Ticker

6/recent/ticker-posts

Namijin Dare: Hulɗar Soyayya Tsakanin Ɗan Adam Da Iska


  
Al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki. Tarihi ya nuna wannan hulɗa ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Bincike a kan addinin Bahaushe na gargajiya ya samu karɓuwa sosai ga masana al’adun Hausawa. A yau, goshin ƙarni na ashirin da ɗaya Hausawa sun buɗe wani sabon shafi na hulɗa da iskoki. A da, ’yan bori da bokaye da malaman tsibbu su ke cin karensu ba babbaka a kan sha’anin hulɗa da iskoki. Yanzu an sami rukunin wasu malaman addini da suke hulɗa da iskoki ta hanyar ruƙiyya[1], domin warkar da cututtukan da…

Namijin Dare: Hulɗar Soyayya Tsakanin Ɗan Adam Da Iska


Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
È08035605024, email: yagobir@yahoo.co.uk


1.0             Gabatarwa
Al’ummar Hausawa sun daɗe suna hulɗa da iskoki. Tarihi ya nuna wannan hulɗa ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Bincike a kan addinin Bahaushe na gargajiya ya samu karɓuwa sosai ga masana al’adun Hausawa. A yau, goshin ƙarni na ashirin da ɗaya Hausawa sun buɗe wani sabon shafi na hulɗa da iskoki. A da, ’yan bori da bokaye da malaman tsibbu su ke cin karensu ba babbaka a kan sha’anin hulɗa da iskoki. Yanzu an sami rukunin wasu malaman addini da suke hulɗa da iskoki ta hanyar ruƙiyya[2], domin warkar da cututtukan da suka shafi iskoki. Daga cikin waɗannan cututtukan da suka shafi iskoki akwai abin da Hausawa ke kira, ‘Namijin Dare’ ko ‘Macen Dare’, wato hulɗar soyayya da ke gudana tsakanin ɗan Adam da iskoki (Tsakanin mace mutum da aljani namji ko tsakanin aljana da mutum namiji). Gano yadda Hausawa ke warkar da wannan cuta shi ne maƙasudin wannan maƙala.

2.0     Waiwaye
Hausawa na cewa ‘waiwaye adon tafiya.’ Bisa ga haka, akwai bukatar waiwaye don mu ji matsayin iskoki a idon Bahaushe. Masana al’adun Hausawa irin su Greenberg, J. (1946), Besmer, F.E. (1973), Ibrahim S.M. (1982), Bunza, A.M. (1990), Ismaila, H.A (1991), Iliyasu, G. (2000) da sauransu Greenberg, J. (1946), Besmer, F.E. (1973), Ibrahim S.M. (1982), Bunza, A.M. (1990), Ismaila, H.A (1991), Iliyasu, G. (2000) da sauransu, sun yi rubuce-rubuce da dama a kan iskoki da matsayinsu a rayuwar Bahaushe. Sun tabbatar da imanin Bahaushe a kan samuwar iskoki, duk da yake ba ya ganin su amma ya yi imani da samuwar su da kuma kasancewar su buwayayyi, masu ban tsoro, masu ƙarfi a kan mutane kuma masu iya cuta musu. Za a iya fahintar haka tun daga sunayen da Bahaushe ke kiran su da shi. Ya kira su ‘iskoki’ ne domin ba ya ganin su kamar yadda ba ya ganin iskan da muke shaƙa. Yana kiran su ‘masu abu’ don suna nuna isa ga duk abin da suke nufi aikatawa ko suke bukata. Yana kiran su ‘mutantani’ saboda sun yi tarayya da mutane ta ɓangaren jinsi da hali. Wato suna da jinsin maza da mata, suna aure da haihuwa da cin abinci da sauransu.[3] Kodayake imanin Bahaushe a da, ya yarda cewa, iskoki ba su mutuwa, amma yanzu malaman rukiyya, (Iliyasu: 2000) sun tabbatar da cewa iskoki suna mutuwa. Sai dai suna da tsawon rayuwa ba kamar ta mutane ba. Ta fuskar yadda Bahaushe ya fahinci iskoki kuwa, ’yan bori na ganin cewa akwai farare da baƙaƙe. Fararen su ne masu sauƙin kai da daɗin hulɗa, saɓanin waɗanda ake kira baƙaƙe masu mugunta da sharri. Haka su ma masu ruƙiyya, sun kasa iskoki gida biyu dangane da mu’amala da su. Waɗanda ’yan bori ke kira farare, su masu ruƙiyya ke kira Musulmi, Kafirai kuwa su ne baƙaƙe.

Bayan bayyanar Musulunci a ƙasar Hausa, Bahaushe ya fara amfani da sunaye irin su ‘Aljani’ da Ira’izzai, da Rafani da Shaiɗan, da sauransu. Dalili kuwa saboda waɗannan sunaye sun zo a cikin nassin Alƙur’ani da Hadisin Manzon Allah (SAW). Saboda haka a yau, Bahaushe ya fi amfani da waɗannan sunayen, saboda sun fi kusanci da addininsa na Musulunci.

3.0     Wuraren Zaman Iskoki
Kamar yadda kowane abu mai rai ko maras rai yake da muhalli ko wurin zama, haka su ma iskoki suke da nasu muhalli. Bahaushe ya yi imani cewa iskokin ƙasar Hausa ana samun su a ko’ina a ƙasar Hausa. Duk da haka, akan same su a wurare ayyanannu kamar kan duwatsu ko gindin manyan itatuwa kamar su itacen kuka da tsamiya da gawo da gamji da sauransu. Akan kuma same su a dokar daji ko a cikin ruwa da gidajen tururuwa da faƙo da suri (ƙunƙuwa) da sauransu. A cikin gari kuwa, ana samun su a mararrabar hanya da kangon gida da maƙabarta da juji (wurin zuba shara) da sauransu. A cikin gida kuwa ana samun su a ban-ɗaki da tsakar gida da ƙofar ɗaki da turakun dawaki da sauransu. A jikin mutane kuwa suna zama a ko’ina cikin jiki, amma sun fi zama a cikin ƙwaƙwalwa. Wannan yana da nasaba da kiran su ‘ƙwanƙwammai.’ Duk waɗannan wuraren da Hausawa ke riya cewa mazaunin iskoki ne, mafi yawansu malaman ruƙiyya da Musulunci sun tabbatar da haka.[4] Wannan tabbatarwar na daga cikin abubuwan da suka ƙara ƙaimin imanin Bahaushe da iskoki, kuma ya ƙarfafa ci gaba da hulɗa da su, duk da samun wayewar kai na zamani da bunƙasar ilimin addini Musulunci.


4.0     Dalilan Hulɗa Tsakanin Iskoki da Mutane
Bayanan da suka gabata, za su iya gamsar da mu cewa lalle akwai hulɗa tsakanin iskoki da Hausawa. Masana al’adun Hausawa sun fitar da dalilai uku da ke sa iskoki hulɗa da mutune. Dalilan kuwa su ne; ƙiyayya da tsoro da kuma ƙauna[5]. Idan mutum ya cuta wa iskoki ta hanyar aibata wa 'ya'yansu ko tsofafinsu ko ƙona gidansu ko kwarara wa gidansu ruwan zafi, da sauransu, to iskokin kan ƙulla ƙiyayya da wannan mutum, su ɗauke shi abokin gabar su, kuma su ɗauki niyyar ramuwa gare shi. Wannan zai kai ga iskokin su shige shi, su raunana masa lafiyar jiki.

Haka kuma a dalilin tsoro mai tsanani, irin wanda ke mantar da mutum tuna Allah, to lokacin iskoki na samun sauƙin shiga jikinsa, musamman idan  mutum ba ya yi wa Allah ɗa’a. Haƙiƙa rashin yi wa Allah ɗa'a yana ƙara sa mutum jin tsoro mai firgitarwa, kuma yana sa shaiɗan ya ƙara masa jin tsoronsa, sai tsoron ya yi tasiri a kansa, kamar faɗar Allah (S.WT):
                        Wancan, shaiɗan ne kawai yake tsoratar da masoyansa.
                         To, kada ku ji tsoronsa, ku ji tsorona, idan kun kasance
masu imani.” (Alkur'ani sura 3: aya 175) (Fassarar Shaikh Mahmud Gummi)

Sai dalili na uku, wanda kuma shi ne bagiren wannan takarda, wato dalilin ƙauna ko soyayya. Idan iskoki na sha’awar surar jikin mutum ko ɗabi’unsa da sauransu sai su nemi yin hulɗa da shi. A wajen irin wannan hulɗar, iskan kan bayyana cikin kamannun mutane kyawawa ta yadda ba su tsoratar da abokin hulɗarsu. Wani lokaci sukan bayyana cikin surar mutumin da aka sani. Hulɗar ƙauna ta kasu kashi biyu: Akwai hulɗa tsakanin jinsi ɗaya, wato kamar a samu hulɗa tsakanin namijin iska da namijin ɗan Adam, ko hulɗa tsakanin macen iska da macen ’yar Adam. Akwai kuma hulɗar ƙauna ta bambancin jinsi. Wato tsakanin namijin iska da macen ’yar Adam ko macen iska da namijin ɗan Adam. Daga cikin irin wannan hulɗa ake samun namijin dare ko macen dare.


5.0   Ma’anar Namijin Dare/Macen Dare
Namijin dare ko Macen dare wani nau’in iska ne daga cikin iskoki wanda ke auren mace ‘yar Adam yana saduwa da ita (jima’i), ko kuma iska mace ta auri mutum ɗan Adam ta rinƙa saduwa da shi ta hanyar mafarki ko a farke, musamman cikin dare. Irin wannan saduwa tana haddasa cututtuka ga jiki ko zuciyar ɗan Adam. Malaman ruƙiyya na kiran irin wannan iska da sunan ‘Aljanin/Aljanar soyayya’.  

6.0  Aure Tsakanin Aljani da Mutum
Malaman addinin Musulunci, musamman waɗanda suka zurfafa a cikin sha’anin ruƙiyya da aikin asibiti, sun tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan matsala ta aure tsakanin aljani da ɗan Adam.[6] Abin da ya tabbata ga malaman ruƙiyya shi ne auren yana yiyuwa, amma bai halatta ba a shari’a. Wato Namijin iska na iya saduwa da mace ’yar Adam, ko ɗan Adam ya sadu da macen iska, kuma su samu jin daɗi irin wanda ake ji na saduwa (jima’i), amma shari’a ta yi ƙyama ga aikata haka. Saboda an tambayi Imam Malik ɗan Anas cewa wani aljani ya zo yana neman a ba shi wata bazawara aure? Sai Imam Malik ya ce, “Ban ga illa ba ga haka, sai dai ina ƙyamar idan macen ta yi ciki aka tambaye ta, waye mijinki? Ta ce ‘wani aljani’. To wannan zai haifar da ɓarna da fasadi a cikin Musulunci.”[7] 
7.0     Dalilan Shigar Namijin Dare/Macen Dare
Daga cikin dalilan da kan jawo shigar Namijin dare ga mace su ne:
·        Tsiraitar da al'aura ga mace ko namiji cikin gida, kamar mace ta tsiraita zindir ko ta sanya tufafi maras kauri, kuma ta zo ta tsaya gaban madubi, tana mamakin kyawon kanta, idan aka yi rashin sa’a aljanin soyayya yana kusa, sai ya yi sha’awar ta, kuma son ta ya kama shi sai ya shige ta[8].
·        Idan mace ko namiji suna kwantawa a tsiraice a waje, misali lokacin bazara, kuma ba su ambaci sunan Allah ba, Namijin dare ko macen dare kan yi sha’awarsu, kuma su shige su.
·        Idan mace ko namiji na shiga ban-ɗaki wajen wanka a tsiraice, ko shiga ruwa (gulbi ko kududdufi) wajen wanka a tsiraice kuma ba a ambaci sunan Allah ba. Namijin dare ko macen dare kan samu sauƙin shigarsu kuma ya aure ta ko ta aure shi.
·        Idan mace na bayyanar da ƙawarta a titi ko bainar jama’a, Namijin dare na iya kai mata hari.
·        Idan mutum na saduwa da iyali ba tare da ambaton sunan Allah ba, shaiɗanin aljani kan samu damar shiga jikinsa ko jikin iyalin.
·        Idan mutum ya sadu da iyalinsa alhali tana haila namijin dare zai riga shi gare ta. Idan ta samu ciki sai abin da aka samu ya zama Mukhannas, wato ɗan aljani[9].
·        Idan mace ko namiji na kwana shi kaɗai a ɗaki.

8.0     Alamomin Shigar Namijin Dare ga Mace ’Yar Adam
Akwai alamomi da masu ruƙiyya suka fitar wajen gano Namijin dare ga mace. Alamomin kuwa kashi biyu ne; akwai bayyanannun alamomi, akwai kuma ɓoyayyu.

8.1     Bayyanannun Alamomi
Bayyanannun alamomi a nan na nufin ciwon gaɓoɓin jiki ko na zuciya, waɗanda suka bayyana a cikin maras lafiya.
i)                   Ta riƙa jin matsanancin ciwon kai kullum.
ii)                 Ta riƙa samun yawan faɗuwar gaba.
iii)              Ta riƙa jin ba ta son zama gidan miji, ko jin ɓacin rai wanda babu dalili.
iv)               Ta riƙa jin ciwon kwankwaso ko ƙuncin ƙirji.
v)                 Ta riƙa jin ciwon mara a kai-a kai.
vi)               Ta riƙa fama da rashin isasshen barci ko yawan farkawa cikin dare,    kuma cikin tsoro.
vii)            Rashin tsayar da miji idan ba ta da aure, kuma ga mabiɗa na zuwa      wurinta.
viii)          Daɗewa ba ta yi aure ba idan budurwa ce.
ix)               Yawan mutuwar aure, ta kasa tsayawa ga miji ɗaya. Idan aka ga haka ga       mace, ƙari da wasu alamomi, to ana tuhumar tana tare da namijin dare
x)                 Ta zama mai wabi (yawan mutuwar ‘ya’ya tun suna ƙanana tsakanin shekara ɗaya zuwa biyar).
xi)               Yawaitar samun ɓari (zubewar ciki), daga wata ɗaya zuwa uku[10].
xii)            Yawan zubar jinin haila a kai - a kai, musamman lokacin da namijin dare     zai sadu da ita.
xiii)          Rashin haihuwa.

8.2          Ɓoyayyun Alamomi
Ɓoyayyun alamomi a nan na nufin abubuwan da ke wakana cikin duniyar mafarki, da za a iya gane namijin dare ga mace, kamar mace:
i)       ta riƙa ganin wani yana saduwa da ita a cikin mafarki.
ii)     ta riƙa ganin ana ba ta jarirai, kamar ta haihu a cikin mafarki.
iii)  ta riƙa ganin kamar ana taron buki a cikin mafarki.
iv)   ta riƙa mafarkin tana cikin ruwan teku ko gulbi.
v)     ta riƙa ganin wasu dabbobi a cikin barcinta, kamar raƙumi, ko sa, ko       macizai.

9.0    Alamomin Macen Dare ga Namiji Ɗan Adam
Kamar yadda mace ’yar Adam ke fama da namijin dare haka shi ma namiji ɗan Adam ke fama da macen dare. Kuma alamomin da ake gane haka kusan duk ɗaya ne da na mace, illa wasu ’yan bambance-bambance da ake samu na halitta. Saboda haka, shi ma alamomin sa kashi biyu suke wato bayyanannun alamomi da ɓoyayyun alamomi:

9.1          Bayyanannun Alamomi
Bayyanannun alamomi a nan na nufin ciwon gaɓoɓin jiki ko na zuciya. Idan mutum ɗan Adam yana fama da cutar iskan dare zai haifar da samuwar waɗannan cututtuka:
            i)         Mutuwar mazakuta ko rauninta.(Rashin tashin gaban namiji.
            ii)        Rashin son aure ko jinkirinsa, na tsawon shekaru masu yawa.
            iii)       Rashin sha’awar mace.
            iv)       Saurin samun biyan buƙata wajen jima’i.
v)        Rashin haihuwa.
9.2   Ɓoyayyun Alamomi
Ɓoyayyun alamomi a nan na nufin abubuwan da ke wakana cikin duniyar mafarki, da za a iya gane macen dare ga namiji, kamar namiji:
i)                   ya riƙa ganin yana saduwa da wata mata a cikin mafarki.
ii)                 Ya riƙa ganin kamar ana taron buki a cikin mafarki.
iii)              ya riƙa mafarkin yana cikin ruwan rafi ko tabki.
iv)               ya riƙa ganin wasu dabbobi a cikin barcinsa, kamar raƙumi, ko sa, ko macizai.
Waɗannan alamomin da aka zayyana ba su kaɗai ne ba, illa su suka fi bayyana ga mai wannan matsalar. Sannan kuma ba sai duka alamomin sun taru sun bayyana a lokaci guda ba. Wani lokaci ɗaya daga cikin alamomin zai iya gamsar da malaman da ke wannan aikin su tabbatar da cewa lalle akwai namijin dare ko macen dare ga maras lafiya.

10.0        Hanyoyin Warkar da Cutar Namijin Dare ko Macen Dare
Hausawa na cewa: “Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.” Hanyoyin da Hausawa kan bi wajen warkar da cutar namijin dare ko macen dare sun kasu kashi biyu; akwai hanyar girka da ’yan bori kan bi da kuma hanyar ruƙiyya da malaman ruƙiyya ke bi.

10.1        Hanyar Girka
Girka wata hidima ce da ‘yan bori ke gudanarwa ga marar lafiyar da suke ganin ta iskoki ce. Gudanar da aikin girka ga marar lafiya na nufin ko dai iskokin su fita daga jikinsa ya samu lafiya, ko kuma a girke su ga jikinsa su zauna cikin salama, ba tare da cutar da shi ba, amma tare da yarda da bin ƙa’idojin da za su ɗora masa ga rayuwarsa. Bayanin yadda ake gudanar da girka ya gabata a wasu ayyuka.[11]

10.2  Hanyar Ruƙiyya
Hanyoyin da malaman ruƙiyya suke bi suna warkar da cutar namijin dare ko macen dare na da matakai guda uku.
1.                  Mataki na farko shi ne ƙoƙarin gano alamomin da aka yi bayani na bayyanar namijin dare ko macen dare. Idan alamomin sun tabbata, za su gudanar da ruƙiyya ga maras lafiya kamar yadda sukan yi ga sauran cututtukan da suka shafi iskoki[12].
2.                  Mataki na biyu shi ne gabatar da wasu ayyuka da karance-karance ga maras lafiya. Malam Usamah[13], daga daga cikin malaman ruƙiyya ya tabbatar da cewa, namijin dare ko aljanin soyayya shi ne mafi haɗari da sharri cikin nau’o’in aljannu. Kuma mafi tsanani ga riƙe jikin ɗan Adam. Bisa ga haka ya fitar da wasu matakai na musamman, waɗanda idan mai wannan cutar ya kula da su, to insha Allah zai rabu da matsalar gaba ɗaya. matakan su ne:
i)          Ya riƙa sauraren ko karanta Surar baƙara, da Surar Nur, da ayoyin Suratul Yusuf  (23-43), da wasu rukunin ayoyin da ake kira ‘ayoyin  ƙuna da azaba’ da ‘ayoyin tsoro’ da ‘ayoyin Muhibba’, kullum sau uku a wuni.
ii)        A karanta Sura Ar-Rahman  a cikin ruwan da ke isa wankan tsarki, sannan a rubuta surar a allo  a wanke rubutun cikin ruwan, sai a yi wanka da ruwan ranar Juma’a. Za a yi wankan a wurin da babu najasa.
iii)     Maras lafiya zai kula da shafe mahaɗar gaɓɓan jikinsa duka da turaren Almisk baƙi, lokacin shiga barci.
iv)      Maras lafiya zai kula da azkar, wato addu’o’in tsari na safe da yamma, da na shiga gida da na fita gida, da na shiga barci da sauransu, domin samun cikakkiyar nasara.
3.                  Bayan ɗaukar waɗannan matakai na sama, to dole ne maras lafiya ya yi ƙoƙarin kiyaye dokokin Allah da nisantar saɓon Allah. Allah ya kare mu, amin.      

11.0        Naɗewa
Hulɗa tsakanin Iskoki da Hausawa daɗaɗɗiya ce tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Har bayan samun wayewar kai da bayyanar addinin Musulunci a ƙasar Hausa, wannan hulɗa ta ci gaba da wanzuwa. Daga cikin irin wannan hulɗar akwai ta ƙiyayya da ta tsoro da kuma ta ƙauna. Hulɗar ƙauna tsakanin iskoki da mutane ita ke haifar da namijin dare ko macen dare. Wannan ya nuna a fili cewa, iskoki na iya auren ’yan Adam kuma suna sha’awar su.  Kodayake ’yan bori da malaman ruƙiyya sun tabbatar da yiyuwar saduwa (jima’i) tsakanin ɗan Adam da iska, amma Shari’ar Musulunci ta ƙyamaci irin wannan saduwar, saboda illolin da ke tattare da shi da kuma cutarwa ga ’yan Adam. Suturce jiki da yawan karanta Alƙur’ani da addu’o’i su ke magance matsalar namijin dare ko macen dare. Da fatan Allah ya kare mu.




MANAZARTA
                                 
Shiga domin kallon manazarta...

[1] Don karin bayani a kan ma’anar ruƙiyya da yadda ake yin ta,  dubi:  Gobir, Y.A (2002) “Iskoki a Idon ‘Yan bori da Masu Ruƙiyya”. Kundin digiri na biyu, Jami’ar Usamu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
[2] Don karin bayani a kan ma’anar ruƙiyya da yadda ake yin ta,  dubi:  Gobir, Y.A (2002) “Iskoki a Idon ‘Yan bori da Masu Ruƙiyya”. Kundin digiri na biyu, Jami’ar Usamu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
[3] Don karin bayani sauran sunayen iskoki dubi:  lamba ta 1, da Bunza A.M. (2006)Gadon Feɗe Al’ada. TIWAL LTD.
[4]  Don ƙarin bayani dubi Aliyu Muhammad Bunza: “Magana da Iskoki ta Bakin Dokinsu”. (2004). Muƙala da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na 6 kan Nazarin Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeria, Jami’ar Bayero Kano.
[5]  Don ƙarin bayani: Dubi Aliyu Muhammad Bunza: Boruƙiyya: Tazarar Bori da Ruƙiyya a Idon Manazarta
Takardar da aka gabatar a taron tattaunawa da ƙara wa juna sani na musamman da Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami'ar Bayaro, Kano ta shirya kan "Bori" da "Ruƙiyya", ranar 19 ga Maris, 2005.
[6] Don ƙarin bayani dubi Badarud din Abdullahi Asshabli (1985) Akamul Murjaan Fi Ahkaamil Jaan. Maktabah Ibn Sina, Misra, Alƙahirah. Shafi na 77 – 89.
[7] Dubi lamba ta 7, shafi na 78.
[8] Iliyasu (2000) ya tabbatar da haka, sun yi wata mata ruƙiyya a Sakkwato, aljanin ya ce ya shige ta ne tana tsiraice bayan ta ba shi sha’awa.
[9] An yi ruƙiyya a Sakkwato ga matar da ke da wani jinjiri lagwas kamar ba ya da ƙashi a jikinsa, aljanin ya ce ɗansa ne, sai an ba shi abinsa zai fita. Da aka ce an ba shi jinjirin, cikin dare ya zo ya ɗauke shi ana barci, sai uwar ta samu lafiya.
[10] Likitoci asibitocin zamani sun tabbatar da haka. A hirar da na yi da wani ƙwararren likita Dr. Yakubu Ahmad na Asibitin Koyarwa ta Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato, ranar Alhamis 13/11/2008, ya tabbatar da cewa mafiyawan zubar cikin mata daga aljani ne.
[11] Bayanin yadda ake girka dubi: Aliyu Muhammad Bunza (1990), “Hayaki Fid Da Na Kogo”. Kundin digri na biyu (M.A.), Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano, da Gobir, Y.A (2002) “Iskoki a Idon ’Yan bori da Masu Ruƙiyya”. Kundin digiri                                  na biyu, Jami’ar Usamu Ɗanfodiyo, Sakkwato.shafi na 92.
[12] Don ƙarin bayani dubi lamba 12, Gobir, Y.A (2002) shafi na 100 – 119.
[13] Usamah Muhammad Al’iwadiy (Babu Shekara) “Alminhajil Kur’aniy Fi Ilajis Sihir Was Massis Shaidaniy”. Darul Kalimatut Tayyib. shafi na 62 -99.

Post a Comment

0 Comments