Tsakure: Mazaunin wannnan maƙala shi ne nazari kan yadda mawaƙan Ƙ21 suke baddala waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau
zuwa waƙoƙin zamani na kiɗan fiyano, shi ya sa ma aka
yi mata take da ‘Hankaka Mai Da Ɗan
Wani Naka’.
An kawo tarihin rayuwa da gwagwarmayar da Sa’in Makafin Zazzau ya yi da kuma shahararsa
a fagen waƙa
duk da kasancewarsa makaho mabaraci. Binciken ya kawo mawaƙan da suka bi salon waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau tun
daga makafi almajiransa da kuma mawaƙan zamani da suka baddala waƙoƙin nasa suka gwama su da kiɗan fiyano. Maƙalar ta gwama tsakanin gwanjo
da orijina inda aka fito da waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau waɗanda mawaƙan Ƙ21 irin su Adam A. Zango
(Ba ni bayanin Zango) da Funkiest Malam (Ga Lemu) da Sadi Sidi Sharifai (Direba
Makaho, Idi Wanzami, Bayanin Naira) da sauransu.
Hankaka Mai da Ɗan Wani Naka: Waƙoƙin
Salisu Sa’in Makafin Zazzau a Bakin Mawaƙan Ƙarni
na 21
Na
Abdullahi Mujaheed
Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna
Waya: +2348069299109, +2348156747550
i-mel:mujaheedabdullahi@gmail. com
1. 0 Gabatarwa
Salisu Abdullahi Sa’in Makafin Zazzau
ɗaya
ne daga cikin shahararrun mabarata kuma mawaƙa
a ƙasar Hausa. Cikin
barar ne yake gudanar da waƙoƙinsa waɗanda
suke ƙunshe
da saƙonni
daban-daban a ɓangarori na rayuwa
da suka haɗa da siyasa da zamantakewa
da nishaɗi da faɗakarwa
da yabo da zuga da sauransu. Bisa wannan shahara tasa ne wasu mawaƙan zamani na Ƙ21 suka tasirantu daga waƙoƙin nasa, suke bin salo da
tsari da karin muryar waƙoƙin Sa’in suna gudanar da nasu
waƙoƙin na kiɗan
fiyano. Domin haka wannan maƙala
ta nazarci fasalce-fasalcen hankakancin da mawaƙan fiyano a Ƙ21 suka yi wa wasu daga cikin
waƙoƙin nasa suka mayar da su nasu
ɗauke da kiɗan
fiyano. A wasu wuraren mawaƙan
salo da tsari suke ɗauka
na waƙoƙin Sa’in, a wasu wuraren kuwa
har da jigon suke juyawa ya zamo nasu. Waƙoƙin da aka bi ta kansu wajen
fito da wannan fasali su ne ‘Bayanin Naira’ da ‘Bayanin Ƙira’ da ‘Idi Wanzami’ ‘Direba
Makaho’.
2. 0 Tuna Baya Shi Ne Roƙo
Duk da cewa
ba a yi wani aiki kacokan a kan Salisu Sa’in Makafin Zazzau da waƙoƙinsa
ba illa aikin Mujaheed (2017), manazarta kamar su Karofi (1980:160-203) da Ummar
(2002:35) da Tukur (1985) sun yi tsokaci game da Salisu
Sa’in Makafi da waƙoƙinsa ta fuskoki mabambanta.
Karofi (1980:160-203) ya mai
da hankali ne ga mabarata jimillarsu, ya nazarci tasirinsu da gudummuwarsu ga adabin
Hausa, cikin mabaratan da ya bayar da misalai a kansu ne har da Sa’in Makafin Zazzau
da waƙoƙinsa uku. Shi kuwa Tukur
(1985), ya nuna cewa mawaƙan
baka ciki har da Sa’in Makafin Zazzau sun bayar da gagarumar gudummuwa wajen yayata
manufofin gwamnati. Sai dai bai taɓo
wani abu game da waƙoƙin Sa’in ba, illa abin da
ya sha masa kai na manufofin gwamnati cikin waƙoƙin nasa. Kamar yadda Ummar (2002:35), ya mayar da hankali ga nazarin illolin
waƙoƙin bara na yau, amma duk da haka sai da ya nuna cewa
waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau cike suke da faɗakarwa da nishaɗantarwa. Yayin da ita kuma Karima
(2012), ta nazarci yadda mawaƙan
baka ke ambaton abinci ne a waƙoƙinsu da kuma irin salon da
suke amfani da shi wajen rattaɓo
nason abincin Hausawa cikin waƙoƙin nasu, sai nazarin nata
ya yi gam-da-katar ɗin
kawo waƙa
ɗaya ta Salisu Sa’in Makafin
Zazzau cikin misalai wato waƙar
‘Bayanin Wulli”. Ita kuwa wannan maƙala
ta fito da yadda mawaƙan
zamani na Ƙ21suke
baddala waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau cikin
waƙoƙinsu na kiɗan
fiyano.
3. 0 Sa’in Makafin Zazzau Da Waƙoƙinsa
An
haifi Sa’in Makafin Zazzau Salisu Abdullahi Rafin-Mai-Baka, cikin shekarar 1933
a ƙasar
Daura, daga bisani kuma shi da iyayensa suka baro ƙasar Daura da ƙuruciyarsa, suka koma Rafin-Mai-Baka.
Iyayen Salisu Sa’in Makafin Zazzau ba makafi ba ne. Ya sami lalurar makanta ne tun
yana jariri, lokacin bai wuce kwana arba’in a duniya ba, sakamakon cutar ƙyanda da ya yi fama da ita.
Sa’i ya yi karatun addinin Musulunci gwargwado a lokacin ƙuruciyarsa, sai dai bai samu
yin karatun boko ba (Hira da Haruna Galadima, ranar 20/12/2012).
A
wajajen shekarun 1960 Salisu Sa’in Makafin Zazzau ya koma Zariya da zama. Maigidansa
a Zariya shi ne Sa’i Ibrahim ɗan
Tofa (wato mutumin Tofa ne kamar yadda sunansa ya nuna) kuma daga gare shi ne Salisu
ya sami sarautar ‘Sa’in Makafi’ bayan rasuwar Sa’i Ibrahim ɗan
Tofa. A birnin Zariya, Salisu Sa’in Makafin Zazzau ya zauna a yankin da ake kira
‘Marmara’ cikin ‘Unguwar Juma’ ta birnin Zariya daga bisani
ya koma garin Kaduna da zama a farkon shekerun 1970. Sa’in Makafin Zazzau ya kasance
ma’abocin hulɗa da gwamnati domin
yana waƙoƙin farfaganda da yaɗa
manufofin gwamnati. (Hira da Muhammad Lawal Salisu, ranar 10/03/2013). Bayan shahararsa, kusan kowane lungu na arewacin
ƙasar
nan da kudu-maso-yamma babu jihar da Salisu Sa’in Makafin Zazzau bai sanya ƙafarsa ba. Wani lokacin yakan
yi tafiye-tafiyen ne a karan kansa, wani lokacin kuma gayyatar sa ake yi.
Salisu
Sa’in Makafin Zazzau ya auri mata shida tsawon rayuwarsa ta duniya. Amma kamar yadda
addinin Musulunci ya gindaya cewa namiji ɗaya
zai iya auren mata huɗu
ne kacal a lokaci guda, saboda haka Sa’in Makafin Zazzau bai zauna da waɗannan
mata lokaci guda ba. Ana hasashen cewa mata uku ne ya zauna da su lokaci guda, wato
Rabi da Amina da kuma Yalwa. Shi kansa Sa’in Makafin Zazzau ya jaddada haka da bakinsa
cikin waƙarsa,
inda ya ambaci waɗannan
mata uku daga cikin matan nasa.
Ga
abin da yake cewa;
“Kai mai mata ukku,
Rabi da
Amina,
Saboda hakan nan
Zuwa kuma Yalwa
In ka samu Nairar ba su,
Kai ka zauna kai hakuri,
('Y/ Amshi: An mana sabon
launi). ”
Ta yiwu lokacin da ya yi wannan waƙa, matansa uku ne, bai riga
ya yi ta huɗun ba. Dangane da ‘ya’ya
kuwa, Salisu Sa’in Makafin Zazzau ya haifi ’ya’ya goma sha uku, cikin goma sha ukun
nan, goma maza ne, uku mata. Sa’annan cikin wannan adadi, uku suna raye, goma kuma
sun rasu a mabambantan lokuta.
An
naɗa Salisu Abdullahi a matsayin
Sa’in Makafin Zazzau a shekarar 1968, lokacin Sarkin Makafi Umaru. Kafin naɗin,
ana kiran sa ‘Wazirin Samari’ ne. A ƙarƙashinsa kuma, akwai yaransa da suke masa amshi waɗanda
kowannensu da sarautarsa. Salisu Sa’in Makafin Zazzau ya rasu ne a watan 8, na shekarar
1988 (Hira da Sarkin Makafin Zazzau Ahmadu Tijjani Hassan, ranar 03/03/2013).
Sa’in
Makafin Zazzau bai gaji waƙa
ba, walau ta wajen mahaifi ko mahaifiyarsa, basira ce Allah (SWT) ya ba shi daga
waƙoki
na bara, har ya kai ga shahara ga waƙoƙi na fadaƙarwa da isar da saƙonnin gwamnati ga al’umma.
(Hira da Haruna Galadima, ranar 20/12/2012). Ya fara waƙa ne tun yana Kano, musamman
a lokacin da yake tare da ubangidansa Magaji na Ɗambatta, wanda aka ƙaddara shi ne ya koya masa
waƙoƙin baran. Har ila yau, ya
daɗe yana ‘yan waƙoƙinsa na bara, kafin shahararsa
a wajajen shekarun 1965/1966 sakamakon rikicin juyin mulkin da ya kunno kai a lokacin.
Wannan ne ya haifar da waƙarsa
ta “Soja” wadda ta shahara sosai kuma ita aka fara sanyawa a gidan rediyo domin
fadaƙar
da jama’a dangane da muhimmancin haɗa
kan ƙasa.
(Hira da Haruna Galadima, ranar 20/12/2012).
Tun
daga wannan lokaci, duk abin da ya tusgo daga manufofin gwamnati da take buƙatar a jawo hankalin jama’a,
ko a gargaɗe su, sai Sa’in Makafin
Zazzau ya shirya waƙa
a kan abin, ya riƙa
gudanar da ita yayin da yake bararsa a matsayinsa na makaho. Idan ‘yan jarida suka
ji shi, sai su ɗauka
su watsa a gidajen rediyo. Da abin ya ci gaba, tun yana yi a matsayin sa-kai, har
ya kasance gwamnati ko hukumomin gwamnati musamman Hukumar Watsa Labarai da Gidan
Rediyon Tarayya na Kaduna, suka riƙa
neman sa domin ya tsara waƙoƙi game da wasu manufofin gwamnati,
idan sun kunno kai ana buƙatar
a yi wa jama’a farfaganda har manufofin suka sami gindin zama a zuƙatan jama’a. Alalmisali, sauyin
kuɗi da aka yi a shekarar 1973
Sa’in Makafin Zazzau ya yi waƙar
‘An mana Sabon Launi’ wadda ta yi matuƙar tasiri ga manufar da ake
son cim ma ga al’umma. Haka kuma ya yi waƙa game da sauya tuƙi daga dama zuwa hagu, duk
a waɗannan shekaru. Shi
kuma a ɓangarensa, Sa’in Makafin
Zazzau yakan sami abin masarufi daga hukumomin da suka ɗauki
alhakin waƙokin.
Wannan ya haifar da dangantaka kyakkyawa irin ta cuɗan-ni-in-cuɗe-ka
tsakanin Sa’in Makafin Zazzau da gwamnati.
Wajen
shirya waƙoƙinsa, Salisu Sa’in Makafin
Zazzau da yaransa, sukan zauna ne su tsara yadda amshinsu zai kasance, bayan tattaro
bayanai game da abin da kayan cikin waƙokin
za su ƙunsa,
kafin su rera kowace waƙa.
Daga nan ne, sai su rera a duk lokacin da ake buƙata. A wasu lokutan kuma,
yakan ƙiri
waƙa
nan take idan buƙatar
hakan ta taso. Dangane da waƙoƙinsa na farfaganda kuwa, gidajen
rediyo su ne suke kasancewa mahaɗa
tsakaninsa da gwamnati. Ta hanyar su ne yake samun bayanai game da abin da duk ake
buƙatar
ya waƙe. (Hira da Haruna Galadima, ranar 20/12/2012).
Kafin
rasuwarsa, ya yi waƙoƙi da dama, kuma ta hanyar
waƙoƙin ne, yake samun duk abin
masarufin da yake buƙata
a rayuwarsa ta yau da kullum. Haka kuma ta hanyar waƙa ya sadu da jama’a daban-daban.
Kuma ya sami shahara da ɗaukaka
a duniya fiye da sauran takwarorinsa makafi. Wannan ya tabbatar da faɗin
malam Bahaushe cewa ‘nakasa ba kasawa ba ce’.
Sa’in
Makafin Zazzau yana daga cikin rukunin mawaƙan baka masu shirya waƙoƙinsu cikin ƙungiya inda yake a matsayin
jagora, sannan da yaransa waɗanda
su ne suke a matsayin ‘yan amshi. A tsarin ƙungiyar Salisu Sa’i, akwai
shi kansa a matsayin jagora, sai kuma ‘yan amshinsa, waɗanɗa
dukkansu makafi ne. Kowanne daga cikin ‘yan amshin nasa da matsayinsa kamar haka:
-
Abdu, shi ne Sarkin Yaƙi
-
Hudu, shi ne Ciroma
-
Haruna, shi ne Madawaki.
Sa’in Makafin Zazzau da bakinsa ya jaddada
haka inda yake cewa:
“Ciroma Hudu,
Da Sarkin Yaƙi Abdu,
Da Madawaki Haruna,
Da ni kuma Sa’i Makaho…,
(‘Y/Amshi: An mana sabon
launi. )”
Haka
wannan ƙungiya
take zagayawa tana waƙe-waƙenta na bara a kasuwanni da
wurare na musamman da sukan kai ziyara, ko idan an gayyace su. (Hira da Haruna Galadima, ranar 20/12/2012).
Wasu
daga cikin waƙoƙinsa sun haɗa
da ‘Waƙar Yabo’
ta 1 da ta 2 da ‘Kun Ji Barar Zamani’ da ‘Sa’idu Mai Mota’ da ‘Mahammadu
ɗan Shu’aibu’
da ‘Alhaji Baƙo Zuntu’
da ‘Mainasara Daga Allah’ da ‘Shehu Kwasau Zazzau’ da ‘Gai da Aminu Haruna’ da ‘Alhaji Baital Lahi’ da ‘Don Mu Wadata
Ƙasarmu’ da ‘A Daina
Shan Ƙwaya’ da ‘Yan Ƙasa
Mu Yi Ɗa’a’ da ‘Ba Ni Bayanin Naira’ da
‘An Mana Sabon Launi’ da ‘Zamani Na Rajista’ da ‘Mu Duba Sunayenmu’ da kuma ‘Gyara Ƙasa Sai Soja’. Sai kuma‘Bayanin
Wulli’ da ‘Idi Wanzami’ da‘Bayanin Ƙira’ da ‘da ‘Direba
Makaho’ da sauransu.
4. 0 Mawaƙan Da Suka Bi Salon Sa’in Makafin Zazzau
Karofi (1980:160-203), ya bayyana cewa:
“Malam Salisu shahararren mabaraci ne a ƙasar nan kuma Allah yi masa basira mai yawa, duk da
Allah ya yi shi makaho. Shi ya sa ma kashi sittin cikin ɗari na mabarata makafi ɗalibansa ne kuma akasari shi ne ya ƙirƙiri waƙoƙin da suke rerawa,
sai dai ‘yan canje-canjen da ba a rasa ba.
Misalin ɗaliban nasa su ne,
Malam Ibrahim Kunkunna da Malam Ibrahim Sakkwato da Malam Audu Sakkwato. ”
Wannan
haka yake, domin kuwa ko bayan rasuwar Salisu Sa’in Makafin Zazzau, an sami wasu
makafin da suka cigaba da rera wasu fitattun waƙoƙinsa musamman a ƙasar Kano da Daura. Misali
Ɗahiru
Daura da Tafida Makaho sun shahara da waƙoƙin Idi Wanzami da Direba Makaho,
har ma akasarin mutanen da suka san waƙoƙin a yanzu sun fi alaƙanta su a matsayin maƙirƙiran na asali maimakon Sa’i
Makaho, ciki kuwa har da mawaƙan
zamani da suka kwaikwayi waɗannan
waƙoƙi. A yanzu an wayi gari da
zarar an ji waƙoƙi irin su ‘Direba Makaho’ ko ‘Bayanin Naira’ ko ‘Idi Wanzami’
sai ‘yan zamani su fara tunanin Sadi Sidi Sharifai ko Ɗan Ibro . Ko kuma a fara tunanin
Ɗahiru
Daura ko Tafida Makaho ne maƙirƙiran waƙoƙin na asali (musamman a ƙasar Kano da Daura) alhali
kuwa ainihin maƙirƙirin waɗannan
waƙoƙi shi ne Salisu Sa’in Makafin
Zazzau kamar yadda Karofi (1980:
160-203) ya tabbatar. Sa’annan ga mawaƙan zamani nan birjik kamar
su Adam A. Zango (Ba ni bayanin Zango)
da Funkiest Malam (Ga Lemu) da Sadi Sidi
Sharifai (Bayanin Girki, Idi Wanzami, Bayanin
Naira) da sauransu. Waɗannan
mawaƙa
da ma wasu da dama, sun tasirantu da salon waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau suna
waƙoƙinsu na kiɗan
fiyano a zamanance (Mujaheed 2017: 165).
5. 0 Baddala Waƙoƙin
Sa’in Makafin Zazzau Zuwa Waƙoƙin Fiyano a Ƙ21
Tun
kafin tasirin wasu baƙin
al’ummomi kiɗa da waƙa ya samu gindin zama a al’ummar
Hausawa. Daga baya ne zamani ya shigo da wasu abubuwa cikin waɗannan
waƙoƙi na Hausawa (Gusau, 2012). An bayyana cewa a kafa ta waƙoƙin samartaka ne zamani ya
shigo da tasirinsa a cikin waƙoƙin Hausa, wato waƙoƙin da samari da ‘yammata ke yi (Gusau, 2008 : 345-360). Waƙoƙin zamani sun kunno kai gadan-gadan
ne a tsakiyar ƙarni
na ashirin (Ƙ20) zuwa ƙarshensa , wato bayan yaƙin basasa, lokacin da ƙabilun kudanci Nijeriya suka
yawaita (ɓarko)
arewa da kuma yawaitar otel-otel a manyan garuruwan arewa. Tun a wajen shekara ta
1980 aka sami wasu makaɗa
waɗanda suka dinga rera waƙoƙin Hausa ta amfani da kayan
kiɗa baƙi. An sami makaɗa
irin su Bala Miller da Fumi Adams da Audu Kwarisko da Sa’adu Bori da sauransu. (Gusau, 2008: 348). A wajen shekara ta 1995 wasu
Hausawa, musamman samari, suka fara tsara waƙa a rubuce sannan su samar
mata rauji, su kuma rera ta amfani da kayan
kiɗa baƙi. Wasu su haddace waƙoƙin da ka, wasu su
ajiye su a kasa-kasai da CD – CD. Zuwa shekara ta 2000 jama’a ta fara sabawa da
waɗannan kaɗe-kaɗe
na fiyano da ake tsarmawa a cikin fina-finai. (Gusau, 2008:349). Yawancin irin waɗannan
mawaƙa
idan suka zo maimaita rera waƙoƙin suna bin rerawa ta farko ne daga CD wanda aka riga aka
naɗa a sitidiyo, abin da ake kira ‘Mamming’
da Ingilishi. Wannan kai tsaye tasiri ne baƙo wanda Hausawa suka samo
shi daga tsari na naɗar
waƙoƙin Turawa. Ga abin da Alan
Waƙa
yake cewa game da wannan:
“Baituka
na zo in yi da kiɗa na Nasaranci,
Kun ga na yi gurmi da kiɗa
na Yahudanci,
Baituka da sauti da salon
masu Hausanci,
Yakana na taso in gwada da
badangalci,
Ibrahimu za mu taya godiyar
Allah. ”
(Aminu ALA: Waƙar
Farfesa Malumfashi).
Bisa irin wannan tasiri ne mawaƙan zamani suka riƙa ɗaukar
waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau suna
rerawa a sitidiyo ta amfani da fiyano da sauran nau’o’in kayan kiɗan
zamani. A yawancin lokuta, karin murya da saƙon iri ɗaya
ne da na waƙoƙin Sa’in na asali, sai dai
sukan bi wasu salo na zamani wajen tsara waƙar da kuma gwama su da kiɗa
na zamani.
6. 0 Tsakanin Gwanjo Da Orijina
Sa’in Makafin Zazzau ba ya gwama waƙoƙinsa da amo na kiɗa,
su kuwa mawaƙan
Ƙ21
da suka ari waƙoƙinsa suka baddala zuwa nasu,
sun gwama da kiɗan
fiyano. Waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau
kuwa suna da tsarin amshin Shata ne, wato amshi ɗaya
ne na gindin waƙa
ake ba yara, ba sa ƙarawa
ba sa ragewa, komai ya ce gindin za su ci gaba da maimaitawa har sai ya gaji ya
ba su wani gindin wata waƙar
ta daban. Irin wanna salon amshi shi yake fitar da sunan galibin waƙoƙinsa. Misali, ‘Ba Ni Bayanin Ƙira’ da
‘Ba Ni Bayanin Wulli’ da ‘Gyara Ƙasa Sai Soja’ da
sauransu. A irin wannan tsarin, ‘yan amshin suna maimaita gindin waƙar ne a kai, a kai, ba tare
da sun numfasa ba har yakan zamo tamkar amshin ne kiɗan
waƙoƙin kasancewar ba su da kiɗa.
Abin
da za mu yi a nan, shi ne fayyace fasali biyu na ire-iren waƙoƙin Ƙ21 da suka tusgo daga waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau. Fasali
na farko shi ne ɗaukar
salo da tsari na waƙoƙin nasa domin gabatar da wasu
waƙoƙin zamani na kiɗan
fiyano masu ƙunshe
da saƙonni
mabambanta da waƙoƙin Sa’in. Mawaƙan da suka bi wannan salo
su ne Adam A. Zango da Billy O, a waƙarsu
ta ‘Bayanin Zango’ da kuma Babawo da Habibullahi
a waƙarsu
ta ‘Bayanin Gausi’ sai kuma Funkiest Malam
a galibin waƙoƙinsa.
Abin
lura shi ne, su waɗannan
mawaƙan
zamani sun bi salo da tsari na wasu waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau ne
kamar su ‘Bayanin Ƙira’
da ‘Bayanin Naira’ suka ari karin murya
da tsari da salon waƙoƙin amma sai suka ƙunsa saƙonninsu daidai da zamanin
da ake ciki da kuma manufar da suke so su isar ta amfani da kiɗan
fiyano.
A
waƙar
‘Bayanin Naira’, Sa’in Makafin Zazzau
ya faɗakar da jama’a kan
muhimmancin a tashi a nemi naira don a huce takaici sannan ya tsarma jigon nishaɗantarwa
a waƙar
inda ya dubi alaƙar
maigida da uwargidansa in yana da naira. A cewarsa, naira ita ce:
Abin sha'awa ga mutane
Abin riƙo a ji daɗi
Mai sa farin ciki ga mutane
Mai wanke zuciya sai Naira
Kai! Ku ji zancen Naira
Ku nemi Naira huce-takaici
Mai sa zaman jin daɗi
Ko a wurin zance, da iyali
In kana da Naira
In kai tari mai ƙarfi
Matarka na barci ta tashi
"Mai gida wane aikin za a yi?"
Saboda tsoron kada ka sake ta
('Y/ Amshi: Ba ni bayanin Naira)
A waƙar ‘Bayanin Ƙira’
kuwa, Sa’in Makafin Zazzau ya nishaɗantar
da mutane ne ta hanyar ƙulla
saƙonsa
mai labarta wa maisauraronsa yadda a matsayinsu na makafi shi da yaransa suka je
koyon ƙira,
wani mai ido kuma ya lallaɓo
kallon su, inda a ƙoƙarin makaho na ɗora
ƙarfe
a kan maƙera,
kawai sai ya ɗora kan mai idon nan
da yake kallon su tun da bai yi magana an ji shi ba, shi kuma makaho bai shafa ya
ji shi ba:
Ƙarfe da wuta
Ni kuma babu ido a gare ni
Da nakai magana na biyu
Ashe da mai ido ya raɓe
Ganin ƙira ga makaho
Ina "ku ja sawunku"
Shi bai magana ba na ji shi
Ni kuma ban shafa ba na ji shi
Da na ɗauko ƙarfe
Na jefa za in yi ƙira
Ca nake na sa a maƙera
Ashe a kan cinyarsa na ɗora
Ya ji zahi ya maka ihu
Na ji tsoro na maka ihu
Gaba ɗaya duk muka miƙe
Muka tashi da rumfar ƙira
Ƙirar tun daga nan ta waste
(Ba ni bayanin ƙira)
Irin fasalin waɗannan
waƙoƙi ne wasu mawaƙan zamani suka ɗauka
suka tsara waƙoƙinsu na kiɗan
fiyano. Alal misali, Babawo da Habibullahi sun ɗauki
amshin ‘Ba ni Bayanin Ƙira/Naira’
sun tsara waƙarsu
mai amshin ‘Ba ni Bayanin Gausi’. Yayin
da waƙoƙin ‘Bayanin Naira’ da ‘Bayanin Ƙira’
suke ƙunshe
da saƙonni
na faɗakarwa da nishaɗantarwa,
ita wannan waƙa
ta ‘Bayanin Gausi’ tana bayyana wa maisauare
irin darajoji ne da karamomi ta Shehu Ibrahim Inyasi, sa’annan sun yi amfani da
kiɗan fiyano amma karin muryar
iri ɗaya ne da waƙar asali. Hankaka mai da ɗan
wani naka! Misali:
Jagora: Subahanallahi
'Y/ Amshi: Ba ni bayanin Gausi
Jagora: Subahanallahi
'Y/ Amshi: Ba ni bayanin Gausi
Jagora: Ba ni bayanin Gausi
'Y/ Amshi: Ba ni bayanin Gausi
Jagora: Shin wai wane ne Barhama?
'Y/ Amshi: Ba ni bayanin Gausi
Jagora: Wasu duk sun san shi
'Y/ Amshi: Ba ni bayanin Gausi
Jagora: Wasu ko ba su san komai ba
'Y/ Amshi: Ba ni bayanin Gausi
(Waƙar Bayanin Gausi)
Su ma Adam A. Zango da Billy O, sun baddala
amshin waƙar
‘Bayanin Naira/Ƙira’
ne suka bi salo da tsarinta suka shirya waƙarsu ta ‘Bayanin Zango’. Sai dai kamar yadda aka
yi bayani a sama, yayin da waƙoƙin ‘Bayanin Naira/Ƙira’ Suke kimshe da saƙonnin
nishaɗi da faɗakarwa,
ita wannan waƙa
Adam A. Zango ya shirya ta ne musamman domin huce haushi a kan ce masa arne da ake
yi sakamakon wasu ɗabi’u
nasa a harkarsa ta fina-finan Hausa. Ga abin da yake cewa:
Ku saurara,
Ku ji zancen Malam Zango,
Zan fara bayani,
To ku saurare
ni,
To yau dai zan ɓaro
ta,
Subahanallahi,
Walhamdullahi
La’ilaha illallahu,
Muhammadu Ya Rasulillahi,
Sunana Adamu Zango,
Ɗan Ibro jikan Abdu,
Ɗan Furera baban Haidar
Sannan jikan Hafsatu
Sun ce mini arne,
Malam wane ne arne?
La’ilaha ilallahu,
O! Wai ni ne arne,
Muhammadurrasulillahi,
Ni na kama ƙafa da Muhamman
Domin shi zai cece ni.
(Amshi: Ba ni bayanin
Zango).
Fasali
na biyu kuwa shi ne ɗaukar
salo da tsari da saƙonnin
waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau kai-tsaye
a sake maimaita su da kiɗan
fiyano. Sadi Sidi Sharifai shi ne mawaƙin zamani da ya fi shahara
a wannan fage. Domin kuwa, tun yana yaro ƙarami, Sadi Sidi Sharifai ma’abocin
wasa da dariya ne, akwai shi da son nishaɗi, duk lokacin
da yake cikin sha’aninsa yana ɗaukar muryoyin
mutane daban-daban yana kwatanta su kuma su yi tamkar na wanda yake kwaikwayo. Ko
da a wajen waƙa ne yana
yin amfani da muryar mawaƙi ya dinga
rera waƙa irin ta
mawaƙin ba tare
da samun wani bambanci sosai ba. Yakan ɗauki waƙar Shata ya dinga rera ta da tsarin
muryar da Shata ke amfani da ita a waƙar (Suleiman, 2013:20-21). Da irin wannan ƙwarewa ce Sadi Sidi Sharifai ya
hankakantar da waƙoƙin ‘Idi Wanzami’ da ‘Direba Makaho’
da ‘Bayanin Naira’ cikin muryar ɗan
Ibro. A waɗannan waƙoƙi, salo da tsari da saƙonnin duk iri ɗaya
ne da waƙoƙin na asali, sai dai abin
da ba a rasa ba na tsarma wasu ƙananan
saƙonnin
da kuma uwa-uba rera su da kiɗan
fiyano. Hankaka mai da ɗan
wani naka!
Waƙar Idi Wanzami:
Kamar
yadda aka bayyana a sama, waƙar
‘Idi Wanzami’ tana daga cikin waƙoƙin da Sadi Sidi Sharifai ya
hankakantar. Domin fitar da aya cikin tsakuwa, ga abin da Sa’in Makafin Zazzau ke
cewa;
Idi Wanzami,
Ka ji yana yin aski,
Kamar ana fiɗar ɗan taure.
Idi Wanzami,
Wai wanzaman kirki,
Suna yawo da zabira,
Idi Wanzami,
Sai ya zubo askarsa a sanho.
Askarsa guda huɗu,
Kowace aska ga sunanta:
Ɗaya ‘Kura kya ci da gashi’,
Ɗaya ‘Ladanki na jikinki’,
Akwai wata ‘Wa aka samu?’,
Sannan ga ‘Кare dangi’.
Amma ita ‘Кare dangi’,
Idan ta fito daga sanho,
Rannan mutum dubu sa ƙare.
Askar Wanzamin,
Ka ji ma sunanta:
Walfa’ilati kurfan,
Summa walan luran,
Ɗaya Kurjama’u Jamila,
Kurjama’u Jamila
Wannan ba a biya mata lada,
Da kanta ma ta ɗiba.
(Sa’in Makafin Zazzau: Idi Wanzami)
Shi
kuwa Sadi Sidi Sharifai a tasa waƙar
ta ‘Idi Wanzami’ ya kawaikwayi salon Sa’in
Makafin Zazzau ne kaitsaye ya gabatar da tasa waƙar. Misali:
Idi Wanzami,
Ka ji yana yin aski,
Kamar ana fiɗar ɗan taure.
Idi Wanzami,
Aska da tausayi shi babu,
Wai wanzaman kirki,
Suna yawo da zabira,
Idi Wanzami,
Sai ya zubo askarsa a sanho.
Askarsa guda huɗu,
Kowace aska ga sunanta:
Ɗaya ‘Kura kya ci da gashi’,
Ɗaya ‘Ladanki na jikinki’,
Akwai wata ‘Wa aka samu?’,
Sannan ga ‘Кare dangi’.
Subahanallahi,
Amma ita ‘Кare dangi’,
Idan ta fito daga sanho,
Rannan mutum dubu sa ƙare.
Sannan Wanzaman kirki,
Suna yawo da ƙaho,
Idi Wanzami,
Bakin garwa aka fafe,
Majaujawa ita ce ‘yar kamu,
Idi Wanzami ga shegen ƙarfi a gurinsa,
In yay i ƙahonsa ya
ƙare,
Idan ya je zuƙa,
Sai ya fito da autar hanji.
Askar Idi Wanzami,
Ka ji ma sunanta:
Walfa’ilati kurfan,
Summa walan luran,
Sai Kurjama’u Jamila,
Kurjama’u Jamila
Wannan ba a biya mata lada,
Da kanta ma ta ɗib,
Subahanallahi!
(Sadi Sidi Sharifai: Idi Wanzami)
Idan
aka kwatanta ɗiyan waƙoƙin da suka gabata na Sa’in
Makafin Zazzau da na Sadi Sidi Sharifai, saƙon da salon da tsarin duk
iri ɗaya ne. Hatta kayan
cikin waƙar
da bayanin askar wanzami da yadda yake askinsa duk Sadi ya kwaso ne daga waƙar Sa’in Makafin Zazzau kaitsaye
ya mayar da su nasa. Hankaka mai da ɗan
wani naka!
Waƙar Bayanin Naira:
Waƙar ‘Bayanin Naira’, ta Sa’in Makafin Zazzau ta ƙunshi faɗakarwa
ne ga jama’a a tashi a nemi naira da kuma ɗan
abin da ba a rasa ba na nishaɗantarwa
inda ya dubi musaman alaƙar
maigida da uwargidansa game da sha’anin naira. Sa’in ya ce:
Abin sha'awa ga mutane
Abin riƙo a ji daɗi
Mai sa farin ciki ga mutane
Mai wanke zuciya sai Naira
Kai! Ku ji zancen Naira
Ku nemi Naira huce-takaici
Mai sa zaman jin daɗi
Ko a wurin zance, da iyali
In kana da Naira
In kai tari mai ƙarfi
Matarka na barci ta tashi
"Mai gida wane aikin za a yi?"
Saboda tsoron kada ka sake ta
(Sa’in Makafin Zazzau: Ba ni bayanin Naira)
Shi
ma Sadi Sidi Sharifai a tasa waƙar
ta ‘Bayanin Naira’ ya hankakantar da waƙar Sa’in Makafin Zazzau ya
bayyana darajar naira wajen inganta alaƙa tsakanin mace da namiji.
A cewarsa:
Idan na ce yarinya,
Kin san babu ido a gare ni,
Sai ta ce kai Malam,
Don Allah manta da makanta,
Masu idon ma me suka fi ka,
Ga ka ɗan siririn yaro,
Kuma ga ka da kyawun fuska,
Kuma ga ka da damman naira,
Don Allah manta da makanta,
(Sadi Sidi Sharifai: Ba ni bayanin Naira)
Domin
sake fito da saƙon
fili, a wani wajen kuma sai Sadi Sidi Sharifai ya sake jaddada batun, inda ya ce:
Amma in ba ni da naira,
Ko da mummuna ce,
In na ce ina ƙaunarta,
Sai ta koma gefe,
Ta ce La’ilaha illallahu,
Yanzu ka dubi kamata,
Sai ka ce ni ce matarka,
Ko babu maza a garin nan,
Ni me zan da makaho
Yaya zan yi in auri makaho,
(Sadi Sidi Sharifai: Ba ni bayanin Naira)
Saboda
haka, saƙon
da salon duk iri ɗaya
ne da waƙar
ta asali, sai dai ‘yan ragi da ƙari
da sauran kwaskwarima da ba a rasa ba a waƙar ta biyu wadda Sadi Sidi
Sharifai ya yi.
Waƙar Direba Makaho:
Ita waƙar ‘Direba Makaho’ tun daga farkonta har ƙarshenta, labari ne na yadda
makaho da abokan aikinsa (‘yan amshi) suka tafi Legas domin su kama sana’ar tuƙi, saboda barar da suke yi
ta dame su. Da wannan salo ne mawaƙin
ya labarta yadda suka nemi mota da inda aka ba su motar da kuma yadda lodinsu ya
kasance. Sa’in Makafin Zazzau ya buɗe
waƙarsa
ne kamar haka:
Ina labari?
Direba makaho,
Yaya aka fara?
Wai sai ni direba makaho,
Karen motanmu makaho,
Ɗan kamashonmu makaho,
Kwandastan namu makaho,
Akawun namu makaho,
Duk babu mai ido a cikinmu.
Haba ‘yan amshi,
Kun san halin mota,
Masu ido ma ya suka ƙare,
Balle mota da makaho,
Sannan ba mu da ɗan
jagora.
(Sa’in Makafin Zazzau: Direba Makaho)
Shi
ma Sadi Sidi Sharifai a tasa waƙar
ya fara ne da bayyana yadda tuƙin
motar tasu zai kasance tun daga direba da akawu da kwandasta da karen mato duk makafi
ne, kamar dai yadda Sa’in Makafin Zazzau ɗin
ya gabatar. Misali:
Ina labari?
Ƙaƙa muka ƙare?
Ƙaƙa muka ƙare?
Ahalallah, Subahanallahi,
Faifai na direba makaho,
Karen motanmu makaho,
Ɗan kamashonmu makaho,
Kwandastan namu makaho,
Akawun namu makaho,
Duk babu mai ido a cikinmu,
Haba ‘yan amshi.
(Sadi Sidi Sharifai: Direba Makaho)
A
dunƙule,
wannan ya nuna a fili cewa hankakancin da mawaƙan zamani suke yi wa waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau suna
da fasalce-fasalce iri biyu, yayin da a kaso na farko wasu mawaƙan suke ɗaukar
salo da tsarin waƙoƙin nasa su gabatar da nasu
waƙoƙin da mabambanta jigogi, shi
Sadi Sidi Sharifai kaitsaye yake ɗaukar
waƙoƙin ya sake rera su da kiɗan
fiyano.
7. 0 Kammalawa
Duk da irin shahara da waƙoƙin
Salisu Sa’in Makafin Zazzau suka yi, a yanzu an wayi gari da
zarar an ji waƙoƙi irin su ‘Direba Makaho’ ko ‘Bayanin Naira’ ko ‘Idi Wanzami’
sai ‘yan zamani su fara tunanin Sadi Sidi Sharifai ko Ɗan Ibro. Ko kuma a fara tunanin
Ɗahiru
Daura ko Tafida Makaho ne maƙirƙiran waƙoƙin na asali (musamman a ƙasar Kano da Daura) alhali
kuwa ainihin maƙirƙirin waɗannan
waƙoƙi shi ne Salisu Sa’in Makafin
Zazzau. Ga kuma mawaƙan
zamani nan birjik irin su Adam A. Zango (Ba
ni bayanin Zango) da Funkiest Malam (Ga
Lemu) da sauransu. Waɗannan
mawaƙa
da ma wasu da dama, sun tasirantu da salon waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau suna
waƙoƙinsu na kiɗan
fiyano a zamanance. Saboda haka, aka rarrabe tsakanin gwanjo da orijina, inda aka
bayyana tarihin rayuwar Sa’in Makafin Zazzau da shahararsa a fagen waƙa. Sannan kuma aka fayyace
fasali biyu na irin hankakancin da mawaƙan Ƙ21 suka yi wa wasu waƙoƙin nasa.
0 Comments
Rubuta tsokaci.