Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Abu A Yi Shi




Lokaci wani zamani ne. A hangen wasu masana wani zarafi ne da ba shi da bagiren da za a riske shi bayan an yi gaba da gaba da shi ya ba da baya. A ganin matasa, wani yayi ne da ke tashe sa’ar da aka miƙa wuya gare shi gadan-gadan. Idan aka ba shi baya ko ya ba da baya sai ya wuce kamar ruwan faƙo. A tunanin Bahaushe, komi na da lokacinsa, idan ba a yi katari da lokacinsa ba za a yi aikin banza wa kare wanka. Idan an dace da lokacinsa za a ga an yi dace tsintuwar guru a cikin  suɗi. Ashe gaskiyar masana da ke cewa, mutum uku suna cikin wahalar da ba ta da ranar hutawa. Na farko shi ne, wanda lokacin abu ya yi, ya ƙi mika kai bori ya hau, wai shi bai yarda ba sai ya gani…
Lokacin Abu A Yi Shi

Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua
Katsina, Nijeriya.


Takardar da aka gabatar a bukin ƙaddamar da Littafin Kyakkyawar Safiya Tarihin Mai Girma Sarkin Kabin Yabo Alhaji (Dr) Muhammadu Maiturare II, na Malami Umar Torankawa, Ranar Asabar 31 ga Mayu, 2014 da ƙarfe 11 na safe a ɗakin taron makarantar tunawa da Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, Sakkwato.

Gabatarwa
Lokaci wani zamani ne. A hangen wasu masana wani zarafi ne da ba shi da bagiren da za a riske shi bayan an yi gaba da gaba da shi ya ba da baya. A ganin matasa, wani yayi ne da ke tashe sa’ar da aka miƙa wuya gare shi gadan-gadan. Idan aka ba shi baya ko ya ba da baya sai ya wuce kamar ruwan faƙo. A tunanin Bahaushe, komi na da lokacinsa, idan ba a yi katari da lokacinsa ba za a yi aikin banza wa kare wanka. Idan an dace da lokacinsa za a ga an yi dace tsintuwar guru a cikin  suɗi. Ashe gaskiyar masana da ke cewa, mutum uku suna cikin wahalar da ba ta da ranar hutawa. Na farko shi ne, wanda lokacin abu ya yi, ya ƙi mika kai bori ya hau, wai shi bai yarda ba sai ya gani. Na biyu, wanda lokacin abu bai yi ba ya ce sai ya yi shi. Babban wahaltacce na uku shi ne, mai ba su shawara da su dage su sa ƙwazo, har da faɗar ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Kada in cika ku da gafara sa ba ku ga ƙaho ba, ga bakin zaren tunanina.
Na Gaba Idon Na Baya
Mutumin da ya rasa tarihi an taƙaita masa sake jiki cikin masoya, an hana masa miƙe ƙafafu cikin magabatansa. A kowace al’umma gabaci abin bege ne da tinƙaho ga mamaya baya. A addinance gabaci abin koyi ne. A ilmance wata babbar madogara ce ga na baya. A tarihance, komai saurin Laraba tana barin Talata ta wuce. Sanin irin ƙimar gabaci ya sa a tarihin duniya kowa ƙoƙari yake ya taskace gabacinsa ya zama furen kallo a kowane zamani ya rayu. Dalilin da ya sa ke nan takardun kuɗaɗen duniya ke ɗauke da hotunan magabatan ƙasar. Wasu wurare a sassaƙa surorinsu a matsayin gumaka da za a adana a gidajen tarihi. Wasu a kafa su a ƙofofin birane ko tsakiyar manyan wuraren shawagin jama’a a ji su, a gan su. Wasu a yi wa daularsu ko ƙasarsu ko garinsu ko unguwarsu suna da sunayensu. Wasu a taskace tarihinsu a adabin bakan al’ummarsu. A ci gaban zamani, yau rubutu ne babbar hanyar adana tarihin magabatanmu. A nawa gani, ya yi kusan zama tilas ga ma’ilmantarmu su tashi tsaye ganin sun taskace tarihinmu domin sanin:
Fakon Kaya Ya Fi Ban Cigiya
A tarihin duniyar baƙar fata, ba a taɓa ba Turawan mulkin mallaka mamaki ba kamar yadda aka ba su a ƙasar Hausa. Sun tarar da daulolinmu nagartattu girkakku. Sun sami mutanenmu amintattu fitattu ‘yantattu. Sun tarar da tsarinmu daidai da rayuwarmu. Sun sami ƙasarmu da addinin da ya koro su daga ƙasashensu. Sun tarar da tsarin dokokinmu da shari’armu ba su buƙatar gyaran fuska ga kowane mahaluki. Sun riske mu da ilmin da bai da ƙila-wa-ƙala kuma ba ya jin kunyar idon kowane masani. Babban abin da ya ɗaure musu kai ya ɓatar musu da ƙidaya shi ne, sun tarar da shugabanninmu ba su yarda a ci gajiyar talakka da su ba. Talakawa ba su yarda a taɓi gabacinsu ba sai dai komi taka zama ta zama. Wannan dalilai suka tilasta Turawa ɗaukar makamai na fuskantarmu da sarakunanmu gadan-gadan abubuwan da suka auku su auku.
          Jin haushin haka ya sa masanansu ke ta rubuce-rubucen izgili a kan ƙasashenmu da shugabanninmu. Wasu su ce, ba mu da tarihi. Wasu su ce, daga birai muka fara. Wasu su ce, rayuwarmu ta dabbobi ce. Wasu su ce, ba mu da tsarin shugabanci bale na siyasa da walwala, ga su nan dai. Abubuwan nan suna nan a rubuce a duniyar karatu kuma da su wasu takkwalan ‘yan boko ke cin abinci suna koyar da ‘ya’yanmu cewa kakanninmu dambalallu ne, mayaudara ne, fitinannu ne, wai don ɗai sun ƙi magana da hanci da ƙwambo da kirshe da ragama da soka alƙalami hagu zuwa dama. Wannan ita ce musibar ƙarninmu. Don haka, duk abin da zai yi fito-na-fito da ita tilas mu ba shi goyon baya. Irin wannan aiki na daga cikinsu.
 
Lokaci Ba Ya Jira
          Lokaci ya yi na a ce, a yau tarihin ƙasarmu da na magabatanmu mu muka rubuta abinmu da kanmu. Manyan sarakunan daulolinmu mu tabbata suna cikin kundayen tarihin da ‘ya’yanmu ke karatu. Al’adunmu da harshenmu da adabinmu su taskace a ɗakunan karatunmu. Yaƙe-yaƙenmu da sulhunmu da ƙaurace-ƙauracenmu da abubuwan da suka wakana a ƙasashenmu mun san su mun taskace su da alƙalaminmu. Ku dubi shigen kutsen da baƙin al’adu ke yi muna suna son su rinjayi tantagaryar sahihin tarihinmu. Yau fitattun mawaƙanmu na baka sai dai a garmahon ƙauyawa. Cimakarmu ta gargajiya sai dai a cikin wasan kwaikwayo. Tsarin suturorinmu sai a bukin daba. Uwa uba, ladabi da biyayya da muka yi wa maƙwabta fintinkau a yau ya zama rashin wayewa da rashin sanin ‘yancin kai. Fito-na-fito da hukuma, gwada tsawo da mahaifa, cin zarafin gabaci, yin ido huɗu da kunya, yi wa ƙarya cefane, baƙi ne a ƙasarmu. Wanda duk ya ba su masauki Allah Ya isa muna. Idan muka sa wa lokaci ido zai kama musu gidan haya a ƙarƙashin ‘yancin demokraɗiyya. Don haka, za mu ce:
Da Abinmu Aka Gan Mu
          Idan dai tsarin demokraɗiyya za a yi dodo-rido da shi a  yi wa tsarinmu idon marurugiya, a yi furjin mussa (mussa) da mu da sarakunanmu da shugabanninmu. To! Tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela tana da farinta. A irin tsarin sarautun ƙasashenmu, demokraɗiyya wasan yara ce. Sarakunanmu ba dodanni ba ne irin sarakunan Turai da Asiya da ƙasashen Larabawa. Kowane fanni na rayuwa yana da mai sa ido a kai. Kowace sana’a tana da jagora. Kowane jinsi yana da shugaba. Kowace fasaha tana da jagora. Kai! Hatta da naƙasassu da marasa galihu da ‘yan gudun hijira da tawagogin musiba ba a yi ko oho da su ba. Abin ban haushi, waɗanda suka saci tsarinmu, wai yau su ke da ƙima ga idon masu ilmin boko, kayansu ne na gaske namu ne jabu. Aka sace magungunanmu na asali aka bar bokaye bautar Iskoki. Aka rusa littattafan aƙida na masu jihadi, aka raya na tsibbu. Aka haramta wa maƙeranmu fasahar ƙera makamai, aka bar su da yuƙa da takubban faɗa da junansu. Aka rusa muna fasahar saƙa, aka cika mu da Osho. Haka ma tunanin kakanninmu na, in ka ci ya ƙare, in ka ba wani ya ƙaru, a yau, ya koma in ka ci ka ƙoshi, in ka ɓoye, ka daɗe kana cin abinka. Idan dai an fahince ni, to za a ga, rubuta tarihin shugabanninmu da magabatanmu wani farfaɗon tunatar da mu zancen Farfesa Ibrahim Narambaɗa Tubali ne:      
Jagora: Banza sharanin maras kare
           Sai kuwwa, sai ko wanda yak kasa
           Ya ce mishi anshi rataya
Gindi: Ya ci maza, ya kwan shina shire
            Gamda’aren Sarkin Tudu Alu

Baya Ba Ta Da Kaɗan
          A yau jihadin Mujaddadi bai cika ƙarni uku ba, har yanzu ba za a rasa tsofaffin da kakanninsu aka yi yaƙin ba. Duk da haka, Turawa sun cika shi da ƙura da ature da zantukan ɓatanci irin: Jihadin Fulani, daular Fulani, daular Usmaniyya. Masu jihadi ƙwacen mata suke yi (wato irin na ‘yan ɗaukar amarya). Mujaddadi gabanin ya rasu ya samu motsuwar hankali a kan kashe mutane da ya yi. Mujaddadi ya raba ƙasa biyu ta ɗansa da ƙanensa. Jihadin ƙabilanci ne. Domin tattalin arziki aka yi shi. Sarkin Musulmi Attahirun Amadu layar zana ya yi aka kamo shi aka kashe. Wanda duk ya ratsi ire-iren waɗannan sokiburutsu zai ga hikimar marubutanmu na gida da ke ta ƙoƙarin taskace tarihinmu domin Kabawa cewa suka yi, ba don kifin da ya wuce akan yi saba ba, don mai shirin komowa. A kakkaɓe wundin jawabinmu ina son a lura da lokaci ka da mu yi:

Saki Zari Kama Tozo
          Ga alama mun riga mun yi kamun gafiyar Ɓaidu. Take-taken da tsarin Turai ya yi wa magabatanmu na mulki da siyasa ya sagarta mu muka yi zaton jini a babe. Mun yi wa sarakunanmu da masarautunmu riƙon sakainar kashi. Mun yi wa addininmu dubin mai bisa ruwa. Muka yi wa al’adunmu kallon hadarin kaji. Ƙasarmu da yankinmu muka muzantar da su. Kaico! Wai duk irin wayonmu ya zama na banza, muka sayar da gona muka sayi kwasa. Muka sa gida kasuwa domin biyan dukiyan aure. Ni dai abin da ya fi ba ni takaici shi ne, mu sayar da jaki mu sayo mangala, kun ko san ko Buzu ya haukace ba ya sayar  da raƙumi ya sayo akala. Da gangan muka sa kanmu cikin ƙuncin da babu lada babu la’ada. A gai da Narambaɗa da ke cewa:
Jagora: Ko dauri kyawon ƙunci
           In da Musulmi ka zama
           Ana ta saka kullum
           Ana ta bautan Allah
           Ana ta samun lada
           Kun ji kyawon ƙunci
Yara: Wani ƙunci sai jaɓa
          Sai karen daji
          Sai Ƙadangare sai Tunku
Gindi: Sardauna kandaren Magajin Rafi
           Na Baciri Baban Madaye mai ban tsoro
         
Kayya! Mun riga mun shiga wannan ƙunci. Yanzu ina mafita? Ga nawa Basakkwacen tunani zan ce:
In Ba a Ɗatu da Yaro a ba shi Daddawarsa
        Sarakunanmu sun sa baki an yi biris da su. Da mu ake gama baki a ci musu mutunci saboda biyan buƙatun siyasarmu. Shugabannin addininmu an gano sirrinsu an yi musu takunkumi da Ɗangote da taliya da kujerun Umura. Ƙungiyoyin addininmu sun fi Ɗanƙwairo jiran tsammani. Limamanmu sun zama ‘yan kwangila masu wa’azi da nasiha su ne wakilan mazaɓu. An yi tsaye an raba addini da siyasa a Arewa domin bai wa maƙiya ƙarfin guiwa su karya ko babu gaɓa. Abokanin zamanmu addininsu ɗaya, siyasarsu ɗaya, yankinsu ɗaya, aƙidarsu ɗaya, da burinsu ɗaya na ganin ba mu sake tasiri a farfajiyar ƙasarmu ta gado ba. Gwannoninmu da suka hango wannan ta’asar suka riddance wa kowace irin hanya da za a yi muna kisan kashi a yi muna korar ɓarawo a ƙasarmu ta gado. Kash! Sai wasu daga cikinmu suka fifita aƙidar siyasa sama ga aƙidar Laa’ilaaHa illal Laahu. Allah ka cece mu, ka da ka bari a cuce mu.
Naɗewa
          Duk mai karatun jaridun ƙasar nan ya san Musulunci na cikin ta tsaka mai wuya. Wanda duk ke sauraren kalaman shugabanninmu ya san Musulmi sun shiga uku. Take-taken abokanin zamanmu na tarayya na a kashe mu ne a ƙona, ba na a hura wuta kowa ya ga rabonsa ba ne. In dai da demokraɗiyya muke tinƙaho ta cece mu, to, mun nuta bai wuri. In da yawan ƙuri’a muke zaton mu ƙwato haƙƙinmu, ga irin abubuwan da muke gani an riga an gama ƙidan ƙuri’u tun bara tare da ‘yan’uwanmu (da za a kashe mu tare) abin da ya rage sanarwa. Cikin siyasar BOKO HARAM an yi muna taron dangi. Rugumutsin ‘ya’yanmu na Chibok fassararsa Arewa ta koma Iraqi da Siriya. Allah Ya isa.

Post a Comment

0 Comments