Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Ƙara Aure // 24: Ƙimar Mutum



To bare masu kuɗi waɗanda matsuguni ko suturu da abincin da za a ci ba matsala ne ba gare su... Su ya kamata su zama a sahun farko wajen gusar da matsalolin yawaitar mata a duniya, tun da mun fahimci cewa talauci na ƙara yawaitar mata, ko dai waɗanda suke gidajen aurensu a sako su, ko na gidan su rasa manema...

Zan Ƙara Aure // 24: Ƙimar Mutum

Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah

Wasu abubuwan ana musu kallon suna da jiɓi da al'ada ne kawai, amma a zahiri ba sa rasa nasaba da addini. In kuma aka kalle su a hankalce sai a ga cewa tabbas sun dace da yanayin da muka tsinci kammu a ciki, misali yawaitar 'ya'ya mata da hanyoyin da ya kamata a bi don fuskantar wannan ƙalu-balen. Ba dai zai yuwu ba uban yarinya ya fita da ita kwararo-kwararo yana neman wanda zai aure ta ba, yadda masu arziƙi ba sa a jiye kuɗi na masamman wai ko wani zai zo neman taimako don zai yi auren fari bare kuma ƙarawa. In muka lura da kyau duk wani runtsin da muka tsinci kanmu a ciki mutum 3 ya kamata su haɗa ƙarfi da ƙarfe ko harshe da harsashi don magance mana su.
Wato a dunƙule dai:-

1) Shugabannin al'umma masu ruwa da tsaki a duk lamuran al'umma, waɗanda su ake sauraren su saka doka don hana aikata wasu abubuwan ko su ɗauke ta a lokacin da ya dace, kama daga Sarkin Musulmi da duk sarakunan yanka waɗanda ake girmamawa har zuwa mai unguwan yanki da 'yan mutane ƙalilan ne suka san girmansa. Waɗannan shugabanni ko na ce sarakuna su ne suke tara al'umma don a nazarci matsalolin da suka fuskanto ta ko ma suke addabar ta, a kuma haɗa bayanai don ƙoƙarin kawar da ita kacokan ko rage ƙarfinta.

2) Limamai na duk masallatan Juma'a, waɗanda za su hau mumbari su ja Ƙur'ani da hadisi, su gaya wa mutane gaskiya. Su ne fitilu a tsakanin al'umma. Da su ake raɗa wa yaron da aka haifo suna, kuma su ɗin ne dai suke yi wa mamacin da za a yi bankwana da shi salla. Sukan ja hakulan jama'a har imani ya sauka, hankali ya natsu ya yi tunani mai amfani don gano shiriya da binta ko ƙaurace mata. To daga waɗannan manyan limaman har zuwa ƙanana na gefen shaguna a bakin kasuwa waɗanda ba za su iya yin nisa da kayan sana'arsu duk dai masu faɗi a ji ne.

3) Sai Attajirammu kuma, waɗanda gina gidaje ko rushe su ba wata tsiya ba ce a rayuwarsu, tsabar kuɗi wuri na gugar wuri suna da su, kuma suna kashewa ta hanya mai kyau ko mugunyar hanya. Su da manyan 'yan kasuwa waɗanda Allah ne kaɗai ya san abin da suke samu a duk safiya daga shagunansu dake jahohi daban-daban. Waɗannan mutanen tabbas suna da girma a idanun jama'a kuma ana girmama su, don ba al'ummar da za ta ci gaba ba tare da waɗannan mutane 3 a gaba ba. To daga su har 'yan tireda da musu yawo da kayan talla a hannu.

Mu da su duk mun sani cewa matsalolin yawaitar mata ba ƙananan matsaloli ba ne don su ne ke saurin haifar da zinace-zinace a tsakankanin al'umma. Babbar hanyar da za a taƙaita yawaitar wannan bala'in ita ce aure 'yan matan a kan kari. Duk Bahaushe ya san haka. To da yake babba jagora ne wanda shi ne sauran al'umma kan kalla su yi koyi da shi, to ba shakka duk alamun dattijantaka da sarauta, ko malanta da sani ko wadata da arziki suna nan ne lokacin da mutum zai auri mace sama da ɗaya. Duk mutumin da ake girmamawa cikin mutunennan uku in aka ji cewa yana da mata ɗaya ce rak sai ka ji ya sure maka.

Shi ya sa makusantansu ba sa yadda sai sun tilasta su sun ƙara aure. Jagoranci bai yiwuwa sai da ɗaukar nauyin al'umma. In ka auri mata 4 a matsayinka na shugaban jama'a, ko ba ka buɗi baki ka yi magana ba, wasu daga cikin mabiya za su yi koyi da kai, amma yadda za ka ce wa talakawanka su ƙara aure don matan da ba su sami miji ba su ma su auru alhali matarka guda, to bare malamai da limamai waɗanda suke yin wa'azi har a maƙabartu wurin da imani ke sauka wa kowa. Ba zai yiwu ka ce Allah ya ce Annabi ya ce ba game da ƙarin aure alhali matarka guda. Dole kai ma ka zama abin koyi.

To bare masu kuɗi waɗanda matsuguni ko suturu da abincin da za a ci ba matsala ne ba gare su... Su ya kamata su zama a sahun farko wajen gusar da matsalolin yawaitar mata a duniya, tun da mun fahimci cewa talauci na ƙara yawaitar mata, ko dai waɗanda suke gidajen aurensu a sako su, ko na gidan su rasa manema... A taƙaice dai girma kowane irin ne a ƙasar Hausa babban dalili ne na ƙara aure. Ko ba ka yi kwaɗayin auren ba a ƙashin kanka al'ummar da ke zagaye da kai ba za su bar ka haka kanƙin goro ba, dole ka ƙara aure.

Post a Comment

0 Comments