Ticker

6/recent/ticker-posts

ALH 203: Phonology 1 (3 CU)

Bincike ya nuna cewa akwai Harsuna masu rai sama da dubu hamsin a duniya. Bayan waɗanda suke cikin haɗarin fuskantar mutuwa (endengered languages). Dukkan harsuna suna da tsarin sauti mabambanci. Wannan ya nuna mana cewa kowane bakin wuta da nasa hayaƙi. Wannan kwas ɗin yana ɗaya daga cikin kwas-kwas ɗin da suka shafi fannin nazarin Ilimin Kimiyyar Harshe (Linguistics), wanda zai yi bayani game da Ilimin Furuci (Phonetics) da kuma Ilimin Tsarin Sauti (Phonology) na harshen Hausa. 
By

Muhammad Arabi Umar
Manufofi (Objectives)
Bayan kammala wannan kwas, ɗalibai za su iya sanin:
1. Matashiya kan Ilimin Tsarin Sauti da dangantakarsa da Ilimin Furuci.
2. Matsayin Ilimin Tsarin  Sauti a nazarin Ilimin Kimiyyar Harshe.
3. Bayanin gaɓoɓin furuci (organs of speech) da rawar da suke takawa wajen samar da sautukan magana (speech sounds).
4. Bayyana yadda ake samar da sautukan Hausa na baƙaƙe (consonants) da wasula (vowels).
5. Lamurran da ke faruwa sakamakon zamantakewar sautukan Hausa a cikin kalmomi da jumloli.
6. Karin Sautin Hausa (Hausa tone)

An raba wannan kwas kamar haka:

Batu
Tattaunawa
1
Gabatarwa (introduction)
1.       Share fage kan ilimin harsuna, 
2.       Ma’anar Ilimin Furuci da Ilimin Tsarin Sauti 
3.       Dangantakar da ke tsakaninsu,
4.       Muhimmancin nazarin Ilimin Tsarin Sauti.
2
Fannonin Ilimin Furuci, 
1.                   Fannin furta sauti (articulatory phonetics), 
2.                   Fannin jin sauti (auditory phonetics), 
3.                   Fannin kamannin sauti (acoustic phonetics). 
3
Fannin Furta Sauti:
Gaɓoɓin Furuci (speech organs)
1.                   Mafurtai (articulators): masu motsi (active) da marasa motsi (passive),
3
Yadda ake samar da Sautukan Baƙaƙen Hausa (production of Hausa Consonantal sounds)
1.       Bayanin Zirin Iska (airstream)
2.       Matsayin Maƙwallato (status of the glottis) 
3.       Wuraren furuci (places of articulation)
4.       Yanayin Furuci (manner of articulation) 
4
Ire-iren Furucin Sautuka (types of articulation)
1.                   Tilon furuci (single articulation)
2.                   Tagwan furuci (double articulation)
3.                   Furuci maigoyo (co-articulation)
5
Furucin Wasula (production of Hausa vowel sounds)
1.       Mene ne Wasali? 
2.       Ire-iren Wasulan Hausa: Tilo da Tagwai da kuma Dogaye da Gajeru 
3.       Matsayin Harshe (tongue height), 
4.       Matsayin Leɓɓa (lips rounding)
6
Tsarin Gaɓa da Rarrabewa (syllable structure)
1.                   Ma’anar gaɓa
2.                   Ire-iren gaɓa: Rufaffiya da buɗaɗɗiyar gaɓa (open and closed syllabe), sassauƙar gaɓa da nannauya (light and heavy syllable) 
3.                   Tsarin gaɓar Hausa 
4.                   Rarrabewa: Ta Zaman Bamban da Ta Zaman Daidaito
7
Naso (assimilation)
1.             Ma’anar Naso, 
2.             Ire-iren Naso: Cikakke da Ragagge, Na Dama da Na Hagu, Na Kusa da Na Nesa
8
Karin Sauti (tone)
1.                   Ma’anar Karin sautin 
2.                   Ire-iren karin sautin Hausa: na sama da na ƙasa da faɗau
3.                   Muhimmancin Karin Sauti: wajen rarrabe ma’ana da nahawu.
Manazarta
M.A.Z Sani        Tsarin Sauti Da Nahawun Hausa, University Press PLC Ibadan, 2005.
M.A.Z Sani        Jagoran Nazarin Tsarin Sautin Hausa, Benchmark Publishers Limited, 2005.
M.A.Z Sani        Siffofin Daidaitacciyar Hausa, S.H.N Bayero University Kano, 2009. 
Hyman, L.M.     Phonology: Theory and Analysis, New York 1975.

Website: amsoshi.com

Post a Comment

3 Comments

  1. Assalamu Alaikum waraha matullah wa barkatuhu yaku masa harcen hausa ina mai mika godiya ta agareku Da irin gudun mowar da kuke bamu a ma tsayim taimako mungode sosai sako daga Usman ibrahim daya daga cikin dalibab jahar jigawa karamar hukumar birnin kudu ina karatu colege of Education and legal ringim local govement jigawa state .

    ReplyDelete
    Replies
    1. Wslm

      Mun gode sosai.
      Allah ya sa mu dace baki ɗaya.

      Delete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.