Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 6: Kyakkyawan Tanadi


Wannan shigar kawai suka kalla suka manta da duk sifofin da yake da su. Wai da na tambaye su dalili sai suka ce ba addini zai riƙa koyarwa ba... Wannan ya sa ban yi mamaki ba da na ga takardar wata da take neman aiki a wani gidan talabijin ta rubuta cewa ita fara ce kyakkyawa. Na tabbata da gidan Radiyo ne ƙila sai ta ce tana da...


Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 6: Kyakkyawan Tanadi

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wani abu da ya zama dole a rayuwar mutum shi ne samun yanayi mai kyau ga abin da mutum yake buƙatar ya yi, da kuma shigar da ta dace,  suna daya daga cikin abubuwan da suka wajaba ga mutum, duk abin da zai yi ya dubi dacewa da kuma yanayi, ko sana'a za ka fara ka duba inda za ka yi din in mutanen wurin suna da buƙatar kayan da za ka sayar, ba yadda za a yi wanda yake son gina makaranta ko dakin watsa labarai ya je tsakiyar kasuwa inda ake hayaniya ga ƙara gami da hargowa ya ce anan zai yi.
.
Wanda zai bude maƙerar da zai riƙa ƙera kayan gona to zai fi kyau ya zauna inda manoma za su riƙa ganin abin da yake yi, don wani wucewa kawai zai yi in ya ga abin da yake so zai tsaya ya saya, ko in zai dawo ya riƙo kudi, zan ba da misali daya, wani bawan Allah ya wallafa wani littafi da yake koyarwa game da mutuwa, tun daga rashin lafiya, da yadda ake jinya zuwa fitar rai, wankan gawa, ginin ƙabari da zaman makoki, littafi ne mai matuƙar mahimmanci.
.
Zai yi kyau Musulmi ya mallake shi ya yi nazari don sanin yadda zai suturta waninsa, sai dai ya yi wa littafin suna "MUTUWA" ga gawanan cikin likkafani an dora ta a kan anna'ashi, na ce wa mai sayarwan da za ku canja sunan littafin da hoton da aka saka a bangonsa da littafin ya fi shiga, misali a sanya fure a maimakon gawa, sunan kuma a ce "Tafiyar da ba makawa" ya ce ai komai ya yi daidai, ko ba a gaya wa mutum ba ya san cewa maganar mutuwa ake yi da abin da ya shafe ta.
.
A taƙaice dai wallahi littafin nan ƙwara daya sai da ya gama cin dukar rana ya ƙoƙe ba wanda ya saya, kuskuren wajen nuna wa mutane abin da ba sa son gani ne, duk wanda ya kalli bangon littafin zai yi wahala ya yi sha'awar siyansa, akwai wata yarinya da take tallar abinci, wallahi abincinta akwai dadi ga arha, komai kake so akwai, amma yanayin kayan da take sakawa, da wurin da take zama, da nau'in abincin da mutanen wurin suke buƙata ya sa sam-sam ba a sayen abincinta, ga masu abincinnan a wurin ko kusan nata bai kai ba amma suna samun ciniki ba kadan ba.
.
Sun gyara shagon, ga kujeru da teburi, fanka na kadawa, a gefe ga firinji, na ci abincin wata a cikinsu sau daya ban ƙara ba, wancan ta farkon da za ta riƙa kawo abin da ake buƙata a hankali ta kwaikwayi waɗannan, ta kiyaye dadin abincinta kar ta canja, tabbas sai ta ƙwace komai, akwai kuma lokacin da aka zo daukar malamai aiki, ana neman malamin Turanci, an sami wani Bayerbe komai ake so yana da shi har da ƙari, amma yana da ƙasumba, ga shi ya zo da jallabiya da wando rabin ƙwabri da takalmi silifas.
.
Wannan shigar kawai suka kalla suka manta da duk sifofin da yake da su. Wai da na tambaye su dalili sai suka ce ba addini zai riƙa koyarwa ba... Wannan ya sa ban yi mamaki ba da na ga takardar wata da take neman aiki a wani gidan talabijin ta rubuta cewa ita fara ce kyakkyawa. Na tabbata da gidan Radiyo ne ƙila sai ta ce tana da daddadar murya. Wannan ma abin nema ne a wurinsu can. Duk abin da za ka yi ka dubi buƙatun jama'a da kuma yadda za su kalle ka.
.
An yi wani zamani a ƙauyemmu lokacin da fulani suka rabu biyu, akwai masu sayar da nono a kwano da masu sayarwa a ƙwarya, masu sayarwar a kwano sukan ci ado ka gan su tsab-tsab koda yaushe amma fa suna da tsada, na ƙwaryar ne dai da arha, na tabbata shigar masu sayarwan a kwanon da yarda da kai da yadda suka ƙawata sana'ar suke ganin abin da ya dace a yi kenan, domin duk da tsadarsu da komai wasu sun fi natsuwa da su, ba su sayen nono sai a wirinsu, ko lauyoyi da likitoci gami da manyan ma'aikata ba wani abu ya sa kake ganinsu tsab-tsab ba sai inganta ayyukansu, ana ƙimanta mutum wani sa'in da irin shigar da ya yi ne.
.
Ka lura da kyau ka gani, ko tsayuwa ka yi wurin wanda ya fito tsab za ka ga shi ake girmamawa, na taba yin tafiya wani lokaci da maigidanmu, akwai kuma ma'aikatammu, cikinsu akwai wani Bakatsine da ya sha shakwara da jamfa, duk inda muka shiga sai ka ga an tsallake mu an fuskance shi, ba wani abu ya fi mu ba illa irin shigar da ya yi, ana ganin shi ne ogan gaba daya, zaben wurin aiki, shigar ma'aikacin, nau'in irin aikin duk abin dubawa ne, mu tara a gaba kan wannan batun.Mun yi shekara ɗaya cur tare da malam muna ƙaruwa. Tsakani da Allah ba abin da muka sani. Shi ya riƙa ɗora mu a kan hanya. A shekara ta biyu ya ce mana shi fa...
Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 5: Guji Yawan Kawo Hanzari

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wasu za su iya yin duk abin da ake buƙata, hasali ma su ne kawai za su iya yi din, amma yawan koke-koke ko kawo hanzari shi zai ruguza su ya bata tafiyar gaba daya, wani kana tuntubarsa a kan wani abu mai matuƙar mahimmanci a rayuwarsa sai ya ce maka mu yanzu ai mun girma ya za a yi mu iya? Hanzarin dai shi ne yawan shekaru, akwai kuma wanda zai ce gaskiya ba zai iya ba saboda ƙarancin wayewa, ko ilimi, ko kudi, ko shekarun, ko dai wani abin na daban, matuƙar mutum ya ce ba zai iya yin abu ba saboda wani dalili da ya dogara da shi, da wahala ka ga ya motsa, ya haƙura da nasarar kenan.
.
Wani maƙwabcimmu yake cewa "Lokacin da muka shiga JSAIE (Junior Secondary School for Arabic and Islamic Education) ba mu san komai ba, gaskiya ni ko baƙaƙen da Larabci ban iya ba, mun dai yi karatun allo kuma mun sauke, mun haddace wurare da dama amma sunan Nahawu ma lokacin na fara ji, don haka muka nemi wani malami da zai taimaka mana, shi ya koyar da mu littafai da yawa, a dalilinsa muka fara sanin inda aka dosa, mun ga sa'o'inmu a ajin, da ƙanninmu da ma waɗanda suka haife mu ba yayyimmu ba.
.
Mun yi shekara ɗaya cur tare da malam muna ƙaruwa. Tsakani da Allah ba abin da muka sani. Shi ya riƙa ɗora mu a kan hanya. A shekara ta biyu ya ce mana shi fa iyakarsa kenan sai dai mu nemo wani malamin, hankulimmu ya yi matuƙar tashi, haka dai muka yi ta bundun-bundun mu fada nan mu tashi can, cikin ikon Allah muka shekara shida muka kammala karatun, muka wuce kwalejin share fagen jami'a muka samo kwalin diploma, muka dawo gidan da muka zauna muna tuna baya, cikin ikon Allah a ranar sai ga malamin namu ya yi sallama ya shigo.
.
Abin mamaki sai ya sami wuri a ƙasa ya zauna bayan mu muna kan kujeru a zaune, sai ya ce wai ya zo neman sani ne, haka dukammu ukun muka yi ƙasa, ya ce wallahi shi tun daga shekara ta biyu ya rabke ya kasa ci gaba, yana ganin ya girma ga kuma ƙarancin abubuwan masarufi, mu ga shi Allah ya taimake mu har mun kai ga Diploma, tsakani da Allah ba don neman sani ba da ba zai zo ba, saboda haka mu koma kan kujerarmu in ta so in mun ba shi amsa ma sauko ƙasa, muka ce masa wallahi in dai yana ƙasa ba wanda zai hau kujera.
.
Da dai ya ga da gaske muke sai ya hau din kuma ya umurce mu da mu hau, da farko mun ƙi, amma da muka ga zai shiga wani hali muka hau, sai bayan mun gama sai ya yi mana nasiha da cewa kar mu taba samun raunin gwiwa a kan karatu, da ma duk abin da muka shiga, na san dai yana yin wata sana'ar da tun farko muka san shi da ita, mu kam yanzu muke tasowa amma a dalibansa wasu sun  zama marunbuta, wasu malaman jami'a wasu manyan 'yan siyasa, wasu 'yan kasuwa da malaman muslunci, a sa'o'inmu ni na san waɗanda suka zama manyan sojoji, 'yan sanda, alƙalai, lauyoyi, malamai a jami'u da sauransu, akwai waɗanda suka koma suna koyarwa a zaurukan gidajensu ana ba su sadakar Laraba".
.
Wasu tabbas sun sami karayar zuciya ne a dalilin ƙarancin kudi, wasu za su ce maka ba sa ganewa, akwai wanda muna karatun ya arce abinsa wai shi aure yake so, ya yi auren amma ya kasa dawowa fagen da yake ciki har abokan tafiyar nasa suka yi masa nisa, sai ya gan su ya yi ta sha'awa, akwai wanda ya ƙi karatun wai za a maida shi dan Izala, a daidai lokacin mu kammu muna kukan cewa Dariƙar ake koya mana, don littafan tauhidin sam ba sa taimakon 'yan Izalan a aƙidunsu, amma duk da haka muka yi haƙuri muka dage har muka gama, kuma ba abin da ya shafi aƙidummu, shi kuma har yanzu yananan yau kamar jiya.
.
Akwai kuma wani bawan Allah da muka zauna wuri guda, yana HND a bangaren kimiyyar noma da tsire-tsire, muna koyarwa wuri guda, ya ba ni shekaru da dama kuma ya fi ni wayewa da sanin kan rayuwa ta ko'ina, a haka na je na yo digirina na farko a waje, na dawo na ba shi shawarar ya canja layi kawai ya dawo bangaren koyarwar tunda yana da sha'awa, na yi dace ya manta da shekarunsa da wayewarsa ya koma makarantar, cikin 'yan shekaru ya samo kwalin Digirin shi ma, ya dora digiri na biyu, a maganannan da muke yi shi ke jagorantar wani babban kwaleji.

Post a Comment

0 Comments