Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma'aurata - 2: Tasirin Bambancin Halitta a Zamantakewa



Tabbas ƙauna takan taimaka wajen tsare danshin soyayya a tsakanin ma'aurata na tsawon lokaci. Sai dai tambayar da za a nemi amsarta a nan ita ce "Wace iriyar soyayyar?" Kar ka yi mamakin wannan tambayar, domin duk mun san cewa duk lagwadar soyayyar da aka sha kafin aure takan ƙafe nan da nan da zarar...

Kundin Ma'aurata - 2: Tasirin Bambancin Halitta a Zamantakewa

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Allah SW ya halicci namiji da mace ya kebe kowanne daga cikinsu da irin aikin da zai yi gwargwadon halittarsa, koda a ce maza suna zaluntar mata wurin killace su a cikin gida da hana su fita neman abin na kansu wanda hakan zai iya nuna cewa zalunci ne a sarari da mazan suke yi don nuna mamaya wurin yin amfani da ƙarfin da Allan ya ba su, amma da wani namijin zai tilasta matarsa ta riƙa fita tun safe zuwa yamma don ta yi kafintanci, kanikanci ko leburanci ko tuƙin mota a tasha don neman abin da za a ci a gida da sutura da sauran abin da gidan yake buƙata, ko mazan ba su yi wa junansu magana ba, matan za su kira namijin da suna azzalumi, mara tausayi, mugu, domin ya daura wa matarsa abin da bai dace da ita ba, a nan ba tare da wata jayayya ba za a yi hukuncin cewa aikin da take yi ba nata ba ne, shi ya kamata ya fita ya nemo, nata sarrafawa ne kawai, ba inda aka ce su fita tare bare a sarayar mata da nauyin ciyar da gida, nan fa don aikin na wahala ne, ba a yi ma maganar wanda za a yi a bakin rai ba kamar sha'anin tsaro.
.
Shi kuwa namiji in ya sami wuri ya shantabe a gida ya zama bai neman na kansa, koda ya dauki nauyin shara da dafa abinci a lokacin da matarsa ta fita, ya hada da tarbiyar yaran da ta bar masa, ba za ka taba jin cewa musaya aka yi ba yanzu ita ce maigidar, ji za ka yi ana cewa "Duk abin da take yi taimaka masa take yi a sanadiyyar mutuwar zuciya da ya samu, shi ya sa ya yi watsi da wajibinsa, kuma za ta yi masa gori a duk lokacin da ta ga dama don saboda halin ko oho da ya yi da haƙƙin da yake kansa, ko kuma jin da za ta riƙa yi na cewa tana bayar da dukiyarta kan abin da bai zama wajibi a kanta ba".
.
A Ƙur'ani dai wajen maganar Maryam AS babarta ta fadi cewa "Namiji ba kamar mace ba ne" wato ta wajen ƙarfi, jimiri da tsaro, ga abubuwan da suka shafi zuciya, wadanda suke da alaƙa da saurin fushi, damuwa, sakaci da mantuwa, ko shagala, su ma in aka lura muhimman abubuwa ne da muke yawan samun sabani a kai, in ma ba a yi wasa ba duka da saki kan iya kurdadowa tsakaninsu, babban dalilin da ya sa mahaifammu in sun yi wa diyoyinsu ƙanana aure ba sa bari su yi nesa da su kenan, sukansa ido a duk ma'amalolinsu sai sun sami shekara tare da su suna cikin gandu, in sun tabbatar da za su iya riƙe gidan kafin su sake su.
.
Abin da yake faruwa shi ne: Sau tari namijin yana so ne macen ta riƙa gudanar da al'amuranta kamar yadda shi kansa yake, in ya gaya mata magana yana son ta aikata daidai ba tare da kuskure ba, kuma a lokacin da ya buƙata, wanda hakan dabi'ar namiji ce, in har ba a sami abin da ya nema ba babu ko shakka za a sami rashin jituwa, wasu fada za su yi, wasu batanci, wasu ma har yakan kai ga bulala, ita kuwa macen tana buƙatar maigidan ya riƙa zama a gida, yana tarairayarta yana yi mata magana mai dadi, wannan shi ne galibin abin da matan suke buƙata ba wai yawan jima'i ba, in har hakan ba ta samu ba, sai ka ga ana kai ruwa rana, ba za ta kula da ƙoƙarin da mijin yake yi na kawo ababan masarufi ba, wadanda nemosu shi ne wajibinsa, ita tana kallon kasancewarsa a gida kawai, da sanyaya mata rai, cikin sauƙi za ta ce aurensa bai da amfani, ko ta nemi fita.
.
Shi bai son kuskure, ita kuma ba ta son yawon da yake yi don kasuwanci, ko mauludin wani waliyi, ko wa'azin ƙasa wanda zai shafe kwanaki, komai dimbin amfanuwar da mutane za su yi da shi bai dame ta kamar cutuwar da take yi ita kadai ba, amma fahimtar kowa a dabi'arsa za ta rage manyan matsalolin da muke samu a aure, ita ta fahimci cewa shi namiji ne ta riƙa yankan masa uzuri a kowani lokaci, shi kuma ya fahimci cewa ita mace ce rauninnan na matantaka yana tare da ita dole a yi haƙuri, sai ka ga an dade ba a sami rigima ba, galibin ma'auratan da ka ji su shuru sun fahimci junansu ne, ba wai babu sabani ne a tsakaninsu ba.
.
Ƙaunar Baki Ba Ta Isa
Tabbas ƙauna takan taimaka wajen tsare danshin soyayya a tsakanin ma'aurata na tsawon lokaci. Sai dai tambayar da za a nemi amsarta a nan ita ce "Wace iriyar soyayyar?" Kar ka yi mamakin wannan tambayar, domin duk mun san cewa duk lagwadar soyayyar da aka sha kafin aure takan ƙafe nan da nan da zarar an ɗaura aure da wata 3-4. Wani sa'in ma ko kaiwa hakan ba a yi, da yawa in na tambayi mata dalilin rabuwa da mazajensu sai ka ji sun ce "Wallahi na yi nadamar aurensa da na yi, da a ce na san haka yake wallahi ba zan aure shi ba" kenan wannan zaman fahimtar junan da bata wa juna lokaci da aka yi ta yi ba su da wani amfani don ba sa ba mace dama ta san namiji a haƙiƙaninsa, haka kuma namijin bai iya sanin mace a haƙiƙaninta sai an yi aure, wannan duk sha'awa ce kawai da za ta lullube namijin ya yi ta sakin baki yana fadin ƙarya da gaskiya.
.
Ko sha'awar da takan lullube macen na son jin daddadar maganarsa wace ko bayan aure za ta yi ta tsammanin dole haka abin zai ci gaba, duk kuma wani sabani da aka samu to raguwar soyayyar ce, tun ban yi wayau ba na sha jin uwayena suna cewa "In aka yi aure soyayya kuma ta ƙare saura haƙuri" kenan an fassarata da sha'awa ne, kuma an riga an biya ta, soyayya ta gaskiya tana buƙatar fahimtar juna, da sauƙaƙa wa masoyi a komai, gami da yi wa juna hanzari, namiji ya fahimci shi namiji ne kuma wace take tare da shi ya gane cewa ba namiji ba ce, haka ita ma macen.
.
A tsakankanin namiji da mace akwai bambaci ta wurin magana, mace kan so a yi ta hira, shi kuma ba kowani lokaci yake son magana ba, takan iya yin tunanin abin dake wakana yanzu ne kawai, shi kuma har da sakamakon abin da zai iya faruwa, yana da saurin fahimtar abu, wani sa'in ita ma haka amma a baibai, tana da saurin daukar mataki kafin tabbatar da abu, shi ba haka yake ba, tana da saurin yarda in zuciyarta ta gamsu da abu, yakan so ya yi bincike tukun, ta fi kallon kyawun abu, ya fi kallon amincinsa, tana da hazaƙa wurin duba abubuwan da suke buƙata, shi kuma abin da za a kashe a kansu, to duk lokacin da aka yi gangaci wajen rashin fahimtar juna bisa waɗannan dabi'o'i akan sha wahala ba 'yar ƙarama ba, ko a kai matsayin da ba wani mai fahimtar dan uwansa kuma.

Post a Comment

0 Comments