Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambance-Bambance da Sauye-Sauye a Kare-Karen Harsuna


Cuɗanya da iyaye wajen tashi daharshe shi ne koyon harshe ta wajen yadda yaro ya yi cuɗanya da iyayensa wajen tashi da su da jin abin da suke yi na al’amuran yau da kullum. Ta wannan hanyar yaro kan iya tashi da harshe, musammar na mahaifiyarsa wato L1 ko harshe na farko. Dalili shi ne, duk abin da aka faɗa take yake ji ko kuma ya fahimce shi. Misali idan aka kira abu to daga nan ya ji kuma ya ɗauka. Saboda haka ma ake kiran sa da na farko...


Bambance-Bambance da Sauye-Sauye a Kare-Karen Harsuna

Ibrahim Mohammed
08060287141

Gabatarwa
Kafin na tsunduma cikin aikina na karuruwan harshe (dilectology), zai fi dacewa in an yi waiwaye wanda Hausawa ke cewa ‘adon tafiya’ wato tsokaci a kan harshe, karin harshe. Sannan da magana a kan bambance-bambance da kuma canje-canje, da koyon harshe da tashi da harshe da kuma muhiammancin sadarwa ta yaud a kullum.
Harshe
Bagari, (1986) ya bayyana: “Harshe” da cewa: “Hanya ce ta sadarwa kuma ana amfani da shi wajen sadarwa ta hanyoyi guda biyu, wato ko dai a furta magana da baki mutum ya ji da kunnensa ya fahimta ko kuma a rubuta.” Richard, (1985) ya ce: “Harshe shi ne hanyar sadarwa ta musamman da ɗan’adam ke amfani da ita wadda ta ƙunshi tsararrun sautuka da ake furtawa ko rubutawa domin gina magana tun daga matakin ƙwayar sauti har uwa jimla.”
A wata ma’anar ta daban kuwa, Zaruk, (1987) ya bayyana harshe da cewa, shi ne tunanin ɗan’adam wanda yake bayyanawa da bakinsa ko a rubuce.
Dangane da waɗannan ma’anoni za mu iya cewa harshe wata hanya ce da ɗan’adam ke amfani da ita domin sadarwa a halin rayuwa. Harshe wani abu ne da ɗan’adam kaɗai ya mallake shi. Kuma yake amfani da shi wajen isar da saƙonninsa ta hanyar furuci ga ‘yan’uwansa ‘yan’adam wanda yake bayyanwa a bakinsa ko a rubuce.
Dangane da karin harshe kuwa, Skinner, (1977) ya bayyana shi a “matsayin wani nau’in magana a cikin harshe ɗaya wanda ba shi ne ainihin harshen ba.” Trudgil, (1974) cewa ya yi karin harshe na nufin ‘yan bambance-bambance ne da ake samu a ahrshe da suka has bamban a tsarin kalmomi da tsarin jimla da kuma furuci.
Bambance-bambance
A ta fuskar bambance-bambance ana samun yadda mutane ta ɓangaren maganganunsu da suke yi kamar karin sautin Sakwkatanci da Kananci da Gudduranci da sauransu. Misali:
a.      Biyar – biyat
b.     Kusu – ɓera
Haka kuma ga misali a ta ɓangaren jimloli kamar haka:
a.      Ya yi saje – Ya yi swaje.
b.     Sai ta ce – Sai tac ce.
c.      Ya rubuta – Yar rubuta.
Ga misali daga bambance-bambance na sauti a tsakanin Hausar gabas da ta yamma:
a.      /p/ paataa (skin) - /hw/ whaataa
b.     /ɗ/ ɗoyi - /ɗw/ ɗwai
c.      /t/ taarii (cough) - /tw/ twaarii
d.     Goonarka – goonakka
Akwai kuma bambance-bambance da ya shafi sarakuna da kuma kalmomin ‘yan kasuwa mawaƙa, malamai dattijai da kuma yara kamar haka:
Sarakuna
a.      Ranka ya daɗe
b.     Mu muka ce
c.      Rangadi
d.     Fare
Malamai
a.      Ladantarwa
b.     Alfasha
c.      Muwafaƙa
d.     Faƙiri
Kalmomin Kasuwanci
a.      Saye
b.     Sayarwa
c.      Tayi
d.     La’ada
e.      Albarka
Kalmomin Manya
a.      Mai ɗakina
b.     Zan kewaya
c.      Tsohona
Kalmomin Yara
a.      Yaya dai?
b.     Yawa ne
c.      Bula ce da sauransu
Canje-Canje
Shi canji wani yanayi ne da ke faruwa a wani lokaci mai tsayi ta hanyar faruwar waɗansu abubuwa da suka faru ko suka wuce. Za a iya kasa canji zuwa manyan rassa guda biyu, wato canji na dogon lokaci da kuma wanda bai ɗauki lokai ba.
Idan muka ɗauki canji na dogon lokaci za mu ga yadda abubuwa suka faru masu tarin yawa. Misali, idan muka ɗauki lokacin Shehu Usman Bini Fodiyo, yadda abubuwa suka faru wajen aiwatar da kira da kuma jihadi za mu ga yadda bubuwa suka canja a wancan lokaci wajen aiwatar da mulki na Musulunci da kuma adalic. Idan muka yi la’akari da yanzu yadda abin ya canja wajen gudanar da rashin adalci a kan al’umma.
Shi kuwa canji na kusa za mu ga cewa canji ne da yake aukuwa a wasu taƙaitattun lokuta. Idan muka lura za mu ga cewa a ɓangaren kuɗi an samu canje-canje ta fuskar kuɗi irin su nera da kobo da sulalla da sauransu.
Baya ga wannan, ta fuskar ilimi idan muka yi la’akari da yadda abin yake a da, za mu ga cewa lallai an samu canje-canje wajen ilimi. Dalili kuwa shi ne, a da ilimi ya fi inganci fiye da yanzu. A ta fuskar ilimi lallai akwai canje-canje masu tarin yawa ƙwarai da gaske. Ilimi a yanzu ya samu koma baya tare da taɓarɓareaw sakamakon rashin ba shi muhimmanci wanda gwamnati ta ƙi yi. Ta kuma ƙi mai da hankali kan ilimi wajen rashin kula da malamai tun daga kan na firamare har zuwa na jami’a. wannan ya shafi ƙin biyan su haƙƙoƙinsu da sauran abubuwan da suka danganci kayan ayyukan hidimar makarantu da sauransu.
Tashi da Harshe
Cuɗanya da iyaye wajen tshi daharshe shi ne koyon harshe ta wajen yadda yaro ya yi cuɗanya da iyayensa wajen tashi da su da jin abin da suke yi na al’amuran yau da kullum. Ta wannan hayar yaro kan iya tashi da harshe, musammar na mahaifiyarsa wato L1 ko harshe na farko. Dalili shi ne, duk abin da aka faɗa take yake ji ko kuma ya fahimce shi. Misali idan aka kira abu to daga nan ya ji kuma ya ɗauka. Saboda haka ma ake kiran sa da na farko.
Sau da yawa z a atarar da yaron da ya tashi da iyayensa yana da saurin fahimtar yaren iyayen sosai a sakamakon cuɗanya da yake yi da su yau da gobe tare da jin duk maganganun da suke faɗa. A wani lokaci za ka tarar da yaro na ƙoƙarin faɗin abu amma ba ya iya faɗar sa daidai. Amma kuma ya san ita kalmar. Sai dai wajen furtawa tana ba shi wahala. A nan ake samun tangarɗa, sakamakon harshensa bai nuna ba.
Koyon Harshe
Shi kuwa koyon harshe da ake yi na shiga cikin al’umma ko shiga cikin yare shi ne mutum ya sami wata alƙarya ko taron jama’a ya zauna da su. Wajen aiwatar da mu’amala da su na tsawon lokaci ne zai koyi yaren da suke yi har ma ya laƙance shi. Idan muka ɗauki misalin wannan za mu ga cewa lallai cuɗanya da mutane na iya zmaa hanya ta biyu wajen koyon harshe. Dalili kuwa shi ne, irin wannan hanyar ake koyon yare a matsayin hanya ta biyu. Misali, Bayarabe ko Babarbare ya shigo cikin wata alƙarya ya zauna da su, sannu a hankali sai ka ga yana fahimtar abin da suke faɗa. Daga bisani sai ka ga shi ma ya fara iya yin yaren da suke yi. A nan za mu iya cwewa yaren wajen uwa shi ne yare na farko L1 sannan kuma yaren da aka koya kuma shi ne yare na biyu wato L2. Misali Bahaushen da ya koyi yaren Turanci, bayan ya tashi da yaren wajen uwa, wannan shi ne ake kira L2.
Sadarwa
Sadarwa hanya ce ta turawa da karɓar saƙonni daga wajen mutane ta hanyar amfani da dabaru daban-ddban don isar da saƙonni. Hanyoyin sadarwa sun rabu gida biyu, na gargajiya da na zamani. Hanyoyin sadarwa na gargajiya ta haɗa da amfani da tsoffin hanyoyin sadarwa kamar haka:
a.      Tura saƙo da baki
b.     Tura saƙo ta hanyar shela
Haka kuma hanyar yin sadarwa na zamani hanya ce da ta samu sakamakon ci gaba da aka samu na zamani. Sun haɗa da amfani da rediyo da talebijin da sauransu.
Haka kuma a ɓangaren sadarwa ta yau da kullum (social media) shi ne abin da ya shafi maganganu na siyasa da addini ko kasuwanci ta irin yadda ake amfani da kalmomi ko saƙo ta hanyar amfani da irin tsarinsu. Idan muka ɗauki siyasa za mu ga akwai irin kalmomin da suke amfani da su wajen isar da saƙonsu. Misali kamar :
a.      Tazarce
b.     ‘Yanci
c.      Sai ka yi
d.     Alla maimaita mana
Haka kuma a ɓangaren addini shi ma akwai irin maganganun da suke yi wajen isar da saƙonsu. Kamar haka:
a.      Alfasha
b.     Musulmi
c.      Mahammadawa
d.     Shiriya
e.      Tsoron Allah
Haka kuma a ɓangaren kasuwanci akwai irin kalmomin da akeyin amfani da su wajen isar da saƙo. Misalai kamar haka:
a.      Saye
b.     Bashi
c.      Biya
d.     La’ada
e.      Dillali da sauransu
Bayan haka, a ta ɓangaren sadarwa na zamani akwai hanyar sadarwa ririn su:
a.      Talabijin
b.     Rediyo
c.      Jaridu da mujallu
Talabijin hanya ce ta sha yanzu magani yanzu dangane da isar da saƙo. Rediyo ma hanya ce da ta fi kowace saurin sadarwa da jam’a masu yawa kuma acikin sauri. Haka kuma jaridu da mujallu ma hanyoyi ne na sadarwa ga jama’a. sai dai a nan al’ummar da ta iya karatu da rubutu ne kaɗai ke amfana da irin wannan hanya.
Kammalwa
Wannan aikin ya ta’allaƙa ne kan bayanin bambance-bambance da canje-canje da kuma tashi da harshe da koyon harshe. Sai kuma ya taɓo sadarwa da abubuwand a suka shafe sadarwar. Bambanci da canji dai duka abubuwa ne da ake samu a cikin harshe a bisa wasu dalilai. Wannan ya haɗa da bambance-bambancen da ake samu cikin harshe sakamakon bambancin da ke tsakanin rukunin jama’a. A haka ne har aka samu karuruwan harshe a Hausa.

Post a Comment

0 Comments