Ticker

6/recent/ticker-posts

Azuzuwan Nahawun Hausa


A waɗannan misalai, kalmar wani, wata, waɗansu/wasu kowacce fayyacewa take yi. A misali na farko, littafi ne jinsi namiji, guda ɗaya. A na biyu, takarda ce jinsi mace, guda ɗaya. A misali na ƙarshe kuma, motoci ne masu yawa...


Azuzuwan Nahawun Hausa

Umar Buba
07030156552
Gabatarwa
Nahawu shi ne sanin ƙa’idojin harshe. Sanin ƙa’idojin kuwa iri biyu ne, da adananne da bayyananne. Watau a taƙaice nahawu iri biyu adanannen nahawu da kumabayyanannen nahawu. Adanannen nahawu (watau sanin ƙa’idojin harshe) shi ne wanda kowanne ɗan asalin harshe yake amfani da shi. Alal misali kowane Bahaushe yana sane da iyakacin sautukan harshen Hausa kuma yakan kiyaye ƙa’idar sautukan Hausa, domin ba safai yakan tsoma wani baƙon sauti a cikin maganarsa ba. Haka kuma kowane kowane Bahaushe yana sane da yadda sautukan Hausa suke cuɗanya saboda haka ba ya furta kalmomin Hausa da salo da ba na Hausa ba.
Bayyanannane Nahawu shi ne wanda malamai masu koyar da harshe suke da shi. Alal misali malamin Hausa yana iya yi wa harshen Hausa ɗai-ɗai kamar yadda makanike yakan yi wa inji watau saboda malamin Hausa yana da bayyanannen nahawun Hausa ya san ƙa’idojin harshe bi-dab-bi. Saboda haka sai wanda ke da bayyanannen nahawun Hausa ke iya tantance cewa sauti kaza ba ya haɗuwa da sauti kaza a Hausa, ko kuma kalmomi iri kaza su sukan zo kamin kalmomi kaza ko kuma bayan kalmomi iri kaza a harshe.
Structuralism (Tsofon Nahawu)
Tsarin nau’in nahawu wanda ake yin sa a da wato traditional grammar (structuralism) ya tahallaƙa ne a kan rukunnen nahawu guda takwas (8) kamar haka:
1.     Suna
2.     Wakilin suna
3.     Aikatau
4.     Bayanau
5.     Sifa
6.     Nunau
7.     Mafayyaci
8.     Ma;auni
1.    Suna: Wannan kamar yadda muka sani, kalma ce mai nuni da sunan abu kowane iri mai rai ko maras rai, wanda ake gani da wanda ba a iyawa da dai sauransu. Akwai na yanka, gama-gari, tattaurau, gagara ƙirga.
i.                   Na Yanka: Sunan yanka shi ne kamar sunan da aka san mutum da shi ko ƙasa ko gari misali, Gambo, Delu, Lawan, Audu, Kamaru, nijeriya, Sakkwato da dai sauransu.
ii.                 Gaba-Gari: Wannan suna ne ba na mutum ko na wuri takamaimai ba. In an kwatanta gama-gari da sunan yanka, za a iske cewa gama-gari na gaba ɗaya ne, na yanka kuwa na musamman ne. misali, takalmi, hula, agogo, tuwo, fitila, da dai sauransu.
iii.              Tattarau: Wannan kuma tattara abu fiye da guda waje ɗaya ya yi. Misali: Ƙungiya, gungu, runduna, ayari, da ai sauransu.
iv.               Gagara-Ƙirga: Kamar yadda za a fahinta daga sunan, wannan ya shafi abubuwa ne waɗanda ba a iya ƙirga su ɗai-ɗai. Misali, mai, ruwa, gero, acca da dai sauransu.
2.    Wakilin Suna: Wannan kalma ce da ake amfani da ita a madadin “suna” wato dai kamar yadda sunan ya nuna, wakilin suna yana wakiltar suna ne. shi ma dai kamar suna, iri-iri ne. akwai ɓoyayye, katsattse, gama-duniya, tambayau da dai sauransu.
i.                   Ɓoyayye: Wannan nau’in na wakilin suna shi ne kamar: wane, wance, su wane da wane, su wance da wance.
ii.                 Katsattse: Wannan kuma shi ne kamar ni, mu, su, kai, ke, ku, shi, ita da dai sauransu.
iii.              Gama-Duniya: A nan kalmomi kamar: kowanne, kowacce, su ne misalansu.
iv.              Tambayau: Kamar yadda sunan ya nuna, wannan nau’I ne da ya danganci tambaya. Akwai kamar wa? Me? Su me da me?
3.    Aikatau: Aikawatau dai kalma ce mai nuna aiki a cikin jumla. Shi ma kuma iri-iri ne. misali, so-karɓau da kuma ƙi-karɓau.
i.             So-Karɓau: Wannan nau’I na aikatau shi ne irin wanda aikin da ya ƙunsa yake faɗawa kan wani abu. Misali, tara, ɗinka, wanke ɗauko, sami da dai sauransu.
Ya tara kuɗi.
Ta ɗinka riga.
Sun wanke mota.
An ɗauko kaya.
Na sami aiki.
A waɗannan jumloli, kuɗi, riga, mota, kaya, aiki duk su ne suka karɓi ayyukan da waɗannan aikatau da muka ambata suka ƙunsa. Ma’ana ayyukan cikin waɗannan aikatau a kansu suka faɗa.
ii.           Ƙi-Karɓa: Wannan kuma kishiyar wancan ne. Shi aiki ne da ke cikin rukunin aikatau wanda ke komawa kan wanda yake gudanar da aikin. Ba ya faɗawa kan wani abu daban. Misali, cika, ɓace, wanku, rame, firgita da da dai sauransu.
Tulu ya cika.
Hula ta ɓace.
Riga ta wanku.
A waɗannan misalai, duk aikatau ƙi-karɓau ne domin aikin cikin kowanne yana komawa ne ga mai in aikin.
4.    Bayanau: Shi kuma wannan kamar yadda muka sani, bayyana “aikatau” yake yi. Wato yana yin bayani ne game da aiaktau a jumla. Akawi bayanau iri-iri kamar na wuri da na lokaci da na yanayi da dai sauransu.
i.                   Na Wuri: Shi ne kamar nan, can da dai sauransu.
ii.                 Na Lokaci: Shi ne kamar yanzu, gobe, jibi, baɗi, shekaranjiya da dai sauransu.
iii.              Na Yanayi: Shi ne kamar, da kyar, a guje, a zaune da dai sauransu.
5.    Sifa: Wannan kuma kamar yadda muka sani, aikinta shi ne bayyana “suna”. Wato ita  bayani take yi game da suna. Ita ma iri-iri ce. Akwai sassauƙa, aiwatau, nanatau da dai sauransu.
i.                   Sassauƙa: Kamar shuɗi, shuɗiya, shuɗɗa, ƙarami, ƙarama, babba, manya da dai sauransu.
ii.                 Aiwatau: Kamar masharranci, masharranciya, masharranta, mashiririci, mashiririciya, mashiririta, maƙaryaci, maƙaryaciya, maƙaryata da dai sauransu.
iii.              Nanatau: Shi kuma kamar goma-goma, ƙungiya-ƙungiya, daki-daki, gungu-gungu da dai sauransu.
6.    Nunau: Kamar yadda sunan ya nuna, “nunau” kalma ce da ke nuna abu dangane da nisansa ko kusancinsa da mai magana. Misali:
Wannan yaro
Wancan yaro
Waɗannan yara
A misali na farko yaro da ake bayyanawa kusa yake da mai magana. Wato nunau wannan yana kusanci ne. A misali na biyu yarinya da ake bayyanawa nesa ake da mai magana. Wato nunau wancan yana nuna nisa ne. A misali na ƙarshe kuma, yara da ake bayyanawa ma nesa suke da mai magana, in aka yi la’akari da nuanu waɗancan.
7.    Mafayyaci: Wannan kuma kalma ce mai fayyace abu, kamar yadda sunan ya nuna. Misali:
Wani littafi
Wata takarda
Waɗansu/wasu motoci
A waɗannan misalai, kalmar wani, wata, waɗansu/wasu kowacce fayyacewa take yi. A misali na farko, littafi ne jinsi namiji, guda ɗaya. A na biyu, takarda ce jinsi mace, guda ɗaya. A misali na ƙarshe kuma, motoci ne masu yawa.
8.    Ma’auni: Kamar yadda sunan ya nuna, “ma’auni” kalma ce da ta danganci yawa ko adadin abu, misali:
Doki ɗaya
Mutane bakwai
Ɗalibai tuli
Littattafai kaɗan
Kamar yadda aka gani, ɗaya da bakwai da tuli da kaɗan kowace na nuna adadi ne na abin da aka ambata. Wato kowacce ma’auni ce. Daga ƙarshe duk waɗannan abubuwa da na ambata sama su ne nahawun gargajiya wato traditional grammar.


Post a Comment

0 Comments