ta ba.
.
Samun ma'aikata a gida
hutu ne da Allah SW yake ni'imta bayinsa da shi, amma ba shi ne asali ba,
kamata ya yi kowace uwa ta sanya diyoyinta mata cikin ma'aikatan gidan, komai
tare za su yi, komai kasawarsa kuwa, zancen wanke bayi zuwa dafa nau'o'in
abinci dole diyoyinta su yi kamar yadda kowa take yi, hatta rainon ƙanninsu sai sun yi, haka
ita ce gata, ba wai a sangaltar da yarinya yadda za ta tafi gidan miji ba ta
san komai ba, saboda halin yau ba dole ne gidan miji ya yi mata daidai da
gidansu ba, ta yuwu ba halin daukar ma'aikaciya ko maigidan bai da buƙata.
.
Kwanannan muka ga wata an
maido da ita gida kan matsalar rashin iya abincin, shekarun baya kuma na ga
wace aka sako bayan mako guda tal da daura aurenta, ita ma a kan matsala guda,
mai haƙuri a cikin maza shi ne zai yi ta surutu wai matarsa ba ta iya
dafa abinci ba, wata matsala da ta zama ruwan dare, matan da ba su iya abincin
ba ba sa tambaya ko kadan, sannan wata ba ta isa ta ba mace shawarar ta je ta
koyo dafa abinci ba, sai ya zama rainin hankali ko wata rigimar da ba ta da
iyaka.
.
Mu kuma maza Muslunci ya
yi mana kadada. Ya yi ƙofa kan cewa ban da aibanta abinci. In ya yi maka, ka ci. In ba haka ba ka ja bakinka ka tsuke, duk da cewa hadisin yana
nuna ɗabi'un Manzon Allah ne ba cewa ya yi kowa haka zai yi ba. Sai dai
ai ba mu da wani abin koyi sama da dabi'un nasa. Kenan hanya mafi tsarki
da lafiya kowace uwa kar ta cutar da ɗiyarta! Bakin
abin da kika iya dafawa, ko kuke dafawa a gidanku, koyar da ɗiyarki. Sauran
kuma tura ta duk inda ake koyar da girki ta koyo. In kika yi haka kin buƙaci ta zauna da maigidanta
lafiya kenan.
.
Na zauna da maza da dama
ina jin suna neman mafitar yadda za su magance wannan matsalar, na sami wani da
yake fadin wani nau'in abinci ya ce "Shi nake sa iyalina ta yi, ba wai don
ina so ba, a gaskiya ba abincin da ya fita min a rai irinsa, kawai dai ta fi
iyashi ne" to ina amfanin wannan in ya zama abincin da za ka dafa wa
abokai sai ka zaba tsoron kar a ƙyamaci abin da ka kawo? Sau tari wasu mazan
ba sa so a ziyarce su, wallahi ba rowa ba ce tsabar alhinin abin abin da za a
fito wa abonkan ne da shi, wani kuma sai dai ya ce wa iyalin zan kawo abokaina,
ba zai ce ga abin da za a dafa ba saboda bai da kokwanton duk abin da za ta
dafa, haka ya dace.
.
Na taba jin wasu yara suna
roƙon
wata mata wai za su zo su koyi girki, na ji sha'awarsu tunda har suka san suna
da rauni, kuma suna son su magance matsalar kafin su je inda koyon zai
ta'azzara, ga talabijin ga komai, inda ake koya girkin, mata ko kallo ba sa yi
bare su koya, wasu kuma ba kayan kallon ne, wata 'yar Cross River take ce min
"Ku 'yan Arewa ga ku da kayan abinci kala-kala amma matanku sam ba su san
yadda za su sarrafa ba" ta ce da wasu za su yarda kyauta ma sai ta koya
musu, duk kayan aikin ita za ta kawo abinta, lokacin da na gaya wa wasu ko za
su koya, a maimakon su yi murna sai suka fada ta da zagi wai ta raina su, suka
tsane ta.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.