Duk
da cewa shi yana ganin ya gaya mata ba sau daya ba ba sau biyu ba ba ya son
irin surutan da take yi, amma abin ya ci tura, ita tana ganin taimaka masa take
yi. Shi kuma a fahimtarsa kullum
ƙoƙarin mallake shi da maishe
shi saiwar sala take yi, to da wahala...
Kundin
Ma'aurata - 3: Fahimtar Bambanci
Baban Manar Alƙasim
Zauren
Markazus Sunnah
Idan
ya kasance ko yaushe maza ne a gaba, dole sai abin da suka ce a gida shi ne za
a yi, abin da suka kawo kuma in ba a karba ba ya zama matsala, sannan mace ba
ta isa ta yi aiki ba sai sun yarda, in ma suka ga dama sai ka ga sun han ta,
tanan za a iya cewa sun yi kaka-gida sun ƙwace wa mace haƙƙinta, masamman in ya kasance
alƙalin
da zai yanke hukuncin bai da basira, domin in muka koma baya za mu ga hatta
wajen neman aurennan mace na jira ne sai an furta ana son ta, sannan namijin ya
riƙa
zuwa gidanta zance ba ita ta zabo shi take zuwa zance in sun gama ta kamfato
kudi ta bashi ba, hidimomin da ake yi har zuwa ranar daura aure duk ba ruwanta
da su.
.
Macen
duk da ta dauki nauyin wannan har zuwa daura auren, kuma ta ci gaba da daukar
nauyin gidan ka je ka leƙo
abin dake faruwa, ka ga wanda yake da haƙƙin yanke hukunci a gidan,
asali matsalolin da muke fama da su a yau, ba sa rasa nasaba da ƙoƙarin da muke yi na tsallake
wajibin da yake kammu zuwa karbe na abokin zamammu, in haka ne kuwa to zai yi
matuƙar
wahala a zauna lafiya, kenan mace ta san wajibobinta, shi ma namijin ya san
inda ya kamata ya tsaya da inda zai wuce, kar ka yi mamaki wata macen ta ce
maka maigidanta yana yawan fushi kuma ba ta san dalili ba, don ba ta sami
cikakken lokacin da za ta zauna da shi ba bare ta karance shi, amma wace duk
take aiki a wani wuri ta san oganta da kyau da duk abubuwan dake damunsa don
tana da cikakken lokacin karantarsa.
.
Anan
ba cewa nake yi kar mace ta je aiki ba, ina ƙoƙarin cewa ne ba ta sami
cikakkakken lokacin da za ta karanci gidanta sosai ba, galibin maza abin da ya
sa suke ta samun taho mu gama kenan da iyalinsu ba wai tsabar kishin ba ne, ina
koyarwa a wata makaranta wani mutum ya janye matarsa, mun ji zafin hakan gaskiya
don tana da hazaƙa
matuƙa,
ga zuwa makaranta a kan kari, koda wasu ba su zo ba ita za ka riske ta a cikin
aji, dalilin wannan sai hukumar makaranta ta yi ƙoƙarin sanin ko an yi masa
laifi ne wanda ya sa ya yi yunƙurin
janye ta, amma sai ya ce ba ya samun
kulawar da ta dace ne, kullum tana waje, kafin ya farka barci har ta
fita, in ta dawo kuma sai ta mai da hankali kan ayyukan da aka ba ta a
makantar, a taƙaice
dai sai da ta sauko ta yarda ta gyara wasu abubuwa sannan aka daidaita.
.
Yadda
Muke Ganin Junanmu
Farkon
kokawar da mace za ta yi ita ce: Namiji bai son yawan koke-koke, in ma ya tsaya
ya saurara ɗin sai ka ga abin da
zai yi kawai shi ne ya gama sauraron matsalolin ya fara fadin hanyoyin da za a
warware su" ita mace abin da take so shi ne a nuna damuwa da halin da take
ciki, kuma a ba da cikakkiyar kulawa, sannan a fahimci cewa lallai matsalar da
suke fadinnan fa tabbas matsala ce, to shi gogan duk bai yi haka ba ya fara
binciken warware matsala amma ba ta hanyar da ta dace ba, a ƙarshe ba za a iya warware
matsalar ba.
.
A
irin wannan halin za ka riski wasu matan sun fita harkarsa, wanda a ƙarshe su ma sai su fara wasu
dabi'u da gangan don tura masa haushi, wata kuwa takan dage ne sai ta nuna masa
abin da take so, wanda yin haka shi yake kawo hayaniya a tsakaninsu koda
yaushe, haka za su yi har su gama ba tare da wani ya fahimci dan uwansa ba, a ƙarshe dai akan fi liƙa wa namijin ne laifi,
masamman in ya kasance masu kallon abubuwan dake faruwa mata ne, ta bangaren
namijin kuwa za ka taras galibin abin da suke fara kokawa a kai shi ne: Ita
mace kullum ƙoƙarinta sai ta canza masa
rayuwa ƙarfi
da yaji, kamar irin bai san abin da yake yi ba ne ita za ta nuna masa
ya-kamata, wato dai tana nuna cewa ita ce a gabansa ta fi shi hankali da
tunani, ita za ta ce masa ya yi kaza ko ya bar kaza, ciki har da zumuntarsa.
.
Duk
da cewa shi yana ganin ya gaya mata ba sau daya ba ba sau biyu ba ba ya son
irin surutan da take yi, amma abin ya ci tura, ita tana ganin taimaka masa take
yi. Shi kuma a fahimtarsa kullum
ƙoƙarin mallake shi da maishe
shi saiwar sala take yi, to da wahala su fahimci junansu. Amma gaskiyar maganar tana
baya. Shi kullum
yana waje, tunaninsa yadda za a maida naira daya ta zama biyu, da yadda za a
warware duk matsalolin cikin gida, don haka tunaninsa da tsantsar abin dake
faruwa a cikin gidan kadan ne, ita kuwa mai ɗakinsa
da take gida ba ta da wani abu sai shi din, dole ta fi shi sanin abin dake
faruwa a gidan, da ma alaƙarsa
da 'yan uwansa, da sauran abubuwan da suka shafi zumunta, da za mu yarda mu
karanci juna ba shakka za mu warware matsaloli da daman gaske.
.
Yadda
Namiji Yake Jin Kansa
Namiji
kamar yadda aka san shi yana da ƙoƙarin hangen nesa, da
jajircewa wurin isa ga abin da yake so, wasu mazan ba sa so ma a san abin da
suke ciki bare wani ya yi ƙoƙarin amshe musu abin da suke
nema, ko kuma su ce sun isa gare shi ne da guminsu, ba tare da wani ya sanya
musu hannu ba, to ko a gida ma irin wannan yakan faru tsakanin mutum da
iyalinsa, wani yakan yi mata iyaka ya hana ta shiga lamarin 'yan uwansa, ko
kasuwancinta ko wasu abubuwan da yake ganin ba su shafe ta ba, in ya zama haka
to zai yi wahala ka ga ya zauna da ita ana tattauna wasu abubuwan da yake ganin
shi kadai suka shafa banda ita, amma kuma da a ce ita matar za ta nemi shawararsa
a irin waɗannan matsalalolin za
ka ga yana ƙoƙarin nuna mata cewa kaza ya
kamata, kaza kuskure ne, ashe ba wai yarda ya yi da cewa irin waɗannan
maganganun sun shafi mutum ne shi kadai ba, gani yake yi ba zai bari ta shugo
masa ba.
.
A
irin wannan yanayin shi yana gani tausayawa ce da ƙauna za ta sa ya ba ta
shawara, amma ba zai yarda ita ta nuna tausayawa da ƙaunar ta wannan bangaren ba,
wasu kenan daga cikinsu ba duka ba, babban abin kula a ciki shi ne, in fa ya ba
ta shawara dole ta karba ta yi aiki da ita ba za ta yi gardama ba, don yin
hakan rashin girmamawa ne da ba shi matsayin da yake ganin ya kai, to in muka
lura da wannan sai mu gane cewa ashe babban dalilin tunkude shawarwarinta ya
raina tunaninta ne, ko guje wa yin kafada da kafada da ita kan shugabancin
gida, in muka koma farko, mace tana ƙoƙarin fadin matsalolin da ta
sami kanta ne a ciki, tana son a saurare ta a ba ta shawara a sanyaya mata rai,
shi kuma sai ya yanke ta ya fara ba ta mafita, ko ma ya nuna mata cewa
sakacinta ne, a nan dole ta yi fushi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.